ABDUL-MALEEK BOOK1 CHAPTER 4

Hakane Safna, amma kilura da wani Abu had'asu akayi kowa bayaso, kinga kuwa bazaije mata gaba gad'iba kasancewarsa mutum mai d'aukar kan tsiya, towa

 


    Hakane Safna, amma kilura da wani Abu had'asu akayi kowa bayaso, kinga kuwa bazaije mata gaba gad'iba kasancewarsa mutum mai d'aukar kan tsiya, towaima na tambayeki?, kin aiwatar da aikin malam kuwa?.

     Na aiwatar jiya, amma d'an zafinkan baiciba, canta had'osu  shida ita yafito d'aki rai a 6ace daga nan yafice, Dan jiya abincin safe kawai yaci agidan, inda ALLAH yasoni baduka nazuba bama.

        To aii da sauk'i, yanzun ga shawara d'aya dazata kawo miki nutsuwa harki samu barci, kisamu kota window ne kilek'a su, kiga halin dasuke ciki.

    Kai baseera wannan ba shawara baceba, idan naje Nagano abinda zaisaka zuciyata bugawafa?.

    Karki damu, insha ALLAHU bazaki ganoba.

    Bayan sunyi sallama safna tayi tamaula tanufi bayan d'akunan, cikin ikon ALLAH window d'akinsa abud'e take, da sand'a taje wajen, bobo tahango abakin gadon zaune yana danna laptop, Rahma na kwance nesa dashi tarufa da bargo tana barci.

     Wata sassanyar ajiyar zuciya tasaki sannan tajuya, cikin kwanciyar hankali tayi barcinta.


“Hummm kunjifa saka kai awahala masu karatu, ALLAH yarabamu da aikin Dana Dani.”


Marak'isiyya ta ce, "aunty Billy muma muje mukwanta, bobo ne kawai yajuri Rana dare yana danna laptop.”

    Na ce, “aikinsan mutumin na Madeena kamar k'arfe yake, baya gajiya da aiki.”



.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.

        Yau tsawon kwanan Rahma uku da fara kwana d'akin bobo, amma ko alama baita6a kawomata  wani Abu sa6anin hankalintaba, Dan haka tafara sakin jikinta sa6anin da datake barci a d'arare.

    Tana zaune tanayin addu'ar barci yafito daga wanka, dagashi sai tawul saikuma k'arami dayake goge sumarsa, da sauri Rahma tashafa addu'a ta kwanta.

    Yay murmushi tareda fad'in gsky Rahama kinada sonkai kulum saidai kima kanki addu'a amma banda ni.

     Murmushi tayi sannan ta ce, "kaima ina maka aii.

        Anya kuwa my cute?.

   ALLAH kuwa da gsk nakeyi.

    Toshikenan na yarda yay maganar yana saka kayan barci, tsaf yagama shiryawa yasaka turare sannan yazauna abakin gadon, yad'auki wayarsa yana dubawa Dan d'anzu ankirasa yana wanka, khairiyya ce Dan haka ya kalli agogo sannan yakirata, bugu biyu ta d'auka, ta ce, " ya bobo ina yini?, lfy kawai ya ce, "yad'ora da fad'in k miye nakirana adarennan?.

    Kayi hak'uri Yaya nakira number Anty Rahma ne akashe dama da'ita zanyi magana.

    Miya faru?.

   Babu komaifa, somuke muju kozatazo gobe idan ALLAH yakaimu d'in.

         yaran nan nakula kunefa kuke son koyama matata bakin yawo, yanzu inbanda son gantali mizata muku giben?.

    Ayya Yaya wlhy shirye shiryefa mukeyi, kuma kaga yanzu Ammi tahanamu fita ko ina.

    d'an k'aramin tsaki yaja ya ce, " ALLAH yakaimu, baijira cewartaba ya yanke wayar yama kasheta gaba d'aya.

    Juyowa yayi yana kallon Rahma wadda tai muk'us adole ita barci takeyi, yay murmushi komaidai wayon amarya sai ansha manta, nasan idonki biyu, idan baki juyo kimin addu'aba zakisha mamaki yau.

   Da sauri tajuyo.

  Yako tuntsure da dariya kekam anyi matsoraciya anan, to amin Dan barci nakeji.

    Azuciyarta ta ce, "yaukuma babu latsa laptop.

   Amma afili saita turo baki, cikin shagwa6a ta ce, " nafa yimaka tun d'azun.....

      Murmushi yayi tareda jawota jikinsa yamatseta sosai, suduka suka sauke ajiyar zuciya, jikin Rahma harya fara rawa, hakama k'irjinta sai dukan uku uku yakeyi har bobo yanajin bugawarsa, murmushi yayi Azuciyarsa ya ce, "yazanyi da matsoraciyar nan nikam?.

   Jin tana mutsu mutsun kwacewa yasakashi k'are matseta tareda tallafo kanta, kissing d'in wuyanta yafarayi, daddyn Nawal pls kayi hak'ur.......

    Bai bari tak'arasaba yahad'e bakinsa danata, sosai yake wasa da harshenta da jikinta, ganin yana Neman wuce gona da iri tafara haure haure da k'afarta tana mintsilinsa.

    Saida yayi mai isarsa sannan yasaketa yana maida numfashi.

    Da sauri itama tamatsa gefe tana maida numfa, saida yanutsu sannan cikin murya mai taushi amma asark'e ya ce, " kizo kimi Addu'ar inba hakaba namiki abinda yafi haka.

    Babu shiri tajuyo tamasa addu'ar tashafa masa kamar yanda yabuk'ata,, shikam sai dariya yake k'asa k'asa wai matsoraciya.

   Shiru tamasa tana tunanin hali irin na maza, Dan itakam wannan *_SABON AL'AMAREE_* yazarce wayonta.



Safna kam hankalinta a kwance yake yanzun, tunda malam da'u yace mata aii babu abinda zai shiga tsakanin Rahma da bobo tunda basusan junansu, acewarsa yaturo wani aljani dazai dinga gadinsu karsuji sha'awar junansu ma bare har wani Abu yashiga tsakaninsu.


Hummm kaji masu jayayya da hukuncin ALLAH.



######

     DA SAFE haka Rahma tatashi tanamai tsananin jin kumyar Bobo, Sam tak'i yarda su had'a ido.

   Safna tana lura dasu, Dan haka ko awajen break tayi kicin kicin da fuska tanata harare harare, babu Wanda yakula da ita, bobo idonsa nakan matarsa, itakam Rahma tamaida hankalinta wajen bawa Nawal abinci abaki dankarta makara, dahakadai aka gama break, bobo yad'auki Nawal suka fice, Rahma tarakasu har wajen mota, tafiyarsu babu dad'ewa itama Safna tatafi makaranta.




Har gabda magriba safna bata dawo daga makarantaba, hankalin Rahma dukya tashi, gashi takirata amma yak'i wucewa, duk halin datake ciki bobo nakula da ita ammadai baice komaiba.

    Bayan yayi shirin masallaci yafito, afalo ya iske Rahma tanata safa da marwa, yay mata  kallon tsaf, kamar zai wuce saikuma yajuyo, wai lfy kuwa?.

    Yatsine fuska tad'anyi, wlhy aunty Safna ce har yanzu bata dawoba, gashi nakira wayarta tak'i hucewa, dan ALLAH kozakad'an gwada kiranta? muji.....

    Yanda tayi maganar saita bashi tausayi, baice komaiba yazaro wayarsa a aljihu, harzaiyi amfani da family layinsa saikuma yafasa daya tuna wazai kira, layinsa dakowa yasani na office yay amfani dashi, ido yad'ago yana kallonta alamun tafad'a masa number.

          Tafad'a shikuma yana sakawa, cikin mamaki sosai yake kallon number dan ana kiransa da turo masa message da ita, basarwa yayi yakirata Dan bayaso Rahma tafahimci komai, cikin sa'a kuwa yana kira tashiga, bugu biyu tad'auka jikinta har rawa yakeyi Dan ganin Wanda yakirata.

      Cikeda salo tace assalamu alaika, sanin muhimmancin sallama kawai yasakashi amsawa, murya adak'ile ya ce, "kina inane?."

     Wani sanyin dad'i Safna taji, takuma kashe murya can k'asan mak'oshi, wlhy moto nane yad'an samu matsala kozakazo ka taimakeni.......

    Baibata amsaba yakashe wayar gaba d'aya, ya kalli Rahma ya ce, "tace tana zuwa motantane yasamu matsala amma angyara.



Hummm kunfaji bobo da k'arya🤣.


 ita kam safna yana yankewa tayi saurin kallon wayar, ranta yad'an 6aci amma saita danne takirashi, jin wayar akeashe yasa tayi zaton ko bashida caji.

        

  Babu dad'ewa kanikawan data kira suka iso, mukullun mortar tabasu tatari adaidaita tayo gida............











*_luv you oll_*

*_(((S))).....2017_*




👩🏻‍💻typing........


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣

      _•{🅱🅾🅱🅾}•_



*_NA_*

_*Bilyn Abdul*_


_sadaukarwa_

*_Abba Gana_*

*_Batul mamman_*

*_Billy giro_*



_assalamu alaikum, kwana biyu kunjini shiru masoya bobo, wlhy wutarmuce tasamu Matsala, amma yanzu komai normal._



5⃣5⃣

      

     Ana cikin sallar isha'i safna ta shigo gidan, babu kowa afalon sai k'arar TV  tawuce d'akin Rahma suna sallah itada Nawal.

     Da sauri tadawo baya dan tanada tabbacin Rahma bata gantaba, kai tsaye wajen abincin kan dinning tanufa, ta bud'e abinci tayi barnad'e barbad'enta tamaida tarufe sannan tanufi d'akin.

     Zuwa sannan sun idar da sallah, Rahma ta ce, "kai aunty har hankalina yatashi wlhy, naga dare yafarayi kuma nakira wayarki tak'i tafiya.

     Safna ta ce, " ayya my lil motatace tasamu matsala gashi wajen babu network.

     To ALLAH ya kiyaye gaba.

    Ummi takiraki kuwa?.

    A'a safna tafad'a cikin kallon Rahma, miya farune?.

    Babu komaifa d'azu bayan tafiyarkine takirani wai Abba yanata fad'a yakamata ki koma gida tunda nasamu sauk'i, shine nace suyi hak'uri ayi bikinsu khairiyya saiki koma ko?.

       Numfashi safna ta sauke, azuciyarta ta ce, "su ummi fa kuna k'ok'arin 6atamin aiki, amma zanyi k'ok'ari acikin 'yankwanakin dasuka ragemin nayi duk abinda yadace, afili kuma saitayi murmushi haka yayi Rahma, abinda tafad'a kenan kawai tamik'e zata shige bayi.

     Bobo yak'arasa shigowa d'akin Dan tund'azun yana bakin k'ofa tsaye yana sauraren firar tasu.

     Safna dake k'ok'arin shiga bayi tajuyo tana kallonsa, suna had'a ido tasakar masa wani lallausan murmushi, ya Bob ngd fa da d'akkoni ALLAH yabar zuminci tak'arashe maganar da d'aga masa gira.....

     Bobo kam ya daskare atsaye miyarinyar nan take nufi?, agidan uwarwa nad'akkota d'in?.....

     Rahma madai kallon tuhuma take masa, Dan duk abinda Safna tamasa akan idonta, tuni idonta yaciko da kwalla saboda kishi, ita kanta batasan tanada kishi mai zafiba kamar haka, ta had'iye wani Abu mai d'aci daga mak'ogoronta, mik'ewa tayi tafice daga d'akin kawai.

      Da sauri yajuyo yabi Rahma da kallo harta fice, Nawal ma dabatasan bikin da akeba tatashi tabi bayan Rahma, daidainan Safna tafito daga bayi, murmushin mugunta tasaki sannan ta tako ahankali har zuwa gabansa, my jaan rago baya zama gwani, nasan kaima kana sona, amma bansan mike hanaka nunawaba?, so karka damu ni bana tsoron Rahma zan fahimtar da ita ta kurman bak'i, idan bata ganeba zan mata fassara.

     Tunda tafara maganar kallonta kawai yakeyi, yama rasa wane mataki zai d'auka akanta, kafin yafarga tafice abinta, haka shima yabi bayanta tamkar soko.

        A dinning suka tarar da Rahma da Nawal sunacin abincinsu, bobo yaja kujerar dake kusada Rahma ya zauna, itama safna tazauna akusa dashi suka sakashi tsakkiya, tunda suka fito ko Inda suke Rahma batama kallaba, abincinta kawai takeci.

      Safna taja filet tafara zubama bobo abinci, tunda yafahimci shiitake zubamawa saiya d'auki cokali kawai yafaraci acikin filet d'in Rahma.

     Abin yak'onama Safna rai, amma saita dake tafaracin abincin data zuba masan, Rahma kam koda bobo yasaka hannu a abincinta bata kulashiba, shikam mamaki take bashi Dan baita6a ganin fushintaba saiyau.

      Bayan sun k'are cin abinci bobo yamik'e zaitafi d'aki, Safna tai saurin cewa ya Bob maganarmufa ta d'azu?, kosai ka kaini makaranta gobe?.

     Juyowa yayi yana kallonta kamar zaiyi magana saikuma yafasa yajuya yatafi.

      Rahma tayi saurin share hawayen dasuka cika mata ido, ita tama kasa fahimtar inda maganganun Safna suka dosa, kuma takasa fassara yanayin fuskar bobonta bare tagane mike faruwa?.

      Hakadai takama hannun Nawal suka koma falo, kallo takunna musu sukeyi dukda ita hankalinta baya a wajen, hotunan mutane kawai take kallo, amma bata fahimtar komai.


Safna kam tana d'aki tanata zuba tsallen murna Dan dad'i aikobabu komai tasaka rud'ani atsakaninsu, gashi kuma yau bobo yaci abinci da maganin data zuba, tadaka wani tsalle tareda fad'in saini Safna ikon ALLAH, k'adangaruwar baking tulu nake, akasheni akar tulu, abarni na 6ata ruwan, takuma tuntsurewa da dariya.


Na ce, "hummm safna kenan ba girin girin badai tayi mai."



Bobo madai yana d'akinsa, sai safa da marwa yakeyi, yamarasa tunanin dazaiyi akan Safna da kaidinta, ganin Kansa ya tushe yad'auki waya yakira Ammar.

      Cikin zolaya Ammar yad'aga wayar, kaga barrister dodon 'yan iska, mijin Rahma baban Nawal ya yadai my guy?.

      Numfashi Bobo ya sauke tareda fad'in Ammar ajiye wasa gefe inaso muyi maganane.

         To inajinka Ammar yafad'a cikin gyara nutsuwarsa.

    Ammar wata matsalace agidana nakeson kanemamin hanyar maganinta danni kaina gaba d'aya ya kulle.

    Ammar ya ce, "kaida Rahma ne.

     A'a no Rahma batayimin komaiba yayartace Safna.

   Haba bobo tokai miya had'aka da safna kuma?, bayan kai yanzu mijin k'anwartane.

    Hakane Ammar ni mijin k'anwartane, amma yarinyar tana Neman shigowa rayuwata, yakwashe kaf abinda Safna tamasa yafad'ama Ammar, yanzun zancennan danake maka nadawo daga masallaci na Tatar tana barbad'a magani a abincinmufa, amma bata ganniba, Rahma kuma suna d'aki itada Nawal suna sallah.

     Ammar yaja wani gwauron numgashi, lallai yarinyarnan hatsabibiyace, to amma kunci abinci?, a tomizai hana, sammu yakanyi tasirine da izinin ALLAH, Dan haka zuba maganinta bazai hanani cin abinciba nikam.

    Hakane Abdulmaleek, ammafa natayaka murna da aurenka bai kasance da yarinyarnan ba wlhy.

   Aikodai nima haka naketa godema ALLAH akullum Ammar, Dan nasan da itace matar tawa nasan saita rabani da Nawal.

   Wlhy kuwa zata iya. ni yanzu hanya d'aya nake ganin mafita kuma maganin yarinyarnan.

    Da sauri bobo ya ce, " minene?.

    Maganinta  d'ayane Wanda zata gane lallai kamata nisa fintin kawau shine kayi k'ok'arin kusantar matarka, ka ajiye batun Barin Rahma sainan gaba, Dan wlhy Idan kayi sake sai shaid'aniyar yayarta d'in nan taci galabar rabaku nan gaba, Dan kuwa 6arakar ta hango har take iya tunkararka kasaki 'Yar uwarta ka aureta, inhar tabud'e ido taga Rahma daciki, tom dolene tasakama zuciyarta salama ko itace shigabar jaheelai ta duniya, kuma yakamatama ta tattara takoma gida tunda su Rahman sun sami sauk'i.

      Duk abinda kafad'a gsky ne Ammar, saidaifa gsky Rahma yarinyace.

    Ammar yay dariya to abokina yaza'ayi, yaran k'auye da'akemusu aure shekara 12/13 fa?.

    Hummm kai asuma mazan yarane shiyyasa.

     Wata dariyar shak'iyanci Ammar yasaki cikin dariya ya ce, "kaikuwa gaka k'ato ko?, so kabimusu yarinyarnan ahankali wlhy Dan nasanka sai a slow.

    Kai d'an iska saida safe, dankasamu nafad'a maka sirrina shine zakamin wulak'anci.

    Hhhhhhh haba angon Daren yau maida wuk'ar mana.

    Murmushi bobo yayi tareda yanke wayar yana fad'in kai Ammar mafa d'an iskane wlhy.

          Jiyayi zuciyarsa yayi wasai kamar anyaye masa damuwarsa, mik'ewa yayi yashiga bayi ya salla wanka tareda d'auro alwala, bayan fitowarsa yad'an shafa mai da turarur rukansa yazira doguwar Riga ya zauna yana jiran shigowar Rahma.

     Jareda yad'auka yana karantawa, saidai lokaci lokaci yakan kalli agogo, tun yana saran shigowarta harya fara mamakin miya hanata zuwa Dan 11:47pm, yad'anyi tsaki tareda gyara kwanciya yamaida Kansa ga jaredar, sai yakasa cigaba da karantawa, wayarsa yajawo yakirata amma bata shigaba yakumayin tsaki, afili yace mi yarinyarnan take nufi danine?.

    Ganin wankin hula zai kaishi dare yasakashi mik'ewa yafito, fitilir falo yakunna Dan har ankashe alamar sunma kwanta kenan, le6ensa yacije yanufi d'akin Rahman.

    Nanma fitilar akashe take saida ya kunna, yakai dubansa ga gadon Safna da Nawal ne kawai kwance suke barci, ad'an kid'ime yafara baza idanu, can yahango Rahma zaune akan sallaya tana karatun alkur'ani mai girma, ajiyar zuciya yasauke ahankali.

     Itakam Rahma tun shigowarsa tana jinsa amma ko d'agowa ta kalleshi batayiba.

    Ahankali yataka har inda take, wani d'an tsugunnon gayu yayi agabanta, ido tad'ago ta kalleshi, kallo d'aya tayi masa ta kauda kai, wani d'an murmushi yayi mai had'eda ta6e Baki, yay wani k'asa da murya yana mata kallon nan nasa na k'asan ido, Sayyada yau baza'a bani shayibane?, konayi laifine?.

    Idanunta dake cike tabda hawaye tad'ago suka had'a ido, tai saurin juya k'wayar idonta Wanda yabama Hawayen damar zubowa, alkur'anin ta ajiye tamik'e batareda ta tanka masaba tafice.

    Shima mik'ewa yayi yana murmushi azuciyarsa ya ce, "yammata kwantar da hankalinkima yanzun bada dad'ewaba zakiyi kukan mai dalili.


Ficewa yayi yakoma d'akinsa.

    Itakam tana kichin, bayan tadafa masa shayi tad'ora atire tareda yanka lemon tsami kamar yanda tasaba, d'auka tayi tanufi d'akinsa.

    Yana zaune abakin gado yajingina da fuskar gadon yana latsa waya tashigo, idanunsa yad'ago yana kallonta, itakam ko Inda yake bata kallaba taje saman dirowar gefen gado ta ajiye tiren shayin, batareda ta tanka masaba takama hanyar juyowa, da sauri bobo yarik'e hannunta, cak tatsaya amma bata juyoba, yawani narke murya can k'asan mak'oshi, miyake damunki?.

    Hawayene suka k'ara zubo mata akumatu, dama Rahma akwai arhar kuka, ganin bazata amsashiba yajawota tafad'o jikinsa, mutsu mutsun kwacewa tafara amma yay mata nagartaccen rik'o, hannunsa yasaka yakama ha6arta yarike yanamai fuskanto da fuskarta gareshi my cute kishi ko?.

   Da sauri tad'ago idonta dayay ja tana kallonsa, ya akayi yagane asirin zuciyarta, ita kanta tana mamakin yanda ta nuna kishinsa ayau, wani 6angare na zuciyarta ya ce, "kin kamu da sonsane, da sauri ta ta6e baki.

    Bobo yamatso da fuskarsa gabda tata tamkar zaimata kiss murya k'asa k'asa ya ce, " miyasa kike ta6e Baki?, kobaki yardaba kina kishina?.

    K'ok'arin mik'ewa tafarayi tana fad'in shayinkafa zai huce.

   K'ara k'ank'ameta yayi, cikin salon maganarsa ya ce, "aii shayi yagama aikinsa daga yau, saidai idan nasha da marmari amma badan damuwaba, daga yau kece zaki zama shayina.

    Da sauri ta kalleshi saikuma ta kauda kai yayinda suka had'a ido, bata fahimci Inda zancen nasa yadosaba amma taji aranta akwai shak'iyanci aciki.

   Yunk'urawa tasakeyi zata tashi, ta ce, " tonaji kabarni naje nacigaba da karatuna.

   Ayya aynanma karatu zamuyi kuma jira kigani, tashi kiyi alwala kizo.

    Dukda gabanta yafad'i amma saita dake Dan batason rud'a kanta da zargin abinda ba hakaba.

    Inada alwatafa. Tayi maganar kamar zata fasa kuka.

    OK tom tashi muyi sallah, bata musa masaba tamik'e suka hau sallaya, shine yajasu jam'i, raka'a hud'u sukayi kafin daga bisani yafara kwararo addu'oi Wanda ita bama tata6a zaton ya iyaba, daganan yadafa kanta yay addu'a da *Annabi tsira da amincin ALLAH su tabbata agareshi* ya koyar damu, yayi musu addu'oi sosai sannan suka shafa tareda mik'ewa.

    Da sauri Rahma takama hanyar ficewa, bobo yay azamar shan gabanta, idanu tad'ago tana kallonsa, yad'aure fuska tamau tamkar bashine yagama lalla6ataba yanzun, k miye haka wai?, yaushe raini yashiga tsakaninmune?.

     Yanda yacanja mata lokaci d'aya saitaji tsoransa yak'ara kamata, murya na rawa ta ce, "kayi hak'uri zanje nacanja kayane.

    Hannunta yakama zuwa gado, karki damu bama saikin canjaba yay maganar yana k'ok'arin zame dogon hijjabin dake jikinta.

    Idanu kawai Rahma ta runtse, zuciyarta sai faman bugawa takeyi da k'arfi............







Hummm.....😎Rahma yau kinga takanki👻.






*_luv you oll_*

*_(((S))).....2017_*



👩🏻‍💻typing........


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣

      _•{🅱🅾🅱🅾}•_


 

*_NA_*

_*Bilyn Abdul*_


_sadaukarwa_

*_Abba Gana_*

*_Batul mamman_*

*_Billy giro_*



5⃣6⃣

       

       Daga ita sai zani d'aurin k'irji, ya ajiye hijjabin gefe shima yazauna yana kallonta, yayinda itakuma taduk'ar dakai k'asa idanunta cike da kwalla.

     Tashi yayi daga bakin gadon, yajawo d'an k'aramin tebir na gilas dake gaban kujera ya zauna a agabanta suna fuskantar juna, saida yay mata kallon tsaf sannan yasaka hannu yad'ago ha6arta.

     Idanunta talumshe, kwallan datake mak'alewa suka zubo, yad'an lumshe ido yabud'e akanta, murya k'asa k'asa ya ce, "wai miye damuwarkine?, shin kukan nan bazai k'arebane?, kokuwa ban cancanci sanin matsalarkiba?.

      Girgiza kai tayi alamar a'a.

   Ya ce, " nafison kimin maganar da bakinki.

    K'ara matso hawayen tayi muryarta na rawa ta ce, "babu komaifa.

   Ya ce, " amma kike yin kuka?, kinga fad'amin kinji my cute.

    Yanda yaymata maganar cikin muryar lallashi saitaji sanyi aranta, wannan yabata kwarin gyuywar kallonsa, ta d'an kauda idonta sannan ta ce, "Dan ALLAH ya Abdulmaleek miye had'inka da aunty Safna?.

              Tabashi dariya kwarai da gsk, amma saiya dake, yad'an tsura mata ido nawani lokaci kamar mai nazarinta, batareda yabata amsartaba yamik'e tsaye, doguwar rigarsa yacire yarage dagashi sai gajeren wando.

    Itadai satar kallonsa takeyi da mamaki, tamasa tambaya amma yashareta yacigaba da harkar gabansa.

    Fita taga yayi, bayan kamar minti 3 saigashi d'aukeda fresh milk da cup, sake zama yayi akan tebir d'in, yatsiyaya fresh milk a cup, itadai tana kallonsane kawai, saida yacika kofin taf sannan yamik'a mata, girgiza kanta tayi ahankali ta ce, " nak'oshifa.

    Yanzu d'inma baitanka taba, saidai yakai kofin saitin bakinta, yanda yatsareta da mayun idanunsa wad'anda ayanzu suka sake canja kala yasata dole tabud'e baki tasha, haka yayta bata tanasha badan tanasoba, data janye bakinta saiya had'e fuska dole nacigaba da kar6a, ahaka dai harta shanye tas, shima zubawa yayi yana sha yana kallonta, itadai kanta na k'asa tana wasa da zoben hannunta.

    Bayan yagama yamik'e ya ajiye cup da kwalin fresh milk adurowar gefen gadon, bayi yashiga yayi brush, ya umarceta itama dataje tayi, sanin datayi akwai sababbin brush a bayinsa dayakan ajiye yasa batayi musuba yashiga, aiko tararwa tayi ya ajiye mata sabo a Leda, tad'auka ta6are tayi brush abinta sannan tafito.

      Abakin gado ta iskeshi zaune yana kashe wayoyinsa, yad'ago ido ya kalleta, hau gado ki kwanta mana ko bakyajin barcine?.

     Kaita jinjina masa alamar eh.

    Murmushi yayi ya ce, "karkidamu kwanta barcin zaizo, ko kin manta gobe kunada hidima agidan Appa.

     Tunowa da gobene zasuje gidan Appa Dan k'arasa shirye shiryen bikinsu khursiyya  yasakata hayewa gadon, saidai gabanta sai fad'uwa yakeyi, Dan ita lamarin bobo yau tsoro yake bata wlhy.

     Hakadai ta kwanta tamkar wata munafuka ta k'udundune waje d'aya, yad'an kalleta ya girgiza kai sannan yagyara kwanciyarsa shima.

      Kwanciya yayi sosai tareda Jan bargon ya lillu6e kamar yanda tayi, jawota yayi jikinsa, yay mata k'yak'yk'yawar runguma wadda ita kanta saida taji yarrrrr, daurewa tayi tadake Dan bataso tanuna masa tsoronta afili, saidai tamakaro Dan tuni bobo ya harbo jirginta.

    Jitai yana mata wasu abubuwa sa6anin hankalinta, tunda take dashi bai ta6a mata hakaba, tuni k'irjinta yafara dukan Tara Tara.

    Hawaye tafarayi ahankali kuma tafara sheshshekar kuka wadda tadawo dashi hankalinsa, cikin muryar kuka ta ce, "Dan ALLAH kayi hak'uri, d'an murmushi yayi sannan yajuyo da ita suna fuskantar juna dukda dai acikin duhu suke, cikin wata irin murya dabata ta6a jinsa da itaba yake maga, cikin kunnenta ya ce, " plss Rahma ki daure ki mallaka min kanki, karki manta nata6a fad'a miki inaso da sauri shiyyasa nakeyi da sauri, inaso na numa duniya ked'in dabance kuma kin cancanta, sannan kuma kinmini tanbaya d'azun tom yanzufa zanbaki amsar tambayaki, amma kafin sannan kema zan tanbayeki, Rahma kina kishi nane?.

     Tambayar yabata kunya Dan haka taisaurin sinne kanta ak'irjinsa daketa tashin k'amshi mai saka zuciyarta nutsuwa, yanda take fidda numfashi ak'irjinsa saiyakejin dukkan ga6o6in jikinsa sundaina aiki, yasa hannayensa duka ya rungumota sosai tareda mannata da k'irjinsa bayan ya zame zanen data d'aura.

    Wata wawuyar ajiyar zuciya suka sake gaba d'aya, bai zauna 6ata lokaciba yafara bata hot kisses masu rud'ar da sabon shigarsu, masukuma k'ara k'aimi ga Wanda yasaba, to a6angaren Rahma dai rawar jiki take masa, ganin yanda tarikice masa ya lalubi kunnenta cikin sark'ewar murya ya ce, "my cute kinutsu bazan cutar dakeba, duk Wanda aka kira jarumi to kitabbata yakasance mai jarumtarne, Nima nakai mak'urar tik'ewar dabazan iya hak'uriba plz helf me my life.....

      Kuka Rahma tafarayi ahankali, damasa magiyar yayi hak'uri Dan ALLAH, amma ina hankalin mutumin naku yagushe, bayajinta ko kad'an, k'ok'arin Isar da sak'wanni kawai yakeyi.

    Bata ankaraba taji yafara addu'ar saduwa da iyali kamar haka.👇🏻

   *_“Bismillaahi, Allaahumma jannibnashaid'ana, wajannibshaid'ana maa razak'tana”._*

     Rahma ta kwalla k'ara data sakani kwasa aguje nayo waje, bobo yagama aiki, shima dukda baya cikin hayyacinsa saida yay nasarar saka tafin hannu yarufe mata bakinta.

        Afalo na rak'u6e tamkar Minafuka, kukan Rahma danake jiyowa Nima yasakani hawaye, babu sunan Wanda bata kiraba ya taimaketa har Nawal yau saida Rahma takira amma babu mataimaki sai ALLAH.


Safna cikin barci taji kamar Rahma tayi k'ara amma daga baya kuma saitaji shiru, d'an tsaki tayi tareda gyara kwanciyarta .

      Safna lol🤣😜.


Nakai dubana ga agogon falon k'arfe 3:34am araina nace dukdai rashin imaninsa ai yanzu ya sarara mata, cikin sand'a na nufi d'akin amma sainaji k'ofar gam😒mutuminku fa yarufe k'ofa dankar naga 6arnar daya tafka, inagadai yana tsoron kar 'yan gidan billy ladan suji labarine sufad'ama Safna, dantanada masoya awanga gida lol.😘

      Ta kafar mukulli nasamu na d'an lek'a, kunsandai bilynku akwai d'an Karen naci, lallashi na hango bobo nayi, saboda kukan wahala da Rahma takeyi, sai saka mata albarka yakeyi  da kalaman soyayya masu sanyin dad'i, _wad'anda ba'ayima ballagazar mace adaren farko, ALLAH dai yarabamu damasu halin akuyoyi._😏

     Saida yaga barci ya d'auketa, Wanda nakeda tabbacin barcin wahalane, ahankali yazame kanta daga cinyarsa yamaida saman filo, yajawo bargo Yakuma lullu6eta sannan yamik'e.

     Fuskarsa cikeda annuri yanufi bayi domin tsarkake jikinsa.

     Hak'ura nayi nadawo falo nakwanta, ko barci awa biyu nasamu nayi, kar bobo yafito yace nacika sa ido.😏🤥.



*_washe gari._*

       K'arar bud'e k'ofarne yatadani da asubahi, bobone naga yafito daga d'akinsa sanye da jallabiya, abinda yaban mamaki shine kwankwasa kofar d'akin Rahma dayayi, bayan kamar minti biyu Safna tabud'e k'ofar.

   Kallo d'aya yaymata yakauda Kansa Dan sanye take da rigar barci iya guywa.

    Ganin bobo tsaye yasakata d'an zaro ido my jaan lfy kuwa?.

    Wani murmushin mugunta naga yamata Wanda ita bata fahimci hakanba saima wani dad'i data ratsa zuciyarta, azatonta aikin malam yafara tasiri.

    ya ce, "pls auntynmu kid'an dafa mana ruwa tunda 'yan nefa sund'auke, Dan ALLAH maid'an yawafa bara naje masallaci.

    Duk da taji wani iri dayace mata aunty, amma saita kauda tunanin aranta ta d'akko na fara'ar dayamata tamaye gurbinsa dashi, aranta ta ce, " to komi zaiyi da ruwan zafi oho?.

     

Nidai bilynku nace hummm.


Ruwan zafin Safna tanufi kicin tad'ora sannan takoma d'aki danyin sallar asuba. 

     Saida gari yad'anyi haske bobo yashigo gidan, hakan yayi daidai da fitowar Safna daga kicin d'aukeda boket dake cike daruwan zafi yanata turiri.

    Ya ce, "yauwa auntynmu sannu da k'ok'arifa, lallai wannan jiyya dakikazo tayi amfani Dan yanzune zakiyi jiyyar gsky.

   Cikin rashin fahimtar kalamansa Safna take kallonsa, ta daure ta ce, " wai batada lfy ne?.

    Kibari kawai batajin dad'in wlhy, Dan adaren jiya girma ya risketa, baijira cewartaba yad'auki boket d'in yanufi d'akinsa yana murmushinsa.

    Binsa Safna tayi da kallo cikeda so da k'auna azuciyarta ta ce, "to wane kuma irin girmane yariski Rahman?, komi yake nufi oho, shidai bazaima mutum magana sak ba saidai amurd'e tak'are zance da ta6e baki had'eda d'aga kafad'a alamar sudai suka sani.

      A d'akin bobo kuwa yanacan ya had'a ruwa maid'an zafi abayi, bayan yagama yafito tareda nufar gado Inda Rahma ke kwance tana barci, zama yayi abakin gadon kusada ita, sai faman mirmushi yakeyi, yakai hannu yana shafa fuskarta ahankali, aransa ya ce, " lallai d'an Hakim Daka raina shike tsonemaka ido, kullum yanama Rahma kallon yarinya k'arama saigashi adaren jiya tabashi dukkanin farin cikin daya dace, lallai shikam yakasance mai sa'a..

    Ahankali Rahma tabud'e idanunta dasuka kumbura saboda kuka, takai dubanta ga bobo dake zaune kusada ita yana shafa fuskarta, aranta ta ce, "dubi yanda yake farinciki babu ruwansa bayajin ciwon komai, amma ni ganinan ko motsawa banasonyi saboda azaba....... d'ago idon da bobo zaiyi suka had'a ido da Rahma, da sauri tamaida nata ta lumshe.

     Cikin muryarnan tasa mai dad'i ya ce, " aina ganki, Ashe kin tashi?.

   Itadai shiru tayi bata tankaba.

   Yad'an murmusa tareda janye bargon datake ciki.

    Da sauri tazabura zata tashi, saikuma takoma ta kwanta tana fad'in wayyo zafi.

   Saurin tallafota yayi zuwa jikinsa, yasaka hannu ya share mata hawayen dasuke zurara, cikin tausayawa ya ce, "sorry my cute ALLAH yay miki albarka kinji, lallai kinci sunanki Rahma, _Rahmar ALLAH_ nagodema ALLAH daya azurtani da samunki alokacinda banyi zatoba, Rahma kingama mallakata da komai nawa, ked'in wata abuce mai daraja daga cikin rayuwata, nabaki dukkan ragamata kijani inda kikeso kikuma yi yanda kikeso dani, daga yau *Abdulmaleek* nakine ke kad'ai da yaranmu, ina rok'on *_Ubangin Al'arshi ya albarkaci rayuwarmu ya saukar da albarka da soyayya nagartacciya mai tsafta arayuwarmu._*

    Rahma wlhy bamma San Kalmar dazanyi amfani wajen gode mikiba, saidai inaso kisaka aranki *_Abdulmaleek_* yana sonki da k'aunarki marar adadi, I luv you so much my cute, I luv you, I luv you, I luv you 4ever, yak'are maganar da sumbatar goshinta💋.

     Wani murmushine yasu6ucewa Rahma Wanda bata shirya yinsaba.

   Bobo ya rungumeta, acikin kunnenta ya ce, " lallai murmushinki ya nunamin kin kar6i soyayyata ngd sosai.

    Sunkutarta yayi sai bayi, jin asakata cikin ruwan zafi ga wani rad'ad'i daya ratsata yasakata k'an k'ameshi tana fad'in wlhy da zafi.

    Kinga yi hak'uri wannnan zafin dakikeji zai daina, idan baki shiga ruwanba akwai damuwa kinji, cikin lallashi da kalamai masu dad'i wad'anda Rahma bata ta6a tunanin bobo yanadasuba yake mata.

    Cikin hikima da dabara yagasata, saida ya tabbatar taji dad'in jikinta sannan yafito yabarta dantayi wankan tsarki.

     Katifar yajuya Dan dukta d'an 6aci da jini, yacire zanin gadon ya sauya wani.

    Babu dad'ewa itama tafito daga bayi, sai duk'ar dakai takeyi saboda kunya.

   Shi dariyama tabashi, abin sallah yashinfid'a mata, tasaka doguwar Riga da hijjaf tayi salan, shikuma yana zaune abakin gado yana jiranta.

     Tana idarwa tayi addu'a, d'an kallonsa tayi fuska a marairaice ta ce, "bacci nakeji".

         Da sauri ya ce, " zoki kwanta abinki my cute, ai yau ranarkice ke kad'ai.

   Tashi tayi tacire hijjab ta kwanta, shima yaje bayanta ya kwanta tareda rungumota jikinsa.

    Wata ajiyar zuciya tasaki, muryarta na rawa ta ce, "Dan ALLAH kayi hak'uri wlhy akwai wahala.....

    Tabashi dariya amma saiya gimtse, ya ce, " matsoraciyata kwantar da hankalinki kinji, barci zamuyi ni babu abinda zan miki.

    Dukda bata yarda dashiba amma tad'anji dad'i.

   Zuwa 'yan mintuna barci yakwashesu suduka.............






💃✈ _jirgin so zaya tashi ked'ai ake jira 'Yar gata Rahman bobo kece da sarauta._😂😂

      *Yau ranarkuce masoya Rahman bobo*❤❤❤❤😘🙋🏼




.   人

. (___)

. ┃口┃

. ┃口┃

. ┃口┃

. ┃口┃.      人.            

. ┃口┃. .-:'''"''";-.  人

. ┃口┃(*(*(*|*)*))(__)

  ┃ - ┃║∩∩∩║. |口||┃

. ┃┃┃┃┃┃┃┃┃┃. |三||┃

. ┃┃┃┃┃┃┃┃┃┃. |三||┃

​بِسْــــــــــــــــــــــمِ اللّهِ الرَّحْمَنِ الرَّحِيْم​

Its another yaomal jumu'ah! May Almighty Allah make it easy for us, purify our mind, put joy in our  hearts , increase our iman, elevate us beyond our expectations.(Amin thumma Amin.)


Juma'at mubarak.🕌🕌🕌







*_luv u oll_*

*_(((S))).....2017_*


👩🏻‍💻typing........


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣

      _•{🅱🅾🅱🅾}•_



*_NA_*

_*Bilyn Abdul*_


_sadaukarwa_

*_Abba Gana_*

*_Batul mamman_*

*_Billy giro_*



_Shafin nakune Biebie, Sawwama & Mrs Amaan gaisuwa da fatan alkairi agareku._

    Luv u so much.😘


5⃣7⃣


        *_8:30am_* Nawal tasakama Safna kuka ita wajen momynta zataje.

    Ita kanta Safna abin mamaki yake bata Dan ganin har tara saura Rahma bata fitoba, kota manta Nawal zataje makarantane?, dukda dai bobo yace mata batada lfy, amma yakamata ace tafito aii, jitai ranta yakuma 6aci, wata zuciyarta ta ce, "idan kin kwantar da hankalinki aii bobon yakusa zama naki gabad'aya.......

    Nawal ta girgizata, aunty naje wajen papa na tambayesa momyna.

   Safna tad'aga mata kai alamar eh.


Bugun k'ofarne yasakashi farkawa, bobo yaja d'an tsaki sannan ya yunk'ura yatashi da k'yar, sakkowa yayi daga gadon yanufi k'ofar, wayene yay maganar dad'an haushi.

    Nawal ta ce, " papa nice.

    K'ofar yabud'e mata tashigo sannan yamaida yarufe.

   Papa ina momyna take?.

   Bobo yanuna mata gado da hannu, da gudu taje ta haye Rahma dake barci, momyna zan makara a school kitashi ki shiryani, kuma yunwa nakeji.

   Bobo yad'an zaro ido Shifa yama manta yau akwai aiki.

    Baby ya haka? Kosai kin tada momyn nakine?.

    Rahma tabud'e idonta ahankali, ganin Nawal akanta yasa ta yunk'ura ta tashi zaune, Nawal kin tashi?.

    Eh momy tund'azu natashi nake nemanki momy yunwa nakeji, kuma ba'amin wankan tafiya school ba.

     Bobo dake tsaye yana kallonsu cikeda sha'awa yakamo hannun Nawal yana fad'in kinga kibar momynki batada lfy kinji, makaranta kuma tunda yau juma'a ki hak'ura kawai dankin makara Tara saurafa.

    Kai Nawal tad'aga MASA, tamaida kallonta ga Rahma, momy kanki keyin ciwo?.

    Murmushi Rahma tayi tareda satar kallon bobo, ta ce, "kaina keyin ciwo amma na warke.

   Momy sorry, Nawal tafad'a kamar zatayi kuka.

   Murmushi Rahma tayi tareda jawo Nawal jikinta ta rungume, karki damu babyna nawarke aii, tashi muje namiki wanka.....

     Bobo yakatseta dafad'in no kwanta ki huta bara namata wankan, itada safna saina saukesu gidan Appa suje suwuni.

   Da Sauri Rahma tad'ago tana kallonsa, ta kwa6e fuska tamkar zatayi kuka, cikin muryar shagwa6a ta ce, " nifa?."

      Zama yayi kusada ita yakamo hannunta yarik'e anasa, kinga kibarsu sutafi tunda bakida lfy, Nima bazan dad'e awajen aikinba zandawo gida muyi zamnmu.

    Nidai ALLAH inason zuwa kumafa ni lfy ta k'alau, Rahma tayi maganar tana hawaye.

    Murmushi yayi yashare mata hawayen, itadai Nawal tana kallonsu, ganin papanta na sharema momyn ta hawaye itama tasa hannu tana goge mata, ta ce, "papa".

   Bobo ya ce, " Na'am.

    Papa kabar momy taje itama kaga tana kuka.

    Shafa kan Nawal yayi tareda fad'in baby aina barta, kutashi Ku shirya idan mukaje can saimuyi breakfast.

    Sakkowa sukayi, Nawal ta ce, "momy muyi wanka a bathroom d'in papa.

   A'a baby muje namu.

   Bobo ya ce, " saboda kina guduna.

   Ahankali yayi maganar yanda Nawal bazatajiba, Dan yakula yanzu dole su iya bakinsu agaban parrot d'innan.

   Babu yanda Rahma ta iya dole suka Shiga bayinsa, bobo yabi Rahma da kallo Dan ganin yanda take tafiya dad'an d'ingishi.


Acikin 'yan mintuna suka gama shiryawa tsaf harda Safna, fitowarsu falo babu dad'ewa saiga bobo yafito cikin ash colour na shadda d'inkin zamani yayi k'yau sosai, Safna tashagala da kallonsa kuwa, jitake tamkar ta rungumeshi amma  babu damar hakan.

    Rahma tanufi kichin danta rufe k'ofa, bobo yabita da kallo dantayi MASA k'yau dukda dogon hijjabine har k'asa ajikinta, tafito tanufosu safna ta ce, "waike lfyarki kuwa kike tafiya haka?.

     Cak Rahma tatsaya amma takasa cewa komai, bobo dake latsa waya yad'ago yakalli Rahma sannan ya maida kallonsa ga Safna ya ce, " bana fad'amiki batada lfy ba.

    Okey namantafa, Safna tayi maganar cikeda rainin wayau, Dan ita bata yarda Rahma batada lfy ba.

    Bobo ya maido kallonsa ga Rahma my cute badai haka babynki zata Fita babu d'ankwaliba?.

     Rahma takalli Nawal dake zaune akujera tana wasa da filoliwa ta ce, "nabata gyale bansan INA ta ajiyeba, Nawal ina mayafinki?.

    Nawal tad'ago tana kallonta, ta turo baki ta ce, " momy nibanason gyalen Nafi k'yau ahaka.

     Tsawa bobo yadaka mata zakitashi ki d'akko kosaina zanekine?.

     Da Sauri Nawal tamik'e zatayi kuka, Rahma tarik'e hannunta kinka fad'amin bakison wancanne na canja miki wani?.

  Kai Nawal tad'aga mata tana satar kallon baban ta.

     Bobo ya harareta Yakama hangar Fita dama Safna tafita, to kinga bisu naje nad'akko miki.

    Bobo yak'arasa ga mota yabud'e yashiga, wuf Safna tabud'e gaban itama tashige, k'ala baice da itaba saima k'ok'arin tada motar dayakeyi, Nawal tabud'e baya tashiga tana satar kallonsa Dan bataso yadaketa.

     Babu dad'ewa saiga Rahma tafito da farin siririn gyale ahannunta, takulle k'ofar falon tanufosu, tunda ta taho ioon bobo na kanta jiyake wata k'aunarta nak'ara ratsashi, ga wani k'yau na musamman dayaga yau tak'ara masa.

    Koda tak'araso taga Safna agaban motar batako kallesuba takama k'ofar baya zata shiga.

   Bobo ya ce, "dawo gaba.

     Kallonsa Rahma tayi, yanda yaymaganar babu wasa afuskarsa kuma ba ita yake kalloba, a ranta ta ce, " to a INA zan zauna?, afili kuma saitayi shiru tana kallonsa.

      Ya ce, "bakijini baneba?.

     Ta ce, " naji amma a INA zan zauna?, badan Nawal dake motarba dasai yafad'i abinda zai saka Safna FASA binsu amma ALLAH ya taimaketa bazai iya kowace maganaba agaban d'iyarsa.

     Duk abinda ke faruwa Safna nagaban mota ta kacire kamar motar mijinta.

    Bobo yawatsama Rahma wani kallo, muryarsa cikeda gargad'i ya ce, "madam kina 6atamin lokacifa kuma kinsan office zanje."

       K'ofar Rahma takama tabud'e Safna tad'ago ta kalleta suka kalli juna, badai ta ce, "komaiba amma fuskarta tanuna alamar bak'inciki.

       Rahma tadaure ta ce, "aunty kifito kikoma baya Dan ALLAH.

     Cikin masifa Safna tabud'e Baki zatayiwa Rahma magana, saidai kuma komi tatuna saita FASA ta fito, tad'an bangaje Rahma tabud'e baya tashiga.

    Itama Rahman gaban tashiga.

     Bobo yagirgiza kai kawai dama yayima Rahman hakane danyafi son taringa takwatarma kanta 'yanci awajen Safna.


Ahankali yake tuk'in tamkar bayaso, wayarsace tafara wringing, yad'auka yana fad'in malam miye nawani kirana da farar Safiya?.

         Dariya ammar yayi, ya ce, "ho d'an duniya basaika nunamin ka girmaba aii.

    Shima bobo dariya yayi ya ce, " ALLAH Ammar bakada mutumci, yanzu nan nine kakecema sai yanzu na girma?.

    Hhhhhh eh mana, kaima Kasan hakane.

    Bakomai zan rama, yanzudai miye na kirana?.

   Dama zan tambayrkane ko kana office?.

    Kabari kawai wlhy namakara, yanzudai INA hanyar zuwa gidan Appa, amma daganan office d'in zan wuce.

   OK to kabiyo tanan mana idan bakada wani uzuri.

     Kai nifa Kasan banason zuwa office d'inka, wannan masu bak'ak'en kayan daka wani baza suyita kallon mutum.

   Hhhhh toka had'une shiyyasa suke kallonka, Inda basu sankabama bazasu barka ganinaba ehe, ato bara nayi zamana Idan kamatsu kazo office kasameni.

    Hhhhhh to yi hak'uri na Ammi kodayake yanzu kazama na Rahma.

   Dariya bobo yayi ya yanke wayar, baikai ga ajiyewaba kiran Ya Sulaiman yashigo, yad'aga suka gaisa.

   Bobo ya ce, "yaya dama wlhy INA niyyar kiranka, magani nake buk'ata.

    Maganinmi bobo?.

   Ummm saidai Nazo, inafata kana asibiti.

   Eh, amma kai kana ina?.

   Gani zanje gaidasu ammi, OK nima yanzu nabar gidan babu dad'ewa nida ya ishaq da Hamza.

   Ayya tosaina shigo.

   Okey, ina jiranka.

  

Bayan ya ajiye wayar yakalli Rahma kad'ain ya kauda kai, murya k'asa k'asa ya ce, " gara naje na k'ar6o miki magani wannan tafiyar taki tadawo daidai, damma kinki hak'ura ne amma yanzu haka zakije gidan Ammi kina tafiyar 'yan kaciy......

    Bai k'arasaba yay saurin rufe bakinsa da hannunsa yana dariya.

   Rahma taturo baki gaba, yakuma kallonta yashek'e da dariya.

    Ba Rahmaba har Safna da Nawal saida suka kallesa, suna had'a ido da Safna ta madubi ya gimtse fuska.

    Aranta ta ce, ''zakazo hannune malam.

    Itakam Rahma ta ce, "mugu d'an masa sai ALLAH yasakamin aii.

   Da hakadai suka k'arasa gidan AMMI.


Safna da Nawal suka fice, Rahma na niyyar fita bobo ya kulle motar, juyowa tayi tana kallonsa shima ita yake kallon, ya ce, "yadai 'yammata namiki k'yaune?.

    Kauda idonta tayi daga kansa, ta ce, " Dan ALLAH kabud'emin.

   Aidama zan bud'e miki, sonake nacemiki kiyi k'ok'ari koyaya kid'an gyara tafiyarki inba sokike kowa yasan miya faruba.

   Kallonsa tasakeyi, saikuma tayi k'asa da kai tana turo baki gaba, nifa wlhy zafi nakeji awajen.

    Shiyyasa nace ai kiyi zamanki sai gobe amma kikak'i, amma babu damuwa bara na kar6o miki magani wajen ya sulaiman, yanzudai muje ciki, amma idan kinje kiyi kwanciyarki ki huta kinji.

    Batace komaiba takama k'ofa zata bud'e yarik'o hannunta haba tawan ko sallama babu?.

    Tokai bazaka shigaba?.

   Jawota jikinsa yayi yana fad'in zan shiga mana, amma ai bazan dad'e ba, k'ok'arin saka k'wayar idonsa yake anata itakuma tak'i basa dama, saima talumshe idanunta gaba d'aya, wani murmushi yayi Wanda har tanajin sautinsa, jin bakinsa kan nata yaskata saurin zabura, amma ina tamakaro yarigada yayi nasarar cafkar harshenta.

   

Na ce, "humm bara nakoma daga waje najiraku."


Ak'alla sunkai minti biyar sannan naga Rahma tayi saurin fitowa tana murmushi, shima bobo yafito yana dariya, gaba tayi abinta hartana had'awa dad'an gudu, bin bayanta yayi yana fad'in matsoraciya kawai.

     Ak'ofar falo tatsaya ta daidaita nutsuwarta sannan tashiga.

   Gaba d'aya yaran suka taso suka tareta, itama tahad'asu tarungume tana dariya, Rahma akwai San yara shiyyasa duk inda taje saikaga yara suna sonta.

     Bobo yana shigowa suka saketa suka nufeshi, zama Rahma tayi suka gaisa da su aunty Rasheeda, aunty ummy, aunty sameera, khairiyya da khursiyyama suka gaisa.

    Bobo yak'araso shima suka gaisa su aunty Rasheeda suna tsokanarshi, Rahma dai mik'ewa tayi tanufi d'akin Ammi itada khairiyya.

    Bobo ya ce, "ALLAH idan baku daina matsaminba saina saka mazanku sun k'ara aure.

    Da sauri aunty Sameera ta ce, " a'a Abdulmaleek wlhy nikam nabari yi hak'uri, tashi yayi yana murmushi ya ce, "waiku mata miyasa kuke tsoron kishiyane?.

    Aunty Rasheeda ta ce, " jeka katambayi Rahma, d'akin Ammi yanufa yana fad'in ai ita bata tsoron kishiya.

   Dariya suka saka gabad'aya shikuma yashige d'akin Ammi da sallama.


Ammi ta ce, "a'a mukarram d'ina kaine?.

    Wlhy nine Ammi wad'ancan 'ya'yan naki duksunbi sun rainani, nakusa daina musu dariya.

    Dariya Ammi tayi ta ce, " kunfi k'asa aii.

   Shima dariyar yayi sannan yagaida Ammi cikin girmamawa, yanayi yana satar kallon Rahma dake zaune kusada Ammi suna ware wasu kaya itada khairiyya.

   Ya ce, "Ammi yunwa nakejifa.

 Kallonsa Ammi tayi tana dariya, haba mukarram aii gwauro aka sani da zama da yunwa, murmushi yayi shima, ya CE, " Ammi nima tawa matarce babu lfy."

   Ayya, Ammi tafad'a tana kallon Rahma, nima tunda tashigo nake kallonta duk naganta sukuku babu walwala sosai, ga idonta sund'an kumbura, mike damunta?.

   Sosa kansa yayi yana fad'in em...em.. Ammi zazza6ine.

    Dariya Ammi tayi ta ce, " mukarram magana da in ina kamar mara gsky.

   No Ammi inada gsky kawai inaso natuna sunan zazza6inne.

   To ALLAH yabata lfy kunje asibitine?, a'a ammi jiya da daddare zazza6in yasameta, dama yanzu zanbiya tawajen ya sulaiman na kar6o mata magani.

   Okey to Aida tayi zamanta agida tahuta ko.

   babu yanda banyi da ita tazaunaba amma fir tak'i wai itadai saitazo, yayi maganar yana kallon Rahma.

    Tana jinsu amma tashare kamar batasan zancen da akeba, Ammi ta ce, "khairiyya jeki had'omusu break fast ko, suma su Safna haka.

   To Ammi khairiyya tafad'a tana mik'ewa.


Ammi da bobo suna 'Yar hirarsu khairiyya takawo break fast, bobo yalangyare wai saidai Ammi tayi feeding d'insa.

   Rahma tad'ago ta kalleshi saiya yimata gwalo, Ammi na kallonsa, danhaka tayi murmushi had'eda girgiza kai, koba komai tasan d'anta yasamu farinciki daga matar tasa,.

   Rahma  d'auke idonta tayi daga kansa tana d'an murmushi, aranta ta ce, " Indai ta6arace kaganta salo salo ga daddyn Nawal, wani abunma idan yayi saiya baka dariya wlhy.

     Ammi kam dakanta tabama bobo abincin yaci, saida yak'oshi sannan yamik'e, AMMI bara nad'anje office naga mike tafiya.

   To ALLAH yabada sa'a  yatsareka babana.

  Amin ammina.

  Ya kalli Rahma, ya ce, "my cute nawuce.

    ALLAH yabata kunya amma saita dake ta ce, " ALLAH yabada sa'a, ameen yafad'a yana fita, idon ammi kawai yahanashi mata kiss.

    Afaloma yamusu sallama yafice.

   Da sauri Safna ta tashi tabi bayansa..................















*_luv you oll_*

*_(((S))).......2017_*


👩🏻‍💻typing........


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣

      _•{🅱🅾🅱🅾}•_



*_NA_*

_*Bilyn Abdul*_


_sadaukarwa_

*_Abba Gana_*

*_Batul mamman_*

*_Billy giro_*



5⃣8⃣

    

     Bobo dabaisan Safna nabinsa abayaba yabud'e mota yashiga, harya tada motar yaji ana kwankwasa masa gilas.

    Sauke gilas d'in yayi ahankali Dan atunaninsa Rahma ce kosu khursiyya, had'e fuska yayi Dan ganin safnace, baice komaiba ya kauda kai daga kallonta.

    Rik'e k'ugu tayi tanamai jifansa da shu'umin kallo, cikin narkewar murya ta ce, "haba my jaan wai miyasa kakeson wulak'antanine?, aiko bakomai ance kaso mai sonka, yanzu Dan ALLAH abinda kamin agaban Rahma d'azun yadace?.

            Tsaki yaja tareda yatsine fuska tamkar Wanda yaga kashi, ya ce, "ke awa? dabazan miki abu agaban Rahma ba?.

   Ya nunata da d'anyatsa wlhy kifita hanyata, karki yarda kibari na nunamiki asalin colour d'ina, ina d'aga miki k'afane saboda 'Yar uwarki, amma zakisha mamaki idan kikacigaba da bibiyata.......

    Kafin ta ce, " wani Abu yaja motarsa yafice, dama tuni mai gadi yabud'e masa gate.

    Hawaye suka kwararo afuskar safna, wani d'an lungu tasamu dagacan baya ta zauna, saida tad'anyi kuka sannan tad'auki waya takira baseera, bata d'agaba takuma kira nanma haka, ajiye wayar tayi tazabga tagumi cikeda damuwa.

   

Su Rahma suna ciki basusan bikin da akeba, bayan sungama ware kayan da ammi tasakasu suka dawo falo wajen sauran 'yan uwansu suna hira, saidai hankalin Rahma yana kan tunanin ina aunty Safna?, gashi batason tashi Dan gudun karsu fahimci halin datake ciki, tasan ko kowa bai tanka tafiyartaba sai aunty Rasheeda tayi magana, Dan tun d'azu take binta da kallo, itakam idan antambayeta batasan amsar dazata bayarba.


     Da sauri Safna ta kalli wayarta ganin Baseera CE yasa tad'auka da hanzari, ko gaisuwa bata tsaya sunyiba ta ce, ''kekam baseera ina kika Shiga haka inata kiranki tun d'azun?.

     Safna muna lectures ne, kinsan ba'a d'agama sir hamza waya idan yana lecture, waimi yahanaki zuwa school yaune?.

     Wlhy babu komai hakanan naji banason zuwa.

   Lallai kinyi wauta Dan wlhy sir hamza yayi test yanzu.

   Ke babu damuwa aii ina gidansu, kinsan ankusa bikin k'annenesu nextweek, to muna gidan ana shirye².

      Hummm ALLAH yasa yad'aga miki k'afa to, Dan wlhy ya CE........

     Da sauri Safna ta katse baseera kenifa bawannan bane damuwata, nakirakine muyi magana.

    To inajinki baseera tayi maganar tana zama kusada zeenat data fita harkarsu tuntuni dantaga sunyi nisa basa jin kira, idanma zasuyi k'ulle k'ullensu basaya akusada ita.

      Safna ta ce, "baseera wlhy inacikin matsala."

    Matsala kuma kamar ya?.

    Safana tafara zayyanama baseera abinda yafaru tundaga Daren jiya da motarta ta lalace harzuwa abinda bobo yamata yanzunnan.

     Jinjina kai baseera tayi sannan tad'an kalli zeenat dake karatu amma hankalinta na Kansu kuma tanajin duk abinda safna ke fad'ama baseera awaya, baseera ta ce, "lallai safna bakida wayo wlhy, keyanzun harya sakaki dafa ruwan zafin Gaza Rahma amma ki Gaza ganewa?, kumafa k'uru k'uru yafito yace miki Rahma tagirma amma duk Baki ganeba.

    Safna tad'an ta6e baki baseera ban... bangane kema mikike nufiba aii.

    Tsaki baseera taja tana fad'in aikin banza, asheke zaman banzama kikeyi agidan, ayanzukam kid'auka bobo yamiki nisa wlhy dankuwa adaren jiya ya angwance kenan.....

    Agaban safna yafad'i cikin masifa ta ce, " baseera karki k'ara 6atamin rai kema banason fatan tsiya, taredakefa malam da'u yacemana yaturomusu aljani dazai hana ya kusanceta.

    Baki baseera ta ta6e ta ce, "wannan zancekam yazama labari tunda bobo ya aikata hakan ajiya, saidai kuma kujira result d'in ciki.

    Kuka wuy wuy safna tasaka tana kuran tashiga uku bobo yaci amanarta itakam rayuwarta tazo k'arshe garama tamutu ta huta.

    Tsaki baseera tayi tareda yanke wayar tana fad'in 'Yar wahala keni nagaji da matsalolinki, wlhy da bobon zaice yana sona nimafa sonshi nakeyi harma nafiki Dana kula yamin nisa saina hakura, amma nakula ke kinkasa ganewa *_" ANNABI"_* yafaku, haba Dan ALLAH ayi mutum da tosashshiyar basira, idanma bakisaniba kisani dagani har malam da'un cin k'ud'inki kawai Mukeyi babu wani aiki dayake miki Dan tun farko yafad'amin komai wlhy, ya ce, "kwata kwata babu aure tsakaninki da bobo Dan bazaima sokiba.

     Zeenat tayi galala tana kallon baseera wadda da alama tamanta tana wajen shiyyasa taketa sakin zance babu (,) babu (.).

     Ganinfa da gsk tamanta tana wajen yasaka zeenat zungurar ta baseera kinsan mikike fad'a kuwa?.

     Figigit baseera ta kalleta saikuma tafara Kame kame au.. au.. Ummm zeenat dama kina nan?, Dan ALLAH kinji minake fad'a?, pls kirufamin asiri maganarnan tatsaya dagani saike Dan ALLAH, kitaimakeni Zeenat wlhy su6utar bakice.

    Girgiza kai kawai zeenat tayi tamik'e tabar mata wajen Dan wlhy yau bak'aramin tsoro baseerar tabataba, lallai maganar Sajna gsky CE datace *_wata k'awar tafi guba_*, itakam yau ta shaida akan baseera, idan bata mantaba baseera CE tasaka safna ahanyar bin malami da bokaye, amma Ashe tanacan tahad'a baki da bokayen sunacin dunduniyar safnar, ALLAH ma ya k'ara, aiduk Wanda baiji bariba yaji hoho, babu irin nasihar da bataima safna ba amma tak'i saurarenta daga Bayama daina mata magana tayi wai bata k'aunarta, toga baseerar datake d'auka tana k'aunarta d'in nan tajefata arami mai zurfi kuma mai duhu, aii duk Wanda yagagara yima iyayensa biyayya to yanatareda gamon wahala, to ita baseera CE gamon wahalarta kuwa.

     Ganin baseera tanufota yasakata saurin yin gaba.

    Da gudu baseera tacimmata kuwa.


A6angaren Safna kuwa baseera tana Yanke wayar tAk'ara sautin kukanta, tama rasa wane irin sambatu zatayi?, amma jitake Duk duniya babu Wanda ta tsana kamar Rahma arayuwarta, jitake zata iya kashe Rahma wlhy, afili ta ce, "wlhy natsaneki Rahma, natsaneki tsana irin wadda banta6ama wani mahalukiba, Rahma kin cuceni kedasu Ya Shaheed munafukai kawai, duk bakwa sona nimakuwa natsaneku bana sonku harma ya munnir d'in dasu ummi dukna tsaneku, kuka take Rurus da sambatu.


Zeenat Dan ALLAH ki saurareni pls.

    Mizaisa na saurareki baseera?, aini yanzu kinfi k'arfina wlhy, keba k'awar rayuwa bace, tunda har kika iya cin amanar safna data d'auki sirrinta Dana gidansu tabaki duka, tonikam sai yaya kenan?, ALLAH abin tsoro kema baseera dole aji tsoron kaidinki, kecefa kika jefa rayuwar Safna a halinnan amma Ashe kina gefe kina cin dunduniyarta, haba baseera miye ribarki Dan ALLAH?, tundaga sanda iyayen safna sukace sun mata miji kika Shiga kika fita kika kanainaye rayuwarta, kin hana afad'a mata gsky bare ta fahimta, saboda son zuciya irin naku yanzu kun koma danku 6ata rayuwar auren k'anwarta, haba baseera kashe aurefa ba abin wasa bane, *_"ALLAH ne ya halatta aure da saki, amma shikanshi bayason sakin aure, duk  sanda igiyar aure ta katse sai al'arshin ubangiji ta girgiza saboda kad'uwa, shaitan yakanyi farinciki awannan rana saboda yaraba aure, shin kuma kunaso kuzama daga jerin shaid'anu?."_*

   Wlhy kuji tsoron ALLAH kutuba tun kuna da dama, idan kuka bari damarku ta su6uce kunci amanar kanku, kutuba tuba na gsky ALLAH zai iya yafe muku *_"domin shi gafurun rahimunne, kuma maji6incin al'amuran bayine."_*, kuma godema ALLAH daya fargar daku da wuri Dan yana sonku da rahmarsane.

    Tunda zeenat tafara maganar baseera kuka takeyi, tabbas ta tafka babban kuskure kuma sharrin shaid'anne, wlhy tayi nadamar halayenta, tarik'o hannun zeenat tana hawaye ngd sosai zeenat kin tunatar dani abinda ban saniba kuma ngd wlhy kinsamu ladana Dan nayi nadamar abinda na aikata, kuma daga yanzu insha ALLAHU zan tuba, zan samu Safna na warware mata dukkan k'ulli, amma inaso ki taimakamin da nuna mata hanya itama, Dan inaso yanda natuba na dawo hanya itama ta tuba ta gyara kodan mugudu tare mu tsira tare.

    Jinjina kai zeenat tayi tana murmushi had'eda sharema baseera hawayenta, karki damu 'Yar uwa ngd Nima dakika fahimceni kika kuma gane abinda nake nufi, ALLAH ya yafe mana gabad'aya ya kar6i tubanmu, ALLAH yasa mufi k'arfin zuciyarmu, ina fata yanda kika fahimta da wuri ALLAH yasa Safnama ta fahimta d'in.

   Ameen zeenat ngd.

   Karki damu muje Dan sir koba hakabane,😜 yakusa Shiga mana, muje muk'arasa lecture d'in muwuce gida.

    Jinjina kai baseera tayi tana murmushi suka kama hannun juna suka nufi holl.

    

😁 _wlhy abinda yaburgeni kuma yamin dad'i masu karatu, ALLAH yasa safna itama ta fahimta kamar yanda baseera tagane kuma ta tuba.🙏🏻ameen._


Su Rahma duk suna kichin suna aikin soya cincin d'in gara, amma jitake zazza6i yana neman rufeta, ga k'asanta yana mata zafi har yanzu ko motsi bata sonyi ma, Ammi dake kallonta tun d'azun ta ce, "Rahma yaya dai?.

     Murmushi yak'e Rahma tayi ta ce, " babu komai Ammi."

    Aunty Sameera ta ce, "kai Rahma bakida lfy gsky, tun d'azun nima ina lura dake, aunty Rasheeda ta ce, " wlhy nima nakula tundama tashigo batada walwala kamarma tana d'ingishi, kokinji ciwo ak'afarne?.

    Shiru Rahma tayi kanta ak'asa, jitake duk kunya ta isheta, itakam bobo yaja mata, yanzu hakama kowa yagane abinda yafaru........

    Ammi CE ta katse mata tunani dafad'in tashi muje kisha magani.

   Ahankali Rahma tamik'e tana duk'ar da kai, duk sukai mata sannu amma banda safna, azuciyarta ma sai tsinema Rahma takeyi.

    Kama hannun ta Ammi tayi suka nufi d'akinta, ta zaunar da ita abakin gado sannan itama ta zauna tana fuskantarta, kallonta take cikeda nazari, ita kam Rahma kanta na k'asa tana wasa da zobenta.

   Rahma kodai fad'a kukayi keda mukarram d'in?.

    Girgiza kai Rahma tayi ta ce, "a'a Ammi bamuyi fad'aba."

    To mike damunki?.

    Ammi babu komaifa k'afatace kemin ciwo, shuru Ammi takumayi tana kallonta, zuwa can ta ce, "fad'uwa kikayine?, a'a, to ciwo kikaji kenan?.

   Eh, Rahma tafad'a cikeda kunya, ga hawaye suncika idonta taf, bata fata ammi tasake tambayarta wani Abu kuma bayan wannan Dan batasan mizataceba kuma.

   Ammi ma batasake cewa komaiba Dan sai yanzu tafahimci komai, amma tayi mamakin hak'urin mukarram dahar ya iya barin Rahma har zuwa yanzun, dawani yagaya mata bazata yardaba, amma gashi tagani da idonta, koda yake tasan duk cikin 'yayanta babu Wanda yakai mukarram kawaici saidai zuciya da masifar tsiya.

   Bayi tashiga tahad'a ruwa mai zafi tareda magunguna masu k'au cikin wad'anda takema su khairiyya gyara, fitowa tayi tana fad'in Rahma taso kigani.

    Rahma tamik'e tamkar wata muna fuka tanufi Inda ammi take tsaye, bayi ammi tanuna mata da hannu, kishiga ruwa na nan aroba kicire kayanki saiki shiga ruwan, amma saikin daure Dan yanada d'an zafi, idan yahuce kikuma Tarar wani ga maganin nan ajiye aroba saiki kuma shiga kinji, shima saiya huce insha ALLAHU k'afar zata daina ciwo sannu, nima idan k'afata na ciwo dashi nake amfani.

     Sanyi Rahma taji aranta Dan duk tunaninta Ammi taganene, amma dataji tace itama dashi take amfani idan tana ciwon k'afa saitaji dad'i, risinawa tayi Tanama Ammi godiya.

    Ammi tayi murmushi tana fad'in aii babu godiya tsakaninmu Rahma, kud'inma 'ya'yanane, matsayinku d'aya dasu mukarram araina.

    Murmushi Rahma tayi tashige bayi tanamai jin k'aunar tsohuwar aranta, itama jinta take tamkar umminsu.


    Ammi tana niyyar fita saiga ya hamza da bobo sunshigo d'akin da sallama.

   Baya ammi takoma tana musu sannu, suka gaisheta sannan suka zauna abakin gado, shi boboma kwanciya yayi, Ammi ma zamatayi saman kujerar d'akin tareda jawo k'atuwar ledar dasu bobo suka ajiye, miye kuma anan?.

    Ammi d'unkunanmune wlhy muka amso cewar bobo dake kwance male male agado.

    Ammi tayi murmushi a alallai manyan yayye sun shirya, harkun kama d'inkinku ahannu?.

    Ya hamza yay dariya to Ammi aigara haka, inba hakan mukayiba aiki cud'e mana zaiyi, Dan kinga daga yau babu hutu, sauk'inma banida lectures gaba d'aya satin nan, boboma nashi mai sauk'ine tunda zai iya d'aukar Hutu, ya sulaiman da ya ishaq nedai babu dama.

    Hakane amma aii ansamu sauk'i tunda gaku, ALLAH dai yayi muku albarka.

    Ameen Ammin mu.

    Ammi appa bai dawoba?.

   Eh bai shigoba, k'ila yau a can zaiyi sallar juma'a Dan yacemin sunada meeting.

   Okey nima bara naje gida nayi wanka to kafin su ya ishaq su taso.

   To shikenan saika dawo.

   Bobo ya ce, "saika dawoto, bara nayi barci kona minti30 ne, plz idan kadawo katadani.

    Humm ALLAH ya shiryaka kaikam, to kana nufin bazakayi wankan masallaciba?.

   Ah zanyi mana, nikasan inada kaya anan gidan, to Dana tashi zand'an watsa ruwa na shirya, kafinma ad'akko yara school amusu wanka ashiryasu aina d'an huta.

    Dariya ya hamza da Ammi sukayi, ya hamza ya ce, " Ammi wannan autan naki bansan yaushe zaisan yagirmaba?.

   Bobo ya ce, "babu wani auta, kana ina ammi ta tureni daga sannan kujerar ta d'ora hibba.

   Yanda yay maganar cikin shagwa6a yasaka Ammi da ya hamza yin dariya, ya hamza yafice yana fad'in bara na dawo sai azauna shari'a.

   Ammi ma mik'ewa tayi tafice zuwa kichin tana dariya.

 

Bobo yagyara kwanciyarsa yana murmushi, arayuwarsa yanason rayuwar irinta gidansu, Inda ace hakane akowane gida toda zuminci bai lalaceba, ALLAH yak'arama amminsu da Appa tsawon kwana.


   Na ce, " ameen.


Lumshe idanu yayi dansonyin barci, baisan Rahma tana d'akinba.

     Itakam tanad'anjin hirarsu sama sama, daga baya taji shiru duk zatonta sunfita gaba d'aya.

       Tamik'e daga cikin ruwan da ammi tahad'a mata Dan har ya huce, wani takuma had'awa kamar yanda ammi ta umarceta, tasake shiga, nanma takai minti 15 aciki ruwan yana ratsata, yanzukam taji dad'i sosai, harma jitake wajen yabar zafi, wanka tayi kawai tafito.

    K'arar bud'e k'ofarne yasaka bobo bud'e ido ahankali ya sauke akan Rahma.

   Sosai yakuma bud'ewa Dan yayi mamakin ganinta, dama tana band'aki tun d'azun amma tayi muk'us kamar babu kowa?.

     Shiru yayi bai motsaba Dan yakula batama gansaba.

    Aiko Da gsk Rahma bata kula dashiba, tasa k'aramin tawul tatsane jikinta, jinta take wasai yanzun kamar iska zata d'auketa, kujerar madubi taja ta zauna tana mai fad'in kai ALLAH yabiyaki Ammi, Ammi uwa tagari, dabadankeba k'ilan saina had'a sati ina fama dazafin wajennan Dan wlhy ciwo yakemin, ALLAH yak'aramiki tsawon Rai Amminmu Dan zuciyata kullum k'ara k'aunarki takeyi wlhy.

    Murmushi bobo yasaki danjin furucin Rahma ga mahaifiyarsu, jiyayi sonta yak'ara nunkuwa azuciyarsa.

    Itadai hidimar shafa manta takeyi harda yaye yawul Dan ko kad'an hankalinta baikai akanshiba, tsaf tagama sannan tad'an gyara fuskarta dukda bawata kwalliyar kirki tayiba amma tayi k'yau.

    Kayan su data d'akko ta d'auka tasaka, tayi d'as cikin siket da rigar na farin material mai d'igo d'igon bak'i.

    Bobo dai yana kwance yana kallon ta cikeda k'auna, baimasan sanda yafurta woow my cite kinyi k'yau.

    Arazane Rahma tajuyo tana kallonsa, tako wage baki zata tsala ihu Dan ita azatonta aljanine yay shigar siffar bobo yazo mata.

    Da sauri bobo yajawota yarufe mata baki da lallausan tafin hannunsa...............











*_luv you oll_*

*_(((S))).......2017_*

👩🏻‍💻typing........


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣

      _•{🅱🅾🅱🅾}•_



*_NA_*

_*Bilyn Abdul*_


_sadaukarwa_

*_Abba Gana_*

*_Batul mamman_*

*_Billy giro_*


*_duk Wanda yasake d'aukar number ta yay amafani da'ita ta hanyar dabata daceba, dasakani a group d'in banza, ko turomin sak'on banza ta PC ALLAH ya Isa ban yafeba, nabarsa da  ALLAH shine zai sakamin, tunda nayi magana harna gaji ank'i bari._*

😭😭😭😭😭😭


5⃣9⃣


      "K!, 'yammata karki taramin mutane mana, bobo yay maganar yana mai matse Rahma ajikinsa.

     Sotake ta kwace kanta amma yak'i bata damar haka, ganinfa kamar da gsk atsorace take dashi yahad'e bakinsu waje d'aya, wata sassanyar ajiyar zuciya Rahma tasaki saidai har yanzun jikinta baibar k'yarmaba, saima k'aruwa dayayi Dan ayanzun ta shaid'a lallai bobone, to amma baya gudun Ammi tashigo tagansu?, kokuma wani daga cikin matan yayyensa.

    Mintsininsa take amma yak'i sakinta, dole tahak'ura tazubama sarautar ALLAH ido wadda ta girma ta d'aukaka, daga kiss yafara kauce hanya, ayanzukam bazata iya jurewaba musaman idan ta tuno da azabar datasha adaren jiya wadda har safiyar yau wajen namata rad'ad'i, iya k'arfinta take turesa amma mutumin naku ko gazau sak'wanni kawai yakai son isarwa cikin nuna k'warewa.

   Hawayene suka fara zurara akumatun Rahma Dan ayanzu kam batada wata hanyar ku6ta saidai kuka dan shikad'aine yarage mata.........

       Da gudu khairiyya da khursiyya suka shigo d'akin suna kwala kiran aunty Rahma! Aunty Rahm.........

    Suduka maganar tamak'ale amak'oshi Dan ganin abinda yafi k'arfinsu.

   Shima da sauri bobo yabar abinda yakeyi yad'ago, yayinda Rahma ALLAH yabata nasarar mik'ewa daga jikinsa.

     Bobo ya k'ank'ance idonsa dasukayi jaa yana kallonsu khairiyya dasukayi tsuru²,  yasan tabbas idan yayi magana saiya fallasa asirin muryarsa, to amma bazai iya k'yale yarannanba.

     Rahma tara6a tagefensu khursiyya zata fice yace karki fita.

   Cak tatsaya cikeda mamakin wannan k'arfin hali irinnasa.

    shikam kallonsa yamaida akansu khairiyya ya ce, "ku bakuda hankali Baku iya sallamabane idan zaku shiga waje?.

    Yaya wlhy bamusan kana nanba munzata ita kad'aice Dan ALLAH kayi hak'uri bazamu sakeba.

   Le6ensa yacije yama rasa mizaice musu, tsaki kawai yayi dallah kutashimin kai shashashu, haka za a kaiku gidan miji kunama mutane shirme.

     Da sauri sukayi waje, suna fita khursiyya tarufe bakinta da hannu ta shek'e da dariya, itama khairiyya dariyar tasaka, suka tafa suna cigaba da dariyarsu, saidai sukayi mai isarsu sannan khairiyya ta ce, " kai ya bobo an iya mazuran rashin gsky, nakulafa yama rasa mizaice manane shine ya koromu, dariya suka kama tuntsurewa da ita.

      Khursiyya ta ce, "yar uwa yau naga ruwan soyayya, dama irinsu ya Abdulmaleek akwai iya soyayya, amma akwai dai mazuran tsiya, badan karyaci ubanaba wlhy saina koma naga mi akeyi yanzu.

    Idanu khairiyya tazaro ta ce, " tabd'i wlhy badaniba, kingama tafiyata baza'a kaini gidan miji da karyayyar k'afaba, haka kawai su sunacin tasu soyayyar da allura ni akaima mijina jiyya yakasa nunamin.

    Rahma dake bayansu ta ce, "ALLAH ya shiryaku wlhy.

    Da sauri suka juyo ganin Rahma yasasu nufowa gareta harsuna 'Yar rigerigen tambayarta ya aikayi tafito?.

      Hararar wasa tamusu ta ce, saiya fito yaritsaku wlhy.

    Da sauri suka bar wajen itakuma tabi bayansu tana murmushi.


      Tundaga wannan lokacin Rahma bata sake bari sun had'a hanya da bobo ba har dare lokacin tafiyarsu yayi.

   Bansan miya faruba Ammi tace safna tayi zamanta anan danta tayata wasu ayyukan.

   Ina kallon bobo yayi wani murmushi mugunta, Rahma dai batace komaiba, Safna kam jitayi tamkar tafasa ihu Dan Bak'inciki.

   Rahma ta ce, "ina Nawal mutafi.

   Kinga d'iyata kuyi tafiyarku tunda weekend za'a shiga kuma dukan yaran nan za'a barsu.

   Jiki a sanyaye Rahma ta ce, " to Ammi saida safe.

    ALLAH yakaimu d'iyata kinji.

  Tunda suka fita bobo yake wata 'Yar dariyar mugunta k'asa² itadai Rahma batace dashi k'alaba saidai jikinta duk yayi sanyi.

   Da kansa yabud'e mata motar tashiga, shima yazagaya yashiga, har suka fice daga gidan baikuma cewa k'alaba, bayan yahau babban titi yana tuk'i ahankali yad'an juyo ya kalleta ya ce, "matsoraciya har an hau network d'in tsoronne?.

    Shiru tamasa kamar batajiba, murmushi yayi yasaka hannunsa d'aya yakamo nata yana murzawa, d'ayan kuma yana tuk'i dashi, batace masa komaiba bakuma ta hanashi abinda yakeyiba.

    Wai baza'amin maganaba ne my cute?.

    Idanunta tad'ago ta kalleshi ganin hankalinsa nakan titi yasa takauda kai, miye kuma kike kallona?, bobo yay maganar har yanzu idanunsa atiti.

     Nifa ban kallekaba, Rahma tafad'ad'a kamar zatayi kuka.

   Humyim yarinya zaki maganane, ainasan hanyar dazansaki maganar bara mu Isa gida dai kigani.

    Gaban Rahma ne yafad'i, saikawai hawaye yafarabin kumatunta, aranta ta ce, " wlhy ka k'aramin irinna jiya mutuwa zanyi.

   Karya kwana yayi yashiga layin gidansu, anguwar shiru babu kowa sai haushin karnuka, yay hon mai gadi yabud'e masa gate bayan sun gaisa yashige ciki damotar.

    Yana tsayawa ko kashewa bata tsaya yayiba tayi wuf tafice, sauri sauri gudu gudu tashige ciki bayan tabud'e k'ofar falon, kafin yak'araso harta shige d'aki ta kulle kanta.

    Tabama bobo dariya danhaka yashige d'akinsa yana wata 'Yar dariya.

      Tana Shiga d'akin tadafe k'irji tanama kanta dariya, wata zuciyarta ta ce, "kai Rahma akwai tsoro?, yo badole naji tsoroba, wlhy nabari mutuminnan idani zaiyi, afili tayi maganar Tanana kanta dariya.

      Wanka ta shiga  bayan tagama ta d'auro alwala tafito, shirin barci tayi sannan tahau abin sallah tayi shafa'i da wutiri, tayi addu'ointa tamik'e, aranta tana fad'in yaudai ba'a nemi shayin k'addaraba.

     Gado tahaye ta kwanta hankalinta kwance taja bargo ta lullu6a.


Shimadai bobo yana Shiga d'akinsa wankan yashiga, yay shirin barci tsaf, duk abinda yakasance al'adarsa yagudamar sannan yajawo laptop akahau aikin k'a ida.

     Har wajen k'arfe d'aya yana gaban laptop sai biyu saura yad'ago yana kallon agogon dake d'akin, mik'a yayi tareda hamma, yarufe laptop d'in yamik'e, dirowar gefen gado yabud'e ya d'au key da wayoyinsa yakashe fitilar d'akin yafice.

     d'akin Rahma yanufa yasandai yanzu tayi barci, ahankali yabud'e k'ofar yashiga yamaida yarufe, kallonta yayi kwance akan gado ta k'udindine abargo, aransa ya ce, " yarinyar nan sai abarki, gakida bargo na gsky mai  laushi kin 6uge da shiga bargon bogi.

    Wayoyinsa yazube adurowar gefen gadon yahau yakwanta ahankali, bargon ya janye yashige ciki tareda rungumeta a faffad'an k'irjinsa mai yalwar k'amshin turare.

    Ahankali yasauke ajiyar zuciya tareda lumshe idanu, Alhmdllh yafad'a azuciyarsa.

      Rahma kam dabatasan yanayiba takuma gyara kwanciyarta sosai a k'irjinsa, ahankali tarink'a sauke numfashi mai d'umi ak'irjinnasa.

    K'ara lumshe idanu yayi yana mai lashe la66ansa da k'yar ya iya control d'in Kansa yay barci.


_washe gari_

        Da asuba Rahma tariga bobo farkawa, jinta kamar ajikin wani Abu yasakata saurin bud'e idanu, ganin bobo yasakata zare k'yawawan idanunta, aranta ta ce, "to yaushe yashigone?, mutum tamkar aljani?, k'yak'yk'yawar fuskarsa tazubama idanu, aranta ta ce, " mutumin nan akwai sirrin k'yau, babu Abu mafi d'aukar hankalinta ajikin bobo kamar Sajensa, tanason sajensa sosai danya k'awata sirrin k'yawun fuskarta, ahankali talumshe idanunta tareda kai hannu bisa k'yakykyawar fuskarsa tana shafa sajensa daya kwanta luf luf yanata tashin k'amshi mai dad'i kamar yanzun yasaka masa turaren.

     Tunda tafara shafa masa fuska yafarka, ta k'asan ido yake kallonta, aransa ya ce, "ALLAH yabani magulmaciyar mata, anasona ana kaiwa kasuwa, Rahma tajanye hannunta tana murmushi Dan duk zatonta bai tashiba, k'ok'arin zare jikinta tafara daga NASA, jin haka yasa bobo k'ara rungumota, acikin kunnenta ya ce, " guduwa zakiyi kibarni?.

    Shiru tayi wai ita a adole barci takeyi, ya ce, "humm nizakima pretending? Bayan kingama shafemin fuska kina shauk'i?.

    Rahma ta cusa kanta ak'irjinsa tana dariya k'asa k'asa, shima dariyar yayi ya ce, " oh ni dama matana ta iya gulmar soyayya saikace matar k'auye?.

   Itadai luf tayi ajikinsa Dan kunya.

   Jin ana kiran assalatu yasashi yunk'urawa yatashi da ita ajikinsa, to madam pretending tashi muyi sallah.

    Zame jikinta tayi daga nasa batareda tad'ago ta kalleshiba, shimadai mik'ewa tayi yashiga bayinta ya d'auro alwala, Inda take ya iso yana gyara  hannun rigarsa daya nannad'e saboda alwala, sunkuyowa yayi yasumbaci kumatunta sannan yafice yana fad'in saina dawo.

     Batace komaiba saidai tasaci kallonsa tagefen ido tana murmushi, yana fita tatashi itama Dan d'auro alwala.

   Saida yaje d'akinsa ya canja kayan barcinsa zuwa doguwar Riga sannan yafice masallaci.


Saida gari yayi haske sannan bobo yadawo, lokacin Rahma ma tana zaune akan sallaya tana addu'a bayan ta k'arasa karatun alkur'ani.

    Zama yayi suka shafa addu'ar tare.

   Kan Rahma ak'asa ta ce, ''ina kwana?."

    Bazan amsaba saikin kalleni.

  Murmushi tayi tareda rufe idanunta da tafin hannu, kamata yayi yamik'ar tareda zare hijjabin sannan yajata suka zauna a bakin gadon, my cute wai ita wannan kunyar bazata raguba haka?, nafa rage kusan 60% acikinta amma ank'i nunamin hakan.

   Murmushi tayi kawai batareda tace komaiba, ya ce, "idan kinaso nakaiki gidan Appa yau saikin kalleni, yafad'a yana tsura mata mayun idanunsa.

   Ahankali tad'ago k'yawawan idanunta masu kasheshi ta sauke akansa, kallon ido cikin ido sukema juna, suduka sunshagala cikin shauk'in so, bobo yad'an lumshe idanunsa yabud'e ahankali, cikin muryarsa mai dad'i ya ce, " ina k'aunarki dayawa Rahma, tabbas da ubangiji bai sauya al'amuraba danayi asarar rashin kasancewarki matata, ALLAH na gode maka dakamin wannan k'yauta.

    Rahma talumshe fararen idanunta, ta ce, "nice na cancanci gidema ALLAH ya *_Abdulmaleek_*, kaid'in namijine mai wahalar samu acikin maza, zanta godema ALLAH har k'arshen numfashina da kasancewarka mijina, Nawal d'iyata, tabbas kai alkairine ga rayuwata, hawaye yafara bin kumatunta na dad'i......

    Ganin haka yasaka bobo fara bata Sumba ako ina najikinta, saida ya yamutsata San ransa, itakam dukda tsoron dake cikeda ruhinta haka tadake zuciyarta tana kar6ar sak'wanninsa.

   Rungumeta yayi yana sauke numfashi asarek'e, muyi barci yafad'a ahankali yana gyara mata kwanciya.

     Shiru tayi kamar tana barcin, shikam bobo mintuna kad'an barcin yay awon gaba dashi, ganin barcinsa yayi nisa tazare jikinta ahankali tamaida masa filo a madadinta.

    Ficewa tayi domin had'amusu breakfast.

    Cikin 'yan mintuna ta kammala komai ta gyara ko ina yad'auki k'amshi, abayinsa tayi wanka sannan tadawo d'akinta, mai tashafa tayi 'Yar kwalliya yau harda jambaki tasaka, aiko tayi k'yau tamkar kasaceta kagudu.

     Siket dariga tasaka na atanfa fara da adon jajayen fulawoyi.

   Masha ALLAH nafad'a araina Dan babu k'arya Rahma tahad'u.

   Kum tad'auka tana taje kanta, wani d'an ruwa daya d'id'd'iga asaman gashin yafara tsalle harya sauka akan fuskar bobo.

    Bud'e ido yayi ahankali yasauke akan Rahma dake tsaye agaban madubi tana faking d'in gashinta da jan ribom.

   Lumshe ido yayi yabud'e yana murmushi aransa yace masha ALLAH.

    Itakam dabatasan yanayiba tad'auk'i d'ankwali ta tayi d'auri mai k'yau na zamani, tad'auki 'yan kunne jajaye tasaka sannan takuma feshe jikinta da turarenta.

    Juyowa tayi danufi fita saitaga idon bobo akanta, hannu tasa tarufe fuska tana 'Yar dariya, shima mik'ewa yayi zaune yana murmushi, yatako ahankali zuwa gabanta, hannunsa biyu yasaka yarik'o k'ugunta, muryarsa anarke ya ce, "beautiful Lady kinyi k'yau sosai, shine kikamin wayau ko?.

    Girgiza masa kai tayi haryanzu hannunta nakan fuska.

   Ya ce, " to bud'e fuskar naga kwalliyar tawa ko?, akunyace tacire hannunta, woow my beautiful wife kwalliya namiki k'yau amma bak'yasonyi, todaga yau haka nakeso aringa tsantsaramin wadda zata ringa hanani fita office.

   Yabata dariya Dan haka tatuntsure da dariya, shima dariyar yayi tareda rungumeta, bayan sund'an sarara ya ce, "to muje nima kimin wankan.

   Idanu tazaro waje ta ce, ''rufamin asiri."

   Asirinki arufe yake aii, shima yafad'a yanad'an zaro ido kamar yanda tayi.

  Murmushi yayi, shikuma yafita yana fad'in tom bara naje nayi my cute, amma next time bazan d'aga miki k'afaba.

    Murmushi Rahma tayi tareda d'aga hannunta sama tana fad'in ALLAH ngd maka daka daidaita al'amurana alokacin dabanyi zatoba.

     d'akin tahau gyarawa cikin lokaci k'alilan takammala takoma falo tazauna jiransa yafito.

     Shima baid'auki lokaci mai tsawoba yafito cikin k'ananun kaya wando 3½ da k'aramar Riga tashan iska duk farare tas, yasaka Jan silifas ak'afarsa, sai zabga k'amshin turarensa yake na alfarma.

   d'agowa tayi tana kallonsa, yasakar mata murmushi itama ta mayar masa tareda mik'ewa, a dinning suka yada zango, tazuba musa abincin tana k'ok'arin zuba nata yarik'e hannunta tareda mata magana da ido.

   Zama tayi danta fahimci inda yadosa, indai tak'aice muku dakansa yabata abinci itama tana basa, haka sukaci suka k'oshi tagyara wajen suka dawo falo suka zube.

    Rahma takalli bobo ta narke murya, wai bazamuje gidan AMMIN ba?.

    Ido d'aya ya kanne mata, ya ce, "a'a yau zamu huta agida musha soyayyarmu my cute.

   Baki taturo kamar wata bebyn roba.

   Zamewa yayi yakwanta bisa kujera yana murmushi.

    Sallamar da akayice takatsema bobo maganar dayayi niyyar yi......

    Rahma ta amsa tana maida kallonta ga k'ofa, ta ce, " kushigo.

    Zeenat da baseera suka shigo da sallama, mik'ewa Rahma tayi taje ta tarbosu cikin farincikin ganunsu, zeenat ta ce, "oh ni Autar ummy amare.

    Hannu Rahma tasa tarufe fuska tana fad'in kai aunty zeenat, baseera ta ce, " Yar lukutar ummi kin k'ara kibafa, aunty baseera kema hadake ko?, Rahma tayi maganar cikeda shagwa6a.

    Dariya sukayi tareda k'arasawa cikin falon, baseera da zeenat suka kalli juna Dan basuyi zaton bobo yana nanba.

    Zama sukayi suna gaisheshi, baiko kallesuba ya amsa da lfy amma fuskarsa asake, mik'ewa yayi yana fad'in yakuke?.

   Sukace lfy lau wlhy.

    Fita yayi harabar gidan danya basu waje, dandanan Rahma tacika musu gaba da kayan ciye ciye, ta zauna suka gaisa.

    Zeenat ta ce, "nibanji motsin mutuniyarba.

   Wai aunty safna?.

Sukace eh.

   Lah tana gidansu ya Abdulmaleek aii, a can takwana wlhy. Dama tunda naganku nasan zuwantane tunda Baku ta6a zuwaminba.

     Dariya sukayi baseera ta ce, " a'a dama gunki mukazo ko zeenat, gyad'a kai zeenat tayi tana dariya.

    Daganan hira sukashigayi, bayan kamar minti30 suka mik'e tareda alk'awarin suma zasu halarci bikinsu khairiyya d'in.

    Godiya tamusu tarakosu har harabar gidan, bobo nasaman mota zaune, suka masa sallama sannan suka tafi.

    Dirowa yayi daga saman motar idonsa akan Rahma, batayi auneba taji yad'auketa cak kamar jaririya yanufi  cikin falon da ita.

    Direta yayi saman doguwar kujera suna dariya, yakwanta tareda d'ora kansa saman cinyarta suna kallon juna, ya ce, "wad'an nanfa daga ina?.

    K'awayen aunty Safna ne?.

   Baice komaiba, saima ya kauda zancen da d'akko wani daban.................







*_"Dan ALLAH duk masoyina yamin addu'a acikin sallarsa, ALLAH yabiyamin buk'atata ta alkairi, yakuma azurtani da abundana nake buri na alkairi."_*

😭😭😭🙏🏻🙏🏻🙏🏻






*_luv you oll_*

*_(((S))).......2017_*


👩🏻‍💻typing........


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣

      _•{🅱🅾🅱🅾}•_



*_NA_*

_*Bilyn Abdul*_


_sadaukarwa_

*_Abba Gana_*

*_Batul mamman_*

*_Billy giro_*


*_duk Wanda yasake d'aukar number ta yay amafani da'ita ta hanyar dabata daceba, dasakani a group d'in banza, ko turomin sak'on banza ta PC ALLAH ya Isa ban yafeba, nabarsa da  ALLAH shine zai sakamin, tunda nayi magana harna gaji ank'i bari._*

😭😭😭😭😭😭


6⃣0⃣


      Wunin ranar gaba d'aya haka bobo da Rahma suka kasheshi asoyayya da tattalin juna, dukda Rahma tanad'anjin kunyar bobo har yanzu.

     Ganin shiru basuzoba Ammi takira bobo tana tambayar ko jikin Rahmar ne har yanzu?.

    Cikin Sosa kai na jin kunya ya ce, "a'a ammi taji sauk'i bamuzoba daine kawai, sai gobe idan ALLAH ya kaimu.

   Murmushi Ammi tayi ta ce, " toshikenan ALLAH yakaimu goben tunda dai lfy Alhmdllh, ka gaishemin da ita

   To Ammi zataji.

  Rahma dake kwance ajikinkinsa ta ce, "ya Abdulmaleek ko kunya bakajiba Dan ALLAH.

    Murmushi yayma tareda fad'in kunyar wa zanji?.

   Ta Ammi mana.

Nanma murmushin yasakeyi batareda yace komaiba.



.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.*.

       Shirye shiryen biki ya kankama sosai, hidima akeyi babu kama hannun yaro.

    Rahma da bobo kan sai godiyar ALLAH, soyayyarsu suketa zubawa kamar babu gobe, amma dai baisake mata komaiba Dan yana tausayinta sosai, kuma bobo ba irin fitunannun mazan nan baneba, tattalikam tana shansa, azuciyarta har mamakin bobo takeyi Dan bata ta6a tunanin yanada sauk'i hakaba, ada tana masa kallon muskili masifaffe.

   Amma yanzun data k'ara kusanci  dashi saitaga Bahaka bane, dukda yanada fad'a amma sai anta6oshi yakeyi.


Safna kam abin duniya ya isheta, k'iri² Ammi tahanata komawa gidansu Rahma, kayantama ranar gabad'aya bobo yakawomata gidan Ammi, bak'aramin 6aci ranta yayiba dantasan wannan Duk shirin bobone.

    Yau tunda safe take tsumayensa amma yak'i zuwa gidan kamar yanda yasaba, suna zaune itadasu khairiyya dake had'a kayansu saboda daga gobe shagalin biki zai fara.

    Kad'an kad'an saita lek'a window d'akinsu khairiyyar Dan daganan ana hangen Wanda zaishigo gidan, ta kalli agogon hanunta tareda yin tsaki.

    Khursiyya ta ce, "aunty safna lfy kuwa?.

    Murmushin yak'e tayi tareda wayancewa ta ce, " wlhy ya Abdulmaleek nake jira sonake nakar6i sak'o awanjensa.

   Su khairiyya basu kawo komaiba aransuba sukace ayya k'ila yanacan yana shan sharafin soyayarsama, kinsan su ya Abdulmaleek sai addu'a, k'ila kuma bazaizo gidanba saiya tashi daga aiki Dan wataran haka yakeyi.

    Dammmmm safna taji gabanta yafad'i, azuciyarta ta ce, "soyayya kuma?, wani kululun bak'in ciki yatokare mata mak'oshi ta had'iyeshi dak'yar, zamewa tayi takwanta visa gadon su khursiyya tana sauk'e ajiyar zuciya wadda su bama sukulaba hankalinsu nakan rigima akan wani wandon jins dakowa ya ce, " yanaso sukahau kokawa, can ALLAH yabama khursiyya sa'ar kwacewa daga hannun khairiyya ta sambad'a da gudu zuwa waje.

   Itama khairiyya ta take mata baya tana fad'in wlhy baki isaba saidai kowa yahak'ura mu badashi, daidai zasushiga d'akin Ammi bobo yashigo falon da sallama.

     Sanye yake cikin suit blue, komai na jikinsa blue ne amma banda belt da takalmi dasuka kasance jajaye, dressing d'in bak'aramin feeting d'insa yayiba, masha ALLAH.

    hannunsa yatura cikin aljihun wandonsa yajingina da kujera yana kallonsu khairiyya daketa zagaye falon batareda sunkula dashiba.

    Ganinfa bamasu gansaba yasakashi daka musu tsawa, kai!!! Wane irin iskancine wannan?, zaku maida mana gida filin polo?.

   Can suka tsaya suna mazurai, yacire hannunsa daga aljihu ya nunasu Ku nakula kafin kubar gidannan saina ta6a lfyar jikinku?, dannaga wani tashen iskanci kukeji yanzu?, to ubanmiye ya had'aku?!!.

    suduka saida sukad'an razana da tsawar dayayi, sukad'anja baya khairiyya ta CE, "Yaya wandonefa nad'auka shine ta kwace tagudo.

     Tsaki yayi ya ce, " wandon nawaye?.

   Da Sauri khursiyya ta ce, "nawanefa, itama khairiyya ta CE, " Yaya k'arya takeyi nawanefa.

     Kansa yadafe Dan suna Neman samasa ciwonkai ma wlhy...

    Ammi tafito ta ce, "miya faru kuma tom and Jerry?.

    Suduka suka nufi Ammi suna mata bayani.....

    Hannu Ammi tad'aga musu ta ce, " ainagaya muku kubar sayen Abu guda d'aya saboda gudun irin wannan ranar to gashinan kun saya kuma yanzu bawaje d'aya zaku kasanceba sannan kowa yanaso.

   Khairiyya tayi kwalkwal zatayi kuka, Ammi tafasan Nafi son wandon kuma nace ta d'auki rigar nitabani wandon amma tak'i yarda.

   Hannu bobo yamik'a ya ce, "kubani wandon.... 

     Jikin khirsiyya na Rawa tamik'a masa, yana kar6a ya haura saman Appa batareda yasake maganaba.

     Khairiya tafara hawaye tana hararar khursiyya Ammi ta ce, " wlhy ALLAH yabaku sa'a kunsandai halin mukarram sarai ba bak'oku bane, idan darabon saiya zaneku kuna a amare kukuka sani, idan kunason kanku da arzik'in toku kama kanku danni babu ruwana wlhy, tana gama fad'a itama tahaye saman Appa.

     Jiki asanyaye suka koma d'akinsu, Safna ta kallesu tana fad'in kukuma lfy INA wandon?.

     Baki Khairiyya ta turo ta ce, "bataja ya Abdulmaleek ya kwaceba.

    Zumbur safna tamik'e tana fad'in yazone?.

      Basu tanka mataba Dan duk haushinsa ya ishesu.

    Itama bata saurari amsa daga garesuba tafito falon, jin k'amshin turarensa daya tafi yabari yasakata murmushin jindad'i, tasan yanzu yana wajen iyayensa danhaka tafito  harabar gidan.

     Ganin motarsa yasakata k'ara sakin wani murmushin, bud'e gaban motar tayi tashige Dan bai kulleba.


Shikam yanayanacan gaban Appa suna magana.

     Appa ya ce, "Mukarram tunda Alhaji sunusu dala yabada hak'uri miyasa bazaka hak'ura dakaishi koti ba, bakamar yanda kayi niyya tun farko ba?.

     Appa idan na k'yaleshi to bansan mizaimin agaba ba, badan ALLAH ya tak'aita wahalabafa nasan yaransa zasu iya kashe Rahma da Nawal alokacin nan, Amma shine yanzu zai dawo yana 'Yar murya wai ayi hak'iri, naga da ko magana baya maka amma dayake yanzu yasan miya shirya shine zaizo yay maka dad'in baki akan kahanani kaisa kotu?.

    Hakane mukarram amma ni aganina duk bak'in halin mutum idan yay nadamar kuskure dayayi to yanada k'ayau agafarta MASA tunda ALLAH ma muna MASA laifi kuma idan muka rok'eshi saiya yafe mana, amatsayina na mahaifinka INA rok'ama alhaji sunusi gafara agareka da iyalanka, daga nan idan yasake yunk'urin cutar dawani namu saika d'auki matakin daduk yadace bazan hanakaba saidai na taimaka maka akan hakan.

    Shikenan Appa zan yafe MASA to amma Alhaji Abdurrazak fa?, na tabbata tare sukayi k'ulle k'ullen sacemin mata da 'ya.

     Eh nasani Dan yafad'ami. Shinema yazugashi akan suyi hakan, to amma wani nacin arzik'in wani aii, to shima Alhaji Abdurrazak yaci arzik'in Alhaji sunusi.

    Shikenan Appa zanfad'ama Ammar karsu tura maganar kotu dama sonake agama bikinnan sannan mushiga kotu, tunda hakane zan fad'a MASA najanye amma akwai shari'ar damukeyi da Alhaji Abdurrazak akan kisan Barrister Lawan Usman D/tofa, da ake zargin su suka saka akasheshi akan wata shari'a daya tsaya da lauyansu kuma yasamu nasara.

   Ranar dayaje office d'ina danyimin gargad'i kuma yaso tabbatar min dahakan saidai bodyguard d'insa yak'atseshi.

    Ajiyar zuciya APPA yasauke ya ce, "a'a wannan bazan hanakaba kam Dan waccan shari'ar daban wannan daban Dan haka saidai nace ALLAH yabaka Nasara, Yakuma k'ara kareka daga Sharrin mak'iya da azzalumai, ALLAH yamuku albarka kaida sauran 'yan uwanka.

    Ammeen Appa, bobo da Ammi suka amsa.

   Daganan wani zancan suka d'akko.

   Bobo yakalli agogo tareda mik'ewa, Ammi Appa bara nashiga Office time na wuceawa kuma inada shari'a yau k'arfe 11:30.

     To ALLAH yabada nasara jarumin babammu.

    'Yar dariya yayi yana k'ok'arin fita, to kugaidamin inna da Baba Dan bazan samu shiga wajensuba nayi latti.

    To zasuji idan sun fito.

   Ficewa yayi da hanzari, abakin k'ofa yaci karo da Idris tareda ya sulaiman zasu shigo.

        Tofa kukuma daga ina haka?, bobo yay maganar yana mik'amusu hannu, gaisawa sukayi cikin musabaha.

   Ya sulaiman ya ce, "yanzu nashigo muka had'u da idris zashi gaida su Ammi.

   Bobo ya maida kallonsa ga idris, ya karatu idris?.

   Alhmdllh yaya komai normal munata fama.

  To ALLAH ya taimaka, ni bara nawuce nayi latti.

   To ALLAH ya tsare yabada sa'a.

   Ameen ngd.

Ya sulaiman ya ce, " yauwa idan katashi kuma Kannada lokaci plss kad'an biyo ta asibiti dama inason ganinka.

   Okey babu damuwa saina shigo.

  Okey saina ganka shima ya sulaiman yafad'a suna nufar ciki shida idris, shikuma bobo yafito.


Motarsa yanufa hankali kwance yabud'e yashiga yana fad'in masha ALLAH yanzu kuma sai office.

    Idan ka gama dani ko?........

    Da sauri bobo yakalli gefensa dan son ganin waye?.

     d'aure fuska yayi tareda fad'in miyasa kina shigarmin  mota?, wama yabaki izinin shiga?.

        Wani murmushi Safna tasaki tareda k'ara lafewa cikin kujerar tana shak'ar k'amshin mortar da turaren bobo, tayi far da idanunta tana kallon k'yak'yk'yawar fuskarsa, aibasai anbani izinin shiga motar mijina ba, tayi maganar tana d'an d'aga gira.

   Kauda kansa yayi daga kanta tareda k'ara had'e fuska, ke banason k'aramin iskanci fitarmin amiota.

    Safna ta marairaice fuska harda hawaye, cikin muryar kuka ta ce, "Dan ALLAH ka saurareni wlhy magana nazo muyi kuma mai muhimmancice.

     d'agowa yayi yakalleta haryanzu fuskarsa ad'aure take, ganin tana kuka saikuma tabashi tausayi, bayason mutum yashiga damuwa akansa, yad'an huro iska daga bakinsa tareda kallon jan agogon fatar dake hannunsa 8:45, batareda ya kalletaba ya ce, " nabaki minti5 Dan inada abinyi.

     Hawayen fuskarta ta share ta ce, "wlhy minti5 yamin kad'an pls ka k'aramin.

    d'agowa yayi yad'an kalleta saikuma ya kauda kai, saidai ki hak'ura kuma saina taso daga aiki Dan yanzu haka nayi latti, so idan nadawo zanzo nan saiki sameni amma ki tabbata magarki tanada muhimmanci, kuma ki tabbata itace magana tak'arshe dazata shiga tsakaninmu daga ita kifita arayuwata, ina d'aga miki k'afane saboda banaso nazama silar rushewar zumincin iyayenmu, sannan bazan iya wulak'anta jinin Rahma ba, dan itama bata wulak'anta jininaba.

   Batareda yasake kallontaba yatada motarsa, ya ce, " sai anjima.

   Jiki a sanyaye Safna ta bud'e motar ta fito, hakan yayi daidai da fitowar ya sulaiman da idris.

   Suduka cikin mamaki suke kallon Safna da kuma motar bobon.

  Bobo dake kallonsu ya sulaiman ta madubi yad'anja tsaki, dama abinda yake gudu kenan, ganin ya sulaiman kamar yanufoshi yaja motar da sauri yabar gidan Dan bayason tambaya, musammanma akan safnar.

     Cak ya sulaiman ya tsaya yabi motar da kallo har bobo yafice daga gidan, kallonsa yadawo dashi akan Safna dake ida share hawayenta.

    Rissinawa tayi tana gaisheshi sannan tara6a ta gefensa zata wuce.

   Jimana ya sulaiman yafad'i yana kallonta.

   Safna tatsaya harya k'araso gabanta suna fuskantar juna, lfy kuwa mike faruwa?.

    Babu komai safna tayi magana muryarta nad'an rawa, shiru ya sulaiman yay yana kallonta da nazarin yanayinta, yad'an gyara tsayuwarsa yana sauke numgashi, ya ce, "keba yayar Rahma bace?.

     Yayartace, cewar Safna.

   To amma miya had'aki da Abdulmaleek? har kike kuka?.

   d'ago ido tayi ta kalleshi, bazata iya kallon idonsaba Dan yana mata kamada na bobo, tayi shiru batareda ta iya cewa komaiba.

   Ganin bazatayi maganaba ya ce, " to shiga cikin....

    Da sauri tawuce batareda ko juyowaba.

   Shima binta yayi da kallo cikin mamakin miye tsakaninta da bobo?, bai zargi komaiba Dan yasan bobo dodon matane, bazai ta6a zarginsa da fasik'anciba, amma tabbas akwai wata ak'asa tunda har bobo yafice daga gidan Dan bayaso suyi magana.

    Yabud'e motarsa yashiga zuciyarsa cike da waswasi, shima ficewa yayi da zummar zai tambayi bobo inhar sun had'u.


++++++++++

     a6angaren bobo kam yana fita office yanufa kai tsaye.

    Sakatariyarsa ta gaishesa cikeda salo kamar yanda ta saba, babu k'arya yau wankan bobo yakasheta, datanada dama har pic zata masa.

    Turare tad'auka tafesa tareda k'ara kallon kanta amadubi, komai daidai, tagyara zaman siket d'in material d'inta da rigar, shima mayafin aka sake salon yafawa sannan. Tanufi office d'in.

   Masinja Kamilu dake la6e yana kallonta Dan yasan dolene indai oga yashigo saitayi gyare gyarennan ya tuntsure da dariya yana fad'in kai iska na wahalar da maikayan kara, kedai awahala zaki k'are yarinya, mutum kamar wannan aii kasan matarsama abar kalloce, tomizai tsaya kallo ajikinki wannan karfata.

     Itadai Sakatariya Madeena😂😜 dabatasan masija nayiba tanufi office d'in cikin takun k'asaita da salon yanga irinta d'aukar hankali.

     Bobo na zaune akan kujerarsa ta alfarma yana rubuce rubuce sakatariya tayi sallama.

    Bai d'agoba amma ya amsa mata, yad'ora dafad'in waye yazo nemana?.

   Lissafa masa tafarayi daga k'arshe ta ce, "ad'arare sai Alhaji sunusi da la..

   Tak'are maganar da in ina.

    Dukda haka bai d'agoba sannan baice komaiba itakuma baice tatafiba.

  

Araina na ce, " mulki kenan."


Yakai kusan minti 4 yana rubuce rubucensa saida yagama sannan yad'ago yana linke takardar.

   Mik'a mata yayi, tamatso tareda rissinawa takar6a.

  Yamaida bayansa yakwantar ajikin kujerarsa yana d'an lilawa kad'an, idonsa akanta ya ce, ke yanzu dakikayi shigar mutunci bakijin kinfi kima a idon mutane ba?, amma da ko kunya bak'yaji kisakko kananun kaya kina tallar jikinki ga jama'ar gari da sunan wayewa, wannan ba wayewa bace shashancine, ki kama kanki sai miji nagari yaganki yasoki, shigar banza babu abinda yake jawomuku sai mazan banza suyita bibiyarku dankoba 'yan iskanbane tofa kallon 'yan iska irinsu suke muku, ki kiyaye banason shashanci.

    Kaita gyad'a duk kuma sai jikinta yayi sanyi, ta ce, "sir ngd ALLAH yak'ara girma da d'aukaka yatsareka daga sharrin mak'iya.

    To amin, ALLAH yasa mudace yafad'a yana d'agowa daga kwanciyar dayayi akujera, yanuna takardar hannunta, wannan takardar kibama Kamilu yakai office d'in Barrister Kamal Abubakar, yatsaya yakaranta yabasshi Reply yakawo min.

   Okey sir madeena sakatariya yafad'a tanad'an rissinawa cikeda girmamawa.

   Hartakai k'ofa tajuyo sir baka buk'atar wani Abu?.

   Kai bobo ya girgiza mata yana jawo laptop d'insa daga cikin jakka.

    Itama ficewa tayi tana fad'in OK sir.


Tana fita ta tararda Kamilu zaune akujerar dake gefen tebir d'inta, fuska ta had'e dantasan gulmace ta kawoshi.

    Ilaikuwa kallonta yayi yana 'Yar dariya, madee ince dai yau andace oga ya k'yasa?.

   Harararsa tayi tareda fad'in ban saniba magananne ni dalla kar6i oga ya ce, " ka kaima sir Kamal, kuma kajira yabaka Reply ka kawo masa.

    Mik'ewa yayi yakar6i takardar, to madee bara naje nadawo muyi magana, tunda har yanzu oga yak'i k'yasawa nisaina taya.

    Wata uwar harara tawatsa masa, kaidai shashashane Kamilu, yoko mazan duniya sun k'are aibanga abinda zanyi da sakaren namiji irinkaba.

   Tab yarinya aii ba'a fuska ake gane sakaran namijiba.

  Tsaki tayi tareda mik'ewa wlhy zanje nafad'ama oga baka tafiba.

    Da sauri yawuce a'a Madeena rufamin asiri Dan ALLAH, wannan zakin faman yanzu saiya hau kaina aii.

     raka bayansa tayi da harara, taja tsaki tazauna tana mita.

  

Bobo yakalli wayarsa dake wringing ganin Ammar yasashi d'aukar wayar da hanzari, gaisawa sukayi tareda tsokanar juna kamar yanda suka saba.

   Bobo ya ce, "dama kobaka kiraniba zan kiraka.

   To miya faru angon Rahma?.

   Murmushi bobo yayi, ya ce, " so inaga anjima zanshigo gidan saimuyi magana atsanake yanzu time d'ina k'urarrene nanda 'yan mintuna kad'an zanshiga wata shari'a.

     Okey babu damuwa to saina ganka, nima inada ganawa da Governor nanda minti 10.

   Hummm mutumina kuna sha'aninkufa, idan kukayi wasa duk ad'aure zakuje lahira Dan daku ake mulkarmu ak'asarnan.

   Dariya Ammar yayi ya ce, "masheranci aii kaima ad'auren zakaje indai hakane.

   Can abakinka d'an fatan tsiya sai anjima.

   Yanke wayar sukayi suduka suna dariya.

            Harzai ajiye wayar saikuma yafasa yakira Rahma.

    Tana zaune afalo ita kad'ai tana kallon wani India film, takalli wayarta dake wringing, ganin sunan dake a screen d'in yasakata murmushi, *_Nurulk'albee_*, d'auka tayi muryarta can k'asan mak'oshi tace amincin ALLAH ya tabbata agareka ya *_Nurulk'albee._*

       Wata sassanyar ajiyar zuciya bobo yasauke, murya akasalance ya ce, " kema amincin ALLAH ya tabbata agareki my *_Nusfulhayat_*. Ina fata kina cikin k'oshin lafiya da kuzari?.

        Alhmdllh sai godiyar ALLAH kam.

    Wani k'asaitaccen murmushi yasaki Wanda hartanajin sautinsa akunnenta, ya ce, "nagodema ALLAH da kika kasance cikin k'oshin lfy, kinga kenan yau za'a kar6e ni 100/100 abani kulawa ta musamman awajen barci.

    Kamar tana gabansa tafara buga k'afafu cikin shagwa6a ta ce, " nidai a'a wlhy inajin tsoro kuma har yanzu wajen akwai zafi.

    Yanda take masa magana cikin shagwa6a yasaka jikinsa yin sanyi, k'ara lafewa yayi acikin kujerar yana shak'ar kamshin turarensa dana office d'in, yakuma narke murya can k'asan mak'oshi haba my Angel kedai kincika tsorone kawai, amma yau kwana hud'u ace haryau anajin zafi?, kodai ana gudunane?.

     Hannu tasaka tarufe fuska wai ita kunya kamar tana gabansan, nidai Dan ALLAH kabarmin wannan maganar banaso.

    'Yar sassanyar dariya yayi harda shashsheka wadda tasaka Rahma shagala tana saurarensa, ya ce, "shikenan idan nadawo gida zamuyi aii, kafinma nadawo kisaka d'iyarki tayi barci, ummuch💋 yamannama wayar kiss, batareda yajira amsartaba ya yanke Kiran.

       Lumshe ido Rahma tayi tana murmushi, afili ta ce, ''kai maza sai'a barsu sudai ko kunya basaji?.

      Shimadai a can murmushi yayi, yamik'e yana had'a takardu, yad'auki k'atuwar rigarsu ta lauyoyi tareda hular yarik'e sannan yad'akko siririn farin Gil's d'insa yasaka yafice domin gabatar da shari'a...............












*_luv you oll_*.

*_(((S))).........2017_*


👩🏻‍💻typing........


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣

      _•{🅱🅾🅱🅾}•_



*_NA_*

_*Bilyn Abdul*_


_sadaukarwa_

*_Abba Gana_*

*_Batul mamman_*

*_Billy giro_*


*_masu karatu bara namuku gulmar Xoxo da 'Yar ficika,😎 hummm Xoxo cedai Xoxo cedai da Yar Ficika, saimukaje gidan Hafsat Rano aka kawo mana gasashshiyar kaza da lemo🍗🍹🍾hummm ina gaya mukudai, shikenan dai shikenan dai, sai.....🙊um bara nayi shiru kar zarah Bukar da hajja sufad'a musu gobe su sassambad'i k'eyata alungu🏌, kekuma Rano saura kifad'a ehe♀😏._*

    _😂luv you so much, my sweet sisters, Hafsat xoxo, Hafsat Rano, 'Yar Ficika & Zarah Bukar, hajjace, Ayusha ilyasu, gaisuwa agareku dafatan Alkairi._

😘😘😘😘😘👌🏼.


6⃣1⃣


           *_5:12pm_* bobo yamik'e tareda harhad'a takardun dazai buk'ata agida, yacire laptop d'imsa daga caji yasaka a jakka, bayan yagama had'a komai yakashe kayan wutar office d'in sannan yad'auki rigarsa ta lauyoyi ya sak'ala ahannu, yarataya jakar aikinsa akafad'a yafito.

      Da sauri Kamilu yataso yana fad'in oga kafito?.

    Nafito kamilu, zan wuce gida kuma.

   Kamilu ya washe baki tareda kar6ar key d'in hannun bobo ya kulle k'ofar, fitowa sukayi har wajen mota yarakishi, Dan tuni sakatariya Madeena tana gida, k'arfe hud'u da rabi yake sallamarta ita.

     Saida yashiga motar sannan yad'ago yana kallon Kamilu, to kashigo muwuce mana Dan naga garin kamarma hadarine.

   Dariya Kamilu yayi yabud'e mortar yashiga yana fad'in oga ai damunar tafara kankamane, nanda 'yan satittika zakaga ruwa yafara wadata.

     Murmushi kawai bobo yayi danyasan surutun Kamilu baya k'arewa, ahankali yake Murza kan motar yana kuma sauraren karatun alkur'anin dake tashi amotar cikin k'ira'ar shriek Abdurrahaman sudes, har k'ofar gida yakai Kamilu yamik'a masa kud'i yana fad'in gashi asaima uwargida kaza.

     Cikin washe baki Kamilu yakar6a yana godiya, wannan dalilin yanasakashi k'ara ganin kimar ogan nasu, kwatakwata bashida k'yankyamin talaka bare girmankai irinna alhazan birnin nan, gashida alkairi kullum baya gajiyawa.

    Har bobo yafice daga anguwar Kamilu natsaye yana kallonsa, saida ya6acema ganinsa sannan yashiga gida cikeda farinciki.

    Ganin hadarin nak'ara tasowa yasaka bobo k'ara gudun motarsa cikin 'yan mintuna k'alilan ya Isa gida, guri yasamu yay parking sannan yakwashi tarkacensa yanufi ciki, zuwa sannan anfara yayyafi.

        Rahma tana kichin Dan k'ok'arin had'a abincin dare taji ana kwankwasa k'ofa, fitowa tayi da hanzari dakuma tunanin wanene haka? Acikin hadarinnan.

    Batayi gaggawar bud'ewaba saida ta ce, "wayene?.

    Jin haka yasa bobo niyyar tsokanarta, ya mak'e murya kamar mace ya ce, " nice hafsat Xoxo budurwar bobo.

    Gabantane yafad'i gakuma wani k'ululn bak'inciki aranta, cikin masifa ta ce, "ai bayanan saiki koma sai sanda yadawo kizo.

    Pls madam ki taimakeni ruwafa na jik'ani.

    Yo ya kasheki mana, Rahma tafad'a ak'ufule tareda juyawarta kicin.

    Magana yasakeyi yaji shiru, ga ruwa yafara jik'ashi, da Sauri yanufi baya yaduba ko k'ofar kichin abud'e take ta baya, yana turawa tabud'e, yashigo da hanzari Dan tasowar wata iska mai sanyi.

    Da sauri Rahma tajuyo dansan ganin waye, ido tad'an zaro waje Dan mamaki, sannu dazuwa tayi maganar a cunkushe Dan tuna abundana yafaru yanzu tsakaninta da Xoxo.

          Dariya tabashi danganin kishi k'uru k'uru kwance afuskarta, amma saiya gimtse ya ce, " yawwa.

    K'arasowa tayi inda yake tsaye takar6i jakarsa da rigar, sai wani kakkauda kai takeyi.

    Lfy kuwa?, naganki haka?.

   Lfy lau tafad'a tana nufar cikin falo.

     Binta yayi da kallo yana murmushi, zame rigar suit d'insa yayi danta d'an jike yaja kujerar dake kicind'in ya zauna yana cire takalminsa.

    Rahma tadawo kichind'in ganinsa azaune yasata binsa da kallon mamaki, dukda yaji shigowarta amma bai d'agoba saida yagama cire takalmin yad'ora k'afarsa fara Sol Asama.

     Rahma ta ce, "azuciyarta, hummm jik'afa kamar ba'a takata ak'asa........

     Bobo yad'ago shima yana kallonta, nikam Nusfulhayat wana ganin  ak'ofar falo tsaye kamar mace?.

    Baki Rahma taturo gaba, ta kauda kanta gefe, nima bansaniba.

   Ido yazaro waje bakisanibafa kikace?, datazo batayi Knocking bane?.

     Hawayen datake mak'alewa suka zubo akumatunta, cikin shagwa6a ta ce, " bakai tazo nemaba, kuma ta ce, "budurwarkace ita.

   Yaso ya shek'e da dariya amma saiya dake, yamik'e da Sauri yana fad'in amma kika barta awaje ruwa na dukanta, yanzunan cute sokike kifara korarmin 'yammatane?, kwasar takalmansa yayi ahannu yawuce cikin falon.

     Rahma taduk'e kanta ajikin cabinet d'in kicin tana kuka.

    Shikam bobo d'akinsa yanufa yana 'Yar dariyar farincikin ana kishinsa Ashe?, kayansa yacire yafad'a wanka.

    Itakam Rahma saida taci kukanta ta more sannan tad'ago tacigaba da girkin, jitake dama batayi MASA girkinba, tsaf ta kammala komai tajere a dinning sannan tagyara kichind'in tsaf.

    Dubanta takai ga agogon falon, ganin lokaci yayi nisa tanufi d'akinta ta tatada Nawal dake barci Dan magriba ta k'arato, hannunta taja zuwa bayi tawanke mata fuska sannan suka dawo falo tabata ruwa.......hummm ni shinema yau ko ruwan ba'a baniba bare akula dani, maganar bobo tadaki dodo kunnenta.

     Da Sauri Nawal takwace hannunta taje tarungumeshi tana fad'in my papa oyoyo.

    Shima d'aukarta yayi yad'aga sama, my baby INA kika shigane bangankiba?.

     Papa barci nakeyi yanzu momyna ta tadani magriba tayi.

    Oh 'yargatan momynta yafad'a yana sumbatar kumatun yarinyar.

   Rahma dai tana tsaye tana kallonsu cikeda sha'awa, hannunsa yasa yakare fuskar Nawal sannan yad'agama Rahma gira, kauda kai tayi tanad'an murgud'a baki.

   Ya ce, "Niko?.

   Nidaifa banceba ehe, itama tafad'a kamar badashi takeba.

    Murmushi yayi sannan yadire Nawal, baby sauka nasha ruwa tunda an hanani.

     Da d'an gudu Rahma taje gaban firij tad'akko ruwa da cup takawo MASA.

   Bobo yayi dariya tareda fad'in ashedai ana tsoron kishiya.

   Gaba tayi tashige d'akinta tana tura baki, shikuma yazuba ruwa a cup yasha yana dariya.

     Nawal ta CE, " papa yaushe zamu tafi gidan Ammi?, gobene bikinsu aunty khursiyya.

     Saida ya shanye ruwan sannan ya ce, "jekiyi sallah idan nadawo masallaci zan sanar miki.

    d'akin momynta tanufa shikuma yadoshi hanyar fita, yabud'e sannan yad'an lek'a, ruwa akeyi sosai Dan haka yahak'ura yajuya d'akin Rahma dansuyi jam'i.

         Shigar tasa tayi daidai da fitowar Rahma daga bayi, da alama alwala tayi, baice da ita komaiba ya gyara shimfid'ar sallayar, itama ganin haka yasa tagane abinda yake nufi.

   Yana gaba suna baya itada Nawal yajasu jam'in magriba.

    Bayan sun idar Rahma ta d'akko alkur'ani tana koyama Nawal, shima yana zaune yana kallonsu cikeda jin dad'i, har lokacin sallar isha'i yayi suka mik'e domin gabatarwa.

    Saida yamusu doguwar addu'a sannan kowa yamik'e suka fito falo.

   Bobo yazube saman kujera yana fad'in wash ALLAH na, Nawal tazauna kusadashi my papa bakada lafiyane?.

  A'a baby nagajine kawai....... ga abinci fa....Rahma takatse musu zancen tana kallonsu.

   Fararen idanunsa yad'ago yana mata wani shu'umin kallo, ta kauda idonta daga kansa shima saiya ta6e baki.

   Nawal tamik'e shikuma ya ce, "nidai nagaji bazan iya hawan dining ba.

    Yanda yay maganar ashagwa6e saiyabama Rahma dariya, dinning tanifa tana murmushi, komai saida suka sakko dashi tsakkiyar falon.

    Tana niyyar zuba abincin taji ya ce, " kihad'amana a filet d'aya kawai, batace k'alaba tacigaba da zuba abincinta, bayan tagama ta tatura gabansa.

    Gyara zamansa kawai yayi yafara cin abincin atsanake, Rahma azuciyarta ta ce, "guy d'innan komai yahad'a, cin abincinsama abin kallone.

   Hakadai suka gama cin abincin anutse, daganan aka koma kallo, Nawal najikin papanta kwance yana shafa kanta ahankali.

     Tuni barci yad'auketa, yakalli Rahma dake kwance a 2sita tana game da wayarta, momyn Nawal zoki d'auketa tamin barci ajiki.

    Mik'ewa Rahma tayi domin d'aukar Nawal amma saiya jawota ta zauna akusadashi, hannunta yarik'e gam sannan yashiga k'ok'arin janye Nawal daga jikinsa cikin dabara.

   Rahma ta turo baki gaba, yatsu biyu yasa ya d'alli bakinta, da sauri tasaka hannunta awajen Dan zafi, cikin shagwa6a ta ce, " wayyo bakina.

    Habawa yarinya nagafa kamar kinfara rainani, bobo yay maganar yana matseta ajikinsa.

   Shinwai ni sa'ankine?.

  Da sauri Rahma ta ce, "a'a dantaji zafin d'allar mata baki dayayi. Ya ce, " to miye kiketa wani kumbura fuska?, nifa babu komai kaina yake ciwone.

   Ayya my Angel sorry, namiki kamu?.

   Kai tad'aga masa alamar eh.

   Ahankali ya kwantar da ita acinyarsa, maimakon yamata kamunkai saitaji bakinsa akan nata, tabud'e baki zatayi magana yasamu damar zira harshensa......


🚶🏻‍♀baya najuya musu karsuce nacika saka musu ido.

     Saida aka d'auki tsawon lokaci sannan na juyo Dan inada tabbacin komai ya kammala.

    Raham nagani tana cusa kanta acikin bobo suna dariya, da alama wani abun yafad'a mata taji kunya.

   Ya ce, "kinga tashi muje mu kwanta, mik'ewa tayi cikin jin kunya, ta d'auki Nawal takai d'akinta, kayan barci ta canja mata itama ta canja, tana k'ok'arin hayewa gado saiga Bobo yashigo sanye cikin kayan barci shima.

   Kallo d'aya tamasa ta kauda kai, shima baibi ta kantaba yamatsa kusada Nawal yamata kiss akumatu sannan yaja bargon yarufeta yana fad'in saida safe d'iyar albarka.

    Itadai Rahma batace komaiba Dan harta kwanta agefen Nawal, jitayi anyi sama da ita, tafara wutsil wutsil da k'afafu wayyo ya Abdulmaleek kabarni barci nakeji, nidai yau bazanbar Nawal ita kad'aiba, pls kabarmu mu kwanta.

     Bai sauraretaba har yakaita d'akinsa yadire agadon, tana k'ok'arin tashi yasa k'afa ya danneta, wayoyinsa yad'auka ya kashe sannan shima yahaye gadon yakwanta tareda jawota jikinsa.

   Itakam tuni tafara kuka zuciyarta cike fal da tsoro, jin yafara mata abinda hankalinta bazai d'aukaba tafara kuka tana zame zame.

   K'ara matseta yayi ajikinsa yana k'ara rud'a jikinta da sakwanni wad'anda sukeyin tasiri ajikinta da zuciyarta, amma kuzarinta na k'ok'arin turesu domin ku6tar kai.

     Ina mutumin naku baiko saurara mataba Dan tuni jikinsa da ruhinsa sun Lula duniyar begen aika aikar dayakeyi, da zafifi yake aikamata sak'wannin soyayyarsa, kafin tafarga yad'auki hanyar mallakarta daga ita har zuciyarta Dan tuni itama tabada kai dukda d'unbin tsoro da fargaba dasuka kanainaye ilahinrin lungun da sak'on zuciyarta.


_Hummm masu karatu nima bara naja camryn 🚶🏻‍♀k'afafuna nanufi wajen angona kuma sarkina mamallakin zuciyarta da ruhina_ *_{Abdus'salam)_* d'ina adon zuciyata😘😂.



_washe gari_

      Hummm yaukam na iso amakare Dan natarar har Rahma tagama tsaftace ko ina na gidan, takuma had'a breakfast mairai da lafiya.

     Zaune na isakesu a dinning suna karyawa, Rahma da bobo dasun had'a ido saisu sakarma juna murmushi, bobo kam harda d'aga mata gira, takan kauda kai tana murmushi Dan gudun kar Nawal tafahimci wainar da suke toyawa.

    Bayan sunci sun k'oshi suka mik'ewa tareda yin hamdala ga sarkin sarakuna mai k'yauta da k'ari.

    Bobo yad'auki jakar aikinsa ya rataya, yaukam sanye yake cikin wani farin yadi mai laushi, Wanda akaima ado da bak'in zare, rigar dakad'an tawuce d'uwawunsa amma yayi d'as aciki kamar kazauna kayita kallonsa,

    _Hummm karkuma ka kalla k'ilu tajawo bau, Rahma ta ce, "kana kalan mata miji🤥, my Xoxo ki kalleshi kad'an keda Rano_o😎.

       Rahma tasakama Nawal jakarta abaya sannan tad'auki d'an kwandon abincinta suka fito, itama Rahma sanye take da shadda ruwan k'asa mai turuwa zani da Riga, tasaka farin hijjabi har k'asa Asama.

     Saida suka fara sauke Nawal a school sannan Bobo yad'auki hanyar gidan Appa.

   Juyowa yayi ya kalleta hayateena awajefa zan saukeki dannayi latti.

   Itama kallonsa tayi sannan ta kalli agogon motar ta ce, " k'arfe 7:34am yanzu".

      Eh nasani, sonake naje office dawuri yau, nayi duk aikin dazanyi zuwa 4 nadawo gida mukasance tare.

    Hannu Rahma tasa tarufe fuska tana 'Yar dariya, ALLAH kana bani kunya.

   Murmushi yayi idonsa atiti ya ce, "tom nadaina baki kunya Nusfulhayat d'ina mai kuka, yaya Dan ALLAH kabini ahankali, daddyn Nawal wlhy yauma a kwai zafi, wayyo ummina kizo ki cecen...........

     Bata bari yak'arasaba tasaka MASA kukan shagwa6a.

    Ohh sorry my cute nadaina fad'a, cikin dariyar shak'iyanci yay maganar.

    Maigadi yabud'e masa gate yashiga, ko gama tsayawa da motar baiyiba tafice tayi cikin gida.

      Binta kawai yayi da kallo yana murmushi, afili ya ce, "wato idan ka auri yarinya k'arama  tana maka ta6ara kaima saika zama ta6ararre, ya shafa sajensa daya kwanta luf, yad'an lumshe ido yana fad'in ALLAH yak'arama ANNABI daraja da fadila da Wasila.

  Rahma kin mallake  *_Barrister Abdulmaleek Aliyu Abdulmaleek hamshak'i_* gaba d'ayansa da komai nasa, kin mantar dani damuwata gabad'aya, ya ALLAH kak'ara mana soyayyar juna, kakuma nisanta shaid'an daga garemu.

  

Na ce, " Ameen bobon Rahma.


Fitowa yay shima yanufi cikin gidan, babu kowa afalon sai kamshi dake tashi da sanyin AC.

    Shiru yay atsaye yana nazarin gidan, sallamar Baba hansai mai Aiki yasakashi juyowa, ta ce, "a'a Alhaji kaine agidan.

   Murmushi yamata sannan yarisina ya gaisheta, baba hansai masu gidan basu tashi bane?.

    Khairiyya da khursiyya sun tashi tun d'azu, amma banga Ammi ba gsky.

    Okey bara to nawuce office kawai saina dawo.

   To Alhaji bazakaci komai bane?.

   Ahhh baba nidanake da mata, ai tuni nafita agandu.

   Dariyar jin dad'i baba hansai tayi, ta ce, " to madallah Alhaji, ina Nawal da mamanta?.

   Nawal na makaranta, mamanta kam tana nan cikin tare mukazo, kud'i yazaro a aljihu yamik'a mata yafice.

   Itakuwa tarakashi da k'yawawan addu'oi.


Rahma kam koda tashigo taga falon babu kowa saita wuce d'akinsu khursiyya, cikeda ihun murnar ganinta suka tashi suka ruk'unk'umeta, akan gado suka zube suna dariya.

   Daga nan hira suka farayi.

            fitar bobo badad'ewa safna tafito daga bayi, dama tana wanka sanda Rahma tashigo.

   Rahma ta gaisheta, da k'yar ta amsa, itakam batabi takantaba Dan abunda su khairiyya suke nuna mata ya d'auke hankalinta.

   Khursiyya ta ce, "aunty Rahma wai waya kawokine?."

    Ya Abdulmaleek mana Rahma tafad'a tana dariya.

   Kai yana ina?.

Inaga yakoma Dan yace dama bazai shigoba sauri yakeyi.

   Ajiyar zuciya Safna ta sauke aranta ta ce, "yagama guje gujensa yazo yasameni daram.

    Sudai su Khairiyya dabasusan tanayibama hirarsu suketa zugawa suna kwasar dariya kamar wasu k'awaye.................





*_💃🏻Taka rawar gani akalla kome kayi kanka duniyace, mai jimirin zama cikinta, shike zuga kansa d'an magori._*


   (zancenka haka yake nura m inuwa😎).












*_luv u oll_*

*_(((S)))........2017_*


👩🏻‍💻typing........


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣

      🅱🅾🅱🅾



*_NA_*

_*Bilyn Abdul*_


_sadaukarwa_

*_Abba Gana_*

*_Batul mamman_*

*_Billy giro_*


*_yau gaisuwar da shafin duk nakune sister Fertymerh xarah & Nafi Anka, alkairin ALLAH yakai muku aduk inda kuke, bilyn Abdul na gaisheku tareda bobon Rahma._*

     _I Luv you manya manya😘😂_

6⃣2⃣


     Sai wajen k'arfe biyar su bobo suka dawo gidan, kamar had'in baki suka dawo kusan lokaci d'aya suduka hud'un, bayan kowa yafito daga motarsa suka gaisa cikeda k'aunar juna.

    Ya Hamza ya ce, "lallai gida yafara kar6ar bak'i irin wannan hayaniya.

   Dariya sukayi gabad'aya, ya ishaq ya ce, " tokumu k'arasa ciki..

    Cikin falon suka nufa suna 'Yar hirarsu da dariya.


Na ce, "masha ALLAH, biki ya kankama Dan falon yad'an cika da bak'i wad'anda suka iso yau, ga hayaniyar yaransu ya ishaq daketa wasa da yara sa'anninisu bak'i.


Su bobo suka rissina suna kwasar gaisuwa, kowa kallonsu yake cikeda sha'awa, bayan gaisuwa aka ta6a 'Yar hira da tsokanar juna, shidai bobo banda murmushi babu abinda ya iya, dama haka yake ko tsokanarsa kakanni sukeyi iyakarsa murmushi, amma baya iya maida murtani, saidai 'yan uwansa idan suna kusa su kare masa.

     Yanzuma wata 'Yar tsohuwa ke tsokanarsa, ta ce, " mai sunan Alhaji wai kaidai kana nan babu canji?, maganama wahala take maka bare dariya?.

     Nanma murmishi kawai bobo yayi kamar yanda yasaba baice komaiba.

   Ya sulaiman ya ce, "Hajiya iya aii maganar Abdulmaleek tsada gareta saikin saya da kud'i.

     Yo sule mizanyi da maganarsa nikam barema na siya, wannan sai matarsa dai amma baniba.

   Dariya suka saka gabad'aya falon.

   Bobo Yakama gemunsa nagayu yana shafawa fuskarsa cikeda murmushi, ganin zasu saka rayuwarsa gaba yamik'e ya haye saman benen, aiko suka rakashi da dariya, ya ishaq ya ce, " Hajiya iya kinga kin koreshi?.

    Isahaqa ai dankar yayi maganane yatashi, nibansan halinwa mai sunan Alhaji yakwasoba?, tunda nake ban ta6a ganin muskilin mutum irinsaba, mifa zan iya k'irga maganarsa mai tsawo danaji atsawon rayuwata, mutum kulum dund'un dunkum, sai murmushi shima idan ya gadamar yi.

    Dariya aka sakeyi, su ya Hamza suka mik'e suna dariya, suma sama suka haura, cikin dariya da zolaya ya Hamza ke kiran Dund'un Dunkum! Kana inane?.

   Bobo dake zaune kusada Ammi yaturo bak'i gaba, ammi kingansu ko?, wlhy nasan dani suke.

    Murmushi Ammi tayi kafin tabashi Amsa su ya sulaiman suka shigo d'akin suna dariya dacigaba dakiran dund'un Dunkum.

    Ya Hamza ya kalli bobo haba Dund'un Dunkum ya munata kira kaki amsa mana?.

   Hararsu yayi cikin sigar wasa, ya ce, "halan faratun tsohurcan ce tafad'i sunan nan?.

   Ammi dake k'unshe bak'i tana dariya ta rankwashi kan bobo, mukarram k'aniyarka wace faratun?..   

    Uhhhchch bobo yafad'a Dan zafi yana dafe kai, wayyo Ammi ALLAH da akwai zafi.

    aidama dankaji zafin namaka tayi maganar tana k'ara kai masa wani rankwashin.

   Da Sauri ya kauce, su ya ishaq suka saka dariya, gefe bobo Yakoma yana turo bak'i kamar wani k'aramin yaro, sai shafa Inda Ammi ta rankwasheshi yakeyi.

    Sudai su ya hamza dariya suketa masa.

     Ana cikin haka Appa yashigo d'akin da sallama, duk cikin dariya suka amsa harda ammi, Amma banda bobo dake gefe zaune ya shagwa6e fuska.

   Tofa dariyarmi kuma akeyi uwa da 'yayanta?, Appa yafad'a yana zama abakin gadon Dan duk su ya Hamza suna ak'asan kafet ne zaune.

    Bak'i bobo Yakuma turowa ya shagwa6e fuska kamar zaiyi kuka, Appa nifa sukema dariyarnan.

     Kai kai kowa ya saurara, yazaku tasamin babana a gaba kuna dariya?, haba Ammi harda ke?. Babana zonan naji miya faru?..  

     Tasowa bobo yayi yazo yazauna kusada k'afafun Appa, yad'ora Kansa bisa cinyarsa, Appa yasaka hannu yana shafa kan bobon dayawani narke kamar yayayye.

     Babana mikayi ake maka dariya haka?.

    Appa ba Hajiya iya bace tacemin wai Dund'un Dunkum shine suka tasani gaba da dariya, ita kuma Ammi Dan nacema Hajiya iya 'Yar fara shine tarankwasar min kai, kumafa kaina harya fara ciwo.

     Shima Appa sunan yabashi dariya wai Dund'un Dunkum, amma saiya gimtse saidai yayi murmushi, yacigaba da shafa kan bobo kaga mukarram d'ina barsu duksai na Rama maka, kowa saimun za6i suna sannan musaka masa.

    d'agowa bobo yayi yana dariya shima, aii Appa harnama tanadi sunan dazan saka musu sai ranar deener zan fad'a idan za'a gabatar da manyan yayye yakare maganar dayimusu gwalo.

     Appa yasaka dariyashida Ammi, sukam su ya ishaq kowa ya tsaya da dariyarsa suna hararar bobo Dan sun San zai iya aikatawa sarai.

    Ya sulaiman ya ce, "haba bobon Ammi garadai kafad'a anan komai ya wuce.

     Hum'im ban yarda da wayonba a can zan fad'a dankuji ehe.

     Kaga sulaiman barsa yafad'a d'in , ALLAH yakaimu muma aisaimu fad'a, muce INA yayansu Amarya Dund'un Dunkum.

    Appa ka gansuko?, bobo yay maganar cikeda shagwa6a.

   Yanzunkam kowama saida yadara harsu aunty Rasheda dake k'ok'arin shigowa Dan gaida Appa, dama duk suna tsaye tun d'azun sunajin diramar family d'in, kowa sai kunshe bak'i take tana dariya dankar ajisu, zuwa yanzun sun kasa rik'eta Dan haka suka sheke da dariya suduka suna shigowa cikin d'akin.

     Ya Hamza ya ce, "ALLAH bobo kaji kunya, wai yaushene zaka daina shagwa6ar nan takane?, Rahma kina fama gsky.

     K'asa Rahma tayi da kanta tana dariya, Dan maganar ya Hamza tabata kunya.

      Bobo ya kalli Rahma dake dariya tana to she bak'i da hannu, ba k'aramin birgesa tayiba.

      Safna ma dai yau ba abarta abayaba Dan dariyar takeyi, ba k'aramin birgeta shagwa6aar bobo tayiba.

     Saida aka tsagaita da dariya su Rahma suka gaida Appa, ya amsa fuskarsa wasai.

    Mik'ewa su Aunty Sameera suka fara da zummar Fita su basu waje.

 Appa ya ce, " a'a INA zakuje kuma?, kuzauna ayi hirar zumunci asamu ladan juna, komawa sukayi suka zazzaauna cikeda kunya da k'aunar sirikan nasu masu kamala da dattako.

    Hira aka cigaba dayi cikin farinciki har aka kira sallar magriba kowa ya mik'e mazan suka wuce masallaci, sukuma kowa yayi alwala sukayi agida.


       Basu dawoba saida akayi isha'i.

   Safna dake la6e ajikin motoci tayi saurin rik'o rigar bobo.

   Da Sauri yajuyo dansan ganin waye?, ganin Safna yasashi saurin zare ido, ya maida kallonsa gasu ya ishaq yaga babu Wanda yajuyo harma sun shige falo, hamdala yayi azuciyarsa dabasuga aika aikar da Safnar tayiba.

   Juyowa yayi yana kallonta fuska a gimtse ya ce, "sakarmin Riga.

     Babu musu tasaki Dan gizagon fuskarsa yabata tsoro, ta marairaice fuska kamar zatayi kuka ta ce, kacika "alk'awari.

      Yagane mitake nufi amma dukda haka saiya yatsine fuska ya ce, " alk'awarin mi?, ke nifa kin addabawa rayuwata.

    Safna ta marairaice fuska saiga hawaye sharrrr, ta ce, "bobo kana wulak'antani saboda ALLAH ya jarabceni da Sonka ko?, pls ka taimakeni ka taimaki rayuwata, wlhy sonka zai kasheni Abdulmaleek, bana iya barci, Sonka yana neman haddasa k'iyayya tsakanina da 'Yar uwata, Dan ALLAH karda kayadani Abdulmaleek wlhy Sonka zai halakani, inasonka INA Sonka fiyeda son dAnakema kaina..... Takasa k'arasawa saboda kuka dayaci k'arfinta.

    Shikam tsayawa kawai yayi yana kallonta, zuwa yanzu tafara basa tausayi, jiyayi zuciyarsa tana shawartarsa daya taimaketa koda da nasihane k'ila tagane ta farka daga nannauyan barcin daya d'auketa.

      Yad'an lumshe idanunsa yabud'e akanta, kinga tashi yafad'a cikin muryarsannan mai dad'i da amo.

     Safna ta tashi tsaye tana share hawayen fuskarta.


     A can ciki kuwa saida su ya sulaiman suka zauna sannan sukaga babu bobo.

    A'a INA Abdulmaleek ya tsaya?, cewar ya ishaq.

    Kasansa shida baba mai gadi yanzu haka yana can.

    Ammi ta ce, "Rahma jeki kira mijinki yazo yaci abinci tukunna saiya tafi suyita hirar.

    Akunyace Rahma tamik'e, zata fita Appa yafito shima daga d'akinsa, ya kallesu ya ce, " a'a INA mukarram d'in?.

       Gashi can antafi kiransa wajen baba mai gadi.

   To Aida kun k'yalesa babu dad'i suna hira kuma akatsesu, shima bazaiji dad'iba malam salen, daga yau kar a k'ara haka kunji?.

    Insha ALLAHU Appa baza'a sakeba suka had'a baki wajen fad'a.


     Rahma kam tana fita domin kiran bobo, harta kusa tsakkiyar gidan saita hango safna da bobo tsaye safna tana masa murmushi, badai ta hango fuskar bobo ba Dan ya juyasaiata baya, Dan haka batasan shi miyakeyiba, amma wata zuciyarta tana shaida mata shima murmushi yakeyima safna, tsayuwar sojan badakkare tayi, bata gama farfad'owaba ta hangosu sun nufi hanyar lambun gidan, jitai hawaye nabin kumatunta, yaukam abinda take zargi ya tabbata, inhar bobo da Safna ba soyayya sukeyiba a6oye mizaisasu ware kansu alambu kuma arin wannan lokacin?.

   Ta share hawayenta tareda cije le6enta da k'arfi, juyawa tayi takoma cikin gidan, ta daure ta ce, "yana tareda baba suna hira awaje.

   Appa ya ce, " kinga Rahma barsa kawai, idan sun gama yazo yaci abincin.

   Jinjina kai tayi cikin ladabi ta ce, "to Appa."

   Amma azuciyarta saitace aibama saiyaci abinciba soyayya zata k'osar dashi, d'akin su khairiya tashige tashiga bathroom tasha kukanta San ranta, zuciyarta sai tafarfasa takeyi Dan bak'in ciki, jitake gaba d'aya yau tatsani bobo dakomai nasa.

    Haka tasha kukanta, bata fitoba saida taji aunty ummy na kwala mata kira tazo suci abinci, wanke fuskarta tayi tafito tana murmushin yak'e, ganinan aunty ummy wani abune yashigarmin ido shine nake cirewa.

    Ayya sannu yafita ko?.

   Eh ya fita aii ruwa naita sakawa.

  To sannu, muje muci abinci ko.

   To kawai tace mata suka fito falon k'asa inda kowa yake har Ammi, mazan ne kawai babu suna sama tareda Appa.

    Aunty Sameera ta ce, "a'a INA safna wai?.

    Da sauri Rahma ta ce, " tana waje tana waya, aii muci abincinmu kawai wannan ba yanzuba, idan tafara waya sai ALLAH.

    Dariya sukayi gaba d'aya, aunty rasheeda ta ce, "wlhy kubarta ta soye abinta, itama muje musha biki, tunda tak'i bobon mu, madai gani ko guy d'in nata yafishine haka?.

    Babu Wanda yace komai saidai anyi dariya, harda Rahma datayi na yak'e, tasan sarai habaici aunty Rasheeda tayima Safna, amma bataga laifintaba tunda itama ga aunty Safnar can suna cin dunduniyarta itada mijinta datad'auki so ta d'ora masa ayanzun.

    Hakadai sukecin abincinsu, Rahma tanacine kawai badan dad'iba, amma jitake kamar tana cin magani.


Safna da bobo kam suna lambu zaune, bobo ya d'aure fuska kamar bai ta6a dariyaba Dan ganin yanda Safna takafeshi da idanu tamkar zata cinyeshi.

   d'an tsaki yaja yana kauda kai daga kallinta, ke kinga inada abunyifa nazo nan nazauna, kuma matata banaso taduba bata ganniba Dan haka miye maganar taki?.

      Dukda maganarsa ta 6atama safna rai, musamman dayace bayaso matarsa taduba taga bata nan amma saita danne ta matso hawaye tana shashshekar kuka.

   Hannu ya d'aga mata, kinga ba kuka na tambayekiba fa malama.

   Share hawayenta tayi, ta durkusa agabansa guywa ak'asa tana cigaba da hawaye, Abdulmaleek pls kasamo mana mafita, nidai nasan kaima kana sona, idan zaka iya daurewa wlhy ni bazan iya jurewa ba ka taimaki rayuwata karta salwanta akan sonka.

   Wani murmushin mugunta bobo yayi, ya ce, "tabbas ina sonki amma so na 'yan uwantaka, irin Wanda nakema khursiyya da khairiyya.

    So na gsky irin na soyayya da tsan tsan k'auna da begen juna, mai ratsa jijiya da ruhi da 6argo mutum d'aya tak nakemashi, itace Rahma, my Nusfulhayat d'ina, farin cikina uwar 'yayana, sarauniya mai sarautar dukkan zuciyata da duk abinda ke cikinta.

    Safna kamar yanda na gaya miki wannan zaman shine zai zama zama na k'arshe tsakanina dake, kuma itace zata zama magana ta k'arshe tsakanina dake wadda ta danganci wannan, zan baki shawara kuma zan miki nasiha, idan kin d'auka kin huta, idan kin watsar ke wahala, nidai ALLAH yagani nafita hak'k'inki amatsayina na d'an uwanki musulmi.

   Zamansa yagyara yana mai k'ara tattara nutsuwarsa waje d'aya.

   Cikin murya mai nuna muhimmancin maganar dazaiyi ya ce, "Safna!.

       d'agowa tayi tana kallonsa amma bata tankaba.

       

Ya ce, "Safna ina d'aga mini k'afane saboda darajar Rahma amma nakula ke bakisan zuruba.

   Zan baki shawara ta k'arshe atafiyamu Dan inaso mugudu tare my tsira tare..............










*_Luv you oll._*

*_(((S)))......2017_*




👩🏻‍💻typing........


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣

      _•{BoBo}•_



*_NA_*

_*Bilyn Abdul*_


_sadaukarwa_

*_Abba Gana_*

*_Batul mamman_*

*_Billy giro_*



6⃣3⃣

      

      Ina mai baki shawara amatsayina na mijin k'anwarki, ki nutsu kinemi miji kiyi aure kidaina wahalar da kanki akaina.

   Amatsayinki na wadda tayi kuskure abaya yakamata kiyi zaman gyarashi yanzu, sannan ki d'auki sona dakike ik'irarin kinayi ki jefar dashi gefe ki tsarkake zuciyarki, ki daina biyema k'awayen banza suna sakaki a hanyar hallaka na bin bokaye.....

     Cikin matuk'ar mamaki Safna take kallonsa, azuciyarta ta ce, "a ina yasan wannan?.

    Kamar yasan tunanin datake yayd'an murmushi tareda jinjina kai, yacigaba da fad'in kina mamakin ina nasani ko? Humm hakan babu inda zai kaiki wlhy saidai kiyita komawa baya arayuwarki, Safna babu abinda ke cutar da rayuwarki sai son zuciya, to son zuciya kuma facin zuciyane.

     Na tabbata ALLAH ya jarabceki da sonane saboda hakan yazamarma masu hali irinnaki ishara.

   Da'ace su Abba basuda Rahma dasunji kunya awaccan ranar dakika nuna musu basu isaba, saboda k'ok'arin kunyatasu dakikayi akan dalilinki mara tushe.

   Shin alokacin kinada tabbacin sake ganina?, kokuwa idan kin ganni kinada tabbacin zan kar6i soyayyarkine?, amma saboda son zuciya kika bijirema iyayenki akaina, wannan itace jarabawa tafarko dakika fara fad'uwa arayuwarki.

    Safna iyayenmu sunfi kowa sonmu Dan haka bazasu cutar damuba, idan baki saniba zan fad'a miki ayau, tunda nake banta6a za6ar matar aureba da kaina.

   Matata ta farko ma iyayenane suka za6amin, dukda banasonta amma nayima iyayena biyayya nakar6i k'yautarsu da hannu bibbiyu, biyayyar danamusu ban bijireba sainaci riba, daga ni'ima har Rahma sunzamemin alkairi arayuwata, wadda na tabbata da auren soyayya nayi bazanci riba hakaba, kema na tabbata dakinma iyayenki biyayya dakinyi gamon katar da abinda kikeso, amma kinga sakamakon da bijirewar taja miki yanzu, saidai sharri shaid'an dana zuciya sun danneki kin kasa ganewa bare kiyi nadama harki nemi afuwar iyayenki.

   To inamai tabbatar miki idan baki gyaraba haka zakiyita fad'uwa ak'asa, ki k'are rayuwarki a bibiyar tamu rayuwar, gashi mukuma kullum farincikine ke k'ara baibaye rayuwarmu saboda albarkar iyaye dake bibiyarmu.

    _amatsayinmu na 'Ya'ya wad'anda iyayenmu sukasha wahala wajen haihuwarmu, rainanmu, karatunmu, tarbiyyarmu, basa son kukanmu, kulada lafiyarmu daduk wani motsinmu, amma ayayin damuka girma muka mallaki hankalinkanmu lokacin daya kamata mu share hawayensu, amma sai suka nemi wata alfarma agaremu  muka bijire musu, saboda mu muna ganin mun waye su mutanen Dane, mukuma 'ya'yan zamani wad'anda boko tagina, shin kuwa muna ganin ALLAH zai k'yalemu kuwa?, aganina babu abinda 'ya'ya zasuyi aduniya su biya iyayensu akan hidima da d'awauniyar dasukayi dasu suna k'anana._

       Akwai inda zaka iya bijirema iyaye kaci riba, shine idan sunce kasa6ama ALLAH, wannankam ba'a yarda kamusu biyayyaba.

     Idanfa ta gsky da tsarin addini za'abi, iyaye akace suza6ama 'Ya'ya mijin farko, idan kuma k'addara ta gifta hartayi zawarci to wannan tanada 'yancin za6ama kanta akaro na biyu tunda ta mallaki hankalin kanta.

    Safna kije ki tsugguna ga iyayenki kinemi gafararsu na tabbata insha ALLAHU ko yayane saikinji sona yaragu azuciyarki.

     Inhar iyaye na fushi dakai tom dolene kaita tsintar kanka cikin asara, bafa zaka sami sassauciba harsai sun janye fushinsu akanka, tokema ki gwada ki gani insha ALLAHU zaki dace.......

    

Shashshekar kukan Safna ne yakatsemasa dogon bayanin daya d'akko, d'ago k'yawawan idanunsa yayi yana kallonta, ya ce, "ba kuka zakiyiba inhar nasihata tashigeki, nadama zakiyi, kuma ki d'auki hanyar gyarawa.

     Cikin shashshekar kuka safna ta ce, " duk abinda kafad'a gsky ne, amma wlhy akowane dak'ika na rayuwata k'ara sonka nakeyi, narasa yanda zanyi nacireka araina, ina sonka so bana wasaba.

    Tabashi tausayi kwari da gsk, Dan haka cikin taushin murya ya ce, "kiyi hak'uri Safna, kimik'a lamarinki ga ALLAH shine zai taimakeki, na tabbata shaid'an nak'ara hura wutar sonane azuciyarki Dan kawai yaraba zumincin dake tsakaninki da 'Yar uwarki, Yakuma cigaba da 6atar dake acikin duhuwa kikasa rok'ar gafarar iyayenki bare harkici riba a rayuwarki.

   Zan tayaki da addu'a ALLAH yacire miki sona azuciyarki kema yabaki miji nagari maisonki fiye da komai amadadina, nabaki kwana uku kije kiyi tunani kuma kiduk'ufa da addu'a Nina zan tayaki.

    Jinjina kai Safna tayi cikin sanyin jiki, ga hawaye sha6e sha6e afuskarta, yazaro farin handky d'insa daga aljihu sai tashin k'amshi yake yabata.

   Hannu biyu tasaka takar6a tareda fad'in ngd ya Abdulmaleek, ALLAH yabiyaka da mafificiyar nasara, yasakama rayuwarka da mafificin alkairi.

   Jinjina mata kai yayi tareda lumshe idanunsa fuskarsa d'aukeda murmushi Wanda bata ta6a ganin irinsaba daga gareshi.

   Itama mayar masa da murmushin tayi, tashare hawayenta da handky d'in.

     Gaba tayi yana binta abaya gabad'aya saiyaji tabashi tausayi Dan baiyi tunanin zatayi sanyi dawuri hakaba.

   Cak safna tatsaya tanabin mutanen Dake tsaye da kallo a harabar gidan d'aya bayan d'aya.

   Da Rahma suka fara had'a ido, tunda take bata ta6a ganin 'Yar uwarta Rahma hakaba, ta tamke mata fuska tamau kamar batasan miye dariyaba arayuwarta, juyawa tayi da kallonta ga sauran saitaga ya ishaq da matarsa ya Sulaiman da mayarsa ya Hamza da matarsa, wannan ya tabbatar mata sunfitone dazummar tafiya k'ila anata Neman bobo, gaba d'ayansu takula kallon tuhuma da tsana suke mata, k'asa tayi dakanta idonta cikeda hawaye, batason su maidata ruwa, tanason kowa ya fahimceta kuma ya k'aunaceta, juyawa tayi ta kalli bobo, shikam hankalinsa kwance yake, Dan fuskarsa da murmushi ya ce, "oh kunata jirana ko?, bara nama su Ammi Sallama mu wuce.......

     Baijira amsar kowa acikinsuba yayshige warsa falon.

    Sum sum safna itama tayi yunk'un tafiya Dan tsorata da kallon tsana dasuke mata kuma harda 'Yar uwarta a ciki, da Sauri aunty Sameera tayi yunk'urin Tarar safna amma sai Yaya ishaq yad'aga mata hannu alamar tabarta.

    Ganin haka yasaka safna saurin shigewa falon sukaci karo da bobo dake fitowa, kallonta yayi d'an murmushi ya ce, " karfa komai yadameki nida kaina zan warware musu k'ullin kinji.

   Kanta ta d'aga Dan koba komai taji sanyi tunda bobo yafara nuna mata kulawa, saida safe tafad'a a sanyaye.

    ALLAH yakaimu yay maganar yana fita, Itakuma tahaye sama zuciyarta na k'ara k'arfafata akan karta bari dalilin wasu tubanta ya ruguje.

       Koda bobo yafito saiya Tatar ya ishaq nagaya musu karkowa yatada maganar sai bayan biki, suna ganinsa kowa yagyara tsayuwarsa kamar basa maganar komai.

    Shima bai nuna musu yaji komaiba yabasu hannu sukayi musaBaha kowa yashiga motarsa, hannun Rahma Yakama saita fisge..    

     Cikin d'an mamaki yakalleta ta kauda kanta gefe, k'ara damk'ar hannunta yayi yatura amota, Duk abinda ke faruwa 'yan uwansa suna kallonsu amma babu Wanda yay yunk'urin yin magana.

    Yana turata amotar yamaida yarufe, shima yazagaya yashiga suka fice kowa Yakama hanyar gidansa.

          Tunda suka fice agidan Rahma tafara shashshekar kuka, baice da ita komaiba dukda kukan NATA na ta6a zuciyarsa, tsayawa yayi wajen wani gashin kaza yasaya sannan yadawo motar, gefen Rahma yakalla saiyaga tayi barci, girgiza kai kawai yayi yatada mortar yay gaba.

   Bayan sun gaisa da maigadi yashiga cikin gidan yay fakin Inda yadace, baitadasuba sai kawai ya d'auki Nawal yakai cikin gidan, yadawo Yakuma d'aukar Rahma, yana tafiya yana kallon fuskarta daduk yayi jurwayen hawaye, lallausan murmushi yasaki ahankali ya ce, "my Nusfulhayat sarakan kishi, Ashe kema rigimammace?,...da wannan tunanin yakaita d'aki itama, yadawo yakwashi tarkacensa yay ciki.

    Bai tadasuba amma cikin dabara yasauya musu kayansu zuwa na barci, yamik'e yanufi d'akinsa, shima wankan yayi sannan yazauna yaci naman ya k'oshi yad'ora da ruwa mai sanyi, yay hamdala ga ubangiji ya mik'e Yakoma d'akin Rahma.

      Shima gadon yahaye yakwanta a bayanta tareda rungumeta, hannu yakai danufi shafa fuskarta amma amamakisa sai yaji hawaye sha6e² wasu na korar wasu.

     Tashi yayi zaune ya kunna fitilar d'akin yana mai kallon fuskarta, yakai tsawon minti 6 ahaka, amma har sannan kukan takeyi kuma idonta arufe ruf.

   gyarama Nawal kwanciya yayi, itakuma Rahma yad'auketa cak yay waje, duk abinda yakeyi tana jinsa amma tak'iyin koda motshin kwarai.

   Koda ya direta asaman gado saiya kuma dawowa yakashema Nawal fitila yasake yimata addu'a, Yakoma Inda yabarta anan yatarar da ita, yagirgiza kai kawai yakashe fitilar tareda hayewa gadon.

      Jawota yayi jikinsa yarungume, cikin taushin murya ya ce, "my Nusfulhayat!.

    Shiru Rahma tayi kamarma batasan da wata halittaba awajen, yakira sunanta yakai so hud'u amma ko motsi batayiba, ajiyar zuciya ya sauke tareda k'ara k'ank'ameta ajikinsa yana aika mata da wasu sakwanni cikin nutsuwa da kwarewa.

    K'arfin kukan Rahma ne yak'aru, tad'an fara mutsu mutsu ganin haka sai kawai ya manne bakinsa da NATA........


  

  Hummm saida safenku bobo.


Washe gari tunda yadawo sallar asuba bai Tarar da Rahma ad'akin saba, yata6a k'ofar d'akinta yaji gam. Kyaleta yayi yatafi d'akinsa yakwanta.

       Rahma kam tana zaune tana jinsa, saida taji shiru alamar yakoma d'akinsa sannan tafito tahau hidimar gyran gidan da had'a breakfast, fuskarta dukta kumbura saboda kukan datayi, yanzun haka tana aikinne babu ko d'igon walwala atattare da ita.

    Bayan ta kammala aikin tsaf tayima Nawal wanka tamata shirin makaranta, itama wankan tashiga, batawani dad'eba tafito, 'Yar kwalliya tayi cikin atanfa zani da riga takama hannun Nawal suka fito falo.

       Bayan sun hau dinning ta had'a musu breakfast, Nawal ta kalleta cikeda shagwa6a momyna ina papana?.

    Kallonta Rahma tayi da zummar mata magana saiga bobo yafito cikin shigar gayun zamani ajin farko.

   Dukda tana fushi dashi ita kanta saida ta yaba, kauda kanta tayi daga kallonsa, yad'an ta6e bakinsa afili ya ce, "gulma.

   Tana jinsa kuma tasan da ita yake amma ta share kamar batasan yana yibama.

     Sumbatar kumatun Nawal yayi, itama yabata nasa tayimasa, ta gaisheshi, fuskarsa cikeda murmushi ya amsa, yak'arasa inda Rahma take, muryarta can k'asa ta ce, " ina kwana?.

    Bai amsaba saida ya sumbaci kumatunta, acikin kunnenta ya CE, "inafata kintashi lfy?, sarauniyar zuciyata. 

    Batako kalleshiba tacigaba da bama Nawal break abaki.

   Shima baikuma cewa komaiba yad'auki cokali yasaka a abincin nasu yanaci, shayin gaban Rahma yajanyo yafara sha, yitayi kamar bata gansaba har suka kammala suka mik'e.

     Yauma saida suka fara ajiye Nawal a school sannan yakaita gidan Appa, yanda tashareshi babu magana shima haka ya shareta, saidaifa idan yafaki idonta saiya kunshe baki yana dariyar mugunta, itadai batamasan yanayiba.

     Agurguje ya gaisa da mutane yafice Dan zuwa office, bayaso ya had'u da yayyensa ko d'aya.

    Gaba d'aya yinin Ranar haka Rahma tayisa sukuku babu walwala, kuma ko kad'an bata kula Safna bare shiga sabgarta.

    Dukda Safna bataji dad'in hakaba amma taso ace Rahma ta fahimceta, saidai zatayi hak'uri har shi dakansa ya kwance kullin kamar yanda yagaya mata ajiya.

     Ammi taso fuskantar wani Abu amma hidimar saukar bak'i ta d'auke hankalinta gabad'aya, saidai dukda haka saida ta tambayi Rahma gameda kumburin fuskarta, sai Rahman tace tayi zazza6ine jiya da daddare.

    Ammi Tamata sannu dukda bata yarda da abinda taceba, amma tabar komai sai zuwa bayan biki.


*_4:15pm._* na yamma aka fara gudanar da kamu wanda ya k'awatar da jama'a, amare sunsha k'yau masha ALLAHU kamar kasacesu ka gudu, dangin angunan sunzo kuma suntaka rawar gani ta burgewa, taron yakasance na mata zallah Dan haka babu su bobo awajen bama su dawo daga aikiba.

    Can na hango Rahma tasha k'yau cikin doguwar rigar material blue sun nad'a farin d'ankwali, ankone itada matan su ya Hamza, sunyi k'yau sosai dukda dai yau Rahma bata cika walwalaba amma tana iyakar k'ok'arinta Dan ganin tarage damuwar fuskarta.

   Abinda yak'ara mata dad'ima shine zuwansu Basma da ihsan da aunty Ameera, Anty Naja'atu matar ya Muneer, aunty haleema matar ya Shaheed duk sunzo mata, ganinsu yasakata sakin jikinta tanamai jin dad'in ganinsu.

    Alhmdllh kamu ya k'ayatar kuma antashi lfy kowa yakama gabansa.

      Mutane basu ida barbajewaba su bobo suka dawo, rarraba ido yashigayi danson hango matarsa amma yakasa ganinta.

    K'awayensu khairiyya sai fad'in kai guy d'innan ya had'u sukeyi, wau su khursiyya sumusu jagora wajensa.

   Khursiyya ta ce, "Ku yanafa da mata wlhy kubari babu ruwana, wlhy ya Abdulmaleek d'an hayak'ine, idanma kuka cigaba da yawan kallonsa sai rankowa ya6aci awajennan Dan haka ku kama kanku.

   Wata ta ce, " amma ba gidannan yakeba?, Dan ban sanshiba.

    Dariya khairiyya tayi ta ce, "to k'arewar gidannanma shi muke bimawa, dagashi saimu.

   Cikin mamaki sukace amma dai wasu sun rasu a tsakaninku?, kumafa mudai bamu sanshiba, kai 'yan biyu kuji tsoron Allah.

    Hhhhhh lallai baku yardaba kenan?, to yagirmemu sosai Dan  Ammi ta ce, " wajen ahekara 12 yabamu, bayan shi harma ta fiddarai da haihuwa saigamu mun wuntsilo, abinda yasa Baku sanshiba bashida hayaniyane, kuma bakowace sabga bace zaku ganshi aciki, shinefa wanda kukazo bikinsa wata biyar dasuka wuce baya.

    Idanu suka zaro, Zainab kabeer ta ce, ''wlhy bamu ganeshiba kinsan da daddare muka Ganshi awajen deener, masha ALLAHU, ina matarsa?.

    Tana nan bara zaku ganta aii.


Bobo dabaisan sunayiba yahaye saman mota yazauna Dan bayason shiga falon saboda duk matane, harabar gidan tad'anfi k'arancin mutane tunda an ragu, Taufiq babban d'an ya ishaq yakira, ya ce, "my son ina auntynka?.

   Taufiq ya ce, "uncle aunty Rahma?.

   Eh, ita.

Yanzu naganta itada heebba sunshiga falo.

   Yauwa jeka kiramin ita to.

   To uncle.

Babu dad'ewa saiga Taufiq yadawo ya ce, " uncle tana zuwa.

    Okey my son, yanzu kuma sai ina?.

      Uncle muna tarene nida abokaina.

   Kaima gayyan kayo wajen taron mata?, maimakon kabari sai ranar d'aurin aure ko gobe wajen brother's Night.

    Uncle aii duk zasuzo shima.

   Dariya bobo yayi ya ce, "to na mata.

    Shima Taufiq tafiya yayi wajen abokansa yana dariya.


   Na ce, " masha ALLAHU yaron yafara zama saurayi, su bobo ankusa ajiye surukai, lol.


Yana zaune awajen yana latsa waya saiga Rahma tafito.

   Kamshin turarenta kawai yaji yad'ago.

   Kallo d'aya tamasa ta kauda kai.

   Murmushi yayi yana kallonta, ya ce, "kai my Nusfulhayat kinyi k'yaufa, kamarma kece amaryar wlhy.

      Ganin ta kauda kai ya ce, "madam har yanzu fishinne?.

   Batace komaiba itadai, kuma fuskarta asake take gudun kar mutane su fahimci wani Abu.

    Ya ce, " my Nusfulhayat yunwafa nakeji, gashi duk mata agidan nama rasa yanda zanyi.

    Murmushi mugunta tayi ta ce, "ina Safnar tabaka abinci?, ko sak'one naje nafad'a mata?.

    Kallonta yayi ido cikin ido, tai saurin kauda kanta Dan bazata juri kallon cikin idonsaba, shima murmusawa yayi ya ce, " idanma kinyi hakan ai babu laifi, yadiro daga saman motar, ki kaimin falon su inna munacan nidasu ya Sulaiman.

   Baijira amsartaba yawuce............









*_"happy juma'at Mubarak."_*🙋🏼🙋🏼🙋🏼🙋🏼






*_luv u oll._*

*_(((S)))......2017_*



👩🏻‍💻typing........


❣ *_ABDUL-MALEEK_*❣

      _•🅱🅾🅱🅾•_



*_NA_*

_*Bilyn Abdul*_


_sadaukarwa_

*_Abba Gana_*

*_Batul mamman_*

*_Billy giro_*


_a *RASHIN SANI* nayi *AUREN K'ADDARA ko BIYAYYA,* mizan d'auketa?, *K'ANWAR UWACE ko KISHIYAR UWA?.* San zuciya yakawo sa6ani *NI DA AMINIYATA*, salon *NAWAFF* yasani fuskarntar *SABON AL'AMAREE*, *KUKAN KURCIYA JAWABINE* dan haka kugane *BAN SAKETA BA* masoyan *ABDUL-MALEEK BOBO* mukasance tare a *BABU SO, MIYA KAWO KISHI?!!!*._👌🏼

      _wad'annan sune rukunin jerin books dani bilyn Abdul narubuta a social media._

   Zaku iya samunsu a shafina kamar haka.👇🏻

https://mrsbilkisa.blogspot.com

     *_sai kunje👌🏼._*

*_BAK'IN HAURE!_*

    zaizone a sabuwar shekarar 2018 insha ALLAHU, karku bari ayi babu ku😘.


6⃣4⃣


   Binsa tayi dakallo tana k'unk'unai, amma baijitaba Dan yayi gaba abinsa.

    Safna tana dagacan saman kujera tana kallonsu, hawaye suka cika mata ido taisaurin saka handkyn daya bata jiya tagoge, ta Yanke shawara yau zatabi su Ameera sutafi gida, Dan inhar tana ganin bobo bata tunanin sonsa zai ragu azuciyarta barema ayi tunanin fita gaba d'aya, amma idan tayi nesa dashi k'ila taji sauk'in zuciyarta, Dan insha ALLAHU tayi tuba na gsky kenan.


Rahma tahad'a musu abincin Wanda dama tun d'azu ta tanada domin su, ihsan da Basma ne suka tayata d'auka zuwa 6angaren inna.

      Duk sunacan harda Ammar dawasu mutum biyu dabata saniba, bayan sun ajiye suka gaidasu, idanun bobo nakan matarsa, itama tasaci kallonsa ganin idonsa akanta yasa ta kauda idonta tareda Jan hannun su ilham suka fice.


...........................÷

      Bayan sallar isha'i su anty Hafsat sukace zasu wuce, Safna data gama had'a kayanta tamik'e itama, kallonta kawai Rahma takeyi amma batace komaiba, su dama su aunty Ameera tafad'a musu zata bisu Dan gidan yacika damutane kuma Rahma anan zata kwana itama, basu kawo komai aransuba sukace eh gara kawai tatafi gida.

      Har harabar gidan tarakasu saida suka Shiga mota taga fitarsu sannan takoma ciki.

       Amota Safna cikin dabara take share hawayenta, wata zuciyarta tana fad'a mata anya zata iya daurewa kuwa?, da sauri ta ce, "insha ALLAHU zan iya.


.+.+.+.+.+.

      Tafiyarsu Safna babu dad'ewa sosai bobo yashigo falon, wasu kallo sukeyi wasukuwama harsun kwanta, yagaidasu sannan ya haura sama, afalo yatarar dasu zaune sunata kulla kayan rabo, zama yayi yana fad'in wai Kodai yau anan zamu kwanane?.

     Kallonsa ammi tayi, ta ce, " nidama zaku barsu su kwanan Aida yafimin, idan bamu gamk'ullin nan yauba nasan zuwa gobe gidannan zai d'inke da mutane.

     Kansa yashafa yana d'an murmushi Ammi sudai gama kawai saimu wuce ko zuwa 12 ne.

     Hararsa Ammi tayi cikin wasa, ta CE, "fin k'arfi za'a nunamin akan 'ya'yana?.

       A'a Ammi mu mun isane.

    Hira sukaitayi har su ya ishaq suka shigo suka had'u gabad'aya sukayi k'ullin sannan kowa ya d'auki matarsa sukai gida.


Biki yacigaba da kankama cikin farin ciki, komai yana tafiya yanda yadace, washe gari da safe akayi k'unshi, zuwa yamma gida kam ya d'inke da bak'i na nesa Dana kusa, su Rahma kam aii ko ganinsu ba'ayi Duk sun zama busy, to barema su bobo manya manyan yayye.

     Da daddre k'arfe takwas aka fara d'ibar mutane zuwa wajen brother's night dasu bobo suka shirya, abokansu sosai suka gayyato, taron 'yammata da samarine kawai saikuma irinsu bobo masu mata, amma babu yara bare tsofaffi.

    Taro yak'ayatar kam masha ALLAH, amare da angwayensu ansha k'yau abin sai Wanda yagani, su bobo suntaka rawar gani irinta manyan yayye, ko INA yashiga yana mak'ale da matarsa abin zak'yk'yau da burgewa, 'yammata kam dayawa sun k'yasa, saidai ganinsa mak'ale da matarsa yakansa sushiga taitayinsu.

    Alhmdllh dahaka taro yatashi lfy kowa Yakama gabansa.


_washe gari_ 

     Aka d'aura auren khairiyya Aliyu Abdulmaleek hamshak'i da angonta Ahmad m sadiq, sai Khursiyya Aliyu Abdulmaleek hamshak'i da angonta Zaharadden usman Aliyu.

      Masha ALLAH d'aurin aure yatara d'unbin jama'a nanesa Dana kusa 'yan siyasa da masu mulki, 'yan kasuwama ba'a barsu abayaba.

    To khairiyya da khursiyya saimuce ALLAH yasanya alkairi yabada zaman lfy da zaman hak'uri.

    Hummmm abun mamaki wai harda alhaji sunusi dala a 'yan d'aurin aure, (araina nace su alhaji sunusi anji yaji🌶🤣 ahanun bobonmu😎😂😜) aiko bobo sai antaya MASA kallon banza yakeyi.

    Shidai baimasan yanayiba.


Bayan kammala d'aurin aure su bobo sukaima anguna  jagora zuwa cikin gidan, shidasu Yaya ishaq duk wankan farar shadda sukayi, masha ALLAH daka gansu kaga 'yan uwa jini d'aya.

      Har cikin falon suka Shiga anata gaisawa da 'yan uwa da abokan arzik'i, bakin anguna yak'i rufuwa hakama su ya sulaiman suna cikeda farin cikin yau k'annensu sunyi aure.

     Tunda sukashigo falon bobo yaketa baza ido domin hango Nusfulhayat d'insa, rabonsa da ganinta tun jiya bayan sun dawo daga faty.

    Ganin duk d'unbin taron Matan falon bai Gantaba har sama dasuka haura aka gaisa dasu ammi nanma bata nan baimaga Matan yayyensaba ko d'aya.

          Sakkowa yayi yabarosu a can, wayarsa yaciro a aljihu yafara kiran number ta amma bata d'aukaba, yana nan tsaye yanad'an waige waige saiga Nasiba zata shige itada wasu 'yammata, Nasiba ta gaidashi ya bobo ina yini.

   Juyowa yayi danson ganin wanene, oh Nasiba dama kinzo?.

   Wlhy nazo jiya Yaya, tunda nazo bangankaba kaida ya sulaiman, amma naga ya hamza da ya ishaq.

   Muna nan muma munyi busy ne da yawa, Dan ALLAH ko kin ganemin Rahma?.

   Aunty Rahma, naganta anan baya itada umminta da Ammi dawasu mata, saidai ban saniba ko sun koma ciki.

    Kai a'a bata ciki, amma ummi da Ammi nagansu aciki.

   Okey bara na duba maka ita.

    Ok thanks.


Post a Comment