UWAR RIKO CHAPTER 2 BY FIRDAUSI
Bayan kwana biyu da zuwan Malam
Musa nema wa dansa aure, sai ya sanar da Abubakar kudirinsa, bai dade ba ya fahimci wadda ake nufin hada su. Yasan Hajjo wadda asalin sunanta A’isha, daliba ce a makarantar da yake koyarwa, wani
• lokacin ma yakan leka ajinsu, tana daya daga cikin daliban da. ake yabo a makarantar.
Don haka da yamma ta yi ya kimtsa cikin shiga ta mutunci ya. isa gidan, ya kuma aiki wani yaro domin ya yi masa kiranta. Yaron ya fito ya sanar da shi tana zuwa. A can cikin gidan ta gama gyara jikinta ta fito, kasancewar mahaifinta ya sanar. da ita komai, ta hanyar mahaifiyarta, kuma ta gane waye Abubakar din ta amince. Bayan mintuna biyar Abubakar yana jira, sai ga ta ta fito. Da sallama ta rusuna ta gaida shi cikin boye füska, kasancewar malaminta. Suka samu wuri suka zauna a dakalin wani kofar gida.
Bayan shiru na dan lokaci saboda rashin sabo, musamman daga Abubakar sai ya dan gyara, zama, da alamar nauyi a maganarsa.
“Ina fata Malam… Baba ya yi miki bayani?”
Gyada kai kawai ta yi, yayin da ta ke cizon gefen hijabinta da hakora. Ya dan kalle ta.
“Hakika nayi farin ciki da wannan rana, musamman ganin yadda ki ka karbe ni hannu bibiyu, babu wanda ba zai so hada nasaba da danginku ba, Allah ya sa dai na samu amincewarki.”
Hajjo ta dan dago kai ta kale shi tana dariya, sannan ta yi saurin: rufe fuskarta.
A ransa kuwa sai yake fatan Allah ya sa ba kwafsawa ya yi ba, don bai taba zance irin wannan da wata budurwa ba.
A nata bangaren kuwa Hajjo kunyar Abubakar ta ke ji matuka, sannan ta yardar wa kanta tana sonsa. Ba wata doguwar hira suka yi ba,
- amma Abubakar ya fahimci ta amince da shi dari bisa dari, don haka da zai tafi sai ya yi mata sallama.Sai a sannan ta bude baki da kyar.
“Sauka lafiya, Allah ya kiyaye. Sai - ka dawo””.
Abin ma ya so ya ba Abubakar dariya, amma sai ya gimtse, ya amsa da,Amin
Wannan shi ne mafarin soyayyar da ta kullu zuwa hada zuri’ar da a cikinta ne abubuwa msu yawa suka faru.
DAYA
Gaskiya Malam ka canza magana, ya ya za a bada
sadakar yarinya kamar mún gaji da ita, ko kuma wadda ba ta da manemi? Wannan ai zubar da qimarta ne a idon mijinta, so. ka ke yi watarana mijin ya gorantà mata, ya ce ba shi ya ce yana so ba, taimaka mata ya yi'”.Ladidi ce ke ta bambamin fada tun sarda mijinta Malam Isah ya sanar da ita
cewa, ya kammala shirin aurar da ‘yarsu Sahura ga Abubakar dan gidan Malam Musa. Malam Isah
ya yi shiru yana saurarenta, tana faman kumfar baki.
. «To tun wuri a canza shawara, kuma ma a rasa wanda za a aura mata sai mai mata, wato kishiya ta kashe ta ke nan? Gaskia bazan yarda da wannan gullisuwar ba
Ta gyara zama a gefen gadon da take zaune ta kurawa mijinta ido tana kikkifta idanuwa
Malam isa ya gyara malum malum dinsa ya dubeta
Kin gama? Nace kin gama? To magana na riga na zartar kuma na basu izni su kawo dukiyar aure manema kuma ni banyarda da masu zuwa gurinta ba sam babu daa a tare dasu kuma da kike magana na zubar da kima ai kimar mace dakin mijinta kuma baga wanda baisan mutuncin mace za,a aurar da ita ba batun yana da aure kuma ke ke kadai kike zaune a gidan ina banda ma fitinarki ai da tuni gidan yana zaune lfy
Ya mike tsaye don haka aure babu fashi kuma da ABUBAKAR nayi niyyar yi to kinji.
Ya sabe babbar rigarsa ya nufi kofa
Hmmm
0 Comments