Fatima Muhammed wacce akafi sani da afrah a sakamakon sunan kakarta ta wajen uba da taci nagartacciyar yarinya ce kyakkyawa hafaffiyar garin minna
Mai cikar kamala haquri juriya sune manyan halayenta na gari abin koyi sai kuma tsantsar ilmin islama da Allah ya wadata ta dashi domin tun tasowanta take kokari. Koyon addini har zuwa yanzu data mallaki hankalin kanta ta zama cikakkiyar mace domin tuni ta kammala karatunta na sakandire tana zaman jiran sakamako ne a yanzu idan akwai abinda ya ragi afrah a rayuwa to bazai wuce maraici ba domin ta dandana dacin maraici tun tana yar shekaru biyu kuma itace kadai yar da mahaifiyarta ta haifa tare da mahaifinta mal mahmud bayan rasuwar mahaifiyarta ne rikonta ya koma hannun matar babanta mama hauwa wacce a matsayinta na uwargidan mal mahmud tana da yayyi guda biyar biyu maza mansir wanda shi
ne na farko, a yanzu ma’aikaci ne a hukumar wutar lantarki, wato (NEPA).
Yana rike da babban mukami, ya yi aure har da ‘Yarsa daya, sai Kabir, shi kuma ma’aikacin banki ne, shi bai wuce watanni uku da aure ba, sai Naja’atu da Sakina, su ma duk sun yi aure. Na’ ima ce ta rage, wacce take tsarar Afrah, duk tare suka’ kammala makaranta.
Sai dai abu daya da Afrah ta rasa a gidan mahaifinta, shi ne kulawa da kowace ‘Ya take samu na uwa, domin irin rikon da Mama Hauwa ke mata, ba irin riko bane na amana.Wanda maraya ya kamata ya samu ba’a kowane mataki. Mama Hauwa na nuna bambanci Kiri-Kiri tsakanin Afrah da ‘ya’ yan ta, tana yi mata mugun riko.Ko kadan ba ta kyautata mata, rayuwa take a * gidan tamkar ba ‘yar gidan ba, duk da Malam Mahmud yana iya kokarinsa domin ganin marainiyar ‘Yarsa ta samu riko me kyau daga- Mama Hauwa.
Amma hakan ya kasa tabbata, domin Mama Hauwa ta zama tamkar tauraruwa me wutsiya, domin shi kansa Malam Mahmud din ta fi karfinsa, ta kan yi duk abinda ta ga dama ko a gaban idonsa ko a bayan idonsa.
Inna Halima wacce ita kadai ce kanwar
Malam Mahmud. Kuma ita kadai ce take iya taka ma Mama Hauwa birki akan irin mugun rikon da take ma Afrah.
Hakan ma ya sa, kusan rabin rayuwar Afrah take yi a gidan Inna Halima, domin duka ranar juma’a. Can take tafiya, sai ranar lahadi take dawowa gida, wannan dalilin ya sa Mama Hauwa da Inna Halima ba sa shiri ko kadan.
Makarantar Islamiyyar da Afrah take yi, anan kuma take koyar da Kananan yara, saboda hazakarta. Ya Sayyadinsu Habib ya maida ita Malama, a ajin haddar Kur’ani ta kananan yara, tana daukarsu gun koyon Kur’ ani da Tauhid.
Malam Habib shine mutum na farko da Afrah ta fara tsayawa da shi a matsayin masoyi, ta kuma amshi ta yin soyayyarsa, domin yarda da ta yi da irin son da yake mata na tsakani da Allah da kuma hanyar Ubangiji da yake dorata akai.
Hakan ya sa take da tabbacin céwa daga gare shi zata sami kyakkyawar rayuwa, ko ba kudi da jin dadi, to idan har akwai Allah a cikin rayuwarsu, to ya ishesu daga dukkan komai, don haka ta tsayar da zuciyarta gun mutum daya, wato Ya Sayyadinta Habibu. Yau asabar ne Afrah tana gidan Inna Halima, yau gyara take mata na gidan gaba daya. Inna Halima tana gefe a zaune, duk inda Afrah ta yi, tana bin ta da kallo, tana matukar sha’awar yarinyar da halayenta, domin duk inda ake neman yarinya me hankali wacce ta rike maraicinta, aka sami Afrah, to an wuce wajen.
Tana matukar jin dadin kasancewa da Afrah, a duk sanda ta zo gidanta. ta daina aikin komai, duk* abinda za ta yi Afrah, ta kan dauke mata, hatta girki ba ta yi, ta kan dauke mata komai.
Inna Halima na tsaka da yin wannan tunani aka bugo kofa da karfi. Musaddik ya fado cikin gidan, tamkar wanda aka jefo ba tare da sallama ba.
Inna Halima ta mike tana kallonsa
“Musaddi”. Ta Ambaci sumansa da Karfi, a yayin da Afrah ta yi saurin ja da baya, domin Karya bugeta.
..Musaddik nagartacce, kuma kyakkyawan matashi. wanda ya hada komai da za ka iya kiransa da jarumin matashi, sai dai kallo daya za ka yi masa.
Ka san ya rasa wani ginshiki na rayuwarsa, wanda ya hana shi damar da za’a kira shi da mutumin kirki, ba shi da natsuwa, da ganinsa ka ga wanda ya yi nisa a shaye-shaye, ko a yanzu ba’a cikin hayyacinsa yake ba. “Inna abinci nake so.”Ya fada da
budaddiyar murya. Inna Halima ta yi ajiyar zuciya, sannan ta kalli Afrah ta ce “Afrah, aje tsintsiyar nan, ki zubo ma yayanki abinci.” A hankali ta yi kasa da tsintsiyar, sannan a sanyaye ta wuce kicin.
Inna Halima ta maida kallonta ga Musaddik, wanda yake tsaye ya nannade kafafun wando ta ce
“Zo ka zauna
Ta nuna masa tabarmar da ke shimfide, ya wuce da takalmi da komai ya zauna akan tabarmar, ba ta damu ba, domin ba yau ya saba yin hakan ba, ta ja kujerar da ta tashi akai, ta koma ta zauna tana kallonsa.
Har zuwa lokacin da Afrah a dawo dauke da faranti cike da shinkafa da miya da ta dafa, a hankali ta aje a gabansa, sannan ta juya ta koma dauko masa ruwa, bayan ta aje ne, ta koma kan aikin da take yi. Bayan ta gaida Musaddik.
Zuciyarta cike da tsananin tausayin Musaddik da halin da yake ciki.
“Inna na kan so na zo cin abinci gidanki duk ranar sati, saboda na san Afrah tana gidan nan, ina jin dadin abincinta komai rashin gyaransa.”
Maganar Musaddik ta katse mata tunani da take yi, ta juyo da idonta tana kallon sa, a yayin da Inna Halima ta jinjina kai ta ce. “Ba kai kadai kejin dadin girkin. Afrah ba, kowa yana yabawa, tun daga kan yara har zuwa maigidan kansa.
Ya. yi dan murmushi, a yayin da yake cin abincin, ya dan waiwayi inda Afrah take wacce ke karasa shara yace, “Haka ne Inna, shi ya sa ni ma
•na kan kwaso yunwata zuwa gidanki.
Don na san idan na ce kwadayin girkinta zai dinga kaini gidansu kullum, za mu sami matsala da Mama Hauwa, don na san farantina ba zai dinga cika ba kamar yadda yake cika a gidanki.
Gaba daya suka yi murmushi, a yayin da ya* maida hankali kan cin abincinsa. Inna Halima kuma tana zuba masa ido, tana matukar tausayin Musaddik da kuma rayuwarsa wacce bata taba tsammanin zai koma haka ba. Duk tsananin kamun kansa ilimi da cikar kamalarsa.
Amma rana tsaka rayuwarsa ta koma haka. a lokacin da ya kamata ace rauwarsa ta inganta, babu wanda zai ga Musadik ya yarda ya kuma amince Musaddik din da ne, lamarin yana da matukar daure kai.
Inna Halima ta yi kasa da murya a hankali, ta fara yi masa magana “Musaddik, anya ka na ganin wannan rayuwar da ka dora ma kanka za ta kai ka ga hanya madaidaiciya, wannan wace irin rayuwa ce? Da mutuncinka da darajarka, rana tsaka duk ka kore wannan, ka koma ka na Kaskantasciyar