AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 4 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

“Me kika gani?” Na ce, “Yau ka sake”.

“Kamar ya ya?” Ya tambaye ni.Na ce, “Naga sai wani aikin kashe min ido kake”Kefa ba ki da kunya”.

Na yi saurin mikewa na yi dakin Inna, na same ta kan sallaya tana lazimi, na zauna sai da ta kammala. Tace, “Ya dai?” Nace, “Za mu fita shan Ice-cream da Ya Sagees”. Inna ta dan tsuke fuska,

“Wai ke Bahiyya yaushe za ki girma ne, kullum kina yawo da Sageer”. Na bata rai, “To dan nayi yawo da dan’uwana sai me?” Ta ce, “Yanzu fa ba da bane kun girma, gara a ringa sara ana duban bakin gatari”. Nace, “Sai ki sa Abba ya bani mota, kuma

• hard wani girma na yi da za’a ringa shiga tsakanina da Ya Sageer”

“To ai ke din ce Bahiyya, komai kanki gadi kike, ya kamata ki ringa janye jili, dan kin dan girma’. Na tsuke fuska.Dai-dai lokacin naji Ya Sageer yana Kwalla min kira, na juya cikin iya taku na nufe shi, yana bakin mota yana jira, motarsa wacce Abbana ya sai masa End of discation dark blue, sai shaning take.

Na Karaso, ya yi kyau mutuka, Kananan kaya ya sa, ya yi masifar kyau. Na ce, “Kai Ya Sageer, kana da kyau. Anya ba ka hada ‘yan matan jamia fada”. Ya yi murmushi ya ce, “Duk kyan da na yi ko rabin naki banyi ba, kinga yanda kike haske kuwa, ba dama dai wannan kanwar tawa”.

Ya bude min gaban mota na zauna, ya ja muka tafi. Muna cikin tafiya na ji wani sauti mai dadi yana tashi, na kalli inda nake jin sauti kan dash boad din motar waya ce, na dauko na mika masa nace Kai Ya Sager babu alkawari, shine ka sake wannan hadaddiyar wayar babu labari bare a tuna da sister Bahiyya”. Ya ce, “In kina so dauki ki bani taki, nima wani abokina ya kawo min da ya je China”. Na ce,

“Ina so”. Ya ce, “Dauki”. Hira muke sosai har muka isa Bakers Delagut.

Muka yi parking muka fito, mutane dake gun suka yi mana far suna kallon mu cikin sha’awa, muka shiga muka zauna muna shan Ice-cream da snack, natahowa da Inna nata muka fito. Muna fitowa muka nufi Jifatu Store, na suyo sweet, choculate, jumbo gum da biscuit hadaddu. Ya kalle ni ya ce, “Shi kenan abin da kike so shazumamu?” Na ce, “Um, ya isa”. Dama ni al’ada ina da sham kayan zaki. Daga nan gidan su muka je, sai wajen tara muka koma gida.

Inna kullum burinta in je, daga Ya Sager na ce, “Wai saboda me?” Ta kalle ni Saboda Sageer na

son ki da yawa, yanzu kunyi girman da ya kamata ki gane haka”. Na ce, “To na ji”

Sageer kamili ne sosai, a yanzu ya gama masters dinsa a jami’ar B.U.K Kano, ya soma iki da Nepa a matsayin accounter. A yanzu ni kuwa na kammala secondary school, Abbana ya yi kudi sosai, jin dadi kuwa babu magana, kullum Ya Sageer ba shi da burin da ya wuce nawa. Ranar asabar ya sanar dani zamu dina din wani abokinsa, har anko ya kawo min ya ce in sanar da Inna na fada mata.

Ranar lahadi da misalin karfe goma muka fita dan halattar dina din abokin Ya Sageer, munyi amfani da wata motar Abba wacce sai za shi ishasshen guri yake fita da ita. Dina babu hayaniya sosai, dan mutane Kalilan ne, sai da pass ake shiga.

A can Royal Tropicana aka yi. Muna isa wajen Ya Sageer ya bude min mota mun jera, ni kaina bata lokaci wajen yin kwalliya, dan material din ya lafe da fatar jikina. English gold na yi amfani da shi, na yi kyau ainin.Muna isa wajen idanu suka yi walai kaina, domin na zama wata cikin zara, kowa kallona yake.

Shi kuwa Ya Sageer kishi ya ishe shi ganin yanda idanu suka yi min ca, ni kuma ko a jikina, domin da kallo yana damuna kila da na dena fita.

Ina zaune na ji an dafani, na dan razana. “Ke dai Allah ya sauwake miki”. Na kalli Shukura na ce,

“‘Ashe kema kin zo”. Shukura Isma’il kawata ce, dan ga gidanmu ga nasu, mun shaku, tare muka yi pri sch, har da muka kammala bani da aminiyar data shige ta, mun shaku.Ganin mun hadu da Shukura ya sa Ya Sageer

shiga cikin abokansa. Muna zaune ni da Shukura,

wani yanayi na dinga ji a jikina, hakan ya sani gane

wani ne ya samun na mujiya. Ban aune ba na ji voice

dinsa a kaina, “Barka da hutawa”. Na mike tsam dan

sake guri, Shukura ce ta tsaya yi masa bayanin

sunana da unguwarmu, har da lambar gidanmu.

Haba, tana Karasowa na ce, “Dan me kika tsaya da

shi? Ni fa shi yasa bana son irin zuwa wannan gurin”.

A nan Shukura. take bani labarin

dangantakarta da amarya. Bamu bar wajen ba sai sha biyu, muna isa gida Abba ya soma fada, shi baya son

fitar dare. Na ga bacin rai gurin Inna, hakana shi ya

hana Umma tanka min.

Ko da sakamakon mu ya fito ya yi kyau sosai,

tunda kuwa Day Science na kammala, na shiga

B.U.K Kano cikin nasara, inda nake karanta Micro-

Biology, shima Ya Sageer ne ya zaba min. Ina cikin

karatu a wannan lokacin ne shakuwata da Ya Sageer

ta ci gaba, wanda ya nuna min burinsa na mu zama

abu daya. Iyayenmu sun aminta da hadamu tunda

muna son juna, mun shimfida babin soyayya ta gaskiya. Na shiga dakin Ya Sageer na same shi yana

danne-danne kan lab top, na zauna gefensa. Muryar

Inna na ji tana cewa, “Bahiyya ki fito kun yi baki”. Daga ni har shi muka fito, ba kowa bane bakin sai

‘ya’yan abokin Abba da yake a London, Alh, Sa’ad, dama su kan zo.

Muka calke ni da su Jamila, hira muka ringa yi sosai. Ta dan kalli Ya Sageer tace, “Yayanki yana da kyau”. Na dan ji kishi a raina. Ta ce, “ai muma haka muke da Yayanmu”. Na ce, “Ya kuke?” Ta ce, “Brother Adman karshe ne”. Na ce, “Kwana nawa za ku yi?” Ta ce, “Sati za muyi, su Daddy suna Zaria, ni na ce sai nazo naga Bahiyya”. Dariya na yi. A dakina na sauke su, Ya Sageer shi ya ringa dawainiyar yawo damu duk inda zamu, na ji dadin ziyararsu. A nan na fa da musu ina B.U.K ina karatu. Suka ce, “Me ya sa ba ki tafi London ba? Ai kin ga da tuni mun hade”

“Kin san kuwa aminiyata Shukura tana can, kai ina ma ina da adress dinta dana hada ku”. Nan dai muka sha hirarmu dasu.

Duk yanda kuke tunanin gayu da wayewa su

Jamila: sun shige nan, sun hadu karshe. Mun sha yawo da su, ga uwar tsaraba da suka kawo min,

•yawanci kananan kaya ne.

Jameel ita ba doguwa ba, ba gajera ba, jajir take, tana da maganar manya, tana da gajeran hanci, tana da daukar kwalliya, ga iyayi, tana da beauty point da ta yi murmushi za su lotsa, tana da diri, domin tana da hips ga shi ta cika daga kirji, tana da

Hmmm