Responsive Advertisement

UWAR RIKO CHAPTER 3 BY FIRDAUSI

“Saura kuma in Kara jin wata magana, tunda ita ta amince idan na ji batun zuga ta, ko muguwar huduba daga wurinki to ki kuka da kanki Ya yi waje fuu! A fusace. Ladidi tasa hannu da haba ta rafka tagumi. Ta tabbata idan Malam ya fadi magana ba ya maimaitata, sai dai kawai aiki.Malam Isah a nan garin Bauchi yake zaune, yana da mata biyu da yara kusan goma.

Uwargidansa Ladidi

(mahaifiyar Sahura) na da ‘ya’ya shida duka mata, Sahura ce ‘ya ta biyar a gidan.

Sai amaryarsa Asabe tana da maza biyu, mace daya.

-Malam Isah haifaffen garin Bauchi ne, domin kuwa nan ne asalin tushensu.

Yayyen Sahura kowacco na dakin mijinta, sunada aure, sai Sahura kadai ta rage da Kanwarta.

Mahaifiyar Sahura itace mafadaciya ta kin Karawa, ga ta da kishin tsiya, ba kamar Asabe (amarya) ba, mace mai sauki kai, ga ta da kawaici da gudun magana. ‘Ya’yanta ba karamar wahala suke sha a wurin Ladidi ba, da ita kanta, don ma dai Malam Isah ya fi karfin gidansa, yana tsawatar musu, duk da dai wani abun ba a kan idonsa ake yi ba, domin ko me zai faru Asabe ba za ta taba gaya masa don kanta ba, sai dai ta lallashi yara, in ita aka yi wa haka za ta daure wa zuciyarta.

A tsawón rayuwar aurensu yau fiye da shekaru biyar, ba ta taba fuskantar matsala da mijinta

Abubakar ba.Danginsa ko iyayensa da suke zaune tare súna matukar jin dadin zama da ita, duk dadewar da suka yi Inna Luba(mahaifiyar Abubakar) ba za ta ce ga abin da Hajjo ta taba yi musu don ta bata musu rai ba, balle ga mijinta wanda kullum kyautatawa ce a tsakaninsu. Wannan shine yake Kara wa Abubakar sonta azuciyarsa, mafi yawan lokaci idan ya ganta cikin damuwa, sai ya yi kokarin raba ta da ita.

Don haka Hajjo ta samu kanta cikin rayuwar farin ciki, wadda matsala daya ce ke damunta, ita ce rashin haihuwa, kuma mijinta ya sha nuna mata ta cire wannan damuwar a, ranta, domin dai haihuwa ta Allah ce, kuma tun da danginsa ba su damu ba, me zai sa ta damu kanta? Ya nusar da ita yin addu’a, domin babu abin da ya gagari Allah.

Babbar damuwar Hajjo (kamar kowacce mace da ke da matsala irin tata) ita ce, kada a dalilin rashin haihuwarta ya ce zai karo aure, a kullum idan ta fada masa haka sai ya kwantar mata da hankali tare da nuna mata ba shi da niyyar haka matukar ba qaddara ce ta gifta ba, wadda babu yadda bawa ya iya da ita ba. “‘Ki ci gaba da addu’a, wani jinkirin alheri ne, fatanmu dai Allah ya kawo masu albarka”.

Da wannan kalamin yakan rufe zancensa, duk sadda ya ga ta damu.

Yau ma kamar kullum Hajjo ta kammala sallar la’asar tana zaune tana nazarin yadda rayuwarta ke garawa, da yadda mijinta yake lallashinta, ko kuma wani lokci ya bata rai idan ta ki lallasuwa.

Ya taba kai Kararta ga iyayenta akan matsalar, su -ma dai kamar shi, kwantar mata da hankali suka yi. A dole ta daure ta cire damuwar daga ranta ta fauwala wa Allah ikonSa, musamman da tayi la’akari da yadda ta ke zaune lafiya da shi, yana dauke mata bukatunta manya da kanana, kuma ga shi duk da wannan matsalar ba ta taba fuskantar matsin lamba daga danginsa ba.

Zuciyarta ta koma baya ta tattaro yadda aurensu ya kasance kamar wasa da farko, da yadda suka amince wa zabin iyayensu tun a zuwan Abubakar wurinta na farko.

Malam Umar mahaifin Hajjo

haifaffen garin Bauchi ne shi da iyalansa, shi ma dai kamar Malam Musa manomi. ne, duk da yana gudanar da wata sana’ar a nan cikin gari. Ko a lokacin da ya yi aure Allah bai ba.shi haihuwa da wuri ba.

Daga baya ne ya fara da Hajjo (A’isha) sai mai bi mata Sadiya, to fa daga nan haihuwa ta tsaya masa.

Akwai tazara sosai tsakanin Hajjo

Sadiya,

suna zuwa makarantar

arabiyya safe da yamma, iyayensu na kokari wurin ba su tarbiyyar da ta dace.

Zuciyar Hajjo ta gangara zuwa abin da ya faru hayan haduwarta da Abubakar har zuwa sanda maganar biki ta kankama ka’in da na’ in.

Dukkansu, iyayensu ba su tsara za a dauki wani lokaci mai tsawo ba; kuma hakan ce ta kasance, an umarci Abubakar da ya gyara wani sashe daga gidansu (kamar yadda ya taba gaya mata).

Gidan malam Musa babba ne, mai dauke da sashe har hudu. Shi yana zaune a cikin sashen farko wanda kana shigowa

• shi za ka tarar, yana Kunshe da dakuna hudu, sauran sassan guda uku ne.

Kafin lokacin bikin kuwa Abubakar ya ci gaba da zuwa wurin Hajjo lokaci zuwa lokaci, domin Kara samun fahimtar juna.

Malam Musa ya turo wakilai zuwa gidan su Hajjo, an kawo kusan komai da ake bukata.

Lokaci yana zuwa aka shiga hidindimu. An daura auren Abubakar da Hajjo a wata ranar juma’a, bayan an sauko daga masallaci.

Ranar ce ta kasance ranar farin ciki ga dukkanin bangarorin guda biyu, domin wannan ne aure na farko, kuma na ya’yan fari a kowanne gida

An ci an sha, sai dai fatan Allah ya ba da zaman, lafiya, kuma Ya mayar da kowa gidansa lafiya.

An kai amarya gidan mijinta wanda yake a nan Gangare, kafin sannan gidansu sukayi mata nasiha akan zaman aure da biyayya ga miji da iyayensa, tare da sanin ita ba mai hayaniya ba ce.

Ta tuna kukan da ta yi na rabuwa da

Iyayenta, da kuma ‘yar Kanwarta Sadiya.

Bayan an kai ta kowa ya watse, sai aka kai ta sashen iyayen miji aka damka ta amana, sannan aka wuce da ita nata sashen.

A nan ne fa tunane-tunane barkatai

•suka cika mata Kwakwalwa, bayan ta kammala koke-kokenta kamar kowace amarya, ta hakura.

Za ta iya tuna lokacin da sallamar angwaye suka katse mata sarkar tunani, ta amsa da sauri tare da faduwar gaba. Abubakar ne a gaba, abokansa na biye da shi a baya.

Ta gyara zama tare da kara rufe jikinta da mayafi. Bayan ta gaida su sai suka dora da nasiha, wadanda suka sake kashe mata jiki, sannan suka yi musu sallama suka tafi tare da yi musu fatan alkhairi.

Bayan Abubakar ya dawo daga raka su sai ya yi mata umarnin ta yi alwala, domin su mika godiyarsu wurin Allah., Suna idar da sallar suka yi addu’o’i sannan ya yi mata wasu ‘yan tambayoyi game da ibada da sauransu. Alhamdu lillahi! Kusan duka ta amsa, sai dai wanda ba za a rasa ba, domin kuwa gyara kadan ya yi mata. Ya fito da abin da abokansa suka rako shi da shi, ya tilasta mata ci. Da kyar ta ci, sannan ta wanke hannu, ya yi mata umarnin ta je ta kwanta abinta.

Shi ma ya kammala ya rufe musu

Kofa ya nufi makwanci.

Post a Comment

0 Comments