mata gaskiya ko dai ba ke ce ki ka haife ta : ba? Ya aje cokalin hannunshi, na rasa me take miki, ita dai ba ma a kasan nan take karatun ta ba. Sai ta zo hutu irin haka, amma samba kya ko yin kewarta.
Hajiya ta tsiyaya masa lemun abarba, wanda ta hada masa, a cikin kofi sannan ta tabe baki ta ce, halin ta kawai za ta canza, in dai tana son soyayyata. Yanzu baka kalli shigar da ta yi ba? Tun daga Abuja ka sako ta gaba har Katsina, kana mahaifinta ga shi kanta a waje, kayan jikinta duk sun dame ta, wai ita dole ta waye.
Ya kalli Mimi sannan ya kalli Sauda, da dan murmushi, ina laifin kwalliyarta, ni ban ga aibun ta ba, haka ‘yan mata matasa irin ta ke yi. Ya kalli Mimi, ci kifin ki uwata kar ki damu kin ji?. Tsaki Hajiya ta yi sannan ta nufi dakinta. Sai lokacin Mimi ta samu damar yin mita, kaga ko Dad, sai da na ce ka barni can in gama hutu na, ka ce a’a sai na zo, ni daman na san Hajiya ba za ta taba so naba. Ta mike tsaye tare da kallon jikinta, shiga ta fa, mene ne aibunta? Ya kalle ta cikin sigar lallashi ya ce, ban ga laifi ba. Ita Hajiya wai sai ta ce, sai na saka hijabi da atamfa, ni kuma ba zan iya sa irin wannan kayan zafin ba. Na yi karatu na waye ni ba irin su Usaina ba ce kauyawa. Ya yi murmushi, shagwabarta tana burge shi.
Kallon ta ya ke yi tamkar ‘yar shekara biyu.
Ya mike ya zagayo wajen ta ya dafa kafadarta, kar ki damu uwata. Mamanki tana sonki, na san wannan ta ga na fi damuwa da ke ne cikin ‘ya’ya na, kin san don ita ce ta haife ki, shi ya sa fa. In da a ce kamar Hajiya Binta ce ko Nafi da tuni na sallame su, kin manta na taba korar Hajiya Binta saboda ke? Ta ce na tuna Dad, ya ce to kar ki damu ina son mahaifiyarki ko da ba ta haifamin ke ba, bare ta haife ki.
Kina son a ce mahaifanki biyu ba su tare? Ta ce ba zan so ba Dad, amma ka yi mata magana ta daina matsa min, ya ce zan yi mata, amma ke ma ina son cikin kwana biyun nan ki canza kayan sawarki, ki rinka saka irin wadanda take so. Ta ce zanyi in dai za ta bar ni in yi abinda na ke so, ya ce za ta barki mana kin ji, ki dai na kuka. Yayi ta• lallashinta har ta daina kuka.
Suna cikin cin abinci Hajiya ta sake fitowa daidai lokacin yara suka dawo daga Islamiyya da Sallama suka shigo. Ita ce ta amsa sallamar, Husna da Hasina ne a gaba, suka ce sannu da gida Hajiya ta ce yawwa sannunku da dawowa yara na. Ina sauran?
Kafin su ba ta amsa sai ga su suna ta yin
“Sallama, da hannu ta nuna masu gurin Dining, ga Dadin ku, suka nufi gurin suna gaida shi da daidaya. Ya dafa kan Husna da Hasina, su ne kanana a gidan, yana ta amsa masu. Mimi ta hada rai ita ba ta son hayaniya. Dady ya ce, ba ku gaida sista Mimi ba. Suka kalle ta don suna tsoron ta, sannu yaya Mimi, cikin daure fuska ta ce, yawwa, na amsa duka ne, ba sai kowanne ya gaishe ni daya bayan daya ba. Hasana da Usaina su ne ‘yan matan da suka bi Mimi a haihuwa. Dad ya kale su ku shirya da kannen ku,
Ya’u ya zo ya kai ku Super Market ku sayo tsarabarku, don ban riko komai ba, kowa ya je ya za6o abinda ranshi ke so.
Yaran suka shiga murna Hasana da
Hussaina suka ce Dad, mu kam ba zamu je ba. Ya ce, saboda me? Suka ce, muna da karatun hadda gobe, malamin mu zai z0, Bin Abdulrahaman. Hajiya ta ce, tabbas ba ku da halin fita, in ba haka ba za ku sha dukan tsiya gurin shi. Duka kuma ? In ji Dad dinsu, Hajiya ta ce sun wuce duka kenan? Karatu sai da zare ido.
Abdulkarim ya yi sallama, ya shigo falo suka amsa, ya iso gurin Dadin shima ya gaida Alhajin. Mimi tanata chatin dinta ba ta dago kai ba, shima bai ko kalle ta ba. Ya dubi su Hasana ya ce, kun dawo? Suka ce eh! yaya sannu da zuwa, dazun Hajiya ta fada mana zuwan ka, mun je dakin ku kana wanka, kuma lokacin Islamiyya ya yi dole muka tafi. Ya ce, na ji shigowar ai, ya ya Islamiyya? Suka nufi kujera su ukun suka zauna, Usaina na fadin, Islamiyya lafiya, munyi muraja’a ne yanzun. Ya ce, kun kusa fara Jarabawa kenan suka ce eh! Hasana ta ce, yawwa yaya don Allah ka amsar mana hadda in anjima mun yi magariba, gobe da safe muna da malamin gida Bin Abdulrahaman. Abdulkarim cikin sigar tsokana ya ce, bani da lokaci, ku ce gobe zanyi kallon duka. Usaina ta ce agaji yaya Abdul, bulalarshi akwai zafi, suka sa dariya tare. Ya ce, bari mu yi sallah sai in karbar maku, suka ce, yawwa yayanmu, mun gode.
Mimi daga wurin da take zaune tana jin su tana kuma kallon su, sai ta soma mita, ni na san duk ‘yan gidan nan ba sa so na, dole kawai suke gani na, kalli yaya Abdul, ko kallo na bai yi ba. Alhaji ya ce, kai!
Abdulkarim, ya ce, na’am, ya zo ga ni Dad, ya ce ba ka ga Mimi ba ne? Ran Abdulkarim ya baci, nan a take fuskarsa ta nuna, cikin wata murya marar dadi ya ce, na ganta mana Dadi. Shine ba za ka yi mata magana ba?.
Kafin ya yi magana Hajiya ta amsa da cewa, in duniya da gaskiya ita da shi wanene gaba? Shine ya kamata ya gaida ta, ko ko ita ce ya da ce ta gaishe shi?. Alhaji ya ce, amma ita bakuwa ce, bayan haka kuma yaushe rabonsa da ganinta? A kalla ya nu na kewarsa gare ta ko? Kan Abdul yana kasa tamkar ya sa kuka don haushi da takaici.
Hajiya ta ce, bai gaishe ta din ba, tafi abinka Abdulkarim, cikin sauri ya wuce. Su Hasana ma suka yi dakinsu ita ma Hajiya ta juya zuwa dakinta, Mimi ta kalli mahaifinsu Dad, kawai mu koma kalli fa duk yanda suka watse suka barmu, ya dafa ta kar ki damu ina zuwa.Bakin gado Hajiya Sauda ta zauna ta zabga tagumi, wannan abin ya ci mata rai, a ce mutum kamar Alhaji ya dinga irin wannan abu sai ka ce yaro. Kirikiri yana ganin gaskiya sai ya runtse ido saboda son zuciya, bai san cewa haka zai sa kan
‘ya’yansa ya rabu ba ne?. Sallamar shi ce ta katse ta, ta dago ta dube shi, shima ya iso ya zauna bakin gadon. Haba Hajiya ki sakarwa ‘yarki fuska mana? Ke ba abin faharin ki ba ne a ce na fi son ‘yarki, duk cikin ‘ya’ya na? Ya kama hannunta cikin sigar lallashi ya ce, haba Sauda kin fa san ina tsananin sonki, sonke ne fa ya shafe ta, ko ba ki lura ba?. Ta daga ido ta kalle shi, ban musa ba, na san kana so na, amma ni buri na shine ka yi adalci tsakanin yaranka Alhaji, ko don gudun rarrabuwar kansu.
Ya ce, menene na yi mata wanda ban yi masu ba? Ta kalli cikin idon shi, ai ba za su kirgu ba, banda nuna tsantsar kulawa a fili, duk cikin yaranka wanene ka kai kasar waje karatu bayan ita? To indan wannan ne, karatun na su na gida ya fi na ta cin kudi Sauda. Umm, haka dai za ka ce, tunda kana son kare kanka, ya ce, ni dai ina neman alfarma ki sakar mata fuska ki dan ja ta a jikin ki har mu tafi. Ta kalle shi, ta rasa me za ta ce masa, sai kurum ta ce to. Don tana son kawo karshen zancan, ya shafi kumatun ta, na gode, ya matso da bakin shi saitin kunnuwanta, ina son a kyuatata shimfida ta anjima. Don na iso da muradin
hakan.
Ta sake murmushi tare da kallon shi, wai Alhaji yaushe za’a girma ne? Ta yi tambayar cikin sigar wasa. Ya janyo ta jikin shi, wa ya ce miki ana girma da lada? Sai dai in mutuwa ce ta dauka. Suka sa dariya
tare, daidai lokacin aka yi kiran sallar
magariba. Suka mike, ta ce lokacin sallah ya yi bari in fita ‘yan mazan nan sai na yi fama sannan su wuce masallaci. Tare suka
fita ya nufi dakin shi, har lokacin Mimi tana zaune a falo. Sai dai lokacin ta koma kan
kujerar zaman mutum biyu tana ta chatin.
Alhaji ya nufe ta yana cewa, mamana kina hutawa ne? Ba tare da ta dago ba, ta ce eh Dady. Ya ce da kyau sannu, ya
wuce dakinsa. Hajiya Sauda ta dube ta, ki
tashi ki yi sallah, ta dago ta kalli Hajiyar ta
ga fuskarta a daure, ta zabga mata harara nace, ki tashi ki yi Sallah. Tsam ta mike ta nufi dakin su Usaina inda nan ne take sauka in ta zo, kayan ta ma ciki suke. Sai dai ita ba ta
son hakan saboda a Abuja sasanta dabam, amma a nan Hajiya ta hana ayi mata
dakinta dabam. Ta sami su Hasana suna sallah, ta fadi kan gado ta ci gaba da chatin dinta.
Ga al’ada Alhaji in ya fita sallah
yakan kai sha biyu bai shigo gida ba, Ga al’ada Alhaji in ya fita sallah yakan kai sha’ biyu bai shigo gida ba, saboda zai yi ta gaisawa da mutane, abokai zuwa ‘yan’uwa wadanda sukaji cewa ya shigo gari. Don haka ita ma Hajiya Sauda
•ba ta fito ba sai bayan sallar isha, ta shiga dakin Alhaji don sake kalailaice shi, tare da kunna turarukan Kamshin daki, ta fitar ma da Alhaji kayan barci, ta dama masa fura, sannan ta nufi dakin yaranta don ta tabbatar suna cikin koshin lafiya.
Dakin mazan ta fara shiga, Umar da
Aminu suna ta yin Home work, Abdullahi yana kwance kan gado, Sadik yana buga Game a TV. Ta ce, sarkin Game kai ka yi Home work dinka? Ya ce, eh! Na yi Hajiya, ta kalli Abdullahi, kai fa bawan Allah yau da wuri za ka yi barci kenan?. Ya tashi zaune kaina ke ciwo Hajiya shi ya sa ki ka ji na ce Dad ya bari sai gobe mu je Super maket din. Don ba zan iya kula da su ba.
Ta ce, ba sai kun yi haka ba, ya ce, kin shiga daki lokacin ta ce, to ka sha magani?
Ya ce eh! Ta ce to Allah ya sawwake, ya ce, Amen. Ta ce, Sadik tashi ka kulle muku kofar ku sai da safe, suka ce, to ta ce, kar. fa ku manta da yin addu’a lokacin barci, suka ce to. Ta nufi dakin su Husna da Hasina da kuma Zainab ‘yar gidan Hajiya Binta, wacce ta ki komawa wajen uwarta, tun lokacin da Alhaji ya saki Hajiya Binta, ya. kwaso yaran ya kawo su nan. Hajiya Sauda ta ce, sam ba zai yiwu ba, lallai ya mayar da ita, ta rike kayanta. Domin ita kanta ba za ta. so a raba ta da ‘ya’yayanta ba. Shine da ya dawo da ita ya mayar mata da yaran amma ban da Zainab, don kuwa ta kekashe ba za ta bi suba.
Ita ta fi son zama a nan, Hajiya Sauda ta rike ta, ta hada da ‘ya’yanta guda goma sha biyu da ta Haifa suka zama sha uku, su kam sun fara barci. Don haka ta shigo ta yi masu addu’a tare da kulle masu kofar dakinsu. Hasana suna zaune suna kara ma juna haddar Alkur’ani mai girma, ita kuwa
‘yar gwal, wato Mimi tana kishingide kan gado: Tana ta chatin, kai tsaye gurinta Hajiya ta nufa ta fisge wayar da sauri Mimi
Hmmm