GARIN BAUCHI
Malam Musa tare da matarsa Lubabatu, wadda aka fi kira da Luba, sun kasance haifaffun garin Bauchi, tun asalin iyaye da kakanni.
‘Allah ya yi wa Malam Musa da Luba haihuwar yara uku; maza biyu, mace daya;
Abubakar, Yahaya sai kuma Mairo. Allah ya yi musu rufin asiri daidai gwargwado. Malam Musa sanannanen manomi ne, ba shi da wata sana’a wadda ta wuce noma, yakan nome hatsi da sauran nau’in abinci a fitar da su wasu garuruwa domin a siyar. Wannan ‘ya mayar da Malam Musa shahararren manomi a fadin garin Bauchi. Yaransa sun taso da tarbiyya da kwazo, saboda. Kokarin da iyayensu keyi don ganin sun zamo magari, suna zuwa makarantar arabiyya safe da yamma, kasancear a garin a daidai wannan lokaci an fi maida hankali akan ilimin
Muhammadiyya. Abubakar yaro dan shekaru sha biyar ya sauke alkur’ani mai girma, daga nan ya maida hankalinsa kan harkar noma kamar mahaifinsa. Sauran Kannensa sun ci gaba da zuwa makaranta, Abubakar ya hada da koyarwa a wata makaranta ta addini.
Shekarun Abubakar sun ja, ta yadda mahaifinsa ya kira shi ya yi masa maganar aure.
Duk da a tsarin Abubakar babu aure a wannan lokaci, domin ko budurwa ba shi da ita, amma ba ya taba tsallake maganar iyayensa, don haka da aka tuntube shi da maganar sai ya gyara zama.
“Duk abin da ka gani Baba ya yi, amma ni yanzu ban fara tunanin aure ba.
Malam Musa ya kalle shi, “To akwai wani tunani da na yi akan maganar nan, amma na ba ka lokaci ka je ka yi tunani, ko akwai abin da ka ke gani kafin *ka ji nawa hangen, Shawara muke yi.”
Abubakar ya san mahaifinsa na nufin ko akwai wadda yake so, shi kuwa ko.da yana da ita to ya fi son zabin iyayensa, in dai har suna da shi.
“Ba ni da wata shawara ko tunani da ya wuce naku, don haka duk abin da ku ka zartar daidai ne.
Abubakar ya ce da mahaifinsa.
Cikin. fara’a Malam Musa ya gyara zama.
“Madallah, Allah ya yi maka albarka, hakika na ji dadin kalamanka.”
Da haka maganar auren Abubakar ta fara. Malam Musa ya tuntubi iyayen wata yarinya a nan cikin unguwar tasu, wadda kowa ke yabon dabi’u da hankalinta. Ya yi magana da Luba a kan zai je da kansa ya samu mahaifan yarinyar, idan babu wani tsayayye to yana nema wa dansa.
Bayan kwana biyu malam Musa ya kai ziyara.
gidan Malam Umar, wato
mahaifin Hajjo. Bayan sallama ba a dade ba ya fito.
Suka gaisa, ‘kasancewar da ma sun dade da sanin juna. Malam Musa, ashe kai ne tafe haka?” Cewar Malam Umar.
Da murmushi Malam Musa ya amsa.
“Ni ne, wata muhimmiyar magana ce ke tafe da ni.
Suka samu dakali suka zauna, Malam Umar ya nutsu yana saurare. Malam Musa ya gyara daurin
rawaninsa.Wato wata alfarma ko arziki, ko iri na zo nema a wurinka, saboda dacewar zumuntarmu.”
Malam Umar ya ce, “Haba Malam, ai
• babu wani abu da za ka nema a wurina
matukar ina da iko da shi na hana ka, fade shi ko mene ne.”Malam Musa ya sadda kai.
“Wato zumuncinmu nake Kaunar a Karfafa, ta hanyar nema wa Habu auren yarinyar wajenka, idan har babu wata magana a kasa.
Malam Umar ya dan yi shiru, sannan ya dubi malam Musa.Ko kana nufin Hajjo?”
“Kwarai kuwa, haka aka ce min sunanta.
Malam Umar ya fadada fara’arsa.
“Ikon Allah! Ai kuwa babu wata magana a kasa.”
Ya dan yi shiru, kafin ya ci gaba.
«Ai wannan abu ne mai kyau, sai dai fatan Allah ya sa hakan shine mafi alheri.”
“To shine nake nema masa izini, don ya fara zuwa suna zantawa, in. Allah ya hada kansu falillahi hamdu.”
Malam Umar ya yi murmushi.Ah! Wannan ai abu ne mai kyau, da ma ni ma ina tunamin abin da ya dace a yi, domin da wsu samari ne ke zuwa wurinta, to saboda lalacewar zamani da kuma rashin yarda da tarbiyyarsu, ya sa na taka musu burki. Ai ko wani ka nema wa ni mai baka ne, ballantana Abubakar da na dauke shi kamar dana.”
Malam Musa ya yi godiya mai tarin yawa, ya tashi cike da farin ciki.
Da shigar Malam Umar gida, sai ya kira zainab mahaifiyar Hajjo, ya sanar da ita waye yayi masa sallama, da kuma dalilin zuwansa.
Zainabu ta yi farin ciki matuka, domin ta san zuri’ ar gidan Malam Musa, ta kuma san Abubakar, domin kawace a wurin luba mahaifiyar Abubakar, duk da kawancen nasu ba wani zurfi ya yi ba. Ta sanya albarka da fatan Allah ya tabbatar da alkhairi.
Hmmmm
0 Comments