MUSABBABI CHAPTER 2 BY HAJ HABIBA

rayuwa mara dadin ji ko gani, shin meye dadin

wannan rayuwar?

A hankali Musaddik ya cire cokali a cikin abincin, fuskarsa gaba daya duk ta canza ya shiga cikin damuwa, ya ce a sanyaye, “Inna babu wani dadi ga rayuwar da na ke ciki, hakika inda ina da ikon canja hanyar da na bio, da na yi gaggawa na canja, domin ko kadan ban jn dadin rayuwar.

Amma na rasa dalilin da ya sa na kasa yaki da zuciyata na daina, duk da ina kyamar abinda na ke aikatawa ni ma.”

Inna Halima ta jinjina kai fuska cike da tausayinsa tace. “Ka yi yaki da zuciyarka ne, ka dage ka kori shaidan, domin hakika shine yake yi maka huduba, ka tuna irin gata da arziki da ka taso a ciki.

Musaddik ka yi tunanin irin girma da kamalarka da dubban jama’ a suke gani a da, sannan ka tuna irin ilimi da hangen nesa da ka ke da shi wanda a yanzu duk sun tattara sun gudu, a sanadiyyar tsarin rayuwarka da ka canja, ka duba ka ga yadda ka maida kanka, hakika lamarinka na . damun mu, yana kuma daure mana kai kwarai da gaske.

Afrah da ke tsaye gaba daya sai ta juyo ta dora ma Musaddik idanunta wadanda suka cika da hawaye, zahiri tana daya daga cikin wadanda lamarin yayanta Musaddik ke damu, ta kan shiga dimbin damuwa da tunani idan ta tuna halin da yake ciki.

Sannan ta kan rasa inda za tasa kanta, idan ta kasa gane dalilin canjawar Musaddik, mutumin da ya taso da nagarta, kamala, natsuwa, ilimi da matukar hangen nesa, tana daya daga cikin wadanda rayuwar Musaddik ke matukar burgeta.

Yana matukar ba ta sha’awa, rayuwarsa da yadda yake tafiyar da lamuransa, abin a tsaya a kalla ne a kuma yi koyi da su.Inna kada ku gaji,

ku yi ta tayani da addu’a don Allah”

Furucinsa ya Kara dasa tausayinsa a zuciyar

Afrah. Inna Halima ta ce “Addu’a muna nan muna yi Musaddik. Allah ya shiryeka, ya dawo da kai hanya madaidaiciya, ba za mu gaji da yi maka addu’ a ba.

Ya gyada kai ya ce “Na gode Inna, bari na tafi”. Inna Halima ta ce “Ka Karasa cin abincin mana”. Ya girgiza kai lokaci daya yana mikewa. Na koshi Inna, na gode.

» Ya juva ya kalli Afral yace “Na gode da girki.”

‘ Yana gama fadin haka, ya juya da sauri ya fice.

Inna Halima ta numfasa ya ce, “Allah ka yi mana maganin abinda ya fi karfinmu.” Afrah ta amsa da “Amin.” Sannan ta juya ta ci-gaba da aikinta, amma zuciyarta na cike da tunanin Musaddik da tausayinsa, domin ta san hakika yana bukatar taimakon addau’a, ta kuma Kara Kudurar ma kanta za ta ninka akan addu’ar da take yi masa da. Haka ta kasance cikin tunaninsa da tausayinsa a wannan ranar kamar yadda ta saba a duk lokacin da suka hadu da juna.

Washegarin lahadi. Inna Halima sai dare, sannan ta sa Afrah a gaba zuwa gida, domin tana son ganin Dan-uwanta Malam Mahmud, hira suke yi a hanyar har suka isa gida. Dawowar Malam Mahmud kenan daga masallaci sallar Issha’i, fuskarsa ta fadada da fara’ a yana kallon ‘Yar-uwarsa, ya ce.

“Halima, ai na dauka ‘yar ta ki sai gobe za ta dawo, da na ga dare ya rufa? Ta yi murmushi, ta ce

“A’a yaya. Na ce ta jirani ne mu taho tare, saboda ina son ganinka, na san kuma iyanzu ne zan sameka a gida a tsana ke.”

Ta karasa maganar tana zama a

gefen tabarma da yake zaune akai.

A yayin da Afrah ta durkusa ta gaishe shi, cike da so da kauna ya amsa mata, sannan ta wuce dakin Mama Hauwa, domin ta gaida ta, amma haka nan ta amsa ba yabo ba fallasa fuska a hade, Na’ ima ko tana kwance akan gado ko kallonta ba ta yi ba har ta fice, ta shige dakinta. Malam Muhmud ya dawo da kallonsa ga Inna

Halima bayan sun gama gaisawa, sannan ya ce

“Halima ina fatan dai lafiya ki ke son gamina, da. daddaren nan?” Inna Halima ta gyara zamanta tana “Yaya ba wani abu bane dama magana ce na ke son mu yi akan Musaddif”.

Malam Mahmud ya jinjina kai ya ce “Ya Kara dauko wata maganar ne?”” Ta girgiza kai Ta ce

“A’a, wani tunani dai na yi akan halin da yake ciki, wanda yaya ka fi kowa sanin duk duniyar nan.Mu ke nan mu uku iyayen mu suka haifa, daga kai sai

•marigayiya Harirah mahaifiyar

Musaddik sai ni, yadda ba za mu so mu ga “ya’ yan da muka haifa cikin wata fitina ba.

Haka shi ma. Musaddik ba shi da kowa duk duniyar nan sai mu, kuma mu kadai ne ba za mu juri ganinsa cikin wani hali ba, don ina da tabbacin da mahaifiyar sa ce take a matsayinmu.

Ita ma sai inda Karfinta ya kare akan ‘ya’ yan mu, shi kadai ta haifa a duniya kuma shine sanyin idaniyarta, don haka duk yadda za mu yi, ya zama dole a kanmu mu yi kokarin daidaita rayuwarsa.” Malan Mahmud ya numfasa, damuwarsa ta

Kara fitowa fili. Ya ce “Halima kin fi kowa sanin duk duniya bani da wata damuwa da ta wuce damuwar Musaddik.ina cikin tsahanin tashin hankali akan rayuwar da yake yi, ina kuma takaicin da na kasa taimakonsa akan ya natsu, babu kuma abinda ba zanyi masa ba, matukar zai zama sanadiyyar

shiryuwarsa. Inna Halima ta ce “Ni Yaya akwai hanyar da na ke ganin wata kila zai iya zama sanadiyar shiryuwarsa”. Malam Mahmud ya ce “*Wace hanya ce wannan Halima?” Ta dan muskuta ta gyara zamanta, sannan ta ce.

“Aure, yi ma Musaddik aure ina ganin zai iya zama wata hanya ta natsuwarsa, domin duk iskancin mutum, idan ya yi aure ko yaya ne akan samu ya natsu, ko bai daina abinda yake yi duka ba, zai rage”

. Malam Mahmud ya ce.

“Haka ne, aure hanya ce ta samun natsuwa, zai kuma iya canja wa rayuwarsa tsari, amma wace ce za ta aure shi, kada ki manta a dalilin halinsa ya rabu da matarsa, sannan tun daga lokacin babu wata da ta Kara sauraronsa, saboda ba shi da natsuwa, to yanzu ina zai samo, wace ce za ta yarda da shi har ta aure shi a haka?”

Inna Halima Ta ce.Tabbas! Abinda kamar wuya, samun me auransa, domin kowace mace burinta ta sami kintsattsen namiji. Domin ta samu kwanciyar

“hankali a gidan auranta, don haka yaya ya zamar mana dole mu yi sadaukarwa saboda zumunci.”

Malam Mahmud ya dubeta ya ce.

“Sadaukarwa? Ban fahimceki ba?” Inna Halima ta ce “Ina nufin dole a cikin ‘ya’ yan mu mu sadaukar da daya ga Musaddik ya aura, mu yi aikin zumunci.” Ta gyara zamanta fuskarta ta canja alamun damuwa ta ce. «Ban taba jin ina takaici ace ba ni da ‘ya mace ba irin yau, amma ko’ina da ‘ya mace ma, yaya ka san, babu aure tsakaninta da Musaddik, tunda Musaddik ya riga ya sha nono na, amma yaya me ka gani akan shawarata?”Malam Mahmud ya dubeta ya ce “Shawararki ta yi, abar kuma dubawa ce, kuma kada ki kara tunanin ba ki da ‘ya mace, domin ‘yayana naki ne, haka zalika hada Musaddik aure da ‘yar-uwarsa shi kadai ya kamata, domin ‘yar-uwarsa ita kadai ce za ta rufa masa asiri, za kuma ta yi hakurin zama da

shi “Inna Halima Ta ce “Haka ne”. Ya ce “Saboda haka, zan hada shi da Na’ima, tunda ita ce gaba da Afrah.

.» Inna Halima ta yi murmushi sosai. “yaya

Allah ya saka da alheri ya kara dankon zumunci”.

Ya ce.

“Haba Halima wannan duk yi ma kai ne, na kuma gode da wannan tunanin naki, wanda ni ban yi irinsa ba, na kuma ba ki damar ki yi magana da Musaddik ki gaya masa hukuncin da muka yanke

Ta ce “‘Inshaa Allahu zan yi magana da shi.”

Daga nan suka ci-gaba da tattaunawa na dan wani lokaci kafin su yi sallama ta tafi, ba tare da sun gaisa da Mama Hauwa ba, yadda ba ta fito sun gaisa ba, haka nan ita ma ba ta bita daki sun gaisa ba, dama sun saba yin hakan. Washegari bayan sallar azahar. Afrah na zaune tana wanke-wanke. Na’ ima kuwa dawowarta kenan daga gidan kitso, tana zaune akan kujera ‘yar tsuguno tana latse-latsen waya. Malar Mahmud ya yi sallama ya shigo, ya dawo daga masallaci, cike da tausayawa ya dubi Afrah ya ce.

“Sannu da aiki, har yanzu ba ki samu hutawa ba, kin yi sallah dai ko?”” Ta amsa “Nayi sallah

Baba”. “Sannu da zuwa.

” Cewar Ni’ ima, ya dubeta fuska tamke ya ce.

“Yauwa, ke ba kya aikin komai ne?” Kafin ta yi magana Mama Hauwa ta cafke a lokacin da take fitowa daga daki “Ta gama nata, ko shi ma aikin sai an sa ido a kansa.Bai Kara magana ba har ya isa kofar dakinsa, sannan ya kwala ma Mama Hauwa kira, kai tsaye ta nufo inda yake ba tare da ta amsa ba. “Ga-ni.” Ya dubeta gami da girgiza kai sannan ya ce.’Ba ni

abin zama, magana za mu yi.” Nan ma ba ta amsa ba, ta shige ta dauko tabarma ta shimfida masa ya

zauna.Ita kuma ta jingine jikin katanga tana

• kallonsa.Wace magana za muyi?”

Ya ce a yayin

da yake kallonta “Ina bukatar natsuwarki, domin

‘magana za mu yi me muhimmanci”Ta ce “To ai ina jinka.”” Ya ce “Maganar

Na’ima ne, ina gain lokaci ya yi daya kamata ace ta yi aure, don haka na yanke shawarar ni da

Halima akan zan hada ta aure da Musaddik.”

Haka nan Afrah ta ji gabanta ya fadi, wanda ta rasa dalilin hakan, sai dai ta ji ta sami kanta da matukar tausayin *yar-uwarta, duk da ba wani shiri suke yi ba, amma ya zama dole ta tausaya mata, domin ta san auren miji irin Musaddik hakika rashin dace ne ga ko wace ‘Ya mace.

Mama Hauwa ta zaro idanu waje, tamkar za su fado kasa, bakinta na tsuma ta ce Wane

Musaddik din?” Ya ce “Musaddik din har nawa garemu? Musaddik dai nawa mana.”

Mama Hauwa ta saki salati tana tafa hannu. Ta ce “Eh, sai yau na Kara tabbatar da cewa Malam Ba ka son ‘ya’ yana, sannan Halima ba za ta barni na zauna lafiya ba, yau ko maza sun kare kaf a duniya.

Me Na’ima za ta yi da Musaddik?” Sakaran yaro mara natsuwa, babu wanda bai san halin da yake ciki ba na barbada, da can sanda yake na kwarai me ya sa ba kayi tunanin hada shi auran da

*yarka ba, sai yanzu daya zama lalatacce.

Sanda yake da kumbar susa yake shiga mota. yana fita, ai ba ka ce za ka ba shi *yarka ba, duk da lokacin har tayin Sakina na yi maka, akan ya aureta.

Ka ce ya riga ya sami mata, yanzu ina matar, halinsa ya koreta, ya zama shakulatin Gangaro, sai da ya zama mara amfani shine za ka ce Na’ ima ta aure shi, to ba ka isa ba.”

Malam Mahmud ya nuna kansa ya ce “Ban isa ba a matsayina na ubanta?” Ta turo baki. “Eh, in dai akan wannan ne, ba ka isa ba, kada ma ka kara furtawa. Na’ima ta fi karfin Musaddik, ko shi ne autan maza ba za ta aure shi ba.

Malam Mahmud ya fusata ya ce. “To zan ga wanda ke da iko da ita tsakanin ni da ke, domin na

‘riga na gama magana, na ba Musaddik Na’ima.” Mama Hauwa ita ma ta fusata.

“To za mu ji, za mu gani, wai an binne tsohuwa da rai, domin in dai ina raye Na’ ima ba za ta auri wannan tambadaddan yaron ba, aniyarku duk za ta bi-ku kai da Halima”.

Ta juya fuuu! Ta tafi. Malam Mahmud ya tashi ya bude dakinsa ya shiga cike da matukar bacin rai. A yayin da Na’ ima ta saki tsaki ta mike tana turo baki, tana kallon Mama Hauwa “Allah ya yi min tsari da wannan mutumin, lallai babu kauna tsakanina da Baba.”

Mama. Hauwa ta yi tsaki ita ma ta ce “In dai ta Kauna ce, ai baya kaunarmu gaba daya.

Musaddid din me. Allah ya tsari gatari da saran Kota, wuce ki shiga daki.” Na’ ima ta shige daki tana surutai na rashin tarbiyya da ilimi.

Haka Mama Hauwa ta wuni a cikin gidan tana sababi, wanda duk akan Afrah ya kare, domin harara da hantara da sa aiki duk ta sha su a ranar, don dai Malam Mahmud ya tanka, ta Kara juye kwandon masifarta a kansa, duk dalilin haushin hukuncin daya yanke akan Na’ ima.

A yayin da Inna Halima a ranar dai ta nemo

Musaddik ta zauna da shi, ta yi masa bayanin duk hukuncin da suka yanke a kansa. Musaddik ya numfasa gami da kallon Inna Halima.

Sannan ya ce “Anya Inna ki na ganin Mama

Hauwa za ta amince da wanna maganar, idan aka yi la’ akarin da abinda ya faru a baya na Sakina, kuma ki na ganin ita kanta Na’ima za ta yarda ta aureni, a halin da na ke ciki a yanzu?”• Inna Halima Ta ce.

«Wannan duk ba damuwarka bace, kawai kai ma na gaya naka ne saboda ka sani, ba don mu zauna muna tattaunawa ba.” Ya gyada kai ya ce

“Shi kenan Inna. Allah ya yi mana zabin abinda ya fi zama alheri.” Ta jinjina kai, ta ce “Amin. Allah kuma ya sa sanadiyyar ce ta shiryuwarka”.

“Ameen.” Ya amsa a sanyaye, sannan ta dube shi, ta ce «Zuwa yau da daddare ko gobe ina son ka bulla gidan Kawun naka, domin ka yi magana da Na’ima ka kuma samu Kawun naka, ka yi masa godiya tare da nuna masa amincewarka akan hukuncinsa’

Yace “To zan yi Kokarin yin hakan.” Daga nan ya yi sallama da ita ya fice daga gidan.

Hmmm