CANJIN RAYUWA CHAPTER 23 BY HALIMA A K/MASHI

jikin Dadynsu da sauki a sa musu abinci su ci. Nice ma ban riga na ci ba. Saboda na fi son abu mai ruwa da’ safe, mai kuma dumi kamar shayi. Hajiya Binta ta ce, ya fi dadi ai. Hasana sa min wainar. Allah ya rufa asiri, Suka ce amin.

Duk da gudun da motar da su Mimi suka shiga take yi, gani take yi kamar ba gudu ba. Sannan ba ta tada shiga motar haya ba tunda aka haife ta sai yau. Bugu da Kari ba ta ta6a shan wahala ba a rayuwarta tunda take kamar wannan lokacin da ta bar gidan iyayenta. Shirun da ta yi daga zaune. abubuwan da take lissafawa ke nan. Duk da tsananin son da take yi wa Khalil ba ta jin za ta sake barin gida, ba tare da yardar Mahaifinta ba. Abin nufi ba tare da sun yi mata aure ba.

Cikin haka ne ta ji mutanen cikin motar suna salati, wadansu kuma wadanda ba musulmi ba suna ambatar abin da suka yi imani da shi. Ta zaro idanu, lokacin da ta ga motar ta su ta saki hanya. Sosai ta firgita, ta soma fadin Wayyo Allah! Daf da wani rami motar tasu ta tsaya cak. Wai ashe taya ce ta fashe, tana duniyar tunani, ba ta ji kara ba. Babu wanda ya zaci motar nan za ta tsaya. Motoci suka tsaya ana ta yi musu Allah ya kyauta. Hankalin Mimi ya sake tashi. Har aka canza taya jikinta bai daina bari ba. Haka nan duk lallashin da Khalil ke yi mata ba ta daina kuka ba. Shi kansa ya yi da na sani sosai na tahowa da ita. Da kyar ma ta yarda ta sake shiga motar suka nufi

hanya.Karfe biyu daidai, aka daura auren

Na’ima da Abbas. Daurin auren mai dimbin tarihi saboda irin manyan mutanen da suka halarci gurin. Babbar matsalar, Angon ya ki halartar daurin auren, yana gida kwance.

Ita kuwa Na’ima suna can gidan Yayar Mommy Nafisa suna cashewa da makadan da suka dauko. Sun koma can ne saboda wai kar a ce suna murna da auren ya koma kan Na’ima. Wani Karin abin aushin ma Na’ima ita da Abbas din ba su taba yin magana ko da ta waya ba. Kuma daga Momy har Na’ima ba su taba tunanin cewa wannan wata matsala mai zaman kanta ba ce.

Uku saura tasi din da suka dauka shata ta karyo kwanar layinsu. Kasancewar layin ba ya fita, sai ta tsargu da ganin motocin da aka ajiye a layin, sannan ga mutane. Ta ce, me ke faruwa? Ва dai Daddy ya mutu ba? Dan tasi din ya ce, gaskiya ina zaton ba mutuwa ba ce, sai dai biki. Ta ga nisan su karasa har kofar gidan, don haka ta ce, tsaya, ina zuwa. Yana tsayawa ta dauki jakarta, ta zura da gudu.

Kofar gidansu duk jama’a. Gate dinsu a bude. Tana shiga da Malam Ismail ta soma yin ido hudu. Mutane ba su gane ta sosai ba, saboda ita ba ma’abociyar saka hijabi ba ce.

Isma’il ya ce, daga ina kike? Ta ce, me ake yi a nan gidan? Ya ce, auren Na’ima.Ta zaro ido, an daura da

Na’ima? Ya ce, tabbas! Sai ta juya, yana cewa ke! Za ta fita ke nan su Abba da Abdulkarim za su shigo don yin sallama da Hajiya Sauda don ba su so su kai wannan lokacin ba a Abuja. Dad ne ya tsare su, wai

sai an gama daurin aure. Sannan yana ta nuna su ga abokansa, wadanda a da Mimi suka sanì, ba su san ma yana da wasu yaran ba. Sai abokansa na tun farko irin su Alhaji Isa.

Abdulkarim ne ya gane ta, don Abba ne a gaba, amma bai kalli fuskarta ba, kuma hijabin da ta sa ya Kara boye ta. Da karfi Abdulkarim ya rike hijabinta, saboda har ta dan gota shi. Ya jawo ta ya falla mata mari.

Sai da ta ga wani haske, sannan ya ce, gidan uban wa za ki koma? Ta tsala ihu, wanda ya janyo hankalin duk mutanen da suke harabar gidan. Ismail ya iso gurin yana cewa a yi mata hakuri. Abba ya ce, haka shi ne daidai da ita. Suka iza keyarta tana kuka, suna rankwashin ta, gami da zagi.Momy Nafisa ta fito da gudu, domin wata Kawarta ce za ta tafi gida, sun yi sallama. Amma tana fitowa ta ga Mimi a hannun su Abba. Sai ta koma da gudu ta sanarwa Momy Nafisa cewa ga fa Mimi.

Da farko Momy Nafisa idanu ta zaro, tana cewa, “na shiga uku! Me zai sa yarinyar nan ta dawo yanzu?” Sai Yarta ta ce, “kar ki damu, ta yi ta dawowa. An riga an daura

‘Momy Nafisa ta ce, “kuma fa haka ne. Bari in fita in ga yadda wannan fim din zai kare.” Suka sa dariya gami da shewa, ita da kawayenta. Ta kalli wata Hajiya Nana,

“ba ni wayata! Ga ta nan kusa da ke in sanar da Ubanta. In ya zo fim din zai fi dadin kallo.

Shi ne nan ta fito da gudu. A daf da hawa sama ne ta iso ta rungume Mimi ta fashe da kukan karya. Ina kika shiga ne yata? Me ya sa kika yi haka?” Abdulkarim ya ce, “Momy sake ta mu je sama. Sake komawa za ta yi.” Abba cikin fushi ya ce,

“ki wuce mu je mana! Don shi yana jin haushin Momy Nafisa ta taimaka gurin lalacewar Mimi. Momy Nafisa ta sake ta, suka iza keyarta zuwa sama. Abdulkarim yana rike da jakarta.

Momy Nafisa cikin wannan kukan ta kira Alhajin. Ya ce,

“lafiya?”tana shesshekar karya ta ce, «ka zo gida, ga

Hmmmm