BUZU BOOK 3 HAUSA NOVEL




78

Gaban Nana ya faΙ—i, cikin tsoro da razani ta ce "Waye? Waye a nan?" Sai dai shiru ba a yi mata magana ba.


Ta kunna fitilar kawai ta ga Imam Hammad a tsaye a cikin Ι—akin. Ja da baya ta yi a razane tana toshe bakinta saboda ihun da take shirin kurmawa saboda razani da tsoro.

"Idan ki ka yi ihun da Asal ta ji ki, za ki yi mata bayanin abin da ya kawo ni Ι—akin nan, kuma duk hukuncin da ta zartar a kan ki sai an yi miki shi, komai tsaurin sa."


Ta marairaice ido tana kallon sa cike da tsoro.

Ya tako a hankali ya Ζ™araso gabanta, ya zuba mata idanunsa da suka Ζ™ara rikita ta, jikinta har tsuma yake yi.


"Wace ce ke?" Ya yi maganar yana kafe ta da idanunsa.


"Ni ba kowa ba ce" Ta furta jikinta na tsuma cike da tsoron ko yana hayyacinsa jiya da ta je turakarsa.


"Ki gaya mini wace ce ke? Kuma da wace manufar ki ka zo gidan nan?"


Ta rintse idanunta tana girgiza masa kai ta ce "Wallahi ni ba kowa ba ce ba, Matarka ce ma ta kawo ni nan"


"Kin sanni a wani gurin kafin nan?" Ta Ι—ago kai ta kalle shi, ta girgiza masa kai a hankali, idanunta na cika da hawaye.


"Kin hana ni cin ayaba, kin ci kin yi rashin lafiya, kin hana ni hawa kan taguwa, na hau na faΙ—o. Idan na ganki ina jin wasu abubuwa da ba na ganewa a jikina, tamkar ke ba Ι—an Adam ba ce. ƊanΙ—anon Abincinki na yi mini kama da wani Abinci da nake ci a wani guri da ba zan iya tunawa ba, idan ba Abincin da ki ka dafa ba, ba ya yi mini Ι—anΙ—ano a bakina. Ki na shafa irin turarena kin ba ni madara da habbatussauda, wani abu da ba kowa ya san ina sha ba. Ki gaya mini wace ce ke, kuma a ina ki ka sanni?" Ya yi maganar yana Ζ™ara matsawa daf da ita yana Ζ™ara Ι—aga mata murya.


"Ni ban sanka ba, ban taΙ“a zuwa Agadez ba sai a wannan karon, ni babu abin da na sani game da kai" Ta yi maganar hawaye na ta sintiri a kan fuskarta.


Ya numfasa ya ce "Idan wani ne ma ya turo ki, ki ke yi mini wasa da hankali, ki ji tsoron Allah, jarrabawoyin da suka yi wa rayuwata ma Ζ™awaanya sun ishe ni. Kar ki bari na kama ki da kowane irin nau'i na rashin gaskiya"

Ta yi shiru tana sunkuyar da kanta Ζ™asa.


"Nana ko?" Ta jinjina masa kai cikin tsoro.


"Ki yi haΖ™uri na tsorata ki, ba na son Asal ta gane wani abu, za ta Ζ™ara tsanar ki ne." Daga haka ya juya ya bar Ι—akin nata.


Neman guri ta yi ta zauna tana mayar da numfashi, saboda yadda ta tsorata.


*****


Sagir ne ya Ι—auki Yusra suka tafi gidan su Shukura, domin Ζ™ara jajantawa juna tare da su Hajiya Amina, ta kuma tabattar da iyayen Shukura ba sa zarginta da Ι“atan Yusra kamar yadda take faΙ—a.


A babban falon gidan suka zauna, Hajiya Amina duk ta rame saboda tashin hankali da kuma damuwa.

Gefe ga Yusuf yayan Shukura, da shi ma fuskarsa take Ι—auke da damuwa.

Bayan sun gaisa Hajiya Amina ta ce "Sagir har yanzu babu wani labari game da Ι“atan Shukura ko?"


"Wallahi Mami babu, na yi sintirin gurin jami'an tsaro amma babu wani labari, kullum sai dai su ce mini a kan bincike. An kasa tracking Ι—in in da wayarta take, abin dai sha'anin binciken na rasa gane wane iri ake yi"


Hajiya Amina ta ce "Babu komai, akwai Allah mu ci gaba da gaya masa, in sha Allah za ta kuΙ“uta"


Alhaji Zailani ne ya fito da shirin fita, Cikin girmamawa.


Bai amsa ba ya ce "Yaya ake ciki da batun Shukura haryanzu babu wani labari?"


"Eh Daddy, amma mu na ta addu'a in sha Allah za a gan ta"


"Ka ga ni fa na gaji da wannan kwana-kwanar, ta Ι“angarena zan Ζ™ara saka wa a tsananta bincike, dan kai kan ka ban yarda da kai ba. Ta yaya za a ce rana tsaka a nemi yarinya a rasa ga tsohon ciki, kai me yasa ba a neme ka an rasa ba ko matarka sai ita?"


Hajiya Amina ta ce "Haba Alhaji, ya za a yi Sagir ya sanya a sace Shukura a sace ya kai ta ina?"


"Ni ki yi mini shiru, babu abin da ba zai iya faruwa ba" ya gama bambaminsa ya fita.


Hajiya Amina ta ce "Ka yi haΖ™uri Sagir, kawai yana cikin tashin hankali da damuwar Ι“atan Shukura ne. Dan Allah kar ka damu za a gan ta da yardar Allah"


Yusra ta ce "Da Ζ™awata tana nan wataΖ™ila da tuni ta gaya muku inda Shukura take".


Gaba Ι—aya suka kalli Yusra, ta ce "Eh Nana mana, ai kin tuna ta ko?" Ta yi maganar tana kallon Hajiya Amina.


Ta jinjina kai. Amma Sagir ya ce "Mami bari mu tafi, kin san ba ta da cikakkiyar lafiya ne"


Mami ta ce "Allah sarki, amma ta yi gaskiya na san Nana, a ina ki ka santa?"


Yusra sai ta yi shiru, saboda ba ta son ta ji an ce ba ta da cikakkiyar lafiya, amma tun da suka shigo gidan, ta ji Ζ™amshin Nana.


*****

Nana kuwa bayan sallar asuba, ta kashingiΙ—a tana ta zancen zuci, tana tunanin mece ce mafitarta ta Ζ™arshe, ta fuskanci kullum al'amuran cikin Ζ™ara rikice mata suke.

Wayarta ta Ι—aukko tana kallon hotunan Muhsin, kewarsa take yi sosai da sosai, har sai da hawaye ya cika mata ido. Sai ta yanke shawarar neman izini daga gurin Imam, ta je gida, dan ta ga ya fi Asal kan gado.


Sai dai wani abu mai kama da bacci ya Ι—auke ta, sai dai ta iya kiran shi da dannau, wato sleep paralysis, da wasu kan ce aljani ne yake danne mutum, ya yi iya Ζ™oΖ™arinsa gurin tashi amma ya kasa.

Iya Ζ™oΖ™arinta take son ta yi addu'a, amma ta kasa. Inuwar mutum ta gani ya shigo Ι—akin, amma ba ta iya tantance wane jinsin ba ne ba, mace ko namiji.

Inuwar na zuwa aka zare wayar da ke hannunta, aka fice.

Cikin razani da tsoro ta farka a galabaice tana ta haki tana rarraba ido, amma ba ta ga kowa a Ι—akin ba, ta laluba ta nemi wayarya ta rasa. Hankalinta ya yi mummunan tashi, ta Ι—aga fulon, ta zazzage inda take zaune, amma babu waya babu dalilinta.

Ta tashi cikin azama ta hau buΙ—e kayanta, ko wayar tana ciki, amma wayam babu waya babu dalilinta.

Ta fita da sauri ko za ta ga alamar wanda ya shigo sashen amma ba ta ga kowa ba.

Hankalinta ya yi mummunan tashi, saboda rashin sanin wanda ya shigo ya Ι—auke mata waya.


Gudun masifar Asal idan ta makara gurin hattama abinci ya sanya ta shiga Ι—akin girki.

Ta fito jiki a sanyaye tana gyaran falon Asal ta fito, kamar Nana ta share ta sai kuma ta ce mata "Barka da wannan lokaci"


"Yauwwa. Amm kar ki damu da ajiyewa Imam abinci, tun asuba baya nan, za su yi zaman majalisar Sultan." Nana ta jinjina kai.

Idan haka ne ba shi ne ya sake shigar mata Ι—aki ba kenan, to ko Asal ce?


Da sauri ta ce "Amm ranki ya daΙ—e, na ce dan Allah.. sai kuma ta yi shiru kar ta tambaye ta, ta canza mata fassara.


Asal ta ce "Ina sauraren ki"


"Amm shikenan ba komai" Asal ta yi gaba ta yi waje abin ta.


Gaba Ι—aya hankalin Nana ya Ζ™i kwanciya, ba ta san a hannun wa wayar take ba, ba ta san ta ina balli zai tashi ba, tun da wayar babu security a kai.

Ba kuma ta tunanin ma'aikatan gidan, saboda ba su da ikon shiga wannan sashen.


*****

Gaba Ι—aya su ke zaune cikin shiga ta alfarma ana tattaunawa, Sultan ya ce "Ina mai farincikin sanar da ku cewa kamfanin masarauta na zinari, zai shiga wata yarjejeniya da Ζ™asar faransa a kan zinari da kuma sindarin uranium da muke haΖ™owa. Dan haka ina ganin sai mu tura Imam Hammad da Omar, su je su karanta tsarin yarjejeniyar.

Sai kuma a nan gida mu na da taro shi ma, a kan yadda zamu bunΖ™asa harkar safarar raΖ™uma da muke yi zuwa Ζ™asashen Ζ™etare. Akwai buΖ™atar fito da sabbin hanyoyi na Ζ™ara faΙ—aΙ—a kiwon su da kuma shige da ficen su. Ina ga wannan da kaina zan je taron tare Imam Asad, Zahradeen"


Tafawa Maleek ya ce "Wai dan Allah Jalaludeen ba ka jin nauyinmu da ka ke fito da son zuciyarka da son kan ka Ζ™arara a gaban jama'a?"

Gaba Ι—aya suka Ι—aga kai su na kallon Tafawa.


"Za ka tura Ι—anka yarjejeniyar Zinari da sinadarin uranium, mu kuma ka haΙ—a ka 'ya'yanmu da harkar raΖ™uma"


Abduou matawalle ya ce "Tafawa, yakamata ka san abin da ka ke faΙ—a fa, Sultan ka ke yi wa magana"


"Ban saka da kai ba, da Ι—an uwana nake magana" Tafawa ya yi maganar yana dakatar da Matawalle.


Sultan ya yi murmushi ya ce "Ba abin da ka ke zargi ba ne Tafawa. Hammad ai Ι—anka ne, kuma ni duk matsayinsu Ι—aya a gurina."


"Ba matsayinsu Ι—aya ba, me yasa ba ka tura Zahradeen ba sai shi, mutumin da ko cikakkiyar lafiya ba shi da ita?"


Imam Zahradeen ya ce "Mai girma Tafawa, da ni da Imam Hammad ai duk Ι—aya ne, ni dan ya je masarautar Agadez ya wakilta babu wani abu a ciki"


"Yi mini shiru, kai har ka na da zarafin da ina magana da babanka ka din ga sanya baki? Ni na gaji da wannan bambanci da ka ke nunawa, sai Ζ™oΖ™ari ka ke lallai sai ka tura Ι—anka kan kujerar Sultan ta Ζ™arfin tsiya, bayan bai cancanta ba. Shi ba cikakkiyar lafiyar zuciya ba, ga rashin lafiyar Ζ™waΖ™walwa, kalli yatsunsa babu zobensa na tambari, ga shi tsawon shekaru da aure ba shi da magaji, ta yaya ka ke tunanin makaho ya jagoranci mai idanu? Ta yaya mutumi  da shi kansa ba zai iya tsayuwa da Ζ™afarsa ya yi rayuwa ba za a ce ya wakilci masarauta kamar Agadez a harkar kasuwanci"


Cikin tsawa Sardaunan Agadez ya ce "Wane irin lafazi ne wannan ka ke yi Tafawa? Kar ka manta da wanda ka ke magana, babu ruwan masarauta da gaba ka ke da Sultan, zamu iya sanyawa a warware rawaninka a hukunta ka. Hammad ba Ι—anka ba ne kai ma? 'yar ka fa yake aure, kuma Ι—an Ι—an uwanka ne, kai ba mai rufa masa asiri ba ne idan ma hakan ne? Batun zoben sa zamu yi bincike a kai, haihuwa kuma Allah ne yake bayar da ita, bai zama hujjar da za a ce an hana shi wata dama ba. Ko yana da Ι—a ko babu idan Allah ya nufi ya yi mulkin Agadez wallahi sai ya yi" Gaba Ι—aya gurin suka yi tsit.


Ya mayar da idonsa ga Sultan cikin girmamawa ya ce "Ina neman afuwa ya shugabana bisa Ι—aga murya da na yi a gaban sarki"


Hammad ya dubi Sultan a tsanake ya ce "Ina neman a yi mini izini, zan Ι—an fita" Da ka Sultan ya yi masa alama, ya yinΖ™ura ya tashi ya fita.

Zuciyar Sultan tamkar ta kama da wuta saboda damuwa da jin zafin kalaman Ι—an uwansa ga Ι—an nasa.


Kai tsaye Imam Hammad ya koma gida, zuciyarsa na yi masa wani irin zafi na maganganun da Tafawa ya faΙ—a a kansa.

Ɗakin saukar baΖ™insa ya wuce, da nufin ya zauna ya kaΙ—aice a ciki. Kawai ya tarar da Mahmoudu a Ι—akin.

Bai kula shi ba kawai ya nemi guri ya zauna idanun nan jawur.

Mahmoudu ya tashi ya koma kusa da shi, ya kalli yadda idanunsa suka yi jawur ya ce "Imam, lafiya kuwa?"

Yayi shiru kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Mahmoudu, ina son na roΖ™i Sultan ya cire ni daga duk wani abu da ya shafi harkar mulkin nan ba na so"


Mahmoudu ya waro ido ya ce "Saboda me? Kai ma ka san abin da ba zai yiwu ba ne ai. Ka riga ka kai matsayin Imam kuma ka san me hakan yake nufi"


"A cire ni a maye gurbina da wani, tun da akwa masu so. So nake na yi nesa da gidan nan, na samu nutsuwa na yi rayuwata cike da 'yanci yadda babu wanda zai dame ni ya takura mini. Gidan nan ji nake yi tamkar a kan wuta nake. A kan abin da bai taka kara ya karya ba an ci mini mutunci ana ce mini juya. Ni Tafawa yake ci wa mutunci saboda kawai Sultan ya ce na je faransa na wakilci masarauta? Wallahi wataran za su neme ni su rasa"

"Mahmoudu a ransa ya ce wancan karon ma da ka gudu ni ka saka a bala'i'


A zahiri ya ce "Dan Allah ka yi haΖ™uri, duk inda ka je ma ba zaka iya zama ba sai ka dawo, dan Allah ka yi haΖ™uri"


Ya yi wa Mahmoudu shiru, ya lumshe idanunsa.


Yana kwance a kan cinyarta, ya zuba mata idanu yana kallonta. Sai shafa gashin kansa take yi tana yi masa murmushi mai Ζ™ayatarwa. Bai yi mata magana ba, ita ma ba ta yi masa ba, amma yanayin ya yi masa daΙ—i sosai da sosai.


Wata babbar mace ce a zaune, tana ta huci tamkar za ta fashe, cikin takaici da Ζ™unar rai take kallon matashin saurayin da yake gabanta.

"Zahradeen wai kai wane irin mutum ne mara kishin zuci da bai san ciwon kansa ba? Ina nan na samu labarin ka na cewa Sultan wai a tura Hammad wakilci kai da shi duk abu Ι—aya ne, a gidan uban wa ku ke abu Ι—aya, ana Ζ™oΖ™arin nemo muku 'yanci, amma kai kana shirme da shiririta?. Ƙarara Sultan yake nuna bambanci a tsakaninku ammma kamar ya yi maka asiri ka zama nusari. To wallahi ni ba nusara ba ce, ban tsaya tsayin daka ka zama Imam ba, sai dan ka zama Sultan Ι—in Agadez. Dan haka ba zan zuba ido shashancinka ya Ι“ata mini wahalata ba na gaya maka".

Zahradeen ya yi shiru bai ce komai ba, shi sam bai ga wani abu da Sultan yake yi na nuna fifiko a kan Hammad ba, kawai yana ba shi kulawa ta musamman ne, saboda yanayin matsalar hawan jini da yake da ita, da kuma rashin mahaifiya.

Aka ci gaba da dambarwa, a kan tafiyar sa Faransa.

Ko da aka koma zaman tattaunawa, Mayan 'yan majalisar Sultan ra'ayinsu ya kasu biyu, wasu su na goyon bayan a tura Hammad, saboda nagartarsa da jajircewa ya cancanta mussaman da duk ya fi sauran Imam Imam Ι—in ilmi da mu'amala, ga yarurruka da yake ji. Ya yinda wasu suka goyi bayan Tafawa a kan Hammad ba zai ce wakilci Agadez ba, sai sun ji ba'asin zobensa, sai kuma sun ji matakin lafiyar Ζ™waΖ™walwarsa. Da rahoton lafiyarsa na tsawon shekarun da ya yi a faransa.

Wannan Ζ™a'idoji da suka shimfiΙ—a Ζ™a'idoji ne da sai an kwashe lokaci kafin cika su, wanda har lokacin taron ya zo ya wuce, ba a kammala cika su ba.


Ganin gurin zai sake yamutsewa, ya sanya Imam Hammad yin gyaran murya. Cikin girmamawa ya ce "Ina godiya matuΖ™a da wannan dama da aka so ba ni, amma zaman lafiya da kwanciyar hankalin Agadez shi ne a gaba da komai. Ina roΖ™on a yi mini alfarmar yi mini afuwa, ba zan samu damar yin tafiya wakilcin nan ba, sakamakon hali na rashin lafiya da nake fama, ciwo zai iya kama ni a ko ina, dan haka Tafawa ya yi gaskiya, ina buΖ™atar hutu"


Cikin tsawa Sardauna ya ce "Ba kai ka ke da wannan hurumin ba."


"Mai girma Sardauna, gaskiya Tafawa ya faΙ—a, ban cancanci duk wannan abubuwan ba, shugabancin Imam ma zan sauka na nemi lafiyata"


"Mun san ba ka da lafiya, amma ka ka na kan magani, dan haka larura ba za ta hana ka aiki ba"


"Larurar Ζ™waΖ™walwa, mahaukaci ba zai wakilci masu hankali ba, ina neman afuwarku"


Daga wannan maganar ya yi waje, saboda yadda idanunsa suka yi jawur, jikinsa ya fara tsuma.


Tsit gurin ya yi aka hau kallon-kallo.


Sardauna ya ce "Ka ga abin da ka janyo ko?"


"Ai ba Ζ™arya na yi ba, shi ya faΙ—i cewa Ζ™arya nake yi Ι—an sa ba mahaukaci ba ne?" Ya yi maganar yana kallon Sultan.


AREWABOOKS 


Har wani duhu yake gani a idanunsa, saboda matsanancin Ι“acin rai da tashin hankali. Mutumin da yake uba a gare shi, shi ne ya yi masa wannan kausasan laffuzan a gaban jama'a.

Ya daΙ—e yana nuna masa Ζ™iyayya, amma lamarin bai fito Ζ™arara ba sai bayan da ya zama Imam.  Mussaman wannan dswowar da ya yi, dan ya matsa a kan lallai sai ya ji wani ciwon ne ya zaunar da shi a Ζ™asar waje har shekara biyu, kuma aka hana kowa zuwa duba shi?

Ya kawo kai cikin falo, Nana tana ta aikace-aikacenta. Ɗan turus ta yi bayan da ta tuna Asal ta ce mata ba yanzu zai dawo ba. Fuuu ta ga ya nufi uwar Ι—akinsa. Ta Ι—an taΙ“e baki ta ci gaba da aikin gabanta. Sai dai zuciyarta na kan abin da ya sanya shi cikin fushi da tashin hankali haka.

Duk da ba ta da wani kusanci da shi a wannan Duniyar tasa, amma mutum ne mara magana, amma yana da yawan fara'a.


Asal ta fito daga wanka ta gan shi kwance a kan gado. Ta kalle shi ta ce "Amour ya na ga ka dawo kuma? Lafiya kuwa?" Muryar Asal kawai ta fusata shi, saboda abin da mahaifinta ya yi masa a fitarsa. Dan haka ya yi mata banza.

Ta nufi gaban mudubi ta amsa wayar da take ta ringing, ta ajiye ta dawo ta dube shi ta ce "Sultan yana neman ka a sashen sa yanzun nan"

Ya yi mata shiru, bai yi magana ba, ta nufe shi ta zauna a kusa da shi, ta Ι—ora hannunta a kan kafaΙ—arsa. Ya tashi zaune a fusace ya ture hannun Asal, ya tashi ya fita.

Sororo ta tsaya tana mamakin me yake damunsa haka?

Gaba Ι—aya ya fita ya bar sashen.


****

Cikin matsananciyar damuwa Mama take kallon Jamila da ta yi wata irin rama mara fasali, duk ta bushe ta yi haske sai uban kai Ι—auke da gashi.


"Jamila ni fa na rasa gane kan ki gaba Ι—aya, kalli yadda ki ka koma, dole ki shirya mu je gurin masu magani ko mayu ne suka kama ki, ki ke ta wannan wahalar duk kin Ζ™i lafiya"


"Ni babu wasu mayu da suka kama ni"


"To idan ba mayu ba wannan ciwon na mene ne haka? Fitar nan ma da ki ke yi gurin kasuwancin naku kin daina gaba Ι—aya"


"Ki Ζ™yale ni zan warke ne" Ta yi maganar cikin Ζ™osawa da maganganun Mama.


Su na haka Yaya Atine ta yi sallama, Mama ta amsa tana yi mata maraba.


Mama ta ce "Ke ki ke tafe a yammacin nan?"


Ta ce "Wallahi kuwa, na ga kwana biyu ban leΖ™o ba, na ce bari na shigo, Isan ba ya nan ne?"


"Eh ya fita baya nan"


"Ita kuma wannan fa?"


Cikin damuwa Mama ta ce "Ba ta da lafiya ne, nayi-nayi da ita, mu je gurin mai magani ta Ζ™i yarda, ga na Asibitin an yi ya Ζ™i jiki kullum Ζ™ara rikicewa yake yi"

"To me yake damunta ne har haka?"

Mama ta ce "To gata nan dai, kullum zazzaΙ“i ba ta kuma son cin abinci ko fita ba ta yi, na Asibitin ya Ζ™i yi mata, mu koma na gargajiya ta Ζ™i"


Yaya Atine ta Ι—an zura wa Jamila ido, har sai da haushi ya kama Jamila, ta tashi ta bar gurin. Yaya Atine ta ce "Mhmm" Ta Ι—aukko wata hirar daban.


Ba ta wani jima ba ta yi wa Mama sallama ta tafi, sai dai cikin sa'a ta haΙ—u da Baba a Ζ™arshen layin, dan haka ta zauna suka dasa hira a hanya.

Ta ce "Ashe Jamila babu lafiya?"

"Eh wallahi ana ta fama, an kasa gane abin da yake damun ta"


"Lallai, to gaskiya yakamata ku zurfafa bincike dan kuwa Ι—an yau ka haife shi ne, amma ba ka haifi halinsa ba"

Cikin rashin fahimta ya ce "Me ki ke nufi?"


"Ni babu abin da nake nufi, balle a ce na ce, ni dai kawai na ce a zurfafa bincike ka ga tafiyata" Ya yi shiru yana nazarin maganganun 'yar uwattasa.


****


Cikin fushi Sultan yake kallon Imam Hammad, ji yake yi tamkar ya kwaΙ—a masa mari ko ya huce.

"Sai yanzu ka ga damar amsa kiran nawa?"


Ya girgiza kai ya ce "A yi mini afuwa, jikina ne ya so motsa mini shi ya sanya ban samu fitowa ba"


Sai kuma ya sassauta murya ya ce "Wani abin ne ya faru da kai bayan tafiyar taka?" Ya girgiza wa Sultan kai.


Cikin rarrashi ya ce "Hammad, ba a cin nasara da karaya da kuma miΖ™a wuya farat Ι—aya. Kuma Tafawa Maleeka bai yi Ζ™arya ba, ina son ka gaje kujerar Sultan ba dan komai ba sai domin ina buri da fatan ka gyara kura-kuran da na aikata a baya. Ni ba ina burin ka zama Sultan domin son zuciya ko wani abu ba, ko iya haka Allah ya yi maka mai kyau a duniya, ina yi maka fatan mai kyau a Lahira. Ka ma da ilimi, ka na da dukiya, ka na da mulki iko ka ke buΖ™ata gurin aiwatar da wasu abubuwan.

Kai kaΙ—ai ne kujerata ba ta gabanka, kuma ka fi ni jajircewa da tsayawa a kan ra'ayinka da aΖ™idarka, burikanka a kan Agadez da Ζ™udure-Ζ™udirenka abubuwa ne da za su sauya rayuwar mutane da dama, saΙ“anin sauran da hawan kujerar ne kawai a gaban su, ba Ζ™alubale da abubuwan da suka kamata ba. Dan Allah ka yi haΖ™uri ka jure kar ka watsa mini Ζ™asa a ido. Wannan nagartar taka ya sanya manyan nan na majalissata suka Ζ™ara tsanarka ba wani abu ba"


Imam Hammad ya numfasa ya ce "Abie na ji duk bayananka. Amma ka yi haΖ™uri na riga na karaya, kalaman da ake jifa na da su sun yi tsauri da muni, su na taΙ“a zuciyata da yawa"


"Na sani, ba na buΖ™atar ka musanta abin da na zo da shi, ka yi mini biyayya kawai. Kuma majalisa sun zartar da hukunci a kan Tafawa bisa abin da ya aikata"


Hammad ya kalli Sultan ya ce "Ina fatan ba wani abin mai tsauri suka yanke a kansa ba, kar alaΖ™a tsakanina da shi ta Ζ™ara yin tsami, ga 'yar sa ina aure. Ko ba komai uba ne a gare ni, kuma Asal Ζ™anwata ce kuma matata"


Sultan ya girgiza kai ya ce "Kar ka damu, hukuncin ba zai shafi nasaba da dangantaka ba, ka je ka samu ka huta" Ya risuna cikin girmamawa ya yi godiya ya fita.


Bayan fitarsa Sultan ya zauna, zuciyarsa cunkushe da damuwa, tunani yake yi yaya aka yi Tafawa ya san batun larurar Hammad. 

Ya yi tunanin ko Asal ce ta gaya masa, amma ko Asal ba ta san taΙ“in hankali Hammad ya yi ba, kawai dai ciwo ne yake kama shi, gangar jikinsa ta sauya, ya din ga wannan jijjigar da kakarin.

*****

Kaiwa da komowa Tafawa yake yi a cikin falonsa, zuciyarsa a cunkushe da baΖ™in ciki, bayan tuna yadda wasu daga cikin majalisar Sultan suka Ζ™aryata shi, bayan da ya faΙ—i cewa Hammad yana da taΙ“in hankali.

Ya yi Ζ™wafa ya ce "Da ni ku ke zancen, sai na tabattar wa da Duniya Ι—an ka mahaukaci ne, sai ya yi hauka tuburan Duniya ta gani ta shaida, kujerar da ka ke Ζ™oΖ™arin cusa shi ya hau, sai ta zama haramiyarsa ta har gaban Abada. Mulkin ai ba da shi aka haifoka ba, da za ka ce lallai ka yi shi ma sai ya yi ba. A wancan karon mu na ji mu na gani, aka Ι—ora ka aka ce bamu cancanta ba, a wannan karon dole sarauta ta bar gidanka ta dawo gidana, Asadullah sai ya hau kujerar Sultan, ko ka na raye ko ka mutu".


*****

Tun da ya koma gida Asal ta share shi, shi ya manta ma abin da ya yi mata, ya ga tana basar da shi ga damuwa da yake ciki.


"C'heri'"


Ta Ι—ago ta kalle shi. "Me yake faruwa ne?"

Ta girgiza masa kai alamar babu komai.

"Idan na yi miki laifi ne, ki yi haΖ™uri, ina cikin damuwa ne kwanakin nan, ki din ga yi mini addu'a" Ya yi maganar yana hargitsa gashin kanta da ta gyara.

Ya nemi guri ya kwanta ya lumshe idanunsa, yana fatan bacci ya Ι—auke shi, ko ya samu sauΖ™in wannan damuwoyin.

Yana jin ta ta kashe fitilar Ι—akin, sai hasken fitila na gefen gado wanda ba mai takura ba ne. Ta hau kan gadon ta kwanta a bayansa, ta zura hannunta Ζ™irjinsa.

A hankali ya juyo, ya rungumeta sosai a jikinsa yana shafa bayanta, duk da ta ji haushin abun da ya yi mata Ι—azu, amma da yake ya Ζ™ware a iya mantar da mutum laifin da ya aikata masa, dole ta ba da kai bori ya hau. A hankali ya ji jikinsa ya fara Ι—aukar zafi. Ya raba Asal da jikinsa saboda yadda yake jin san tamkar an saka masa fetur an kunna wuta a jikinsa.

Ya miΖ™e ya din ga kaiwa yana komawa a Ι—akin, yana maimaita ya hayyu ya Ζ™ayyum. Ya shiga banΙ—aki ya haΙ—a ruwan Ι—umi ya yi wanka ya fito.

Kasa jurewa ya yi jin yana neman ya fita daga hayyacinsa, ya fita falo. Yana fita ya ji wannan dadaΙ—an sanyin ya ratsa shi. Kan sa tsaye ya nufi inda yake jin sanyin na fitowa wanda hanyar Ι—akin Nana ne.

A corridor din gurin ya yada zango, ya samu guri ya zauna, ya jingina da jikin bango yana numfarfashi.


*****


Kwanaki biyu a tsakani, aka kuma zama, sai dai a wannan karon ba da duka Imam Ι—in aka zauna ba, Hammad ne kawai, sai manyan masu faΙ—a a ji na kusa da Sultan, wanda an yi zaman ne saboda abin ya shafi Hammad Ι—in.


Sardauna ya yi gyaran murya ya ce "Imam Hammad, kamar yadda Tafawa ya buΖ™ata da shi da wasu daga cikin 'yan majalissar Sultan. Lallai mu na buΖ™atar jin gamsashshiyar amsar ina zobenka na tambarin Imam yake? Gamsashshiyar amsa mai cike da hujja muke so, na wai-wai ko kame-kame ba, dan ka san muhimmancin zoben idan babu shi dole za ka sauka daga kan muΖ™amin da ka ke kai.

Abu na gaba, mu na buΖ™atar sakamakon rahoton lafiyarka, na tsawon lokacin da a ka ce ka shafe a faransa kana jinya.

Kuma hakan baya nufin za a canza umarnin da Sultan ya yi? Zuwanka faransa wakiltar Agadez wajibi ne bisa ga sahalewar Sultan.

Kai kuma Tafawa, duk da uba ne kai ga Imam Hammad, kuma uba a Agadez za a hukuntaka bisa Ι—aga murya da yin jayayya da hukuncin da Sultan ya aiwatar, kamar yadda kwamitin ladabtarwa da sulhu ya yanke. Zaka kawo mana cikakkiyar shaida da hujja, ba wai-wai ko kame-kame ba, a kan Imam Hammad yana Ι—auke da larurar Ζ™waΖ™walwa, akasin haka za'a yanka maka tara mai yawan gaske ka biya shi.

Haka zalika an hukuntaka bisa amfani da kausasan laffuza a kan Imam Hammad, wanda yake shugaba ne da yake jagorantar Imam, da ake sanya ran zaman su sarakan gobe. Dan haka an dakatar da kai tsawon watanni shida, har sai ka gabatar da abin da aka nema daga gare ka"


Cikin fusata ya miΖ™e ya ce "Ai dama na sani, wata maΖ™arΖ™ashiyar da manaΖ™isar ake Ζ™ulla mini, saboda ba a Ζ™aunata. Amma shi Jalaludeen ya musa cewar Ι—ansa mahaukaci ne mana. Ciwon hauka ya yi suka kai shi suka Ι“oye amma aka ce jinya ya yi a Ζ™asar waje. Ba ku burge ni ba da ba sauke ni kuka yi daga muΖ™amina ba har abada ai.

Kuma na faΙ—a na maimaita, Hammad ba zai taΙ“a zama Sultan a Agadez ba, ba shi da lafiyar zuciya, ba shi da ta Ζ™waΖ™walwa kuma ba shi da magaji juya ne, dan haka mai baΖ™in baya ba zai yi mulki a Agadez ba"


Wani irin duka Hammad ya yi wa teburin gabansa da ya bayar da wani irin sauti.

Ya kalli Tafawa ya ce "'yar ka zaka tuhuma ya aka yi ba ta haihuwa? Ni mahaukaci ne ka zagaye Agadez kana maimaita hakan, kuma ba ni da lafiyar zuciya shi ma ban damu ba, na yi sarauta ko kar na yi bai dame ni ba, duk abu dai ka san kujerar Sultan ta fi Ζ™arfinka. Duk abin da za ka faΙ—a a kaina ka faΙ—a amma kar ka sake kira na da Juya mai baΖ™in baya, Asal ita ce juya ita zaka bincika dan ni ina da Ι—a, na haihu ba baΖ™in baya ne da ni ba! Zobe kuma ya Ι“ata ban san inda yake ba" Ɗif gurin ya yi, tamkar an yi ruwa an shanye, ko kuma babu mai sauran numfashi a gurin, saboda yadda maganganun nasa suke buΖ™atar fashin baΖ™i gwari-gwari.


*****


Hajiya Amina cikin damuwa da nuna rashin jin daΙ—inta take duban Alhaji Zailani ta ce "Alhaji ban ji daΙ—in yadda ka yi wa yaron nan mijin Shukura ba. Tare da mu da shi ake ta faΙ—i tashin neman Shukura, bai kamata a ce gaya masa maganganun da suke nuni da cewar wai zarginsa ka ke yi da sace Shukura ba"


Ya dube ta ya ce "To dan yana mijinta kar na zarge shi? Duniyar nan fa babu abin da ba zai iya faruwa ba, ni bincikena ba zai bar kowa ba, ya zama dole a binciki kowa, kuma ki rabu da ni da abin da yake damuna, ki Ζ™yale ni da maganar sani mijin Shukura"


Ta ce "Shikenan, ni ina gudun kar daga baya a zo a ji kunya ne"

Ya Ι—an Ι—ago da sauri ya ce "Me ki ke nufi?"


"Ahh a zo a ganta a gano ba shi da hannu a ciki, su ci gaba da zama da matarsa kai ka zo ka na jin kunya"


Ya yi guntun tsaki, yana sake miΖ™e Ζ™afafuwansa a kan gadon.


*****

Jamila ce a kwance dare ya tsala, amma ta yi Ζ™urii tana kallon roofing Ι—akin.

Tun da Abba ya koma ga Allah, bacci ya Ζ™aurace wa idanunta. Idan kuwa bacci Ι“arawo ya yi awon gaba da ita, to tabbas mafarkin Abba za ta yi ta yi, tana ganin sun yi aure ga yara ta haifa masa.

Sannu a hankali ta tafi tunanin abin da ya faru. Bayan da Hajiya Sa'a ta yi mata bayanin yadda za ta sadaukar da Ι—an gidan Alhaji Fatuhu Ζ™aninta.

Abin ya dame ta, ga shi ta san idan ta je ta sanar wa su Alhaji Fatuhu, asiri ne zai tonu har ita, kuma ma mene ne shaidarta, dan ta san tsaf Hajiya Sa'a za ta zame ta bar ta a ciki.

Ta yi tunanin ko ta sace 'yar tsanar, amma ta fasa, saboda yadda ta rabu da ta ta da Ζ™yar.

Bayan fitar Hajiya Sa'a, Jamila na kwance a falo bacci ya Ι—auke ta, ta yi mafarkin 'yar tsanar nan a Ζ™one ta yi baΖ™i ta biyo ta tana Ζ™oΖ™ari shige mata cikin riga tana wani irin kuka tsiii-tsiii. Cikin ihu ta tashi a razane. Lokacin Abba ya shigo Ι—akin, kawai ta cakume shi tana ihu.


"Ƙanwata lafiya kuwa?"

Ya yi maganar yana kallonta, a hankali ta cika shi, ta nemi guri ta zauna ta ce masa tsorata ta yi a bacci. Ya zauna yana yi mata nasihar mafarki ba gaskiya ba ne, kuma ta din ga addu'a, idan ba haka shaiΙ—anu za su iya shiga jikinta saboda wannan tsoron da take ji.

Sai dai har ta tafi gida, a tsorace take kuma tunani take yi, yaya za ta yi ta tseratar da Ι—an Alhaji Fatuhu.

Ta rasa abin da yake yi mata daΙ—i, ga 'yar tsana ta sako ta a gaba a mafarki, yanzu bin ta take yi da sata sharΙ“eΙ“iyar wuΖ™a a mafarkin za ta kashe ta.

Kawai ta yanke wata shawara a ranta, wajen Ζ™arfe sha Ι—aya ta je gidan Hajiya Sa'a, lokacin bata nan ta fita gantalinta, cikin sa'a ta duba inda ta ajiye 'yar tsanar da tarkacen kayan tsafin ta ga su na nan.

Ta kira Abba a waya, bayan sun gaisa ta tambaye shi yana ina, ya ce mata ya tafi kasuwa ta ce masa ya zo tana gidansu tana son ganinsa.

Ba a yi awa Ι—aya ba sai ga shi ya dawo, har da tsaraba ya sayo mata, cike da murnar ganinta, dan kwana biyu ta Ι—auke Ζ™afa da zuwa gidan.

Yanayin walwalar da ta gani a fuskarsa sai ta ji dana sanin kiransa da ta yi.

Sai dai ya takura mata a kan lallai sai ta gaya masa abin da ya sanya ta kirawo shi.

Ta Ι—ebo tarkacen nan na kayan tsafin Hajiya Sa'a, ta Zazzage masa a gabansa.


Cikin mamaki ya dube ta ya ce "Mene ne wannan haka?"


Ayshercool 

08081012143


79

Tabbas ba ka san ko mene ne ba, kuma na san za ka yi mamakin mene ne wannan Ι—in, amma ina mai baka haΖ™urin abin da zai fito daga bakina, ba ni da wani zaΙ“i ne nima, ina son yin ceton rai, na rasa wanda zan gayawa ya fahimce ni ya sama mini mafita ya rufa mini Asiri sai kai" Ta yi maganar cikin kuka.


Cikin damuwa da Ζ™aguwa ya ce "Babu komai, ko mene ne gaya mini. Wallahi Jamila ina jin ki a raina fiye da yadda ki ke zato, ki gaya mini dan Allah"

Ba ta tsallake masa komai ba, tun daga tariyar Maman Khairat a unguwar su, da fara zuwa gidanta zuwa haΙ—uwa da Hajiya Sa'a, ta gangaro har kan neman jinin Nana yadda suka saka ta a Ζ™ungiyar asiri abin da aka yi mata, hatta labaran da Hajiya Sa'a ta ba ta na yadda ta shiga Ζ™ungiyar sai da ta gaya masa.


Jamila za ta iya cewa tun da take, ba ta taΙ“a ganin idanun Ι—an Adam sun yi jan da na Abba suka yi ba.

Ya Ζ™ame a guri Ι—aya tamkar babu rai a jikinsa.


Cikin rikicewa ta ce "Dan Allah Yaya Abba ka yi haΖ™uri ka yafe mini, ban gaya maka dan na haΙ—a ka da mahaifiyarka ba ko makamancin haka, ceton rai nake fatan mu yi, bawan Allah nan da yake rashin lafiya kar ya kuma rasa Ι—an sa. Kuma dama ni na san mutuwa zan yi, dan ba zan iya bayar da kowa ba ga barazana kuma da ake ta yi mini a mafarki. Dan Allah ka yafe mini ban faΙ—a dan na haΙ—a ka da mahaifiyarka ba.


Idanunsa suka fara tsiyayar da hawaye, yayi kuka, ya yi kuka, Jamila kuma ta kasa rarrashinsa, can ya ce "Tabbas! Biri ya yi kama da mutum, yanayin facakar da Mummy take yi da kuΙ—i tamkar ba ta san zafin neman su ba abin yana Ι—aure mini kai. Ina kula da harkokin kasuwancinta, amma na san abin da take kashewa ya ninka abin da muke samu. Kuma duk yadda zan bi na gano wani abu sai ta toshe.

Jamila na ji daΙ—i sosai da sosai, da ba ki gaya wa wani abin da take aikatawa ba, kuma na ji daΙ—in Ζ™oΖ™arin kare kisan Ι—an Ι—an uwanta. Amma na yi mamakin yadda ta iya bayar da mahaifinmu saboda abin Duniya.

Ita ma idan ba ta sadaukar da kowa ba mutuwa za ta yi ko?"


Jamila ta jinjina masa kai tana kuka.

Ya ce "Shikenan, babu komai, ki daina kuka, daga ke har ita ba zaku mutu ba, zan zama abin sadaukarwar ku, sai dai daga ni ina fatan duk yadda za ki yi ki fita daga cikin kungiyar nan. A razane Jamila ta ce "A'a ba zai yiwu ba, ban gaya maka dan ka Ι—au wannan Ι—anyen hukuncin ba, mafita zaka nemo"


Abba ya ce "Wace mafitar Jamila? Na nuna wa Mummy na san abin da take yi? Ko na bari ke ko ita wani ya rasa ransa? Ko kuma Ι—an Kawu Fatuhu da bai ji ba bai gani ba? Dan Allah Jamila duk yadda za ki yi kar ki yadda ki bayar da jinin wani, ki kuma bar kungiyar nan. Wallahi Jamila kuΙ—i ba su ne kwanciyar hankali da nutsuwar Ι—an Adam ba."

"Yaya Abba to me zaka yi?"


"Ni zan zama abin sadaukarwar taku?"


Ta girgiza kai ta ce "Ba zai yiwu ba gaskiya, na bayar da jininka kenan, ai gara ni na bayar da jinina ba zai yiwu ba"


Ya ce "Ba ke za ki bayar ba, ni zan bayar da kaina, ina fatan hakan ya zame wa Mummy darasi, ya kuma yi silar fitarta daga abin da take aikatawa"


Cikin kuka Jamila ta riΖ™e hannunsa ta ce "Idan ka yi haka ka kashe kanka fa kenan?"


"Jamila wa zan tunkara ya lalata Wannan abun asirin Mahaifiyata ya tonu tana Kungiyar asiri? Wane kallo Ι—an uwanta zai yi mata? Ke idan aka ce ki na kungiyar asiri wane kallo al'umma za su yi miki ko bayan kin tuba? Ina roΖ™onki dan Allah ki rufa mata asiri kar ki gaya wa kowa wannan maganar" Ya Ζ™arasa maganar yana tashi tsaye, ya hau tattare kayan.

Rikicewa ta yi tana Ζ™oΖ™arin hana shi, amma ya ture ta ya Ι—ebe, ta riga ta yi masa bayanin duka yadda ake amfani da kayan. Dan haka ya buΙ—e alawoyin da ta yi niyyar zuwa ta ba wa Muhsin, ya saka a bakinsa.


Ya nufi hanyar fita ya dakata ya ce "Idan na rayu shikenan, idan kuma an yi amfani da jinin nawa, ki tabattar wa Mummy ni ne sadaukarwata na shekara, kuma ki roΖ™a mini ita gafara, da kuma na zama ni ne mutum na Ζ™arshe da zai rasa ransa a dalilin nan duniyarta, ta tuna inda na tafi ita ma za ta tafi" Jamila ta yi kuka da dana sanin gaya wa Abba maganar nan.


Yana zuwa Ι—akinsa ya Ι—au biro da takarda ya yi rubutu, ya caka alluran nan a jikin 'yar tsanar, kawai ya ga ta Ι“ace daga hannunsa.

Bai razana ba, ya saka hankicin a Ζ™asan fulonsa.

Bai yadda ya haΙ—u da Hajiya Sa'a ba, har dare ya yi yana Ζ™ule a Ι—aki, ya kwana a kan fulon da jan Ζ™yallen, wanda shi ma ya Ι“ace daga baya.

Jamila ta yi kuka tamkar ranta zai fita, dan faΙ—iwar gaban da ta ji ce ta tabbatar mata da cewa Abba ya aikata abin da ya ce, kuma Ζ™ungiya sun shanye masa jini.


*****


Da Ζ™yar Abduou matawalle ya yi gyaran murya ya dubi Hammad ya ce "Yanzu Hammad har wuyanka ya yi kaurin da zaka din ga sa in sa da mu? Bamu san ka da haka ba, wannan ba halinka ba ne ba. Kuma ya zama dole a ladabtar da kai bisa nuna rashin Ι—a'ar da ka nuna."


"Da na ce mahaukaci ne ai ba a yarda ba, yanzu ga haukan nan yana yi " Tafawa ya yi maganar a harzuΖ™e.


Cikin nutsuwa Imam ya ce "A cikin hayyacina nake, ina da Ι—a, ka gaya wa ko a ciki da wajen Agadez "


Sardauna ya dakatar da taron ya sallami kowa banda Imam Hammad, da Abdou matawalle sai kuma Sultan.


Sardauna ya ce "Na san maganganun Tafawa ne suka yi maka zafi ka ke wannan iΖ™irarin, amma wannan soki burutsun naka, babu abin da zai haifar sai Ζ™arawa wuta fetur. Kaf faΙ—in Agadez Asal ce matarka, kuma tun da ku ka yi aure ba ku haihu ba, ko ka na da saΙ—aka ne bamu sani ba".


"Allah ya taimaki Sardaunan Agadez, ni fa ba Ζ™arya nake yi ba, kuma ba soki burutsu nake yi ba. Ina da Ι—a"


Matawalle ya ce "Wai wani irin Ι—a a na zaune Ζ™alau? Yaushe Asal Ι—in ta haihu ba mu sani ba?"


Ya girgiza kai ya ce "Asal ba ta haihu ba, Ι—a na kuma ba shi da alaΖ™a da kowace mace a Agadez a ma Nijar gaba Ι—aya"


Sultan da ya fara harzuΖ™a ya ce "Kai ba na son shashanci fa, zan ci maka mutunci yanzun nan, wane irin shirme ne haka? Ko sai ka gazgata maganar Tafawa cewa baka da hankali"


Cikin girmamawa ya ce "Tuba nake ranka ya daΙ—e, amma idan an bani dama zan yi bayanin komai".


Abduou matawalle ya ce "Mu na sauraren ka".


Ya ciro wayarsa a aljihunsa, ya daddana.


"Ga Balaraba can tana jiran ki, ana neman ki a gidan Sultan" Nana ta ajiye tukunyar da take wankewa, ta kalli Asal ta ce ana nema na kuma a gidan Sultan? Laifi na yi?"


"Idan kin je kya ji. Nima ban san me ki ka yi ba, Imam ne ya ce a kai ki"


Gaba Ι—aya sai jikin Nana ya yi sanyi, ta kammala abin da take yi a gurguje, ta shirya ta bi Balaraba.


Su na tafe ta ce "Mama Balaraba, ko kin san abin da na yi ake nema na?"


"A'a nifa Gimbiya ce kawai ta ce na raka ki? Amma idan kin san babu abin da ki ka yi, bai kamata ki Ι—aga hankalinki ba, wataΖ™ila Imam Hammad ne kawai yake neman ki"


Cikin sanyin jiki Nana ta ce "Kuma a gidan Sultan?"


"Eh wataΖ™ila alkhairi ne, ko kuma girkin za ki yi" Duk da wannan kalaman na Ζ™warin gwiwa, da Balaraba ta faΙ—a wa Nana, ita dai Nana ta ji ba ta gamsu da kiran ba.

Tun daga nesa aka dakatar da Balaraba, aka turo wani ya shiga da Nana.


Nana ta yi turus, bayan ganin manyan mutane har da Sultan a wajen, gabanta ya yi wata mummunar faΙ—uwa, suka yi mata wani irin kwarjini ta ja ta tsaya a bakin Ζ™ofar tana rarraba idanu.


Su ma duk suka zura mata idanu, su na mamakin ita wannan da aka kirawo, me ya kawo ta nan.


"Ƙaraso mana" Sayyid ya yi maganar yana kallonta. Sai ta diririce ta kasa gaba ta kasa baya.


Da kansa ya fara takawa, yana tunkarar inda take, yana zuwa ya kamo hannunta, yana tafe tana bin sa a baya har zuwa tsakiyar gurin. Bai saki hannunta ba ya kalli idanunta ya ce "Ma Vie"

Gabanta ne ya yi wata irin mummunar faΙ—uwa, tsigar jikinta ta tashi, numfashinta ya fara fita sama-sama, jin abin da ya fito daga bakinsa tamkar almara.


"Ki shaida musu ni ba juya ba ne, ina da yaro"


ƘoΖ™arin ja da baya ta fara yi, tare da son fizge hannunta tana girgiza masa kai.


Sardauna ya ce "Imam, wace ce wannan Ι—in? Me ka ke Ζ™oΖ™arin yi ne haka?"


"Matata ce, ita ta haifa mini yaro" Ya ba shi amsar yana kallon Nana da idonta ya yi ja, ya cika da hawaye.


Cikin rashin fahimta Matawalle ya ce "Ta yaya, wace ce wannan Ι—in daga ina take?"


Hammad ya yi shiru bai ce komai ba, shi kuwa Sultan tuni ya karaya, bayan ganin asirin Hammad ya tonu na taΙ“in hankali sa saboda soki burutsun da yake yi.


Sardauna ya ce "Wai Imam kan ka Ι—aya kuwa? Ita wannan Ι—in daga ina ka samo ta, ta ina ta zama matarka?"


Matawalle ya dubi Nana ya ce "Ke Baiwar Allah, daga ina? Kuma mene ne alaΖ™arki da shi?"


Cikin ruΙ—ewa da hawaye Nana ta ce "Ni babu wata alaΖ™a tsakanina da shi, aiki kawai Gimbiya Asal ta Ι—aukko ni na yi mata, ni ban san shi ba"


Hammad ya girgiza kai ya ce "A'a Husnah, kar ki ji tsoro, ina tare da ke. Kar ki yi mini haka dan Allah"


"Dan Allah ka yi haΖ™uri ni ban san ka ba" Ta yi maganar kuka mai Ζ™arfi na Ζ™wace mata.


"Cika ta tafi" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni. A hankali ya saki hannunta, ta juya da sauri ta fice.


"Hammad, anya maganar Tafawa babu Ζ™amshin gaskiya a cikin ta, na ga baΖ™a ce kamar ma ba 'yar Ζ™asar nan ba ce? Meye haΙ—in ka da ita?"


Ya yi shiru ya sunkuyar da kai ya Ζ™i magana.


Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Ina ga a bari zan yi magana da shi"


Nana kuwa tun da ta fita take kuka, tana zuwa babu kowa a falon, ta wuce Ι—akinta ta tattare kayanta cif ta yi waje. Sauri take zumbuΙ—awa tamkar za ta tashi sama, tana tafe tana fatan Allah ya bata nasarar ficewa daga gidan, ba tare da dakarun Asal sun ganta ba su hana ta fita, kamar yadda suka taΙ“a yi mata aka hana ta fita daga gidan.

Sai dai ba Ζ™aramar tafiya ba ce ba, daga sashen da gidan Imam Hammad yake a cikin gidan zuwa shi kansa gidan.

Ta sha doguwar tafiya kafin fita babban gate.


Masu gadin Ζ™ofar suka Ζ™are mata kallo Ι—ayan ya ce "MaraΙ—i za ki tafi ko? Ga mota can Imam ya ce a kai ki"

Ta girgiza cikin mamaki ta ce "Ba zan hau ba, ni ba can zan je ba"


"Idan ba za ki hau ba, ga wannan ya ce a baki" Aka miΖ™a mata envelope. Ba ta duba meye a ciki ba, ta karΙ“a suka buΙ—e mata Ζ™ofa ta fice. Tana tafe tana waiwaye tana fatan kar a biyo ta a mayar da ita gidan nan.

Ta Ζ™udurce a ranta, tana zuwa gidan Nene za ta Ι—auke Muhsin ta yi Nigeria.


Sai dai tana tafe tana kuka zuciyarta cike da takaici, yanzu dama duk tsawon wannan lokacin Sayyid ya gane ta. Amma ya bari take ta wahala saboda shi, ya ci amanarta bai yi mata adalci ba.

Ba Ζ™aramin gudu motar da ta hau take yi ba, amma gani take kamar ba a sauri.

Ta buΙ—e envelope Ι—in da aka ba ta kuΙ—i sabbi kar a ciki.

Sai wata takarda. "Dan Allah ki samu nutsuwa, za mu yi magana Asmy, kar ki yanke mini hukunci a yanayin da ki ke" Wani uban tsaki ta ja a fili. Tana furta "Ba ka yi mini adalci ba, ka cutar da ni" Ta yi maganar kaΙ—an-kaΙ—an.


Sun sha tafiya ba kaΙ—an ba a hanya, kafin su isa MaraΙ—i. Daga nan Nana ta nemi abin hawa zuwa garin da suke da Nene. Sai dai tana zuwa ta tarar da gidan a rufe, ga babu waya a hannunta.

Cikin matsananciyar damuwa ta shiga gidan su Ashura.

Ashura na ganinta ta hau tsalle ta rungume ta, Nana ta maze suka gaisa cikin yaΖ™e.

Suka din ga yi wa Nana maraba da zuwa, mutan gidan su na ta yaba yadda Nanan ta yi haske ta Ζ™ara Ζ™iba.

Nana da gabanta ke tsananta faΙ—uwa ta ce "Nene fa, ko ta tafi gurin sayar da Abinci?"


"A'a Nene kusan kwana huΙ—u ba ta nan"


Gaban Nana ya faΙ—i, ta ce "Ba ta nan ina ta tafi?"


"Gaskiya ba na tunanin akwai wanda ta yi wa sallama, kawai dai gani muka yi ba ta nan"


"Babar Ashura, dan Allah ku bani aron waya na kira ta" Ta yi maganar cikin tashin hankali, muryarta na rawa.


Aka ba wa Nana waya, ta saka lambar Nene, wayar ta shiga, amma ba ta Ι—auka ba.

Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, ji take yi tamkar ta kurma ihu, gaba Ι—aya ta rikice, ta ji numfashinta yana fita sama-sama.

Da kyar ta iya daidaita nutsuwarta ta gabatar da sallolin da suke kanta.

Su ka kawo mata abinci, amma ta Ζ™i ci, ta yi musu sallama ta Ι—auki kayanta ta fice.

Gidan Hajara ta nufa, inda suka kawo ta gidan Nene.

Hajara ta din ga murna ganin Nana, suka rungume juna cikin farin ciki, duk da Nana cikin tashin hankali take.


Hajara ta kawo mata Abinci, ta din ga jan ta da hira.

Nana ta numfasa ta ce "Na je gida gurin Nene, na tarar ba ta nan, ga babu waya a hannuna, ko za ki kira mini ita a wayarki?"


Hajara ta ce "Bari na kira ta"


Sai da aka kira sau biyu, sannan Nene ta Ι—aga.


Cike da rawar jiki Nana ta ce "Nene"


"Na'am Nana, ki na lafiya?"


Nana ba ta amsa ba ta ce "Nene na zo ba kya nan, na kira wayarki ba kya Ι—agawa ina ku ka tafi?"


Nene ta numfasa ta ce "Nana ina mai baki haΖ™uri, baban Ι—an ya zo ya karΙ“i Ι—an sa"


Cikin matsanancin tashin hankali Nana ta tashi tsaye ta ce "Nene waye baban Ι—an? Nene wa ki ka ba wa Ι—a na? Haka muka yi da ke Nene?"


"Dan Allah Nana ki yi haΖ™uri, nima fin Ζ™arfina aka yi, babu yadda na iya, masu garin ne"


"Nene ba ki kyauta mini ba, bamu yi haka da ke ba, dan zatin Allah Nene ki gaya mini inda Ι—a na yake, dan Allah Nene, ki yi mini rai ki bani Ι—a na"


Nene ta ce "Nana da zan cutar da ke, da ban zauna da ke tsawon wannan lokacin ba, yadda muka yi a rubuce, haka ya karΙ“i Ι—an sa a rubuce da hukuma, idan na hana su matsala zan shiga"


Cikin rauni da hawaye Nana ta ce "Nene waye ya karΙ“e shi?"


"Imam Hammad Jalaludeen Agadez "


"Na shiga uku" Nana ta furta cikin matsanancin kuka da tashin hankali.


AREWABOOKS 


Cikin tausayawa Hajara ta ce "Dan Allah Nana ki yi haΖ™uri ki daina kukan nan haka? Kuma wai me yake faruwa ne?"


Nana ba ta saurari Hajara ba, ta ci gaba da kuka, tare da lissafa yadda za ta ninka ta koma Agadez, ta Ζ™udurce a ranta gara ajalinta ya riske ta, a yi duk wadda za a yi ta karΙ“i Ι—an ta, ko hakan zai yi silar tarwatsewar Agadez gaba Ι—aya.', a kan ta tafi ta bar Ι—an ta, a wannan gidan.

Bugun Ζ™ofar gidan aka din ga yi da Ζ™arfi ana sallama.

Hajara ta tashi ta fita, ba a jima ba ta dawo, ta dubi Nana ta ce "Ki na da baΖ™i a waje"


Nana ta Ι—ago jajayen idanunta da suka kumbura saboda kuka ta ce "Suwaye?"


"Ki je ki gani, baΖ™inki ne dai"


Nana ta yinΖ™ura ta tashi ta fita, tana jan Ζ™afafuwanta, mutum biyu ta gani cikin kaaki, sai Ι—aya da rawani, ya rufe fuskarsa sinkif, ba ta ganin komai sai idanunsa, duk da hakan bai hana ta yi masa kallon sani ba. Ba ta tsaya takura wa kanta ina ta san shi ba, saboda matsananciyar damuwa da tashin hankalin da take ciki.

Cikin girmamawa ya ce mata "Barka da wannan lokaci"

"Yauwwa sannu" Ta furta da dasashshiyar muryarta.


"Imam Hammad ne ya aiko mu, ya ce mu tafi da ke"


Ta yi wa mai maganar wani irin mugun kallo ta ce "Ya aiko ku ku tafi da ni ku kai ni ina? Ba zan bi ku ba, babu in da zan je"


"Gurin yaronki za a kai ki" Sai kuma ta yi turus tana kallon su.


"Tafiyar da Ι—an nisa, ki Ι—aukko kayanki, inda yaronki yake ya ce mu kai ki"

Ba ta tsaya ta zurfafa tunani ba, ta shiga cikin gidan. Hajara ta ce "Nana yaya?"


"Tafiya zan yi"


"Ki je ina? Wai ni, me ya haΙ—a ki da Buzayen nan ma? An ce mini daga gidan Sultan Ι—in Agadez aka zo gurinki, me yake faruwa ne?"


"Zan yi miki bayani daga baya, bari na je tukuna" Ta ja jakarta, ta yi waje. Wata irin haΙ—aΙ—Ι—iyar mota ce, ta haΙ—u ga kyau ga wani daddaΙ—an sanyi da take fitarwa.

Sai dai Nana ba ta tsaya tantance kyan motar ba, lissafinta kawai Muhsin ya zo hannunta, ta gudu. Dan ko me za a yi ba za ta bayar da Ι—an ta ba, kuma ba za ta bar Nijar ba sai Sayyid ya sake ta.

Sun sha tafiya, kafin su isa wani irin Ζ™aton gida, sai da ta ga an shiga gidan, ta waiwaya ta ga an rufe jibgegen gate Ι—in gidan, sai kuma tsoro ya fara kama ta, dan ta san barin wannan gidan ba abu ne da zai yi sauΖ™i ba.

Sai dai hanakalinta baki Ι—aya ya fi karkata, ga ta yi tozali da Ι—anta, ta san a halin da yake ciki.

Ta sauka daga motar ta tsaya tana rarraba ido, mai rawanin ya yi mata jagora zuwa katafaren falon gidan.


Ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Akwai banΙ—aki, da abinci, ki yi salla ki ci abinci kafin Imam ya zo" Wata irin muguwar razana Nana ta yi, ta ce "Sule? Kai ne dama? Me yasa..? Ta rasa wace tambayar ma yakamata ta Ζ™arasa.

"Ki yi haΖ™uri, ba ni da damar ce miki komai, ki yi salla tukuna" Nana ta Ζ™ara rikicewa kanta ya kulle. Da kyar ta samu ta yi sallolin.

Jikinta sai ciwo yake yi saboda azabar zirga-zirgar tafiya ga cikinta babu komai.

Gaba Ι—aya rarraba ido kawai take yi, tana tunanin ta ina za ta ga Muhsin, ga fafur Sule ya Ζ™i tsayawa ya yi tafiyarsa ya bar ta sai itakaΙ—ai, balle ya yi mata wani gamsashshen bayani.

Jin ana turo Ζ™ofar falon, ya sanya ta miΖ™e tana Ζ™ara leΖ™awa ko za  ta ga Muhsin.


Sai dai ba ta ga Muhsin ba sai baban Muhsin, yana sanye cikin baΖ™ar jallabiya, ya yafa hirami a kansa, bayansa kuma Mahmoudu ne, wanda ta fi sani da Habu.

Razana ta yi, ta tsaya Ζ™yam tamkar an dasa ta, ta haΙ—iye wani abu mai masaifar zafi tamkar wuta a maΖ™ogwaronta zuwa Ζ™irjinta.


Ya kalli idonta, yana Ζ™oΖ™arin tantance wane irin kallo take yi masa, ya rasa ta ina ma zai fara.


"Ina Ι—a na?" Ta jefa masa maganar a zafafe tana huci.


Habu ya matso gaba ya ce "Nana, ki yi haΖ™uri ki ci abinci ki huta, ki samu nutsuwa, sai mu yi miki bayani"


"Bayani? Wane bayanin nake buΖ™ata bayan wanda na gani? Kun cuce ni, na Ζ™arar da lokacina ban tsinana wa rayuwata komai ba, na tsaya na yi biyayyar aure na rabauta, ashe mutumin da nake tausayawa azzalumi ne, kuma mugu ne. Kun zalunce ni kun yaudare ni, kun Ι“oye mini abubuwa da dama, ba dan ba ni hakkinku ba Allah ya saka muka haΙ—u ba, da shikenan haia zan ci gaba da gararamba, ba ni da makoma. Ba zan yafe muku ba. Allah ba zai bar zaluncin da ku ka yi mini ba. Ka bani Ι—a na dan ba Ι—anka ba ne, baka da hurumi da shi Muhsin ba shi da uba na zaΙ“i ya tashi da wannan tambarin da ya san ubansa azzalumi ne da ya wofantar da rayuwar mahaifiyarsa".


Wata irin suka maganganun Nana suke yi wa zuciyarsa, amma ya san koma Nanan ta faΙ—a a kansa, ba ta yi laifi ba, ya kuma cancanci hakan daga gare ta.


Mahmoudu ya ce "Nana, kin san wa ki ke gaya wa haka? Mijinki ne fa?"


Cikin kuka ta girgiza kai ta ce "Wannan ba mijina ba ne, mijina Buzu ne da bai san waye shi ba, babu kowa a duniyarsa sai matarsa da ta nuna masa Ζ™auna saboda Allah. Ba wannan mayaudarin da ya yaudare ni da cewa ni rayuwarsa ce ba, na yi asarar lokacina a kan nemansa ba. Ka bani Ι—a na ka haΙ—a mini da takardar sakina na koma Ζ™asata na sama wa rayuwata mafita" Ta yi maganar tana riΖ™e rigarsa tana kuka mai fallasar da dubban damuwoyin da suke binne a Ζ™arΖ™ashin zuciyarta tsawon lokaci.


"Ma vie" ya furta a kasanlance idanunsa fal hawaye, yana kallon Ζ™wayar idonta.


"Kar ka sake kira na da wannan sunan da na fi tsanar ji a rayuwata, Ni da nake mummuna, baΖ™a 'yar Nigeria da ba kowa ba hadima kuma baiwar da ake ci wa mutunci a gaban wanda yake yi mini iΖ™irarin ni rayuwarsa ce yana ji kuma yana gani. WataΖ™ila ma alhakin iyayena ne ya kama ni, da na baro su saboda wauta irin ta soyayya da Ζ™oΖ™arin sama wa Ι—a na mafitar rayuwa. Ka bani Ι—a na ka sake ni na koma inda na fito" Ta yi maganar tana zare masa ido tamkar numfashinta zai Ι—auke.


Ya saka hannunsa yana Ζ™oΖ™arin kamo ta jikinsa, amma ta yi baya tana kai masa duka ta ko ina, cikin kuka tana faΙ—in "Na tsane ka, na yi nadamar saninka, rayuwata da kai bai amfana mini komai ba, ban taΙ“a zaton za ku iya haΙ—a kai ku cutar da ni haka ba, ka bani Ι—a na na gaya maka"

Mahmoudu sai da ya tsure, ganin yadda kamaninta har canzawa suka yi saboda faΙ—a, idanunta tamkar ta tauna barkono saboda ja, ga ambaliyar da hawaye suke yi a fuskarta.

A Ι—an iya sanin da ya yi mata, tana da sanyin hali, banda tsiwa da ta kan yi wasu lokutan, bai taΙ“a tunanin za ta iya burkicewa haka ba.

Shi kansa Imam Hammad sai da ya tsorata, yanayin da take ciki ya tabattar masa, sai ya yi aiki tuΖ™uru kan ma ya samu ta saurare shi.

Ya shammace ta ya damΖ™e ta, ya nufi wata hanya da ita, ta din ga fizge-fizge, tana ci gaba da kuka da turjewa. 

"Ki nutsu, kar ki yi mini asarar cikin da yake jikinki" Wani irin burki ta ci, cike da rikicewa jikinta na tsuma, ji take tamkar ba ta ji daidai ba, sai dai kafin ta tantance, jikinta ya saki ta yi baya za ta faΙ—i ya riΖ™e ta.

Jikinta ya yi sanyi Ζ™alau, sai hawaye da yake fita daga gefen idonta.

Da haka ya yi nasarar shiga da ita Ι—akin, ya kwantar da ita a kan gadon. Ya zare mata hijjabin jikinta.

Ya zura mata idanunsa, a hankali yake lumshe su yana buΙ—ewa a kan ta.

Ya kamo hannayenta a cikin nasa, ya sumbaci hannayen, sannan ya ce "Duk abin da ki ka yi mini, kuma duk abin da ki ka kira ni da shi, na cancanta, ban kyauta miki ba, na sani ban kyauta ba, amma ki bani dama ko sau Ι—aya ne ma viee, sau Ι—aya tak, ki bani dama na ce wani abu. Na san ba halinki ba ne, wannan ba halin Husna ta ba ce, amma na karΙ“i laifina ki yi mini afuwa. Ban yi abin da na yi domin na zalunce ki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a Ζ™irjinta yana sauraren yadda zuciyarta ke bugawa da wani irin matsanancin sauri.


*****


Asal ce take ta shiga tana fita cikin takaici, bayan jin Nana shiru ba ta kawo Abincin safe ba, ga babu alamar na rana, kuma ba  ta gyara sashen ba. Ita a tunaninta tuni ta dawo daga kiran da aka yi mata a can gidan Sultan.

Takaici ya ishe ta, dan ta tsani zuwa Ι—akin da Nana take a ganinta Ζ™asΖ™anci ne, amma jin shirun ya yi yawa, ta fara duba kitchen ba ta nan, ta wuce Ι—akin Nana, saboda ya ci a ce ta dawo, duk da ba ta san kiran me Imam ya yi wa Nana ba.

Sai dai tana zuwa ta ga wayam, hatta kayan Nana babu sai katifarta.

Cikin tashin hankali ta fito ta tara su Balaraba da sauran ma'aikatan cikin gidan.

Duk su ka taru "Wai gidan uban wa yarinyar nan, mai yi wa Imam girki ta tafi? Tun jiya ba ta gidan nan, hatta kayanta ta tattara ta tafi ta bar gidan nan."


Cikin girmamawa Balaraba ta ce "Wallahi ranki ya daΙ—e, bamu ganta ba, kin san ta koma cikin sashenku, ba ganinta ma muke yi ba" 


"A ce kaf cikinku babu wanda ya ga fitarta?" Suka yi shiru, su na sauraren jarabar Asal.

Ta Ζ™are musu rashin mutunci, ta sallame su.

Kai komo ta din ga yi tana tunanin ina Nana ta tattara kayanta ta gudu? Haka kurum ta din ga jin kamar akwai abin da Nana take Ζ™ullawa ta bar gidan.


Tana komawa sashenta, ta tarar da tarin missed calls Ι—in Tafawa.

Cikin rawar jiki ta bi kiran wayar, aikuwa ya Ι—aga hasale.

"Wace irin wawuya ce ke, ina ta kiran wayarki amma kina can kina shashashanci ba ki Ι—aga ba?"


"Dan Allah ka yi haΖ™uri, ina can wani uzuri ne"


"Uzurin banza uzurin wofi? Asal kin san me yake faruwa? Yau ni mijinki ya kalla ya ce mini na bincike ki, ke ce juya shi ba juya ba ne ya na da Ι—a"


Wani irin dumm maganar baban nata ta daki zuciyarta, ta ji wani banbarakwai, banda ba abokin wasanta ba ne, da ta ce Ζ™arya ya sharara mata, kuma da sai ta hukunta shi a kan hakan"


"Na ji kin yi shiru?"


"To ai na kasa ganewa ne, wai wane Imam Ι—in ne yake da Ι—an?"


"Wanne ki ke aure? Kuma kaf cikinsu waye ba shi da Ι—a ban da mijinki?"


Cikin kuka ta ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, na shiga uku na lalace. Abba ya zan yi, ni Hammad zai yi wa haka? A ina yake da Ι—an?"


"Ki nutsu ki kwantar da hankalinki, haryanzu ban tabattar ba tukuna, ina ga faΙ—a kawai ya yi dan ya huce takaicinsa, kuma saboda tsagwaron munafunci aka sallami kowa daga zaman, ba a bari na ji Ζ™arshen zancen ba, amma zan bincika na tabattar da gaskiyar maganar?"

Ba ta iya tantance sauran abin da yake faΙ—a ba, ta kashe wayar jikinta yana rawa, ta hau kiran lambar Hammad, sai dai shiru wayarsa ba ta shiga, ta kira ya kusa sau hamsin, amma shiru ba ta shiga. Ta yi jifa da wayar tana huci. "Wallahi Hammad, zancen nan ko ba gaskiya ba ne ba, sai ka fuskanci mummunan tashin hankali da abin da ba ka taΙ“a zato ba. Wallahi ta tabatta ka haihu da wata mace, sai an mutu har Liman." Ta zauna Jikinta yana wata irin tsuma ta tashin hankali.

Sultan kansa ya kasa zaune ya kasa tsaye, dan babu yadda ba su yi da shi ya yi magana ba, bayan tafiyar Nana ba amma ya Ζ™i.


Hankalin Sultan ya yi mummunan tashi, Abduou matawalle ne ya din ga rarrashin sa yana kwantar masa da hankalin a kan su bi komai a hankali, har su samu Hammad ya yi musu bayani dalla-dalla.


Sultan ya ce "Matawalle, a tsorace nake, Tafawa ya yi nasara, ya yi nasarar tabattar wa da Duniya cewar Hammad mahaukaci ne, idan ba haka ba ta yaya zai zo ya ce yana da Ι—a, Ι—an ma ba da buzuwa ba, 'yar wata Ζ™asar bayan ya san me hakan yake nufi.

Tafawa ya ce "Kar ka yi mamaki, yanzu dole mu jira ya yi magana, mu Ι—an ba shi lokaci ya nutsu, dan mu tabattar jikin ne, ko kuma da gaske yake. Kar ka manta tsawon lokacin da ya shafe ba tare da mu ba, bamu san me da me ya faru ba, kuma kar ka manta a Nigeria a ka gano mana shi"


Sultan ya goge gumin da yake tsatstsafo masa ya ce "Matawalle, akwai gagarumar matsala, babu buΖ™atar mu ba shi wani lokaci na daban, dole ya warware mana zare da abawa mu ji yadda aka haihu a ragaya. Kira mini wayarsa, duk inda yake a nemo shi, kuma a kira mini yarinyar ma"


Matawalle ya ce "Haka ne, kuma a nemo  wannan munufukin yaron Mahmoudu, domin tabbas ya san komai, ya san duk abin da ya faru"


"Wai ni ita yarinyar ma, ni kamar na taΙ“a ganinta, a ina aka samo ta ne?"


Matawalle ya ce "Eh, lokacin da Hammad ya dawo, tana cikin waΙ—anda suka yi girki, wai Gimbiya Asal ce ta kawo ta"


"Asal kuma?" Sultan ya yi maganar yana nazari.


Sai dai duk tarin kiran wayar da aka yi wa Imam Hammad, ko sau Ι—aya wayar ba ta shiga ba.

Hakan ya Ζ™ara jefa su a tashin hankali.


A hankali Nana ta yi miΖ™a, dan tamkar ta ci wani abu, haka ta yi wani irin nannauyan bacci. Cikinta ne yake wata irin Ζ™ara, saboda azabar yunwar da take ji.

Ta yinΖ™ura da Ζ™yar, za ta tashi zaune, ta yi tozali da kyakykywar fuskarsa, yana kallonta. Ja da baya ta yi tamkar ta yi tozali da wanda ba muharraminta ba. Ta kalli jikinta babu hijjabi, rigar jikinta ma an canza mata wata.


"Kin tashi?"


"Ina Ι—a na yake? Kuma waye ya ce ka taΙ“a ni ka canza mini riga, waye ya baka wannan damar?"


"Sadakina" ya ba ta amsa kai tsaye. Ita tsantsar mamakin halayyarsa take yi ma a yanzu, gaba Ι—aya ya canza mata.


"Na haΙ—a ka da girman Allah, ka bani Ι—a na, ka bani Ι—a na, ni ban sanka ba, Ι—ana kuma ba Ι—an ka ba ne, dan Allah ka bani yarona na tafi, dan Allah ka taimaka mini, na karΙ“i yarona na koma Ζ™asata" Ta yi maganar hawaye na bin fuskarta.


Ya wani lumshe ido yana murmushi ya ce "To ni kuma ina za ki kai ni idan ki ka tafi?"


"Ni ban sanka ba"


"Haba?" Yayi maganar yana Ζ™anΖ™ance idanunsa. Wani marurun takaici ne ya Ζ™ule Nana.


"Ki tsaya ki saurare ni, na yi miki bayani"


"Ni ba zan ji wani bayaninka ba, duk abin da zai fito daga bakinka, ba zan taΙ“a yarda da shi ba. Ka bani Ι—a na na tafi"


Sayyid ya yi ajiyar zuciya ya ce "To ki bari ki haifa mini abin da yake cikinki, ki bani abina, sai mu san abin yi"


Daina ganewa Nana ta yi na wani Ι—an lokaci, ta yi shiru ta tuna ya ce mata tana Ι—auke da juna biyu ma Ι—azu. Ta kalli cikinta, ta Ι—ago ta kalle shi, ya Ι—age mata girarsa Ι—aya.


Ayshercool 

08081012143

80

Gaba Ι—aya kanta ya kulle, ta zuba masa idanunta da suka yi jawur.


A mugun kasanlance ta ce "Ciki kuma?"


Ya jinjina mata kai, ta rasa abin da za ta yi gaba Ι—aya. Ciki yaushe? Yaushe wani abu ya shiga tsakaninsu da har za ta Ι—auki ciki? Ta tambayi kanta, sai dai ta kasa tambayarsa. Sai tsare shi da ta yi da idanunta.


Ya gyara zamansa sosai ya ce "Kina ji na?"


"Babu abin da zan ji? Kar ka gaya mini komai, ba zan ji ba kuma ba na fatan ji. Abin da ka yi mini haka ma ya isa, ka bar ni na ji da kaina". Ta yi maganar a matuΖ™ar zafafe.


Ya ce "Shikenan na ji. Na rabu da ke. Amma ina so ki sani, muddin ba ki saki jikinki ba, ki din ga cin abinci ki rage wa kanki wannan damuwar ba, to fa ba zan ba ki Muhsin ba. Gwargwadon sakin jikinki, da cin abinci da zaki yi, shi zai sanya ki gan shi. Akasin haka kuma zan ci gaba da tsare ki a nan, na kai wa Asal shi ta riΖ™e shi, tun da dama ita Allah bai ba ta haihuwa ba. Wannan ma idan ki ka haifa ki bani abina tun da ba za ki saurare ni ba" Kallon ba ka da hankali ta yi masa. Ya yinΖ™ura da kyar, jikinsa babu Ζ™wari, ya Ι—auki hiraminsa ya rufe kansa ya fice ya bar Ι—akin.

A Ι—aya falon ya tarar da Mahmoudu, cikin zaΖ™uwa ya ce masa "Yaya ta saurare ka kuwa?"


Jiki a sanyaye ya girgiza kai tare da zama ya ce "Fafur ta Ζ™i saurar ta, duk wani rarrashi da ban baki da zan yi, taΖ™i saurarta kawai na ba ta Ι—an ta na sake ta ta nanata mini, na rasa yadda zan yi ko na minti Ι—aya ta saurare ni. Babban abin da yake Ι—aga mini hankali gani nake kamar da gaske Husna ta daina so na"


Mahmoudu ya girgiza kai ya ce "Ka yi haΖ™uri, Ι“acin rai ne kawai ya sanya ta faΙ—ar haka, amma a irin so da sadaukarwar da ta yi maka ba zai yiwu a ce ta daina sonka ba"

Ya tashi zaune sosai yana kallon Mahmoudu ya ce "Kana ganin idan ta huce, za ta ci gaba da so na kuwa?"


"Sosai ma, yanzun ma Ι“acin rai ne kawai. Amma za ta ci gaba da sonka da zarar ta huce"


Ya koma ya kashingiΙ—a yana kaΙ—a Ζ™afafuwansa.


Mahmoudu ya numfasa ya ce "Yanzu Imam mene ne abin yi, na san fa yanzu ana can ana nemanmu, ta ina zaka fara Fuskantar wannan balahirar? Ta ina za a fahimce mu, akwai gagarumar matsala fa"


Ya Ι—an kwaΙ“e baki ya ce "Wannan balahairar ba ta kai fushin da Asmy take yi da ni ba. Ni duk yadda za su yi da ni sai dai su yi. Ko su bar ni a raye ko ma su yanka ni, burina da fatana na ga ta haΖ™ura ta yafe mini ta saurare ni."


"Yanzu soyayyarka gaba take da gagarumin tashin hankalin da yake gabanmu?"


"Nesa ba kusa ba kuwa, idan aka kamanata shi da zunzurutun soyayya mara algus Ι—in da na samu. Ko ka manta abu ne da nake nema ido rufe"


Mahmoudu ya ce "TurΖ™ashi, to yaya za ka yi da Gimbiya Asal?"


Kawai ya saki murmushi, ya shafa sajensa.


"Au dariya ma na baka?"


"Eh mana, ni fa duk wannan masu sauΖ™i ne, ban Ι—auke su matsaloli ba, zan gaya wa kowa gaskiya ko me za a yi mini sai dai a yi mini, ni fatana Asma'u ta yafe mini" Ya Ζ™arasa maganar cikin damuwa.


"Ka kwantar da hankalinka, in sha Allah za ta saurare ka, ta Ι—auki zafi ne, amma tana hucewa za ta saurare ka"


*****


Doctor Sharif ne yake kallon matarsa cikin tausayawa, cikinta ya tsufa, amma sai fama take da rashin lafiya, duk da haihuwa ta biyar za ta yi. 

A dole ya ba ta gado a Asibitin, cikin wata bakwai da sati Ι—aya, amma tana ta zubar da ruwa, ga matsalar numfashi da suga da yake hawa yana sauka.

Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Gida zaka tafi ka bar ni?"


Ya ce "Eh mana, ba ga Yaya za ta kwana tare da ke ba? Kin ga yara su na gida, ga shi gobe in Allah ya kaimu akwai makaranta, dole na koma gida. Da na kai su school zan taho nan, duk wani abu da za a yi miki, na yi shi a rubuce duk za a yi miki"

Ta numfasa ta jinjina kai ta ce "To shikenan, sai da safe"

"Yauwwa Madam, ki samu isasshen bacci dan Allah"


"Idan na kwanta ne, baccin ko na fara sai na ji numfashina yana yi mini sama, kwanciyar babu daΙ—i sam"


"Na sani, ki yi haΖ™uri sai ki kwanta a side Ι—in hannunki na hagu ko na dama"


Ta ce "To, sai da safe" Suka yi sallama ya tafi cike da tausayinta, wannan cikin tun yana Ζ™arami ya zo da tangarΙ—a yake wahalar da ita, ga shi ya tsufa ma amma ba ta daina wahala ba.


Hankalin Alhaji Zailani ya yi mummunan tashi, ganin sauΖ™i sosai da sosai a tattare da Alhaji Fatuhu.

Ga 'yan kasuwa sun yi masa caaa a ka, a kan lallai ba sa son shugabancinsa, sai dai ya sauka a canza wani. Ya tattara nutsuwarsa ya yi burusu da su, domin ba ya son ya rarraba hankalinsa, wani abin ya Ζ™wace masa.


****


Nana kuwa ji ta yi da gaske yunwa na Ζ™oΖ™arin hana ta sukuni.

Tashi ta yi ta fito, ta fara dube-dube. Yana daga inda yake tsaye yana kallon ta.

"Me ki ke nema ne?"


Firgita ta yi ta juyo tana kallon inda yake, ganin yadda yake Ζ™are mata kallo ne, ya sanya ta haΙ—e rai.

"Ina fatan ba wani gurin ki ke shirin tafiya ba, babu hanyar da za ki bi ki je ko ina"


"Ni ba guduwa zan yi ba, idan na ci Abincin yau za ka bari na gan shi?"


Ya yi murmushi ya ce "Ki ci Ι—in tukuna, Bismillah biyo ni" Jiki a sanyaye ta bi bayansa, cikin matsanancin tsoro, dan ganin shi take yi kamar wani mutum na daban.


HaΙ—aΙ—en bedroom ya kai ta, ta tsaya saroro tana kallon Ι—akin, ta Ι—aga kai ta kalli agogon Ι—akin, Ζ™arfe Ι—aya da rabi na dare.


"Zauna ki jira ni a nan" Ta tsaya tana kallon sa.


"Ki zauna mana" Ya yi maganar yana nuna mata bakin gado.

Ta yi Ζ™yam tana kallonsa. Bai sake ce mata komai ba, ya fita ta tsaya tana zazzare ido, tana Ζ™ara Ζ™arewa Ι—akin kallo. Ta gaji da tsayuwa, ta samu guri ta jingina da jikin bango, sanyin AC da yake Ι—akin ya fara damunta.

Falon ta koma, tana nan zaune sai ga shi ya shigo da leda a hannunsa.


"Me yasa ki ka fito?"


"Sanyi nake ji" Ta ba shi amsa a taΖ™aice.


"Ohh yi haΖ™uri, mu je sai na kashe miki A.C" Ta girgiza masa kai tana sake haΙ—e rai.


"Shikenan, zauna ga abincin na samo" Ya yi maganar yana riga ta zaman.


Ta zuba wa ledar ido, bayan da ya fito da gasassun zabi guda biyu, babu abin da ya faΙ—o ranta, sai zaman su a gidan Hajiya Halima, lokacin da ya saka Habu ya kawo mata zabbi gasassu.


Ya kalle ta ya ce "Ko na dafo miki shayi?"


Ta girgiza kai ta tashi tsaye. "ina za ki je?"


"Ɗakin da nake zan koma,a can zan ci" Ta ba shi amsa ciki-ciki.


"To mu je can Ι—in, nima ban ci komai ba, wataΖ™ila idan muka ci tare, zan iya sakin jiki na ci Abincin"


Nana ta Ζ™ara haΙ—e rai ta ce "Ni fa ba zan ci wani abinci tare da kai ba, bana buΖ™atar duk wani abu da zai Ζ™ara kusanta ni da kai. Ni a yanzu neman maraba nake yi da kai".


"Neman maraba ki ke yi da ni?" Ya yi maganar yana murmushi mai ciwo, daga bisani ya ce "Shikenan, Ι—auki abincin ki je ki ci, sai ki kwanta ki huta" Ya tashi ya bar mata falon.

Ta tattare kan kayan abincin, ta tafi Ι—akin da aka ajiye ta.

Sosai ta fara Ζ™oΖ™arin cin abincin, saboda azabar yunwar da take ji, sai kuma ta tuna da gaske idan ba ta yi girki ba, ba ya cin abincin.

Kenan tun da ta tafi bai ci cikakken abinci ba kenan ko yaya? Wata zuciyar ta tambaye ta.

Har za ta yinΖ™ura ta tashi, sai ta tuno batun cikin da ya ce tana da shi. A take wani malolon takaici ya Ζ™ule ta, ta Ζ™uduri aniyar sai ta yi dalilin zubewar cikin nan.

To tayaya ma za a yi a ce ina da ciki? Yaushe kuma ta yaya?" Ta tambayi kanta.

Gaba Ι—aya ta ji kanta yana juya mata, dan haka ta haΖ™ura da tunanin, ta je ta wanke hannunta ta ta rufe abin da ta rage ta kwanta.


Sai dai ta Ζ™i yadda ta yi bacci, saboda gudun kar ya biyo dare ya zo ya yi yinΖ™urin yi mata wani abin.


Sai dai ko mintuna goma ba a yi ba, ta tsinci kanta a cikin Libraryn Ƙaisar.


Ta gan shi a kwance a kan wani gado, ya lulluΙ“a da wani baΖ™in mayafi.


Ya kalli fuskarta da ke Ι—auke da damuwa ya ce "Ya dai?"


Ta Numfasa ta ce "Ya na gan ka a kwance a nan?"


"Eh to zan yi ta zama ba zan kwanta ba ne?"


Ta ce "A'a, amma galibi sai ba ka da lafiya ka ke kwanciya a nan gurin"


"Lafiyata Ζ™alau. Na Ι—auka zan gan ki cikin murna da farin ciki, tun da mijinki ya dawo hayyacinsa ya gane ki, sai kuma na gan ki cikin damuwa?"

Ta nemi guri ta zaune a gefen Ƙaisar ta ce "Ni fa ba na Ζ™aunar mutumin nan, fatana kawai ya bani Ι—a na, na koma Nigeria Ubangiji Allah ya sanya su Baba su yafe mini, ina kyautata zaton alhakinsu ne ya kama ni"


Ƙaisar ya ce "Waye ba kya Ζ™aunar yanzu?"


"Sayyid"


"Ƙarya ki ke yi" ta ce "Ƙarya kuma?"


"Da dai ban san halinki ba ne"


Cikin sanyin jiki ta ce "Da gaske nake, ba wasa nake yi maka ba. Ba na ko Ζ™aunar jin sunansa, ya yaudare ni, sun cutar da ni. Gaba Ι—aya kimarsa da son da nake yi masa sun zube a idanuna"


Ƙaisar ya yinΖ™ura ya tashi zaune, yana Ζ™ara rufe jikinsa ya ce "Tun da ya ce ki saurare shi, ki tsaya ki ji mai zai ce miki mana. Kar zuciyar da ki ka yi ta sanya ki yanke hukuncin da ba zai Ι“ulle muku ba"


"Ni fa babu abin da zan ji daga bakinsa, ba na buΖ™atar sa a rayuwata gaba Ι—aya" Ƙaisar ya yi murmushi yana gyara zamansa a hankali. Idon Nana ya sauka a kan Jakar Sarkin baka da ke gefen gadon da yake.

"Ƙaisar, me ka ke yi da jakar Sarkin baka?" Ya yi mata shiru kamar bai ji ta ba.

MiΖ™ewa ta yi da sauri ta ce "Wani abu ya faru tsakaninka da Giyaz ko?"


"A'a aron jakar na yi, wani aiki na yi da ita".


Nana ta saka hannu ta Ι—an ja mayafin da ya rufe jikinsa da shi, wani irin haske ne ya haske mata ido, daga bisani hasken ya ragu a hankali.

Jikinsa ya yi wani irin kore-kore, wani gurin kuma ya yi baΖ™i Ζ™irin tamkar an Ζ™ona shi.

Nana ta ce "Meyafaru? Me ya same ka haka? Giyaz ya yi maka wani abu ne?"


"Babu abin da ya faru, zan dawo miki da jakar ki kuma, ki je sai na sake neman ki" Nana ta farka daga baccin da take yi, fuskarta duk hawaye.

Gaba Ι—aya jikinta a sanyaye ta tashi ta yi alwala, ta yi nafilfili, sannan ta gabatar da sallar asuba.

Har gari ya yi haske, tana zaune a Ζ™asa. Shiru ta yi tana tuna yadda ta ga jikin Ƙaisar, sai ta ji abin ya dame ta sosai da sosai.


"Mene ne makomar wannan sakankancewar da nake yi da Ƙaisar yanzu? Me yasa kuma yake taimakona a wasu guraren? Anya ba wani tarkon na yaudara ya yi mini ba, yake son na afka ya yi amfani da damar ba? Ko ma dai yaya ne, Ubangiji Allah ka tsare ni daga sharrin duk wani abin Ζ™i." Sosai take son mantawa da tunanin Ƙaisar, ta koma tunanin Muhsin, da wannan balahirar ta gabanta, amma abu ya ci tura, a jikinta take jin Ƙaisar, take jin ta damu da halin da ta gan shi a ciki.


Sallamarsa ce ta katse mata tunani, ta amsa masa ciki-ciki. Ya je gabanta ya ajiye tray. Ya Ι—an tsura mata ido ya ce "Barka da safiya Rayuwata" Wani mugun kallo ta yi masa, haΙ—i da uwar harara.


Ya yi murmushi ya ce "Ga abin karyawa nan, kar ki manta sakin jikinki, da cin abincinki ne zai sanya ki ga Ι—ana"


"Ka daina danganta mini Ι—ana da kanka, ba shi wata alaΖ™a da kai" Ta yi maganar cikin tsiwa.


"Ba shi da alaΖ™a da ni, sai da Ƙaisar?" Ya yi maganar ya kallonta yana murmushi. Bai ba ta damar ba shi amsa ba ya ce "Yau zan koma gida, zan je na ji yadda za mu yi da su Sultan, amma ki nutsu ki kwantar da hankalinki dan Allah"


"Ba ni da wata nutsuwa ko kwanciyar hankali, idan ba Ι—a na na gani ya zo hannuna ba".

Ya yi shiru yana tsare ta da idanunsa.

Ta Ι—aga kai ta kalle shi, ta ji gabanta ya faΙ—i, ta rasa gane wane irin kallo ne yake yi mata haka.

Ta sunkuyar da kanta tana haΙ—e rai.

Ta sake Ι—aga ido ta suka haΙ—a ido, ya yi mata murmushi, ya ce "Ma vie, ban san daga ina nake jin Ζ™aunarki ba a rayuwata, kar ki hukunta ni da abin da ki ka gani kawai a zahiri. Ina sake roΖ™onki, ki bani dama ki ji ta bakina"


"Ni babu abin da zan ji, na ce maka Ι—ana kawai nake buΖ™ata"


Ya shafi sajensa ya ce "Muhsin ai nawa ne ni da Asal. Idan ki ka haihu kuma nawa ni da ke, shi ma idan ba kya so sai ki bani abina"


Wata irin Ι—agowa ta yi, cike da takaici, ya shammace ta ya rungume ta ya haΙ—e bakinsu.

Nana ta tattara nutsuwarta, da duk wata jarumta dan ganin ba ta biye wa Sayyid. Ta din ga ture shi iya Ζ™arfinta tana kai masa duka, amma tamkar dutse ba jikin Ι—an Adam take duka ba. Sai da ta gaji ta Ζ™yale shi. A hankali ya zare bakinsa daga nata ya Ι—ago fuskarta yana kallonta.


Hawaye sharkaf a kan fuskarta, ya ce "Kar ki wahal da rayukanmu, ni da ke abu guda ne Asmy, ko kin tafi kin bar ni, ba za ki taΙ“a samun nutuswa da kwanciyar hankali ba. Kamar yadda tun da muka rabu nawa ruhin ma bai samu nutsuwa ba. Ina Ζ™aunarki rayuwata" Duk yadda Nana ta so yi masa rashin kunya, ta gaggaya masa maganganu masu zafin gaske, amma ta kasa tamkar ya saka wani abu a cikin idanunsa da ya yi tasirin da ya hana ta maganar.

"Ki yi mana addu'a rayuwata, akwai kaya a Ι—akin da muka je jiya, idan kin yi wanka akwai kayan sakawa. Sai akwai kitchen shi ma, duk za ki iya shiga ki dafa mana duk abin da ki ke so. Sai na dawo" Ko tari Nana ba ta kuma yi ba, har ya tashi ya bar Ι—akin, ta bi bayansa da harara.


Nene ce rungume da Muhsin, ya sha ado cikin kayan buzaye, kayansa iri Ι—aya da na jikin babansa, sai Ζ™oΖ™arin cire mayafin da aka rufe masa gashinsa da shi yake yi, sai Ζ™amshin turare yake yi.

Hammad ya saka hannu ya karΙ“e shi fuskarsa Ι—auke da murmushi har da wata irin Ι“oyayyiyar ajiyar zuciya.


Hammad ya ce "Mu je ko?"


Nene jiki a sanyaye ta ce "Ina mai neman afuwarka, ni tsoron zuwa gidan nan nake yi. Kuma a wane hali Nana take ciki yanzu, na kasa nutsuwa gaba Ι—aya, ina jin ban kyauta ba gaba Ι—aya"


"Ki kwantar da hankalinki, Nana tana tare da ni, kuma babu wanda zai yi miki komai a cikin gidan, ki taimaka mini dan Allah"


AREWABOOKS 


Nene ta numfasa ta ce "Alfamarka ce kawai za ta sanya na yi maka abin da ka nema, dan na yi alΖ™awarin babu abin da zai sake haΙ—a ni da wannan gidan naku, saboda mummunan tabon da yake binne a zuciyata. Kuma da ko me za ka yi mini ba zan ba da Ι—an nan ba, saboda ya saΙ“a alΖ™awarin da muka yi da Nana, ban kyauta mata ba za ta yi mini kallon mutuniyar banza mara alΖ™awari. Amma kai ma Ι—a ne a gurina, ban da dalilin haka gaskiya ba zan iya ba"


"Na sani, kuma na gode sosai da sosai, da wannan alfarma da ki ka yi mini"


Ta risunar da kanta cikin girmamawa. Ya miΖ™a mata Muhsin ta karΙ“e shi, suka shiga mota.


*****

A tsanake Tafawa ya kalli Asad ya ce "Asad, wai waye ka ce ya karΙ“i ayabar nan ya ci?"


"Wata yarinya ce, ni ban santa ma a gidan nan ba gaba Ι—aya"


"Dole a nemo ko wacece, saboda an tabattar mini, da cin ayabar da ta yi, da gayya ta karΙ“a ta ci, dan aikin da aka yi ya Ι“aci ya lalace."


Asad ya yi shiru, ya ce "Gaskiya ban san ko wace ce ba, sai dai ko a tambayi Asal, ko ta santa abinci dai ya kawo mana. Ina kyautata zaton ko kuku ce ko dai makamancin hakan. Ban ma san yadda aka yi ta   zo inda muke ba, dan kamar ba buzuwa ba ce gaskiya"


Tafawa ya yi shiru yana nazari, ya ce "Babu yadda za a yi wadda ba buzuwa ba, ta tsallako ta shigo gidan sarautar Agadez, ta yi wannan abin, lallai zuwanta na manufa ne, dole a binciko wace ce."

Asad ya jinjina kai cike da gamsuwa.


Asal duk ta rasa nutsuwarta da kwanciyar hankali, mussaman da Imam ya kwana uku ba ta san inda ya shiga ba, hakan ya sanya ta fara jin kamar akwai Ζ™amshin gaskiya a maganar da Tafawa ya gaya mata. Ta kasa jurewa ta je ta samu Sultan, tana yi masa kuka.


Cikin damuwa ya ce "Yarinyar kirki lafiya kuwa?"


"Sultan ji na yi an ce wai Imam yana da Ι—a, dama aure ya yi ban sani ba? Kuma tun shekaranjiya ban sake ganinsa ba, kuma ba na samun sa a waya"


Sultan ya ce "Waye ya gaya miki?"


Ta yi shiru ta sunkuyar da kai. Ya numfasa ya ce "Shikenan na fahimta, amma ki kwantar da hankalinki, na tabattar da Hammad ba zai aikata abin da zai zubar da kima da mutuncin gidan nan ba, dan haka ki yi haΖ™uri ki bani lokaci, ina kan bincike ne"


"Amma Abie, to ina ya tafi, haryanzu ban san inda yake ba, kuma wayarsa ba ta shiga"


Sultan ya ce "Na sani, ki yi haΖ™uri ki kwantar da hankalinki. Zai dawo in sha Allah" Asal ta jinjina kai, ta tashi ta tafi, sai dai zuciyarta ta gaza haΖ™uri da samun nutsuwa.


Washegari, Sultan na tare da Sardauna da kuma Matawalle su na tattaunawa, aka zo neman iso cewar Imam Hammad yana neman izinin shigowa.

Cikin takunsa mai burgewa, ya shiga. Gaba Ι—aya suka zuba masa ido suna kallonsa.

Hammad ya nemi guri ya zauna a Ζ™asa tare da gaishe su. Matawalle ya amasa masa. Sultan kuwa rasa abin cewa ma ya yi sai daga bisani ya numfasa ya ce "Ina ka tafi tsawon kwanaki uku haka, ka kashe wayoyinka ka tayar mana da hankali?"


Hammad ya numfasa ya ce "Ina mai bayar da haΖ™uri, na laifin da na aikata, na yi hakan ne, domin tabattar muku da abin da na faΙ—a. Ina cikin hayyacina na faΙ—i abin da na faΙ—a, kuma da shaida a kan abin da na faΙ—a".

Sardauna ya ce "Ka na da hankali kuwa? Ka na nufin da gaske ka haihu da matar da ba mu sani ba?" Ya jinjina kai daidai lokacin da Mahmoudu ya shigo Ι—akin shima."


Matawalle ya ce "Ga munafukin nan, ya san komai"


Sardauna ya ce "Ni kun sani a duhu, shi kuma wannan waye ya kawo shi cikin wannan mas'alar?"


Sultan ya ce "Bari mu ji ta bakinsa"


Mahmoudu ya zauna ya gaishe su. Sannan ya numfasa ya ce "Da fari ina neman afuwar mai girma Sultan, da ahalinsa da 'yan majalissar sa, da ma duk wani wanda abin ya shafa. Na san na aikata laifin da na cancanci hukunci, kuma a shirye nake na karΙ“i hukuncin laifina, na aikata abin da ya saΙ“a wa dokar masarauta duk da girman matsayin Imam Hammad a Ζ™asar nan"


Sardauna ya ce "Mu na jin ka, ka yi mana bayani, me ka aikata, kuma me a sani a kan lamarin?"


Sultan ya numfasa ya ce "Wato Sardauna mun Ι“oye wa mutane abubuwa da dama da suka faru. Magana ta gaskiya Imam Hammad ya samu matsala ya bar Ζ™asar nan bamu sani ba. Mun yi ta bibiyar inda zamu samo shi. Muka rufe muka ce yana faransa babu lafiya. Da muka rasa shi, aka rasa hadiminsa Mahmoudu, shi ne muka koma binciken Mahmoudu ta Ζ™arΖ™ashin Ζ™asa, aka yi nasarar gano su a Nigeria. Sai dai da aka dawo da shi Agadez tamkar ya manta da mu baki Ι—aya, baya cikin hayyacinsa. Bamu san haΖ™iΖ™anin abin da ya faru a Nigeria ba, sai dai idan sun yi mana bayani yanzu.


Abin ya Ι—aurewa Sardauna kai, gaba Ι—aya bai san lamarin nan ba sai a yanzu, jin abin yake tamkar almara.


Mahmoudu ya ce "Bayan na tafi da Shugabana Imam Hammad Nigeria, nema masa magani, bayan da na fuskanci ya manta duk wani abu da ya shafe shi. A can muka haΙ—u da yarinyar a gidan da muka zauna, mahaifinta ya ba shi aurenta. Shi da kansa ya ce a biya sadakin aurensa da ita. Tun da shugabana ne ba ni da 'yancin yi masa musu. Na yi Ζ™oΖ™arin tunatar da shi, amma ko na tuna masa, ba zai iya tuna komai da ya shafe shi ba"


Matawalle ya ce "Wai wannan wace irin shiririta ce ku ke karanta mana? Wane irin abu ne haka? Ta yaya mutumin da ya manta komai ya san ya ce a biya masa sadaki ya yi aure?"


Mahmoudu ya ce "Imam waye shi, da duk abin da ya shafi Agadez ya manta, amma duk wani abu na rayuwa na yau da kullum ya sani. Kuma ga shi a tambaye shi, tun da yanzu yana iya tuna abubuwan da suka faru a Nigeria"


Sardauna ya ce "Shi tunanin nasa network ne kenan, ko zamani da idan wannan ya zo wannan zai wuce?"


Kafin Mahmoudu ya bayar da amsa, Matawalle ya ce "Wato Mahmoudu ba ka ji kashedin da na yi maka ba a kan sanar da shi wani abu ba"


Mahmoudu ya ce "Ba laifina ba ne ranka ya daΙ—e, shugabana ne duk abin da ya umarce ni, dole na yi ba ni da zaΙ“i"


Hammad ya miΖ™e ya ce "Ina zuwa"

Ko da Hammad ya fita, Mahmoudu suka ci gaba da yi wa tambayoyi, yana ta Ζ™oΖ™arin basu amsa da rufa wasu abubuwan.


Tsit suka yi da suka ga Hammad ya dawo, Nene na bin sa a baya da Ι—a a hannunta.


Matawalle ya ce "Imam me ya kawo wannan matar gidan nan kuma?" Nene ta yi turus tana haΙ—e rai ta sunkuyar da kai.

Kafin su Ζ™ara magana, Muhsin ya jefo mayafin kansa Ζ™asa, tare da waiwayowa yana kallon mutanen gurin.

A sukwane Sultan ya miΖ™e tsaye. Imam Hammad ya karΙ“i Muhsin daga hannun Nene, ya nufo Sultan da shi. Jikin Sultan ya hau tsuma, yana kallon yaron da ya jiye tamkar Hammad Ι—in sa yana Ζ™arami.

Shi kuwa Muhsin kallon babansa ya din ga yi yana kallon Sultan, ganinsu iri Ι—aya. Ya miΖ™a hannu ya Ι—auki Muhsin yana faΙ—in "La haula wala Ζ™uwwata illa billah"


Su kan su Sardauna da Matawalle, Ζ™ura wa yaron ido suka yi, duk sharrin mai sharri Ζ™arya ne ya ce wannan Ι—an ba na Hammad ba ne ba.


Matawalle ya ce "Ikon Allah, da gaske dai Hammad yana da Ι—a"


Sultan ji yake yi tamkar ya haΙ—iye Muhsin, da a yake son ya sauke shi ya koma gurin Nene. Ya juya yana miΖ™awa Hammad hannu ya Ι—auke shi.


Sardauna ya miΖ™e ya ce "Yanzu ina uwar yaron take"

"Tana nan" Imam ya faΙ—a yana sunkuyar da kansa Ζ™asa.


Sardauna ya ce "Akwai rikita-rikita a lamarin nan. Dole a san yadda za a yi. Mu na buΖ™atar ka zo mana da uwar yaron nan, gobe in Allah ya kaimu.

Ku kuma zamu tsare ku har sai komai ya daidaita mun gano komai."


Nene ta ce "Ranka ya daΙ—e me zai sanya a tsare ni? Mahmoudu ne naku dama, ku ci gaba da tsare shi da duk abin da za ku yi masa, amma ni ina roΖ™on alfarma a Ζ™yale ni na tafi"


Matawalle ya ce "Jayayya za ki yi da abin da muka ce kenan?"


Nene ta sunkuyar da kai ta yi shiru. Hammad ya ce "Zan cika miki alΖ™awarin da na Ι—auka, babu abin da zai faru in sha Allah, ki yi haΖ™uri gobe in Allah ya kaimu zan zo da ita" Nene ta yi shiru cikin sanyin jiki.


Duk yadda Sultan ya so Ζ™anΖ™ame Muhsin ya Ζ™i yadda, ya zamo ya sauka daga jikinsa, ya koma jikin Nene ya kwanta, ya saka hannunsa a baki.

Gaba Ι—aya Sultan ya kasa zaune ya kasa tsaye, saboda ganin Muhsin, bayan shafe lokaci yana fatan Ι—an nasa ya samu haihuwa.


Sardauna ya ce "To ita matar Mamman me ya kawo ta cikin wannan lamarin ne? Na ga kamar yaron ma ya santa?x


Hammad ya ce "Eh, a gurinta yake ne" Haka aka killace Nene da Mahmoudu, aka hana su zuwa ko ina.


*****


Ko da ya shiga sashensa babu kowa, Asal ba ta nan, ya yi mamakin inda ta tafi. Ya tafi kitchen Ι—in da Nana take girki, ya shiga ya buΙ—e fridge ya samu sassanyar madarar raΖ™uma, ya tsiyaya ya fita.

A Ζ™alla ya kai awanni biyu a zaune, sai ga Asal ta dawo, babu tsammani ta gan shi a falo a zaune.

Ɗan turus ta yi tana kallon sa. Ya ce "Ƙaraso mana" Jiki a sanyaye ta Ζ™arasa ta zauna a kusa da shi.


"Ina ki ka je haka?"


"Nemanka na je yi" ta furta jiki babu Ζ™wari.


"To zan gudu ne? Ai gani na dawo"


"Wancan karon ma ai ka tafi ka bar ni"


Ya yi murmushi ya ce "Wannan na larura ne ai CheriΓ©" Ya yi maganar yana miΖ™ewa, har ya nufi bedroom ta ce "Hammad" tsayawa ya yi cak, jin ta kira shi da gundarin sunansa na yanka.

"Da gaske ka haihu da wata a waje ban sani ba?"


"Waye ya gaya miki?"


Asal ta kalle shi ta ce "Kar ka amsa tambayata da tambaya, ka bani amsa ko na samu nutsuwar zuciya, babu abin da yake yi mini daΙ—i. An ce ka kira ni da juya, kuma ka ce ka na da Ι—a, da gaske haka ne?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido.


Sai ya fasa shiga Ι—akin, ya nufi inda take zaune, ya tsura mata ido sannan ya ce "Ni da ke na taΙ“a gaya miki haka? Ta girgiza kai jiki a sanyaye.


"Wanda ya gaya miki ya so cin mutuncinki ne, amma da bakina na taΙ“a faΙ—a?" Ta girgiza kai jikinta a sanyaye.


"To ki toshe kunneki daga jin abin da za a zo a gaya miki wai wai, ki jira abin da zai fito daga bakina zuwa kunnuwanki"


Ta yi ajiyar zuciya ta ce "To, amma ba ka gaya mini inda ka je ba"


"Wani aiki nake yi wa Sultan, ki kwantar da hankalinki" Ya miΖ™e ya tafi ya bar ta a gurin.

Da magariba ta ga yana ta shiri, ta ce "Amour ina zaka je ne?"

Ya ce "Eh yanzu zan yi miki bayani, zan je wani aiki da Sultan da ya saka ni ne, sai gobe in Allah ya kaimu zan dawo"


"Aiki kuma sai da daddare?"


Ya kalle ta ya ce "Asal, wai ki na zargina ne, yau na fara fita yin aiki da daddare, me yasa za ki tsare ni da tambayoyi kamar ba ki yarda da ni ba, shirya mu tafi tare" Yayi maganar yana haΙ—e rai.

Ta risunar da kai cikin girmamawa ta ce "Tuba nake yi, zuciyata ce ta cika fargaba, amma ka yi haΖ™uri" 

Ya miΖ™e ya nufi hanyar fita, haka nan zuciyarta ta tsananta bugawa.


Bayan fitarsa ya tsaya a harabar gidan, ya Ι—auki wayarsa ya kira Tafawa.

Tafawa ya Ι—aga tare da yin sallama.

Hammad ya amsa tare da cewa "Barka da dare ranka ya daΙ—e"


"Barka dai" Ya amsa a taΖ™aice.


"Yauwwa, dama na kira ka ne na sanar da kai, ka san abin da za ka din ga sanar da Asal, ka daina shiga cikin batun iyalina, idan ba haka ba za ka iya saka wa ta rasa ranta ko lafiyarta"


"Hammad, ni ka ke gaya wa haka?"


"Kai ka bani damar na gaya maka hakan ai. Abin da ba ka sani ba shi ne, Asal ta riga ta fara so na, tsawon lokacin da ya gabata, ci gaba da gaya mata magana kowace iri a kaina, ka iya haifar mata da matsala. Amma 'yarka ce duk abin da ka ke ganin shi ne daidai ka yi ba wani abu" Ya kashe wayarsa gaba Ι—aya, ya shiga mota da kansa ya ja motar ya bar gidan.


A zaune ya tarar da Nana a Ι—akin da kayanta suke, ta sanya atamfa riga da skirt, kanta babu Ι—an kwali. Ta yi parking Ι—in black natural hair Ι—in ta, da siririn band na yi wa yara kitso. Dan zabura ta yi, da ta ji motsinsa. Hannunsa riΖ™e da ledoji, ya Ζ™arasa ya zauna ya ajiye ledojin ya ce "Sannu da gida, na bar ki ke kaΙ—ai ko?"


"Dama can ai nikaΙ—ai Ι—in nake rayuwata"


Ya yi murmushi ya ce "Haka ne, amma dai kin rayu da ni Ι—in ko?" Ta yi masa shiru tana kai hannunta ta Ι—auki Ι—an kwalin kayan, za ga Ι—aure kanta. Ya janye Ι—an kwalin ya ce "A haka nake son ganinki, kin yi mini kyau sosai da sosai"


"Sayyid, duk wannan abubuwan da ka ke yi, ba za su taΙ“a tasiri a kaina ba, ka bani Ι—ana kawai na kama gabana"


"Gaskiya ne maganganuna ba za su yi tasiri a kan ki ba, ciki har da kirana da Sayyid.  Ga abinci na kawo miki, ki ci"


Ta kalle shi cikin damuwa ta ce "Ai na ci Abincin kamar yadda ka ce, yaushe za ka ba ni Ι—a na?"


"Kin ci, amma ba kamar yadda nake buΖ™ata ba, sonake ki Ζ™ara Ζ™iba, alamu sun nuna ba kya nutsuwa ki ci abinci ki Ζ™oshi" Ta kawar da kanta gefe, dan kar ma ya ci gaba da jan hirar. Dan ba ta son duk wani abu da zai sanya a ranta ta ji za ta iya ci gaba da rayuwa da shi."


Ya kwance rawaninsa, ya rage kayan jikinsa, ta kawar da kanta gefe, Ζ™irjinta na bugawa da sauri da sauri.

Ya zauna a kusa da ita ta Ι—ago ta kalle shi, gashin nan a kwance ya sha gyara. Ya Ι—ago mata yatsunsa ya ce "Ina zobena ne? Kin saka an addabe ni a kan zoben nan da yawa" Yana nuna mata yatsunsa.


Ta yamutsa fuska ta ce "Na yar da shi"


"Kin yar da zobena, kin ajiye turarrukana da mayukan gashina, ki na kallo ki na jin daΙ—i. Soyayyar gaskiya mara algus. Gobe in Allah ya kaimu za mu je gaban Sultan, mu ji hukuncin da za a yanke mana. Saboda na aikata laifi mai girman da babu wanda ya taΙ“a aikata shi sai ni."


Ayshercool.

08081012143

81

Nana ta taΙ“e baki ta ce "Wanda za a yanke maka dai, ni babu abin da ya haΙ—a ni da masarautarku, kawai a bani Ι—a na na tafi"


Ya zura mata ido, ya jinjina kai ya ce "Kin daina so na dai kenan ko?"


"Eh" ta faΙ—a tana kawar da kanta gefe.


"Shikenan, zan Ζ™ara miki lokaci, zuwa lokacin da ki ka ga ya dace ki saurare ni, amma ki sani, ni shugaba ne, kuma wasu lokutan idan aka tashi kawo gyara, toshe kunne muke yi, mu farantawa wani mu Ι“atawa wani, domin samar da gayar. Dan haka duk abin da ya kama zan banΖ™ara na aikata, domin ganin ba ki suΙ“uce mini ba, ko da kuwa abin da zan aikata Ι—in na nufin Ζ™ara miki Ζ™iyayyata. Yanzu dai ga abinci ki samu ki ci, sai ki kwanta ki huta da wuri zamu tafi" Ta murguΙ—a baki ta sake kawar da kanta gefe.

Duk wannan abubuwan da take yi masa, ko sau Ι—aya bai ji haushinta ba, shi dai fatansa da roΖ™onsa ta saurare shi cikin nutsuwa, ya warware mata zare da abawa, saboda ya san ko shi ne haka ta faru a kansa, zai ce wulaΖ™anci ne aka yi masa.

Ganin ya Ζ™i tashi ya bata guri, ya sanya ta Ι—ago ta kalle shi, ta ga ya zuba mata ido, kamar zai lashe ta.

Ta sake kai hannu ta Ι—auki Ι—ankwalinta, amma ya jefa shi bayansa.

Wannan kallon da yake Ζ™anΖ™ance ido ya fara yi mata, ta Ζ™ara tsuke fuska tana tattara nutsuwarta, amma ya kai hannunsa kan gashinta, ya fara shafawa a hankali. Bai sani ba ko dan ya saba ganin irin gashinsu Asal na buzaye nai laushi da santsi ya sanya na Nana yake burge shi.

BaΖ™i Ζ™irin da shi natural, mai cika sosai da sosai. Ta hau ture hannunsa, amma yaΖ™i barin abin da yake yi, sai ma lumshe mata ido da ya hau yi.

Duk wani abu da Nana za ta yi ta baΖ™anta masa rai, tana aikatawa domin gujewa barin nusarar zuciyarta ta sake yarda da shi, ta ba shi wata damar ya cutar da ita.


Sai da ya bar Ι—akin ta samu ta ci abinci, ta tura Ζ™ofar Ι—akin, sai dai babu mukulli yadda za ta datse Ζ™ofar dan kar ya shigo mata.

Tana kwanciya bacci, nannauyan bacci ya sake yin awon gaba da ita.


*****

Doctor Sharif ne ya tashi a razane, bayan mummunan mafarkin da ya yi da Shukura, ta biyo shi tana kuka jikinta duk jinin haihuwa, da wata sharΙ“eΙ“iyar wuΖ™a tana, ya ba ta jaririnta.

Ya din ga gudu yana ihu, ya Ι—an tsaya ya waiwaya kawai ya ganta a tsaye a kan matarsa, da wannan wuΖ™ar a hannunta, tana kallon cikin tana kallonsa tana faΙ—in "Ka zo ka bani jaririna, ko na farka cikin matarka na Ι—auke nata, ka ji abin da na ji" A daidai nan ya tashi cikin razani, ya haΙ—a uban gumi.

Ya kalli agogon Ι—akinsa ya ga Ζ™arfe biyu da kwata na dare, kawai ya ji zuciyarsa ta kasa nutsuwa, so yake ya je ya ga halin da matarsa take ciki, amma ya tuna wa zai fita ya bar wa yaransa mata su biyu da suke bacci. Doctor Sharif bai samu haihuwa da wuri ba bayan ya yi aure, sai da suka shekara goma sannan ta haifi yara mata biyu, yanzu za ta yi na uku ciki yana ta wahalar da ita. Tun da ya haΙ—a kai da Alhaji Zailani ya ba shi jaririn Shukura abin yake damunsa, amma tun da Alhaji Zailani ya shaΖ™a masa kuΙ—i, sai ya manta sai kuma yau da ya yi wannan mummunan mafarkin.


****

Yau ma Nana a kan gadon rannan ta hango Ƙaisar, lulluΙ“e da mayafi, hannunsa kawai ya ziro ta Ζ™asan mayafin yana rubutu a kan wani littafi.


Ya Ι—ago kai ya kalle ta, ya ci gaba da rubutunsa.


"Ƙaisar"


"Na'am" ya amsa ba tare da ya kalle ta ba. "Wai dan Allah me ya same ka?"


"A ina?"


"Na ga yanzu kullum ka na kan gadon nan, kuma a lulluΙ“e. Giyaz ne ya yi maka wani abin ne?"


Ya girgiza kai ya ce "A'a me ki ka gani?"


"Na san shikaΙ—ai ne yake iya cutar da kai" Ta yi maganar a sanyaye.


"In ji wa? Akwai Aljanu masu Ζ™arfi da suka fi ni Ζ™arfi da za su iya cutar da ni. Kawai ni ba na shiga harkar kowa ne, ina gefe ina jin daΙ—in rayuwar kaΙ—aicina da litattafaina da haΙ—a magunguna na"


Nana ta yi murmushi ta ce "Yaushe za ka yi aure ne kai?"


"Sai na girma"


"Au yanzu baka girma ba? Ina Haula ne?"


Tsuke fuska ya yi ya ce "Je ki Ι—akin magungunana, akwai wata kwalba taswirarta kamar zanen Duniya, ki Ι—aukko ki kawo mini"

Nana ta ce "To" Ta nufi Ι—akin da yake ajiye-ajiyen kayan maganinsa.

Ta tsaya tana ta kallon kwalaben, da yadda wasu magungunan suke yawo a cikin kwalaben, tamkar abubuwa masu rai.

Ta ga wanda ya ce ta Ι—aukko ta waiwayo kawai ta ga Giyaz a tsaye a bayanta.


"A'uzubikalimatillahi tammat" Ta furta cike da tsoro, a suffarsa ta tsoho tukuf ya bayyana a gabanta.


Ya buΙ—e baki ya ce "Ban taΙ“a ganin halittar da na tsana a doron Ζ™asa ba sama da ke, sai na sabauta rayuwarki, sai na kashe ki na Ζ™arar da zuriyarku na huta da wannan bala'in. Ya ja da baya ya nuna ta da sandarsa, da take ci da wata irin wuta mai tartsatsi.

Nana ta ja da baya, ta saka hannayenta ta rufe fuskarta, tana jiran jin wutar ta fara Ζ™ona ta, amma ta ji shiru. Ta buΙ—e idanunta a hankali ta ga Ƙaisar ya shiga tsakiyarsu, tartsatsin wutar ya Ζ™ona shi, ya faΙ—i a gefe jikinsa yana hayaΖ™i.

Nana ta saki kwalbar ta nufe shi da gudu. Cikin tashin hankali da tsoro ta ce "Ƙaisar, me ya same ka?" Sai a lokacin ta ga tarin raunukan da suke jikinsa, ga Ζ™onewar da ya yi yanzu.

Giyaz ya Ζ™araso kan Ƙaisar da sauri, ya saka hannunsa ya Ι—ago shi, amma ya ga jikinsa ya saki.


"Wallahi muddin Ι—a na ya mutu sai na kashe ki har lahira"


Cikin dakiya da kawar da tsoro ta ce "Me ka yi masa? Kai wane irin azzalumar halitta ne wai, kowane abu yana alfahari da Ι—ansa da Ζ™oΖ™arin ba shi kariya, amma kai kullum cikin Ζ™oΖ™arin cutar da shi ka ke. Ƙaisar ka tashi dan Allah. Ta yi maganar cikin kuka tana Ζ™oΖ™arin taΙ“a shi, amma wani irin matsanancin sanyi ya ratsa ta.

Ta buΙ—e idanunta a hankali cikin sheshsheΖ™ar kuka, har da majina kawai ta ganta a jikin Sayyid ya riΖ™e ta gam yana kallonta cikin tausayawa.

Ta yinΖ™ura za ta tashi amma ya hana ta, ya ce "Ki bari ki Ι—an nutsu. Me ya same shi ki ke wannan uban kukan haka? Idan komai ya lafa mini, dole na Ι—auki mataki a kansa, dan ba zai yiwu ya din ga bibiyar matata ba, ina baΖ™in ciki da hakan"


"Ba za ka yi masa komai ba, babu ruwanka da shi, tun da dai duk da tsana da abubuwan da nake yi masa, shi bai gudu ya bar ni ba, kamar yadda ka yi mini ba"


Ya Ι—an zura mata ido har zai yi magana sai kuma ya fasa.

Ta zame daga jikinsa ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa da tashin hankali, tare da fatan Allah ya sanya ba wata mummunar illar Giyaz ya yi masa ba. Ya tashi ya bar mata Ι—akin, dama kukanta da sheshsheΖ™arta ya jiyo, shi yasa ya fito ya je Ι—akin nata.

Washegari da safe, ya kawo mata kayan da za ta saka su tafi. Ya kalle ta cikin magiya ya ce "Ma vie, na san ni mai laifi ne a gurinki, amma dan Allah ki tattara nutsuwarki guri guda, domin mu samu mafita.

Duk abin da za su tambaye ki, ki sanar musu da komai, kar ki Ι“oye musu komai saboda makomarmu"


"Ni ba wata makomarmu, kawai Ι—a na za a bani na tafi"


Ya ce "To na ji, ga riga da za ki saka, ki je ki yi wanka ki shirya, ina jiran ki" Ta kalli rigar kamar ba zata karΙ“a ba, sai kuma ta karΙ“a ta ce "Na gode"


Ya yi murmushi ya ce "Ko mu je ki yi wankan a Ι—akina, akwai mayukan shafawa"


"A'a ina da man da zan shafa"


"To su ma nawan ne dai ki ke shafawa, saboda tsabar Ζ™auna" Ta murguΙ—a baki ta juya ta ajiye kayan, murmushi ya gaza barin fuskar sa. Ya ce "Kin san me na tuna? Lokacin da ki ke yi mini wanka mu na Nigeria, sauran ki yi mini wanka a Agadez".


"Sai ka je gurin Gimbiya hamshaΖ™iya, farar fata da take biladama ta yi maka" Ta yi maganar ba tare da ta juyo ba.

Ko da ta yi yinΖ™urin juyowa, sai jikinsu ya haΙ—u, sam ba ta san ya Ζ™araso bayanta ba, saboda cikin takunsa mai kama da hawainiya ya Ζ™araso. Dan sam ba shi da hayaniya ko karakaina.

Ya saka hannunsa ya zagaye Ζ™ugunta, Ζ™irjinta ya tsananta bugawa tsoro ya bayyana Ζ™arara a fuskarta.


"Ma viee banda dalilin soyayyarki, ta sarΖ™e ni ta ko ina ta hana ni motsi, da sai na saka an sa bulala an zane mini ke. Imam Hammad ki ke yi wa magana a haka? Ki yi mini magana cikin girmamawa, ki daina Ι—aga mini murya" Ya yi maganar yana sunkuyo da fuskarsa daidai ta ta har su na jin numfashin juna. 

Yana murmushi ya ce "Na taΙ“a yi miki wannan kashedin, kin tuna?" Ya yi maganar yana kashe mata ido.

"Dan haka ke za ki yi mini wanka a Agadez da ma"


"Ni ka cika ni ba na son irin wannan abin" Ta yi maganar kamar numfashinta zai Ι—auke.


Ya cika ta ya bar Ι—akin, ta zauna tana sauke numfashi.


*****


"Jamila ki yi bayani, na kasa gane kan wannan ciwon naki, na fara jin tsoro ki gaya mini me yake faruwa?" Ta girgiza kai ta ce "Babu komai"

"Wallahi sai kin gaya mini, damuwarki ta yi yawa, ciwo ya Ζ™i ci ya Ζ™i cinyewa mene ne yake faruwa ki ke Ι“oye mini" Mama ta yi maganar cikin tashin hankali tana zazzaro ido cikin fargabar abin da Jamilan za ta sanar da ita.

Ta girgiza kai hawaye na bin fuskarta ta ce "Dan Allah Mama ki yi haΖ™uri ki Ζ™yale ni, ni babu abin da yake damuna"


"Wallahi Jamila sai kin gaya mini uban abin da yake damunki, mene ne yake damunki?"


"Ni ma ban sani ba" Ta yi maganar tana kuka mai Ζ™ona zuciya.


"Wallahi kin sani sai kin gaya mini" Ta yi maganar tana Ζ™ara zazzare wa Jamila ido.


Kawai Jamila ta yi mata shiru, ta ci gaba da sheshsheΖ™ar kuka.


"Za ki gaya mini ko sai na shaΖ™e ki?"


Jamila ta girgiza kai ta ce "Ciki ne da ni"


Wata irin mummunar faΙ—uwar gaba ta ziyarci Mama, ta ja da baya ta dafe Ζ™irjinta, tana wani irin haki, tare da kallon Jamila cike da tsoro.


"Jaa..jam..jamilahh me ki ka ce? Ciki fa a ina? Kuma garin yaya?" Jamila ta ci gaba da sheshsheΖ™ar kuka ba ta yi magana ba.


Mama ta shaΖ™e Jamila ta ce "Ki gaya mini uban waye ya yi miki ciki kafin na take ki na kashe, da ki janyo mini abin kunya"


"Ke Rabi, kina ina ne? Waye yake yi mini kuka, kuma maganar me na ji ana yi?" Muryar Baba ta katse ta. Da hanzari ta saki wuyan Jamila, ta ja da baya tana hararta cikin Ζ™unar rai. Ta yi Ζ™wafa ta fito daga Ι—akin su Jamila.


"Me yake faruwa ne?"


"Babu komai, jikinta na shiga na duba"


Baba ya ce "Kuma shi ne take ta kuka haka? Ni na gaji da larurar nan ta Jamila, wannan banke-banken hayaΖ™in da ki ke yi mata duk ba ne ba"


Ta ce "To in sha Allah za mu je. Ka san mun je, mun kuma zuwa amma abu ya Ζ™i ci ya Ζ™i cinyewa, amma za mu koma"


*****

Nana ta tsaya tsuru da rigar nan a jikinta, ita kanta ta san ba dan albarkacin kaza Ζ™andagare kan sha ruwan kasko ba, ta san ba ta kai ta saka wannan rigar ba.

Ta jikin mudubi ta hango shigowarsa, kayansa royal blue, kalar rigar jikinta.


Ya Ζ™araso gabanta, ya fesa mata turare, ya zura hannu a aljihunsa, ya ciro zobuna da abin hannu ya saka mata. Ta yi Ζ™uri da ido tana kallon hannun nata, rabon da ta sanya wani abu na ado, har ta manta.

A tsorace ta ce "Ni dai zan cire wannan abin tsoro nake ji"

Banza ya yi mata ya gyara zaman mayafin rigar a kanta. Ya din ga Ζ™are mata kallo yana mamakin yadda Asal take aibata Nana da muni, dan kawai baΖ™ar fata ce.

Idanunta manya sexy eyes, farare Ζ™al da su, gwanin ban sha'awa, ga shi rigar tamkar dan jikinta aka yi ta.


Ya numfasa ya ce "Ina Ζ™ara tuna miki, duk wani abu da za a tambaye ki, kar wanda ya baki tsoro, kar kuma ki rufa komai, muddin ki na son Muhsin ya dawo hannunki"


"Meyasa kai ba za ka yi musu bayani ba kawai?"


"Da bayanina ya wadatar, ba zan bari a zo wannan gaΙ“ar ba". Ya ciro niΖ™ab ya saka mata.

Sannan ya saka hannunsa ya ciro wayarta daga aljihun rigarsa.


Nana ta waro ido ta ce "Wayata, ya aka yi ta zo hannunka? Dama kai ka Ι—auka?"


"Eh ni na Ι—auka, kin Ζ™i saurarata, balle na yi miki bayanin komai, mu je" Ya yi maganar yana nuna mata hanya.

Bakinta fal magana, amma ya yi mursisi, ya yi mata shiru. Ta tarar da takalma a falon gidan. Nana ta din ga ganin abin tamkar a mafarki.


Su na zaune a baya ita da shi, ana jan su a motar. Ta yi shiru tana zabga addu'a Ubangiji Allah ya bata nasarar karΙ“ar Ι—anta, dan ko kaΙ—an ba ta sha'awar gidan nan, Ι—an zamanta a gidan kawai ta fuskanci akwai kitimurmura a gidan.


Tun da aka doshi gidan gaban Nana yake tsananta faΙ—uwa, haka kurum take jin ba ta Ζ™aunar gidan. Gefe guda kuma Nana tana ta tunanin halin da Ƙaisar yake ciki.


Tun da aka yi parking suka fito, hadimai suke gaida Imam Hammad yana Ι—aga musu hannu. Ya riΖ™e hannun Nana yana ratsa cikin gidan da ita. Gaba Ι—aya aka zubo musu ido, ana son sanin wacece wannan ya riΖ™o hannunta, saboda kowa ya san ba Asal ba ce, saboda ba ta kai Asal tsawo ba, kuma Asal ba ma'abociyar niΖ™ab ba ce, ko kanta ma ba ta damu da rufewa ba.


Jikin Nana ya hau rawa, bayan da suka shiga Ι—akin zama na musamman na cikin fadar Sultan.

A can suka tarar da Sultan Ι—in, ga Matawalle ga Sardauna, su na jiran isowarsu.

Nana ta ja ta tsaya jikinta yana wata irin rawa, har Ζ™afafuwanta, gabanta ya din ga faΙ—uwa. Duk ta kowacwa kusurwar Ι—akin, akaai na'urar sanyaya Ι—aki, amma Nana ta kasa gane wane irin yanayi ma take ji.


Ya kalli Nana ya ce "Ki nutsu mana, kar ki ji tsoro, dan Allah kar ki yi wani abu da zai rusa mana rayuwa, kar haushina da ki ke ji, ya sanya ki makance, ki yanke mana hukuncin da zai cutar da rayuwarmu" Nana dai ta gaza ko Ζ™waΖ™Ζ™waran motsi.


Ya ja hannun Nana, suka Ζ™arasa tsakiyar Ι—akin suka zauna. Duk suka zubo musu ido.


Sardauna ya yi wa Nana alama da ta cire niΖ™abinta. Ta saka hannu ta cire tana sunkuyar da kai.


Abdou matawalle ya ce "Wannan kamar na taΙ“a ganinki ko?" Nana ta sunkuyar da kai.


Sardauna ya dube ta ya ce "Ya sunanki?"


"Nana Asma'u" Ta yi maganar kanta a sunkuye.


"Daga ina ki ke?"


Ta ce "Nigeria"


"Kin san wannan?" Ya yi maganar yana nuna mata Imam,Nana ta Ι—aga kai ta kalli Imam, ta kalli Sardauna, ta sunkuyar da kai.


Matawalle ya ce "Ki yi magana mana, kin san shi?" 


AREWABOOKS 


Nana ta kalle shi, ya kalle ta, ya tsare ta da idanunsa, yana jiran ya ji me za ta ce.


Abdou matawalle ya ce "Mu za ki kalla ki yi wa bayani. Ke ba ke muka gani cikin waΙ—anda suka kawo abinci ranar da aka yi taro ba?"

Ta jinjina kai alamar eh.


"To kin san shi ne dama?" Ya sake jefo mata tambayar.


Ta jinjina kai. Sardauna ya ce "Ki buΙ—e baki ki yi magana mana, ki daina amsa mana da kai".


"Eh na san shi"


"Waye shi a gurinki?"


Ta yi shiru tana nazarin amsar da za ta bayar, kar ta zama ta kwafsa su hana ta Ι—an ta. Cike da karaya ya sake kallon Nana ya ce "Ma viee, talk ki yi magana mana"


"Ni sai na ga Muhsin zan yi magana, dan Allah ka fara nuna mini Ι—a na"


Ya ce "To shikenan"


Ya ce "Ina neman alfarma, zan saka a kawo mata Muhsin, za ta yi magana"


Matawalle ya ce "Wane irin abu ne wannan? Ta san a gaban su wa take kuwa?"


Sardaunan Agadez ya ce "Bari Matawalle, a saka a kawo shi, mu ji me za ta ce"


Sardauna ya ciro wayarsa yana Ι—an taΙ“awa, yana satar kallon Nana.


Sultan kuwa rasa abin yi ya yi, ya tuna fuskarta a gurin taron cin abinci da aka yi, ya so ya bibiyi me ya kawo baΖ™uwa wannan gurin, amma abubuwa suka sha kansa.

Wani irin gumi ne yake tsatstsafo masa bayan tuna irin taΙ“argazar da Hammad ya aikata, ka iya janyowa. Babban abin da ya Ζ™ara sanya masa fargaba, shi ne abin da yake iya gani daga idanun Hammad a kan yarinyar. Ko a yanzu ya tattara hankalinsa a kanta, ta sunkuyar da kai sai zubar da hawaye take, da alama ma tamkar ya manta da zamansu a gurin.


Wata hadima ce ta shigo, hannunta Ι—auke da Muhsin. Yana ganin Nana, ya yi wani irin zillo daga jikin hadimar, yana wata irin Ζ™ara yana cewa "Naaa" kamar yadda yake kiranta, Nene  kuma ya ce mata umma"


Nana ta yi wata irin zabura ta nufe shi da gudu ta Ι—auke shi, ta Ζ™anΖ™ame shi a jikinta, tana zubar da hawaye cikin damuwa da kewar tilon Ι—an nata. Shi na Muhsin Ι—in, Ζ™anΖ™ameta ya yi ya fashe da kuka.


Jikin Sayyid ya yi sanyi sosai, ya din ga jin abin da ya aikata bai kyauta ba, kamar ya shiga hakkinsu da yawa, amma babu yadda ya iya ne, hakan ne kawai masalaha a garesu baki Ι—aya.


Sultan ya kalli Abdou matawalle suka haΙ—a ido, suka mayar kan Nana da ta durΖ™ushe a gurin tana ta uban kuka.


Matawalle ya yi gyaran murya ya ce "Wannan yaron wane ne shi a gurinki?"


"Ɗa na ne" Ta faΙ—a cikin kuka.


"Shi kuma wannan fa?" Ya nuna mata Hammad.


"Mijina ne" Ta furta cikin sanyin jiki.


"Waye baban yaron naki?" Ya sake tambayarta. Ta kalli Hammad ta ce "Shine"


"Kin tabattar shi ne mahaifin yaron nan, kuma ke ki ka haifi yaron?" 


Ta jinjina kai ta ce "Na tabattar"


"Ya aka yi ku ka haΙ—u ku ka yi aure?"


Ta numfasa ta ce "A Nigeria muka haΙ—u, a can muka yi aure"


"Waye shaidarki cewa mijinki ne shi?"


Takaici ya fara kama Nana, wace shaida kuma bayan wannan Ι—an wata shaida suke nema?.


"Ni ba ni da wata shaida, Allah ne shaidata sai babana da ya Ι—aura mana aure."


Sardauna ya ce "Yaya aka yi mahaifin naki ya aura miki wanda bai san daga inda yake ba, ko ku Ζ™asarku ba ka bincike ku ke aure?"


Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ana yi, akwai 'yan uwansa da suke gadi tare, sun san aure muka yi, su Habu"


Matawalle ya ce "Ban gane gadi ba, gadi kamar yaya?"


Hammad ya ce "Ina neman alfarma dan Allah a tsagaita yi mata tambayoyin nan haka, duk a rikice take. Ga wannan wayar akwai video da hotuna a ciki, lokacin da muna rayuwa ne da ni da ita a Nigeria"


Sulta ya ce "Hammad, ya zama dole ka yi mana shiru, a kammala binciken da yakamata, domin tabattar da gaskiyar lamarin nan"


Sardauna ya sake kallon Nana ya ce "Ya aka yi ki ka zo gidan nan yin aiki?"


Ta haΙ—iye yawu ta ce "Mu na Nigeria lokaci Ι—aya na nemi 'yan uwansa na rasa, ya haΙ—u da larurar zuciya, ina tsaka da jinyarsa na neme shi na rasa. Kawai na yanke shawarar na zo Nijar ko zan haΙ—u da shi" Mamaki ya kama Hammad, yadda kai da fata taΖ™i bayanin ainihin ciwon da ya din ga yi bayan hawan jini.


Matawalle ya ce "Ya aka yi da ku ka haΙ—u ba ki sanar da kowa mijinki ne ba? Kuma me yasa wacan karon da ya kira ki a nan, ki ka ce ba ki san shi ba? Anya akwai Ζ™amshin gaskiya a maganar nan?"


Imam ya ce "Wancan karon laifina ne, kuma gaba Ι—aya a ruΙ—e take"


"Ba kai ake tambaya ba, ita muke tambaya" Matawalle ya katse Sayyid.


Cikin kuka Nana ta ce "Dan Allah ku yi haΖ™uri, ni ba na buΖ™atar na ci gaba da zama da shi, ku bani Ι—a na kawai zan tafi na yi muku alΖ™awarin ba za ku sake ganina a inda yake ba"


Suka yi tsit suna kallon Nana, daga bisani Sardauna ya ce "HaΖ™iΖ™a idan ta tabatta kin auri Imam Hammad, to kun tafka babban kuskure mussaman shi da ya san Ζ™a'ida da dokar masarauta. Sai dai uzuri Ι—aya za a yi muku, shi ne shi ya haΙ—u da larura, ke kuma ba ki san wannan Ζ™a'idar ba. Babban mai laifi shi ne Mahmoudu kuma sai ya haΙ—u da tsatsauran hukunci. Babu buΖ™atar mu ci gaba da bincike da wani bin diddigi.

Daga nan za a Ι—auke ki a kai ki gidan baΖ™i na musamman, ki huta kwana biyu zamu haΙ—a miki sha tara ta arziki, za kuma mu sanya a mayar da ke har Ζ™asarku. 

Imam Hammad dole zamu san yadda zamu juya wannan lamarin, mu Ι“oye gaskiyarsa, idan haryanzu da aurenka a kanta, zaka sauwwaΖ™e mata zamu karΙ“i Ι—anmu a mayar da ita Nigeria"


Wani irin mugun kallo Hammad ya yi wa Sardauna. Nana kuwa zabura ta yi tana Ζ™anΖ™ame Muhsin ta ce "A'a Sayyid ne Ι—anku, Muhsin kuma Ι—a na ne, ba zan baku Ι—a na ba, da shi zan tafi Nigeria"


Matawalle ya ce "Ba zai yiwu ba, mu zamu karΙ“i Muhsin ki yi haΖ™uri. Abu ne da muka daΙ—e mu na nema daga Hammad. Ki yi haΖ™uri dole mu kare kimarsa da mutuncinsa a Agadez"


Hammad ya miΖ™e a rikice, jin matakin da za a Ι—auka, amma Sultan ya kira sunansa cikin Ι—aga murya. Da ido aka yi wa hadimar nan magana, ta nufi Nana gadan-gadan za ta Ζ™wace Muhsin.

Nana ta Ζ™ara Ζ™anΖ™ame shi tana kuka cikin Ι—aga murya ta ce "Ba zan baku Ι—a na ba, ku Ζ™yale mini Ι—a na, baku san baΖ™ar azabar da na sha kan na haife shi ba. Zan bar muku naku Ι—an har abada nima ku bar mini nawa" Matar ta fi Ζ™arfin Nana, Muhsin na zunduma ihu, Nana na kuka ta fizge shi.

Nana ta bita da gudu tana janta "Ki bani Ι—a na, wallahi ba zan bar muku shi ba. Ba za a kassara rayuwarsa kamar yadda aka kassara ta Sayyid ba".


Wasu hadiman ne maza suka shigo, za su tasa Nana a gaba su fita da ita. Amma mugun kallon da Imam ya yi musu ya sanya suka tsaya.

Ya Ζ™arasa inda Nana ta riΖ™e hadimar, ya saka hannu ya cire hannun Nana daga jikin hadimar da ta riΖ™e gam.


"Ka ce su bani Ι—a na, kuna ina lokacin da nake gantalin nemanka ba ni da ko muhallin zama da tsohon cikinsa? Ka damu da Ι—an naka, ka tafi baka sake waiwayata ba? Ka bani Ι—a na na tafi na barku"


Idanunsa fal hawaye ya ce "Na sani, ki yi haΖ™uri Ma viee, ba a son raina ba komai ya faru ki yi haΖ™uri ki saurare ni"

Sai dai tamkar yana Ζ™ara ziga ta, ta ci gaba da cewa "Na yi dana sanin saninka a rayuwata, soyayya da tausayi ba su amfana wa rayuwata komai ba. Da na san abin da zan tarar kenan da na zauna inda Allah ya ajiye ni ban fito neman ka ba. A kan Muhsin zan iya karΙ“ar Ƙaisar da abin da yake so na aikata sai dai masarautar taku ta tarwatse" muryarta tuni ta fara dashewa, saboda Ι—aga murya da kukan da take yi mai tsuma zuciya.


Matawalle ya ce "Imam wannan wace irin yarinya ce, mara Ι—a'a da rashin tarbiyya? Kai ku fita da ita"


"Kar wanda ya taΙ“a mini mata, zan fita da ita da kaina" Ya yi maganar yana Ι—aga musu hannu alamar dakatarwa.


Nana kuwa tuni ta silale jikinta ya saki, ya riΖ™e ta a jikinsa ba ta iya cewa uffan sai sauke numfashi da take yi kawai.


Sultan ya yi shiru, yana Ζ™ara jujjuya lamarin a cikin zuciyarsa.


Imam da kansa ya saka Nana a cikin mota, ya babbake ya hana kowa ya taΙ“a ta. Ya rufe motar ya zagaya zai buΙ—e Ι—aya Ι“angaren ya shiga, amma wasu manyan hadimai suka tsare Ζ™ofar.


Ya kalle su ba tare da ya yi magana ba.

Ɗayan ya ce "Tuba muke yi, umarni ne daga sama, cewar kar a kuskura a bari ka bar gidan nan"


Cikin mamaki ya ce "Daga sama gurin wa?"


"Daga sama gurina, kar wanda ya bar shi ya fita ko ina daga gidan nan, har sai mun bayar da umarnin hakan, ku kaita inda muka yi umarni, za mu sanya a mayar da ita Nigeria. Ina sake jaddada muku, kar wanda ya kuskura ya bar Imam Hammad ya fita daga gidan nan sai mun ba da damar hakan" Sardauna ya yi maganar cikin bayar da umarni, aka ji motar da Nana take ciki aka fita da ita daga gidan.


Da ya san haka abubuwan nan za su kasance, da babu abin da zai hana ya Ι—auki Nana da Ι—ansa ya bar musu Ζ™asar gaba Ι—aya. Sai dai halin da Sultan zai shiga kawai yake tunani.


Cike da baΖ™in ciki da takaici, ya koma ya iske Sultan, gabansa ya je ya tsaya cikin tashin hankali ya ce "Me yasa za ka yi haka? Idan ni ne a matsayin da take za ka so a yi mini haka? Ka kalli lamarin nan a matsayinka na uba, ba Sultan ba. Dokar masarauta  ba dokar addini ba ce ba. Me yasa 'yan majalissarka za su ziga ka ka yi haka? Babu wata hujja da ake buΖ™ata domin tabattar da Asma'u matata ce, Mahmoudu su suka Ι—aura mini aure. Shi ma kun ce a kulle shi ya yi laifi. Aure muka yi da Nana ga yarona ku na gani me yasa za a raba ta da Ι—anta kuma a mayar da ita Nigeria haba Abie"


"Hammad, ni ka zo gabana ka tsaya ka na gaya mini magana a haka saboda mace? Dole ne mu girmama tare da martaba al'adun masarautar nan, mu samu mu binne babban kuskuren da ku ka aikata ko dan tsira da mutuncinka.


Hammad ya girgiza kai ya ce "Sultan, Asma'u ba mace ba ce kawai, ba zan binne laifukana saboda al'ada na je lahira ba ni da abin da zan gaya wa Allah ba. Zan Ι—auki matata na bar Ζ™asar nan gaba Ι—aya. Na bar muku sarautar da al'adar. Da na rayu babu su ma babu abin da ya same ni, ka gafarce ni"


Mari Sultan ya kifa masa, ya janyo rigarsa yana kallon sa ya ce "Ko ka fara shan wani abu ne Hammad? Ni ka ke gaya wa ka bar mana sarautar za ka Ι—auki wata bare ka bar Ζ™asar nan?"


Jiki a sanyaye ya ce "Ba bare ba ce ba, matata ce kuma akwai Ι—a a tsakaninmu. A halin yanzu a Duniya bayan kai ba na tunanin akwai wani wanda zai iya yi mini abun da ta yi mini. Gaskiyar da ba ka sona faΙ—a Abie ina tare da baΖ™in aljani, da yake burkita ni. Nana na iya ganinsa kuma itakaΙ—ai take iya fahimtar halin da nake ci. Abie Nana ba mace ba ce kawai, waliyya ce a cikin mata, har shanyewar Ι“arin jiki na yi, lokacin da ku ka gano su Mahmoudu aka Ι—auke su, ba ta da wani mataimaki sai Allah kuma ba ta taΙ“a gajiya da ni ba. Asma'u har najasata ta wanke da hannunta. Da jikinta da lafiyarta da lokacikta da zuciyarta ta rayu da ni cikin kulawa da tausayawa. Idan na bari aka yi amfani da rashin gatanta saboda ni shafaffe da mai ne aka cutar da ita ban yi wa kaina adalci ba. Tsakanina da ita ba alaΖ™a ce gangar jiki ba kawai, akwai tasirin ruhika, da kuma tasirin alaΖ™ar uba da Ι—a. Wannan wani abu ne da ni da ita ne kawai muka sani. Abie ba za ku iya raba ni da Asma'u ba, idan ma ku ka raba mu, sai kun nemo ta da kanku" Ya Ζ™arasa maganar yana ja da baya ya fice ya bar Ι—akin.


Sultan ya dafe gaban goshinsa da yake yi masa wani irin raΙ—aΙ—i, ya nemi guri ya zauna. Duk yana jin maganganun Hammad a matsayin soki burutsun neman mafitar yadda zai samu ya zauna da Nana. 

Shi ma yana ganin ba a kyauta ba, a Ζ™wace mata yaro kuma a kore ta.


Asal kuwa tana can ta gigice, bayan da ta samu labari cewar, an ga Hammad da wata mata ya riΖ™e hannunta sun shiga sashen Sultan. Ta rasa wa zata dosa domin ta ji gaskiyar lamarin.


Tana cikin wannan gigitar, Tafawa ya kira ta, ta Ι—aga jikinta yana ta tsuma.


Ya ce "Asal, wace hadima ce a gidanki, ta kai abinci lokacin da su Asad suka zo?" Sai ta manta me ma ake nufi da hadima, sai da ya yi mata tsawa sannan ta farga ta ce "Wata hadima ce a gidan nan. Ce mini a ka yi an ga Imam Hammad da wata ya riΖ™o hannunta sun shiga sashen Sultan, ko ka na da labarin wace ce?"


Ya ja tsaki ya ce "Sai me kuma? Ina tambayarki ki na tambayata wani abu daban."


"Abbu dan Allah ka gaya mini idan ka san wani abu, ka ga ka ce mini ya ce yana da Ι—a, a tsorace nake"


Tafawa ya ce "Asal, kina nufin kina son Hammad ne?"


Cikin kuka ta ce "Abbu mijina ne fa, ko ba na son sa ina duba makomata nima" Sai dai tana rufe bakinta, Hammad ya banko Ζ™ofar Ι—akin da Ζ™arfin gaske.

A razane ta saki wayar hannunta, ta waiwaya tana kallon sa.

Da sauri ta tunkare shi tana faΙ—in "Hammad wace mata a ce an ganku kun shigo tare yau, har kana riΖ™e da hannunta kun shiga sashen Sultan? Kar dai maganar da aka gaya mini gaskiya ce?" Ko kallon inda take bai yi ba ya nufi kan gadonsa ya faΙ—a kai.


Ta nufe shi a hasale ta ce "Ka tashi ka yi mini bayani, wace matar a ganku tare? Kuma da gaske ka na da Ι—a ko ba ka da shi? Yanzu da mutuncinka da kimarka ka zaΙ“i ka tozarta kanka ka kwanta da wata mace a waje dan ta haifa maka Ι—a. Wallahi Hammad baka isa ba, ina yi maka rantsuwa da zatin Allah kowace matar ce sai na sanya an kashe ta, kuma an kashe mini banza dan duk cikin Agadez da kewayenta na san duk wata 'yar gata a bayana take. Ka tashi ka yi mini bayani"


Wuyanta ya damΖ™a, jikinsa na wata irin tsuma, gani ta yi gaba Ι—aya ya canza ya koma kamar wani horo, jikinsa ya koma jajawurr tamkar tumatir. Babu baΖ™ar Ζ™wayar idanunsa sai farar nan tas, duk wata jijiya da taje jikinsa duk sun kumbura. ya faΙ—o daga kan gadon yana burgima, saboda yadda yake jin tamkar wuta na ci a Ζ™asan fatarsa.


Tofa!


Ayshercool 

08081012143.


Kar dai ku gaji da ni, ina yi muku tuni da cewar labarin Buzu ya shiga gasa a YouTube channel Ι—in limamin tsakar gida, wanda da yawan likes na kashi goman farko za a yi amfani gurin alΖ™alanci. Ku taimaka ku je ku danna like a kashi goman farko na labarin BUZU na gode.


82

LITTAFIN KUƊI NE, KARKI RAINA GIRMAN HAKKI, 1K NE VIA 0069685771

Aisha Adam stanbic 

08081012143

Hankalin Sultan da muΖ™arrabansa ya dunguzuma nesa ba kusa ba. Suka gaza gane kan Imam Hammad ta ko ina.

Ga Muhsin shi ma yana ta rikici, ba ya cin abinci sam, sai koke-koke ya Ζ™i saurar kowa saboda rashin sabo.


Cikin tashin hankali Sultan yake kallon Hammad da yake wance kamar itace, ya dubi Matawalle ya ce "Anya Matawalle ba Asibiti zamu kai shi ba. Ina ga wannan Ι“oye-Ι“oyen da muke yi, lokaci ne ya yi da asirinmu zai tonu. Sai dai ina jin tsoron a san halin da muke ciki".


Matawalle ya ce "Wannan ba abin da ya shafi Asibiti ba ne, ko ka manta haka ya yi ta yi a lokacin da aka dawo da shi daga Nigeria? Sai da muka fita faransa sannan ya daina wannan abin,har tunaninsa ya dawo?"


Sultan ya ce "Haka ne, amma kamar wannan karon, abin ya ninka wancan da ya yi. Ba ya ci ba ya sha fa" Ya yi maganar cikin damuwa.


Matawalle ya ce "Nima abin da ya tsorata ni gaskiya, amma dole mu nemo masu magani da za su duba shi. Amma ya zama dole mu samo waΙ—anda ba za su furta komai ba, idan ba haka ba nan ma akwai matsala"

Sultan ya dafe kansa yana kallon Hammad, tamkar ya fashe da kuka.

Asal ta shigo Ι—akin da sallama, ta kalle su ta gaishe su cikin girmamawa suka amsa mata baki Ι—aya.


Cikin damuwa ta ce "Abie yau ma bai farka ba ko?"


Sultan ya jinjina kai ya ce "Bai farka ba Asal"


Daga nesa inda take tsaya take Ι—an leΖ™a shi ta ce "Baccin dai yake yi?"


Matawalle ya ce "Ƙaraso ki gan shi mana"


Ta girgiza kai ta ce "A'a shaΖ™e ni yake yi ya kusa kashe ni, daga nan ma ina hango shi" 


Babu babban abin da yake sake Ι—aga wa Sultan hankali, sama da wannan azababben zafin da jikinsa yake yi mai ban tsoro, kamar ba jikin Ι—an Adam ba.


Da yamma Sultan na cikin Ι—akinsa, yana ta kai komo, ya rasa mene ne mafita, ya san muddin batun ciwon nan na Hammad ya fita, ba su da wata mafita.


Aka sanar masa da isowar Imam Zahradeen. Ya bayar da iznin ya shiga. Bayan shigarsa suka gaisa. Ya dubi Sultan ya ce "Abie, wai ko ka aiki Imam Hammad wani gurin ne? Ya saka ni wani aiki, na je gidansa Gimbiya Asal ta ce "Baya nan, kuma a iya sanina ban san ya yi wata tafiya ba"


Sultan ya ce "Haka ne, yana Ζ™arΖ™ashin takunkumi na hana shi zuwa ko ina ne".


Ya ce "Na sani, ina son ganinsa ne, a yi mini alfarmar nan, wani saΖ™o zan isar masa na aikin da ya sanya ni"


Sultan ya dubi Zahradeen ya ce "Aikin me kenan?" Zahradeen ya sunkuyar da kai ya yi shiru. Sultan ya ce "Shikenan na fahimta, amma a yanzu dai ka yi haΖ™uri ba zaka samu ganinsa ba, yana Ζ™arΖ™ashin takunkumi "


Imam Zahradeen ya Ι—an yi jimm sannan ya ce "Shikenan, godiya nake ranka ya daΙ—e" Daga haka ya tashi ya bar sashen. Ya san iya takunkumin hana fita aka Ζ™aΖ™aba masa, banda na killace shi a hana ganinsa gaba Ι—aya, amma lokaci Ι—aya an ce har ganinsa ma ba zai yiwu ba.


*****

Nana ce zaune ta saka kwanon abinci a gaba ta yi shiru, Nene ta taΙ“a ta ta ce "Ki ci Abincin mana, kin bari yana ta shan iska"


Nana ta numfasa ta ce "Nene wai zuwa yaushe zan je na karΙ“o Ι—a na ne, ci gaba da zama fa bai kamace ni a garin nan ba, ni duk hankalina ya yi gida wallahi"

"Nana na san duk abin da nake yi, ba na son ki faΙ—a komar mutanen nan, su ci moriyar ganga su yada kwaronta. Mutane ne masu bala'in son kansu fiye da yadda ki ke tunani, dan haka ki Ι—an yi haΖ™uri. Sai dai Nene na rufe baki, wayarta ta fara ringing.

Nene ta Ι—auki wayar ta saka a kunnenta tare da yin sallama.


"Barka da wannan lokaci Ummana"


Ta amsa da "Barkanmu dai"


"Umma dan Allah Nana tana tare da ke ne? Idan ke ki ka Ι—auke ta ki taimaka ki sanar mini inda ki ka kaita, kan Imam Hammad ya farga ba ta nan, wallahi ban san me zan ce masa ba"


Nene ta ce "Idan ya fargan me ya yi saura a tsakaninsu? Ba dai Ι—anku ba ne kun Ζ™wace? Takardar sakinta kawai muke jira, zan mayar da ita Nigeria har gidansu"


Mahmoudu ya ce "Ummana, wannan wani abu ne da ya shafi Nana da Imam da iyalinshi. Ni fa kamar ya san za a yi haka ya haΙ—a ni da Imam Zahradeen ya sanya aka killace ku a wannan gidan, kuma lokaci guda sai ki Ι—auke ta ki tafi na neme ki na rasa. Dan girman Allah da buwayarsa ki taimaka ki gaya mini inda ku ke"


"Kai ka kiyaye ni, ba zan faΙ—a ba Ι—in, ba ku da wani haΙ—i da Nana, ka gaya wa ubangidanka ya aiko mini da takardar yarinyata, zan mayar da ita gaban iyayenta ta nemi gafararsu" Ta katse wayar.


Nana ta ce "Nene to idan ya sake ni ba su bani Muhsin Ι—in ba fa?"


"Shi Muhsin Ι—in da shi aka haife ki ne?"


Idon Nana fal hawaye ta ce "Ni dai a bani Ι—a na kan ya sake ni"


Nene ta girgiza kai ta ce "Nana kina cikin jarrabawa, wannan Ι—an shi zai sanya ki lalata komai ki kasa Ζ™watarwa kanki 'yanci, ai sai ki yi"


Nana ta Ι—an Ι“ata fuska ta ce "Amma Nene, ya aka yi aka saki Mahmoudu na ji sun ce wai sai sun hukunta shi, sun Ι—ora masa laifin aurenmu, sun sake shi kenan sun fasa hukunta shi?"


Nene ta ce "Oho musu, su kashe shi ma kar su bar shi da rai."


Nana ta waro ido ta ce "Nene wai ke ba kya son Ι—an nan naki ne?"


"To Nana idan ma ina son nasa, zan goya shi ne?"


"To Nene dama mutum yana daina son Ι—ansa ne?"


Nene kawai ta yi murmushi, ta tashi ta bar Nana da wasi-wasi.


*****


Wasa-wasa aka shafe kwana uku curr ba a ga 'yar gidan Doctor Sharif ba, ga matarsa a Asibiti, hankalinsa ya tashi kamar zai haukace. Ga jikin matarsa kullum babu afuwa ga shi ta fara damuwa da ina Hafsa take. Sai dai ya ce mata tana gida ba ta da lafiya.

Ya din ga yawo gurin 'yan sanda da gidajen radio, yana bayar da cigiya ko za a ganta. Ya din ga jin tamkar ya Ι—ora hannu a ka ya zunduma ihu. Gefe guda ga mummunan mafarkin da yake yi da Shukura babu Ζ™aΖ™Ζ™autawa har fargabar kwanciya bacci yake yi. Saboda munanan mafarkai ne marasa daΙ—i.


Ya shiga Asibiti ya tarar da wata katoΙ“ara, an yi wa matarsa insulin allurar sauke sugar, fiye da kima suganta ya yi mummunan sauka, har ta shiga shock.

Tare da sauran abokan aikinsa likitoci, suka yi ta fafutuka Ζ™oΖ™arin ganin sun ceto ranta. Yana tsaka da wannan tashin hankalin 'yan sanda suka kira shi, ya tafi cike da fatan 'yarsa Hafsa aka gani. Sai dai 'yan sanda suka ce masa Asibiti za su je ya ga wata yarinya da aka tsinta aka kaita domin a duba lafiyarta. Suka Ι—auke shi a mota suka tafi. Sai dai suna zuwa aka tafi da shi Ι—akin adana gawarwaki. Sam bai kawo komai a ransa ba, idonsa ya rufe kawai Hafsansa za a nuna masa. Sai dai aka fito da gawarwaki biyu. Ɗaya a kango a ka tsince ta, an fafe cikinta an kwashe wasu sassa na jikinta a can wata unguwa. Yarinyar sanye da Uniform Ι—in makarantar da ya fasaltawa 'yan sanda.

Tamkar ba Namiji ba, haka ya kurma uban ihu ya faΙ—i Ζ™asa sumamme, bayan ganin 'yarsa Hafsa a wannan mumman yanayi.


Bangaren Sagir ma bai fitar da rai ba, yana ta addu'a, da ji a jikinsa Yusransa za ta dawo. Ga shi satin haihuwarta ya kama. Ya daure ya lallaΙ“a ya je duba Yusra. Wadda ita ma jiki yake a rikice.

Sai dai da yaje ya tarar da jikinta da Ι—an sauΖ™i, dan har suka Ι—an fara hirar hankali.

Ta ce "Haryanzu ba a ga matarka ba ko?"


"Haryanzu Yusra, amma kina yi mata addu'a Allah ya bayyanata?"


Ta ce "Ina yi mana, ina so Allah ya sanya a ganta, kuma fa a satin nan za ta haihu, dan ta ma fara naΖ™uda kaΙ—an-kaΙ—an"


Ya ce "Yaya aka yi ki ka sani?"


Ta ce "Mafarkinta na yi mana, tana kulle a wani Ι—aki mai duhu, ta ce mini ba ta jin daΙ—in  zaman gurin, baka gani ba abin tausayi"


Idonsa fal Ζ™walla ya ce "Duk a mafarkin ki ka ga haka?"


"Eh mana, tana ta kuka ma"


Ya ce "Shikenan, ya isa haka. Ki ci gaba da yi mata addu'a bari na je gida. Amma yaushe za ki zo mu koma gida, ina fama da kaΙ—aici"


Ta ce "Ko yau ka yi wa Anty magana sai na bika mu tafi"


Ya jinjina kai ya ce "To shikenan, babu laifi"


Shukura kuwa tana kwance a Ζ™asa, zama babu daΙ—i, kwanciya babu daΙ—i duk inda ta motsa cikin nan sai ya tokare ta. Ga ciwon baya da na Ζ™afafuwa da take yi da take kyautata zaton naΖ™uda ta fara a tsaitsaye.

Sai dai tana yawan ganin Nana cikin mafarki, tana nanata mata ta yawaita addua babu Ζ™aΖ™Ζ™autawa babu ji babu gani. Duk da tana yi Ι—in amma ta Ζ™ara Ζ™aimi gurin yi.


*****

Ko da aka shiga kwana na biyar da shigar Hammad halin da yake ciki, Sultan ya gama tsurewa babban tashin hankalinsa rashin cin komai da ba ya yi ga abin kullum gaba yake yi.

Tafawa ya samu Sultan a kan lallai a sake zaman majalissa, a ji bayanin Hammad a gaban kowa da kowa a kan yadda aka yi yake da Ι—a kamar yadda ya faΙ—a."


Matawalle ne ya amsa masa da cewar "A tunanina wannan maganar ai ta wuce ko?"


"Ta wuce ta je ina? Kun san zata wuce ku ka dakatar da ni daga majalissa. Ya faΙ—i abin da dole sai ya fito ya kare maganar da ya yi. Ya ce yana da Ι—a, ina Ι—an yake? Kuma wacece uwar yaron? Idan kuma shaci faΙ—i ne to ta tabatta ba shi da lafiyar Ζ™waΖ™walwa da na faΙ—a ku ke Ι“oyewa"


Matawalle ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ka san abin da zaka din ga furtawa a kansa, ko babu alaΖ™ar jini a tsakaninku shi shugaba ne."


"Eh Hammad Ι—a na ne, kuma shugaba ne, amma ba zai yiwu na zuba ido ina ganin ba daidai ba, a ce yana shugaba babu cikakkiyar lafiya ba kuma ku na dannewa ku Ι“oyewa ba. Ita larura ai ba abin kunya ba ce, kuma abu ne da yakamata a sani domin a nemi lafiya"


Cikin nutsuwa Sultan ya ce "Imam Hammad ba mahaukaci ba ne ba, ban sna meyasa ka ke aibata shi da da wannan larurar ba"


"Allah ya taimake ka, idan ba haka ba ne, mene ne gaskiyar batun Ι—an da ya ce yana da shi?" Tafawa ya yi maganar yana tsare Sultan da ido.


"Abu ne da muke kan bincike a kai, koma mene ne zaka ji daga baya"


Ya ce "Shikenan na ji wannan, ina son zan yi magana da shi, magana ce a kan Ι—iyata Asal"


Sultan ya kalli Tafawa cike da takaici, ya san yana sane yake wannan bin Ζ™waΖ™Ζ™wafin da bin diddigin a kan lallai sai ya ga Hammad."


Sultan ya ce "Za ka gan shi, amma nan da wani Ι—an lokaci" Hakan ya sanya Tafawa sake tabattar da maganganun Asal.

A ransa ya ce "Idan ka san wata baka san wata ba Jalaludeen"


*****

Tun washegarin dawowar Nana daga gidan su Hammad, yanayin jikinta take jin babu daΙ—i, kamar akwai wani abu mara daΙ—i da yake faruwa. Sai dai ta danganta hakan da kewa da kuma tashin hankali da take ciki a kan Muhsin. Amma idan ta nutsu sai ta ji wannan damuwar daban ce, wannan a cikin jikinta da ruhinta take jin damuwar, sai dai ta yi iya Ζ™oΖ™arinta gurin danne damuwar, da duΖ™ufa da addu'a Allah ya dawo mata da Ι—anta.

Yau da safe Nana ta fito ta tarar da Nana, ta Ι—ora tukkwane daban-daban har uku a kan murhu, tana ta harhaΙ—a wasu irin saiwoyi da sassaΖ™e-sassaΖ™e tana ta zubawa tana dafawa.

Nana ta ce "Umman Muhsin, yau kuma baya aka tuna wa ake dafa wa magani"

Nene ta yi murmushi ta ce "Ba kula ki zan yi ba ai ki Ζ™arata, daΙ—in abin Ζ™waryar sama ce ke dukan ta Ζ™asa daga ni har ke"

Nana ta yi dariya ta ce "Yasin ni ban bayar da magani ba"

"A'a tuna dai, tuna dai yarinya"

"To ai Sayyid kawai na yi wa"

Nene ta ce "Kash, an zo gurin dan haka ki yi mini shiru" Ta Ζ™arasa maganar tana janyo wayarta da ta yi Ζ™arar shigowar saΖ™o. Ta tsuke fuska ta kira Mahmoudu a waya. Ya amsa tare da gaishe ta.

Bayan ta amsa ta ce "Wannan uban kuΙ—in fa da ka sako mini?"


"A'a ki yi haΖ™uri ai ba naki ba ne, na kula da Gimbiyar Imam ne"


"Da can ku kuke bani abin kula da ita? Lokacin da take gararambar neman taimakon ba ku neme ta ba ba barin ta ku ka yi tana gantali a titi ba?"


Ya ce "Dan Allah ki yi haΖ™uri, ba zan iya gaya masa haka ba. Haryanzu fa ma ni ban sake ganinsa ba tun ranar da ya je tare da ita. Ba ya gidansa baya fitowa zaman majillisa, ko hawa ba ya fitowa. Duk da na san an saka masa takunkumi shige da fice amma an tsaurara masa sosai. Ki yi haΖ™uri har gida za mu zo ban haΖ™uri. Dan Allah ki taya mu rarrashinta dan ta Ζ™i saurararsa gaba Ι—aya, kuma wallahi hankalinsa a tashe yake nesa ba kusa ba. Ga tarin magauta da yake da su a cikin gidan su ma da ba barinsa suka yi ba. Dan Allah ku yi haΖ™uri Umma ke kin san sha'anin gidan sarauta kin san komai"

"Ni rabu da ni sai daΙ—in bakin tsiya, ai ko mutum zai danne ya yanka sai ka kare shi"

Yayi dariya ya ce "Ai Ι—anki ne, kin san ba zai aikata haka ba, tuba muke ranki ya daΙ—e. Wallahi ina ta faΙ—i tashin na gan shi ne ma, na san halin da yake ciki. Amma a Ζ™ara ba wa Gimbiyar Imam haΖ™uri"


"A'a babu ruwana, idan ku ka zo kwa bata da kanku" Suka yi sallama ta kashe wayar.


Ta kalli Nana ta ce "Kafin ki yi wanka, fara Ι—ibar ruwan maganin nan, ki je ki yi wanka ki gama, sai ki yi wanka da shi. Ki fito ki sha wannan maganin sai ki karya.

Nana ta ce "Shi kuma Nene na mene ne?"

"Na tsarin jiki da kariya ne, saboda kariya ne" Ta yi maganar tana basarwa, tare da tsuke fuska dan kar Nana ta addabe ta da tambayoyi.

Ganin hakan ya sanya Nana amsawa Nene, ba dan tana so ba.


*****


Mahmoudu ne ya iske Sultan a gurin shan iskarsa da yamma. Kasancewar shi ma ba shi da iyaka a shiga da fita a gidan Sultan, saboda Hammad, dan haka ganinsa ba wahala yake yi masa ba.

Sai dai yau kasancewar Sultan shikaΙ—ai ne, ya fi sakin jiki da shi.


"Barka da wannan yammaci Sultan"


"Barkanmu dai Mahmoudu, kuna lafiya?"


Ya amsa da "Alhamdillah. Alfarma nake nema daga gare ka Sultan"


"Ina sauraren ka"


"Dan Allah a yi mini izini na ga Imam Hammad ne. 


Sultan ya numfasa ya ce "Hammad babu lafiya. Ta so muje ka gani"


Ya tashi cikin ladabi, ya bi bayan Sultan. Suka yi tafiya mai nisa a sashinsa, can cikin wani Ι—aki suka je ya buΙ—e masa Ι—akin.

Cikin damuwa ya ce "Mahmoudu ya tabatta Hammad hauka yake yi, haukan ma irin wanda ban taΙ“a ganin kalarsa ba. Na ce ko a Nigeria da ku ka zauna ya yi irin wannan? Yanzu idan ka je kusa da shi zai iya shaΖ™e ka, tsawon wannan lokacin bai ci abinci ba, a haka kawai yake"

Cikin tashin hankali ya ce "Yayi ciwo daban-daban, amma ban ga ya yi irin wannan ba, ina kyautata zaton mutum Ι—aya ne ya san matsalolinsa ciki da waje, ya san bakin zaren wannan ciwon nasa"

"Wane ne? Mahmoudu ba ma son asirinmu ya tonu fa"

"Da asirinmu zai tonu da tuni ta tona, sai dai a zo da Mahaifiyar Muhsin"


AREWABOOKS 


Cikin rashin fahimta Sultan ya ce "Ban gane me ka ke nufi ba?"


Cikin girmamawa ya ce "Matarsa da ya zauna da ita a Nigeria, saboda ni kaina na fuskanci wasu abubuwa masu ban mamaki a tsakanin su, bayan sun yi aure." Ya yi maganar yana kallon inda Imam Hammad yake ta mimmiΖ™ewa yana kakari, kamar ana yanka rago.

Cikin damuwa ya ce "Yanzu tun wancan lokacin a haka yake?" Sultan ya jinjina masa kai ya ce "Ko ruwa bai sake sha ba, hankalina a tashe yake. Ga Tafawa ya sako ni gaba a kan Imam Hammad sosai da sosai; Yanzu dai mu je ka yi mini bayani gwari-gwari na fahimta"


Bayan sun fito, suka zauna tare da Mahmoudu. 

Mahmoudu ya numfasa ya ce "Idan ban manta ba, bayan mun dawo daga bikin buΙ—e gidan cin abincin Imam na MaraΙ—i, mun dawo ka sanar masa da batun tafiya Damagaran ya wakilceka a taron sarakuna da za a yi a Zinder. Ba zan manta ba an kai ruwa rana sosai a kan tafiyar.

A tsukin lokacin ya kan gaya mini cewa, shi gaba Ι—aya ji yake yi baya Ζ™aunar zaman Ζ™asar nan, yana jin kamar a cikin wani bala'i da masifa yake. Da fari na zata da wasa yake yi, amma sai na fuskanci da gaske yake a lokacin. Na ce masa mu sanar maka ko Ι—aga tafiyar za a yi, amma ya ce mini a'a kar na gaya wa kowa, baya son ya Ι—aga wa kowa hankali.

Tare muke kwana da shi a cikin gidan nan, muna shirin tafiya , kawai ya ce mini na same shi a Ι—aya gidan nasa na kusa da gidan tarihi da yamma, mu yi tafiyar. Na ce masa mu tafi tare amma ya ce mini a'a.


Haka kurum bayan tafiyarsa hankalina ya Ζ™i kwanciya. 

Kawai na kira shi na ce masa yana ina? Ya ce mini ya tafi zagaye can wajen gidan adana kayan tarihi na Agadez. Kawai na hau raΖ™umi na bi shi.

Sai dai na je gidan adana kayan tarihi na tarar bayanan, aka kira ni da Ι“oyayyiyar lamba, aka ce mini an san Imam Hammad nake nema, ya bi cikin sahara. Ba tunanin komai na kewaya bayan gidan inda Sahrar nan take.

Na yi tafiya ta kai ta awa huΙ—u, saboda ina ganin sahun raΖ™umi a gurin. A tsakiyar sahara na ci karo da Imam Hammad cikin fita hayyaci a sume. Abin ya bani mamaki, na ciro shimfiΙ—a a jikin raΖ™umina, na yi na kwantar da shi na dudduba jikinsa na ga babu wata alama ta ciwo. Na jira ya farfaΙ—o ko na Ι—auke shi mu koma gida.

Cikin ikon Allah ya farfaΙ—o, na ce masa meyasa ya taho cikin sahara haka? Ko ba shi da lafiya ne?" Ya yi mini shiru. Na ba shi ruwa ya karΙ“a ya sha.

Na Ι—ora shi a raΖ™umina ina mamakin yadda yanayinsa ya canza.

Muka doshi dawowa, sai dai muna nufo Agadez ya din ga wani irin ihu, ya faΙ—i a cikin sahara daga kan raΖ™umin ya din ga burgima yana kururuwa. Na sauka na riΖ™e shi ina tambayar ko lafiya? Amma ba ya iya magana sai ihu kawai.

Hankalina ya tashi na rasa yadda zan yi da shi. Da mun nausa cikin sahara sosai sai ya yi shiru da mun nufo gida, sai ya rikice. Na rasa yadda zan yi ga yamma tana yi. Ba zai yiwu na Ι—aukko shi na taho da shi yana wannan kururwar ba kowa yana ganinsa. Kawai aka kira ni da Ι“oyayyiyar lambar nan aka ce, kar na dawo Niger da Imam, idan ba haka ba zai yi hauka tuburan Ζ™arshe ya rasa ransa gaba Ι—aya. Na tambayi waye amma ba a bani amsa ba a ka kashe wayar.

Na din ga mamakin waye wannan ya kira ni haka? Kasancewar na ga alamun gaskiya a abin da aka faΙ—a, da na juya da shi yake rikicewa, kawai sai na nufi Nigeria da shi cike da fargaba da zullumi.

Akwai abokan hulaΙ—armu na Nigeria, da muke kasuwancin asuwaki da dabino wanda da yawa ba su san waye ni ba, kuma ba su san Imam ba, kawai sai na neme su a waya. Aka ci gaba da kirana da wannan lambar ana gargaΙ—ina kar na saka a masarauta a san da abin da ya samu Imam Hammad, saboda za a ce dole sai an dawo da shi, idan aka dawo da shi kuma zai rasa hankalinsa da rayuwar sa.

Haka na Ι“ad da kamanni da Ι“oye waye Imam, na shiga da shi Nigeria muka fara neman magani. Sai ya shafe sati bai yi magana ba, ya manta waye shi gaba Ι—aya.

Sai dai aka Ι“oye lambar asusu, aka din ga turo mini kuΙ—i cikin asusuna, na ci gaba da harkar safarar dabino zuma da asuwaki tsakanin Nijar da Nigeria, ina tsoron taΙ“a kuΙ—in da ake turo mini saboda ban san na waye ba.

Sai dai duk gurin masu magungunan da muka je, sai su ce mu yi haΖ™uri ba za su iya ba shi magani ba. Mun je gurin masu magunguna daban-daban amma bamu samu magani ba. Ya manta komai nasa da ya shafi Agadez.

Na samu wani gida da abokan hulΙ—ata suke gadi, muka shiga cikinsu.

Zai yi wanka zai ci abinci zai yi salla, amma ba zai yi magana ba sai jefi-jefi. Idan kuma abin ya juyo ba ya ko cin abinci ba ya magana. Sai dai gaba Ι—aya al'amuransa sun Ζ™ara rikicewa, ya din ga abu kamar yana gane-gane. Kwatsam aka kawo mahaifiyar Muhsin, ita kuma za ta din ga aikin rainon yaro. Duk lokacin da ya ganta ya kan Ζ™ure ta da idanunsa kamar yana ganin wani abu a tare da ita. Sai da na taΙ“a tambayarsa ko ya santa ya ce mini a'a amma tana da wani abu da yake nema domin ya tuna waye shi.

Tsawon wannan lokacin ban taΙ“a gaya masa waye shi ba, saboda fatana ya tuna da kansa kuma kar na yi wani abu, da asirinmu zai tonu ko a cutar da shi.

Kwatsam! Ban san abin da ya faru ba, muka tarar da ita a sume a cikin Ι—akinmu, daga ita sai shi. Babu alamun ya yi mata wani abu na cutarwa, sai dai an ce abinci aka bata ta kawo mana ta suma a Ι—akin. Mahafinta ya ce ba zai yadda ba ya ce sai ya aure ta. Ba zan Ι“oye maka ba Sultan mahaifiyar Muhsin yar masu Ζ™aramin Ζ™arfi ce. Aka din ga dambarwa babanta ya ce sai dai Imama ya aure ta. Ina ta lallaΙ“awa ina bayar da haΖ™uri, amma ya ce na biya masa sadakin.

Ba ni da ikon yin jayayya da shi, dole aka Ι—aura musu auren. Sai dai mai kirna a wayar nan ya kira ni, ya sanar mini da ya san batun auren da aka yi wa Imam Hammad.

Tun bayan aurensa da ita, ya fara samun sassauci, ya dawo yana magana, wasu daga halayensa suka canza. Yana kishinta fiye da kima, yana sakin jiki da ita ya yi hira da ita, ya yi wasa da ita abin da ba ya yi ma a rayuwarsa ta nan.

Na sani akwai abin da ta din ga Ι“oye mini game da zaman da take yi da shi, duk da nima ban bayyana mata waye shi ba. Amma na san ciwon nan yana motsa masa, duk da na yi mata bayanin ciwon nasa amma iya abin da na sani. Sai dai har aka je aka Ι—auke mu daga Nigeria bata taΙ“a nuna mini yana yin wani abu na irin wannan rashin lafiyar ba. Dan haka ko dai tana da maganin ciwon sa, ko kuma rufa masa asiri ta yi."


Sultan ya sauke wani irin nannauyan numfashi ya ce "Gaskiya na ji daΙ—i sosai da yadda ka rufa wasu abubuwan a gaban su Matawalle duk kusancina da su, akwai abin da ba zan so su sani ba. Amma ya aka yi ta san yana Agadez ta zo, nifa ina jin tsoron raΙ“a Ι—a na da wanda zai cutar da shi"


"Allah ya taimake ka, neman Imam ne ya sanya ta baro Nigeria babu wanda ya sani ta taho da tsohon ciki Nijar. A hannun mahaifiyata ta zauna. Duk da ba komai na sani ba, bayan na baro Nigeria, a bakinta za a ji komai. Amma Umma ta ce mini, ta gaya mata rashin lafiya ya yi sosai bayan an Ι—auke mu daga Nigeria"


Sultan ya jinjina kai ya ce

"Kuma haryanzu baka san waye ya Ι“oye lambar yake kiranka ba?" Ya girgiza kai ya ce "Ban sani waye ba, lokacin da aka rufe ni an karΙ“i wayata, da aka dawo mini da ita ma, ba a sake kirana ba"

Sultan ya Ι—an yi shiru sannan ya ce "Shikenan, amm zan yi magana da Matawalle, a je a taho da ita, idan ma an mayar da ita Nigeria ne, duk inda take a Nigeria a nemo ta. Amma ko waye yake kiran nan naka, yana da masaniya a kan abin da ya same shi. Amma shikenan"

Mahmoudu ya Ι—an yi Jimm, yana tsoron a gano Nene ta Ι—auke ta, dan kuwa ba ya tunanin an sake waiwayar Nana tun da aka ce a je a killace ta, dan da tuni sun farga an baza nemanta, ko dan kar ta je ta faΙ—i cewa ita matar Hammad ce. Sultan ya sallame shi ya tashi ya tafi.

Sultan ya dafe kansa ya yi shiru, saboda yadda al'amura suke Ζ™ara rincaΙ“ewa. Duk tarin yaransa babu wanda yake tausayi kamar Hammad. Kuma yana burin Hammad Ι—in ya gaje shi, amma shi ne wanda jarrabawa kala-kala take bibiya.


*****


"Nene, wai wannan naman da nake ta ci kashi-kashi na mene ne, ni gara ki bani hatsi kawai"


Nene ta ce "To mijinki ne ya turo kuΙ—in ciyar da ke, kin ga kuwa dole na baki ingantaccen abinci."


"Ni k Ζ™yale masa kuΙ—insa, kawai lokaci nake jira idan ba ki yi wani abu ba, na je duk bala'in da za a yi, a yi a bani Ι—a na, kan na basu mamaki wallahi. Dan ko zan mutu sai na raba su da shi"


Nene ta ce "Ba ma za ki mutu ba. Za ki karΙ“i Muhsin, ki koma Ι—akin mijinki Gimbiya, ina jinjina lamarin Ubangiji Nana, ashe duk wahalar da ki ka sha, duk zaman da muka yi Gimbiya ce ke Nana"


Nana ta Ι“ata fuska ta ce "Dan Allah Nene ki daina, sai na ji wani banbarakwai, ni Sayyid nake so, ba Imam Hammad ba, ko kaΙ—an ba na sha'awar wannan gidan. Azabar tension Ι—in da na sha a baya ma ta ishe ni, yanzu hutu nake buΖ™ata"


Nene kawai dariya tana girgiza kai, ta ce "Yaro man kaza, Nana na taΙ“a soyayyar nan fa nima, ba za ki yi mini wani alaye ba. Amma ni da ke mun sha banban. Allah ya zaΙ“a abin da ya fi alkhairi ".


Nana ta yi shiru, gaba Ι—aya magungunan da Nene take bata, bata taΙ“a kawo na mene ne ba.

Gaba Ι—aya tana kwance ta kasa bacci, sai juye-juye take yi, a jikinta take jin yanayinta ya Ζ™ara canzawa fiye da yadda take a baya. Dama lallaΙ“a rayuwarta take yi a hankali.

Shiru ta yi tana tunanin ko wani hali Muhsin yake ciki?. Sai kuma ta tuna ta ji wayar da Nene ta yi da Mahmoudu a kan cewa, an sanya wa Hammad takunkumin fita. Ta tafi tunanin tun daga wane lokaci ya gane ta, amma ya share ya nuna kamar bai santa ba.

Guntun tsaki ta ja, ta juya zata gyara kwanciyarta. Ta fara jin wannan Ζ™amshin na Ι—akin nan da take ganinta tare da Sayyid yana ratsa hancinta.

"Ina fatan ba da ni ake wannan tsakin ba?" Ba shiri ta buΙ—e idonta, kamar yadda ta yi tsammani a Ι—akin ta gan su sai dai ya rame sosai da sosai.


Tsiwa ta so yi masa, sai kuma jikinta ya yi sanyi ta ce "Ba ka da lafiya ne?"


"Lafiyata Ζ™alau, kewarki kawai nake yi, shi ya sanya rame" 

Ya tashi zaune ya matsa kusa da kta da ita ya rungumota jikinsa ya ce "Ma vie komai zai wuce in sha Allah, amma kar ki yanke hukuncin haΖ™ura da ni, ba zan iya jurewa ba, ruhina da gangar jikina sun yi mugun sabo da ke, sabon da ba zan iya misalta miki ba" Ya yi maganar yana kwantar da kansa a kafaΙ—arta. Duk da wata zuciyar na azalzalarta da ta ture kan sa daga jikinta. Amma ya sake riΖ™o hannunta cikin sanyin jiki ya ce "Ki yi magana ko na ji daΙ—i mana"


"Sayyid, ci gaba da rayuwa da kai ba zai haifar wa tawa rayuwar Ι—a mai ido ba, zaren ba kalar yadin ba ne, kuma sama ta yi wa yaro nisa"

"Ban ma gane me ki ke nufi ba, ni duk wata rayuwa da zan yi. Nutsuwata da kwanciyar hankalina na tattare da ke Ma vie" Ta yi masa shiru daga bisani ta ce "Ni fa gaskiya ka yi mini nauyi, ka Ι—aga ni"


Ya yi murmushi ya ce "Lokacin da ki ke so na, ba kya jin na yi miki nauyin, lallaΙ“a ni ki ke yi. Asmy"


"Na'am"


"Yanayin akwai zafi sosai, ina buΖ™atar sanyi"


"Ko fifita ba zaka samu ba, balle wani sanyi"

Sai dai tamkar a zahiri, haka ya ci gaba da lallaΙ“a Nana, da daΙ—aΙ—an kalaman da sai da ta manta da fushin da take yi, ta saki jikinta da shi. Babu tsammani Nana ta farka tana ta ajiyar zuciya. Ta tashi ta zauna ta jingina da bango. Jin yanayinta abin da ya faru ta yi tamkar a zahiri ba mafarki ba.

Ta daΙ—e ba ta yi mafarki makamancin wannan ba. Tana son sanin ainihin abin da yake faruwa take ganinsu a wannan Ι—akin.

Mararta ta Ζ™ulle ta kifa kanta a kan gwiwoyinta, ta tsorata da ramar da ta ga ya yi, jikinta ya ci gaba da bata yana cikin damuwa.

Ga abubuwan da ta gani a cikin gidan game da shi. Ƙarshe dai kasa komawa bacci ta yi, ga tunanin Ƙaisar da shi ma ba ta san halin da yake ciki ba.


Wayewar garin Allah, haka Nene ta sake zubowa Nana kajin nan da Ι—uminsu sai Ζ™amshi suke yi. 

Nana tana ta lissafi da son yin gwajin ciki, domin tabattar da maganar Sayyid, dan sai da ta yi mafarkinsa jiya sannan ma ta tuna. Sai dai tana jin tsoro, ga shi tana jin Kunyar Nene balle ta gaya mata. Yaushe ma za ta fara bayanin ta na da ciki, cikin da ba ta san ya aka yi ya faru ba?.

Tana cikin Ι—aki tana cin naman nan, ta jiyo muryar Nene na waya.

Mahmoudu ka kiyaye ni da batun Nanan nan fa"


"Dan Allah Umma ki yi haΖ™uri, zamu shiga matsala sun farga Nana ba ta nan, yanzu haka nemanta ake yi"


"Su neme ta, me ta yi musu?"


"Babu abin da ta yi, Sultan ne yake son ganinta"


"Sultan, ita ma za a yi mata abin da aka yi mini Ι—in ne?"


"A'a Umma dan Allah ki yi haΖ™uri dai, babu wanda ya san inda take. Ni na ce musu na san inda take, yanzu masalaha suke nema. Wallahi an kasa gane kansa gaba Ι—aya. Yau kwana na tara kenan yana sume ko ruwa bai shiga cikinsa ba. Dan Allah ki gaya mini kuna ina?"

Gaban Nana ya yi wata irin faΙ—uwa, ta miΖ™e tsaye tana sauraren me Nene za ta ce.


"Zan neme ka zuwa anjima, sai na yi magana da ita, idan ta kama sai dai ku bi ta can Nigeria gurin iyayenta, ku roΖ™o alfarmarsu, ku Ι—aukko ta"


"Umma, Nigeria kuma ta koma? Shikenan mun kaΙ—e."


Ta ce "Ka dai saurare ni na ce" Ta kashe wayar. Tana shiga Ι—akin ta ga Nana a tsaye.

Nene ta ce "Za ki je kenan?" Nana ta yi shiru tana kallon idon Nene.


Nene ta yi murmushi ta ce "Ai ba zan hana ki ba. Ban sani ba ko daga nan ki karΙ“o takardar sakin naki. Ki haΙ—a abin da ki ke buΖ™ata, zan kira shi na gaya masa su zo su Ι—auke ki" Jiki a sanyaye Nana ta ce "Kina ganin idan na je, ban yi wauta ba ko kuma tarko suka yi mini ba?"


Nene ta ce "Sam, ba na tunanin hakan, ba za a haΙ—a kai da Mahmoudu a yi miki haka ba. Ina yi miki fatan nasara."


Nana ta ce "Nene mu tafi tare mana"


Nene ta girgiza kai ta ce "A'a wace ni, ni da mijina bawa ne, ba sa Ζ™aunata ba sa son ganina. Ai ke ciwon ido ce, babu yadda suka iya da ke. Mussaman da yake Muhsin a tsakanin ku."


Nene ta yi ba ta Ζ™warin gwiwa, Nana kuwa addu'a take yi, da fatan Allah ya sanya ba Giyaz ne ya ci gaba da azabtar da shi ba.


Bayan la'asar sai ga Mahmoudu a wata hamshaΖ™iyar mota zai Ι—auki Nana. Nene ta yi masa kashedi sosai da sosai a kan ya ji tsoron Allah, kar a haΙ—a kai da shi, a cutar da Nana. Ya yi wa Nene alΖ™awarin hakan. Nana ta Ι—auki kayanta Nene ta raka su har bakin Ζ™ofa, tare da yi wa Nana fatan alkhairi.

A motar Mahmoudu ya ci gaba da ba wa Nana haΖ™uri ya ce "Idan mun je, kar ki nuna musu fusata ko jin haushin sun Ζ™wace miki Ι—a sun kore ki, bamu san abin da Allah zai yi ba idan mun je tare da ke. WataΖ™ila rashinki ne a kusa da shi da abin da aka yi miki ya sanya shi a wannan halin. Nana kwanan Hammad takwas ko ruwa bai shiga bakinsa ba, yana sume kawai. Ki yi haΖ™uri da abubuwan da suke faruwa mu je mu gani ko Allah zai sanya a dace." Nana ta jinjina masa kai, Ζ™asan zuciyarta tana addu'a.

Ta wata hanya da bata taΙ“a sanin da ita ba, duk da gidan ba Ζ™aramin gida ba ne, suka bi. Ya yi parking gurin babu kowa an Ζ™awata shi da wasu irin dakakkun kujeru na gini da fulawoyi.


Su na bin wata Ζ™ofa suka shiga, sai ga su a sashen Sultan. Nana ta yi shiru ta ga yadda aka yi wa Ζ™asa ado da dukiya, kamar ba za a mutu a bar ta ba.

Tsahirtawa ta yi da tunanin nata, bayan ganin mutanen da a yanzu ta tsani ganinsu, tun bayan yin Ζ™arfa-Ζ™arfar rabata da Ι—anta. Sun kame a kan kujeru cikin manyan kayansu da rawani, sai dai sun sauke rawanin fuskarsu tana iya gane kowanne a cikin su. Tuna abin da Mahmoudu ya gaya mata, ya sanya ta daidaita nutsuwarta, ta tsuguna a gabansu ta ce "Ina wuninku" Suka yi shiru ba su amsa mata ba.


Mahmoudu ya ce "Barka da yammaci za ki ce musu"


Ta ce "Barkanku da yammaci, na same ku lafiya?"

Matawalle ya ce "Alhamdillah, sai ki ka ji mun sake neman ki ko?"


Ta ce "Eh, ina fatan ba wani laifin na sake yi ba?"


Ya girgiza kai ya ce "Ba ki yi laifi ba. Alfarma ma muke nema a gurinki"


Ta risuna ta ce "To, Allah ya bani ikon yi"


Ya ce "Kafin nan zan tambaye ki. Ke ce ki ka rayu da shi a Nigeria a matsayin matarsa bayan barinsa Agadez. Shin ko yana yin rashin lafiya mai kama da taΙ“in hankali, bayan larurar da ya yi na manta ko shi waye?" Nana ta Ι—an Ι—aga kai sannan ta mayar ta sunkuyar. Ta girgiza ta ce "A'a bai taΙ“a yi ba" Gaba Ι—aya sai suka yi shiru su na kallon ta.


Sardauna ya ce "Ki na nufin bai taΙ“a wani na larurar rashin lafiyar Ζ™waΖ™walwa ba?"


Nana ta ce "Eh sai matsalar zuciya da ya yi fama da ita"


Sardauna ya ce "To idan haka ne, babu amfani kawo ta kenan, tun da babu wani haske da za ta iya bamu, ko wani abu da za ta iya yi"


Nana ta risuna ta ce "Dan Allah ina son a bani dama, ko sau Ι—aya na gan shi, dan Allah"


Sardauna ya ce "A'a, babu buΖ™atar hakan"


Sultan ya yi shiru yana nazarin fuskar Nana, daga bisani ya ce "Duk da haka, mu je ta gan shi, ko da wani abu da za ta iya yi a kai, ko abinci a samu ya ci"


Matawalle ya ce "Gimbiya Asal ma ta gaza yin wani abu, balle ita?"


Sultan ya miΖ™e sannan suka tashi. Su na gaba Nana da Mahmoudu su na baya.

Ɗakin kansa an rage hasken fitilun cikinsa, hanyar da suka bi zuwa Ι—akin ba zaka taΙ“a cewa akwai wani Ι—aki a gurin ba.


Daga nesa Nana ta hango shi, yana kwance a dunΖ™ule guri Ι—aya. Gashin kansa ya baje a Ζ™asa. Sardauna ya kunna fitilun Ι—akin haske ya gauraye Ι—akin.

Ziiiiiiiiii ta fara jin wannan sautun, na turnuΖ™ewar Ζ™urar sahara. Ta tattare nutsuwarta guri guda, ta din ga ambaton Allah. Kawai ta nufe shi. Sardauna zai yi magana Sultan ya hana shi, dan ba a yi wa Nana iznin zuwa inda yake ba.

Ta durΖ™usa a kansa, ta ga an Ι—aure masa hannayensa, jikinsa ya yi jawurr ga wannan hucin zafin da take iya ji, fiye da yadda sauran mutane idan sun raΙ“e shi suke ji.

Ta hau kiciniyar kwance masa hannunsa. Wata irin miΖ™a ya yi tana gama kwance masa hannun. Ya miΖ™a hannunsa wuyanta, da wannan kalar idanun nasa mai ban tsoro. Cikin jarumta da dakiya, ta riΖ™e hannun nasa ta ce "Sayyid, nice. Ka saurari sautin muryar. Asmy ce ka ayyana addu'a a cikin ranka ko ba zaka iya furtawa ba." Bakinsa ne yake karkarwa yana son ya yi magana.


Ta ce "Ka yi shiru, kar ka yi magana" Ya yi wani yinΖ™uri ya fizgota jikinsa da Ζ™arfi.


Ayshercool 

08081012143


84

LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAN KI KARANTA. VIA 0069685771.AISHA ADAM STANBIC 

08081012143



Gaba Ι—aya suka yi cirko-cirko suna kallon ikon Allah. Tamkar matafiyin da ya shafe tsawon lokaci yana tafiya a sahara ba tare da ci ko sha ba, haka cacumar Nana da wani irin gigitaccen Ζ™arfi. Haka nan Nana ta ji jikinta babu Ζ™wari sosai.

"Habu ku bamu guri" Nana ta furta cikin Ζ™arfin hali tana Ζ™oΖ™arin riΖ™e hannunsa.


Mahmoudu ya ce "Amma kar ya shaΖ™e ki fa, ko ya yi miki illa"


Ta ce "Ba zai yi mini ba, zai dawo daidai in sha Allah, idan ma ya shaΖ™enin zai dawo daidai in sha Allah, amma ku bani guri" Tamkar zai shige cikinta haka yake Ζ™oΖ™arin rungume ta.


Gaba Ι—aya Sultan ya ruΙ—e, Mahmoudu ya ce "Ranka ya daΙ—e, ta ce mu basu guri"


Sardauna ya ce "Tayaya za mu tafi mu bar su, idan ta cutar da shi fa?"


Mahmoudu ya ce "Ba za ta iya cutar da shi ba. Abin tsoron ma kar ya cutar da ita shi" Haka suka fita suka bar shi da Nana.

Su na fita Nana ta sassauta murya ta ce "Sayyid, ka nutsu ka yi addu'a, kar ka yi ihu, ka yi addu'a ka ji" Sai dai sam yanayinsa bai nuna yana cikin hayyacinsa ba.


Ta saka hannunta ta zuge rigarta ta cikin hijjabinta. Sai dai tana yi tana kokawa da shi. A hankali ta ba shi damar Ζ™anΖ™ame ta kamar yadda yake Ζ™oΖ™arin yi. Wani irin nishi ya din ga saukewa mai sauti, jin sanyin jikin Nana. Sai dai sanyin bai kai wanda ya saba ji a jikinta ba.

A hankali ya yi lamo a jikinta, da fari Nana ta fara Ζ™oΖ™arin karanta masa Alqur'ani, sai dai ta kasa jurewa ta fashe da kuka. Saboda wani irin gigitaccen zafi ne yake ratsa ta daga jikinsa kamar an kunna musu wuta. Ga shi yadda ya danne ta ba za ta iya matsawa ba, balle ta samu afuwa.

"Ya hayyu ya Ζ™ayyum Allah ka kawo mana Ι—auki" Ta furta a lokacin da take jin yana Ζ™ara matseta tamkar zai karya Ζ™asusuwanta.

Sun Ι—auki lokaci a haka, kafin ta ji jikinsa ya saki, ya sassauta riΖ™on da ya yi mata. Ta ture shi da kyar ta Ι—aukko pillow ta tayar masa da kansa da shi. Sai dai idanunsa a lumshe kamar mai bacci, saΙ“anin da da idanun a buΙ—e tar sai dai babu Ζ™wayar idon sai farar.

Ta koma gefe ta jingina da gadon da yake Ι—akin, ko rigarta ba ta iya gyarawa ba, ta gyara hijjabinta ta jingina ta lumshe idanunta.

Hawaye ne suka fara bin gefen idonta, wani irin azababben ciwo jikinta yake yi mata, kamar an yi mata dukan tsiya da kulki. Ga raΙ—aΙ—in da take ji a kan fatarta.

A tsorace take waige-waige, ganin bugiren da Ƙaisar yake kwnaciya babu kowa. Ta duba gurin zamansa nan ma baya nan. Ta fita da sauri zuwa Ι—akin magungunansa, nan ma baya nan ga inda Giyaz ya yi Ι“arna ba a gyara ba, tabbacin bai da lafiya bai gyara ba. Ta din ga shiga tana fita a cikin Libraryn tana kiran sunansa amma ta ji shiru.

Wata siririyar hanya ta bi, da haske ya ratso gurin. Ta bi hanyar sannu a hankali tana addu'a a cikin zuciyarta, da fatan Allah ya sanya ba wani abin ne ya samu Ƙaisar Ι—in ba.


Bayan Library Ι—in ta Ι“ulla, ta hango shi a cikin tafkin da yake gurin a kwance, ya lumshe idonsa. Da sauri Nana ta Ζ™arasa tana faΙ—in "Ƙaisar, wannan ai sai ka tsorata ni, meyasa ka dawo nan ka kwanta, jikin ne dai?"

Ya buΙ—e idanunsa ya kalle ta ya ce "A'a hutawa kawai nake yi" Nana ta samu guri ta zauna a gefe ta ce "A'a ai na san jikin ne, ba zaka faΙ—a mini ba ne"


Ya ce "Ya jikin mijinki?"


Ta Ι—an yi shiru ta ce "Yana can Giyaz na ci gaba da azabtar da shi. Na rasa me ma zan yi gaba Ι—aya, ni kaina a jikina nake jin na Ζ™one"


Ƙaisar ya tashi zaune sosai a cikin ruwan ya ce "Ba Giyaz ba ne kawai, akwai tasirin asirin nan da ake yi masa da wuta. Sannan kuma ga Giyaz, shi Giyaz yana wasa da Ζ™waΖ™walwarsa ne, ya sanya ya tuna wannan ya manta wancan. Sai kuma ya kan shafe shi sai ya yi wannan suman. Amma wannan Ζ™onewar yana da alaΖ™a da wutar da ake hurawa wadda aka yi masa asirin da ita"


Cikin damuwa Nana ta ce "To dan Allah waye ya yi masa asirin, kuma a ina aka yi masa?"


Ya girgiza kai ya ce "Ki yi haΖ™uri, ba na shiga duk abin da bai shafe ni ba, saboda ni har kullum zaman lafiya nake fata. Sai dai na ga uwargijiyarki a dalilinki ta tuna gadon nasu gidan, da ke ki ka guji naki. Babu lallai sihiri ya yi tasiri mai Ζ™arfi a jikinki. Zai iya yiwuwa kina daf da inda aka yi masa sihirin. A wannan karon ne za ki yi faΙ—an Ζ™arshe, kar ki yi da wasa ki yi da gasken gaske. Ki buΙ—e idanunki, kibiyoyin da ki ka gani ana harbinsa da su mahaifinsa na karewa, yanzu ke za ki tare su.

Ya fito daga cikin ruwan jikinsa yana Ι—igar da ruwa, yana takawa da kyar, jikinsa duk wasu irin ramuka duk ya yi baΖ™i. Ya gyara zaman rigarsa ya rufe jikinsa sosai.


Ya sake duban Nana ya ce "Kar ki yadda ki komawa iyayenki gida, babu wani kyakykywan sakamako. Za ki sake komawa farko dan sunanki zai Ι“aci. Kar kuma ki yarda a raba ki da Ι—anki, kar ki aminta da duk wani murmushi da za ki gani a fuskokin mutane, kuma kar ki sakankance da Ζ™iyayyar da za ki gani. Kowanne na iya taimaka miki ki samu haske. 

Kai da fata ki dage, duk rintsi kar ki kuskura a ci moriyar ganga a yada ke a gefe, saboda kin gama yi musu amfani. Ki kula sosai da sosai. Allah ya ba da sa'a"


Cikin damuwa Matawalle ya ce "Shirun nan fa ya yi yawa. Anya ba za mu je mu sake dubawa ba"


Sardauna ya ce "Abin da nake tunani kenan, kar abin da ba a so ya faru. Kai Mahmoudu tashi ka wuce gaba ka duba, idan lafiya mu shigo. Ni na kasa samun nutsuwa tun da na ji tana wai mu bata guri."


Mahmoudu ne ya fara yin gaba, ya tura Ζ™ofar Ι—akin a hankali ya hango Nana a jingine shi kuma yana kwance a kusa da ita a kan fulo.


Ya Ζ™arasa da sauri yana kiran sunan Nana, amma ba ta motsa ba, sai hawaye da yake ta fita daga idanunta da ta lumshe.


Ƙarasowa suka yi su ma, suka rufu a kan Hammad. Sai suka ga jikinsa ya saki, idanunsa a rufe wannan jijiyoyin duk sun koma yadda suke.


Sardauna ya ce "Ya aka yi ya koma daidai? Me ta yi masa?"


Mahmoudu ya ce "Ban san me ta yi masa ba, Nana" Ya yi maganar yana kallonta.

Sai dai shiru ba ta amsa ba.


Sultan ya taΙ“a Hammd yana kiran sunansa, amma shi ma bai motsa ba.


Kawai su ka ga Nana ta fara jijjiga, duk su ka Ι—an ja da baya a tsorace su na kallonta. Mahmoudu ya rasa me zai yi. Sai bin su da kallo. A hankali kuma ta daina ta nemi guri ta kwanta a Ζ™asa.


Matawalle ya ce "Wai ni na kasa fahimtar wannan abin, me ya same su haka?"


Mahmoudu ya ce "Kamar akwai wani abu da bamu sani ba, ko za mu Ι—an Ζ™ara ba su lokaci?"


Matawalle ya ce "Ni kaina duk ya kulle, ban taΙ“a ganin abu irin haka ba ai"

Ƙarshe sai sake fita suka yi, suka bar Nana da Imam Hammad.


Can jimawa Nana ta farka, ta yi miΖ™a tana salati, ta kalli agogon bangon dakin ta ga lokacin sallar magariba ya yi. Ɗakin ba kowa daga ita sai Sayyid da yake bacci.

Ta yinΖ™ura da kyar ta tashi tsaye, ta fara dudduba Ι—akin, ta samo banΙ—ak a cikin sa. Ta yo alwala ta Ι—ebo ruwan a wata container ta zo ta ajiye ta tayar da salla.

Tana idarwa ta koma kansa, ta Ι—auki ruwan da ta Ι—ebo a container ta yi shiru tana kallon ruwan, a hankali suratul Mulk ta zo kanta. Ta karanta Bismillah ta tofa, ta karanta suratul Mulk har Ζ™arshe.

Wata addu'a ce da Malam Auwwal ya kan yi mata, musamman idan ba ta da lafiya ta faΙ—o mata, wanda tun da take bata taΙ“a kwatanta karanta ta ba, ba ma ta taΙ“a sanin ta iya ba sai yanzu da ta faΙ—o mata a ka.

Da sauri ta yi Bismillah shashshafa masa ruwan da ta yi tofin. Ta dafa kansa ta fara karanto addu'ar "Bismillahi arΖ™ik, min kulli shai'in yu'dika, wa min sharri kulli nafsin, au ainun hasid, Allahu yashfika, Bismillahi arΖ™ik."

Ta Ι—an koma gefe ta yi shiru tana kallonsa, tana fatan Ubangiji Allah ya ba shi lafiya. 

Ta tattaΙ“a shi tana kiran sunansa a hankali "Sayyid ka na ji na?" A hankali ya motsa ya buΙ—e idanunsa da suka yi jaa ya kalle ta. Ƙara ware idon ya yi sosai domin ya tabattar ita ce ko kuma dai mafarki yake yi. Ya yinΖ™ura gaba Ι—aya zai tashi, ya ji wani irin jiri ya kama shi, ga cikinsa a Ζ™ulle.


"Alhamdillah" Ta furta tare da faΙ—in "Sannu yi a hankali" Ta sassauΖ™e fululluka, ta jingina su a jikin gadon, sannan ta Ι—ago shi da kyar, ya yinΖ™ura ya zauna sosai ya jingina.

Sai dai tamkar zai cinye ta, haka yake bin ta da kallo. Ya motsa baki yana son ya yi magana amma bakin ya din ga rawa. Ta girgiza masa kai ta ce "Kar ka yi magana".

Ya yi shiru yana ci gaba da kallonta. Ta ce "Ka sanni ne?" Ya lumshe idanunsa ya buΙ—e.


Ta yinΖ™ura ta nufi wani jibgegen fridge da yake Ι—akin, ta je ta buΙ—e. Ta Ι—aukko ruwan roba ta zo ta zauna a kusa da shi. Ta cire masa rigarsa jikinsa. Ta Ζ™ara shashasha masa ruwan nan. Ta lura da yadda jikinsa yake rawa, yake kallon ruwan hannunta da har raΙ“a yayi saboda sanyi.

Ta kalli ruwan hannun nata ta kalle shi, kamar yadda ta gan shi a bacci, ya rame sosai fatarsa duk ta bushe saboda rashin ruwa. LeΙ“ensa har tsagewa yayi. Ikon Allah ne kawai ya raya shi zuwa wannan lokaci ba ci ba sha.

Ta ce "BuΙ—e bakinka" bakin yana rawa ya buΙ—e. Ta Ι—aga jarkar za ta zuba masa ruwan su Matawalle suka sake shigowa.


Sardauna ya ce "Ke, mene ne wannan za ki ba shi?"


Nana ta ce "Ruwa ne, a fridge Ι—in can na Ι—aukko"


Sultan kuwa sai da ya Ι—an rikice ya ce "Matawalle ya tashi"

Nana ta fara zuba masa ruwan a bakinsa, ya kai hannunsa biyu ya danΖ™e jarkar yana Ι—aΙ—Ι—akar ruwan. ƘoΖ™arin Ζ™wace ruwan Nana take yi, amma ya shanye. Yana shanyewa kuwa ya yi mata amai a jikinta har ta hancinsa haka ya din ga fitowa.


Matawalle ya ce "To ko Asibiti za a tafi a kai shi?"


Sultan ya ce "Ɗan jira mu gani"


Yana gama aman ya kifa a kafaΙ—ar Nana. A hankali ta ce "Ka gani, saboda kar ka yi amai ya sanya na so na baka a hankali. Sannu" Ya yi shiru yana ajiyar zuciya.

Ta kalli Mahmoudu ta ce "Taimaka ka kuma ba ni wani ruwan" Da sauri Mahmoudu ya sake Ι—aukko ruwa ya kawo mata.


Ta Ι—ago shi ta ce "Yanzu a hankali za ka sha, kar ka kuma yin aman, za din ga zuba maka kana haΙ—iya" Haka aka yi, ta din ga zuba masa a hankali yana sha, yana yi yana Ζ™oΖ™arin kai hannu ya riΖ™e robar, tana riΖ™e hannunsa tamkar Ζ™aramin yaro.

Nana tana son ta sake da shi, amma idonsu Sultan, ya sanya ta din ga komai a Ι—arare gudun kar ta yi wani abu su yi mata wata fassarar ko sharrin. Ya jingina yana ta haki saboda duk ya galabaita.


Mahmoudu ya ce "Kuma ke bai shaΖ™e kin ba da muka fita?"


Nana ta yi murmushi ta ce "Ramin kura ai sai 'ya'yanta Habu. Ka samo mana ko kayan marmari ne da shayin Buzaye ya sha. Ai za ka sha ko?" Ta yi maganar tana kallonsa.

Ya ci gaba da kallon Ζ™wayar idon Nana, maganganu ne fal a cikinsa, amma babu halin furta su"

Su na ta jera masa sannu, amma babu wadda ya amsa a ciki.


Matawalle ya ce "Bari na yi magana, a sanya hadimai su kawo kayan marmarin ya ci"


Nana ta ce "A'a ranka ya daΙ—e, a saka Mahmoudu ya kawo" Duk suka tsaya suna kallon Nana, amma aka rasa mai magana.


Nana ta nuna masa Sultan ta ce "Ka san wannan?" Ya jinjina mata kai alamar eh. Wannan fa? Ta nuna Mahmoudu nan ma ya jinjina kai.

Ta ce "Ni fa?" Sai ya yi shiru, har ta fara karaya, da tunanin ko memory Ι—in nasa ya sake Ζ™wacewa ya manta da ita.


Kawai hawaye ya fara zirarowa daga idanunsa.


AREWABOOKS 

Cikin damuwa Nana ta yi masa murmushi ta girgiza masa kai.


Sultan ya ce "Hammad, me yake damun ka ne? Akwai wata matsala ne?"


Ya yi shiru bai kula Sultan ba, Nana ta yinΖ™ura ta ce "Bari na je na wanke aman da ya yi"


Sardauna ya ce "Kar ki damu, za a kai ki inda za ki kwana, ba ma son kowa ya san kina nan. Za a baki wasu kayan ma sannan za a zo a gyara gurin. Kai kuma idan ka kawo Abincin sai a ba shi"


Nana ta jinjina kai, ta yinΖ™ura da niyyar ta tashi, amma ya damΖ™e hannunta cikin nasa gam.

Ta dube shi ta ce "Mene ne?" Ya tsare ta da idanu.


Ta ce "Kar ka damu, ba nisa zan yi ba, zan dawo in sha Allah" Ya damΖ™e hannunta ya Ζ™i saki, yana murzawa a hankali.


Matawalle ya ce "Ka na ji Imam, zamu je a kai ta masauki ne, inda za ta zauna ta huta, kaima ka ci abinci kafin a san abin yi, an tafi samo mai magani da zai duba ka."


Kamar sassaΖ™e, haka ya yi shiru ya riΖ™e hannun Nana.


Sardauna ya ce "Ina ga mu bar ta tare da shi kawai, zuwa da safe sai mu san abin yi"

Haka suka mimmiΖ™e, Ζ™iri-Ζ™iri suna ji suna gani, suka kama hanyar fita, su bar shi da Nana.


Nana ta ce "Habu, dan Allah Ι—an tsaya ka taimaka mini" Ya ce "To"

Bayan fitar su Nana ta ce "Dan Allah ka kawo mini kayana, sannan ka kawo mini kayansa guda biyu. Ka kawo mini Alkur'ani. Sai kuma Abincin nan dan Allah duk yadda za a yi kai tsaye daga hannunka zai zo, kar ya biyo ta hannun kowa. Sai kuma ina son ka kawo mini habbatussauda da tazargade, da ganyen magarya sai almiski ja"


Ya ce "In sha Allah ranki ya daΙ—e, yanzu kuwa. Sai dai su abin da ki ka lissafa Ι—in nan, sai dai na shigo da su a Ι“oye kar su ce wani abin za a yi masa"


Nana ta ce "Idan da matsala ba sai ka kawo su ba, kawo mini Abincin da kayan kawai, kar na saka ka a cikin matsala. Amma lokacin da hakan tana faruwa da shi da muna Nigeria, idan na yi masa amfani da su yana samun sauΖ™i sosai"


Mahmoudu ya ce "Kina nufin a Nigeria, yana irin haka?"


Nana ta jinjina kai ta ce "Har Ι“arin jikinsa sai da ya shanye, ka kawo mini Abincin da sauri na ba shi" 


Ya ce "To" Ya kalli Hammad ya ce "Sannu Imam, Ubangiji Allah ya sanya kaffara"


Sai da Mahmoudu ya fita sannan ta kalle shi ta ce "Cika ni na je na wanke jikina, ka ga ka yi mini amai a jiki" A hankali ya saki hannunta, amma har ta shiga banΙ—akin nan kallonta yake yi. Ta wawwanke jikinta ta fito ta Ζ™ara goge gurin da ya Ι“ata da aman.


Matawalle ya ce "Anya abin nan ba shiri ne yaran nan suka yi ba, saboda ya ci gaba da zama da yarinyar nan ba?"


Sardauna ya ce "Nima sai da na yi wannan tunanin"


Sultan ya ce "Bana tunanin shiri ne, babu yadda za a yi ya kwana takwas babu ci babu sha, a kwance a guri Ι—aya a ce shiri ne. Kai Matwalle ka manta abin da ya din ga yi, lokacin da aka gano shi a Nigeria aka dawo da shi. Ba magana ba cin abinci a sume kawai kuma aka rasa abin da yake damunsa sai da muka je faransa sannan ya dawo hayyacinsa?" Ya yi maganar yana Ζ™oΖ™arin hana kansa, yi musu cikakken bayanin labarin da Mahmoudu ya ba shi, mussaman cewa da aka yi idan aka dawo da shi Nijar, zai iya haukacewa ko ma ya rasa ransa gaba Ι—aya".


Sardauna ya jinjina kai ya ce "To ai ita kanta yarinyar abar tsoro ce, ba ku ga abin da take yi ba? Ni abubuwan sun Ι—aure mini kai sosai da sosai fa"


Sultan ya ce "Tabbas lamarin akwai Ι—aure kai, da ayar tambaya, dama Hammad ya gaya mini wani abu, amma dai bari mu ga abin da Allah zai yi, sannan mu jira zuwan mai maganin da aka tafi nema"


*****


Mama ce take kallon Jamila cike da baΖ™in ciki da takaici. Kamar ta danne ta ta yanka ta ce "Jamila, so ki ke sai duniya ta san halin da muke ciki? Kin zaΙ“i mutuncinmu ya zube a rasa wanda zai aure ki saboda wannan abin kunyar. Tun kafin ya riΖ™a mu je a cire shi kin Ζ™i, Jamila kin fi son asirinmu ya tonu ko?" Ta yi maganar muryarta na rawa.


Jamila ta girgiza kai hawaye na zuba daga idanunta ta ce "Mama ba zan iya zubar da cikin nan ba wallahi, ni tsoro nake ji, kuma kar zunubin ya yi mini yawa ba ki san adadin tarin zunuban da suke kaina ba. Ki bari na ji da wasu dan Allah, ki Ζ™yale ni kawai"


"Jamila ni ki ke cewa na Ζ™yale ki? Kin gwammaci ki durΖ™usa ki haife mana shege a gida, Duniya ta gani a shaida?"


Mama "Na duniya daga baya ne, Allah ya riga ya shaida ya ga komai, ni yanzu addu'ata Ubangiji Allah ya yafe mini. WataΖ™ila haifar Ι—an nan ne zai sanya na samu nutsuwa ni dai dan Allah ki Ζ™yale ni"


Cikin takaici ta ce "Jamila kin san haihuwa kuwa? Kin san azabar haihuwar Ι—an sunna balle shege, tsaf za ki mutuwa fa"


Jamila ta goge hawayenta ta ce "Idan na mutu gurin haihuwa na yi shahada, wataΖ™ila Allah ya yafe mini tarin kura-kuren da na aikata"


Cikin tsawa ta ce "Uban waye ya ce miki mai cikin shege za ta yi shahada"


Jamila ta ce "Mama ba ki san tarin zunuban da suke kaina ba, tuban da na yi sai Allah ya karΙ“i shahadata." Takaici ya sanya Mama fara rafka wa Jamila maficin hannunta ta ko ina. Jamila ta tashi da sauri, amma ta bi bayanta tana ci gaba da raΙ—a mata.

Baba ya kawo kai cikin Ι—aga murya ya ce "Rabi, wannan wane irin rashin imani ne haka? Yaya yarinya ba ta da cikakkiyar lafiya za ki biyo ta kina duka, me ta yi miki?" Mama ta tsaya tana mayar da numfashi cike da baΖ™in ciki da takaici.

Suwaiba kuwa da take gefe, ta din ga tuntsura wata irin dariya mara daΙ—in ji, wadda ke bayyanar da rashin cikakken hankali ga mai yin ta.

Mama ta rasa ihu za ta zunduma ta ji daΙ—i, ko kuma me yakamata yi ta ji sanyi. Hutu da fatan arzikin da take da shi a kan 'ya'yanta duk ba ta samu ba, ga mahaukaciya ga karuwa Nasiru shi ma ya fara 'yan Ι—auke-Ι—auke, dan sau biyu 'yan vigilant na kama shi, da laifin satar tukwanen mutane da kayan Ζ™arafa ya sayar da sunan gwangwan. Dan tun da Jamila ta cire tallafin da take ba su, ta daina zuwa gurin Hajiya Sa'a, suka koma ruwa.

Baba ya ci gaba da yi mata faΙ—a a kan dukan da ta yi wa Jamila, ba tare da ya tsaya ya ji cikakken abin da Jamilar ta yi ba. Ji ta yi tamkar ta kama shi shima ta jibge shi, ko ta huce. Dan duk wannan masifar shi ne sila da ya tsaya ya sauke nauyin da ya rataya a wuyansa da wataΖ™ila ba su shiga wannan halin ba.

Babban abin da ya Ζ™ara Ι“ata mata rai, shi ne rashin zuwan Hajiya Sa'a ta duba Jamila, duk da taga kwana biyu ba ta zuwa maimakon ta neme su ta ji ko lafiya amma ba ta yi hakan ba. Ga Maman Khairat ta tashi daga unguwar da ta so zuwa a rakata gidan Hajiya Sa'a ta ji ko wani laifin Jamila ta yi wa Hajiya Sa'a haka?.


Hajiya Sa'a kuwa tana can tana fama da kanta, dan tun mutuwar Abba ta shiga wani mawuyacin hali, duk lokacin da ta zauna babu abin da take yi sai tunanin ko yaya Abba ya ji da dodon Ζ™ungiya ya zuΖ™i jininsa har ya mutu? Ta daina bibiyar duk wani abu da ya shafi kungiyar. Kasuwancin ma ta tattara ta ajiye a gefe ta koma guri Ι—aya kawai. Daga kuka sai kwanciya da dana sani. Ga shi da ta fara tunanin wani irin mummunan ciwon kai yake yi mata dirar mikiya, har sai ta daina gani sosai. Wasu lokutan haka zata kulle kanta a Ι—aki ta wuni, sai dai mai aikinta ta yi ta sabgoginta itakaΙ—ai. Ta ce ko mutanenta sun zo, kar a bar kowa ya shiga inda take, kaΙ—aici kawai take so.


****


Mahmoudu ya dawo, ya kai wa Nana shayi da kayan marmarin da ta ce . Sai kuma kayansu da AlΖ™ur'ani. Ya haΙ—u da Sultan a hanyar da suke bi su shiga gurin. Domin wani sashi ne a can cikin sashensa da ba kowa ma ya san da shi ba. Hatta iyalansa sai da izninsa suke zuwa gurin. Wasu lokutan ya kan sanar da ya yi tafiya, ya tafi cikin gurin ya kulle kansa ya samu hutu da nutsuwa.

Mahmoudu ya Ζ™arasa gabansa cikin girmamawa. 


Ya ce "Abincin ka kawo musu?"


"Eh ranka ya daΙ—e"


Sultan ya numfasa ya ce "Shikenan, amma ina fatan babu wata matsala barinsa tare da yarinyar nan, duk da na fuskanci tana da hankali akwai abubuwan da take Ι“oyewa. Ni kaina ba komai nake son kowa ya sani ba"


"In sha Allah Sultan, kare martaba, mutunci da kuma sirrikan Imam Hammad abu ne da ya zama wajibi a gare mu. Kuma tabbaci nake da shi ba yaΖ™ini nake da shi, ba za ta taΙ“a aikata wani abu da zai cutar da shi ba"


Ya jinjina kai ya ce "Na ga alamun haka, duk da na ga wasu abubuwa na ban mamaki a tattare da ita. Dama Hammad ya gaya mini sai mun neme ta, amma ban Ι—auki zancen nasa da wani muhimmanci ba. Akwai wasu abubuwa da ya gaya mini da ban gama gane ma'anarsu ba, amma bari mu jira mu gani ya samu sauΖ™i"


Mahmoudu ya risuna ya ce "Godiya muke ranka ya daΙ—e, Allah ya Ζ™ara maka lafiya da tsawon kwana" Ya Ι—aga wa Mahmoudu hannu.


Nana na ganin Mahmoudu ta yi ajiyar zuciya, domin shi take ta jira ya kawo abin da za ta ba wa Hammad ya saka a cikinsa. Yana kwance a kan cinyarta tana shafa gashin kansa.


Ya ajijiye mata kayan, Nana ta ce "Sannu da Ζ™oΖ™ari, Ubangiji Allah ya biya ku da kai da mahaifiyarka, na fuskanci kirki da karamci a jininku yake, gado ka yi Nene akwai kirki"


Ya ce "Allah ya taimake ki, ai kin Ζ™wace mini ita" Nana ita abin dariya yake bata, idan ta ji su na girmamata.


Ta ce "Sayyid, ga abinci an kawo tashi ka ci" Mahmoudu ya taimaka mata, ta zaunar da shi. Ta zuba shayin a kofi, ta fara ba shi a hankali da cokali.

Duk da wata irin yunwa da yake ji, tamkar ya haΙ—a da Nanan ya cinye, amma haka ya daure ya din ga karΙ“a a hankali.


Ta ce wa Mahmoudu "Ka je ka samu ka huta, amma dan Allah ka zo da wuri, ka san ni da kai na saba, kuma kai kaΙ—ai nake jin zan iya sakin jiki da kai. Sannan dan Allah abincinsa kar a bari ya biyo ta hannun kowa, ta gurinka kawai"


Ya ce "In sha Allah, zan yi yadda ki ka ce, sai da safe"


Sosai ya din ga cin kayan marmarin nan, yana sake shan shayin girfae da Habu ya kawo. Sai da Nana ta lura jikinsa ya daina rawa. Ya Ι—an huta sannan ta tashi tsaye ta ce masa "Sayyid yinΖ™ura a hankali ka tashi mu gani" 


Ya dafa gadon, ya tashi a hankali amma ya ji kamar kayan cikinsa zai zubo. Ta riΖ™e hannunsa yana durΖ™ushe yana tafiya a hankali.


Ƙofar banΙ—akin suka je, ta tsaya ta kalle shi ta ce "Mun yi wanka a Nigeria, yau za mu yi a Agadez ko?"


Murmushi ya yi mata sai da haΖ™oransa suka bayyana. Suka shiga banΙ—akin. Sai dai wata irin kunyarsa da ba ta san daga ina ba, ta bujiro mata. Za ta iya cewa yau jiΖ™a-jiΖ™a kawai ta yi masa, saboda yadda ya Ζ™ara yi mata kwarjini take ganin kamar wani aka canza mata. Babban abin da ya Ζ™ara takura ta, shi ne kallon da yake ta bin ta da shi, kamar zai lashe ta. Da kanta ta yi masa brush, hakan ya din ga tuna mata da rayuwarsu ta Nigeria.

Ta saka ya yi alwala, suka dawo Ι—akin ta saka masa doguwar rigar jallabiya. Ta ce "To an ce kwananka takwas baka hayyacinka, yanzu zaka lissafa sallolin da suke kanka. Ka yi wanda zaka iya yanzu sauran sai ka ci gaba ko gobe in Allah ya kaimu ne"


Ya jinjina kai, ya kalli gabas daga zauna ya tayar da salla, saboda ba zai iya tsayuwa ba. Nana ta din ga tunani ko ta roΖ™i alfarmar su nuna mata Ι—anta ta gan shi, tun da nasu Ι—an ya farfaΙ—o, amma wata zuciyar ta hana ta hakan, duk da tarin kewar Muhsin da take yi. Ta shiga banΙ—akin ita ma, ta yi wanka ta gama ta sako hijjabinta ta fito.

Jakar kayanta ta buΙ—e, tana duddubawa, ta ga magungunan da Nene take bata na sha da wanka a ciki.

Kawai ta yi murmushi ta shafa mayukanta, ta duba kaya masu sauΖ™in nauyi dan ta saka, dan duk da ba shi da lafiya ba za ta kwana shimfiΙ—a Ι—aya da shi ba, da haryanzu ba ta san matsayinta ba, da matsayin kawo ta gurinsa ba, duk da da aka zo ita ta nema. Ga uwa uba rashin tabbacin da gaske tana da juna biyu ko kuwa?.


Ta sakankance da salla yake yi, saboda a bayansa take zaune tana Ζ™oΖ™arin canza kaya. Kawai ta ji ya faΙ—o jikinta, suka faΙ—i Ζ™asa a gurin, hasken wutar Ι—akin ya Ι—auke baki Ι—aya duhu ya mamaye Ι—akin.


Ayshercool 


85


LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAFIN KI KARANTA. VIA 0069685771

AISHA ADAM STANBIC BANK 

08081012143



Nana ta razana ta ce "Sayyid lafiya kuwa?" Ya rirriΖ™eta jikinsa na rawa.


Nana ta yi shiru cike da damuwa, ga shi yanzu ta fara wahala da riΖ™on da yake yi mata, dan ya ninka wanda yake yi mata su na Nigeria. Haka ta haΖ™ura Ζ™yale shi.

Can bayan wani lokaci, hasken Ι—akin ya dawo, a lokacin ya samu bacci, Nana ta yi shiru tana tunani daban-daban a kansa. Tabba! Tana da tarin tambayoyi da take buΖ™atar samun amsarsu, daga gare shi, dan akwai tarin abubuwan da suke faruwa, da suke Ι—aure mata kai.


Ta ture shi da kyar, ta tashi ta saka kayanta, ta kwanta a bayansa, tana jin yadda jikinta ya Ζ™ara tsami da ciwo.

Sai dai bayan bacci ya Ι—auke ta, ta din ga munanan mafarkai marasa kyau da ban tsoro a cikin baccin. Abubuwan da ta din ga gani a gidan, sun tsorata ta. Har da yaΖ™e-yaΖ™en da aka din ga yi, kafin kafuwar masarautar, da irin azabar da bayi suka sha haka ta din ga gani. Ban da miyagun Aljanu masu Ι—auke da siffofi daban-daban na ban tsoro a cikin baccin.

Juyi ta din ga yi tana haΙ—a wani irin gumi, tana sauke numfashi saboda tsoro. Ga shi a baccin da fari a gefe take tana kallon abin da yake faruwa, kafin daga bisani ta ganta tsamo-tsamo a cikin rikicin da ake yi, daga bisani ma miyagun abubuwan suka din ga nufo ta. Cike da tashin hankali ta farka tana waige-waige. Amma ta yi ido huΙ—u da Hammad a zaune yana kallon ta, da alama ma sallolinsa ya yi.

Mamaki ya kama ta, yaushe ya tashi har ya yi alawala ya zo yana rama sallolin. "Sannu ya jikin naka?" Ya jinjina kai yana kallonta.


Ta sake cewa "Ka gama rama sallolin ne?"


Ya girgiza mata kai, ta ce "To shikenan, bari na Ζ™ara maka kayan marmarin, zuwa da safe sai ka fara gwada cin abinci" ya jinjina kai ta din ga Ι“are masa ayaba yana ci, tana ba shi ruwa yana sha. Sai da ya yi mata nuni da ya Ζ™oshi. 

Ta tashi ta tafi banΙ—aki domin ta yi alwala ta ji mararta ta Ζ™ulle. Ta tsuguna ta yi fitsari kawai ta ga fitsarin haΙ—e da jini. Ta shi ta yi cikin tsoro, ta gyara jikinta sai dai ta kasa gane jinin Al'ada ne, ko kuma na Ι“ari? Tun da dai ya ce mata tana da ciki. Ta kintsa jikinta ta fito, tun da ta fito idonsa a kanta, ta Ζ™araso tana cewa "Sayyid, ka ce ina da ciki, yanzu kuma na ga jini ya zo mini, period ne ko Ι“ari?" Ta yi maganar tana tsare shi da ido, cike da son tabbatar da abin da take zargi.


Kawai ta ga yana murmushi. Cikin rashin fahimta ta ce "To ka yi mini bayani ko da hannu ne, zan gane. Dan Allah cikin ne da ni da gaske Ι“ari na yi? Ko kuma ba ni da komai dama?"

Ya ci gaba da murmushi yana Ζ™anΖ™ance idanunsa yana kallonta, kamar ba mara lafiya ba.

Ji suka yi ana bubbuga Ζ™ofa, ya tsuke fuska kamar ba shi ne yake murmushi ba. Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci. Mamaki ya kama Nana yadda ya iya zuwa da duku-dukun nan.


Ya Ζ™araso suka gaisa da Nana, ya kalli Hammad ya ce "Wai ya na ga daga jiya zuwa yau kamar ba kai ba. Ko dama rashin lafiyar ta ta ce?"

Hammad ya Ι—auki fulon hannunsa zai kai masa duka, amma ya kauce yana dariya. Sai mamaki ya kama Nana, dama yana wasa da Mahmoudu haka? Kodayake ko da suna Nigeria, su na hira amma ba sosai ba, a nan ma tun da ta fara ganinsu tare, duk maganar da zai yi masa cikin girmamawa yake yi masa. Amma kuma yanzu ta ga yana zolayarsa.


Mahmoudu ya ce "Gimbiya ya jikin nasa, duk da daga haka ma Alhamdillah na ga alamun sauΖ™i a tattare da shi"


Nana ta Ι—an Ι“ata fuska ta ce "Dan Allah ka daina ce mini gimbiyar nan."


"Wallahi dole a ce da mijin Iya Baba Nana, babu wadda ta dace da wannan sunan a kaf Agadez idan ba ke ba. Ya jikin naka?" Ya Ζ™arasa maganar yana kallon Imam Hammad.


A sanyaye Nana ta ce "Ai maganar ba ta dawo ba tukuna sai a hankali"


"Ikon Allah, kenan dai da gaske bayan tafiyata ya ci gaba da irin wannan ciwon, ni fa na zata tun da muka tafi bai sake yi ba. Amma Nana yaya abubuwa suka kasance ne bayan tafiyata, na san akwai tarin abubuwa marasa daΙ—i. Na san zuciyar musulunci ce ta sanya ki ke saurarenmu a yanzu ma, amma ki yi haΖ™uri. Har Nigeria aka je aka kama mu tare da su Sule. Sannan aka zo aka matsa ni da azabtarwa sai da na faΙ—i inda yake. Aka je gidan da ku ke gadi, ba kwa nan. Na raka su gidanku ina tsoron ya san yana da mata saboda gudun kar a cutar da ke. Ƙaninki ne ya gaya mini inda ku ke. Lokacin da aka je da ni shikaΙ—ai muka tarar a gidan ba kya nan. Wallahi har aka Ι—aukko shi sunanki kawai yake kira, yana ba zai tafi ya bar ki ba. Babu halin na faΙ—i cewa ya yi aure saboda na san hukuncin hakan a masarautar nan. Ga shi aka rufe ni a kurkuku da zargin ni ne na sace shi na kai shi Nigeria saboda ra'ayin kaina. Amma duk abubuwan da suka faru Nana ba su faru dan ni da Imam mu zalunce ki ba, dan Allah ki yi haΖ™uri"

Tamkar ya sosowa Nana abin da yake yi mata Ζ™aiΖ™ayi, da dannewa kawai take yi, ta fara hawaye.

Ba Mahmoudu da ya Ι—aukko maganar ba, shi kansa Imam Hammad sai ya rikice gaba Ι—aya.


Mahmoudu ya ce "Dan girman Allah ki yi haΖ™uri, da na san maganar nan, za ta Ι“ata miki rai da ban Ι—aukko ta ba, ki yi haΖ™uri"

Ta jinjina kai kawai, dan ita kanta ba ta san cikakken dalilin kukan ba, ta san dai tana buΖ™atar yin kukan ne ta samu afuwa a zuciyarta.


Yau Sultan ne kaΙ—ai ya zo duba Imam, sai dai ya ji daΙ—in yadda ya gan shi. Ya tarar har ya ci abinci ya yi wanka ya canza kaya, sai dai ba magana.

Ya kalli Nana, Ζ™asan zuciyarsa yana yaba wa Ζ™oΖ™arinta da Ζ™arfin halinta. Ya ce "Kuma zai yi magana, na ga haryanzu bai ce komai ba"


Nana ta sunkuyar da kai ta ce "Zai yi in sha Allah, sai dai wasu lokutan ya kan jima bai ce komai ba, kafin maganar ta dawo"


Sultan ya jinjina kai cike da gamsuwa, ya ce "Muna godiya sosai da sosai. Ko akwai wani abu da ku ke buΖ™ata?" Nana ta girgiza kai alamar a'a.


"To shikenan, idan akwai wani abu, ki sanar da Mahmoudu ya gaya mini. An je za a taho da mai magani ya zo ya duba shi, idan kuma abin ba zai yiwu ba zamu kai shi Asibiti" Nana ta jinjina masa kai kawai.


Inda Allah ya taimaki Nana, akwai pad a cikin kayanta, sai dai yanayin gurin babu gurin discarding pad Ι—in. Cikin ikon Allah kuma ba ta zubar da jinin sosai.


****

Sultan na zaune a sashensa, ya gama ganin wasu baΖ™insa, aka yi wa Asal iso, ta shiga gurinsa.

Bayan sun gaisa ta ce "Abie dama na zo ne ina son duba jikin Imam"


Sultan ya gyara zamansa ya ce "Yarinyar kirki, Imam Hammad yana cikin yanayin da ba zai so a cika kawo masa ziyara ba. Dan haka mu na son ya samu hutu ne, kafin lokacin da za a samo mai maganin da zai duba shi"


Cikin damuwa Asal ta ce "Ko sau Ι—aya ne Sultan, jiya kwana na yi ina mafarkinsa, ina cikin damuwa ne"


Ya ce "Na ga alamun hakan a tattare da ke, amma ki yi haΖ™uri ba za ki samu ganinsa ba, zuwa lokacin da zai samu afuwa sai ki gan shi har ma ku koma gida ma"


Ba dan Asal ta so ba, haka ta haΖ™ura ta tashi ta tafi. Tana kan hanya kiran Tafawa ya shigo wayarta.


"Yaya ake ciki?" Ya tambayeta ba tare da amsa gaisuwar da ta yi masa ba.


Ta ce "Yau ba a bani damar ganinsa ba, Sultan ya ce mini jikinsa ya yi zafi, dan haka ba zan samu ganinsa ba. Dole na jira zuwa lokacin da za a samo mai magani ya duba shi"


"Ya dai tabatta haukan yake yi ko? Lokaci ya yi da zan bankaΙ—a abin nan, yadda Sultan zai kunyata daga shi har Ι—an nasa"


Asal ta ce "Dan Allah ka yi haΖ™uri, ba hauka yake yi ba, rashin lafiya...


"Ke yi mini shiru, abin da na yanke dole haka za a yi, kar ki sake ki sake yi mini musu" Ya katse ta yana yi mata tsawa da dole ta sanya ta yin shiru.


*****

Alhaji Fatuhu ne ya kira wani abokinsa, ya ce ya zo ya kai shi gidan Yayarsa Hajiya Sa'a a motarsa, saboda yadda baya samun ta kwana biyu a waya.


Ko da yaje gidan, mai aikinta ta sanar da shi cewa ta ce ko waye ya zo, kar a sake a dame ta.


Ya kalli mai aikin ya ce "Ko wannan dokar za ta yi aiki a kan kowa, ba za ta yi a kaina ba, dan haka yi mini magana da ita"


Mai aikin ta shiga ta fito, ta ce "Na yi mata magana ba ta kula ni ba"


Ba shi da zaΙ“in da ya wuce ya shiga Ι—akin nata da kansa. Ya tarar da ita a zaune, daga mutuwar Abba zuwa yanzu ta yi wani irin tsufa, jikinta duk ya saki. Fuskarta duk ta yi wani iri kamar ba ita ba.


A hankali ya taka da sandarsa, sai ta Ζ™ura masa ido tama fara tunanin a ina ma ta san shi? Gaba Ι—aya sai kanta ya toshe ta kasa tuna waye shi.


Sai da ya ce "Yaya Sa'a, lafiya kuwa?" Yana yin maganar, sai kuma ta tuna shi. Ta yi zuru tana tunanin ya aka yi ya samu lafiya haka har yake iya takawa?


"Yaya Sa'a me yake damunki?" Ya yi maganar cikin damuwar halin da ya tarar da ita. Kawai ta fashe da kuka.


Cikin damuwa ya ce "Haba ke kuwa, kamar ba musulma ba, yanzu da ke Allah ya jarabta da halin da nake ciki yaya za ki yi? Dan Allah ki yi haΖ™uri mu ci gaba da yi wa Abba addu'a, amma wannan hanyar da ki ka Ι—aukko, ba mai Ι“ullewa ba ce ba" Ya yi ta rarrashinta da lafuzzan Ζ™warin gwiwa. Ya sanya mai aikinta ta kawo Abinci, ya tabbatar ta ci sannan ya yi mata sallama ya tafi. Sai dai bayan tafiyarsa sai ta hau tunanin abin da ya faru gaske ne ya faru, ko kuwa dai mafarki ne. Gaba Ι—aya. Haka ta zauna tana ta lissafin yanayin.


*****


Bayan majalisar Sultan ta cika, domin ci gaba da gudanar da sha'anin mulki na Agadez. Akwai takardu da a kan turo domin gabatar da su a tattauna.


Mai karanto takardun ya warwareta, ya zuba wa takardar ido sannan ya numfasa ya ce "Zuwa ga Sultan da 'yan Majalisar sa baki Ι—aya. Sanin duk wanda ya kwana ya tashi a Agadez ne, babu wani abu da muke martabawa, bayan addininmu kamar al'adarmu. Mu na kira ga Sultan da 'yan majalissar sa, su gaggauta duba ga al'amarin Imam Hammad. Babu yadda za a yi ya ci gaba da jagorantar majalissar Imam, ba tare da zoben tambari ba, wanda kawo yanzu babu wani cikakken bayani a kan inda zoben nasa yake. Sannan ya yi iΖ™irarin yana da Ι—a, wanda haryanzu ba mu ji matsayar binciken da aka ce za a gudanar ba. A dan haka muke kira ga sauran 'yan uwanmu na majalissar Sultan, a gaggauta sanar da mutane sakamakon binciken da aka gudanar, sannan Imam Hammad ya fito gaban majalisar sarki, ya kare kansa, ko kuma ya sauka daga kan muΖ™aminsa na shugaban majalisar Imam, har zuwa lokacin da sakamakon binciken iΖ™irarin da ya yi na yana da Ι—a zai fito. Idan kuma shaci faΙ—i ne abin da ya faΙ—a ta tabatta yana da matsalar Ζ™waΖ™walwa, kamar yadda jita-jita ta yi yawa.


86

A SAUKE HAKKI, A BIYA KUƊIN KARATU 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 08081012143

Gaba Ι—aya tsit majalissar ta yi, aka rasa wanda zai sake cewa wani abu. Wani abu mai Ι—aci ya tsirga wa Sultan a zuciyarsa, yana takaicin kasancewar Tafawa Ι—an uwansa, yadda yake nuna son ganin bayan jininsa wato Hammad duk saboda mulki. Ya san ko ba a gaya masa ba, da saninsa aka rubuta wannan takardar aka kawo. Surutu 'yan majalissar suka fara yi Ζ™asa-Ζ™asa. Sardauna ya numfasa ya yi gyaran murya, duk aka yi shiru Sannan ya ce "Ina ga wannan maganar mun riga mun yi ta a baya. Ban ga amfanin sake dawo da ita ba, mu na nan ana kan bincike a kan al'amuran kuma za a zo da sakamakon binciken, sake dawo da maganar ba abu ne da zai taimake mu ba, duba da yadda muke da tarin abubu a gabamu, da yakamata a ce an mayar da hankali a kai"

Ɗaya daga cikin mutanen majalisar ya ce "A'a Sardauna, ba na tunanin wannan ba maganar da za a tattauna ba ce ba. Kar ka manta goben Agadez ta ta'alaΖ™Ζ™a da waΙ—annan Imam da aka naΙ—a, su ma suke jagorantar wasu al'amuran na sha'anin sarauta, muddin aka ce da tangarΙ—a kuma ba a Ι—auki wani mataki ba, to yana nufin goben Ζ™asar nan yana cikin hakin da ba a sani ba"


Matawalle ya ce "Turaki ai dama sanin gobe sai Allah. Mu muna bulayinmu ne kawai. Amma kamar yadda mai girma Sardauna ya ce, a jira sakamakon binciken ya fito tukuna. Sannan wani batun taΙ“in hankali da ake danganta Imam Hammad da shi, batu ne mara tushe balle makama, sannan duk wanda muka samu da yaΙ—a wannan zancen, za a Ι—auki Ζ™waΖ™Ζ™waran mataki a kansa."

Haka aka so tayar da hatsaniya, sai da Sultan ya tsawatar, haka aka watse daga zaman babu wata Ζ™waΖ™wΖ™warar magana. Sultan ya san tabbas tun da  Tafawa ya samu magoya baya a Majalisa, al'amura za su sake dagulewa ne, kuma za su ci gaba da bibiya su ji Ζ™wal uwar daka.


*****


Shukura ce a kwance a Ζ™asa, sai burgima take yi, wani irin matsanancin ciwo yana ratsa ta. Sai jujjuya kanta take yi a galabaice. Kamar kullum mai ba ta abinci ya buΙ—e Ζ™ofar ya ziro abincin ya ajiye mata ya tafi. Sai dai a duk lokacin da aka kawo mata abincin, idan aka rufe Ι—akin duhu ne yake gauraye ko ina, amma sai ga yau da sauran haske. Ta Ι—aga kanta a mugun galabaice ta kalli Ζ™ofar ta ga kamar Ζ™ofar ce ba ta rufu ba. Ta lumshe idanunta cike da azabar ciwo, wata zuciyar na azalzalarta ta je ta buΙ—e Ζ™ofar ko a buΙ—e take, wata zuciyar kuma ta ce mata wahalar ciwo ne kawai amma Ζ™ofar a rufe take. Ta ji ciwon na Ζ™ara tsananta, yayin da wani abu mai Ι—umi da ba za ta iya tantance ko na mene ne ba, yake bin Ζ™afarta.

Ta din ga jan jikinta a hankali, ta lalubi bango ta dafa, a durΖ™ushe ta Ζ™arasa gaban Ζ™ofar ta saka hannu ta ja, kawai ta ga Ζ™ofar ta buΙ—e. Ta zura kanta ta lelleΖ™a ta ga babu kowa a harabar gurin, daji ne sosai aka yi Ι—akin a cikinsa.

Tana faΙ—in "La'ila ha illa Anta Subhanaka Inni Kuntu mina Zalumin" Ta ci gaba da jan Ζ™afafuwanta tana takawa a hankali.

Ko da ta duba jikinta sai ta ga alamun faya ce ta fashe, ga ruwanan mai haΙ—e da jini a jikin Ζ™afafuwanta da rigarta. Ba ta damu da yadda take gani dishi-dishi ba, saboda azabar galabaitar da ta yi, da kuma haske da ya cika mata ido, kawai ta saΙ“i hanyar da ba ta san ina ne ba, ta hau tafiya. Duk da duk taku ji take yi tamkar Ι—an cikinta zai faΙ—o saboda nauyin cikin da azabar ciwo. Tafe take tana addu'a Allah ya kuΙ“utar da ita.


Alhaji Fatuhu kuwa bayan komawarsa gida su na hira da Fadila ya ce "Fadila yakamata ku je ku duba Yaya Sa'a, saboda tana jin jiki nesa ba kusa ba, duk ta rame ta fita daga hayyacinta. Ta bani tausayi sosai da sosai haryanzu tana jin raΙ—aΙ—in mutuwar nan"


Fadila ta ce "Allah sarki, har na tuna lokacin da na rasa Muhsin Ι—ina, da ta ce ba ni da tawakalli kamar a kaina a ka fara haihuwa, Allah sarki yanzu ta ji abin da na ji"


Ya tsuke fuska ya ce "A taΖ™aice dai, gaya mini magana ki ke yi"


Ta girgiza kai ta ce "Wace ni? Ai ban isa ba, kawai dai na tuna abin ne, kuma ya daΙ—e yana yi mini zafi"


"To koma dai mene ne yanzu ya wuce, zan gaya wa Suwaiba, yakamata ku shirya ku je ku duba ta, a yi mata sannu, idan babu hali ma ina ga gara ta dawo gidan nan da zama, wataΖ™ila kai komonmu zai rage mata damuwa da kaΙ—aici"

Cikin sanyin ta ce "Ka manta ne? Ka manta mu ma a under notice muke, daga yanzu ko wani lokaci an ce mu fita mu bar gidan nan?"


Ya yi shiru ya tafi zancen zuci. Ta ce "Dan Allah kar ka Ι—aga hankalinka, mun samu Allah ya sanya ka farfaΙ—o da kyar. Ni da Maman su Janna za ta yarda da Ι—an abin hannuna da nata, mu samu ko karamin gida ne a saya, ni ba na son hayar nan ko Ι—aki uku ne mu koma"


Ya waro ido ya ce "Ɗaki kuma? Ina Ι—aki uku zai ishe mu rayuwa? Ko sashenki Ι—akuna huΙ—u ne da falo biyu, ya yi mana kaΙ—an"


Fadila ta ce "Daddy ka manta wacece Fadilan taka ne? Sai dai ku ya yi muku wahalar rayuwa ai ni na riga na saba, gidanmu ma na da daka auro ni ai Ι—aki biyu ne ni da Umma"


Ya ce "Ki daina tuna abin da ya wuce mana, ni ba ga shi kin zamo mana alkhairi ba. Da na tsaya duba wani shrime da Ζ™yale-Ζ™yale da daga ke har Suwaiba ba na tunanin za ku kasance da ni, duk da halin da muka tsinci kanmu. Ina Ζ™ara yi muku godiya sosai da sosai"


Fadila ta ce "Haba Daddy, ka cancanci fiye da haka daga gare mu, lokacin da ka ke da wadata ba mu ba, na kusa da mu ma ka yi musu, ka gatantamu ka kula da mu, sai Allah ya kawo mana jarrabawa kuma mu juya maka baya, da Allah bai barmu ba kuwa"


Ya ce "Ke dai a yi sha'ani masoyiyya, idan Allah yana Ζ™aunar bawa, idan ya jarrabe shi ta nan, sai ya sassauta masa ta can, da yawa idan larura ta same su, iyalan nasu barin su suke yi. Kin san wani abu kuwa?"

Ta ce "A'a sai ka faΙ—a Angona" Ya tuntsure da dariya ya ce "Ango ko?" Ta Ι—aga masa gira tana murmushi. Ya Ι—an ja kumatunta yana murmushi. Ya ce "Wannan rahar ma da nake yi da ke, ba tare da kin sauya mini ba saboda ba ni da lafiya, kuma ba ni da abin hannun yanzu ba, wallahi ba Ζ™aramin daΙ—i nake ji ba. HaΖ™iΖ™a larurar nan ta Ζ™ara mini tsoron Allah da imani, ya Ζ™ara kusantar da ni da Ubangijina, a duk lokacin da na motsa ambaton Allah kawai nake yi, gani nake rayuwata ce ta zo Ζ™arshe. SaΙ“anin lokacin da nake da dukiya da lafiya, ina ambaton Allah amma ba can sosai ba, ba kamar yadda na Ζ™ara samun kusanci da Ubangiji ba lokacin da na rasa komai. Kuma a jikina nake jin wani tagomashin alkhairi yana kusanto mu in sha Allah"


Ta ce "Haka ake so Daddy, ina fatan kuma ka canza tunaninka a kan magungunan gargajiya da na addini yanzu"


Ya yi dariya ya ce "Na canza tuni, ke dai madalla da ke matar aljanna" Suka ci gaba da hira cike da nishaΙ—i.


*****


Kwanakin Nana uku tare da Hammad, jikinsa ya yi Ζ™alau abin sa, sai dai magana ce babu. Nana ta yi iya Ζ™oΖ™arinta gurin tana kauce wa duk wani abu da zai sanya faruwar wata mu'amala tsakaninsu. A Ζ™asa suke kwana, ba ta taΙ“a kwanciya sai ya yi bacci, sai dai wasu lokutan ta ji ya Ζ™anΖ™ameta idan ciwon ya motsa

Sai dai tun da ya warware sosai, take ganin kamar ya canza mata, wani irin kwarjini yake yi mata yanzu, mussaman idan ya saka ta a gaba da kallo duk sai ta rikice. Ta kasa gane take-taken sa. Sai dai ta riΖ™i karatun Alkur'ani sosai da sosai. Sai dai tun wannan ganin na Ζ™arshe da ta yi wa Ƙaisar, ba ta sake ganinsa ba, ko a farke ko a cikin bacci ba. Duk ta damu shi ma ta na son sanin halin da yake ciki. Ga shi gaba Ι—aya ta rikice, a kwana Ι—ayan da ta ga jinin nan, ba ta iya tantance wane jinin ta yi ba. Ɓari ko na haila.

Tuni aka Ζ™ara Ζ™awata Ι—akin da kayan alatu, da kayan wanka da shafe-shafe na Imam Hammad, da duk wani abu da za su buΖ™ata.

Yana banΙ—aki yana wanka, ta gama cika cikinta da kayan marmari, dan ba ta fiye cin abincin da Mahmoudu yake kawowa ba, fruit take samu ta ci ta Ζ™oshi ta ci nama. Sai da ta fara tsorata kanta da tunanin anya ba cikin ne da gaske ba. Ta yi zurfi sosai da sosai a cikin tunani. Razana ta yi jin yadda ba ta ji alamun fitowarsa daga banΙ—akin ba, sai ji ta yi ya zagaya hannayensa a cikinta. Duk da Ι—akin Ζ™ato ne sosai da sosai amma duk Ζ™anΖ™antar motsi tana iya jinsa, amma sam ba ta ji motsinsa ba. 

Tsigar jikinta ta hau tashi, ta ji jikinta ya fara tsuma, tana neman ta rasa nutsuwarta.

Ya Ι—an yi murmushi ya cika ta, ya nuna mata gadon da yake Ι—akin, alamar ta hau ta kwanta. Amma ta yi mursisi ta Ζ™ame a gurin. Ya kama hannunta zai ja ta, amma ta Ζ™wace hannunta ta ja ta tsaya. Sai ya rabu da ita, yaje ya haye gadon ya kwanta.

Ta tsaya a gurin tana rarraba ido, sai da ta ga ya jima da hawa gadon, ta lallaΙ“a ta Ι—auki fulo ta ajiye a Ζ™asa ta kwanta.

Kwanciyarta ke da wuya, ta fara jin sukuwar wasu halittu da ba ta san ko na mene ne ba, a cikin Ι—akin. Hayaniyar  halittum ya ci gaba da yin amsa kuwwa a cikin kunnuwanta tamkar a filin yaΖ™i. Wani mutum ta gani ya shigo ta wata Ζ™ofa, ba a iya tantance jinsinsa, ya rufe ko ina na jikinsa, yana shigowa ya nufi gadon da Sayyid yake kwance, ya ajiye wannan takardar, ya nufi wata Ζ™ofa. Da azama Nana ta bi bayansa duk da yadda yake wani irin gudu kamar iska na kaΙ—a shi. Sai dai wannan sautin Ζ™arar ya hana ta ci gaba da bin sa.

Rungume ta ya yi a jikinsa, jikinta na ta rawa, duk ta toshe kunnenta da hannayenta biyu. Saboda yadda take jin hayaniyar kamar zata tarwatsa mata kai. Ta Ι—aga kai ta kalli Sayyid, ta kalli Ζ™ofar ta ce "Akwai wani abu a nan?" Ya Ι—an yi shiru, sai kuma ya yi gaba, ya buΙ—e Ζ™ofar. Ya riΖ™o hannunta suka ratsa hanyar da take baΖ™iΖ™irin mai Ι—auke da duhu, kai ba ka ce a cikin wannan katafaren Ι—akin mai Ι—auke da hasken fitilu hanyar take ba. Babu tsammanni ta ga sun Ι“ullo wani guri kamar corridor. 

ShimfaΙ—aΙ—Ι—en yashin sahara ne a gurin, gurin ya bayar da wani ni'imtaccen sanyi, ga tsilla-tsillar bishiyu da suke a bushe a gurin hasken farin wata ya haske saharar. Ta waiwaya Ι—aya gefen, ta hango wani irin gini, mai kama da tsaunin dutse, hasken wuta na ci na tashi ta wata kafa mai kama da taga a jikin ginin Dutsen.

Bakinta na rawa ta kalle shi ta ce "Sayyid na san gurin nan, tun kafin na sanka nake mafarkin saharar nan, har na zo na sanka, ina mafarkinka a cikin saharar nan. Kuma a nan nake yawan ganin ka tare da Giyaz. A waccan bishiyar ku ke zama da su Habu ku sha shayi da wasu mutane ma da ban san su ba. 

Ina ne nan, kuma meyasa abubuwan da nake gani a bacci suke dawo mini a zahiri, haryanzu ina da ayoyin tambaya da dama a kanka" 


"Yanzu kin yarda da nake gaya miki ruhinmu a haΙ—e yake? Ɗaya ba zai iya rayuwa babu Ι—aya ba"


"Ba wannan nake son ji ba, haryanzu akwai wasu abubuwa Ι“oyayyu da ban gama fahimta game da kai ba"


"Komai zai warware a hankali, za ki fuskanci komai rayuwata, amma ba na nufin cutar da ke ta kowace fuska, amma sannu a hankali za ki fahimci abin da ki ke kokwanto a kai."


Ta buΙ—e idanunta tana Ζ™arasa jin sautin muryarsa a cikin kunnuwanta. A kan gadon ta gansu tare, fuskarsa na kallon ta ta, yana ta yi mata numfashi a fuska a hankali, wanda hakan ya Ζ™ara dagula mata lissafi dan kuwa ita ta san a zahiri abin ya faru, amma ya rikiΙ—e ya juye ya koma kamar mafarki. Ga shi yanzu Ƙaisar ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba, balle ta ce ko shi ne yake wujijjigata, hakan ya Ζ™ara hargitsa mata tunaninta.

Ta  tsura masa ido, kamar a fuskarsa za ta gano gaskiyar abin da take fata.


"Meyafaru?" Sautin muryarsa ya doki dodon kunnuwanta.

Ba ta ce masa komai ba, ta zame jikinta ta juya masa baya, tana ta tufka da warwara a zuciyarta. Sake matsawa ya yi kusa da ita, sai dai wannan karon bai yi magana ba, sai dai jin manufarsa, ya sanya ta zabura da sauri tana Ζ™anΖ™ame jikinta.


AREWABOOKS 


ƘanΖ™ance idanun ya yi, kasancewar fitilar Ι—akin a kunne take, ya din ga bin Nana da kallo, yadda ta tsuke fuska ta sanya hannayenta tana kare jikinta.


"Nana" Ya kira sunanta kamar yadda ake kiranta. Sai ta ji wani iri gaba Ι—aya babu daΙ—i, ta kalle shi a tsorace.


"Me yasa?" Ya furta a hankali. Ba ta ce komai ba ta sunkuyar da kanta, tana Ζ™oΖ™arin matsawa kaΙ—an.


"Matata ce fa ke? Da gaske kin daina so na ko?"


Ta ce "Ko ina sonka, ba zai yi mini wani amfani ba. Kuma a da ne nake da cikakken 'yanci a matsayin matarka, a Duniyar da nikaΙ—ai ka ke kallo. Wannan duniyar kuma ka yi mini nisa, a yanzu ma na san da na gama amfani za a sallame ni, sake yadda da kai shi ne ganganci mafi muni da zan sake aikatawa"


Ya Ι—an fesar da wata iska daga bakinsa ya ce "Ki yi mini alfarma ki bani dama, na san tun da ki ka yadda ki ka sake dawowa kina so na, idan ba kya so na ba za ki yarda ki sake zuwa inda nake ba." Ya riΖ™o hannunta yana murzawa a hankali ya ce "Ba kya yi mini kwatankwacin son da nake yi miki. Kar ki hukunata ni da abubuwan da ki ke gani a zahiri kawai"


A Ι—an Ζ™ufule ta ce "Ka ke son dai wadda ka ke so, ga matar so can kana da ita, wadda al'adarku ta amince ka so ka zauna da ita. Ai ni ina ga sai dai a saka ni a cikin bayi saboda baΖ™i da muni" Ta Ζ™arasa maganar tana tashi zaune. Shi ma tashi zaunen ya yi ya ce "A'a ai ni ban faΙ—i haka ba, ina da farar amma, nake ta bin ki ina lallaΙ“a ki. Dan Allah ni dai ki yi haΖ™uri, daga ni har ke mun yi kawar juna, wallahi ba Ζ™aramin kawaici nake yi ba kasancewata da ke a guri Ι—aya" Baki buΙ—e take bin sa da kallon mamaki da rashin sanin abin yi.


Cike da son tura masa takaici ta ce "Idan ba ka ce ba, amma ai a gabanka ta bautar da ni, ta wulaΖ™anta ni. Ba Ζ™aramin tozarta na yi ba da abubuwan da matarka ta yi mini ba. Ka je gurin halattacciyar matarka, da ahalinka suka san da zamanta, ba ni matar Ι“oye ba"


Ya ce "Haka ki ka ce?"


"Eh" ta furta cikin tsiwa. Ya zuba mata ido yana kallonta, shi wani irin kyau mata Ζ™ara masa, zuciyarsa har wani harbawa take yi da sauri kasancewarta a kusa da shi. Shi kansa ba zai iya cewa ga adadin abin da yake ji a kanta ba.


A ransa ya ce "Ba komai ki yi yadda ki ke so, kin cancanta" A zahiri kuma sai ya sauka daga kan gadon, ya nufi hanyar fita.


A Ι—an ruΙ—e ta sauka daga kan gadon ita ma tana faΙ—in "Ina zaka je?"

Bai yi magana ba ya ci gaba da tafiya, bayansa ta biyo da sauri tana faΙ—in "Sayyid ba ka da cikakkiyar lafiya fa, ina za ka je?"


Ya rufa ta a cikin Ι—akin, ya tafi. Ta jijjiga Ζ™ofar amma ta ji Ζ™ofar a rufe. Ta koma ta nemi guri ta zauna jikinta a sanyaye tana tunanin, kar wani abin ya same shi.


*****


Tun da Ι—an da ke cikin Shukura ya faΙ—o Duniya, ta fara ganin duhu, saboda wani irin bleeding da ta din ga yi. Matar da ta kawo ta Asibiti, gaba Ι—aya a ruΙ—e take, saboda tun da ta haΙ—u da ita ba ta yi magana ba. Ga shi ta kawo ta Asibiti har ta haihu ba ta yi magana ba.

Likitan ya ba ta shawarar ta kira jami'an tsaro ta sanar musu, saboda kar a je wani abu ya faru da ita.


*****

Doctor Sharif kuwa tun da ya farfaΙ—o ya tashi da shanyewar Ι“arin jiki, saboda tashin hankalin yadda ya ci karo da gawar 'yarsa cike da tozarci. 

Duk da maganarsa ba ta fita sosai, amma Ζ™oΖ™ari yake yi ya tambayi ina matarsa, ya jikinta. Amma aka ce masa tana samun sauΖ™i, sai dai abin da bai sani ba shi ne, bayan tafiyarsa gurin 'yan sanda Allah ya yi mata cikawa.


*****


Matawalle ne tare da Sultan suke tattaunawa, fuskar Sultan fal damuwa yake faΙ—in "Na rasa abin da na yi wa Tafawa a rayuwa, da yake nuna wa jinina wannan Ζ™iyayyar haka, abin da ba zan taΙ“a yi masa ba"


Matawalle ya ce "Ai dama ba halinku Ι—aya ba sam, ka kwantar da hankalinka mu bi a sannu, in sha Allah zamu samo mafita. Amma kwana biyu yaya ka ke ganin jikin Imam Ι—in?"


Ya ce "Jikinsa da sauΖ™i, ana samun ci gaba, sai dai ba ya magana sam. Jiya da yau nima ban shiga ba, ba na son yawan zarya da nake yi musu, kamar yarinyar a tsorace take da mu. Amma na yi mamakin yadda ta iya sarrafa shi ya dawo hayyacinsa."


Matawalle ya ce "Allah ya baka nasara, ni fa ina jin tsoron a sake samun matsala"


Sultan ya ce "Matsalar me fa?"


"Kar a je wani abu ya faru, kana ganin yadda muke fama, ake tunanin yadda za mu Ι“ullo da lamarin bayyanawa Duniya Ι—an gurin Imam Hammad da bayanin da za mu yi a gamsu. Yanzu kuma mun bar shi ya keΙ“e da ita idan aka kuma samun matsala fa?"


Sultan ya Ι—an yi murmushi ya ce "Sai mu karΙ“i Ζ™addara, mu jira ta sake haihuwa. Amma ba na tunanin wani abu ma zai iya faruwa, tun da ba cikakkiyar lafiya ce da shi ba. Kuma mai maganin da aka je Ι—aukkowa ne ya Ι—an yi balaguro, yana Ζ™arasa warwarewa za a raba su daga Ι—akin, mu ga me ya kamata a yi mata"

Matawalle ya ce "Haka ne, Ubangiji Allah ya ba shi ingantacciyar lafiya.


Sultan ya amsa da "Amin"


Hammad bai sake dawowa ba sai bayan sallar asuba. Da ya shigo ma bai kai ko kalli inda Nana take ba.


"Ina kwana" Nana ta gaishe shi tana satar kallon sa, amma ya yi mata shiru bai amsa ba.

Gaba Ι—aya sai ta ji babu daΙ—i shirun da ya yi mata. Ya je gaban mudubi yana gyara gashinsa, ta Ζ™arasa gaban mudubin ta ce "Kawo na gyara maka?"


Ya harare ta, ya share ta ya ci gaba da taje gashinsa.


ƘwanΖ™wasa Ζ™ofar Ι—akin aka yi, ya ajiye comb Ι—in, ya kalli Nana ta je ta Ι—aukki hijjabinta ta saka. Ya Ζ™arasa ya buΙ—e Ζ™ofar.

Mahmoudu ya shigo da kwanukan Abinci.

Ya gaida Hammad, ya Ι—aga masa hannu. Nana ta gaishe shi ya ce "Ni yakamata na din ga gaishe ki, uwar gijiyarmu. Ya mai jiki?"


Nana ta ce "Asma'un dai. Mai jiki da sauΖ™i Alhamdillah ina Nene?"


"Tana nan Ζ™alau, ga saΖ™on ki nan in ji ta, ina ta lallaΙ“ata ta dawo Agadez, na ajiye ta a gidana amma ta Ζ™i" Ya yi maganar yana nuna wa Nana flask.


Nana ta ce "Dan Allah idan ka koma idan za a bari na ganta, ka ce dan Allah ta taimaka ta zo na ganta, Kodayake da an sallame ni daga nan, gurinta zan je ta ce za ta raka ni gid.. sai dai sauran maganar ba ta fito ba saboda harar da Sayyid ya yi mata.

Mahmoudu ma ya kawar da maganar, ya koma yi wa Hammad magana da yarensu. Hammad ya yi shiru yana saurarensa. Ba ta san me suke tattaunawa ba, amma da alama abin da suke tattaunawar ya Ι“ata masa rai. Ya tashi ya Ι—aukko biro da takarda ya fara rubutu.

Sai gaban Nana ya faΙ—i, zuciyarta ta fara raya mata ko takardar saki yake rubuta mata. Ya gama rubutunsa ya miΖ™a wa Mahmoudu, suka fita tare.


Ta yi ajiyar zuciya ta buΙ—e flask Ι—in da Nene ta bayar a kawo mata. Nana ta yi murmushi ganin naman kaza cikin flask Ι—in, ta ce "Nene so take sai na fashe saboda girma"


Ba ta sake ganin Hammad ba, sai da daddare, da yaje ya yi wanka, ya canza kaya ya nufi hanyar fita. Nana ta ce "Sayyid wai yau ma nikaΙ—ai zan kwana a Ι—akin nan? Amma ka san Ι—akin nan tsorata ni ake yi"


Ya ce "Me zan zauna na yi miki, zan iya Ι“ata miki rai idan na ci gaba da zama a Ι—akin nan, gurin matata zan tafi" Ya yi mata maganar a gadarance. Ƙifta ido kawai ta yi idanunta suka yi jawur. Sai a lokacin ya yi dana sanin abin da ya gaya mata, biyo bayan tuna matsanancin kishi da take da shi.

Ji yayi kamar ya bata haΖ™uri, ya koma ya zauna, amma ya yi jarumta ya fice. Sai dai tun da ya fita abin duniya ya dame shi. Tausayin Nana ya mamaye shi, ya sa dole ta yi kishinda Asal kuma ta ji haushin sa, mussaman yadda Asal Ι—in ta din ga yi mata isa da iko, da nuna mata ita ba komai ba ce ba. 

Tun da ya fita Nana ta kasa zaune ta kasa tsaye, wani abu mai raΙ—aΙ—in gaske, ya soke mata a Ζ™irjinta zuwa wuyanta. Duk da ta saba ganinsu guri Ι—aya, tana kishin hakan amma na yau ya yi mata ciwo nesa ba kusa ba.

Bacci Ι“arawo ne ya Ι—auke ta, sai dai wannan mummunan mafarkin, na halittun nan, suka din ga bin ta, gaba Ι—aya baccin ya gaza yi mata daΙ—i.

Kafin Asuba ta farka da wani irin zazzafan zazzaΙ“i da ciwon da kai.

A inda ta yi salla ta kifa kanta ta kwanta, zuciyarta cike da damuwa, ga jikinta babu daΙ—i.

Ji ta yi an danne ta, ta buΙ—e idonta ta ga Muhsin ya Ζ™anΖ™ame ta. Tashi ta yi zaune a rikice tana faΙ—in "Muhsin Ι—ina"

Ya Ζ™anΖ™ameta, ita ma ta rungume shi tana wani irin murmushi tamkar ta mayar da shi cikinta.

Ta Ι—aga kai ta ga Hammad a gefe, yana karyawa. Muhsin ya tashi daga jikinta, ya je gaban Imam ya Ι—aukko dabino, ya dawo ya saka mata a baki, ya sake komawa ya Ι—aukko ya kawo mata. Ta saka hannu ta karΙ“a tana jin wani irin tasirin alaΖ™a ta tsakanin uwa da Ι—a. 


Sayyid ya Ι—auki Muhsin, ya ajiye shi a kusa da shi, yana ba shi Abincin. Ya waiwaya ya kalli Nana ya ce "Naaa" ya din ga nuna mata kusa da shi, wai ta zo ta zauna ta ci.

Sam Hammad bai nuna ya san tana gurin ba. Amma duk da haka yanayin ya yi mata daΙ—i mara misatuwa, yau ga mijinta ga Ι—anta a guri Ι—aya. Kuma alamu suka nuna mata, a zaman da Muhsin ya yi da su, akwai alaΖ™a mai Ζ™arfi a tsakaninsu. Dan duk Ζ™yuyar Muhsin ba ta ga alamar yana yi masa ba.

Ƙarshe ta yi shiru tana kallonsu, ya shirya cikin jallabiya fara Ζ™al, ya shirya Muhsin da kansa, sai dai ga mamakinta ba ta ga ya naΙ—a rawani ba, ya saΙ“a Ι—ansa a kafaΙ—arsa ya yi waje. Ƙasan zuciyarsa kuwa raya masa ya din ga yi ya rungume ta, ya ji damuwarta, yana da abubuwan gaya mata da yawa, amma ya daure ya share ta.


Sultan yana zaune, yana saka hannu a wasu takardu, tare da Tafawa da Sardauna. Aka shigo aka nema wa Tafawa iso. Gaba Ι—aya suka shiga mamakin me ya kawo shi a daidai wannan lokacin.


Bayan sun gaisa ya ce "Na samu takardar kiran da ka yi mini ne, shi ne na amsa kiran.


Cikin mamaki Sultan Ι—in ya ce "Ni Ι—in kuma?"


Tafawa ya ce "Amma saΖ™onna samu har gida aka kai mini takarda"


Sultan ya ce "Ai ni ba zan aika maka da takarda dan ina neman ka ba, amma da mamaki"


Tafawa ya ce "Ikon Allah, to waye ya aikata hakan?"


"Ni ne" Imam Hammad ya amsa ya na Ζ™arasa shigowa gurin.


Ayshercool 


87

LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KAN KI KARANTA 08081012143


Ƙwalalo manyan idanunsa Tafawa ya yi, ganin Imam Hammad ya fito gashinsa a buΙ—e, saboda hakan abu ne mai girman gaske, mussaman ga shugaba kamarsa,hakan kuskure ne.

Ba wannan ya fi kaΙ—a shi ba ma Ι—an Ζ™aramin yaron da yake hannunsa ne ya fi tafiya da tunaninsa. Ya girgiza matuΖ™a gaya da ganin yaron.


Su Sultan ma sak suka yi, su na mamakin yaushe ya Hammad ya samu sauΖ™i har haka, har bakinsa ya yi wannan buΙ—ewar? Ga uwa uba wautar da ya yi na zuwa da Muhsin ba tare da an gama shirya yadda za a kare hakan ba.


Imam Hammad ya nemi guri ya zauna, cikin girmamawa ya gaishe su, bai damu da jiran su amsa ba. Ya dubi Tafawa ya ce "Mai girma Tafawa, ina fatan ban yi laifi ba, kasancewar a Ζ™arshen wasiΖ™ata, ban sanar da cewa ni nake nemanka ba, ba Sultan ba. Na zaΙ“i saka gurin haΙ—uwar ya zama nan ne, saboda sai ya fi dacewa da abubuwan da suke bakina.

Kun aika da takarda Majalisar Sultan, sannan an aika da wata majalissar Imams. Duk da kwana biyu ba na samun sukunin zaman majalisar. Na gayyace ka nan ne domin warware maka duk wani abu da ka ke son sani, ba kai ba duk sauran wanda suke son sani ma. Ba sai mun ci gaba da wahalar da shari'a ba. Kamar yadda na gaya maka wannan shi ne Ι—a na Muhsin, ina da Ι—a, kamar yadda na din ga jaddada maka, ka din ga ganin kamar shaci faΙ—i ne, wanda nan gaba kaΙ—an zan bayyana wacece mahaifiyarsa ba na son mu zurfafa a kan wannan bangaren dan abu ne da ya shafe ni. Abu na gaba kuma ana cewa ba ni da cikakkiyar lafiya ba zan ci gaba da gudanar da shugabanci ba. Haka ne, yakamata na matsa gefe na samu cikakken hutu da nutsuwa kamar yadda ku ka buΖ™ata. Sannan kuma babu zobena na tambari a hannuna. Ina mai farincikin sanar da kai cewa daga yau, na sauka daga kan muΖ™amina na shugabancin majalisar Imam. Ba iya wannan ba ina san a cire ni daga cikin Imam da ake sanya ran a cikinmu ne za mu gaji sarautar Sultan shi ya sanya na fito maka haka babu rawani. Ka na damar maye gurbina na Imam ko ma shugabancin majalisar Imam Ι—in baki Ι—aya, ko kuma ka Ι—ora Imam Asadullah na muddin hakan zai sama maka farinciki da kwanciyar hankali. Ka bar mu mu huta da ni da mahaifina. A Ζ™arshe ina Ζ™ara gabatar maka da ma petit Hammad wato Imam Muhammad H.J Agadez wato Muhsin" Ya yi maganar yana murmushi tare da shafa kan Muhsin.

Ya sake kallonsa ya ce "Idan babu sauran magana, za ka iya tafiya, ina muma fatan ka fahimci abubuwan da suka shige maka duhu game da ni"


Tafawa mutuwar zaune ya yi, tare da bin Hammad da ido, jin sun Sardauna yi shiru kuma babu wanda ya musa, ko Ζ™aryata abin da Hammad ya faΙ—a  ya sanya shi tabattar da abubuwan da Hammad ya faΙ—a gaskiya ne.


Sultan da tuni gumi ya jiΖ™e shi ya ce "Ina  fatan ka ji daΙ—i, da ka kai shi bangon da ka sanya ya fito ya tabattar maka da abin da ka ke son tabattarwa? Ina ga shikenan za ka iya tafiya."


Tafawa bai iya furta uffan ba, jikinsa a matuΖ™ar sanyaye, ya tashi yana jan Ζ™afarsa, da yake jin kamar ba a jikinsa take ba, da kyar ya fice.


Gaba Ι—aya suka yo kan Imam Hammad da faΙ—a kamar za su dake shi. Hammad ya ce "Ina neman afuwarku, a kan abin da na aikata ba tare da izninku ba. Amma har abada Ζ™arya fure take yi, ba ta 'ya'ya, ba zamu dauwwama Ι“oye wa duniya abin da komai daren daΙ—ewa sai ya bayyana ba. Ba zan iya ci gaba da jure kullum lokacinku ya tafi a kan bani kariya ba, duk na san na aikata laifi, zan tsaya a kan laifina na karΙ“i duk hukuncin da ya dace".


Sardauna ya ce "Kuma saboda shirme sai ka ce ka sauka daga kan kujerar Imam? Dama kai ka Ι—ora kanka?"


Suka din ga yi masa faΙ—a, shi kuwa ko a jikinsa, dan gara ya Ι“allo duk abin da zai Ι“allo a san abin yi, duk abin da za a yi masa a yi masa, ya san yadda zai da matarsa da Ι—ansa.


*****

Kamar yadda Alhaji Fatuhu ya umarci Fadila,ta shirya tare da babbar 'yarsaJannat, suka tafi duba Hajiya Sa'a. Sai dai Hajiya Suwaiba ba ta je ba, saboda ba ta jin daΙ—i.

Ko da suka je, Ζ™in fitowa falo ta yi, sai su ne suka shiga cikin bedroom Ι—in ta, suka same ta. Sai dai kamar yadda Alhaji Fatuhu ya ba ta labari, haka ta ga tsufan Hajiya Sa'a ya fito. Kamar ba ita ce 'yar Ζ™walisar nan mai ado da kwalliya ba.


Suka gaishe ta, amma sai dai ta sake shiga halin Ι—imuwa ta kasa gane su, kawai dai ta amsa musu.

Fadila ta sauke Muhsin da yake bayanta, tana ba shi ruwa saboda daga bacci ya tashi. Hajiya Sa'a ta Ζ™ura masa ido, har sai da ya lafe a jikin mahaifiyarsa yana kawar da kansa daga kallon Hajiya Sa'a.


Hajiya Sa'a ta ce "Da tuni wannan tsinannen Ι—an ne zai mutu, amma nawa Ι—an ya mutu, Allah ya isa ban yafe ba, kuma shi ma in Allah ya yarda sai ya mutu"


Cikin mamaki da rashin fahimta Fadila da Jannat suke kallonta.


Fadila ta ce "Tsinanne kuma Yaya Sa'a, me ya yi miki? Ba ki gane shi ba ne? Muhsin ne Ι—an gurin Ζ™aninki Alhaji Fatuhu"


A fusace ta ce "Shi Ι—in fa, Allah ya tsine masa Albarka, shi ma Fatuhun Allah ya tsine masa Allah ya sa ya mutu. Da tuni Abba yana raye, amma bai sha alawar ba sai Abba ya sha ya mutu. Ke ma Allah ya tsine miki shashasha"


Waro ido suka yi gaba Ι—aya, cike da tsoro.

Jannah ta ce "Kin ga Anty, tashi mu tafi na fara jin tsoro, kar ta fara kai mana duka"


Babu shiri suka miΖ™e, Fadila ta goya Ι—anta suka bar gidan, sai tsine musu take yi, tana faΙ—ar wasu abubuwa da ba su gane kan abin da take nufi ba.


*****


Asal ta sha mamaki, ganin mahaifinta a gidanta wanda idan ba da wani dalili ba baya zuwa, sai dai yanayin fuskarsa ya sanya gabanta faΙ—uwa.


Kan ta yi magana ya ce "Hammad da gaske yake yana da Ι—a, domin na ga Ι—an nasa yau ido da ido, aurenki da shi bai amfana mini komai ba gurin cikar muradina ba, kaiconki da gaza cika wa mahaifinki burinsa"


A burkice ta ce "Wane Hammad Ι—in, yana tsare babu lafiya bai san waye a kansa ba ma?"


Cikin tsawa ya ce "Zan yi miki Ζ™arya ne? Daga cikin gidan Sultan nake, lafiyarsa Ζ™alau sai dai idan raina miki hankali suke yi, na yi magana da shi, kuma har Ι—an nasa na gani da idanuna"


Hannu Asal ta Ι—ora a ka, tana lissafa maganganun da mahaifinta yake gaya mata. Da ta rasa mene ne gaskiyarsu.


Imam Hammad kuwa, tun da ya shiga Ι—akin, ya hango Nana ta yi ruf da ciki a kan gadon, ga sautin sheshsheΖ™ar kukanta na tashi. Ya rufe Ζ™ofar ya Ζ™arasa gaban gadon da hanzari.


Ya Ι—ora hannunsa a bayanta ya ce "Ma vie" Tashi ta yi zaune idanunta jawur, ta ce "Ina Muhsin Ι—in?"


"Na mayar da shi inda yake. Ya na ji kamar jikinki da zafi ne? Meyafaru ma ki ke kuka? Wani ya shigo ne, ko an yi miki wani abu ban sani ba?"


"Ni ka mayar da ni gurin Nene, tun da ka samu lafiya"


"Yaushe na samu lafiyar? Ni ban samu lafiya ba tukuna, ba ki san me nake ji a jikin nan nawa ba" Yayi maganar yana ci gaba da shafa ta a hankali.


Cikin kulawa ya ce "Ba ki da lafiya rayuwata, jikinki da zafi. Ga shi haushina ki ke ji kin Ζ™i yadda da ni, balle na ce ko Muhsin ne zai samu Ζ™ani"


Nana ta ci gaba da kuka, da ita kanta ta kasa tantance kukan me take yi. Ya yi murmushi ya ce "Yanzu kishin ne ya saka miki zazzaΙ“i ma viee?" Ture hannunsa ta yi tana kuka. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "Da wasa nake miki, ban je ko ina ba fa da na bar Ι—akin nan, a Ζ™ofar Ι—akin nan nake kwana, saboda idan mu na tare guri Ι—aya akwai matsala ne. Ba kuma na son Ι“ata miki rai" 

Kwanciya ta yi sosai a jikinsa, ta saka hannu ta zagaye bayansa ita ma, ta yi shiru tana mayar da numfashi. Ya din ga murmushi yana shafa bayanta ya ce "Ki yi haΖ™uri, ba na Ζ™aunar na din ga aikata duk wani abu da zai sanya mini ke fushi da damuwa. Je vous aime ina son ki rayuwata".


Nana ta Ι—ago tana kallon Ζ™wayar idonsa, idanunta fal hawaye.


Ya jinjina kai ya ce "Da gaske nake Asmy, ina yi miki so mai tsananin gaske. A jinina nake jinki ba iya zuciyata ba"


"Sayyid"


"Na'am rayuwata"


"Kar na sakankance da kai, 'yan uwanka su ce ba zaka zauna da ni ba, ban san ya zan yi ba Sayyid. Ba gudunka nake dan na daina sonka ba, tsoro nake ji. Na azabtu ko a iya haka a tsaya, ina son na samu nutsuwar Ζ™waΖ™wawa da zuciya. Na kasance da abubuwan da za su sanya ni farinciki" Ta yi maganar a raunane.


"Ke jaruma ce Asmy, kar wani abu ya baki tsoro, kai da fata komai zai faru ina tare da ke, zan zaΙ“e ki da Ι—ana a kan komai, babu butulci tsakanina da ke, ai na san babu wani abu da zan yi miki da zai sanya na biya ki ko na kamanta abin da ki ka yi wa rayuwata ba. Kuma ina fatan a wannan karon za ki ba ni dama ki saurari uzurina, inda na yi miki kuskure kuma ki yafe mini. Ki bani dama mu Ι—ora ginin rayuwarmu rayuwa mai kyau da aminci"


"Ni ba biyana za ka yi ba, ban yi dan ka biya ni ba, ni kawai su bar mini kai, kuma su dawo mini da Muhsin mu rayu tare" Ta yi maganar tana kuka.


Ya yi murmushi idanunsa na cika da hawaye, ya ce "An bar miki ni, halak malak. Hammad naki ne rayuwata" Ya yi maganar yana haΙ—e bakinsa da Nana.


Babu tsammani aka banko Ζ™ofar Ι—akin, Nana ta yi wata irin zabura, shi kuwa cikin nutsuwa ya waiwaya ya ga waye wannan ya shigo musu babu neman izni.

Da Asal ya yi tozali, jikinta na wata irin tsuma take bin su da kallo. Ta nuna Nana da yatsanta bakinta yana wata irin rawa, jikinta ma karkarwa kawai yake yi, tamkar ana kaΙ—a mata gangi.

Ba ta taΙ“a tsammanin abin da za ta gani ba kenan, ko a hasashe da tsammani ba ta taΙ“a hasko ganin Nana tare da mijinta ba. Kasamcewarta baΖ™ar fata da ba Ζ™abilarsu ba.

"Ham..Ha.ha...Hammad!" Ta faΙ—a cikin wani irin Ζ™araji mai razanarwa.


Bakin Asal ne ya ci gaba da rawa, dan da fari ma kanta gaba Ι—aya kullewa ya yi, ta manta wace ce ma Nana. 

Ita da ta zo tambayarsa ba'asin ina ya samu Ι—a, sai ta riski abin da ya fi maganar da ta zo da ita tashin hankali.

Hankali kwance Nana ta gyara rigarta, ba tare da abin da ya faru ya Ι—aga mata hankali ba. 

Ja da baya Asal ta fara yi, numfashinta na fita da kyar, jikinta na wata irin kyarma. A sukwane Imam Hammad ya diro daga kan gadon ya nufe ta, cikin tashin hankali bai so Asal ta san alaΖ™arsa da Nana ta wannan sigar ba. Amma ya san babanta shi ne ya lalata komai.


"Kar ka taΙ“a ni, kar ka Ζ™araso inda nake Hammad. Ka yaudare ni ka zalunce ni, dama rashin lafiyar da ka ke yi Ζ™arya ka ke yi? Ka haΙ—a kai da mahaifinka ne dan ku yaudare ni ku cutar da ni? Lalata da wannan Ζ™asΖ™antacciyar Ζ™azamar matar? Na zaΙ“o ta a matsayin kukunka dan kawar da kanka daga kalle-kallen wasu matan, ashe yaudarata ka ke yi? Tun tsawon lokacin da ta gudu na neme ta na rasa, a she a nan ka Ι“oye ta ku ke lalata."


Cikin azama Hammad, ya danΖ™o hannun Asal, da take ta fizge-fizge ya danna Ζ™ofar ya datse ta. Ya kalli Asal ya ce "Ki nutsu cheriΓ© zan yi miki bayani, ni ba lalata nake yi da Asmy ba"

Cike da baΖ™in ciki take kokowar fizgewa cikin Ζ™araji ta ce "Idan ba lalata ku ke yi ba, me ku ke yi? Tsawon wannan lokacin da ba ta nan, ashe ku na tare ka ji kunya ba ka ji daΙ—in halinka ba. Ke kuma 'yar iska mazinaciya wallahi sai na Ζ™asaΖ™antar da ke, sai na saka an kashe mini ke a kashe banza"


Nana ta ce "Point of correction my dear, ba da kukun mijinki ki ke magana ba a yanzu,  kuma ni ba mazinaciya ba ce ba. Ki dai nemi wani sunan ki kira ni da shi"

Ya kalli Nana da ta tsuke fuska ya ce "Ma vie dan Allah ki yi shiru, mu warware matsalar nan a hankali"


AREWABOOKS 


Daskarewa Asal ta yi jin sunan da ya kira Nana da shi, wanda shi gaba Ι—aya ya manta, saboda yadda sunan ya shiga bakinsa ya zauna.


"Hammad gaskiya ne abin kunnuwana suke jiye mini? A gabana? Hammad" Ta furta tana ajiyar zuciya mai Ι—auke da nannauyan baΖ™in ciki da tashin hankali.

DamΖ™ar hannun Asal ya yi, ya buΙ—e Ζ™ofar suka fita tare.


Kokowa ya shiga yi da Asal, yadda take kai masa duka, tana fizge-fizge.


"Asal, ki tsaya ki saurare ni, kar ki ji wa kan ki ciwo mana"


"Ba zan saurare ka ba, ba na buΖ™atar duk wasu kalaman yaudara da Ζ™arya da za su fito daga bakinka. Me ya rage bayan abin da na gani? Da girmanka da mutuncinka ka Ι“oye kukunka a sashen mahaifinka kana zina da ita, ba ka ji daΙ—in halinka ba" Kalaman Asal sun yi wa Hammad zafi nesa ba kusa ba, da kyar ya haΙ—iye wani yawu mai zafi ya ce "Ni ba zina nake yi ba, idan ba ki tsaya kin saurare ni ba, ki ka fita ki ka yayata abin da ba shikenan ba za ki cutar da ni dan kin yi mini Ζ™azafi"


Kallonsa take yi, tana jinjina girman yadda ya Ζ™ware a iya wasa da hankali, ta ci gaba da Ζ™oΖ™arin fizgewa, amma ya riΖ™e ta gam.


"Hammad ka gama raina mini hankali, dama ga batun Ι—a ana yi, an ce ka na da Ι—a da a Ζ™alla ya shekara biyu, yanzu kuma na kama ka da wata, amma kana iΖ™rarin zan cutar da kai? Da ni da kai waye ya cutar da wani? Wadda ka yi wa ciki ba ta ishe ka ba, ka Ι—auki kukunka ka sanya a sashen Sultan ka ke lalata da ita"


"Ban taΙ“a cutar da ke ba Asal, a shekara goma sha biyu da muka yi da ke, idan zan iya aikata abin da ki ka faΙ—a kin sani, idan akasin hakan ne ma kin sani. Amma mu je gurin Sultan Ι—in ki ji komai daga bakinsa.


Nana kuwa guntun tsaki ta yi bayan fitarsu, ta tashi ta shiga banΙ—akin ta yi wanka, ta yi alwala. Ta Ζ™ura wa kanta ido a mudubin banΙ—akin, tana tunanin yadda Asal ta din ga yi mata kallon Ζ™asΖ™anci, da bautar da ita ta Ζ™arfi da yaji, saboda tana da kuΙ—i da mulki, a matsayinta na kishiyarta, kuma ta daure ta haΙ—iye. Ta ci gaba da tunanin daga bisani ta fito da niyyar ta canza kaya, amma ta kasa, ta nemi guri ta zauna ta yi shiru.

A zuciyarta take addu'a ta ce "Allah ga Nana, bakwarka ce ni mai raunin gaske, ga Ι—an jaririn Ι—a na da nake fatan ya samu kyakykywar rayuwa ya tashi a tsakanin uwa da uba. Ubangiji Allah ka na ji ka na gani, ka ga wahalar da na sha a baya, ga shi na zo wani bugire da nake sanya ran samun afuwa, sai dai alamu sun nuna an fi Ζ™arfina. Allah idan sun fi Ζ™arfina ba su fi Ζ™arfinka ba, da ni da su duk bayinka ne. Ubangiji Allah ka sassauta mini ka kawo mini Ι—auki. Ubangiji Allah ka yaye mini wannan kishin da nake ji, ka sanya su bar ni na rayu da mijina da Ι—a na. Ubangiji Allah ka ba wa mijina ingantacciyar lafiya ka yaye masa abin da yake damunsa, Allah ka ba kare mini Ι—ana daga dukkanin sharrin da ido ka iya gani, da wanda ma baya gani. Ƙaisar ma bawanka ne, Allah ka ba shi lafiya. Allah ka ga wahalar da na sha a baya, yanzu idan na koma suka raba ni da Ι—a na, wata wahalar zan shiga, Allah ka kawo mini agaji" Sai kuma ta yi shiru tana nazari, duk abin da take faΙ—a ai Allahan yana ji yana gani.

'Idan ba ubangijina ba, wa nake da shi da zan kaiwa kukana kai tsaye ya share mini. Na san ya sani amma Ζ™ara gaya masan, yana sama mini nutsuwa da kwanciyar hankali, ko da ina cikin damuwa. Ta ba wa kanta amsa.


Asal ce a gaban Sultan, tana ta uban kuka, fuskar nan ta yi jawurr, idanunta sun kumbura sosai da sosai.


Sultan ya yi shiru, saboda yadda abubuwan shi kansa suka kulle masa kai. Gaba Ι—aya bai yi tunanin abubuwan za su damalmale har haka ba, ya ma rasa ta ina zai fara.

Ya ce "Ki na ji na Asal. Wannan maganar abu ne mai faΙ—in gaske, da ko ba ki gano ba, dole za a yi miki bayani. Amma wannan bayanin ba ke kaΙ—ai yakamata mu yi wa ba, a gaban mahafinki yakamata mu yi shi. Tabbas da gaske Imam Hammad ba shi da lafiya, kuma ke ma shaida ce, saboda kin zo kin gan shi a halin da yake ciki. Sai dai ita wannan yarinyar tana da alaΖ™a da samun sauΖ™insa. Yanzu bayanin da zan yi miki ba za ki gane ba, ina son sai mun zauna gaba Ι—aya za mu yi miki bayani. Amma ki samu nutsuwa ki kwantar da hankalinki. 

Gaba Ι—aya Asal ba ta fahimci abin da Sultan yake gaya mata ba, gani take kawai yana Ζ™oΖ™arin goyon bayan Ι—ansa ne.

Muryarsa ta sake tsinkayowa yana faΙ—in "Kar ki bari kowa ya ji maganar nan, sai mun zauna an yi miki bayani tukuna dan Allah." Ya dubi Imam Hammad ya ce masa ya kai Asal gida, ya rarrashe ta, ta samu nutsuwa kafin a yi mata bayanin komai.


Nana kuwa kajin gurin Nene ta samu ta ci, saboda taga alamun idan ta biye ta kishin nan, yunwa ce za ta kar ta a banza, duk da yanzu naman duk ya ishe ta, abinci take so ta ci sosai. Ga shi ta yi zaton ko zai dawo mata da Muhsin, amma bai dawo mata da shi ba.


Ba ta sake ganin Hammad ba, sai bayan sha Ι—aya na dare. Idanunsa jawur da alama yana cikin damuwa kuma ko abinci ba ta tunanin ya ci. Sau Ι—aya ta kalle shi ta basar, ba ta ko kula shi ba.


Gani ta yi ya cire rigar jiknsa ya yar a Ζ™asa, ya hau kan gadon ya kwanta, ba ta motsa ba ta ci gaba da zamanta, dan haushinsa ne ma ya kama ta. Jin ya fara numfarfashi ya sanya ta tashi tsaye. Ta kalle shi ta ga ya fara komawa ja. Sai kuma jikinta ya yi sanyi, abin da ta lura da shi kamar ciwon ya fi tsananta masa a Niger.

Ta fara Ζ™oΖ™arin ninke masa rigar, kawai wannan takardar ta faΙ—o daga aljihun rigar. Ta Ι—auki takardar ta yi shiru tana kallon takardar. 

Ta hau kan gadon ta juya shi da kyar, taga yana ta taune leΙ“ensa yana jujjuya kansa.


"Ki yi mini addu'a, zan mutu" ya furta da kyar kamar numfasihinsa zai Ι—auke. Suratul Fatiha ta din ga karantawa da Bismillah tana tofa masa. Fizge-fizge ya fara yana girgiza kai ya ce "Tashi mu tafi"


Cikin rashin fahimta ta ce "mu je Ina?"


"Ki tashi nu tafi, kafin na rasa raina" Ya Ζ™arasa maganar yana dafe kansa da yake jin kamar zai yi bindiga. ƘwanΖ™wasa Ζ™ofar Ι—akin aka yi. Amma ba damar Nana ta tashi, saboda yadda ya rirriΖ™eta. Ga shi ta san ko ta ce a shigo babu lallai a jiyota daga waje.


Mai bugun ne ya gaji da bugawa, ya turo Ζ™ofar, Sultan ne tare da wata babbar mace fara solnda ita. Sai kuma Mahmoudu.

A rikice suka Ζ™arasa gaban gadon, cikin tashin hankali Sultan ya ce "Jikin ne?"


"Ki tashi mu tafi, zan rasa raina, Ζ™waΖ™walwata za ta tarwatse. Ki yi mini addu'a"


Tuni Nana ta fara kuka, ta ce "Ina yi maka, kai ma ka din ga yi ko a zuciyarka ne. In sha Allah babu abin da zai same ka"


Matar ta ce "Wannan ce matar tasa?"


Sultan ya jinjina kai ya ce "Ita ce"


Ta ce "Ikon Allah, lallai Allah gwani ne"


Mahmoud kuwa jiki a sanyaye ya ce "Sannu Imam"


"Hamud, dan Allah ka Ι—auke ni ka sake tafiya da ni, ba na son zaman garin nan, ba ku san me nake ji ba."


Mahmoudu ya kalli Sultan ya ce "Ranka ya daΙ—e, a irin wannan yanayin fiye ma da wannan, na bar Niger da shi a wancan lokacin. To kuma na ga alamar jikin na neman sake dawowa.


A hankali ya fara fita hayyacinsa, ya fara lanΖ™wasa Nana, ta rintse idanunta Sultan ya Ζ™arasa da sauri yana faΙ—in "Kai kar ka yi wa 'yar mutane illa, Hammad" Mahmoudu rasa abin yi ya yi, dan ya san ganganci mafi girma da zai aikata shi ne ya taΙ“a jikin Nana garin Ζ™oΖ™arin Ι“anΙ“are shi daga jikinta.


Sai kuma Sultan ya ja ya tsaya shi ma ya rasa abin yi.


"Ke kin san me nake ji ai" ya sake futawa cikin Ζ™arfin hali.


"Na sani, shi ya sanya nake yi maka addu'a"


Sultan ya ce "Hammad, kar ka ji mata ciwo fa"


A hankali Nana ta ce "Ba zai ji mini ba in sha Allah"


Addu'a ta ci gaba da yi masa, tana tofa masa. Sultan kam kasa jurewa ya yi, saboda ba Ζ™aramin tashin hankali yake shiga ba, idan ya ga Ι—an nasa a cikin wannan yanayin.


Sai kusan Ζ™arfe biyu na dare sannan ya dawo hayyacinsa gaba Ι—aya. Ya yinΖ™ura ya tashi zaune yana kallon Nana.


Ta ce "Sannu. Ka daina jin abin da ka ke ji Ι—in?"


Ba ta yi zaton zai iya magana ba ta ji ya yi, ya ce "Ina ji amma ya lafa mini"


Ta ce "To Allah ya baka lafiya ingantacciya. Amm ka yi haΖ™uri kana cikin yanayin larura zan tambaye ka abu" ya yi shiru yana kallon ta.


Ta Ι—ago masa wannan takardar ta ce "A cikin rigarka na ganta, waye ya saka maka ita?" Ya girgiza kai ya ce "Nima ban sani ba"


Ta sake cewa "Shekaranjiya wani abu mai kama da mafarki ya faru, har muka fita ta wata Ζ™ofa, gaske ne ko kuma mafarki nake yi?"


"Gaske ne" Ya bata amsa kai tsaye.


"Ina buΖ™atar fahimtar wasu abubuwan, dan ka na yin abubuwan da ba kowane Ι—an Adam ne zai iya ba. Tun mu na Nigeria ka ke yin wasu abubuwan. Kuma ina buΖ™atar na ji abubuwan da suka faru wanda ban sani ba" Ya numfasa ya ce "Zo ki raka ni shan iska tukuna" Suka sauka daga kan gadon. Ya zira rigarsa ya buΙ—e Ζ™ofar nan, suka Ζ™ara ratsa duhu suka fita wannan corridor.


Yau ma saharar ta gani, gurin ya Ι—auki sanyi sosai da sosai. Ta kalli Wannan tsaunin dake gefen saharar ta ce.


"Wai mene ne a cikin dutsen can, shi nake son sani"


Ya kalli gurin ya ce "Nan ne ainihin inda kakanninmu suka fara mulki, dan haka duk wani kayan tarihi, a ciki a ke adana su"


Nana ta ce "To ka gaya mini abin da na tambaye ka, kuma ina son ka kai ni na ga abubuwan tarihin garin naku"


"Zan kai ki, kuma zan yi miki bayanin amma yanzu ba na jin daΙ—i"


Ta Ι—an shafa bayansa ta ce "Sannu" ya jinjina mata kai. Ya matsa kusa da ita, ya rungume ta, sanyin gurin ya din ga ratsa su a tare.


Ta Ι—aga kai tana kallon wannan tsaunin, da ya ce mata gidan tarihi ne, tana jin kwaΙ—aituwa da son sanin abin da gidan Ζ™unsa.


Tana jin kewar Ƙaisar, ta damu sosai ta san ya jikinsa, amma ko sama ko Ζ™asa ta daina ganinsa.


Ta lumshe idanunta ta buΙ—e, kewar gida kuma na sake bijiro mata, tana cikin matuΖ™ar fargaba a kan irin karΙ“ar da za a yi mata idan ta koma.


"Ma viee"


"Na'am Shugabana"


"Ina da wani kyakykywan albishir da zan baki, amma ba yanzu ba"


Ta yi murmushi ta ce "Sai yaushe?"


"Sai an wa Muhsin Ζ™ani"


Ta ce "Babu rana kenan"


"Akwai mana nan kusa" yayi maganar yana Ζ™ara Ζ™anΖ™ameta.


Asal kuwa yadda ta ga rana haka ta ga dare, dan faΙ—a suka yi kaca-kaca da Hammad, duk da rarrashin da Sultan ya yi mata. 

Ta kira Hasna a waya, Hasna ta Ι—aga tana "FaΙ—in Gimbiya Asal, kwana biyu"


Cikin kuka ta ce "Hasna, kin san abin da Hammad ya yi mini kuwa?" Gaban Asal ya faΙ—i ta ce "Meyafaru?"


"Hasna wai Hammad yana da Ι—a"


"Innalillahi wa Innalillahi raji'un, Ι—a kuma kamar yaya?"


Cikin kuka ta ce"Ɗa dai ya haihu da wata, Tafawa kuma ya tabattar mini da hakan, kin san ba zai yi mini Ζ™arya ba. Kuma ba na ce miki yarinyar nan ta gudu ba, mai yi masa girki ba, har nake ce miki duk inda ta gudu zan saka a nemo ta"


Hasna ta ce "Eh haka ne"


"Na je na kama shi da ita, a can cikin sashen Sultan, duk tsawon lokacin da aka shafe ba ta nan, suna tare su na lalacewa, na shiga uku Hasna, ji nake kamar na kashe kaina na huta. Na tsani Hammad na tsane shi, ban taΙ“a cin karo da abin da ya gigita ni ba, kamar abin da na gani yau ba. Kuma Sultan goyon bayansa yake yi, wai in bari za a yi mini bayani, bayanin me za a yi mini an cuce ni Hasna" Ta yi maganar tana Ζ™ara rushewa da kuka, kamar wadda aka nuna wa ranar mutuwarta.


Hasna ta Ι—an yi shiru sannan ta ce "Asal, ki yi haΖ™uri ki nutsu, ki tattara hankalinki guri Ι—aya kar ki yi ganganci da rayuwarki. Amma ni kwanaki na ji Al Hussain yana cewa ya kira shi ya ce ya yi masa bincike a kanta, a nemo kamfanin da suka kawo ta. To ni ban kawo komai a raina ba, na Ι—auka da saninki, amma zan tambaye shi ko ya san wani abu. Amma dan Allah ki yi haΖ™uri ki kwantar da hankalinki"


"Ba ki san me nake ji ba, hankalina ba zai taΙ“a kwnaciya ba" Haka Asal ta kwana ido biyu, babu abin da take hangowa sai abin da idanunta suka gane mata a tsakanin mijinta da wannan baΖ™ar yarinyar.


Bangaren su Nana da safe, da Mahmoudu ya kai musu abinci, ya sanar musu da cewa Sultan ya ce su zo gaba Ι—ayansu, mai maganin ya Ζ™araso.


Hammad ya ce "Waye mai maganin?"


Ya ce "Ban san waye ba, kawai dai saΖ™on da ya bani kenan"


"Ni fa ba na buΖ™atar wani mai magani, ga maganina nan a gefe na" Ya yi maganar yana kashewa Nana ido.


Ta basar da shi, ta Ι—an yi murmushi. Ya karya sannan suka rankaya suka fita tare. Tun da aka kawo Nana, sai a lokacin ta samu damar sake fitowa daga Ι—akin da suke. Sai dai wani surΖ™uΖ™in Ι—akin suka shiga. Abin har mamaki yake ba wa Nana, yadda ake Ι—akuna a lunguna da saΖ™o na gidan, kamar marasa gaskiya, inda ba ka yi zato ba ma, sai ka ga Ι—aki ne.


Da Asal ta yi tozali a Ι—akin, idanunta jawur, tana ganin Nana ta sake tsuke fuska, kamar ta tashi ta kashe ta ta huta. Suka je gaban Sultan suka gaishe shi, Nana ta basar ko kallon inda Asal take ba ta yi ba.


Sultan ya ce "Asal, na saka an kira ki ne, saboda a yi komai a gaban idonki, a ji me mai maganin zai ce, saboda kina da hakki ki sani kar ki ga ana ci gaba da rufe ki a kan abubuwa, tun da mijinki ne" Ta yi shiru, saboda shi kansa Sultan Ι—in haushin sa take ji.


Sallamar da aka yi ne ya sanya Sultan yin shiru, Nana kuma ta miΖ™e tana faΙ—in "Kaii Sarki, dama ka na nan?"


Ya yi dariya ya ce "Tuba nake uwar gijiyata, tuba nake uwar Ι—akina"


Bakin Nana ya Ζ™i rufuwa, tamkar ta ga wani Ι—an uwanta na jini.


Cikin murmushi ta sake cewa "Sarki mai baka mai aska, kai ne mai maganin da zaka duba Sayyid?"


Ya ce "Ni ne uwar gijiyata, an yi mini lamuni, ko kuwa na koma ba a bani dama ba?.


Ayshercool 08081012143


88

1K NE VIA 0069685771

AISHA ADAM STANBIC IBTC BANK 08081012143


Nana ta kalli Sarkin baka ta yi murmushi ta ce "Wane mutum! Dama zan sake ganinka?"


Ya yi murmushi, hadimin da ya rako Sarkin baka, ya ankarar da shi Sultan. Cikin girmamawa Sarkin baka ya risuna ya kwashi gaisuwa a gaban Sultan.


Sultan ya ce "Na ga kamar ka santa ko?"


Ya jinjina kai ya ce "Ƙwarai uwar gijiyata ce" Sai kuma ya sauke idanunsa a kan Sayyid, ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Kamar ba ka gane ni ba ko?" 

Mahmoudu ya ce "Ina dai yi maka kallon sani"


Ya matsa gaban Hammad, ya zuba masa ido ya ce "Ka tuna ni?"

Hammad ya yi shiru sannan daga bisani ya ce "Na tuna ka"


"Waye ni?"


"Ba zan iya cewa ga waye kai ba, amma mun je gurinka a Nigeria"


Sarkin baka ya yi murmushi ya ce "Yanzu tunaninka kaf na zamanka a Nigeria ya dawo kana tuna komai?" Ya jinjina masa kai alamar eh.


Ya dubi Nana ya ce "Kin ga batutuwan duk da na gaya miki sun dawo ko? Kin yarda ko haryanzu kina da ja?"


Nana ta girgiza kai ta ce "Ba ta sauya zani ba, ina nan a kan bakana"


Ya ce "Babu laifi, amma an bani dama ko kuma na bar lamarin tun da na manya ne?"


Matawalle ya ce "Bawan Allah, ina ganin ka yi abin da aka kawo ka ka yi mana. Idan ma wani abu ne a tsakaninku, kwa tattauna daga baya. Nan ba gurin wasa ba ne"


Sarkin Baka ya tsuke fuska ya kalli Matawalle ya ce "Duk cikin aikina ne, kai ka san wacece wannan kuwa? Ku na da maganin matsalarku a tare da ku, amma ba ku sani ba" Gaba Ι—aya suka kalli Nana, ita ma ta yi sororo cikin mamaki.


Sarkin baka ya ce "Allah ne ya taΖ™aita masa, ba domin tana tare da shi ba, da sai ya zare ko ya mutu" Sultan da Mahmoudu suka haΙ—a ido.


Sarkin Baka ya ce "Ni yanzu  abu Ι—aya zuwa biyu zan ce, sauran magana ce tsakanina da ni da shi da Nana Asma'u Uwar Ι—akina ba Allah ya taya miki" Ya yi maganar cikin girmamawa da jinjina wa Nana. Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi.


Mahmoudu ya ce "Bawan Allah, nan fa a gaban Sarki ka ke, in yi maka da yaren da zaka fi ganewa"


Sarkin Baka ya ce "Nima Sarki ne, dan haka a bari ni na gudanar da aikina. Kai ka manta Garba ga Baka ga Aska da ku ka kai mini wannan Ι—an uwan naku can Nigeria" Mahmoudu ya yi sak ya ce "To ai na ga kamaninka sun canza?"


"Eh, ba kamannina ne suka canza ba, dan baka ganni cikin kayan aikina ba ne ba."


Sultan ya ce "Asal tashi ki je, duk abin da  aka tattauna za a gaya miki"


Asal ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah ina roΖ™on alfarma, a yi komai a gabana, ina son sanin halin da yake ciki nima".

Sardauna ya ce "Ke Asal! Ki nutsu ki saurara tukuna, ki tsaya mu ji kan rashin lafiyar tasa, sannan a yi miki bayani daga baya"


Asal ta tashi jiki a sanyaye, tana kallon inda Nana take da kuma Hammad ta fice.


Sarkin baka ya kalli Nana ya ce "Nana Asma'u, mene ne labari? Meyafaru bayan tafiyarki ne? Kuma yaya aka yi na ganki a birnin Agadez?"


Nana ta yi murmushi ta ce "Komai ma ya faru Sarki, amma dogon labari ne, mai tsayin gaske"


Ya murmusa, ya Ζ™are wa mutanen gurin kallo, sannan ya sake kallon Nana ya ce "Uwar Ι—akina, me ya kawo ki Agadez ne?"


Nana ta nuna masa Sayyid. Mahmoudu ya yi murmushi ganin abin da Nana ta yi.

Ya ce "Uwar gijiyata, kina nan me yasa aka neme ni, kin karΙ“i aikin gurin uban duΖ™usa ne?".


Nana ta girgiza kai. Ya ce "To bani labari meyafaru?"


Sultan ya ce "Bawan Allah, ban fahimta ba me yake faruwa ne?"


"Allah ya baka yawan rai, duk cikin aikina ne. Idan babu damuwa ina son na san matsayin kowa a nan"


Mahmoudu ya ce "Ga Sultan kana gabansa, shi ne mahaifin Imam Hammad, sarkin Agadez, ga Matawalle da Sardauna, su ma iyaye ne a gare shi, kuma manya ne a Agadez. Sai Gimbiya Asal matarsa da ta fita. Sai kuma" Sai ya yi shiru yana bin su da kallo yana tsoron ya faΙ—i matsayin Nana ya yi laifi.


Sarkin baka ya ce "Ba ka gaya mini matsayin uwar gijiyata ba"


Sayyid ya ce "Matata ce"


Sarkin baka ya sake yin murmushi ya ce "Na san a rina, an saci zanin mahaukaciya jikina ya bani tun a lokacin da na ganku. Allah ya baka yawan rai, in dai yana tare da Nana Asma'u zai samu sassaucin matsalarsa. Tana Ι—aya daga cikin dalilan da ya sanya yake zaune lafiya a Agadez, bai sake Ι“allewa ya bar Ζ™asar nan ba"


Sarkin baka ya sake maimaita musu, Nana tana da alaΖ™a da maganin Hammad.


Matawalle ya ce "Me ka ke nufi? Ko dai wani haΙ—in bakin ne, ku ke son ku yi mana" Sardauna ya yi maganar yana kallon Sarkin baka.


Sarkin baka ya ce "Ɗan tsahirta mini tukuna, a kan aikina nake"


Ya sake kallon Mahmoudu, ya ce "Ɗan uwana ko za ka iya tuna abin da na gaya muku, lokacin da ku ka je gurina?"


Mahmoudu ya jinjina kai ya ce "Ka ce mana asiri aka yi masa, da baΖ™in aljani, ya manta duk abin da ya shafe shi, ya bar garinsu ba zai iya zama a garinsu ba. Kai kuma ba zaka iya ba shi magani ba, saboda ba aljani ne da za a iya sasantawa da shi ba, sai dai a je a karya asirin da aka yi masa. Na tambaye ka ko zaka iya karya asirin? Ka ce a'a shiga al'amuran aljanin nan akwai matsala, mu koma Ζ™asarmu a bincika inda aka yi masa sihiri a warware shi a can"


Ya ce "Madalla"


"Uwar gijiyata, ranar da aka kawo ki gidana neman magani, Meyafaru?"


Nana ta Ι—an yi shiru sannan ta ce "Ka ce a je a kira buzayen da suka tafi. Aka ce maka sun tafi. Ka ce da an same su, wataΖ™ila ga maganin nasa ciwon ko nawa"


Sarkin baka ya ce "To Alhamdillah, an zo gaΙ“ar da nake so a zo"


"Allah ya baka nasara. Wannan ita ce rabin maganin abin da yake damunsa"


Matawalle ya ce "Kai kalle mu da kyau, kar ka kuskura ka zo nan ku na gaya mana maganar banza. Idan ma haΙ—a kai ku ka yi, ku ka haΙ—a baki domin ku raina mana hankali, wallahi muka kama ka da rashin gaskiya, sai mun yi maka mummunan hukunci"

Sarkin baka ya ce "Na san dai duk azabar da zaka yi mini ba zaka saka ni a jahannama ba ko? To bayan wuta da Ubangiji zai saka ni a ciki, azaba in dai ta Duniya ce babu wadda ban sha ba, duk wadda za ta biyo baya Ι—azu ce. Ban sanku ba ban taΙ“a ganinku ba, dan me zan yi muku Ζ™arya? Wani abu ne ya faru da tun a baya, na yi hasashen faruwarsa. Zan yi wani bayani amma a gaban mara lafiya da shaΖ™iΖ™ansa da ya yarda da su. Idan na faΙ—a ban ce lallai sai kun yadda ba, amma iya gaskiyata zan gaya muku. Wannan baiwar Allah da na nuna na santa, tabbas na santa amma ni babu wanda na haΙ—a kai da shi domin na zo nan gurin na yi cuta ba. Saboda duk wani abun duniya da nake fatan samu, Allah ya riga ya bani shi. Ranka ya daΙ—e zaΙ“i mutum biyu zamu yi magana.


Duk suka yi zuru da ido, suna kallon Imam Hammad.


Hammad ya kalli Sultan, Sarkin baka ya yi caraf ya ce "Ɗayar, na zaΙ“i uwar gijiyata mutum biyu kenan. Allah ya baka yawan rai, idan babu damuwa ina so mu keΙ“e tare da ku"


Sultan ya ce "Babu laifi, Matawalle ko za ku bamu guri?"


Sardauna ya ce "Mai girma Sultan, ka yi a hankali kar ka bari su yi maka wasa da hankali, su faΙ—a maka abin da ba shikenan ba"


Sultan ya ce "Babu wani abu in sha Allah"


Bayan fitarsu gaba Ι—aya, Sarkin baka ya ce "Allah ya baka yawan rai, ba dan ina tsoron hadisin da Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallam ya ce Allah yana fushi da Ι—an kasuwa mai rantsuwa a kan kasuwancinsa ba, da na yi maka rantsuwa domin nima bayar da magani kasuwancina ne, amma ina baka tabbacin duk abin da zai fito daga bakina gaskiya zan gaya maka. Na san duk alkhairin da zaka yi mini ba zaka yanke mini talauci ba, sai Allah ya yanke mini. Kuma ba zaka talauta ni ba sai Allah ya talauta ni. Babu Ζ™arya ko haΙ—in baki ko yaudara a cikin abubuwan da zan yi maka. Wannan bayin Allah biyu babu wanda ba a kawo mini shi gurina neman magani ba. Asma'u ko ba ta bayar da magani ba, tsantsar tauhidinta da yarda da Allah da ta yi, zai iya sanyawa yadda yake tare da ita ya samu lafiya ko dan albarkacin addu'a. Ai Allah shi ya ce a roΖ™e shi zai amsa. Kafin na ce maka komai, bari na yi maka wasu tambayi m ya ka ji lokacin da ka neme shi ka rasa a Ζ™asar nan?"


Sultan ya ce "Na shiga tashin hankali, ba na iya cin abinci da cikakken bacci saboda rashin sanin inda yake."


"Alhamdillah, yanzu da ya dawo ya ka ke ji?"


"Murna nake yi mara misaltuwa, da jin cewa zan iya yin komai, dan na ga bai sake yin nesa da ni bax


Sarkin baka ya ce "Alhamdillah, ka yi bayani dai-dai da abin da nake son ka faΙ—a. Wannan yarinyar da Ι—anka ba za su rayu guri daban-daban ba. Idan haka ta kasance kuma Ι—aya zai rayu cikin wahala. Saboda alaΖ™arsu akwai tasirin soyayyar uba da Ι—a a tsakaninsu"


Cikin rashin fahimta Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Me ka ke nufi?"


"Aljanin da aka yi wa Ι—anka asiri da shi, Ι—ansa ne a kanta yake ta Ι—awainiya da ita saboda ta yarda ta yi masa wani aiki. Ya Ι—auki tsawon shekaru ba sa tare, kwatsam da aka ba shi aiki a kan Ι—anka, ya yo Nigeria da shi, suka haΙ—u da ita. Dan haka duk abin da zai faru, duk rashin jituwar da ke tsakaninsu, uban ba zai bari Ι—ansa ya Ζ™ara nesa da shi ba. Saboda shi ne Ι—a mafi soyuwa a gare shi"


Sultan ya yi shiru cike da mamaki, yana bin Nana da Hammad da kallo.


Ya ce "To yanzu babu yadda za ayi, a karya sihirin?"


"Ni ba na Ζ™arya dan a so ni, ban san waye ya yi masa asiri ba, ban kuma san a daidai ina aka yi ba, balle na ce kai tsaye ga gurin a je a tona ba. Kuma ba zan yi karambani ba saboda aljanin shu'umi ne zai iya halaka ni. Amma ita tun da Ι—ansa yana tare da ita, ban sani ba ko ya samu sassauci ko makarin abin a dalilnta ba"


Sultan ya yi shiru yana kallon su, lallai biri ya yi kama da mutum, duba da yadda lokaci guda take iya sarrafa shi, idan ciwon nan ya tashi.


Sultan ya ce "Yanzu mene ne abin yi?"


"Abin yi Ι—aya, a ci gaba da addu'a, kuma ku Ζ™ara taka tsantsan, sannan ban sani ba ko uwar gijiyata za ta nema mana alfarmar shugaba, ko akwai abin da zai iya yi a kan lamarin"

Nana ta Ι—an tsuke fuska tana mazewa.


"Wa za ta roΖ™a mana " Sultan ya yi maganar cikin damuwa.


"Ɗan nasa mana, ai hadiminta ne, kuma babu abin da za ta saka shi, ya kasa yi mata"


Sultan ya kalli Nana ya ce "To ko za ki roΖ™a mana Ι—in, duba da mawuyacin halin da yake shiga idan ciwon ya tashi" Nana ta yi shiru ta sunkuyar da kanta.


Sarkin baka ya ce "Kar a yi gaggwa, a bi ta a sannu tukuna, ta yanke hukunci da kanta"


Sultan ya ce "Shikenan, a mayar da kai masauki, kafin na kuma nemanka"


Nana ta ce "Allah ya baka nasara, dan Allah zan yi magana da shi, idan babu matsala a hakan" Sultan ya ce "Babu damuwa"


Hammad ya haΙ—e rai, amma Nana ta tashi ta bi shi waje.


Ta ce "Sarkin baka, dama kana raye? Ƙaisar ya ce mini kashe ka zai yi"


"Nana Asma'u, uban duΖ™usa bai kashe ni ba, sai dai na ji jiki kamar ba zan rayu ba. Shi ya kawo mini magani ma, sannan ya Ζ™ara yi mini kashedi sosai a kanki. Daga nan ma har wasu magungunan ya sanar da ni"


Ta ce "Ikon Allah, sarki ya magunguna ya marasa lafiya? Ina Salamatu da wannan aljanar taka"


Ya yi dariya ya ce "Duk su na nan Ζ™alau"


"To ya aka yi ka san cewa asiri aka yi wa Sayyid?"


Ya harare ta ya ce "Halinki dai yana nan uwar Ι—akina. Mutum mai hankali zai yi abin da mijinki yake yi ne? Abin da nake so da ke, ki Ζ™ara addu'a kar ki yarda da kowa, kunnuwanki da idanunki su zama a buΙ—e komai na iya faruwa idan Allah ya taimake ki wataΖ™ila ya samu lafiya ta hannunki"


Ta Ι—an yi shiru sannan ta ce "Ƙaisar ya nuna mini abubuwa da dama, sai dai ba na son gazgatawa ne, na shiga ruΙ—ani, amma har yadda asirin yake na gani, to amma idan ya rabu da Giyaz iya samun lafiya duka?"


"Ba na ce ba, tun da ban san a kan me da me aka ba shi aikin ba. Kuma ba shi da fuskar da zan tambaye shi. Amma ina jakar da na baki?"


Kafin ta amsa, Sayyid ya fizgi hannunta da Ζ™arfi ya yi gaba da ita.


Bai tsaya da ita ko ina ba, sai da suka je Ι—akin da yake jinya. Idanunsa jawur ya ce "Dan wulaΖ™anci kawai ki je ki tsaya ki na surutun banza da mutumin da ba muharraminki ba"


Ta marairaice ta ce "Haba Shugaba, wa nake da shi a nan daga Ζ™asarmu, yaushe rabon da na ga wani wanda na sani? Kuma Sarkin baka duk da yana wasu abubuwan da nake tantama a kansu, mutum ne da ba zan taΙ“a mantawa da shi ba. Bayan tafiyarka daga gidansa, abubuwa da yawa sun faru, ni a gidan nasa a ka bar ni"


"Ba na son jin koma mene ne ya faru" ya yi maganar yana tsuke fuska.


Ta ce "Haba Shugaba, kar ka manta, maganinsa ya taka muhimmiyar rawa lokacin da ka yi rashin lafiya"


Yayi mata shiru yana huci, tabbas a rayuwarsu da shi a Nigeria ta san shi da azabar kishi.


Ta kwantar da murya, tana shafa bayansa ta ce "Haba Shugaba, dama mutum zai iya fushi da rayuwarsa, tuba nake Ι—an manyan mutane, kuma babban mutum" Ɗan guntun murmushi ya saki, ita ma ta yi masa murmushin.


Ya ce "Yauwwa, ki yi mini addu'a, in ajima za a sanar da Asal da iyayenta, matsayinki a gurina.


Nana ta kwaΙ“e baki ta ce "Na yi maka addu'a, ta mutu mana, nima ban mutu ba da kishiyata ta mayar da ni baiwa saboda tana da kuΙ—i, ga kuma mijina ina kallonsu tare, amma ban isa na ce komai ba".


Tsam ya miΖ™e, saboda ya san idan aka ci gaba da jan maganar faΙ—a za su yi. Ya ce "Ki shirya, idan na dawo yau komai dare, za mu je gurin kayan tarihi na Agadez, kuma zan baki labarin duk abubuwan da suka faru"

Ta yi masa shiru ta cika ta yi fam, kamar za ta fashe.


Ya tausasa murya ya ce "Na san kin yi haΖ™uri, amma ina sake baki haΖ™uri, dan Allah ki saki fuskarki"


"Ni ka rabu da ni, ka je ku lallaΙ“a matar so, da al'adarku ta yarda da ita, ni kuma ka sake ni ku kora ni Ζ™asarmu" Ta yi maganar har da Ζ™wallar baΖ™in ciki.


Ya yi murmushi ya ce "Duk wata matar so a bayanki take Gimbiya Ma vie. Kin ci Agadez kin ci Nigeria" ta murguΙ—a masa baki, ya shammace ta ya yi kissing Ι—in bakinta.


****


Asal ce a gaban Sultan, da Matawalle da Sardauna, ga kuma Tafawa sai Imam Asadullahi, da Imam Hammad sai Mahmoudu.


Matawalle ya ce "Na san za ku yi mamakin dalilin da ya sanya, muka neme ku a yammacin nan, bayan sallar magariba haka.

Mun san za ku ji abin wani banbarakwai, amma mu ma haka nan ya zo mana. Duk ana kan dambarwar Ι—a da Imam Hammad yake da shi, wani abu ya sake faruwa da dole mu yi muku bayani, domin babu yadda muka iya mu ma, sai dai mu na kan tunanin matakin da za mu Ι—auka."


Tafawa ya ce "Mai girma Matwalle, wannan kwana-kwanar ta yi yawa, ka yi mana bayani kai tsaye."


"Kamar yadda ka yi ta bin diddigi a baya, tabbas Hammad ya yi rashin lafiya, ya kuma je Nigeria jinya. Asal na san abin da ki ka gani ya Ι—aga miki hankali kina ta wasi-wasi. Ɗan da Hammad yake da shi, ba Ι—an kowa ba ne face Ι—an matar da ki ka kawo a matsayin kukunsa. Wannan kukun tasa matarsa ce"


AREWABOOKS


Wani irin nannauyan numfashi Asal ta ja, tana jin kamar daga shi ba zata sake jan wani numfashin ba. Gaba Ι—aya sai ta kasa gane me ma ake son a yi mata bayani. Wace ce ma kukun? Take tambayar kanta.

Tafawa ma sak ya yi, yana murza yatsun hannunsa, ya tsare su da idanu Ι—aya bayan Ι—aya, sannan ya numfasa ya ce "Ku na nufin Imam Hammad ya auri wata wadda ba Ζ™abilarmu ba, daga Nigeria har ta haifa masa wannan yaron da na gani?"


Sardauna ya ce "Haka ne"


Ya sake rausayar da kai ya ce "To ina fatan a wannan karon, za ku yi adalci dokar masarauta ta yi aiki a kansa, a yi masa hukunci daidai da abin da ya aikata."


Sardauna ya ce "Tukuna dai, sai mun ga abin da hali ya yi, saboda yanzu hankalinmu na kan samun lafiyarsa"


"Lafiya, wace irin rashin lafiya kenan yake fama da ita? Kuma me ya kai shi Nigeria? Kuma a kan me ya karya dokar masarauta?"


Matawalle ya ce "Wannan duk abu ne da za ka ji daga baya, amma yanzu a kan wannan gaΙ“ar muke, zuwa gaba kaΙ—an za mu duba abin da ya dace a yi"


Wani irin kuka Asal ta fashe da shi ta ce "Hammad, abin da za ka yi mini kenan, ka munafunce ni? Ka cutar da ni, ka ajiye ni hoto ban haihu ba ka je ka haihu da wata. Saboda ka tozarta ni ba ma ka auri Buzuwa daidai ni ba sai wannan Ζ™azama mummunar yarinyar?"


Tafawa ya ce "Rufe mini baki, mutuniyar banza uban waye ya ce ki je ki kawo ta gidan sarauta, a matsayin kukun mijinki, alhalin kin san ba haka dokar masarauta take ba?"


Hammad ya kalli Asal ya ce "Ki yi haΖ™uri, na san na yi miki laifi mai girman gaske, amma ina mai baki haΖ™uri yadda al'amuran suka kasance ba wai da gangan na yi ba. Kin san babu yadda za a yi ina zaune haka kurum na Ι—au jiki na tafi Nigeria na...


"Ka yi mini shiru, babu wata magana da zaka faΙ—a na yarda da kai, maΖ™aryaci...


"Hattara!" Matawalle ya yi mata tsawa.


"Ko me ya yi miki, dole ki ambace shi da girmamawa kar ki kuskura ki faΙ—i wani abu mummuna a kansa, ko me ya yi kuwa. Dan haka ki kiyaye harshenki"


Cikin kuka take cewa "Wallahi sai ka sake ni, ba zan zauna da kai ba, kuma na bar ka da Allah sai ka sake ni"


Sultan ya yi gyaran murya ya ce "Yarinyar kirki, na san za ki ji abin wani iri, amma babu abin da zai raba aurenki da Imam. Haryanzu mu na kan tattauna matakin da za mu Ι—auka amma sai kin bamu cikakken haΙ—in kai kin nutsu. Haryanzu ke ce halattacciyar matar Imam da kowa ya san da zamanta."


A fusace Tafawa ya tashi ya kalli Asal, da gaba Ι—aya ta rikice take kuka ya ce "Ke tashi mu tafi" Ta yinΖ™ura ta tashi ta yanke jiki ta faΙ—i.


Hammad ya taso da sauri ya nufo ta, amma Tafawa ya ce "Kar ka kuskura ka taΙ“a mini 'ya" Ya kalli Asadullah ya ce "Zo ka Ι—auke ta mu tafi"


Hammad ya ce "Ba zai yiwu ba, ba zai Ι—auke ta ba. Kar ya fara taΙ“a mini mata"


"Ni ka ke gayawa kar ya fara taΙ“a maka mata?"


"Ni nake da hurumin Ι—aukarta, ko na taΙ“a ta ban yarda ya taΙ“a mini mata ba" Ya yi maganar yana tsare Tafawa da ido.


Sardauna ya ce "Tafawa ko da an samu rashin fahimta, bai kamata a ce ka hana shi taΙ“a matarsa ba, sai ka gama wannan Ι“aΙ“atun ita kuma ta baka kunya, ai ba a shiga tsakanin mata da miji. Bari a kira barori mata su zo su Ι—auke ta, a kai ta Ι“angaren Gimbiya Bilkisu"


Ya ce "Babu wanda ya isa, ba wanda zai taΙ“a mini 'ya"


Sultan ya ce "Umarni ne, a kaita sashen Gimbiya Bilkisu, idan ta farfaΙ—o ta Ι—an nutsu sai a kai ta gida" Tafawa ya tsaya cak yana kallon Sultan cikin Ζ™unar rai. Ƙaninsa yana ba shi umarni kuma dole ya bi.


*****

Wata kyakykywar matashiya ce ta shigo Ι—akin, ta tarar da ita a zaune tana bawa jaririn Nono. A rikice ta Ζ™arasa da sauri tana faΙ—in "Sister kin farfaΙ—o Alhamdillah, Alhamdillah, Alhamdillah ala kulli halin. Barka da arziki sannu" Ta Ζ™arasa gaban gadon tana rungume Shukura.

Shukura ma ta rungume ta, tana faΙ—in "Na gode sosai, Allah ya saka da alkhairi"


Ta kalli Shukura ta ce "Babu komai, ni dai na gode wa Allah da ya sanya ki ka farfaΙ—o ki ka tashi. Sannu 'yar uwa" Ta sake maganar cikin iyayi da kulawa.


Ta kalli likktar da ta take ta Ι—awainiya da Shukura, ta ce "Sannu da Ζ™oΖ™ari doctor, Allah ya biya ki kema"


Doctor ta ce "Ba komai, yi wa kai ne."


"Yanzu kawo lambar wani a kira miki"


Shukura ta Ι—an yi shiru sannan ta ce "To" Ta bayar da lambar Sagir, aka saka a wayar aka danna kiran wayar"


Shukura ta miΖ™a hannu, ta karΙ“i wayar.

Muryar Yusra ce ta yi mata sallama, ta tsuke fuska ta ce "Ina Baban Haidar"


Wata irin rikicewa Yusra ta yi, ta ce "Shukura ke ce? Ina ki ka tafi muke ta neman bamu ganki ba? Kina ina?"


Sai Shukura ta Ι—an yi saroro, jin yadda Yusra ta rikice da murna.


"Ina nan, idan yana kusa ba shi wayar"


A rikice Yusra ta sake cewa "Baya nan, ki gaya mini kina ina na zo na Ι—aukko ki?"


"A'a ina nan lafiya kalau, idan ya dawo ki haΙ—a ni da shi"


Yusra ta ce "Baya nan, layinsa ya saka a wayata, ni ban san lokacin da zai dawo ba, ki gaya mini kina ina?"


Kamar Shukura ta share ta katse wayar, sai kuma ta gaya mata. Tana can wani Asibitin kuΙ—i, a can wata local government a wajen Kano. Sannan ta Ι—ora da cewa "Amma kar ki gaya wa kowa mun yi waya da ke"


Yusra ta ce "Har mamanki? Tana can hankalinta a tashe fa ita ma"


"Eh har ita, kar ki gaya wa kowa, idan ya dawo ki haΙ—a ni da shi, ina Haidar? Yana lafiya?" Ta yi maganar hawaye na cika mata ido, cike da fargabar ko shi ma ya salwanta.


"Yana makaranta, to kina lafiya cikinki ma yana nan lafiya?"


Shukura ta ce "Eh, lafiya kalau"


"To dan Allah kar ki je ko ina daga nan gurin"


"Tom" Ta faΙ—a a taΖ™aice.


Matar ta kalli Shukura ta ce " 'Yar uwakki ce?"


Ta girgiza kai ta ce "Abokiyar zamana ce"


"Allah sarki, gaskiya daga ji tana sonki sosai ji yadda ta rikice" Shukura ta yi murmushi kawai. Sai dai ta tafi tunanin ta yadda za ta fuskanci Duniya ta sanar da cewa mahaifinta shi ke da alhakin sace ta, da salwantar mata da Ι—a, da kuma mummunan zaluncin da ya yi wa mahaifiyarta da wadda yake tare da ita yanzu. Ita gaba Ι—aya ma ba ta san ta ina zata fara bayanin miyagun ayyukansa a idon duniya ba a matsayinsa na mahaifinta.


****

Nana tana son ta ga Sarkin Baka, akwai maganganu da dama a bakinta, amma Ζ™iri-Ζ™iri Sayyid ya hana. Ga shi ba ta da damar fita idan ba umarnin hakan a ka ba ta ba, tana son sake ganin Nene ma amma babu halin fita.


Zaman Nana a guri Ι—aya, ba fita daga ci sai sha da kwanciya, ya sanya ta Ζ™ara yin kyau, ga lafiyayyen Abinci. Sai dai haryanzu kwanciyar hankali da nutsuwar zuciya ne ba ta da shi.


Tana zaune tana zancen zuci, har bacci ya fara sace ta, ta ji an taΙ“a ta. Ta tashi da sauri tana kallonsa.

"Har kin fara bacci ba ki jira ni ba?"


"Eh, na zata a gurinta zaka kwana ai"


"Idan ma na kwana a can Ι—in, ai ke ki ka ja, kin daina damuwa da ni, ko tausayina ba kya ji"


Ta kwaΙ“e baki ta ce "Garin tausayinka, na kwashi wani cikin na haihu ku kaΙ—a ni Nigeria"


Ya Ι—an marairaice murya ya ce "Haba Ma vie, Sayyid Ι—inki ne fa, ke ba kya kewar Ι—umin jikina ne"


Nana ta kalle shi ta ce "Wane Ι—umin, ai yanzu jikinka ba wani Ι—umi idan ba azaba ba"


Ya rausayar da kai ya ce "Da Ι—in ma akwai, kuma kina jurewa"


Ta girgiza kai ta ce "Amma bai kai na nan ba"


"To ni ki bani Sanyin dan Allah"


Ta tsuke fuska ta ce "Sayyid ka daina taΙ“a ni dan Allah, ni ba Ζ™in ka nake yi ba, amma ka tausaya mini inga yadda al'amuran za su kaya tukuna, ka san dambarwar da ake ta yi haryanzu ni tsoro nake ji kar a yi mini yadda aka yi wa Nene"

Ya kwanta a gefenta ya numfasa ya ce "Ta baki labari kenan?"


Ta jinjina masa kai alamar eh.


"In sha Allah a kanmu wannan muguwar al'adar za ta zama tarihi, dan ba zan yarda na rabu da rayuwata ba"


Nana ta zumΙ“ura baki tana kallonsa, ya ce "Da gaske nake Ma vie" Ya yi maganar sumbatar hannunta.


Ta Ι—an lumshe ido tana kallonsa. Ya ce "Tashi mu je"


"Ina?"


"Zo mu je ki gani mana, ko zan cinye ki ne" Ya yi maganar daga kwnace yana ci gaba da kallonta.


Ta tashi zaune tana faΙ—in "Na sani, ko cinye nin zaka yi. To ka tashi mana kuma ka kwanta"


Ya yi shiru bai ce mata komai ba. Ta waiwaya ta kalle shi, ta ga yana yi mata wannan kallon yana shafa bayanta.


Ta ce "Yane? Ko in kwanciyata ne?"


Ya ce "Allah sarki Hammad bawan Allah, kowa baya so na" Ya yi maganar yana tashi zaune.

Nana ta yi murmushi ta kai hannu ta shafa gashinsa ta ce "To dama wa zai so rigimamme"


"Allah sarki, Ina kewar Ma vie Ι—ina ta da, mai so na da tausayina, ko motsi na yi hankalinta yana kai na, Allah sarki Asmyna ta Nigeria, soyayyarta ta daban ce a cikin zuciyata"


Nana ta ce "Allah sarki Sayyid Ι—ina na Nigeria, da baya ganin kowa a duniyarsa sai Asmynsa kaΙ—ai. Mai kallona da idon tausayi, wanda nake iya gano Ζ™aunata da tausayina a idanunsa, mai yaba duk wani motsina da Ζ™oΖ™arina. Ina kewar Sayyid Ι—ina na Nigeria"


Ya lumshe idanunsa ya buΙ—e ya ce "Wannan Imam Ι—in na Agadez fa?"


Ta kalle shi ta ce "To ga shi nan dai, ban ma san inda ya dosa ba" Ta Ζ™arasa maganar tana murguΙ—a baki.


Ya yi dariya ya ce "Haka za ki ce ko? Ni Ι—in ko? Sayyid Ι—inki ne fa"


"Sayyid nawa, Hammad na Asal"


Ya ce "Wow, sake faΙ—ar sunan na ji?" Ta noΖ™e masa kafaΙ—a.


Ya ce "Shikenan ma, dama Asal ta fiki iya faΙ—ar sunan" Ta harare shi, tare da sauka daga kan gadon. Shi ma saukkowar ya yi, ya wuce gaba ta bi shi a baya. Daga bisani ya jira ta, suka tafi tare. Ƙofar nan da suke bi su fita hanyar saharar nan, suka shiga, sai dai wannan karon canza akalar hanya, zuwa wata matattakala. Tsoro ya fara kama Nana, amma ta kasa magana, sai rarraba ido kawai da take yi.


Wata Ζ™ofa suka iso, ya ce "Kin san ina ne nan muka Ι“ullo?"


Ta ce "A'a"


"Gidan tarihi ne na masarautar Agadez"


Nana ta ce"Wannan dutsen da nake hangowa?"


Ya jinjina kai ya ce "Eh nan ne"


Wani takurarren tsoho suka tarar a bakin Ζ™ofar shiga gurin, yanayin Ζ™ofar ya bayyanar da tsufan da ta yi a Duniya.

Tsohon ya miΖ™e jikinsa na rawa, ya risuna yana gaida Imam Hammad.


Hammad ya amsa cikin girmamawa. Nana ta Ι—an tsaya ta yi shiru, tana nazarin Ζ™amshin turaren da ta ji a gurin, kamar ta taΙ“a jin sa a jikin wani, sai dai ba ta ga alamun a jikin wannan tsohon wannan Ζ™amshin yake tashi ba.


Ya buΙ—e musu Ζ™ofar, suka shiga. Ya kunna makunni, sai ga hasken fitilun ya haske gurin.


Ya ci sunansa gidan tarihi, Nana ta faΙ—a a zuciyarta. Wani irin Ζ™aton guri ne mai kama da falo, da Ζ™ofofi kashi-kashi a gurin.


"Wannan gurin kamar Libraryn Ƙaisar saboda tsufa" Ta Ι—aga kai tana kallon tsawon gurin, jikin dutse ne aka rarake aka yi wannan ginin da Ζ™ofofi. Kanta ne ya sara ta yi shiru tana tunanin kamar ta san gurin nan, ta taΙ“a ganin gurin. A take ta fara jiyo wannan Ζ™amshin da take ji idan ta gan su a wannan Ι—akin tare da Sayyid.


Hammad ya kama hannunta Ι—aya, ya buΙ—e Ζ™ofa suka shiga, a take ta sske rikicewa, jikinta ya hau rawa ta kalle shi ta kalli Ι—akin, ta sake kallonsa ta kalli Ι—akin.


"Sayyid wannan Ι—akin"


"Ɗakin da muke zuwa ko?" Ya yi maganar yana yi mata murmushi.


Ta kalli gadon, da mudubin Ι—akin, komai irin na da sosai da sosai, sai dai yanayin kayan ya nuna, wanda suka yi amfani da Ι—akin masu faΙ—a a ji ne. Ta dafe kanta da take jin wata irin Ζ™ara a ciki, ga Ζ™amshin turaren nan ya cika ilahirin gurin.


"Sayyid wai ya aka yi haka ta faru a zahiri? Kar daga baya ka ce mini mafarki ne, ka fita da ni daga gurin nan kar na haukace Sayyid"


"Ba za ki haukace ba, ki tsaya na yi miki bayani"


Wani irin jiri ne ya din ga Ι—ibarta, ta din ga ganin wasu irin halittu na shawagi a Ι—akin, ga hayaniya da suke yi cikin sauti mara daΙ—in ji.


Jikin Nana na tsuma ta ce "Ka fita da ni daga gurin nan, wasu abubuwa nake gani ka fita da ni"


"Babu wani abun tsoro fa a gurin nan, ki nutsu zan gaya miki komai daki-daki ciki har da abubuwan da suke shige miki duhu a kaina"


Ayshercool 

08081012143


89

LITTAFIN KUƊI NE 1K 0069685771

Aisha Adam stanbic 

08081012143

A hankali Nana take Ζ™oΖ™arin buΙ—e idanunta, zuciyarta cike da matsanancin tsoron, da rabon da ta ji makamancinsa har ta manta, tare da fatan Allah ya sanya ta farka daga wannan mafarkin mara kan gado. A hankali take jin numfashin sa na sauke a fuskarta. Ta buΙ—e idonta sosai ta sauke a kan fuskarsa da ya tsare ta da idanunsa, sai dai kan ta yi wani yinΖ™uri, Ζ™amshin Ι—akin ya mamaye mata hanci, hakan ya sake tabattar mata da ba mafarki ba ne ba zahiri ne. Ta zabura da sauri ta gansu a kan gadon tare ita da shi a cikin Ι—akin dai.

A gigice ta fara Ζ™oΖ™arin sauka daga kan gadon cikin matsanancin tsoro, tana zazzaro masa ido. Sayyid ya riΖ™e ta ya ce "Dan Allah ki daina tsorata kanki, ki nutsu mana. Babu wani abin tsoro a gurin nan"

"Ta yaya zan nutsu, kana caza mini Ζ™waΖ™walwa, na ma rasa me yake faruwa, kuma sannan ka ce babu abin tsoro a gurin"

Ya ce "Zaki fahimci abin da yake faruwar, amma dole ki nutsu, kuma ki saurare ni"  Ya Ι—ago yatsunsa ya kalli zobunan hannunsa, da space Ι—in guda Ι—ayan sannan ya dubi Nana ya ce "Abubuwan da ki ke gani a tare da ni, su na da alaΖ™a da wannan zobunan na hannuna. Nana ta kalle shi ta kalli zobunan cikin rashin fahimta.

"Ina Zoben da na baki, mu na Nigeria?" Ba ta ba shi amsa ba, kawai ta hau Ζ™oΖ™arin tashi ta bar gurin.

Ya din ga kokowa da Nana, amma idonta ya rufe, hanya kawai take nema ta gudu ta bar gurin. Dan gani take idan ta ci gaba da zama zaucewa za ta yi.

Sai da Ζ™yar ya  lallaΙ“a ta ya ce "To shikenan, mu je na mayar da ke mu tafi, tun da ba za ki nutsu ba" Ya riΖ™o hannunta, sai dai duk a tsorace take, su na fita daga wannan Ι—akin ya shiga da ita wani Ι—akin.

Gurin duk an yi wearing Ι—in fitilu, sai dai da ya kunna fitilun gurin ya yi haske. Ta Ζ™ara razana da ganin gurin. Komai na zamanin da ne sosai da sosai.

Wasu zane-zanen mutane ne a manyan frames a kafe, har zuwa kan wasu hotunan da suke dishi-dishi na Black and white na da, zuwa kan hotunan da ake iya gane mutanen jiki sosai wanda ya nuna na baya-baya ne hotunan sai hoton Sultan da ya fita fes. Ɗaya bangon Hoton Sultan ne shi ma, da hotunan Imam Imam na Agadez a jere.

Sai dai mutanen na jikin zanen da na hiton duk masu kyau ne, kuma yanayinsu ya nuna daga zuriya Ι—aya suke.

Sai kuma gefe  wasu Ζ™ananan hotunan a wani Ι“angare na Ι—akin, da suke nuna yaΖ™e-yaΖ™e, da yanayi na zamanin bayi.


Hammad ya ce "Wannan hotunan da ki ke gani, tun daga kan na zanen nan, hotunan wasu daga cikin sarakunan da suka yi gwagwarmaya gurin kafa masarautar Agadez ne.

WaΙ—annan kuma, wasu daga cikin bayi ne, da suka yi wasu laifuka na rashin kyautawa, wanda tun daga zamanin har kawo yanzu, duk wanda aka haifa a zuriyarsu bawa ne, ciki har da wannan dattijon da yake gadin Ζ™ofar gidan tarihi na Agadez. Idan ya mutu dole zuriyarsu za su bayar da wani wanda zai ci gaba da wannan aikin.


SHEKARUN DA SUKA GABATA.


Kamar yadda Nana ta fara karantawa, a cikin littafin Ƙaisar. An sha gwagwarmaya da yaΖ™e-yaΖ™e tsakanin 'yan uwa da suke ciki Ι—aya domin samun damar Ι—arewa karagar mulki. Kowane Sultan da ya zo karaga, akwai kalar mulkin da yake shimfiΙ—awa, wani al'ummarsa su samu sassauci, wasu kuma su shiga halin matsi. Sai dai hawa kan karagar ba shi ne aiki ba, ci gaba da Ι—orewar mulkin, saboda a kowane lokaci ana iya samun masu kawo maka farmaki, a haΙ—a kai da na kusa da kai, a yi maka juyin mulki. Sannan tsugunno ba ta Ζ™arewa duk wanda ya zama Sultan ba, domin bayan kare kansa dole ya kare iyalinsa, idan ba haka ba 'ya'yansa tun da  Ζ™uruciya za a yi ta kashe su, ana gwara kansu da kwaΙ—aita musu kwaΙ—ayin mulki, ta yadda idan ba su kashe junansu ba, za su iya kawar da uban dan su hau karagar mulkin.

Ƙasar Agadez Allah ya albarkace ta zinari, wanda tun a wancan lokacin, shi ne babban dalilin da ya sanya kowa ke kwaΙ—ayin ya hau mulki, aka yi ta yaΖ™e-yaΖ™e ana zubar da jini, tun da aka fuskanci zinaren abu ne mai matuΖ™ar daraja a lokacin.

Suka ci gaba da gudanar da yaΖ™e-yaΖ™e su na mamayar mutane su kafa Daular su. Ana tafe da wannan mulki, wanda mai Ζ™arfi ya kan kifar da na kan mulkin ya Ζ™wata, ya kashe na kan karagar, har aka zo kan mulkin Sultan Azhar.

Zuwan Sulta Azhar ya sauya da yawa daga tarihin Agadez, kowane Sultan yana amfani da wani amintaccen boka, da yake yi masa ta'amalli da Aljanu, domin sanin abin da zai faru da ba shi wata kariya ta mussaman.

Sarki Azhar ya gagari duk magautansa, yana da tarin mabiya. Azhar yana cikin manyan kwamandojin yaΖ™in sarkin wancan lokacin. Kakansa ya taΙ“a zama Sultan, aka yi masa juyin mulki aka rufe shi a kurkuku. Aka kame 'ya'yansa aka mayar da su fursinoni ciki har da mahaifinsa lokacin shi Azhar yana Ζ™arami Nono yake sha. Bayan da ya tasa bai fi shekara sha biyu ba, aka kame shi, aka sanya shi cikin sojojin yaΖ™i. Duk zuriyarsu aka mayar da su bayi, ya tashi da wannan ciwon a ransa, ya zama gawurtaccen Sadauki da ake ji da shi, saboda Ζ™arfinsa. Ashe yaΖ™in sunΖ™uru yake shiryawa Sultan Ι—in lokacin ya shammace shi ya kifar da shi, ya Ι—are karagar mulkin. Ya kame 'ya'yansa ya kashe su, ya kashe matan Sarkin, har ma da sauran 'yan uwansa da yake tunanin za su iya tasowa su nemi su karΙ“i sarauta. 

Ya din ga yaΖ™ar sauran Ζ™asashen da ke kusa da Agadez, yana mayar da su Ζ™arΖ™ashin ikonsa, ya kame baΖ™aΖ™en buzaye ya mayar da su bayi. waΙ—anda suka rage a 'yan uwansa wanda su ma sun tasa, yake ganin za su iya kawo masa tarnaΖ™i ya sanya aka gina wata irin kurku a Ζ™arΖ™ashin Ζ™asa, duk aka zuba su a ciki.

Wannan cikin dutsen da suke ciki, Bayin zamanin Sarki Azhar ne suka rarake shi, suka gina katafariyar fadarsa, kuma a cikinta aka gina kurkun da ya zuba 'yan uwansa.

A cikin kurkukun nan, idan ka mutu a ciki zaka ruΙ“e ka lalace, a cikin rayayyu za ka gama ruΙ“ewa babu mai fita da gawarka. Babu kalar azabar da ba a ganawa fursinoni a wannan kurkuku. Bayi kuma su na aikin Ζ™arfi gurin haΖ™o zinare, da aikinsa a kai wa Sarki Azhar a sarrafa a yi kayan more rayuwa ko a sayar ga maΖ™wabtan Ζ™asashen, ko kuma a yi musayarsu da wani abu mai muhimmanci.

Ya kame bokayen Ζ™asar gaba Ι—aya, aka haΖ™a rami aka cinna musu wuta, a cikin wannan fadar tasa.

Boka Ι—aya ya bari, wanda shi ne ya tallafa masa ya zama Sultan, wanda shi ma iyayensa na cikin amintattun kakan Azhar da ya yi sarauta, kan a yi juyin mulki a kashe su. Bokan nan ya mallaka wa Azhar gangan manyan Aljanu da suke taimaka masa gurin tafiyar da mulkinsa.

Duk wata kafa da zai iya bari da za a iya amfani da ita gurin kawo Ζ™arshen mulkinsa ya toshe ta. Sai da ya fara manyanta, sannan ya auri wata kyakykywar matashiyar budurwa. Ta fara haifa masa 'ya'ya maza. Allah ya Ι—ora masa tsananin Ζ™aunar yaran nan kamar ransa. Sanin a kowani lokaci, ana iya amfani da wata dama a cutar da su, ya sanya ya killace su. Ya sanya bokansa sadaukar musu da wasu Aljanu da za su din ga yi musu hidima.

Ya sanya doka a kan ko bayan ransa, babu wani wanda zai yi sarauta idan ba a cikin yaran nan ba. Duk dokar da ya kafa, babu mai iya yi masa musu. Babban abin da yake bawa al'ummarsa mamaki bai wuce yadda duk wanda ya fara Ζ™oΖ™arin Ζ™ulla wani abu a kan ya kawar da sarkin nan ba, sai dai a wayi gari ya zama gawa.

Sultan Azhar ya shimfiΙ—a mulki da dokoki yadda yake so, ya tara dukiya da haraji, da kuma arzikin zinarin da Agadez take da shi. Duk da haka ya kamanta kawo ci gaba a lokacin, a wani abin talakawa sun samu sassauci, an samu ci gaba a fannin cinikayya a lokacin, sai dai laifi Ζ™alilan sai a kai ka kurkukun Sultan Azhar wanda har abada babu wanda zai sake ganinka, idan kuma ya so sai a gadar wa zuriyarku da wata hidima ga fada da kai da iyalinka har abada.

Sultan Azhar bai bar mulki ya mutu ba, sai da ya tsufa sosai da sosai, yaransa sun tasa sun zama matasa. Bayan ya mutu aka naΙ—a babban Ι—ansa a kan karagar mulki. Shi ma ya Ι—ora daga inda mahaifinsa ya tsaya, kuma shi bai samu tangarΙ—a da 'yan uwansa ba, saboda ya janyo su cikin harkar mulki.

Sai dai mahaifiyarsu ce ta je ta samu bokan mijinta, ta gaya masa kokenta a kan ba ta son kan yaranta ya rarrabu, a kan mulki, ko wani ya kashe wani.

Ya ba ta tabbacin hakan, ta hanyar yi mata surkulle daban-daban a kan yaran nata.

Kasancewar komai nufin Allah ne, da wanda ya yi addu'a, da wanda ya bi hanyar da ba daidai ba ma, yana iya amsa wa kowa idan ya so, Allah ya taimake ta ba su kashe junansu a kan Mulki ba. Shi ma ya yi tsawon rai a kan karagar mulki, sai dai Aljanun nan sun ci gaba  da bibiyar zuriyar 'ya'yan sarakunan, su na ba su kariya. Bayan mutuwar wannan Sarkin da aka zo naΙ—a sabon Sarki, a nan aka samu dambarwa, sai da aka yi hatsaniya aka so yin Ζ™aramin yaΖ™i daga bisani aka Ι—ora Ι—aya daga jikokin Azhar a kan Mulki wato Sultan Sadam. Har a lokacin matar Azhar tana raye haka Bokansa. Ba ta da wani abokin shawara da ya wuce wannan boka. Ta fuskanci kalubale sosai da sosai, saboda yadda magauta suka sako ta da 'ya'yanta gaba da son tarwatsa mata iyali, dan a banΖ™ara Sarautar ta bar gidansu.

Bayan hawan jikanta karagar mulki, a lokacin Bokan nan ya mutu, Ι—ansa ya gaje shi. Shi ma ya samu kyakykywan kusanci da Sultan Sadam a lokacin. Bokan ya ba shi shawarar mallakawa 'yan'yansa Aljanu, domin su Ζ™ara samun tsaro daga duk wani farmaki.

Sarki ya yi shawara da bokan, a kan yana son duk yadda za a yi, ya zamana kar sarauta ta bar gidansu, kar wani daga cikin 'yan'yan 'yan uwansa ko 'yan uwansa su yi sarauta.

Sai ya fara da kafa dokar, duk wanda ya haura shekara talatin da biyar, babu shi babu sarauta a Agadez, sai dai ka na kan mulki ka kai wannan shekarun. Kamar yadda ya zo a tarihi da kakansa, da Sultan Ι—in da ya gabace shi, duk ba su kai shekaru talatin da biyar ba suka hau kan karagar mulki.

Bokan nan ya Ζ™era masa zobuna da azurfa kowanne yana da mallakin Aljani a jikinsa, da wannan zoben za su iya sarrafa aljanun nan yadda suke so.

Tafi a hankali bayan shuΙ—ewar zamaninsa, abubuwa suka ci gaba da juyawa, kowane Sarkin da zamaninsa da kuma yadda yake nasa mulkin.

Sai dai Mallakar zoben nan ya zama sabon tashin hankali, dan daga bisani sai ya zamana wanda yake da zoben nan, shi ne kaΙ—ai zai iya zama Sarki. Sai faΙ—a ya koma kan kowa na son ya mallaki zobe cikin 'ya'yan Sarakuna. Dan sai Zobunan suka zama gado na kowane gida, daga cikin 'ya'yan Sultan Ι—in da ya sanya aka ba shi zobe.

A hankali ya zama doka, duk wanda zai zama Sultan, sai ya zamana bai kai shekaru talatin da biyar ba, kuma sai ya zamana ya mallaki wannan zoben.

Duk wanda ya mallaki zoben, yana da damar sarrafa aljanin da aka Ι—ora wa alhakin Ι—awainiya da mamallakin wannan zobe, da dole sai ya zamana jinin zuriyar Sultan Azhar sannan zai yi masa hidima."


Hammad ya numfasa ya fara nuna mata hotunan nan da bayaninsu ya ce "Kamar yadda yake a babban kundin adana tarihin masarautar Agadez, wannan shi ne Kakan Sarki Azhar, ga mahaifinsa, shi ma ga hotonsa, ga 'ya'yansa ga waΙ—anda suka yi sarauta a cikin 'ya'yansa.

Wannan ita ce Gimbiya Saira, ita ce matar Sultan Azhar, da tun da ya mutu zuriyarsa ce kawai suke Mulkin Agadez ba a sake samun wanda ya Ζ™waci mulki daga hannun zuriyarsa ba.


Nana ta tsare shi da ido, har sai da ya tsargu ya ce "Lafiya kuwa?"


"Sayyid, kana nufin ka na ta'amalli da Aljanu kenan, ta hanyar yin amfani da wannan zoben?"


"Meyasa za ki yi tsalle ki tafi Ζ™arshen labarin? Ki jira na kai da kaina mana"


AREWABOOKS 


Ta Ι—an nutsu tana sunkuyar da kai.

Sai dai ya yi shiru bai ci gaba ba. "Yaya ka yi shiru kuma?"


"Ba na son na ci gaba ki yanke mini hukunci ne haka sama ta ka"


"Ka yi haΖ™uri ba zan yi haka ba, in sha Allah na yi shiru har ka kammala"


Ya kamo hannunta, suka fito daga cikin wannan Ι—akin, ya nuna mata wani Ι—akin ya ce "Wannan Ι—akin, shi ne inda gawarwakin galibin tsofaffin sarakunan Agadez suke, na kusa da shi kuma Ι—akin da a kan binne manyan masu faΙ—a a ji. Ba zan buΙ—e miki ba dan za ki iya tsorata.

Ya buΙ—e wani Ι—akin ya ce "Nan Ι—akin kuma, shi ne Ι—akin da ake sarrafa zinari, a cikin fadar Sultan yake. Duk nacin mutum bai isa ya saci zinare ya fita da shi ba, idan kuwa aka kama mutum a kurkukun nan zai mutu.

Wannan Ι—akin kuma, a ciki duk wani tarihin yaΖ™e-yaΖ™en da Agadez ta yi yake. A nan ake adana duk wani kayan Sultan muhimmai, irin su takalmi, kayan yaΖ™i takobi da sauransu. Shi kuma wancan Ι—akin, wasu daga cikin sassan Ζ™ashi. jikin manyan masu laifukan da aka kashe ne, da Sarakunan da aka yi wa juyin mulki aka kashe su.


Zamani ya ci gaba da jujjuya, hasken addinin Musulunci ya fara bayyana, duk da nisan da Sarakunan Ζ™asar suka yi ba sa jin kira, dan hatta turawan mulkin mallaka ba su yadda sun kassara musu sarauta da tattalin arziki ba.

Tasirin addinin musulunci ya sanya aka fara rage aikata wasu abubuwan, amma ba a daina wasu ba. Tsaface-tsaface da ta'amalli da Aljanu ba a daina su ba, ga su mutane masu tsatstsauran ra'ayi a kan al'adunsu, da tsafi. Domin ma'abota sarauta sun yarda da cewa, duk wanda ya zauna zai ga zama, mussaman yadda zuriya daban-daban suke farautar kujerar ko ta halin Ζ™aΖ™a duk da tushen Ι—aya ne, amma kowa burinsa ya zamana Mulkin a gidansu yake.

Sai dai dokar Sultan Sadam tana nan, ta sai wanda bai kai shekaru talatin da biyar ba ne zai yi mulki, sannan sai wanda yake da zoben nan shi ne zai yi mulki.

Sai dai a baya-baya, aka samu Ι“arkewar faΙ—a a tsakanin zuriyar Azhar, har aka yi Ζ™aramin yaΖ™i, suka zubar wa da juna jini, abin da ba a taΙ“a yi ba a tarihin masarautar. Abin a ya girgiza al'ummar Ζ™asar mussaman ma'abota sarauta, har suka fara tsoron ko Ζ™arshen masarautar ne ya zo, aka samu rikicin da ta kai ga 'yan uwan junan da tun zamanin iyaye da kakanni ba su taΙ“a samun rabuwar kai da ta kai ga amfani da makami ba sai a wannan karon.

A lokacin zuwan ilimin addini da na zamani, da kuma wannan hatsaniya da ta faru, sai aka yi wa dokokin masarautar Agadez kwaskwarima. Domin samar da zaman lafiya da Ζ™ara Ζ™arfafa masarautar sai aka ce sai wanda yake da wasu nagarta da wasu abubuwa masu muhimmanci shi ne zai zamana yana riΖ™e da zoben a kowanne gida da suka gaji zobunan. Sannan aka Ζ™ara yawan zobunan suka zama uku, kowane gida su na da anihin zoben tambari wanda shi ne mai Ι—auke da sihiri da aljanu sai kuma sauran biyu, sannan da abin hannun na tagulla. A zamanin Sultan Ansar, aka yi duk wannan sauye-sauyen, ya Ζ™irΖ™iro Ζ™aramar majalisar masu Ι—auke da wannan zobunan, yadda za a din ga shigar da su cikin sha'anin mulki, da koya musu yadda mulki yake. Aka yi yarjejeniya a kan iya wannan masu zoben ne za su iya zama Sultan, sannan a cikin su duk wanda ya haura shekara talatin da biyar za a karΙ“i zoben daga hannunsa a nemi wanda ya cancanta a ba shi.

A lokacin aka ce duk wanda zai mallaki zoben, domin zama Ι—aya daga Imam, kamar yadda Sultan Ansar ya yi musu laΖ™abi da shi, dole ya zamana yana da ilimin addini, ya haddace kaso saba'in na tarihin Agadez, yana jin wasu yarurrukan bayan yaren su na uwa, da kuma hausa. Domin ya zamana mutanen Agadez su na jin Hausa sosai, saboda yanayin cinikayya da ke tsakaninsu.

Sai dai har a lokacin akwai baΖ™aΖ™en al'adunsu da ba su canza ba, kuma ba a yi wa kwaskwarima ba, ba a daina azabtar da mutane a kurkukun nan ba. Sannan su na Ζ™yamar Ι“akar fata, ta kowace fuska sun daΖ™ile baΖ™aΖ™en buzaye, sun bautar da su, sun hana su motsi, dan kar su yi wani yinΖ™uri su yi musu juyin mulki. Ko a cikin kuyangi, ba a yarda basarake ya yi amfani da baΖ™ar buzuwa ba, saboda kar su haΙ—a zuriya da su, su sanya ran za su samu 'yanci wataran. Kuma baΖ™aΖ™en bayi sun taka muhimmiyar rawa gurin gina daular Agadez, da haΙ“aka tattalin arzikinta, saboda juriyarsu da aiki tuΖ™uru. Sun daga lokacin da suka yi 'yanci, za su iya ajiue aikace-aikacen, kuma su na tsoron su ce za su rama bautar da su da aka yi tun zamanin iyaye da kakanni alhalin kakannin kakanninsu, da su aka kafa Daular kuma sun taΙ“a mulki.

Hukunci na iya zama na kora, zaman kurkuku koma kisa, ga duk basaraken da aka kama, da aure ko mu'amala da baΖ™ar buzuwa. Haka duk cinikayyar da suke yi da sauran Ζ™abilu, ba su yadda auratayya ta haΙ—a su mussaman da baΖ™ar fata, nasu ma ba su aura ba balle na waje. Sannan yana daga sharuΙ—Ι—an da bokaye suka kafa musu, muddin suka yi auratayya da baΖ™aΖ™e, ana iya kawo Ζ™arshen mulkinsu, kuma baΖ™aΖ™e ka iya yin galaba a kansu, su Ζ™wace sarautar baki Ι—aya.

Zamanin Sultan Ansar bayan tabattar da waΙ—anann dokoki, shi ma yana da zobuna da abin hannun tagulla na waΙ—anda za su zama Imam.

Lokacin da aka tabbatar da waΙ—annan dokokin, aka yi musu kwaskwarima, Sultan Ansar yana da tarin 'ya'ya, yana daga cikin dalilan da ya sanya shi Ζ™ara inganta tare da gyara wasu dokokin saboda yana kwaΙ—ayin Ι—ansa Jalaludeen ya zama Sultan a bayansa, saboda kusan duk abin da aka lissafo yana da su. Kuma ya lura akwai zalamar son Mulkin sosai a wasu daga cikin 'ya'yansa, mussaman babban Ι—ansa Saifuddeen.

'Ya'yan suka yi ta zuba ido, domin su ga wa zai ba wa zobunan nan, amma ya Ζ™i bawa kowa, sai daga bisani ya damΖ™a wa Jalaludeen, ya nemi sauran gidajen da suke da zobunan, su ba wa waΙ—anda suka zaΙ“a, a kafa majalisar Imam. Hankalin Saifuddeen da mahaifiyarsa da sauran 'yan uwansa ya yi mummunan tashi, ganin ya Ι—auki zobunan tambari ya ba wa Jalaludeen, duk da ga yayyensa.

Sai dai maimakon a samu Imam shida, sai aka samu biyar aka rasa inda sauran zobunan suke.

Hankalin Saifudeen ya Ζ™i kwanciya, ya tashi hankalinsa da shi da mahaifiyarsa da wanda suke Ι—aki Ι—aya, a kan lallai su san yadda za su yi, ko dai a karΙ“e zoben nan daga hannun Jalaludeen, ko kuma a kashe shi. Sai dai suka fahimci karΙ“e zoben nan, ba abu ne da zai yiwu ba, saboda ya riga ya mallaki Aljanun da aka wakilta tasrifi da zoben.

Duk wani Imam da yake Agadez, askin gashin kai ya haramta a gare shi, haka zalika barin gashin kansa ya haramta. Sannan babu su babu baΖ™aΖ™en bayi, a matsayin kuyangi. Sannan akwai nau'in abincin da ba za su ci ba.

Bayan majalisar Imam ta kafu, da yawa sauran zuriyar, sun shiga taradaddin ina Ι—aya zoben ya shiga?.

A dole Saifudeen ya Ι“oye hassadar da yake yi wa Ι—an uwan nasa, ya ci gaba da Ζ™oΖ™arin ganin bayansa ta Ζ™arΖ™ashin Ζ™asa. Ya din ga bin bokaye, har da na wata Ζ™asar a kan a haukata Ι—an uwan nasa, ko ma a kashe shi, saboda shi ne ya fi dacewa da matsayin da yake kai, amma abu ya ci tura.

Wataran Sultan Ansar ya kira Imam Jalaludeen ya ce masa "Ka Imam Jalaludeen, kana daga cikin manyan dilalan da ya sanya, na dage a kan canza wasu daga cikin dokokin Agadez, wanda za su iya taΙ“uwa. Iyaye da kakanninmu sun tafka kura-kurai, kura-kuran da yakamata a ce mun yi wasu sauye-sauyen da yakamata al'umma su samu sassauci. Sai dai kai nake ganin zaka iya kamantawa wataΖ™ila ko bayan raina. Ragowar zoben da ake nema, yana gurina, idan Allah ya yi ka zama Sultan a Agadez kar ka  danΖ™a shi ga kowa, sai mafi cancanta. Na san da duk farmakin da ake kawo maka saboda damar da ka samu, amma ka yi haΖ™uri ka daure. Sannan zan ci gaba da sanya wa a yi maka duk wani abu na kariya da yakamata. Zan sanya a Ζ™ara sadaukar maka da wasu daga cikin manyan hadiman aljanuna, domin ka samu cikakkiyar kariya. A lokacin an yi ginin zamani, na gidan Sultan, an baro tsohuwar fada ta cikin dutse da ake gudanar da mulki a cikinta.

A zamanin Sultan Ansar, ya samu zaΙ“aΙ“Ι“u, aka gina Ι—akuna-Ι—akuna, a cikin sabuwar masarautar, da hanyoyin tserewa daga cikin gidan, idan an samu farmaki.

Saifuddeen dai bai haΖ™ura ba, ya haΙ—a kai da matarsa, ya aura wa Ζ™anin nasa Ι—aya daga cikin Ζ™annen matarsa Gimbiya Bilkisu.  Saifuddeen ya din ga shiga yana fita, dan kar Jalaludeen ya zama Sultan, ya haΙ—a kai da wasu daga cikin Imam na majalisar lokacin, da ziga su kan cewar lallai su dage, su yi Ζ™oΖ™ari su karΙ“i sauratarsu, mulki ya dawo hannunsu. Masu kwaΙ—ayin mulki suka din ga yadda da zigarsa, wasu kuma suka din ga yi masa kallon ya za a yi ya nemi sarauta ta bar gidansu. Ya din ga ziga su Ι—aya bayan Ι—aya, ba tare da wani ya san yana ziga wani ba. 

Sannan ya koma ya din ga ziga sauran 'yan uwansa, a kan kar su kuskura su yarda su bari, Jalaludeen ya zama Sultan, alhalin duk ga su suna gaba da shi.

A kwana a tashi, Sultan Ansar ya koma ga mahaliccinsa, babu ciwo ba komai, ya yi sallar magariba, ya yanke jiki ya faΙ—i sai gawa.

An shiga cikin matsanancin damuwa da tashin hankali, aka yi masa sutura, sai dai manyan 'yan majalisar Sultan na lokacin, ba su bari an wayi gari ba, suka damΖ™awa Imam Jalaludeen tagullar da kambun Sarautar Agadez, kamar yadda ya bar wasiyya. Sai dai a tsakaninsu ma 'yan majalissar sai da aka so a samu rarrabuwar kai, aka nemi a yi Ζ™aramin yaΖ™i a cikin daren. 

Babban na kusa da Sultan, ya sanya aka je aka Ι—aukko masa Imam Jalaludeen, wanda ya san tun da Sultan ya mutu a kowane lokaci za a iya kashe shi. Abin da ba su sani ba shi ne, tun Sultan Ansar yana kan karagar mulki, suke tsara komai da shi da babban amininsa Matawallen Agadez, wanda shi ma duk zuriyar Azhar ne, sun haΙ—a kakanni.

Aka yi ginin ta Ζ™arΖ™ashin Ζ™asa, daga sabon gidan Saruta, zuwa tsohon gidan Sarauta, da aka mayar da shi gurin adana kayan tarihi na Agadez. An narka dukiya mai yawan gaske, gurin gina sabon gidan nan, saboda yanayin Ζ™asar sahara. Da haka ya saka aka Ι—aukko masa Imam Jalaludeen, aka biyo da shi ta Ζ™arΖ™ashin Ζ™asa, zuwa gidan tarihi, a gidan tarihin ma, cikin kurkukun Ζ™arΖ™ashin Ζ™asa, a nan aka ba shi wannan kambun.


Cikin kuka Sultan Jalaludeen ya ce "Yaya za a yi ina cikin jimami da alhinin rashin mahaifina, amma ku ta naΙ—in sarauta ku ke yi, ni ba zan iya karΙ“ar wannan kayan ba"


"Dole ka karΙ“a, ya kai Sultan Jalaludeen Ansar, wannan wasiyyar mahaifinka ce, da ya nemi muddin mu na numfashi a cika masa ita, tun kan a binne shi ya nemi a naΙ—a ka Sultan a Agadez. Ka zuba ido wayewar gari da an binne mahafinka, yaΖ™i zai nemi ya Ι“arke a Agadez, abin da ba a son faruwarsa a zuriyarku. Dan haka muddin ka na son masaruta ta ci gaba da tsayawa da Ζ™afafuwanta dole ne ka yi haΖ™uri, sai dai a wayi gari da sabon Sultan."

Haka su ka din ga tausar sa, da ba shi baki har ya yi haΖ™uri. Sannan suka ba shi wata Ζ™aramar jakar fata, wadda ta Ι—ara laya girma, amma ba ta kai girman a kirata jaka ba. Suka sanar masa tun Sultan yana raye, ya sanya bokansa ya yi masa ita, domin tsari da kariya daga miyagu. Kuma a matsayinsa na Sultan, zai iya amfani da ita, gurin sarrafa aljanun gidan Sarauta. Can gidansa kuwa tuni har an kame wasu daga cikin 'ya'yansa, ana ta nemansa ruwa a jallo, an tattare matansa an kame. Sai dai ko sama ko Ζ™asa aka neme shi a ka rasa. Washegari da sassafe tun kan a binne mahaifinsa aka wayi gari a kan ganshi an kan karagar Mulkin Agadez da duk wani abu da yake nuna shaidar shi ne Sultan a Agadez.


Ayshercool 

08081012143


90

1K NE A BIYA KUƊIN KARATU KAFIN A KARANTA.

0069685771

Aisha Adam stanbic bank 

08081012143

Mutane sun sha mamakin abin da ya faru. Babu wanda ya isa ya ce dan me? Aka kame waΙ—anda suka yi yinΖ™urin nemansa su kashe shi. A ka yi jana'izar Sultan Ansar. Gaba Ι—aya Jalaludeen baya murna, saboda raΙ—aΙ—in mutuwar mahaifinsu, ga kuma wannan nauyi da ya hau kansa da Ζ™anan shekaru da ba su wuce Ashirin da takwas ba.

Sai dai duk zigar da Saifudden ya din ga yi wa Imam da 'yan uwansa, zamewa ya yi ya bar su, aka kama su sukaΙ—ai.

Mahaifiyar Jalaludeen ta yi masa nasiha sosai da sosai, a kan gudanar da sha'anin mulki.

Duk da ya san tarin Ζ™iyayyar da Saifudden yake yi masa, da wasu daga cikin 'yan uwansa, amma haka ya janyo su a jikinsa, ya basu sarautu domin ya rage musu raΙ—aΙ—in abin da suke ji, kuma ya Ζ™ara musu zaman lafiya da fahimtar juna. Ya yi wa Saifudeen Tafawan Agadez, wanda yana cikin manyan 'yan majalisar Sultan, da suke faΙ—a a ji. Ya yi wa Ι—an uwansa Turakin Agadez, Ι—an wan babansa ya yi masa Sardaunan Agadez. Bayan mutuwar Matawallen Agadez ya naΙ—a Ι—ansa Matawallen Agadez. Ya saka aka saki Imam Imam Ι—in da suka yi zamani tare da su, suka yi yinΖ™urin halaka shi, sai dai gaba Ι—aya ya sauke su daga kan muΖ™amin ya kuma yi amfani da Ζ™arfin mulki gurin Ζ™wace duk zobunansu, ya ce daga lokacin duk wanda zai zama Imam sai ya tantance shi, kuma sai da sahalewar sa. Aka yo caaa a kansa kamar za a cinye shi, su na ganin zai canza musu tsarin Al'ada.

Duk gidajen da suke da gadon, suka bayar da wanda suka zaΙ“o. Hankalin Tafawa ya Ζ™ara dugunzuma bayan da ya san cewa ba shi da makoma, ya san ba zai taΙ“a mulki a Agadez ba, haka 'ya'yansa, saboda rashin zoben, dan ya san Jalaludeen 'ya'yansa zai bawa.

Wata rana Sultan Jalaludeen ya aika aka kira masa Ι—an uwansa, ya zo ya same shi ya dube shi ya ce "Ya kai Ι—an uwana, na san kai ne gaba da ni,  kuma ka so ka yi mulkin Agadez sosai da sosai, amma Allah bai nufa ba, ina mai sanar da kai cewa zobe Ι—aya da aka neme shi aka rasa ya Ι“ace a tsakanin zuriyarmu, yana nan bai Ι“ata ba. Dan haka zan damΖ™a shi a gare ka, ka duba wanda ya dace a cikin 'ya'yanka ka bawa. WataΖ™ila a bayana a iya samun wani ya yi mulki daga gidanka"


Cikin mamaki ya kalle shi ya ce "Amma yaya aka yi ka mallaki zoben da ake tunanin ya Ι“ace?"


"Mahaifinmu ne ya bani shi, bayan nawa da yake hannuna, ya ce bayan ransa na damΖ™awa wanda ya cancanta"

A take Saifudeen ya ji ya Ζ™ara tsanar mahaifinsu, saboda irin wariyar launin fata da aka nuna musu, ya fifita Ι—a Ι—aya a kan su da ya haifa. Wannan abin da Jalaludeen ya yi bai sanya ya rage Ζ™iyayya da jin haushinsa da yake yi ba.

Sai dai duk da haka majalisar Imam ba ta cika ba, ana ta zuba ido a ga wa Sultan zai bawa sauran zobuna biyun.

A lokacin ya auri mahaifiyar Hammad, buzuwar Ζ™asar Algeriya da mahaifinta ya ba shi ita, bayan da yaje taron tattaunawa na bunΖ™asa tattalin arziki. Sai dai cikin ikon Allah, jininsu ya haΙ—u sosai da sosai ta shiga ransa. Imam Jalaludeen yana da kuyangi, da haihu da su, sai dai Gimbiya Bilkisu ta tsani Gimbiya 'yar Algeria Gimbiya Aafaf.

Aurota babu daΙ—ewa, ta haifi Hammad, dan watanninta tara cif ta haifo shi. Gimbiya Bilkisu tana da yara huΙ—u, uku mata sai guda Ι—aya namiji Zahradeen, sai kuma 'ya'yan kuyanginsa mata guda biyu. Ba ta taΙ“a farga Gimbiya Aaafaf tana da juna biyu ba, saboda doguwar mace ce sosai, kuma su kan kwana biyu ba su haΙ—u ba, babu wanda yake shiga harkar wani.

Haihuwar Hammad gaba Ι—aya ya gigita Gimbiya Bilkisu, domin ta gama sakankankancewa Ι—anta zai iya zama Sultan wataran kasancewar shikaΙ—ai ne namiji. Sai dai ta shiga Ι—ar-Ι—ar da tunanin abin da ka iya zuwa ya dawo.

Sultan Jalaludeen Amira yake kiran Aafaf da shi saboda Ζ™auna, ga wani irin so da yake yi Hammad, tamkar shikaΙ—ai ne Ι—ansa. Sai dai ba Bilkisu ce kawai ta shiga Ι—ar-Ι—ar ba, har da sauran waΙ—anda suke sanya ran 'ya'yansu su zama sarakuna wataran. Bayan haihuwar Hammad, aka ci gaba da zuba ido a ga, ta ina sauran zobunan nan biyu za su Ι“ullo.

Bilkisu a tsaye take sosai da sosai, gurin nema wa 'ya'yanta kariya mussaman Zahradeen, ba ta da yadda ko kaΙ—an a kansa abinci ma sai wanda ta tantance ta yarda da shi, sannan zai ci. Ba a daina ta'amalli da bokaye ba har a wannan lokacin.

Hammad kuwa sai dai Sultan ya sanya a yi masa, dan sam Umminsa ba ta iya irin wannan abubuwan ba. Hammad ya tashi da hazaΖ™a da karsashi, sai dai ba ya son mutane. Kwatsam yana da shekaru shida, ya yi wata irin rashin lafiya da sai da aka fitar da rai da shi, da kyar da siΙ—in goshi sannan ya warke.

Daga lokacin Sultan ya Ζ™ara tsananta kulawarsa a kan Hammad. Sai dai a lokacin Mamman, mijin Nene, ya san wanda suka ba wa Hammad guba, kasancewar yana cikin manyan hadiman da yake shiri da Gimbiya Bilkisu. Shi yasa da ya aikata wannan laifin, manyan da suke majalisar kusa da Sultan, suka Ζ™ara kambama abin aka yanke masa wannan hukuncin da babu sassauci a cikin sa.

Shekarun Hammad bakwai a Duniya, ya haΙ—u da Mahmoudu, saboda yawan zuwa da Nene take yi da shi, ganin mahaifinsa a kurku, kuma ta kan je gaida Gimbiya Bilkisu. Sai dai sun Ζ™ara shaΖ™uwa ne lokacin da RaΖ™uminsa ya taka Mahmoudu.

Gimbiya Bilkisu ta so shiga lamarin Maganar mijin Nene, wato Mamman amma Sultan ya ce "Amira, kin ga ke baΖ™uwa ce a Agadez, kuma ni kaina na taka dokar Ζ™asar nan aurenki da na yi, dan dai babu yadda za a yi a hukunta ni ne. Idan na matsa aka saki Mamman matsala na iya faruwa. Dan wasu lokutan a kan al'adu babu abin da ba zai iya faruwa ba. Ina matuΖ™ar gudun abin da ka iya biyo bayan sakin Mamman, duk da na san da girman dokar da na karya.

Har ta rasu, ba ta daina yi masa magiya ba, da roΖ™onsa.

Sai dai rayuwa ta yi wa Hammad tsanani, bayan rasuwar Umminsa. Al'amuran mulki sun yi wa mahaifinsa yawa, bai fiye samun cikakken lokacin saurarar Hammad ba. Ya Ι—auke shi ya ba wa Gimbiya Bilkisu, duk da ya san ba shiri take yi da mahaifiyarsa ba, amma a zatonsa abin ba zai shafi Hammad ba. Mussaman da yake son a Ζ™ara samun haΙ—in kai a tsakanin iyalinsa, baya son kwaΙ—ayin mulki ya yi silar tarwatsewar kawunansu. Sai dai Gimbiya Bilkisu ta din ga samun shawarari daban-daban a kan Hammad. Ciki har da ta kawar da shi ta huta. Dangin Umminsa sun so a ba su shi, amma Sultan ya ce ko da wasa, kar su Ζ™ara yi masa irin wannan zancen.

Gimbiya Bilkisu kan kori Mahmoudu, ta rufe Hammad a Ι—aki, tsawon kwanki a cikin sashinta, idan Sultan baya nan, ta hana shi Abinci ba tare da kowa ya sani ba. Ta san idan namansa za ta din ga sara tana zubarwa, ba zai faΙ—a ba. Sai ta ji Sultan zai dawo zata sake shi. Sai dai su haΙ—u su yi ta kuka da shi da Mahmoudu, wasu lokutan ma Mahmoudun ne yake kuka ban da shi.

Wataran aka kira Mahmoudu, aka ba shi wani lemo Ζ™ato jawur wanda ya ba shi ya ce  "Ka ga wannan lemon, ka je ka ba wa Hammad ya sha, idan ya sha, zan saka a saki babanka, ku tafi gida tare. Amma kar ka gaya wa kowa, kuma kar ka ce ni na baka"

Mahmoudu ya karΙ“a, ya  tafi da murnarsa, ya kai wa Hammad lemon nan. Hammad ba ya tunanin komai idan Mahmoudu ya ba shi abu, ya karΙ“a ya Ι“are har zai kai bakinsa, Mahmoudu ya Ζ™wace, ya gaya masa abin da ya faru.

Hammad ya ce "In dai za a rabu da Abbanka, ka bani zan sha, amma Mahmoudu ya hana shi, cike da Ζ™uruciya Mahmoudu ya karΙ“i lemon ya shanye. Haka ya din ga zubar da jini ta hanci ta baki, har da kafofin jikinsa. Hankalin Sultan ya tashi, saboda ya san kusancin da ke tsakaninsa da Ι—ansa. Ya Ι—auki nauyin maganinsa da Ζ™oΖ™arin zurfafa bincike a kan abin da ya faru amma ba a gano komai ba.

Hammad ya tsallake abubuwa daban-daban na haΙ—ari, na cutarwa a rayuwarsa, wani ya tsallake wani kuma ya rufta ya sha baΖ™ar wahala ya warke. Mahmoudu kuma da yake tare da shi, kullum shi ma cikin farmaki yake da Ζ™oΖ™arin son a yi amfani da shi a cutar da Hammad. Duk wata makaranta da Hammad yake yi, tare suke yin ta da Mahmoudu. Saboda Sultan yana jin zafin abin da ya faru da mahaifinsa, ya san har abada Mahmoudu ba zai daina ganin baΖ™insa ba. Ga gudunmuwar da kakansa, wato Baban Nene ya ba wa masarautar ta Ι“angaren magunan da tsaface-tsaface.

Shekarun Hammad sha takwas a duniya, Imam Sultan ya damΖ™a masa zoben tambari, sai dai ba a son ransa ba, ya kuma damΖ™awa Zahradeen Ι—ayan. Sannan ya shugabantar da Imam Hammad a Majalisar, duk da shi ne Ζ™arami a cikinsu, saboda ko a lokacin ya fisu ilimi sosai da sosai. Nan aka Ι—auki surutun ya yi amfani da Ζ™arfin mulki gurin gwada mugunta, ta hanyar raba wasu gidajen da zobunan tambari, ya ba wa 'ya'yansa da Ι—an Ι—an uwansa.

Sai dai hakan bai ishi Tafawa ba, musamman da ya ga an naΙ—a Hammad shugaban majalisar, ya Ζ™uduri aniyar duk yadda zai yi, ko hakan zai janyo yaΖ™i a Agadez masarautar ta rushe, sai ya yi duk yadda zai yi Asad ya hau karaga, ba zai bari abin da ya faru da su ya faru a kan 'ya'yansa ba, ya zuba ido Jalaludeen ya Ι—ora Ι—ansa a kan karaga ba.

Tafawa ya je ya samu Sultan Jalaludeen, ya ce masa yadda nauyi ya hau kansa kamar haka, bai kamata a ce ba shi da aure ba, dan haka idan ba damuwa ga Ζ™anwarsa nan Asal ya ba shi ya aura.

Sultan ya ce "Tafawa ai Hammad da Asal duk abu Ι—aya ne, kuna duk hukuncin da ka yanke daidai ne. Zan sanar masa, sai dai ina so a bari ya Ζ™arasa karatunsa"

Tafawa ya ce "A'a jinkirin ka iya kawo wani abu daban, a yi auren daga bisani sai ta tare idan ya kammala karatun"

Bayan kwana biyu, Sultan ya kira Hammad, su na zaune su na shan shayi, Sultan ya sanar masa da abin da Tafawa ya zo da shi. A take annurin fuskar Hammad ya Ι—auke, amma bai yi magana ba.

"Na san wataΖ™ila zaΙ“in bai yi maka ba, amma ka san yadda ake ta sururu a kan abubuwan da na aikata. Ka yi haΖ™uri ka karΙ“i auren nan. Hakan shi ne cikar kamala, kuma ka ga 'yar uwakka ce. Sannan na gaya maka, babban burina da fatana, bai wuce ka gaji karagata ba, ina fatan a samu canjin wasu miyagun al'adun a dalilinka" Hammad ya yi shiru, tun da ya zama Imam, ake ba shi kyautar mata duk da Ζ™arancin shekarunsa, amma Tafawa ya babbake ya hana, yanzu kuma ya zo da wannan maganar. Ya jinjina wa Sultan kai kawai bai ce komai ba. Sai dai da ya je sashensa, kamar ya yi wa Mahmoudu kuka, dan dama shikaΙ—ai ne wanda yake sakin jiki da shi, ya gaya masa duka wata damuwarsa.

Mahmoudu ya ce "To mene ne a ciki? Allah ya sanya albarka ya baku zaman lafiya, ai aure abin so ne"

"Ba na son Asal Mahmoudu"

Mahmoudu ya zaro ido ya ce "Ba ka sonta, 'yar uwakka ce fa"

"Ba na sonta kwata-kwata, mahaifinta ba ya Ζ™aunata, muraran yake nuna mini, duk da yana Ι“oye hakan a gaban Abie".


"To ai ba ita ce take yi maka ba, bai kamata laifin mahaifinta ya shafe ta ba"


Hammad ya ce "Amma ka san ba zai Ι—auki 'yarsa ya aura mini haka kurum ba ko? Kamar yadda ya aura wa Abie Gimbiya Bilkisu na sha wahala a hannunta, haka zai aura mini Asal, su ci gaba da azabtar da ni, za kuma ka ce na gaya maka"


"A'a kar ka yi wa auren baki mana tun kafin a yi, in sha Allah babu abin da zai faru sai alkhairi"

Fuskar nan babu annuri ya kwanta, dan gani yake wannan auren kawai takura wa rayuwarsa za a yi, sai kuma ya numfasa ya kalli Mahmoudu ya ce "Ka san wani abu?"


"A'a sai ka faΙ—a"


"Ni wallahi baΖ™ar mace ce take burge ni"


AREWABOOKS 


Mahmoudu ya waro ido ya ce "Dan zatin Allah daga nan, kar ka kuma Ι—aga maganar nan, ka san dai illar hakan, da abin da zai haifar"


Ya gyaΙ—a kai ya ce "Ba ina nufin zan auri baΖ™ar ba, amma ni dai su na yi mini kyau sosai da sosai. Da Umma ta yi maka Ζ™anwa sai na aura"


"Dan Allah ka daina wannan maganar, in dai a Agadez ne, mu ba komai ba ne face masu yi muku hidima"


Hammad ya ce "Babu aya babu hadisi a kan hakan, ina fatan wataran wannan dokar za ta kau, kowa ya auri wanda yake so, kowane kalar fata ya rayu cikin 'yanci ba tare da bauta ba. Har na koma ga Allah ina jin zafin abin da aka yi muku Mahmoudu. Kuma abin da ya faru da ku, yana daga dalilan da ya sanya nake matuΖ™ar son baΖ™aΖ™en buzaye, da ma sauran baΖ™aΖ™en fata, duk farin nan namu fa, duk sunanmu 'yan Afrika kuma baΖ™aΖ™e to mene ne na Ζ™ymar junan"


Mahmoudu ya ce "Ai komai ya wuce ma, dan Allah ka daina wannan maganar kar ma ka sake Ι—aga ta dan Allah"


Ya Ι—an yi shiru sannan ya ce "Na so a ce zan iya ce wa Abie ba zan auri yarinyar nan ba, amma ba zan iya ba"


"Dan Allah ko da wasa, kar ka gaya masa haka, ka yi haΖ™uri dan Allah. Kuma ni gara ka ce ba ka son ta, da dai ka yi waccan kataΙ“orar da ka faΙ—a da farko" Hamamd ya gyara kwanciyarsa, ya ce "Da wasa nake yi maka, kawai dai na gaya maka abin da yake raina ne. Fararen matan duk ba ga su nan ba, duk inda na kalla su ne ba. Amma ina son baΖ™a a ce matata ce, baΖ™a me kyau tubarkallah ka ga da ka na da Ζ™anwa, mai kama da Umma, na aure ta baΖ™aΖ™en mata su na yi mini kyau ma sha Allah"


"Dan zatin Allah ka daina zancen baΖ™ar nan"


Yayi murmushi ganin yadda Mahmoudu da gaske baya son zancen, ya juya masa baya yana murmushi.


Asal ce zaune a gaban Tafawa, yana zaune daga kan kujera. Ya ce "Ki na ji na ko? Na ba wa Ι—an uwanki ke a matsayin matar da zai aura, Imam Hammad dan haka ki shirya a kowane lokaci za a iya Ι—aura muku aure".

Zabura Asal ta yi ta ce "Aure, kuma da Hammad?"


"Eh da shi, mene ne?" Ta sunkuyar da kai tana girgizawa cikin matsananciyar damuwa.


"Dan haka ki je zan sanar da mahaifiyarki a yi shiri"


Tana barin turakarsa ta saka kuka, ta shiga sashen mahaifiyarta. Cikin damuwa ta ce "Kyakykywata Lafiya kuwa?"


"Ammi, Abbu ne ya ce wai aure zai yi mini, dan Allah ban yi Ζ™arama da aure ba? Kuma wai Imam Hammad zai aura mini"

Ta tsuke fuska ta ce "Ban gane ba saboda me? Dama haka ake yi"

Asal ta ce "Dan Allah ni ki roΖ™e shi ya Ζ™yale ni, kar ya aura mini shi ba na son shi"


"Ki kwantar da hankalinki, babu wanda zai yi miki auren dole ina raye".


Mahaifiyar Asal ta tashi ta tafi turakar Tafawa, cikin takaici ta ce "Amma meyasa za ka yanke wannan hukuncin ba tare da amincewar yarinyar nan ba, ba ta Ζ™aunar auren nan fa"


"Saboda 'ya ta ce na isa da ita"


"Amma rayuwarta fa? Ta yaya za ta zauna da mutumin da ba ta so?"


"Ta zauna da shi koma ta yaya ne"


Asal ta din ga bori a kan ba ta son Hammad, ba za ta aure shi ba, dan sam ba ta shiryawa aure a lokacin ba, duk da tana da Ζ™arancin shekaru amma yadda take tsara wa kanta rayuwa sai ta ci Duniyarta da tsinke sannan za ta yi aure.


Can kuma Sultan ya saka Hammad a gaba a kan lalai ya je su gaisa da Asal, duk da sun san juna akwai buΖ™atar su Ζ™ara samun shaΖ™uwa a kuma tsara yadda biki zai gudana. Da to kawai Hammad yake amsa wa Sultan.

Tare da Mahmoudu suka je gurin Asal, sai dai a Ζ™alla sun shafe awa Ι—aya da rabi, Asal ba ta fito ba. Idan ya yi niyyar tafiya, sai Mahmoudu ya hana shi.

Daga Ζ™arshe shi kansa Mahmoudu gajiya ya yi, suka tafi gaba Ι—aya.

Sai dai washegari, Sultan ya kira Hammad, ya ci masa mutunci abin da bai taΙ“a yi ba, wai girman kansa zai sanya ya lalata musu zumunci da Ι—an uwansa. Yarinya ta gama shiri tana jiransa yana zuwa ya yi tafiyarsa. Abin ya yi wa Hammad ciwo, amma ya daure ya bawa Sultan haΖ™uri, ya tashi ya tafi. Sai da ya yi zuwa uku, sannan Asal ta zo. Kallo Ι—aya ya yi mata ya tuna abin da Sultan ya yi masa saboda ita, ransa ya Ζ™ara Ι“aci ya ji wata irin tsanarta ta mamaye shi. Sam Asal ba ta da Ι—a'a. Duk da kasancewarsa yaro Ζ™arami girman sarautarsa ya sanya yana da kamewa da son girma. Amma bai ga hakan a tattare da Asal ba, sai harare-harare da take yi. Ga shi a lokacin shi har cikin zuciyarsa yana son mace mai mamora, Asal kuwa ga yarinta ga babu alamar wani abin kirki a tattare da ita.

Haka Tafawa ya din ga haΙ—a shi da Sultan a kan Asal. Tafawa ya lura idan bai yi a hankali ba, Asal za ta jiΖ™a masa aiki, ga mahaifiyarta sai bala'i take yi ba za a yi wa 'yarta auren dole ba.

Ya same ta da daddare a Ι—akinta, ya kifa mata wani uban mari, da sai da ta ga taurari ya ce "Ke kalle ni da kyau, idan ma babarki ce take ziga ki, to ki shiga hankalinki tun da wuri. Ban haΙ—a auren nan dan ki so ko kar ki so ba. Na haΙ—a auren nan ne domin cikar muradina. Za ki taimaka mini ne, ina son Ι—an uwanki ya gaji karagar mulkin Sultan, dan ba zan bari sarauta ta dauwwama a gidansu ba. Dan haka dole ki haΖ™ura da duk wani abu da ki ke so, domin cikar nawa muradin. Zan aura miki Hammad ne, na wani Ι—an lokaci na samu cikar burina, daga nan ki yi duk abin da ki ka ga dama." Asal ta sha kuka sosai da sosai. Ita ta san Hammad ba shi da wata makusa ko kaΙ—an da za ta nuna a matsayin aibun da za ta ce ba ta son shi, kawai gani take auren kashe mata rayuwa ne. Mussaman yadda Allah ya yi mata kyakykywar halitta.

Ko da ta gaya wa mahaifiyarta abin da Tafawa ya ce, zuwa ta yi ta same shi, tana faΙ—an ya za a yi ita ba da haifar Ι—a ba, a tursasa wa 'yarta saboda cikar muradin wani, tun da yana da Ζ™anne mata a aura wa Hammad Ι—in Ζ™annen Asadullah.

Gudun kar ta Ι“ata masa aiki, ya sanya ya yi mata bayanin ai idan ya aura masa a Ζ™annen Asad, nan da nan za a gano shi, amma wanda suke ba ciki Ι—aya ba, babu wanda zai kawo wani abu. Ya din ga kwaΙ—ai mata abubuwan da za su samu idan Asad ya zama Sultan.

Gimbiya Bilkisu ma har gida ta zo ta samu Tafawa, ta ce "Na ji labarin za ka aura wa Hammad Ι—anka, duk da na san inda ka dosa, na san dalilinka na yin haka, amma kar ka manta da sauran rina a kaba, tun da Zahradeen ma Imam ne, kuma Ι—an Sultan"


Tafawa ya ce "Haba Gimbiya Bilkisu, ai ke 'yar uwata ce, ki zo mu haΙ—a Ζ™arfi da Ζ™arfe mu yi nasarar ganin Hammad bai mulki Agadez ba. Kuma kema kanki kin san alamu sun nuna Hammad yake son ya damΖ™awa mulkin"


Ta ce "Mu haΙ—a hannu, ka yi mini irin yadda ka yi wa wadancan mutanen da suka haΙ—a kai da kai. Kuma idan na haΙ—a kai da kai, waye zai haΖ™ura ya bar wa wani tsakanin Asadullah da Zahradeen iya ruwa fid da kai kawai" Ta Ζ™arasa maganar tana dariya.


Ta shiga gurin mahaifiyar Asal da niyyar su gaisa, amma ta ce mata "Ina fatan idanunki a buΙ—e suke,a kan auren nan da z a a yi wa 'yarki? Idan burinsa ya cika Asadullah ya zama Sultan Asal ba ta da wata makoma. Ita dai mace ce ba sarauta za ta yi ba. Ki bar ganin shi ya haife ta, buΖ™atarsa na biya zai ajiye ku gefe"

Haka aka din ga Ι—auki ba daΙ—i a kan auren nan, Hammad ya din ga fuskantar kalubale daga Sultan saboda yadda Tafawa yake haΙ—a su, har sai da Matawallen Agadez mahafin su Hasna da Al-Husssain ya ankarar da shi, Tafawa haΙ—a shi kawai yake yi da Hammad.


Haka Sultan ya saka Hammad haΙ—awa Asal lefe, na ban mamaki, lefe na 'yar gata. Aka yi gagarumin biki da ya tara manyan mutane, ana ta jinjina yarintar amarya da ango, dan ma dai Hammad a nutse yake sosai.

Bayan an yi aure, Hammad ya tsallaka ya tafi karatu tare da Mahmoudu, ba tare da ya sake bi ta kan Asal ba. Bayan ya zo hutu, Tafawa ya dage sai ta tare. Haka aka ginawa Hammad danΖ™areren gida a cikin gidan sarautar aka saka Asal a ciki.

Tun da Asal ta tare, bai taΙ“a gigin zuwa inda take ba, ta din ga yi masa alwashin tun da ya aure ta, sai ya ga tashin hankali da bala'i. Ta din ga surfa masa rashin mutunci da tijara iri-iri, tun yana jurewa har ya fara gaya wa Mahmoudu zai Ι—auki mataki, amma ya din ga rarrashin sa yana ba shi haΖ™uri.

Bayan sun koma makaranta, ita ma Asal aka mayar da ita makaranta, sai dai aka kama mata gida, saboda makarantar nesa ce da Agadez. Idan ya tafi ko son tuna Asal baya yi. Saboda tashin hankali da rashin biyayya, ango na Ζ™iba shi kuwa ya yi uwar rama.

Tafawa kuma ya din ga nanata mata, duk wani motsi na Hammad, ta din ga sanar da shi. A haka aka shafe shekaru uku da aure, ya mayar da hankali a kan karatunsa, da ginin katafaren gurin cin abincinsa a Agadez.

Ita kuma mahaifiyar Asal ta fara saduda, tare da kwaΙ—aitawa Asal ta kwantar da hankalinta, idan Allah ya sanya ta haifi namiji, babu lallai Asadullah ya yi mulki.

Ko da suka kammala degree na farko, suka dawo Niger, Asal babu abin da ya yi mata zafi da shi, shi ma bu kula ta yake yi ba, duk inda za ta fita yawonta babu ruwanta da neman izininsa.

Wataran da daddare yana zaune a turakarsa, yana duba wasu litattafai ta yi sallama hannunta da tray. Ya amsa mata ta shiga ta ajiye masa ta ce "Ga shayi na dafa maka" Cikin mamaki ya din ga bin ta da kallo. Ya gyaΙ—a kai ya ce "To na gode" Ta na Ι—an murmushi ta tashi ta fita.

Bayan fitarta ya din ga kallon flask Ι—in shayin, ya murza zoben hannunsa, sannan ya kalli kofin a take sai ga wani irin baΖ™in hayaΖ™i yana fitowa daga cikin kofin, shayin ya koma baΖ™i Ζ™irin mai kauri. Ya yi shiru yana mamakin yadda Ζ™iyayyar da take yi masa za ta sanya ta iya cutar da shi, dan tun da ya ga hakan ya san akwai wani abu a cikin shayin.

Har ta fara shirin kwanciya, ya shiga Ι—akin hannunsa riΖ™e da kofin. Bai ce mata komai ba ya zauna a kusa da ita ya miΖ™a mata kofin ya ce "Sha" ta dube shi ta ce "Ai na sha"


"So nake ki sake sha ai". Ta girgiza masa kai tana kallon sa.


Ya murza zoben hannunsa ya shafi saman kofin da yatsunsa, sai ga Asal ta ga abin da ya gani a cikin kofin.


Ya sake kallon ta ya ce "Ki sha, ba za ki kashe ni nikaΙ—ai ba" Ya yi maganar cikin tsawa. Ba ta taΙ“a tunanin zai yi mata kwarjini haka ba, gaba Ι—aya ta rikice ta hau kuka.


"Gaya mini wane ne? Waye ya baki wannan abin ki bani, kuma na mene ne?" Ta hau girgiza kai tana kuka.

"Ki gaya mini kafin na Ι—auki matakin da ya dace" Ta kasa magana ta ci gaba da girgiza kai.


"Shikenan, tun da ba za ki faΙ—a ba, idan na kai ki gaban Sultan kya gaya masa meyasa ki ka yi yinΖ™urin cutar da ni" Ya fice ya bar ta a Ι—akin, hankalinta ya yi mummunan tashi, ta kira lambar Abbanta amma ta Ζ™i shiga, ta karaya ajalinta ya zo a Agadez. Amma kwana uku shiru babu wanda ya kira ta, kuma ba ta sake ganinsa ba.

Kwana na huΙ—u har ta kwanta, ta tashi ta shiga sashensa, ta gan shi a zaune yana cin dabino yana kallon labarai. Yana ganinta ya tsuke fuska ya tashi ya bar mata falon. Ta tsaya a falon tana wasi-wasi, sai dai ta shiga lissafin halin za za ga shiga idan ya tona mata asiri, ta san duk abin da za a yi mata ba za ta iya tona wa mahaifinta asiri ba. Ta daΙ—e tana tufka da warwara ta ga dai ba ta da sauran mafita.

Dan haka kawai ta bi bayansa, gara duk wadda za a yi, a yi. Sai dai da ta shiga kawai ta tarar yana Video call da wata baturiya. Wani abu mai Ι—aci ya tsirga mata ta tsaya tana kallon kyakykywar fuskarsa mai cike da Ζ™uruciya yana murmushi.


Ayshercool 


91


Bai daina wayar ba, kasancewar malamarsa ce a faransa. Sai dai bai bari ta fuskanci hakan ba. Ta Ζ™arasa gabansa cikin Ζ™unar rai da wani abu da ta kasan gano ma mene ne a ranta. Ta je ta tsaya masa a ka. Bai kula ta ba, ya ajiye system Ι—in, ya fara Ζ™oΖ™arin kwanciya. Ta zauna a gefen gadon ya ce "Imam gurinka na zo"


"An sake aiko kin ne?" Ta girgiza kai cikin sanyin jiki.


"FaΙ—i abin da ya kawo ki zan kwanta"


"Dan Allah ka yi haΖ™uri" shiakΙ—ai ne abin da ta iya furtawa, ta fashe da kuka.


"Na yi haΖ™uri da aka yi me?"


"Abin da na yi maka, wallahi ba dan san raina ne ba"


Hammad ya ce "Ba da son ranki ba? Bayan kin gaya mini ba kya so na, ba kya Ζ™aunar zama da ni, sai na yi dana sanin aurenki, ai ba abin mamaki ba ne ba dan an haΙ—a kai da ke an cutar da ni. Amma ko ba ki kalle ni a matsayin miji ba, yakamata ki kalle ni a Ι—an uwanki ki yi haΖ™uri mu zauna lafiya. Koma waye ya saka ki, ku sani ba zan mutu ba sai wa'adin da Allah ya Ι—ibar mini ya yi "


Asal ta din ga kuka tana ba shi haΖ™uri, dan ba ta yi zaton zai ma rufa mata asiri na kwanakin da ya yi ba.

Daga Ζ™arshe ya ce "Tashi ki je babu wanda zan gayawa"


"Dan Allah da gaske?" Ya tsare ta da ido, sai kuma ta nutsu ta ce "Na gode sosai da sosai, ba zan sake ba in sha Allah"


"To ban guri zan kwanta"

Ta ce "Dan Allah" sai kuma ta yi shiru.


"Mene ne kuma?"


"Dan Allah wace ce wadda ku ke waya da na shigo?"


Kawai ya kwanta ya share ta. Yana jin yadda take kuka, ya hau baccinsa, saboda haryanzu yana jin Ι—acinta, a kan yadda ya iya danne abin da yake ransa ya yi wa iyayensu biyayya, amma ita fuskarta a tasa ta gaya masa, ba ta son sa ba ta Ζ™aunarsa.

Kasancewar ya saba baccinsa shikaΙ—ai a Ζ™aton gadonsa, ya sanya shi Ζ™oΖ™arin yin juyi, amma ya ji kamar an yi masa dabaibayi. Asal ce a jikinsa tana ta bacci. Ya yinΖ™ura zai ture ta saboda yadda ya ji shi wani iri saboda rashin sabo. Amma ta hana shi hakan."Ke ni fa kin matse ni, ki koma Ι—akinki mana" Ta yi masa shiru duk da tana jin sa. Ƙarshe dai asancewar su 'yan Adam lafiyayyu, ba su bujirewa abin da gangar jikinsu ta buΖ™ata ba.

Tun daga lokacin Asal ta Ι—an nutsu, musamman da take tsoron, kar wataran ya faΙ—i abin da ta yi masa. Duk da ba daina tsiyatakunta ta yi ba, idan ta bushi iska tana yi. Shi kuma baya son duk wani dalili da zai sanya a ga gazawarsa ko ya yi Ζ™orafi a kanta.

Hankalin mahaifiyarta ya koma kan ganin Asal ta samu juna biyu, saboda zigar da Gimbiya Bilkisu take yi mata, a kan lallai ita ma ta yi Ζ™oΖ™arin ganin, 'yar ta ba ta zama abar morar Tafawa da Ι—ansa ba kawai. Dan ta san dole idan Asal ta haihu ta jiΖ™a musu aiki.

Shi ma Ι“angaren Hammad, sai Allah ya jarrabe shi da matsanancin son 'ya'ya.

Gefe guda Tafawa bai fasa sanya Asal, yi wa Hammad binne-binne ba. Sai dai babban abin da yake ba shi mamaki shi ne yadda abubuwan ba su fiye tasiri a  kansa ba, har kiran Asal yake ya Ζ™are mata zagi, ya yi zaton ko ita ce ba ta yin aikin dai-dai, duk da wasu lokutan tana tsoron asirinta ya Ζ™ara tonuwa.

Aka tafi shekara ta shida da aure, a lokacin ne Hammad haΖ™urinsa ya fara Ζ™arewa, saboda haihuwa yake so, kuma ba dan komai ba shi kawai yaran yake so. Duk Imam Ι—in Ζ™asar su na da aure da 'ya'ya amma shi shiru. Ya ce wa Asal su je Asibiti a duba ko lafiya, amma ta ce ba za ta je ba, ya kaΙ—a ya raya ta ce ba zata ba.

Ya ce mata tun da haka ne, shi aure zai yi, ko ya mallaki kuyanga, dan saboda azabar kishinta ya sanya babu ruwansa da barorinsa.

Tun da ya faΙ—i haka ta hau rashin lafiya, Sultan ya je duba ta, ta din ga yi masa kuka a kan ya roΖ™i Hammad kar ya yi aure, yayi haΖ™uri tana addu'a ta san za ta haihu wataran.

Bata taΙ“a tunanin ta fara son Hammad har haka ba, sai da ya yi zancen aure, dan har iΖ™irarin kashe kanta ta yi. Tafawa ya samu Sultan har da kukan munafunci a kan ya saka baki, kar ya rasa Asal, ya rarrashi Hammad.

Ganin yadda Asal ta gigice, ya sanya Sultan ya din ga rarrashinta, ya samu Hammad ya ce "Hammad, na san kana yi mini biyayya, kuma kai mutum ne mai haΖ™ur da juriya, dan Allah ina son ka sanya a ranka, rashin haihuwa jarrabawarku ce. Kuma ba a san me Allah zai yi nan gaba ba, dan Allah ka yi haΖ™uri da batun auren nan, kuma ka daina yi mata zancen haihuwar nan, saboda a samu hankalinta ya kwanta."


Karo na farko Hammad ya buΙ—e baki zai yi magana, amma Sultan ya dakatar da shi ya ce "Baka saba haka ba, kar ka fara a wannan karon, kai mai haΖ™uri ne, a wannan karon ma ina son ganin tasirin hakan a gare ka" Ya haΙ—iye yawu mai zafi, idanunsa suka yi jawur. Ya din ga zuwa Asibiti shikaΙ—ai aka duba shi aka ce masa lafiyarsa Ζ™alau.

Asal kuma ta ci gaba da yi masa kuka da magiya a kan ya yi haΖ™uri su ci gaba da addu'a, ta san wataran za ta haihu, amma ya bar maganar Ζ™ara aure, dan da gaske idan ya yi aure sai ta kashe kanta. Ya so ya yi mata magana a kan to ta bari su je Asibiti, amma ya tuna abin da Sultan ya ce masa, dan haka a dole ya ja bakinsa ya yi shiru ya ci gaba da addu'a.

Duk wanda ya yi alkhairi fatansa ya yi masa addu'a Allah ya ba shi haihuwa mai albarka, duk inda ya ji maganin haihuwa, da ya yadda da ingancinsa, sai ya karΙ“o ya kawowa Asal. Shi kansa Sultan abin ya dame shi, ba yau ba gobe cikin yi wa Hammad addu'a yake, ganin yadda yake ruΙ—ewa idan ya ga 'ya'ya, duk wanda ya haihu a masarauta muddin ya ji labari, sai ya yi masa kyauta mai tsoka ya ce shi ma a yi masa addu'a.

Matawalle ya samu Sultan ya ce "Anya ba ka ganin kamar an cutar da Imam Hammad da yawa, da an bari ya jarraba auren wata matar mu gani ko Allah zai sanya a dace"


Sultan ya girgiza kai ya ce "In sha Allah zai ga daidai a rayuwarsa. Ina jin tausayin Asal ne, gaba Ι—aya hankalinta a tashe yake, amma a Ι—an Ζ™ara haΖ™uri a ci gaba da addu'a. Kuma ka san mahaifinta ba ya raina abin magana, yanzu sai abin ya zama na surutu.

Ita kanta Asal abin ya dame ta, mussaman ganin yadda Hammad Ι—in yake damuwa da lamarin 'ya'ya, sai dai baya yi mata maganar. Tun da Ζ™ananan shekaru, Hammad ya haΙ—u da larurar hawan jini ake ta fama.

Asal ta Ζ™ara shiga tashin hankali, ganin yadda ake Ζ™ara yi wa Hammad tayin matan aure, ga shi matan ma farmaki suke kawo masa, saboda yadda siffofin kamala da cikar zati ke bayyana a tattare da shi. Su kansu kuyangin gidan su na neman su zama mallakinsa.

Sai dai a ransa ko zai yi kuyanga, baΖ™aΖ™en nan yake so ba farare ba. Duk ya kawar da kansa saboda Asal.

Wataran ya fito zai fita, wata hadima ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi ya ce "Sa'ada na daina ganinki kwana biyu"


"Allah ya taimake ka, na yi rashin lafiya ne"


"Subhanallah, ai ban sani ba, kin rame sosai da sosai. Maza ki je a duba ki, kuma ki ci abinci sosai, kin fi kyau lokacin da ki ke da Ζ™iba, Allah ya sauwwaΖ™e" wasu lokutan Hammad akwai raha, saboda a cewarsa hakan zai Ζ™ara masa kusanci da hadimansa, shi ba ya son wannan tsoron nasa da suke yi.

Ta risuna cikin girmamawa tana murmushi ta yi masa godiya. Aikuwa ta sha bala'i a gurin Asal, Ζ™arshe ta kore ta daga sashen girke-girken gidan, zuwa wani abin daban. 


Asal ta saka masa kukan, dan me zai kula wannan hadimar, sannan ya yabi jikinta. Ya din ga rarrashinta ya ce shi ba da wani abu ya yi ba.

Haka rayuwa ta ci gaba da tafiya, ana tursasa Hammad jure abubuwa da dama Saboda Asal.

Kwatsam Tafawa ya kira Asal, ya ce ta je ta same shi, sai da gabanta ya faΙ—i tana zaton ko wani laifin ta yi. Ya kira ta cikin turakarsa. Ya Ι—aukko mata wata 'yar Ζ™aramar laya, ya ba ta ya ce ta je ta samu wani guri da ido ba zai kai kanta ba, inda Hammad yake zama ta saΖ™ale ta.

Ta yi shiru tana kallon layar, amma babu yadda ta iya haka ta karΙ“a ta tafi da ita. Ta din ga tunani ta saka ko kar ta saka. Saboda ba ta san ta mece ce ba. A iya zaman da suka yi tsawon shekaru tare, ba za ta iya cewa ga wani abu na cutarwa da Hammad ya yi mata ba, sai ma shi da yake shanye abubuwa da dama take yi masa, komai cutarwar hakan a gare shi.

Cikin dare yana tsaka da barci, ya ji tamkar ana girgiza gadon da yake kai, ya din ga ganin wasu irin halittu marasa kyan gani da tsoratarwa. A haka ya wayi gari kansa na neman juyewa, tun gari ya waye ya daina magana. Asal kanta sai da ta tsorata. Sai da suka kwana biyu da kyar yake iya cin abinci, sai ya din ga abu kamar baya cikin hayyacinsa. Tafawa kuma ya din ga kiranta yana tambayarta duk halin da ake ciki.

Sai da ta ga da gaske baya magana, ko majalisa baya fita, ta tsorata ta sanar da Sultan halin da ake ciki. Aka kai shi Asibiti amma aka kasa gane abin da yake damunsa. Sai dai jininsa da yake hawa fiye da kima. Ya yi jinya sosai da sosai.

Da kyar ya warke, sai dai Tafawa bai haΖ™ura ba, gefe babar Asal ta bazama neman maganin haihuwa tana ba wa Asal. Sai dai kwatsam! Ita ma ta haΙ—u da jinya, ciwon suga ba ta san tana da shi ba ya yi ajalinta. Asal ba Ζ™aramin kaΙ—uwa ta yi ba, da rasuwar mahaifiyarta tamkar za ta zare. Hammad ya yi ta rarrashinta yana ba ta baki.

Tafawa bai samu zama ba, ya tashi nan ya faΙ—i can, duk domin ganin burinsa ya cika, gaba Ι—aya rayuwarsa ba shi da cikakken sukuni, haka nan ya hana Asal ta zauna lafiya tare da mijinta. 

Ya zamana ku san kullum ba shi da cikakkiyar lafiya, yau da lafiya gobe babu.

Tafawa ya fara magantuwa a kan yawan rashin lafiya da Hammad yake yi, yakamata ya sauka daga kan shugabancin Majilisar Imam, a bawa wani. A majalisar Sultan aka soke maganar da ya kawo.

Hammad kawai yana tafiya ana ganinsa, amma a cikin jikinsa shikaΙ—ai ya san abin yake ji. Ko Asal bai fiye sakin jiki da ita ya gaya mata damuwarsa ba, saboda sam ba ta da alΖ™ibla, kuma tsawon shekaru da suka shafe tare, ba ta iya fahimtar damuwarsa rashin lafiya kai tsaye, sai idan tana da buΖ™atar wani abu a gurinsa.

A haka ta sake neman komawa karatu, lokacin Hammad ya karaya da neman haihuwa. Idan yana salla har kuka yake yi, abin yana burge shi ya ga mutum da Ι—an uwansa sun haΙ—a kai, shi kuma ba shi da wanda suke ciki Ι—aya. Mahaifinsa kuma ayyuka sun yi masa yawa, matarsa kuma bai gama gane kanta ba. Dan haka duk wani rikicinsa, shi kuma ba ya gajiya. Wasu lokutan ya na jin daΙ—in ya bi Mahmoudu gurin Ummansa, su je su wuni, su ci abinci tare. Duk da yana matuΖ™ar jin nauyinta, na abin da aka yi mata a masarautarsu, sai dai bai taΙ“a ganin hakan a fuskarta ba.


Ya yi shiru yana kallon Nana, da ta yi shiru tana saurarensa.

"Ya ka yi shiru kuma?"


"Na gaji, kuma bacci nake ji"


Ta ce "A'a wannan wayo ne na kar ka Ζ™arasa mini, dama ni Ζ™arsheΖ™arshen nan, ba jin daΙ—insa na yi ba, gara ma farkon labarin tun da tarihi ne."


"Saboda zancen Asal ne?"


"Zan iya cewa eh Ι—in ma, saboda mutane kaΙ—an na tsana a Duniya, kuma ta shiga cikinsu" Ta yi maganar tana tsuke fuska.


"Amma meyasa?"


Nana ta ce "Kawai ba ta yi mini ba"


Hammad ya yi shiru ya ce "Ba na tunanin kishi ne kawai ya sanya ki ka faΙ—i haka, akwai wani dalili, ba kya faΙ—ar magana haka kurum mara ma'ana"


Ta Ι—an gyaΙ—a kai ta ce "Ba mai ma'anar ba ce gaskiya, mu je a haka kawai, kishi ne ya sanya na faΙ—i haka. Yanzu dai ni ka tsallake nan, ka gaya mini yadda aka yi ka din ga wasa da hankalina, da yadda ka gane ni amma ka share ni, nake yi wa matarka aiki cikin Ζ™asΖ™anci da wulaΖ™anci. Kuma alhalin ka na iΖ™irarin ka na so na. Har kuka na yi mata, da ta ce za ta kawo ni Agadez na ce mata ina da jariri, amma buΙ—ar bakin matar nan ta ce ni ta shafa, tun da talaka ce ni dole na yi abin da take so. Ba zan manta wasu abubuwan da ta yi mini ba na cin mutunci har abada"


Ya Ι—ago da fuskar Nana tana kallonsa ya ce "Ba wannan ne dalilin da ya sanya ki ka ce ba kya sonta ba, akwai dalili. Wannan ba halinki ba ne, idan wannan dalili ne da abin da na yi miki ba za ki sake zuwa inda nake ba"


AREWABOOKS 


Ta kawar da kanta gefe ta ce "Ka Ζ™arasa mini kawai, mu bar wannan maganar"


"Asmy, Asal ko ba aure tsakanina da ita matata ce, ban kuma gaya miki halin da muke ciki, domin na tozartata ba, iya abin da na sani na sanar da ke game da zamantakewar mu, saboda shi ne mahaΙ—in labarin rayuwata da ke"


"Ai dama ban ce kar ka so ta ba, ka je ka yi ta son nata"


Ya ce "Ai ba zancen so muka yi da ke ba, ki yi shiru mu Ζ™arasa an kusa fara kiran Asuba"


"Ba na son ji" Ta yi maganar tana kifa kanta tare da tsuke fuska.


"Merci ma viee, ba na son ki din ga Ι“ata ranki, mun bar wannan maganar tun da ba kya so, yadda ba na son kowa ya raΙ“e ki, ke ma haka ne na sani, kuma na san kin yi Ζ™oΖ™ari kin yi haΖ™uri sosai da sosai da juriyar da ki ka cancanci a sara miki, amma ki yi haΖ™uri mu Ζ™arasa maganar, daga Ζ™arshe duk hukuncin da ki ka yanke mini, zan karΙ“a"


Ta Ι—ago kanta, zuciyarta na yi mata wani irin zafi, azababben kishin Asal yana taso mata, babu abin da yake Ζ™ara Ι“ata rai irin cin mutuncin da Asal ta din ga yi mata a matsayin kishiyarta.


"Kin huce mu ci gaba?" Ta yi masa shiru.


Ya ce "Matso na rungume ki, ki nutsu sai mu ci gaba" Ya Ζ™ara matsawa kusa da ita, ya rungumota jikinsa, yana murmushi. Ta kwanta lamo a jikinsa yana shafa bayanta a hankali.

A ransa ya ce "Asmy, ba za ki taΙ“a jin rabi a kwatankwacin abin da nake ji a kan ki ba, ina Ζ™aunarki ina kishinki, Allah ya bamu haΖ™urin zama da juna"


Asal kuwa na can a tsaye, tamkar ta haΙ—iyi taΙ“arya, idanunta suka sauka a kan agogon bangon Ι—akin. Idanunta sun bushe, zuciyarta ta Ζ™eΖ™ashe sai raΙ—aΙ—i da idanun kawai suke yi mata.

Haryanzu ta kasa yadda Hammad ne yake da wata matar, matar ma baΖ™ar fata da a kyau ba ta kai ta komai ba. Babban abin da ya Ζ™ara rikita ta bai wuce batun Ι—a da Tafawa ya tabattar mata da Hammad yana da shi ba, har Ι—an shekaru biyu ba. 

Zuciyarta ta din ga bugawa da sauri da sauri, tsawon lokacin nan ba ta taΙ“a tunanin son da take yi wa Hammad ya kai haka ba, ashe duk abin da take yi bonono take rufe Ζ™ofa da Ι“arawo. Tana zaman zamanta ta janyo masifa da kanta jikinta. Ta din ga tunanin ko dai wata Ζ™ulla-Ζ™ullar ce ta daban aka yi. Sai kuma ta tuna babu yadda za a yi Nana ta samu zarafin shiga har sashen Sultan, su keΙ“e da Hammad idan ba matarsa ba ce ba. Kenan Sultan ya goyi bayan abin da Hammad ya yi na auren baΖ™ar fata da ba Ζ™abilarsu ba?. Kawai ta Ι—ora hannu a ka ta rushe da kuka, hawaye ya Ζ™i zubo mata sai azabar zafi da zuciyarta take yi.

Gimbiya Bilkisu ce ta shigo Ι—akin tana faΙ—in "Asal lafiya kuwa?"


"Na shiga uku na lalace Gimbiya, wallahi Hammad ya cuce ni ba zan yafe masa ba. Kuma wallahi sai ya rabu da ita, an cuce ni an cuci rayuwata"


Ta rungume Asal tana rarrashinta, ta ce "Ki yi haΖ™uri, ki daina wannan kukan kar ki samu matsala, ki kwantar da hankalinki na san Sultan ba zai Ζ™yale shi ba, zai Ι—auki mataki" Asal ta ci gaba da kuka da babu abin da yake Ζ™ara mata sai nauyin zuciya.


*****

Imam Hammad kuwa a hankali ya Ι—an Ι—ago fuskar Nana ya ce "Bacci ki ke yi ne?"


Ta girgiza kai alamar a'a.


"To tashi mu ci gaba" Ta noΖ™e kafaΙ—a tana Ζ™ara rungume shi.

Ta ce "Imam ka ci gaba mu yi mu bar gurin nan, Aljanun gurin nan sun fara tsorata ni, kar a samu matsala"


"Kina ganinsu ne?"


"Su na bayyana a siffofi daban-daban, tsofaffi tukuf da matasa da wasu halittun daban, duk ina ganinsu addu'a kawai nake yi tun Ι—azu"


"Ni da ke duniyarm daban take, Ζ™alubale iri Ι—aya, Ubangiji Allah ya bamu lafiya rayuwar Hammad".

Ta sake lafewa a jikinsa ta ce "Ka ci gaba to"


Ya numfasa.


Rayuwa ta ci gaba da tafiya, Hammad na fuskantar suka da Ζ™alubale kala-kala. A kwana a tashi ya haΙ—u da larurar zafin jiki, idan jikinsa ya Ι—auki zafi tamkar an hura wuta. Babu wanda ya sani sai Asal, dan ya fi kama shi cikin dare, ita ta Ι—auka kawai normal zazzaΙ“i yake yi sai ta yi masa sannu kawai ta ci gaba da sabgoginta.

Sultan ya mallaka masa wannan jakar fatar mai kama da laya, wadda ita ma a cewarsa ta tsari ce, kuma tana Ι—auke da aljanun da suke yi wa mamallakanta hidima. Duk lokacin da ya murza zobensa, ya kan gansu a suffar tsuntsaye, irin wanda bai taΙ“a gani ba a duniya, ko suffar wani abun daban. Wasu lokutan ko be murza zoben ba, ya kan gansu, ko ya din ga ganinsu a barci. Duk da ba shiri suke yi da Yayansa Zahradeen ba, saboda Gimbiya Bilkisu ta shiga tsakaninsu, amma ya taΙ“a tambayarsa, ko yana ganin wannan tsuntsayen shi ma idan ya murza zobunansa. Zahradeen ya ce masa baya ganin komai, an ce duk mai zoben yana iya ta'amalli da aljanun jikin zoben, amma shi baya ganin komai. Ya tambayi Hammad ko yana gani shi. Ya ce masa aa saboda ya karanta tarihin zobunan a littafin Kundin Agadez ne ya sanya ya tambaye shi. Haka ya tambayi sauran Imam Ι—in, su ma dai bai ji alamun akwai wanda yake ganin wani abu ba. Abin da bai sani ba, tun zamanin kakansa, aka canza zobunan, na hannunsa ne kawai na Ζ™waran da babu wanda ya sani, sai mahaifinsa da kakansa, sai kuma marigayi Matawalle.

Kwatsam tafiya ta kama Sultan, ga taron sarakuna da za a yi. Sai ya wakilta Hammad ya ce yaje ya wakilce shi. Nan da nan aka hau surutun da me bai wakilta kowa a majalisar sa ba, zai wakilta yaro Ζ™arami, maimakon ma a ce a cikin Imam Ι—in a zaΙ“i wanda suka fi shi shekaru.

A lokacin Hammad bai daΙ—e da buΙ—e sabon branch Ι—in gidan abincinsa a MaraΙ—i ba, ya wakilta cousins Ι—in sa Hasna da Al Hussain a matsayin masu kula da gidan cin abincin.

Babban abin da yake Ζ™ara Ι—aga wa masu son ganin bayansa hankali, bai wuce yadda mutane suke son sa ba. Saboda ya iya shugabanci, shi wannan Ζ™yamar ma da ake nuna wa baΖ™aΖ™en buzaye ba ya yi. Yana damuwa da lamuran na Ζ™arΖ™ashinsa sosai da sosai, wasu lokutan ma kamar ba basarake ba, saboda yadda yake alaΖ™a da su. Ga kuma girmama shi da suke yi tamkar Sarki. Hasali ya fi nuna saurata da izzarsa a lokacin da yake cikin 'yan uwansa masu Sarauta. Ga shi manyan mutane na son sa, su na son mu'amala da shi, saboda ladabinsa, da iya magana, fiye da sauran Imam, har ma da 'yan majalisar Sultan Ι—in, mussaman da duk wanda ya ga Sultan ya ga Hammad, ya san jininsa ne.

Yana ta shirye-shiryen tafiyar taron nan Niemey, a lokacin ga shi nan ne kawai, kansa kamar zai Ι“are saboda ciwo.

Yana kwance cikin dare tare da Asal su na bacci, ya yi mafarkin wani sanye da baΖ™aΖ™en kaya, yana soka masa allura a ka.

Ya farka a razane, sai dai ya din ga jin raΙ—aΙ—in allurar nan a zahiri. Ya sanya hannayensa biyu ya dafe kansa, yana rintse idanunsa yana ambaton Allah, amma kan tamkar zai yi bindiga. Ya tashi zaune da kyar ya yaye bargon da ya rufe jikinsa kawai ya ga wata takarda. Ya Ι—auki takardar ya duba sai ya ga hoton Ζ™warangwal na ci da wuta, ga sunansa a jiki. Hakan ya yi daidai da sake jin kamar kwanyarsa za ta zazzago.

Ya kifo daga kan gadon ya a rirriΖ™e kansa, ga jikinsa ya fara wannan zafin. Kawai ya din ga jin idan bai bar garin nan ba, mutuwa zai yi saboda wata irin azaba da yake ji mara misaltuwa.

Ya yinΖ™ura ya tashi da kyar, ya ga Asal a zaune a kan gadon tana kallonsa, ya nufi hanyar fita jikinsa na tsuma, amma kasancewar dishi-dishi yake gani, ya faΙ—i a gurin.

Washegari ya tashi normal, sai dai jin da yake yi idan bai bar inda yake ba, kamar zai zauce.

Ya yi tafiyarsa Ι—aya gidan nasa, ko zai daina jin abin da yake ji, amma abu ya din ga jin cigaba, ya din ga jin kamar a cikin wata masifa yake.

Ya yi waya da Mahmoudu a kan tafiyar su, ya ce masa su haΙ—u a Ι—aya gidan nasa.

Gaba Ι—aya ya ji tashin hankalin na Ζ™ara Ζ™aruwa, ga wata kururuwa da yake ji a cikin kunnuwansa, ganin wasu irin halittu su na yi masa shawagi a kansa. Su na ta watso masa takardun nan na zanen Ζ™warangwal. Yana daga kwance ya din ga jin ana kiransa, ana ya tashi ya je gidan ajiye kayan tarihi ana nemansa. Ya toshe kunnunwansa, amma ya gaza daina jin hayaniyar.

Jin da yayi yana neman ya haukace, kawai ya tashi ya fita ya hau tafiya. Duk da da Ι—a  nisa daga gidansa na wajen masaruta, haka ya din ga tafiya har ya je gidan tarihin. Yana zuwa mai tsaron Ζ™ofar ya buΙ—e masa. Da takardar nan mai hoton Ζ™warangwal ya sake cin karo,  muraran a zahiri ya din ga ganin aljanun da ke cikin gidan tarihin nan, muraran a siffofi daban-daban. Su na ta fitowa daga cikin Ι—akunan nan, wasu su na ratso bango su na fitowa, suka nufo shi su na yi masa wani irin ihu. Ya toshe kunnunwansa, sai ga waΙ—anda yake gani a suffar tsuntsaye, sun bayyana su na make masu nufo shin. Wata irin guguwa ta tashi a tsakiyar gurin, aka yi wata irin walΖ™iya mai ban tsoro sai ga Giyaz ya keto ta tsakiyar gidan tarihin ya bayyana a gabansa.

Giyaz ya nufo shi, wannan tsuntsayen suka yi kansa, shi kuma Hammad ya tashi ya fice daga gurin, jiri yana Ι—ibarsa, ya san ya fito daga gidan tarihin sai dai bai san ina ya nufa ba, kawai ya buΙ—e ido ya gan shi a sahara tare da Mahmoudu.

Ya yi shiru yana kallonsa, sai ga Giyaz ya kuma bayyana a cikin saharar, cikin tsofaffin kayan nan tamkar auduga saboda tsufa. Ga wani irin sauti da saharar take yi, tamkar iskar za ta taso.

Wata irin dariya Giyaz yake yi mai ban tsoro.

Ya ce "Ban sani ba, ko haΙ—uwa da kai ya sanya na ce na fi kowa sa'a a cikin sararin Duniyar nan, saboda aikin da aka bani a kanka, ya sanya na samu 'yanci. Ni ne Giyaz ibn Jaddul Jinn, Ι—aya daga cikin aljanun da suka yi wa kakanninka hidima, daga Ζ™arshe aka kore shi daga fadar, saboda wani laifi da ya aikata da bai taka kara ya karya ba. Ya tattara iyalansa ya koma Nigeria da zama, ya cigaba da hayyayafa, can ma aka samu waΙ—anda suka Ζ™ara cutar da shi. Duk da na shafe tsawon shekaru ashirin a tsare, yau wani boka ya bani 'yanci, sannan ya damΖ™a mini aiki a kanka. Dan haka ko zamu mutu tare sai na cika aikin nan da na karΙ“a a kan ka" Hammad bai gama gane me Giyaz yake faΙ—a ba, hankalinsa ya gushe.

Bayan ya sake farfaΙ—owa, ya sake tozali da Habu, sai dai ya manta a inda ya san shi, ko ya taΙ“a ganinsa. 

Duk iya Ζ™oΖ™arinsa ya kasa tuna komai game da kansa. Shi dai ya san shi mutum ne, duk wani abu da ya shafi rayuwa yana iya tuna shi, amma duk wani abu da ya shafe shi, ya manta.

Ko da Habu ya yi yinΖ™urin mayar da shi Agadez, bin sa kawai yake yi, amma bai san waye shi ba, sai dai su na dosar Agadez Giyaz yake bayyana, yana feso mu wata irin wuta mai ban tsoro, a take sai jikinsa ya Ζ™ara rikicewa ya ji tamkar zai zauce kansa yana wani irin gigitaccen ciwo, bugun zuciyarsa ya Ζ™aru, ya din ga jin zafin wutar da Giyaz yake feso masa a jikinsa ta na Ζ™ona shi. Gaba Ι—aya ya rikicewa Habu. A dole suka bar Agadez suka nufi Nigeria. Su na tafe Hammad yana ganin abubuwan da ya lura abokin tafiyarsa wato Mahmoudu ba ya gani. Duk tambayar da ya yi masa a kan waye shi, ya sunansa ya tuna wani abu game da rayuwarsa amma ya kasa.

Da suka shigo Nigeria, suka samu masauki, bai sake ganin Giyaz ba, sai dai lokaci zuwa lokaci wannan zafin jikin yana tayar masa. 

Tun da suka shigo Nigeria, yake mafarkin wata matashiyar budurwa, tare a cikin sahara. Sai ya kwaΙ—aitu da son saninta a zahiri. Idan ya kwanta bacci, ba abin da yake mafarki sai wannan yarinyar. A duk lokacin da ya farka, sai ya din ga jin akwai wani abu mai muhimmanci da yake son haΙ—uwa da shi, duk a duniyar da ya farka, babu wanda ya sani, banda iya mutanen da yake iya gani.

Gurin mai magani na farko da suka fara zuwa da su Habu, wata yarinya ta gifta shi, ya ji wani irin daddaΙ—an sanyi ya ratsa shi, ya din ga jin tamkar ya koma ya bi inda ya ji sanyin nan.

Haka da suka sake haΙ—uwa a gidan Sarkin baka, bai ga fuskarta ba, amma sanyin nan ya Ζ™ara neman ya zauta shi.

Sai dai ya sha mamaki, da ganin wani zanΖ™alelen mutum yana bin ta a baya, sai dai baya iya ganin iyakar tsawon mutumin.

Gaba Ι—aya ya lura, gane-gane da yake yi,  shikaΙ—ai yake ganin abun sa. Lokaci lokaci ya kan yi mafarki da gidan tarihi, sai dai ya kasa tuna ina ne gurin.

Duk lokacin da ya yi mafarkin yarinyar nan, ya kan tashi da matsanancin farin ciki mara misaltuwa, ya kan ji dama su dauwwama a cikin baccin nasa ba sai ya farka ba.

Tun da suka fara aiki a gidan Alhaji Zailani, duk lokacin da zai gan shi, yana ganin jini yana bin sa, da wasu Ζ™anan yara, da wasu mutane su na kuka, amma Alhaji Zailani ba ya ganinsu, sauran mutane ma ba sa ganinsu, sai shikaΙ—ai. Hakan ya jefa shi a cikin damuwa, da jin cewa shi wata halittar ne daban, da sauran mutane.

Sai dai babu zato babu tsammani, ya yi ido huΙ—u da ita, da wani yammaci ta fito daga cikin gidan, wannan dogon mutumin yana biye da ita, sai dai ya ga wannan tsohon ne ya dawo matashi, bai bayyana a suffarsa ta tsohon da ya saba fitowa ba.

Sanyin da ya ji ya ratsa shi ya sanya ya rikice, ya Ζ™udurce a ransa akwai wani abu da bai sani ba, ko yakamata ya sani, kuma wataΖ™ila wannan da suke tare zai iya gaya masa waye shi, kuma daga ina yake!.


Ayshercool.

08081012143

LITTAFIN KUƊI NE, VIA 0069685771 AISHA ADAM STANBIC 

92

Kafin ya yinΖ™ura ya fito daga Ι—akin nasu, wanda yake gani Ι—in ya ziro sanda ya hankaΙ—a shi ya faΙ—i sumamme.

Ya fuskanci mutane kowa yana da ahali, uwa, uba, Ι—an uwa, mata 'ya'ya ya san duk abu ne mai muhimmanci game da rayuwar mutum, amma shi ya kasa tuna komai a kan rayuwarsa.

Su Habu da yake gani a tare da shi, ya san su na yi masa Ζ™oΖ™ari amma ba ya jin su sosai da sosai a ransa, yadda za su iya zama wani Ι“angare na rayuwarsa. Wasu lokutan idan maganar ba ta Ι—auke ba, ya kan yi musu magana cikin iko da isa, ba tare da jin nauyin hakan ba, shi Mahmoudu sam baya damuwa da hakan, amma su Sule wasu lokutan abin yana sosa musu rai.

Aka ci gaba da tura wa Habu kuΙ—aΙ—e cikin asusunsa.

Yana ta tunanin yadda zai sanar da can gida Agadez cewa, ga fa halin da ake ciki, amma aka din ga tura masa saΖ™onni a kan muddin ya kuskura suka koma Agadez, Hammad zai iya rasa rayuwarsa. Ya tura wa Nene saΖ™on halin da ake ciki. Ya sanar mata ko an zo an tambayi yana ina ta ce ba ta sani ba kawai. Ya kashe wayarsa ya cire layin ya ajiye, ya samu na Nigeria ya saya ya saka.

Sai bayan kwanaki biyu, aka farga ba a samun lambar Hammad, wayarsa na ajiye a Ι—akinsa. 

Sultan ya ce wa Asal, kar ta kuskura ta gaya wa wani cewar Hammad ya Ι“ace ba a san inda yake ba, ana nan ana bincike a kan nemansa.

Hammad kuwa sai ya kintaci lokacin da Nana za ta zo gidan Alhaji Zailani ko kuma ta tafi, sai ya fito harabar gidan ya zauna, ko kuma ya buΙ—e taga, ya san dole zai ji wannan sanyin. Sai dai duk lokacin da zai ganta, tare da wannan dogon mutumin ne da babu wanda yake ganinsa, sai dai ya fuskanci duk lokacin zai gan shi tare da Nana, ba ya cutar da shi, ko ya yi masa feshin wuta, amma duk lokacin da ya bayyanar masa a suffar tsoho sai ya cutar da shi.

Duk lokacin da zai ga Nana yanayin fuskarta na nuna damuwa, dan haka sai ya din ga jin kamar ya je ya tambaye ta mene ne yake damunta fuskarta babu walwala. Wasu lokutan kuma Ƙaisar yake kallo, ita kuma sai ta din ga ganin tamkar yana addabarta da kallo.

Ranar da Alhaji Zailani kuwa ya biyo ta, haka kurum ya din ga jin jikinsa babu daΙ—i, tamkar ya bita cikin gidan. Ko da ya ga Nana ta fito a sukwane kuwa, ya san akwai matsala, sai dai Giyaz ya bayyana a lokacin ya shaΖ™e Alhaji Zailani.

A hankali ya fara lura da tsuntsayen da suke bayyana idan ya murza zoben hannunsa, ko kuma ya matsa jakar fatar da yake ratayawa a wuyansa.

Ya kan tambayi tsuntsayen, ko sun san waye shi? Suwaye iyayensa? Da kuma 'yan uwansa? Tun da su na magana wasu lokutan. Ba sa ce masa komai sai dai su zana masa taswirar gidan tarihin Agadez a Ζ™asa. Idan ya kalla ya san gurin amma ya manta a ina ne.

Sannu a hankali ya gane, akwai bambanci a tsakanin Giyaz da Ƙaisar ranar da faΙ—a ya haΙ—a su, Giyaz ya yi jifa da Ƙaisar sai da ya sha mamaki, ganin tsananin kammanin da ke tsakanin Giyaz da Ƙaisar.

A ranar kuma ya fuskanci Nana ma tana gane-ganen abubuwan da ba kowa ne yake gani ba, hakan ya sanya ya ji a jikinsa ita daidai take da rayuwarsa, ita ce suke iri Ι—aya. Amma ta yaya? Tun da yana jin Habu da Sule su na zancen Nigeria da Niger, shi da su irin su Ι—aya, ga yarukan da yake iya yi, wanda alamu suka nuna inda suke ba duka yaren da suke yi mutanen gurin suke ji ba.

Ɓangaren Ƙaisar ma, tun da ya ga Giyaz a tare da Sayyid ya rikice, domin bai taΙ“a tsammanin Giyaz zai dawo ba.

Wataran bayan shafe kwanki biyar Sayyid yana fama da wannan zafin jikin da yake rikita shi. Ga babu magana abinci ma baya iya ci. Ya wayi gari ya Ι—an samu sauΖ™i. Har ya ci abinci ya shiga ya yi wanka da la'asar. Kawai ya ji wannan sanyin yana kusanto shi.

Babu tsammani ya ji muryarta, ta yi sallama sai dai ya yi shiru yana tunanin ko tsabar saka ta a ransa ne ya sanya ya ji muryarta. Yana tsaye cak da matajin hannunsa, ya ji muryar yaro a Ι—akin bai ga yaro a Ι—akin ba, kawai ya ga ta faΙ—o Ι—akin.

Su na haΙ—a ido ya ga ta yanke jiki ta faΙ—i. Ya ga Ƙaisar ya bayyana ya tsaya a kanta yana huci, shi dai ya tsaya yana kallonsa dan bai san abin da ya yi mata ba. Ya gama ya sanya kayansa Nana ta kwance, amma sanyin da yake tattare da ita na saukar masa da wata irin nutsuwa da daidaita zafin jikinsa.

Tun daga lokacin aka fara dambarwar nan, har ta kai ga Ι—aura masa aure da Nana, ya din ga jin amincewa da auren, shi ne hukunci mafi daΙ—i da zai yankewa wannan rayuwar tasa da yake yi mara kan gado. Ba ya jin ko Ι—ar sanya Habu ya yi masa duk wani abu da yake buΖ™ata.

Bayan aurensa da Nana a  jikinsa yake jin, samun nutsuwa a tattare da wannan duniyar da kuma kwanciyar hankali, idan ya matsa ya tuna wani abu da ya shafe shi game da ainihin waye shi, sai ya ji damuwa da baΖ™in ciki ya mamaye shi.

Habu kuma bai taΙ“a gangancin gaya masa waye shi ba, kawai ya Ζ™yale shi a kan duk lokacin da ya tuna wani abin ya sanar da shi.

Idan ya kwanta bacci baya mafarkin kowa, sai wannan dai gidan tarihin da yake gani, sai kuma ya din ga ganin wasu abubuwan da suka faru a Ζ™arnukan baya a wannan gidan sarautar, har ma da mutanen da suka yi rayuwa a gidan. Wasu lokutan har a zahiri yana ganinsa a gidan tarihin amma bai taΙ“a tuna a ina ya san gidan ba, sai dai bai manta abin da ya faru na Ζ™arshe a gidan ba, na firfitowar wannan halittun daga Ι—akunan tarihin. Sai dai yana yawan ganin gidan, sakamakon aljanun da suke tattare da zobensa da kuma jakar fatarsa, ainihinsu mazauna gidan ne, kuma su ma su kan yi kewar gidan, tun da duk inda yake ya murza zoben sai sun zo. Lokacin da aka yi aurensu, aka kai Nana wannan aljanun na zobensa ne suka din ga rangaΙ—a guΙ—a.

A duk lokacin da yake son ya yi wasa da hankalin Nana, sai ya murza zoben hannunsa, idan ya danne jijiyar da ke wajen Ζ™eyarta, sai ta yi bacci. Haka zalika yadda yake ganin gidan tarihin nan, haka ita ma take ganinsa.

Da wannan aljanun yake amfani ya burkita mata lissafi, ya yi abu da ita a zahiri amma ta din ga ganin kamar a mafarki ne. Haka zalika Giyaz da yake taka rawa gurin addaba musu, tare da cutar da su, da abubuwa na ban tsoro. Ƙarfin ibadar Nana ne ya sanya suke samun sassauci a wasu abubuwan. Nana ba ta taΙ“a sanin amfanin zoben nan na hannunsa ba. Ya Ι—auki zoben ya ba wa Nana kyautarsa, saboda abin da yake ji a zuciyarsa game da ita. Saboda a jikinsa yake jin zoben na da muhimmancin gaske, dan haka ya Ι—auka ya bata.

Ƙaisar ya yi ta gargaΙ—in Nana a kan Sayyid, saboda yana jiye mata tsoron Giyaz, da kuma kar Aljanun da yake ta'amalli da su, su cutar da ita.

Duk da yadda Ƙaisar yake jin haushin Sayyid, da yadda Nana ta saki jiki da shi suke rayuwa, amma ya taka muhimmiyar rawa gurin Ζ™ara jirkita hankalin Nana, da sauΖ™aΖ™awa Sayyid Ι—in wasu abubuwan. A sakamakon yarjejeniya da suka yi da hadiman jikin zoben Sayyid, a kan za su ba shi wasu labarurruka da suka faru a wasu zamani da suka shuΙ—e, tun kafin a haife shi a cikin Duniya, bisa yarjejeniyar idan suka cutar da Nana ba za su taΙ“a zama lafiya ba.

Duk da tsamin alaΖ™ar da ke tsakanin Giyaz da Ƙaisar, amma yana jin daΙ—in ganin Ι—an nasa, bayan shafe shekaru masu yawa bai gan shi ba. Ya na tsananta cutar da Nana da Sayyid, saboda ya muzgunawa Ƙaisar.

Ko lokacin da ya bi Nana, har ya duba Baba, a zahiri ya ga Ζ™ullin da Ƙaisar ya yi a Ζ™afar Baban, kuma da aljanun jikin zobensa, ya warware Ζ™ullin.

Rayuwarsa da Nana yana saka shi jin wata nutsuwa a tattare da shi, ga alaΖ™ar Giyaz da ta Ƙaisar da ta shafi rayuwarsa da Nana. Sau Ι—aya ya yi mafarkin Sultan, ya gan shi cikin damuwa da tashin hankali, ya farka a rikice da sunansa a bakinsa amma bai iya tuna ko waye shi ba.

Can Agadez kuwa, bayan Ι“atan Hammad, aka ankara da Ι“acewar Mahmoudu, hakan ya sanya Sultan cewa duk inda Hammad yake yana tare da Mahmoudu. Sultan ba ya iya cin abinci, ba ya isasshen bacci saboda tashin hankalin rashin sanin inda Hammad yake. Ga shi Ι“oyewa suke ta yi, duk da yadda Tafawa da muΖ™arrabansa ke ta Ζ™oΖ™arin bin diddigin gano abin da Sultan yake Ι“oyewa.

Lambar Mahmoudu da ta Ζ™i shiga, sai aka yi ta tracking lambar Mahmoudu, aka gano last inda ya yi amfani da ita a Nigeria ne. Aka din ga bin diddigi har gidan Alhaji Zailani, aka tafi da motoci gaba Ι—aya aka kwaso Buzayen layin kaf. Sai da aka zo Agadez, sannan aka tantance su bayan da aka fahimci su ba su san komai ba, hasali ma wanda ake maganar a kansa ba su san waye shi ba. Aka Ι—auke Mahmoudu daga cikinsu, aka din ga tuhumar sa, ina Hammad yake, amma ya Ζ™i magana saboda yana jin tsoron gargaΙ—in da aka din ga yi masa, a kan muddin Hammad ya dawo Agadez mutuwa zai yi.

Mahmoudu ya sha azaba kala-kala, tamkar ba zai yi rai ba, sai da ya ji azaba sannan ya gaya musu cewar Hammad yana Nigeria. Aka saka shi a gaba zuwa Nigeria, aka taho da Hammad. Sai dai tunda aka taho da shi, sai Ζ™waΖ™walwar ta sak burkicewa, tunaninsa ya rikice.

Bai gama tantance waye shi ba, hankalinsa ya dawo ba, sai da aka fitar da shi Faransa. Dama Ζ™waΖ™walwar a hargitse take, baya tantance komai, sai dai sannu a hankali tunaninsa na rayuwar da ya yi a Nigeria, ya shafe gaba Ι—aya.

Sai ainihin tunaninsa na waye shi ya dawo masa. Ganin ya dawo hayyacinsa ya daina iface-ifacen da yake yi, ya nuna ya gane Sultan da Matawalle, suka yi farin ciki sosai, suka tambaye shi ko ya tuna abin da ya faru da yaje Nigeria, sai ya rikice yake tambayar me ya kai shi Nigeria. Daga nan kawai sai suka Ι“oye masa, suka ce jinya kawai ya yi mai tsawo a faransa. Likitoci suka din ga ba shi kulawa a kan matsalar zuciya da yake fama.

Can a Agadez kuma, aka ci gaba da azabtar da Mahmoud a kan lallai sai ya faΙ—i dalilin da ya sanya, ya sace Hammad ya tafi da shi Nigeria.

Ga Tafawa ya matsa a kan lallai sai an faΙ—i inda Hammad yake, tun da an doshi shekara biyu, babu wanda ya gan shi, ko kuma a ba su dama su je su duba shi, su gan shi ido da ido su tabattar yana raye babu wani abu da ya same shi.

Sai dai Hammad ya kasa yarda da cewa, tsawon wannan lokacin, jinya yake yi. Tiryan-tiryan abin da ya faru na Ζ™arshe daga gidansa, zuwa gidan tarihi daga nan kuma sai ya rikice ya kasa tuna komai.

Ya ce wa Sultan lallai a kawo masa Mahmoudu, Matawalle ya ce "Ko ka tuna wani abu ne? Me Mahmoudun zai yi maka?"


Hammad ya ce "Babu komai, ni ba na jin daΙ—in zama nikaΙ—ai ne, na saba duk inda nake mu na tare, ni dai a kawo mini shi"


Matawalle ya ce "Ka yi haΖ™uri, Likitoci sun ce ba a buΖ™atar kowa ya zo inda ka ke ne"


Ya yi shiru yana tunanin, ina Asal da ko sau Ι—aya ba ta zo ba ita ma. Sai dai a jikinsa ya din ga jin kewar wani abu mai muhimmanci a tare da shi, kamar yana jin matsananciyar Ζ™ishirwa.


Sultan kuwa ya sanar da Asal batun ganin Hammad, amma ya ce mata rashin lafiya ce ta kama shi a Niemey, aka kai shi wani Asibiti a can, daga baya a ka kai shi faransa. Duk da ta yi mamakin yadda za a ce rashin lafiya ta kama mutum, a kai shi Asibiti amma ba a nemi ahalinsa an sanar da su ba tsawon shekaru.

Sai dai hakan ma sai da ta gaya wa Tafawa. Ya ruΙ—e ya rikice dan ya so a ce wani mummunan abin ne ya samu Hammad.

Tun da Asal ta ji labarin Hammad zai iya dawowa a kowane lokaci, take shirin karΙ“ar sa, dan ba Ζ™aramin kewarsa ta yi ba. Dan ta shiga damuwa da tashin hankalin da sai da suka samun matsala da Tafawa bayan Ι“acewar Hammad.

Tun da Sultan ya ce a kowane lokaci zai iya dawowa, ta sanya aka yi gyaran gidan sosai. Sannan ta fara lissafin canza kuyangin da za su din ga yi masa hidima. Ga Tafawa ya yi mata alwashin idan ba za ta ci gaba da ba shi haΙ—in kai ba, zai nemi wani ya yi masa, ko da kuwa ta kama a salwantar da ran Hammad Ι—in ne baki Ι—aya.

Sai dai duk da tunaninsa na Agadez ya dawo, bai fasa fama da wannan matsanancin zafin jikin ba, da yake jin tamkar ana Ζ™ona shi ba. Sai dai ya rage tashi a kai a kai.

HaΙ—uwar Asal da Nana, ya zame wa Asal tamkar tsintar dami a kala, ta ga idan ta kawo Nana gidan sauratar Agdez, kanta a tukunya yake game da sha'anin sarauta, ga girki ta iya, saboda Hammad na son daddaΙ—an Abinci, ga kuma Nana baΖ™a ce 'yar Nigeria, babu yadda za a yi ta Ι—auki hankalin Hammad, saboda baΖ™ar mace ta haramta a gare su, bisa ga Al'adar Agadez. Sai dai abin da Asal ba ta sani ba shi ne; a rashin sani kaza ta kwana a kan dami.


AREWABOOKS 


Tun da Hammad ya sauka a filin tashi da sauukar jirage, gabansaa yake faΙ—uwa, ya kuma rasa dalilin hakan. Jin sa yake yi tamkar yana daf da maganin Ζ™ishirwar da ta addabe shi.

Bayan Nana ta yi amfani da Ζ™arfi, gurin tursasa wa Nana zuwa Agadez, ta sanya Nana cikin jerin waΙ—anda za su yi girkin karΙ“ar Imam Hammad.

Gabba Ι—aya gida ya Ι—auka Hammad zai dawo, bayan shafe dogon lokaci yana jinya. Su kansu wasu daga cikin Imam Imam Ι—in, ba haka su ka so ba duk da abin jita-jita ake ta yi, Sultan bai tabattar da hakan ba, kuma a daren za a yi babban taro tare da 'yan majalisar Sarki, da kuma su Imam na shekara da ake gabatarwa.

Sai dai babu tsammani, su ka ga Hammad ya bayyana a gurin. Tun da ya shiga gurin, ya ji wani irin daddaΙ—an sanyi ya ratsa shi, da kowace irin AC aka kunna, sanyin baya wadatar da shi har cikin Ζ™ashinsa ya ji ya gamsar da shi.

Ya ji wani irin jiri na neman ya Ι—ebe shi, amm ya daidaita nutsuwarsa, ya sunkuyar da kansa Ζ™asa ya rabe ya je ya zauna.

Bai Ι—ago kansa ba, ya ji Matawalle na tambayar me ya kawo wannan nan gurin. Aka sanar masa tana cikin masu girki ne.

Bai dai Ι—ago ba sai murmushi da yake yi, saboda barka da zuwa da ake ta yi masa.

Sai dai Ζ™irjinsa ya tsananta bugawa, da aka ce ta zo ta Ι—anΙ—ana Abincin, ta nufo inda suke. Ya kasa jurewa ya Ι—aga kansa, sai ya ji kamar sanyin da yake ji yana Ζ™aruwa. Wani abu ya ji mara daΙ—i a Ζ™irjinsa ganin yadda ta Ι—aura rigar girki a kan kayanta, ana ganin shape Ι—in kyakykyawar surar da Allah ya yi mata ta bayyana. Kalar fatarta ya Ι—auki hanklinsa, tsohon muradinsa na son baΖ™ar mace ya motsa a zuciyarsa. A kallo Ι—ayan da ya yi mata duk ya nazarci wannan abubuwan ya sunkuyar da kansa. Amma ya nemi ya kasa jure bugun da zuciyarsa take yi babu Ζ™aΖ™Ζ™autawa.

Bai ji daΙ—in yadda Matawalle ya saka a ka fita da Nana ba, saboda yadda duk ta rikice a gurin. Sai dai ya yi ta mamakin yadda aka ta shiga cikin masu girki, alhalin tana baΖ™ar fata 'yar Nigeria.

Da suka tashi daga taron nan kuwa, da Asal ta gan shi, wani irin tsalle ta yi ta maΖ™alΖ™ale shi, tana murna cikin matsanancin farin ciki har da hawayenta. Ya Ι—ago ta daga jikinsa yana murmushi yana kallon idanunta, da son gano ainihin abin da yake gani a idanun nata, dan abin da ya faru daren da ya bar Agadez fes yake dawo masa. 

Ya tsura wa idanun Asal ido, ya ce "Kin yi kewata har haka?"


"Imam, kusan shekara biyu ba ma tare ka ce ko na yi kewar ka? tu me manques(Na yi kewar ka sosai) Ta yi maganar idanunta Ι—auke da hawaye. Bai bari zuciyarsa ta ci gaba da raya masa abin da take raya masa ba. Ya rungume ta a jikinsa ya ce "tu me manques. Na yi kewar ki sosai cheriΓ©. Ina fatan kina lafiya babu abin da ya same ki?"


"Ba abin da ya same ni, sai damuwar rashin sanin inda ka ke, ina ka tafi aka neme ka aka rasa haka, ka tayar mini da hankali na shiga damuwa sosai"

Ya yi shiru yana mamaki, Sultan ya ce masa faΙ—uwa ya yi, ya shiga coma na tsawon lokaci, yanzu kuma tana faΙ—in ya tafi ba a san inda yake ba, ga abin da ya faru na Ζ™arshe kan barinsa Agadez yana dawo masa. Sai ya kawar da tunanin komai daga cikin zuciyarsa.

Duk rawar kan da Asal take yi, da murnar dawowarsa gaba Ι—aya hankalinsa ba a kan hakan yake ba. Jin sa yake yi ba daidai ba. Ya yi iya Ζ™oΖ™arinsa ya sarrafa tunaninsa da nutsuwarsa gurin ba ta dukkanin kulawa da kuma lokacinsa, amma hankalinsa na kan abin da shi kansa bai san mene ne ba.

Da dare ya yi kuwa, ya riga Asal kwanciya dan kar ma ta nemi wani abu a tare da shi, saboda fatansa ya gano takamaiman mene ne yake damunsa. Sannan ya yi mamaki rashin ganin Mahmoudu da bai yi ba.

Yana kwanciya bacci surar Nana ta bijiro masa, a Ζ™asan zuciyarsa ya ji bai ji daΙ—in fitowarta a haka ba. Da sauri ya yi istigfari dan gudun kar shaiΙ—an ne yake Ζ™ara Ζ™awata masa ita. Amma duk da haka bai daina ganin ta a idonsa ba, ds yadda ta zuba masa ido duk ta rikice ba.

Ya yinΖ™ura ya tashi zaune, ya ga Asal ta yi bacci, ya yi shiru yana tunanin wa zai tambaya wace ce ita.

Ya gaji da zancen zucin ya matsa kusa da Asal ya kwanta tare da rungume ta a jikinsa. Sai Ζ™amshin turare take yi da alama ta shiryawa dawowarsa sosai.


Ya shafa gashin kanta, tare da fatan Allah ya sanya Asal Ι—in ta canza gaba Ι—aya, tare da yi musu addu'ar samun rabo na alkhairi. Kamar ya tashe ta, sai kuma ya Ζ™yale ta kawai ya lumshe idanunsa yana addu'a a Ζ™asan zuciyarsa yana jiran bacci ya Ι—auke shi.

Yana tsaye a cikin sahara, ya riΖ™e akalar raΖ™uminsa, iskar sahara sai kaΙ—awa take yi, babbar rigar jikinsa na Ι—agawa, ta cikin iskar yake jiyo sheshsheΖ™ar kukan mace tana faΙ—in "Sayyid" ya waiwaya bai ga kowa ba. ShikaΙ—ai ne a cikin saharar, sai dai bai daina jin sheshsheΖ™ar kukan ba.

A hankali ya buΙ—e idanunsa, wannan shi ne karo na bai san adadi ba, yana wannan mafarkin tun da ya buΙ—e ido a faransa. Jin kiran sallar Asuba ya sanya ya tashi ya tafi salla.

Ranar farko da ya sake cin abinci bayan wanda ya ci da ya dawo, sai ya ji kamar ya san Ι—anΙ—anon abincin, amma ya manta a ina ya san shi.

Ranar da ya sake ganin Nana, Asal ta kira ta a kan ta zabga yaji a abinci ya kasa ci, sai da zuciyarsa ta kusa tsayawa, ya din ga jin kamar abu malaman haka ya taΙ“a faruwa, amma bai san a ina ba. Jikinsa ya din ga tsuma sakamakon jin sanyin da ya fara yi, ga kallon da take yi masa da ya sake burkita shi. Ya din ga matsa Ζ™waΖ™walwarsa, ko za ta ba shi wani abu, amma ya ji ya fara jin jiri.

Bai tsaya kammala karin kumallon ba, ya tashi ya fita ya je ya samu Sultan, baya ya kammala zaman Majalissa, yake ce masa shi fa haryanzu bai ga Mahmoudu ba. Sultan ya ce masa ya yi tafiya ne, amma zai dawo. Haka kurum ya ji bai yadda da hakan ba, amma bai kuma cewa komai ba.

Cikin hikima ya tambayi Asal inda ta samo Nana, ta sanar masa da a gidan Abincinsa na MaraΙ—i take aiki, ganin ta iya girki ya sanya ta kawo ta gidan, domin ta din ga dafa masa abinci.

Sai dai a kullum abubuwan da Nana take yi, su na Ζ™ara dagula masa lissafi nesa ba kusa ba.

Matsin lamba da Hammad ya yi ya sanya aka sako Mahmoudu, kuma Matawalle ya jaddada masa lallai kar ya kuskura ya gaya wa Hammad komai a kan zuwan da suka yi Nigeria, kuma kar ya gaya masa Ι—aure shi suka yi.

Hammad bakinsa ya Ζ™i rufuwa, bayan ganin Mahmoudu da ya yi, saboda yadda yake jin Mahmoud a rayuwarsa ba ya jin Zahradeen yayansa da suke uba Ι—aya haka. Sai ya yi ta yinΖ™urin ya yi wa Mahmoudu bayanin abubuwan ban mamakin da yake gani game da Nana, amma sai ya kasa. Babbn abin da ya sake Ι—aure masa kai da ita, shi ne lokacin da ya hana ta cin ayaba. Ta karΙ“a ta ci, a lokacin ya ga Ƙisar a tare da ita. Ganin Ƙaisar ya Ζ™ara hargitsa masa lissafi, saboda yana ganinsa hoton suffar Giyaz ya faΙ—o masa, amma ya manta a ina ma ya san fuskokin. Sai daga baya sannu a hankali ya tuna yadda Giyaz y fito masa a gidan tarihi, amma wanda ya gani tare da Nana bai kai wancan tsufa ba.


Gefe guda kuma Ƙaisar da Giyaz su na ta dambarwa, Giyaz ya ce ba zai taΙ“a rabuwa da Nana ba, ya mantar da Hammad wace ce Nana da duk wata rayuwa da suka yi a Nigeria saboda ta ci gaba da shan wahala.

Bokan da ya sanya Giyaz aikin Ι“atar da Hammad kuwa, hankalinsa ya dugunzuma bayan da shi ma wands ya ba shi aikin, ya matsa masa lamba da masifar ya aka yi Hammad ya dawo Agadez bayan an ce har abada shi da Agadez.


"Ya kai Giyaz, ina alΖ™awarin da muka yi da kai? Na baka 'yanci bisa sharaΙ—in za ka yi mini aiki, amma kwatsam sai na ga wanda na baka aikin a kansa ya dawo Agadez"


Giyaz ya ce "A cikin aikin naka wanne ne ban yi ba? Na mantar da shi waye shi, na mantar da shi, ya bar Agadez ya yi nesa da ita, kuma ya yi. Ni da kai ba na tunanin akwai wanda yake bin wani bashi, na cika sharuΙ—Ι—anka kaf da muka yi yarjejeniya a kai"


Bokan ya ce "Amma ai ga shi ya dawo Agadez cikin Ζ™oshin lafiya a hayyacinsa"


"Eh, ai ba mu yi da kai zai bar Agadez har abada ba, na kuma yi iya abin da muka yi sharaΙ—i a kai"


"Kar ka fusata ni, ka sanya na sake kama ka na rufe ka, ni bami yi haka da kai ba"


Giyaz ya ce "Ƙarya ne, ni dai ka kama ni ka sake kulle ni, ba za ka iya wannan ba. Kuma duk abu dole na zauna inda zan iya ganin Ι—a na. Kuma ina nan ina ci gaba da gudanar da aikin da ka bani bisa yarjejeniya, tun da haryanzu ina nan tare da shi ban bar shi ba"


Bokan ya ce "Waye Ι—an naka, kuma a ina yake?"


"Babu wannan a cikin yarjejeniyar aikina da kai, ka bar zancen a yadda na bar shi kawai"

Bokan nan ya san faΙ—a da Giyaz ba abu ne da zai haifar musu da Ι—a mai ido ba, sai dai dawowar Hammad mayar musu da aiki baya ne.

Mahmoudu tunanin Nana ya addabe shi, tare da ganin rashin dacewar abin da ya faru. Ga shi alamu sun nuna Ζ™iri-Ζ™iri Hammad bai san ya je ya yi wata rayuwa a Nigeria ba.

Ya kuma san muddin ya ce zai je Nigeria sai Hammad ya bi ba'asi, kuma kwana Ι—aya ko biyu ya yi kaΙ—an ya je ya nemi Nana, balle ya yi masa Ζ™aryar kasuwanci zai je. Ya sha tambayar Mahmoudu a kan ko akwai wani abu dayake damunsa, saboda yanayinsa ya nuna akwai damuwa. Amma ya kan ce masa babu komai.

Hammad ya ce wa Asal baya buΖ™atar sake ganin Nana. Sai murna take saboda ta zata munin Nana yake gani, shi kuwa mafita yake nema, daga burkicewar da yake yi a duk lokacin da ya ganta. Sai dai kuma kwana biyu da ya daina ganinta sai ya shiga damuwa, ya zamana duk ranar da bai ganta ba, sai ya ji shi tamkar a kurku, wunin ranar bai yi masa daΙ—i ba sam.

Yana zaune a Ι—akinsa, yake kallon yatsunsa babu zobe guda Ι—aya, wanda shi ya fi kowanne muhimmanci. Shi dai Matawalle ya ce masa duk wanda ya tambayi zoben ya ce an kai zoben gyara ya samu matsala. Ya kalli tagullar hannunsa, ya din ga murza ta a hankali yana zancen zuci. Saboda gaba Ι—aya a rikice yake, kasancewar Nana ta kai masa abinci tana Ζ™amshin turarensa da yake amfani da shi. Shi dai ya san babu wanda ya bawa turaren, kuma mai aiki kamar Nana ba za ta iya sayen turaren ba, kuma babu yadda za a yi a ce satar turaren ta yi har ta samu Ζ™warin gwiwar shafawa. Yadda take yi masa wasu abubuwan kai tsaye wasu lokutan abin yana ba shi mamaki sosai da sosai.

Ganin ya yi hasken wutar Ι—akin tana Ι—aukewa tana kawowa, daga baya ta tsaya, sai ga wani Ι—an gajeren abu a ya bayyana da tsawonsa bai fi 'yar tsana ba, kansa duk wasu Ζ™ayoyi.

Hammad ya zuba wa abin ido, ganin yana motsi.

"Tuba nake shugabana na tsorata ka, ni ne aljanin da aka wakilta hidima ga duk wanda ya Ι—auke da wannan tagullar, tun da ka ke ba ka taΙ“a nema na ba sai yanzu, me ka ke buΖ™ata?"


Hammad ya ce "Waye kai?"


"Arun, bawan aljani ga Sultan Azhar, wannan tagullar mallakinsa ce, kuma ni mai hidima ne ga ma mallakin tagullar"


Hammad ya zuba ido sosai, ya ga Ι—an abin tsoho ne tukuf sosai da sosai. Domin kuwa gemunsa Ζ™asa yake ja.


Ya ce "Amma da idan na murza zoben ba kai nake gani ba"


Arun ya ce "Ai ba ni ka ke kira, hadiman wancan zoben daban, nima kuma daban"


"To ina zoben nawa yake?"


"Ka yi kyautarsa ga wanda ka ke matuΖ™ar Ζ™auna a matsayin tukuicin soyayya"


Hammad ya ce "Soyayya kuma? Ni Ι—in?


"Ƙwarai ya shugabana"


"To wa na bawa, kuma yaushe na yi soyayyar, kuma mace ce ko namiji?"


Arun ya sake cewa "Ba na son shiga hurumin da ba nawa ba, ina gudun sake rura wutar fitinar da ke tsakanin gangar jiki buyi, ruhika huΙ—u, alaΖ™a huΙ—u. Gangar jiki ta mutum biyu, ruhi huΙ—u, na mutum biyu da na aljan biyu, sai kuma alaΖ™ar mata da miji da kuma uba da Ι—a, sannu a hankali duk za ka fahimci abubuwan da nake nufi" Daga nan ya Ι“ace Hammad ya yi shiru yana juya maganganun da suka fi yi masa kama da shirme.

Ya tashi ya fita falo, ya san lokacin kawo masa shayin dare ya yi, sai dai tun kafin ya Ζ™araso cikin falon yake jiyo sautin muryarta tana waΖ™a. Daga nesa kaΙ—an ya tsaya yana kallonta, yana jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.


*_ina zana ganka_*

*_saΖ™o zana baka*_

*Hotona da naka*_

*_Ko ina zana bika*_

*_Kowa tsane ka, ni na tsane shi sanya a ranka*_

*_Zuciyata na baka duk masu Ζ™in ka su daina shakka*_

*_Rayuwata na baka_*

*_Ni ta ya zan guje ka*_

*_Ka dawo gare ni dan zuciya ta bar kewa*_


Gaba Ι—aya sai ya daskare a gurin, gumi ya din ga tsatstsafo masa, Ζ™waΖ™walwarsa ta shiga Kai komo, kansa kamar zai yi tsawa ya fashe. "Tabbas akwai wani abu, ya san wani abu mai kama da haka, amma yaushe? Kuma a ina?"

Ya daΙ—e a tsaye a gurin, kafin ya saita nutsuwarsa ya shiga falon. Murmushi ta yi ta daina waΖ™ar da ta ga ya fito ta risuna ta ce "Barka da dare"

Ya jinjina mata kai.


"Sayyid ga shayinka nan, ina fatan na kammala komai, zan iya tafiya?" Ya yi shiru yana jujjuya Sayyid da take kiransa da shi.


Washegari da sassafe ya kira Mahmoudu a waya, ya sanar masa da yana son ganinsa za su yi magana.

Amma Mahmoudu ya ce masa yana hanyar MaraΙ—i, zai kai wa Nene ziyara ne.

Hammad ya yi ta mitar me yasa bai gaya masa su tafi tare, su je su gaishe ta, ya ba shi haΖ™uri.

Sai dai tun da Mahmoudu ya je ya ga Muhsin ya rikice, ya din ga yi wa Nene tambayoyi a kan Muhsin, amma ta Ζ™i gaya masa haΖ™iΖ™anin gaskiyar waye Muhsin.

Sai dai yanayin yadda ta ga Mahmoud ya rikice, ya sanya ta tabattar da ya ga abinda take tunani ita ma.

Kwanansa Ι—aya ya shirya ya nufo Agdez bayan ya faki idon Nene ya Ι—auki hotunan Muhsin. Ya nufi Agadez da nufin komai zai faru sai dai ya faru.

Hammad kuwa ya lallaΙ“a Asal ya yi mata wayo ya sanya ta dawo da Nana sashen su, ba tare da ta kawo komai a ranta ba. Amma shi a jikinsa yana jin baΖ™in abubuwa game da 'yar Nigeria da jikinsa bai ba shi cutar da shi za ta yi ba, amma kasancewarta daf da inda yake yana samun nutsuwa da nishaΙ—in kallonta.

Tun da Mahmoudu ya dawo, Hammad ya lura bakinsa akwai magana, amma ya Ζ™i ce masa komai.

"Mahmoudu na lura bakinka akwai magana, amma ka Ζ™i gaya mini, duk da ba ma 'yar haka da ni da kai, amma bari ni na gaya maka tawa damuwar".

Mahmoud ya ce "Ni babu wani abu da zan gaya maka, amma gaya mini mene ne yake damunka?"


"Ina kukun da nake gaya maka Asal ta samo 'yar Nigeria?" Gaban Mahmoud ya faΙ—i amma ya dake ya ce "Eh meyafaru?"

"Wasu abubuwa nake ji game da ita, da tun da nake ban taΙ“a ji game da wani mutum ba"

Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Ko santa ka ke yi ne?"


"Anya kuwa, ban dai sani ba, amma ba normal mutum ba ce"


"Ka na da mata fa a Nigeriar nan"


Hammad ya kalle shi yana jiran Ζ™arin bayani. Mahmoudu ya ce "Da wasa nake yi, na dai ce zan aura maka 'yar maka 'yar Nigeria idan ka na so. Amma ina da wani abin al'ajabi da nake son nuna maka, amma tashi mu je ka shirya, ka ce mini za ku yi hawan raΖ™uma kar a yi ta jiran ka" Babu musu ya tashi suka fita. Kowanne a cikin su yana ta saΖ™e-saΖ™e a cikin zuciyarsa.

Sai dai bayan an yi hawan raΖ™uman, da Hammad ya faΙ—o tare da Mahmoudu aka dawo da Hammad gida. Sai dai ya yi mutuwar tsaye, da hango ta tana leΖ™en mutanen da suke kaiwa da komowa a falon fuskarta Ι—auke da damuwa.


A jere zuciyar Mahmoudu ta buga, addu'a ya fara yi, a kan Allah ya sanya ba mafarki yake yi ba, ko kuma tsabar saka abin a ransa ne ya sanya ta fara yi masa gizo ba.


Ayshercool 

08081012143


93

93

LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KUƊIN KARATU KAFIN KI KARANTA.

08081012143


Cikin hanzari Habu ya ja rawaninsa ya nufi barin falon, yana daf da fita Nana ta waiwaya ta ga wucewarsa, sosai ta tsaya tana kallon bayansa har ya fice tana yi masa kallon sani.

Washegari da safe Bayan Tafawa ya zo duba shi, ya tafi zuciyarsa a cunkushe babu daΙ—i, saboda kausasan kalaman da Tafawa ya yi amfani da su, har da ce masa ko shaye-shaye yake yi, shi ya sanya ya faΙ—o daga kan Taguwa.

Wajen Ζ™arfe sha Ι—aya, da ya ji sauΖ™i, ya lallaΙ“a ya fito, yana mamakin dalilin da ya sanya Nana hana shi hawa kan Taguwa, da ya hau kuma ya faΙ—o. Yana fitowa ya tarar da ita da Asal su na mujadala. Sai dai hangota kawai da ya yi, sai ya ji wani sanyi a ransa.


Nana ce take kallon Asal cikin takaici, bayan da Asal ta ce mata ta din ga sanya da hadiman gidan suke sakawa.

Nana ta rasa dalilin da ya sanya Asal ke son Ζ™asΖ™antar da ita ko ta halin Ζ™aΖ™a.

Nana ta dube ta ta ce "A gaskiya ba zan iya sanya kayan da hadimai suke sanyawa ba, ko ki haΖ™ura ki kalle ni da kayan jikina, ko kuma ki sallame ni. Tun da ni ba baiwarki ba ce ba, aiki kawai ki ka Ι—aukko ni na yi miki"


"Idan na so mayar da ke baiwar tawa ina da halin yin hakan, ke kin san ina da abin da ko nawa za a yi miki kuΙ—i zan iya bayarwa na saye ki"


"Ko da Goma ta lalace a gaban biyar take har gaban Abada Gimbiya Asal. Kuma wani garin ya fi gaban kunu.  Ba ki da arzikin da za ki Asma'u a matsayin baiwarki" Nana ta Ζ™arasa maganar a zafafe. Hammad ya yi gyaran murya, suka tsaya Asal ta haΙ—iye maganganun da ta yi niyyar caΙ“awa Nana.


"CheriΓ©, ba zai yiwu ki Ι—aukko wadda ba hadima ba a cikin gidan nan, alhalin kin san kin taka dokar gidan mulki ba, sannan ki ce ta din ga saka kayan hadimai a nan ta fiki gaskiya."


Cikin mamaki Asal ta kalle shi za ta yi magana, amma ya Ι—ora yatsansa a kan laΙ“Ι“ansa a dole ta yi shiru. Nana kuwa haΙ—a su ta yi, tai musu kallon banza ta wuce ta bar su a gurin. Sai dai kallon da ta yi musun, sai da ya kusa Ι—imaucewa, ji ya yi tamkar ya bi bayanta. Wani murmushi ya saki ya nufi Asal yana lumshe ido ya ce "Ba girmanki ba ne, ki din ga sa'in sa da ma'aikatanki ai kin wuce nan".


"Amma ka na kallo a yadda take yi mini magana, kuma ka hana ni magana?" Ta yi maganar kamar za ta yi kuka.

Ya kamo hannunta ya ce "Yawan musayar yawu da na Ζ™asa da kai, raini yake janyowa, kuma kar ki yadda ki yi fin Ζ™arfi a abin da ba ki da gaskiya, nan ma raini zai din ga janyo miki" Ya Ζ™arasa maganar yana rungume Asal, amma a zahiri hanyar da Nana ta bi, ya bi da kallo Ζ™amshin turarensa da ta shafa ya ci gaba da karaΙ—a hancinsa.


Mahmoudu kuwa bai yi bacci ba, so yake ya tabattar da abin da idanunsa suka gane masa, gaskiya ne ba gizo ba.

Ya kira wayar Hammad, amma bai Ι—auka ba, ga shi tsoron zuwa gidan yake domin kar su haΙ—u da Nana, ya san komai zai rikice ne. Ga yaron da ya gani a gurin Ummansa, ga kashedin su Matawalle, ga kuma wannan abu da ya tarar.

"Anya yaron na ba Ι—an Hammad ba ne?" Ya tambayi kansa. Wayewar garin Allah ya din ga kiran Hammad a waya amma bai Ι—aga ba. Takaici ya ishe shi, sai can wajen Azahar sannan ya kira Mahmoudu.


"Tun jiya nake kiran ka ka Ζ™i Ι—aga wayata"


Hammad ya ce "Ban jin daΙ—i ne, sai yanzu na duba wayar, ya ake ciki ne?"


Mahmoudu ya ce "A ina zamu haΙ—u, ina da magana da kai"


Hammad ya ce "Ina gurin Sultan, haryanzu bai sallame ni ba"


"Idan ya sallame ka, mu haΙ—u a saharar gidan tarihi mu sha shayi, zan nuna maka wani abu"


Hammad ya ce "To, saura na ga ba wani abin kirki ba ne, ba za ka yi mini ya jiki ba?"


Mahmoudu ya ce "To ya jiki Allah ya kiyaye gaba sai mun haΙ—u"


Hammad ya yi murmushi ya ajiye wayar.


Da yamma suka haΙ—u a sahara, lokacin rana ta yi sanyi.

Hammad ya ce "Sai wani nema na ka ke yi, me za ka bani?"


Mahmoudu ya ce "Babu komai shayi kawai nake son mu sha tare."


Hammad ya yi shiru yana kallon saharar, daga inda suke su na hango gidan tarihi, kuma suna hango wani sashe na gidan sarauta.

Ya na shan shayin a hankali yana son ya tuna wani abu, amma ya kasa.

Mahmoudu ya ce "Ya na ji ka yi shiru?"


"Ina tunanin yarinyar nan ne"


"Wacce?"


"Wadda Asal ta kawo, a matsayin mai yi mini girki, abubu da dama su na faruwa da na kasa gane kansu" Nan ya sake gaya wa Mahmoudu yadda ta hana shi hawan taguwa, da abubuwan da yake ji game da ita"

Mahmoudu ya ce "Kuma kai ba ka santa ba, baka taΙ“a ganinta ba ko a wani guri?" Ya Ι—an yi shiru Sannan ya girgiza kai ya ce "A nan kawai na taΙ“a ganinta"

"Baka tuna komai ba, da muka zo gurin nan?" Nan ma ya girgiza kai duk da yadda ya ji kansa ya fara ciwo.

Mahmoudu ya ce "Gaskiya yakamata a ce duk yadda za mu yi, muyi bincike a kanta, mu san daga ina take, kar mu sakankance wani abin ya faru. Ka san ita kanta Gimbiya Asal ba ta yin abu babu dalili, kar mu je shirin Tafawa ne"


Hammad ya ce "Gaskiya ne, amma ta ce mini daga gidan cin abinci na MaraΙ—i ta Ι—aukko ta a gurin su Al-Husssain"


Mahmoudu ya ciro wayarsa ya daddana, ya miΖ™a masa ya ce "Ka ga wani ikon Allah"

Hammd ya sanya hannu ya karΙ“a, ya yi shiru ya zuba wa wayar ido. Jiki a sanyaye ya Ι—ago ya kalli Mahmoudu ya ce "Ina ka samo wannan hoton?"


"Samo shi na yi kawai na nuna maka"


Ya damΖ™e wayar da Ζ™arfi, Ζ™irjinsa ya yi masa nauyi ya ce "Mahmoudu kuma ka tabatta wannan ba Ι—ana ba ne ba? Duk wanda ya kalli wannan hoton zai yi zaton ma nine"

"Ka na da wata matar ne da zata haifa maka Ι—a? Ko kuma Asal ta haihu ne bamu sani ba?"

Ya girgiza kai ya ce "Ko Ι—aya, amma wannan yaron buzu ne, duk inda iyayensa suke ka nemo mini su a faΙ—in Ζ™asar nan"


"Me za ka yi musu?"


"Zan yi musu alkhairi ne kawai. Amma Mahmoudu kawai ji nake kamar ina da alaΖ™a da shi, dan Allah ka tura mini hoton nan"


Mahmoudu ya karΙ“i wayar ya ce "Zan tura maka" Gaba Ι—aya jikinsa ya yi sanyi, ya kuma kasa shan shayin. Sule ne ya zo gurin a kan babur, ya kafe baburin, ya sauka ya gaida Hammad cikin girmamawa. Hammad dai ya amsa yana bin sa da kallo.

Suka gaisa da Mahmoudu ma, ya ga sun sake sun fara hira. Mahmoudu yana ta satar kallon Hammad, ko zai Ι—ago ya tuna wani abin, amma ya ga babu alamar hakan. Bayan tafiyar Sule, yake gaya masa ai abokin kasuwancinsa ne na Nigeria. Kawai ya jinjina kai.


Ƙaisar ne ya bayyana a gaban Giyaz, fuskarsa babu annuri ko kaΙ—an. Giyaz ya Ι—aga kai ya kalle shi, ya ce "Ɗan samari ya dai?"


"Zuwa yaushe zaka ci gaba da wannan mugun wasan da ka ke yi?"


Giyaz ya ce "Wanne daga ciki?"


"Kowanne ma? Ka dawowa da mutumin nan tunaninsa ya tuna da yarinyar nan, ga Ι—a a tsakaninsu ko iya yanzu ka Ι—auki fansar ai, ka Ζ™yale ta ta huta haka?"


"Yaro yaro ne. Yarinyar da kakaninta suka cutar da mu, ta zo ta Ζ™ona ni ta sanya ni jinya, ita ka ke tunanin na Ι—agawa Ζ™afa ma sassauta mata?"

"Ba na son alaΖ™ata da kai ta Ζ™ara tsami, amma zan yi abin da ba ka zato, ba zan zuba ido ka ci gaba da cutar da ita har haka ba" Ƙaisar ya yi maganar cikin Ζ™unar rai.

Giyaz ya ce "To babu laifi, ka yi abin da duk za ka yi"


Hammad kuwa da ya koma gida, ya kasa zaune ya kasa tsaye, hoton yaron nan ya din ga kaiwa da komowa a cikin kwanyarsa. Yaya za a yi a ce a samu yaro yana irin wannan kamanin da shi, ba kamanni sama-sama ba, kamanni na zahiri nesa ba kusa ba. Bayan haka yaron ya yi masa kama da wani wanda ya sani ko ya taΙ“a gani, amma ya manta waye, ya din ga duba wayarsa ko Mahmoudu ya turo masa hoton yaron, amma wayam bai tuta masa ba.

Gefe guda ya so haΙ—uwa da Nana, amma bai ganta ba. Sai washegari da ta kawo masa Abincin safe ta yi masa ya jiki.

Ya ce "Sai yanzu za ki yi mini ya jikin?" Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, saboda wani irin kyau da ta yi masa. Ga Ζ™amshin da take yi, har wani Ζ™ara nutsuwa ya yi yana kallonta.

"Tuba nake ranka ya daΙ—e" Sayyid Ι—in da take kiransa da shi, ya din ga kaiwa yana komowa a cikin kwanyarsa.

Haka da rana da ta yi shigar Atamfa, kamar ya sace ta ya gudu. Ta karya Ι—aurin Ι—an kwali, ta yi kyau.

Ya ce "Amm Asma'u ko?"

Ta jinjina masa kai duk da yadda ta ji Asma'un banbarakwai a bakinsa.

"CheriΓ© ta ce mini a gidan cin abinci na MaraΙ—i ta Ι—aukko ki ko?" 

"Eh Sayyid"

"Me ya kawo ki Niger ne? Ko takanas ki ka nemi aiki da mu, tun daga Nigeria?"

Nana ta girgiza kai ta kalle shi ta ce "Abuna ne ya Ι“ata na zo Niger neman sa, ina son a yi mini izini, nan kusa na koma Nigeria"

Ya jinjina kai kawai ba tare da ya gama fahimtar abin da take nufi ba.

A daren ne kuma Nana ta jiyo kakarinsa, Asal ta fice ita kuma ta shiga Ι—akin.

Ƙara lafewa ya yi tamkar ya shige cikin ta, saboda daddaΙ—an sanyin da ya mamaye jikinsa. A hankali ya buΙ—e idanunsa, ya ji yadda ta Ζ™anΖ™ame shi tana kuka. Ya saurara ya yi shiru ya ji ba muryar Asal ba ce. "Allah ka duba mu, ka yaye masa wannan ciwo, Allah ka yi masa maganin abin da yake damunsa. Yana jin yadda take shafa gashinsa tana ci gaba da kuka tana faΙ—in "Da gaske ba ka gane ni ba Sayyid, ko kuma wasa ka ke yi mini da hankali kawai. Na fara sarewa Sayyid, idan wasa ne ka tausaya mini haka, wahalar da na sha ta isa, ka duba ni ka duba makomar abin da na haifa maka dan Allah" Ta yi maganar tana Ζ™anΖ™ame shi tana ci gaba da kuka. Gaba Ι—aya sai ya rikice, bayan kukanta da maganganun da take yi da suka rikita masa lissafi, gangar jikinsa kuma wani saΖ™on take aika masa na daban, har wata tsuma ya fara yi. Sai dai Allah ya taimake shi, bai yi wani yinΖ™uri ba, ya ji tana magana da Ƙaisar, ta kwantar da shi a kan pillow ta koma gefe.

Tunani ya din ga yi ina Asal ta tafi? Ya aka yi Nana ta shigo har turakarsa kai tsaye haka, kuma wasu irin maganganu take yi haka? Ya yi lamo kamar bacci yake yi, amma idonsa biyu. 

Sai gefin Asuba da ta bar Ι—akin, ya tashi ya zauna, yana jin wani irin raΙ—aΙ—i a tsakiyar kansa, zuwa Ζ™irjinsa gaba Ι—aya ji yake kamar zai fita hayyacinsa Ζ™waΖ™walwarsa na nema ta hargitse.

Garau ya miΖ™e bayan sallar asuba, ya sake tuna yaron da Mahmoudu ya nuna masa, da maganganun da ya ji Nana tana yi. Ya kira Al Hussain a waya, ya ce masa lallai yana son cikakken bincike a kan Nana.

Ga Sultan ya tura shi wakilicin wani Ι—aurin aure, amma kusan baya cikin cikakken hayyacinsa, kansa cunkushe da lissafi kala-kala. Maganganun Nana suka din ga karafkiya a cikin kwanyarsa, da rungumar da ta yi masa ba tare da tsoron komai ba.

Ko da ya dawo, har ya wuce Ι—akinsa, amma kansa ya din ga wani irin ciwo, kawai ya yanke shawarar zuwa ya turke Nana, ta yi masa bayani dalla-dalla.

Sai da ya bari Asal ta yi bacci, sannan ya tashi ya tafi Ι—akin Nana. Sai dai da ya je Ι—akin ya tarar ba ta ciki, sai wayarta da take kan katifarta a ajiye.

Har zai juya ya fita, kawai ya nufi kan katifar ya sanya hannu ya Ι—auki wayar. Ya jujjuya wayar, yanayin yadda screen Ι—in wayar ya dusashe ya sanya ya gane wayar ta kwana biyu. Kawai ya danna madannin gefe a take hoton fuskar Nana da Muhsin ya bayyana a kan screen Ι—in wayar. Mutuwar tsaye ya yi zuciyarsa ta yi wani irin mummunan bugawa da Ζ™arfin gaske. Alamun tahowar Nana ya ji, babu shiri ya jefa wayar kan katifar ya yi sauri ya kashe fitilar Ι—akin.


AREWABOOKS 


Ko da Nana ta shigo Ι—akin, jikinta ya bata akwai mutum a ciki.

Da ta kunna fitilar ta yi arba da shi, ta rikice ta kusa kurma ihu, sai dai duk da a tsorace yake shi ma, amma  kasancewar sa Namiji Ι—an gwagwarmaya ya sanya ya danne tsoronsa da tashin hankalin da yake ciki, ya yi mata duk tambayoyin da ya yi mata, sai dai bai tambaye ta haΖ™iΖ™anin abubuwan da yake son tambayarta ba. Duk amsoshin da ta ba shi, ba su gamshe shi ba, haka ya fice ya bar ta.

Tun da ya bar Ι—akin kusan kwanan tsaye ya yi, ya din ga kaiwa yana komowa a Ι—akinsa ya dafe kansa, ya zauna ya tashi. Duk wani lissafi da ya yi sai ya ji babu mafita. Shi dai bai taΙ“a ganin Nana ba, amma meye haΙ—inta da yaron da Mahmoudu ya nuna masa? Sannan mene ne alaΖ™arta da shi da ta iya shiga turakarsa ta rungume shi take faΙ—ar wannan maganganun da suke nuna da alaΖ™a a tsakaninsu.

Har aka yi kiran sallar Asuba ko gyangyaΙ—i bai yi ba.

Da Asuba da ya dawo daga masallaci, har zai wuce hanyar Ι—akinta, ya koma ya nufi Ι—akin nata. Ya jima a gurin yana kallon Ζ™ofar. Ya buΙ—e Ζ™ofar Ι—akin a hankali. Ya tarar da ita tana bacci. Sai dai abin da bai sani ba, Ƙaisar ne ya Ζ™ara wa Nana nauyin bacci, amma duk abin da yake faruwa tana gani, sai dai ba za ta iya motsi ba. Cikin sanΙ—a Hammad ya Ι—auki wayar ya yi waje.

Bai ko sake nufar Ι—akinsa ba, ya fice. Gidan Mahmoudu ya tafi, ya je ya tarar da shi a zaune yana lazumi.

Sai da Mahmoud ya tsorata ya ce "Lafiya na ganka da duku-dukun nan?"


"Mahmoudu wane ne yaron nan da ka nuna mini? Kuma wace ce yarinyar da Asal ta kawo a matsayin mai yi mini girki?"


Mahmoudu ya kalle shi ya kalli screen Ι—in da yake nuna masa, tabbas Nana ce ba wata ba, amma zai so ya yi magana da Nana kafin gaya wa Hammad wani abu.

"Ka yi magana ka tsaya ka na kallo na" Ya yi maganar cikin hasala.


Mahmoudu ya ce "To ai Asal yakamata ka tambaya ba ni ba, ni fa cin karo kawai na yi da hoton na nuna maka"

Zai yi magana kansa ya sara, ya saki wayar ya fara ja da baya yana dafe kansa, ya tafi zai faΙ—i Mahmoudu ya yi saurin tare shi, ya kwantar da shi a hankali.

Ya Ι—auki wayarsa ya kira Al-Husssain. Bayan sun gaisa Mahmoudu ya ce "Imam Hammad ya yi maka magana a kan yi masa bincike a kan yarinyar da Asal ta kawo Agadez ta din ga yi masa girki ko?"


"Eh ya kira ni, ya yi mini maganar"


"To yaya ake ciki, me aka gano a kanta?"


Al Hussain ya ce "Eh ina kan yin binciken ne, amma dai wani kamfani ne, da suke samar wa mata, guraren aiki suka kawo ta. To na saka Hasna ta tuntuΙ“e su, dan ni gaskiya ban wani tantance ta ba, na Ι—auke ta aiki, saboda ta ce daga Nigeria take. To gidan aikin sun ce, su ma wata mata ce jami'arsu ta kawo musu ita. Amma za a nemo matar yanzu haka su muke saurare"

Mahmoudu ya ce "To shikenan, amma duk abin da aka Ζ™arasa bincikowa, ni zaka sanar, ka gaya masa tukuna"

Sanin alaΖ™ar da take tsakanin Hammad da Mahmoudu ya sanya kai tsaye ya ce masa to.

Hammad kuwa yana kwnace, sai jujjuya kansa yake yi yana wani irin gumi. Giyaz yake gani yana yi masa wata irin dariya, da Ζ™ara wadda ta cika masa kunne. Ya lallaΙ“a ya tashi zaune ya toshe kunnunwansa yana faΙ—in "Hasbunallahu wa ni'imal wakil"

Mahmoudu ya durΖ™usa a gabansa yana kiran sunansa, amma bai amsa ba ya rintse idanunsa.

"Sayyid, Sayyid dan Allah da gaske ba ka tuna ni ba?" Maganganun da Nana ta din ga yi masa ya din ga ji a cikin kunnensa.

"Mahmoudu" ya kira sunansa a hankali.


"Na'am Imam"


"Mene ne alaΖ™ata da yarinyar nan?"


"Amm ban sani ba tukuna, ina jiran abin da Al Hussain zai ce ne tukuna"


"Ka kirawo ta ka tambaye ta, wane ne yaron nan? Me yasa kuma yake kama da ni?"


"Za a yi, amma ka yi shiru da bakin ka mu gano komai tukuna"

Sai zuwa yamma Hammad ya Ι—an samu nutsuwa, sai dai bai sake ganin Nana ba, abincinsa ma ajiye masa ta yi.

Da daddare Asal ta Ι—auki hankalinsa sosai, saboda yadda ta sha kwalliya cikin jajayen kayan bacci sai Ι—aukar ido take yi. Yana ta Ζ™oΖ™arin kar ya shiga hakkinta, saboda damuwoyin da suka yi masa yawa.

Sai dai bai iya taΙ“uka komai ba, hankalinsa ya fara gushewa.

Wani irin haske ya din ga gani a cikin baccin nasa yana Ι“ullowa ta cikin wani mudubi, sama-sama ya din ga hango shi tare da Nana a ciki, cikin yanayin wata rayuwa da take nuna tsananin kusanci da kyakykywar alaΖ™a a tsakaninsu.

Sai dai bai gama fahimtar abin cikin mudubin ba, Giyaz ya bayyana ya huro wata irin wuta a take mudubin ya tarwatse, ya ja da baya yana kare kansa. Giyaz ya gani tare da Ƙaisar, tsananin kamaninsu tsufan Giyaz ne kawai ya sanya shi ya banbance su. Farkawa ya yi jikinsa ya Ι—auki wani irin zafi. Tashi ya yi yana zagaye Ι—akin, amma ya ci gaba da jin zafin ya tsananta kawai ya fita ya je hanyar Ι—akin Nana ya zauna. Zuciyarsa kuma sai azalzalarsa take yi a kan ya je ya samu Nana ya yi magana da ita, amma wata zuciyar ta hana shi hakan.

Giyaz kuwa faΙ—a ne ya kacame tsakaninsa da Ƙaisar.

"Ƙaisar muddin ka yi Ζ™oΖ™arin saka mutumin nan ya tuna yarinyar nan, zan iya hallakaka, ko kuma na saka shi ya haukace gaba Ι—aya"

Ƙaisar ya ce "Kafin ka halaka ni, ni zan halakka ka muddin za ka ci gaba da shiga abin da bai shafe ka ba"


"Ni zaka hallaka, Giyaz bin Jaddul Jinn?"


Ƙaisar ya ce "Ƙwarai kuwa, a kowane lokaci zan iya baka mamaki"


Hammad kuwa da duku-duku ya sake tafiya gurin Mahmoudu. Yana ganinsa gabansa ya faΙ—i.


Ya ce "Mahmoudu ka zauna mu yi magana"


Mahmoudu ya zauna yana rarraba ido"


"Ko dai ka gaya mini abin da ka ke Ι“oye mini, ko kuma zan tari duk wanda nake ganin zan samu abin da nake nema, komai zai faru sai dai ya faru. Ka yi mini bayanin waye yaron nan, kuma wacece yarinyar nan"


"Matarka ce" Ya ba shi amsa kai tsaye. Zabura ya yi ya ja da baya yana kallon Mahmoudu "Yaushe kuma ta yaya?"


"An yi mini gargaΙ—i sosai da sosai, a kan kar na kuskura na gaya maka, duk da babu wanda ya san da wannan zancen ma. Amma ko zan rasa rayuwata na yi alΖ™awarin zan gaya maka iya gaskiyata. Nana matarka ce da ka aura a Nigeria. Bisa ga binciken da nake yi ta Ζ™arΖ™ashin Ζ™asa kuma, kai ta fito nema ta zo Agadez"

Jiki a sanyaye Ya ce " Mahmoudu ban fa gane me ka ke nufi ba, yaushe na je Nigeriar har na aure ta?"


"Bayanan da Matawalle ya yi maka ba haka yake ba, ka manta da komai naka, na tafi da kai Nigeria. Yanzu duk bayanin da zan yi maka ba komai zaka fahimta ba, amma Nana Asma'u matarka ce"


Hammad ya ce "Mahmoudu, anya ba haukacewa na yi ba kuwa? Ji nake yi kamar ba mutum ne ni ba. Gaskiya"


Ya dafa kafaΙ—ar Hammad ya ce "Mutum ne kai, wasu abubuwa ne dai kawai suke faruwa amma ka nutsu, ka yi addu'a. Dan muddin ba ka tuna komai ba, ba zamu iya tunkarar kowa da maganar nan ba. Mutumin da ya zo muna tare a sahara, tare aka kamo ni da su, tare muka yi aikin gadi da su a Nigeria. Hammad ban san yaya zan yi maka bayanin jajircewa da sadaukarwar da yarinyar nan ta yi saboda kai ba." Nan Mahmoudu ya din ga yi masa bayanin wasu abubuwan da ya sani.

Ya yi shiru ya rasa gazgatawa zai yi ko Ζ™aryatawa, idan ya yi duba da wasu abubuwan sai ya ga yakamata ya gazgata batun, dan Mahmoudu ba zai masa Ζ™arya ba. 

Amma ya din ga jin sa kamar ba mutum ba, ko kuma a wata Duniyar yake ta daban.

Da daddare yana tare da Asal, tana danna waya, Nana ta kawo Abincin dare. Kamar ya yi mata magana ya fasa, sai dai Ζ™asan zuciyarsa ya din ga fatan Allah ya sanya gaske ne, Nana matarsa ce, ta kowacce fuska ta yi masa. Tun kan ya ji kan wannan burkitaccen labarin yake jin wani abu na sukan zuciyarsa a game da ita. Babban abin da yake Ζ™ara burge shi da ita, sanin mutuncin kanta da ba ta yadda Asal ta taka ta ba. SaΙ“anin waΙ—anda suke kwantar da kai Asal Ι—in ta taka su saboda abin Duniya. Ya gaza manta rungumar da ta yi masa a turakarsa.

Ta Ι—ago kai suka yi ido huΙ—u da shi, amma bai sauke idanunsa ba ya ci gaba da kallon ta. A Ι—an diririce ta ce "Na gama zan iya tafiya. Bai amsa mata ba ya tuna yadda take ba shi Nonon raΖ™umi da habbatussauda, ga abinciccikan da yake matuΖ™ar da take gwangwaje shi da su.

Asal ta ce "Za ki iya tafiya" Sai da Nana ta je tsakiyar falon sanan ya ce yana buΖ™atar lemon kankana da shayin citta da kanumfari kawai, ba zai sha na kimba ba.

Nana ta yi shiru ta ci gaba da tafiya, Asal ta ce "Kin ji ai"


A hankali Nana ta ce "Na ce miki ba ni da kunne ne, da ba zaki iya tsinana wa mijinki uban komai ba"


"Ke ba magana nake yi miki ba" Nana ta waiwaya ta ce "Ai na amsa na ce to"


Shi kuwa ya yi haka ne, dan ta sake dawowa ya ci gaba da kallon ta ko Allah zai sanya ya iya tuna wani abin.

Amma har ta kawo masa shayin tayi tafiyarta bai tuna komai ba.


Sosai faΙ—a ya Ι“arke a tsakanin Giyaz da Ƙaisar a kan Nana, Giyaz ya din ga Ι—aga Ƙaisar yana bu ga shi da Ζ™asa. Karfin Ƙaisar da na Giyaz ba Ι—aya ba ne ba, duk da Giyaz ya kwana biyu a duniya amma yana da matuΖ™ar Ζ™arfi.

Ƙaisar ya baje a gurin, bayan buga shi da jikin dutsen gidan tarihin Agadez,da Giyaz ya yi, ga Ζ™ona shi da ya din ga yi da wuta. Sai dai ganin Ƙaisar ya baje ko motsi ba ya yi, ya sanya ya nufe shi da sauri yana kiran sunansa, ya Ι—ago Ƙaisar, amma ya shammaci Giyaz, ya fito da jakar gurin Sarkin Baka daga cikin rigarsa, ya naΙ—e masa wuya da hannun jakar. Wata irin kururuwa Giyaz ya din ga yi, yana tumami a gurin yana burgima. Ihun nasa sai da ya razana da yawa daga cikin halittun da suke cikin gidan tarihin.

Ƙaisar ya miΖ™e da kyar ya tunkari wani Ι—aki, aljanun da suke Ζ™ofar Ι—akin su ka dare suka ba shi guri. Ya zura hannunsa a ya Ι—aukko kwalbar da Giyaz ya ce tunanin Imam Hammad ne a cikinta. Ya ajiye ta a nesa kaΙ—an ya ja da baya ya din ga hura iskar bakinsa a jikin kwalbar. A take kwalbar ta yi wata irin Ζ™ara ta tarwatse, a take Ι—an hayaΖ™in da yake cikin kwalbar yana zagayawa a cikin wani ruwa ya bar cikin ta. Ƙaisar ya koma kan Giyaz da ya suma a gurin, ya Ι—auke jakar da ya shaΖ™e shi da hannunta, ya Ι“ace daga gurin. 


A hankali yake juyi, ya buΙ—e bakinsa domin ya jarraba yin magana, ya ji ko maganar ta dawo ya ce "Ma vie" sai dai ya ji shiru. Shi ma shirun ya yi yana ji wani raΙ—aΙ—i tun daga cikin kansa har idanunsa. Ya yi juyi ya ji taushin abin da yake kai ya banbanta da nasu. Ya buΙ—e idanun da suke yi masa raΙ—aΙ—i da kyar yana kallon Ι—akin. Asal ce ta shigo ya kalle ta, ta ce "Amour ta gama abinci, ka taso ka karya" Ya jinjina mata kansa da ya yi masa wani irin nauyi mara misaltuwa.

Tabbas ya san Asal matarsa ce, amma ina Nana. Sai ya yi shiru sannu a hankali Ζ™waΖ™walwarsa ta tariyo masa yadda aka fita da shi daga gidansu na Buda yana fizge-fizge yana kiran matarsa Nana. Ya rintse idanunsa tare da damΖ™ar gashin kansa yana girgiza kan, saboda yadda Ζ™waΖ™walwar tasa ta hargiste, tunanin ma ya rasa wanne zai yi.

"Hasbunallahu wa ni'imal wakil" ya din ga maimaitawa babu Ζ™aΖ™Ζ™autawa. Asal ta sake shigowa ta ce "Amour wai yane? Baccin ne bai ishe ka ba? Sha biyu saura fa na rana, ba ka ko karya ba"

Ya yi mata nuni da hannunsa alamun yana zuwa.


"Ok, ni zan je gida, Abbu yana jira na" Ya jinjina mata kai"


Sannu a hankali ya fara samun nutsuwa, ya miΖ™e tsaye a hankali, ya shiga banΙ—aki ya watsa ruwa, sai dai jiri ya din ga Ι—ibarsa.

Ya fito ya zura rigarsa ya fita, ya hau kan doguwar kujera ya kwanta. Ya lumshe idanunsa, abubuwan da suka faru a Nigeria suka din ga dawo masa saΙ—ara-saΙ—ara, zuwa dawo da shi Niger da aka yi. To ya ya aka yi ya manta da ita komai nasa ya shafe da ya baro Nigeria, kuma yaya aka yi ya manta da komai nasa da yaje Nigeria. "Anya babu wata maΖ™arΖ™ashiya ko wani abu da ban sani ba, game da rayuwata ba?"


Bakinta Ι—auke da sallama ta shigo Ι—akin, hannunta riΖ™e da kwandon kwanukan Abinci.

Wata irin karaya ta ziyarce shi, zuciyarsa ta din ga azalzalarsa ya tashi ya rungume ta, Asmynsa ce, amma zuciyarsa ta din ga gargaΙ—insa kar a samu matsala, dan ya san dokar Agadez.


"Barka da wannan lokaci Sayyid, ga abincinka, na ga na safe ma baka ci ba, ko ba shi ka ke so ba ne?" Hannu kawai ya Ι—aga mata, ya lumshe idanunsa, mamaki ya cika ta, ganin ba shi da niyyar magana, ya sanya ta tashi ta fita cike da damuwa.

Tana fita ya haΙ—e tafukan hannayensa, ya dafe fuskarsa ya fashe da kuka, da wace fuskar zai kalle ta? Me zai ce mata? Ta ina za ta yarda da shi cewar ba yana sane ya Ζ™i kula ta ba. A hankali ya ci gaba da tuna tsantsar juriya da sadaukarwar da ta yi saboda shi. Ba ta haΖ™ura ba ta taho nemansa, sun haΙ—u kuma bai gane ta ba.


Ya so fita ya je ya samu Habu, amma ba zai iya ba, saboda ji yake yi tamkar an sauya masa gangar jikinsa.

Wayarsa da ya bari tun daren jiya a falon tana caji, ya Ι—auka ya duba ya ga Mahmudu ne yake kiransa.

Ya Ι—aga wayar bai yi magana ba, Mahmoudu ya ce "Hammad ina tunanin yaron nan fa Ι—an gurin Nana ne, kuma..


"Nana matata ce, ina iya tuna komai yanzu"

Mahmoudu a rikice ya ce "Ina fatan ba ka gaya mata ba?"

"Babu wanda na gayawa"

"Alhamdillah, kar ka ce mata komai, sai mun tabattar da abin da muke bincike, ka zo mu je MaraΙ—in gurin Umma, na san za ta saurareks fiye da ni. Amma ya aka yi ka tuna komai?"


"Maganar ma da kyar nake yi Mahmoudu, ba zan iya fitowa ba. Mu yi magana anjima" Ya ajiye wayar hawaye na ci gaba da zuba daga idanunsa.


Haka ya wuni ba tare da ya ci komai ba, jikinsa kuma gaba Ι—aya babu Ζ™wari, kamar wanda aka zarewa laka.

Babu abin da yake yi banda tuna rayuwar da suka yi da Nana, da girmama yadda aka yi ya manta da ita, ya kasa tuna ta.

Sai dare sannan ya iya samu ya sha shayi kawai. Sai dai zuciyarsa babu daΙ—i a cunkushe. Ya lallaΙ“a jikinsa da yake a mace, ya nufi hanyar Ι—akin Nana, sai dai ya tsaya a bakin Ζ™ofa yana lissafin me zai ce mata? A hankali ya Ι—ago hannayensa, ya kalli yatsunsa, ya tuna yadda ya yi mata kyautar zoben, a lokacin da yake tsakiyar jin shauΖ™in Ζ™aunarta. A hankali ya murza tagullar hannunsa, sai ga Arun ya bayyana. Ya ce "Na amsa kira ya shugabana"

"Ka duba mini; me yarinyar cikin Ι—akin nan take yi?"


Arun ya risuna ya ce "Tana ninkin kaya ne ya shugabana, amma alamu sun nuna a gajiye take sosai da sosai, kuma akwai damuwa a tare da ita, sai kuma bacci da take ji. Gajiyar da ta yi da damuwar da take ciki ya haifar mata da kasala sosai. Kuma ta yi kuka mai yawa awanni kaΙ—an da suka gabata".

"Ya isa haka, ina son ta yi bacci yanzun nan"

Arun ya ce "Shiga kanka tsaye mai gidana, an riga an gama."

Hammad ya numfasa ya buΙ—e Ζ™ofar Ι—akin ya shiga, ya mayar da Ζ™ofar ya rufe. Ɗakin sai Ζ™amshin turaren wuta yake yi. Tana kwance a Ζ™asa ga kayan ninkin nata a gefe. Daga ita sai zani da ta Ι—aura a Ζ™irjinta, saboda daga wanka ta fito ta zazzage kayan ta hau ninkewa ko za ta ga wayarta da ta nema ta rasa.

Jikinsa har rawa yake yi, ya Ζ™arasa gabanta, bai yi wata-wata ba ya Ι—ago ta yana kallon kyakykyawar fuskarta.

Wata irin karaya da matsanancin tausayinta ya ratsa zuciyarsa. Ya Ζ™anΖ™ameta a jikinsa yana wani irin kuka zuciyarsa na yi masa zafi da Ζ™una.


"Ki yi haΖ™uri Asmyna, ki yi haΖ™uri ki yafe mini, ni kaina ban san abin da ya same ni ba, ban san yaya aka yi na gaza tunawa da ke ba. Ban yi miki adalci ba amma kk yi haΖ™uri rayuwata" Ya din ga yi mata surutai ba tare da ta san yana yi ba, saboda wani irin nannauyan bacci da take yi.

Duk da yadda burki ya so Ζ™wace masa, kasancewarsa da Nana a wannan yanayi, da ya din ga tariyo masa irin rayuwar da suka yi ta tsantsar soyayya da Ζ™auna. Ya yi iya Ζ™oΖ™arinsa gurin sarrafa kansa da kyar gurin ganin bai aiwatar da wani abu ba. A ganinsa yin hakan tamkar rashin adalci ne kai tsaye a gare ta.

Kamar wani zai Ζ™wace ta, haka ya matse ta a jikinsa, yana zubar da hawaye, yana sake jin wani abu na ratsa lungu da saΖ™o na gangar jiki da kuma ruhinsa a game da ita. 

A duniya ba ya jin yana da wani abu da zai iya aikata wa Nana ya yi ko kwatankwacin saka mata a kan abin da ta yi masa.

Har gefin Asuba yana rungume da ita, hawaye kuma bai bar kwarara daga idanunsa ba, lissafi yake yi ko za ta yarda da shi, ta sake ba shi dama ta biyu. Ko kaΙ—an, tunaninsa da hankalinsa ba sa lissafa masa kalubalen da yake gabansa, na auren wata Ζ™abila baΖ™ar fata da buzuwa ba.

Da kyar ya iya raba jikinsa da ita, ya Ι—an yafa mata zaninta, ya gyara mata kwanciyarta, ya durΖ™usa ya sumbace ta, ya ci gaba da kallonta, daga bisani ya tashi da kyar ya fice ya bar Ι—akin.

Ko da Nana ta farka ta sha mamakin yadda ta ga jikinta, ita dai ta san ta yi mafarkin tana tare da Sayyid, amma da ta farka ta ga alamun kamar an taΙ“a ta.

Ga shi a iya saninta ninkin kaya take yi, amma ta farka ta ganta rabin tsirara, ta yi tunanin ko Ƙaisar ne, amma cikin hanzari ta kawar da wannan tunanin daga ranta da take jin tamkar saΙ“o ta aikata, dan ta san Ƙaisar bai taΙ“a yi mata yawo da hankali a abu makamancin wannan ba.

Ta yi iya Ζ™oΖ™arinta ta kawar da tunanin komai daga ranta, ta shiga banΙ—aki ta yi wanka, ta yi alwala ta dawo ta yi sallar asuba tana ta istigfari saboda yadda ta makara.

Gari yana yin haske, ya shirya ya tafi gidan Mahmoudu, duk da yadda jikinsa yake a mace.

Kallo Ι—aya Mahmoudu ya yi masa, ya gane a rikice uban gidan nasa yake.

"Mahmoudu, wallahi na gane ta, na tuna ta Nana ce matata ce, to amma yaya aka yi komai ya shafe a cikin kaina na manta da ita?"

Mahmoudu ya ce "Ka nutsu ka kwantar da hankalinka, yanzu aiki ne ya ganmu jawur, sai dai ba wannan ba dole mu tsananta bincike a kan abubuwan da suke faruwa da kai."

"Ni kaina abubuwan sun Ι—aure mini kai Mahmoudu, ji na nake yi wani iri, kamar an Ζ™wance wani nannauyan dutse daga kaina. Yanzu ta ina zamu fara, ni fa duk abin da za a yi ko Agadez za ta tashi, ba zan rabu da matata ba"

Mahmoudu ya ce "Ban gane Agdez ta tashi ba, a'a gaskiya sai dai ku ku tashi kai da ita"

Hammad ya ce "Mahmoudu ka daina wasa mana"

"Na daina wasa shugabana, amma yanzu ka tuna su Sule?"

"Na tuna shi, yanzu ina iya tuna komai fa a cikin Ζ™waΖ™walwata."

"To ma sha Allah, albishirinka"

"Mene ne?"

"Wallahi sai ka saya, ba zan faΙ—a a sadaka ba"

"FaΙ—i ko me ka ke so, wallahi zan baka"

Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Zan yi tunanin me nake so, amm yanzu yi sujudar godiya ga Allah tukuna"

"Zan yi amma fara gaya mini"

"Ta tabatta yaron nan, Ι—an Nana ne, kuma a bincikena, da Gimbiya ta zo Niger, a hannun Ummana ta sauka. Al-Husssain ya turo mini komai nata, kamar yadda ka sanya shi bincike. A zahirin gaskiya da naje MaraΙ—i na gano yaron nan a gurin Ummana, shiyasa na damu da matsa bincike. Na kira Umma mun yi magana ta tabattar mini da Ι—an Nana ne, kuma Ι—anka ne yana daga dalilin da ya sanya ta turo ta MaraΙ—i aiki gidan cin abincinku, kuma ta Ζ™arfafeta ta taho Agadez Ι—in"

A rikice ya damΖ™i hannayen Mahmoudu a gigice ya ce "Dan Allah da gaske Ι—ana ne? Ina da Ι—a? Mahmoudu? Mahmoudu dama zan haihu zan ga Ι—ana a Duniya. Subhanallahi wa bi hamdihi subhanallahil Azim. Allahumma lakal hamdu wa laka shukur. Mahmoudu dan Allah da gaske ka ke?"

Cikin tausayawa Hammad, mussaman sanin irin Ζ™alubalen da ya fuskanta na rashin haihuwa da jarabtar da Allah ya yi masa na son 'ya'ya, aka hana shi Ζ™ara aure, kuma Tafawa ya din ga Ζ™alubalantarsa da hakan yana nemana a sauke shi.

Mahmoudu ya dube shi ya ce "Nutsu ka kwantar da hankalinka, ka san ka na da matsalar zuciya kar ciwonka ya tashi, amma ka san ba zan yi maka Ζ™arya da abin da ka daΙ—e kana nema ba. Ina da tabbaci a kan abin da na gaya maka, dan sai da na gama bincike na tabattar sannan na gaya maka.

Hammad ya saki Mahmoudu, ya yi sujuda yana yi wa Allah godiya, sannan ya tashi fuskarsa sharkaf da hawaye ya ce "Yanzu mene ne abin yi? Ko ka zo mu je ka yi mata bayani, ban yi burus da ita ina sane ba"

"A'a kar mu kuskura mu sanar mata komai yanzu, sai mun gama daidaita komai da shirya yadda zamu tunkari jama'ar Agadez da wannan babban al'amari"

Ya share hawayensa ya ce "To tashi mu je MaraΙ—i na ga yarona"

"Mu bari sai gobe in Allah ya kaimu"

Hammad ya ce "Ba zan iya jira ba, kuma kar wani abu ya same shi, dole na dawo da shi kusa da ni, ko na ajiye su a wani guri keΙ“antacce, idan yana hannuna sai ta fi tsayawa ta saurare ni. Na san halinta akwai sauΖ™in kai amma akwai kafiya ba za ta saurare ni ta daΙ—in rai ba"

Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "To shikenan, amma ka jira kaΙ—an Sule ya zo, ku gaisa sai mu je MaraΙ—in tare da shi"

Haka kuwa aka yi, ba a jima ba Sule ya shigo, ya risuna yana kwasar gaisuwa gurin Hammad. Ya rungume Sule tare da yi masa godiya, a kan Ι—awainiya da kuma gudunmuwar da suka ba shi a lokacin yana Nigeria.

Suka shirya suka tafi MaraΙ—i gidan Nene, ko da Hammad ya ga Muhsin, ya kasa zaune ya kasa tsaye, ya rungume shi yana kuka, da gode wa Allah da ya sanya yana da rabon haihuwa a Duniya.

Duk da sun kai ruwa rana da Nene, ta ce ba zata ba su Muhsin ba, dan ba su yi haka da Nana ba. Hammad ya ce ba Ι—aukar Muhsin zai yi ba yana son ya nesanta su da gurin da suke na Ι—an wani lokaci, kamar yadda Hammad ma ya yi tunani haka ita ma Nene ta tabattar masa da muddin ya jewa Nana kai tsaye babu abin da zai hana Nana zuwa ta Ι—auki Muhsin ta gudu, dan ta san halinta dole ya bi komai a hankali.


A hankali Hammad ya Ι—ago Nana daga jikinsa ya ce "Asmy bacci ki ka yi?".


"Idona biyu" Ta ba shi amsa.


"Kin yi shiru, Asmy ba da gangan na ganki na Ζ™i kula ki ba, kin san muddin ina cikin hayyacina babu yadda za a yi na share ki. A lokacin ina ta shirye-shiryen yadda zamu Ι“ullowa lamarin, Tafawa kuma ya sanya ni a gaba da da haΖ™ilon ba zan yi mulki ba, ni juya ne, ga rashin lafiya ga hauka ga babu zobe. Ya daΙ—e yana jifana da kalmar juya, abin yana yi mini zafi da ciwo shiyasa na fallasa komai a lokacin da shirin duk abin da zai faru ya faru."


Nana ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yakamata mu tashi, an kira sallar Asuba".


Hammad ya ce "Haka ne, amma ba ki ce komai ba" Ta ce "Zan ce ne, ina jin bacci ne sosai ka ga kwana muka yi ba mu yi bacci ba" Ya ce haka ne. Suka tashi suka koma Ι—akin nan zai rufe amma ya tsaya ganin Nana na Ζ™ara kallon Ι—akin.

Ya ce "Wannan Ι—akin tun zamanin Sultan Azhar yake, duk Sultan Ι—in da ya zo a nan Ι—akin ne turakarsa. Kowane zamani akwai canji da kuma yadda ake Ζ™awata Ι—akin. Kafin daga bisani a daina amfani da gidan gaba Ι—aya."


Nana ta jinjina kai ta ce "Ni yanzu abu Ι—aya nake son ka gaya mini, ina da ciki ko ba ni da shi?" Ta yi maganar a Ι—an shagwaΙ“a tana marairaice fuska. Ya yi murmushi ya ce "A cikin labarin kin ji inda wani abu ya faru ne?"


"Eh mana, tun da kana zuwar mini Ι—aki ba tare da sanina ba"


Ya jinjina kai ya ce "Sosai kuwa, dan tun da na gano ke matata ce, kusan kullum tare muke kwana, ya yi maganar yana rufe Ι—akin. Ya damΖ™i hannunta suka yi gaba, ja ta yi ta tsaya tayi shiru sannan ta ce "Sayyid ba ka nuna mini mene ne a cikin Ι—akin can ba" Ya kalli Ι—akin ya ce "Hanyar tsohuwar prison ce, inda daga baya ake aikin sarrafa gold a ciki, amma yanzu babu abin da ake yi da gurin"


"Ina son ganin mene ne a ciki" Ya ce "To shikenan" Ya ja hannunta zuwa Ζ™ofar gurin, amma suka tarar da Ζ™aton kwaΙ—o a jikin Ζ™ofar. Ya ce "To ai gurin a rufe yake ma"


"Ya aka yi sauran Ζ™ofofin ba a saka mukulli ba sai wannan? A tambayi mai tsaron gidan ya buΙ—e mini zan gani"


Hammad ya ce "To ai lokacin salla ya yi"


Ta ce "Na sani gani kawai zan yi mu tafi"


Ya tsaya yana kallon Nana da rikicin tsiya, ya ce "Zo mu je sai mu yi wa mai gadin magana, ya zo ya buΙ—e mana" ta bi shi a hankali jikinta cike da kasala ga kuma bacci da take ji.


Ko da Hammad ya tambayi tsohon nan mai tsaron Ζ™ofar, sai cewa ya yi "Allah ya taimake ka, ban san wanda ya rufe Ι—akin nan ba, ya kwana biyu a rufe"


Hammad ya ce "WataΖ™ila ko masu yawon buΙ—e ido su na Ι“arna a gurin, shiyasa aka rufe"


Nana ta ce "Waye yake da alhakin rufewar?".


"Ma vie, wai lafiya kuwa?"


"Hammd sai an buΙ—e gurin nan kafin na bar Agadez"


"Shikenan na ji, za a buΙ—e amma muje mu yi salla tukuna" Da kyar ya lallaΙ“a ta suka bar gurin, saboda yadda take nema ta burkice masa gaba Ι—aya.


*****

Shukura na zaune a kan gadon Asibiti,  ta zuba ido tana kallon Ι—an jaririnta, Ζ™ato da shi mai matuΖ™ar kama da Sagir, ta din ga tuno da jaririnta da aka ce ya mutu da haryanzu zuciyarta ta kasa amincewa da hakan. Ji ta yi an turo Ζ™ofar Ι—akin ta Ι—ago da sauri, gabanta ne ya faΙ—i ta yi turus tana kallon mai shigowar.


Ayshercool 

08081012143


94

LITTAFIN KUƊI NE, KI BIYA KAFIN KI KARANTA.

0069685771

AISHA ADAM STANBIC 


Yusra ce ta shigo Ι—akin, Shukura ta yi tsuru da ido tana kallonta.

Yusra ta Ζ™arasa gaban gadon Shukura cikin damuwa ta ce "Meyasa ki ka taho nan, ki ka saka ake ta neman ki, duk hankalin mutane ya tashi?"

Maimakon Shukura ta bata amsa sai cewa ta yi "Ke kaΙ—ai, ki ka yi driving ki ka zo nan? Ina Baban Haidar Ι—in?"


"Wayarsa ce lalace, ya saka layin a wayata, yana can gurin meeting, kafin ya dawo kawai na ce bari na zo na Ι—auke ki. Wannan Ι—an da ki ka haifa ne?" Ta yi maganar tana karΙ“ar jaririn hannun Shukura. Shukura ta jinjina kai jiki a sanyaye.

Yausra ta Ζ™ura wa jaririn ido tana kallonsa, tana Ι—an murmushi ta mayar da hankali kan Shukura ta ce "Wai meyasa ki ka zo nan gurin ki ka zauna?"

"Ba komai"

"A'a da komai, kowa kin saka hankalinsa ya tashi sosai, ga ki da tsohon ciki, ki tashi mu tafi gida idan ya dawo kawai sai dai ya ganki. Abbanki har yana cewa zai Ι—aure shi, shi ne ya saka ki ka Ι“ata, ai ba dan ya dawo da ni ki ka tafi ba ko?" Ta yi maganar jikinta a sanyaye tana kallon Shukura.

Da mamaki Shukura ta ce "Daddyn ne ya ce zai Ι—aure Sagir saboda Ι“ata na?"

Yusra ta jinjina kai ta ce "Wallahi haka ya ce"

Ta yi shiru tana zunzurutun Ι“arna da zaluncin da ya gaya mata ya aikata. Ta numfasa ta ce "Amma ina fatan ba ki gaya wa kowa ina nan ba?"

"Babu wanda na gayawa, ai kin ce kar na faΙ—a, ga abinci can ma na Ι—aukko a mota, da 'yansanda zan gayawa amma na fasa"

Shukura ta yi ajiyar zuciya ta ce "Yauwwa gara da ba ki faΙ—a ba"

Yusra ta ce "To ki taso mu tafi"

"A'a ai sai an sallame ni tukuna, kuma yakamata ki koma gida saboda ki sanar masa inda nake"

"Babu inda zan koma, salon in tafi ki sake guduwa" Ta yi maganar tana Ζ™ara lulluΙ“e jaririn Shukura da yake hannunta.


*****

Cikin damuwa Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, yadda take zubar da yawu tana wani irin ihu, da gurnani duk ta yi najasa a jikinta.

Ga Ζ™afafuwanta sun shanye, ba ta gane kowa sai wannan gurnanin da take yi. Likitoci sai dai su ta mata allurar bacci. Ranar da Fadila ta je duba ta, duk da ba ta magana amma tana ganinta tare da Muhsin ta din ga ihu tana tsine masa tana faΙ—in "Da tuni wannan shegen Ι—an ne zai mutu ba Abbana ba, Allah ya isa ba zan yafe ba" Alhaji Fatuhu yana gurin, ya yi mamakin jin irin wannan maganganun da take yi, amma sai ya bar hakan a sakamakon taΙ“uwa da aka ce Ζ™waΖ™walwarta ta yi.

Likitan da ya kammala rubutu a kan takarda, ya miΖ™a wa Alhaji Fatuhu. Alhaji Fatuhu ya karΙ“a tare da kallon Likitan ya ce "Doctor haryanzu ba a gano takamaiman abin da yake damunta ba?"

"To, duk wani abu da yakamata mu duba mun duba, jininta lafiya kalau ba ta da hawan jini. Babu alamar strock a tare da ita. Sai dai idan sakamakon gwaje-gwajenta ya kammala bamu ga komai ba, zamu tura ku Ι“angaren Ζ™waΖ™walwa dama mu nan mun riΖ™e ta ne domin mu gano maΖ™asudin shanyewar limbs Ι—inta, to haryanzu ba a gano komai ba, zuwa ranar Litinin zamu fara tura ku physiotherapy ko Allah zai sanya a dace"

Alhaji Fatuhu ya jinjina kai cike da karaya, tabbas da lokacin da yake da kuΙ—insa ne, da kansa zai fitar da ita waje a duba ta. Ko a yanzu ba ya jin daΙ—in yadda da kuΙ—inta ake nema mata magani.

Haka ya tafi gida jikina a sanyaye. Alhamdillah jikinsa ya yi kyau sosai, duk da haryanzu da sanda yake yawo bai gama warewa ba, amma yana iya fita shikaΙ—ai.

'yarsa Rauda ya samu a gida yake ta yi wa faΙ—an rashin zuwa duba Hajiya Sa'a da ba son yi. "A Ζ™a'ida kamata ya yi a ce ke ce a gurinta Raudah, kina kallo lokacin da nake kwance kullum tana tafe"

Rauda ta ce "Daddy ni wallahi tsoron ganinta nake yi, kuma duk lokacin da muka je da Maman Muhsin, sai ta yi ta ihu tana tsine masa tana da tuni shi ya mutu ba Ι—anta ba, ta yi ta ihu tsoro take bani"

"To Raudah ai larura ce, ni da Allah ya jarabbe ni, ba har wari na din ga yi lokacin da nake kan fama da larura ba. Jarrabwa ce Allah ya jarabce mu, kuma ku da ku ke kusa da mu, ku ne zaku Ζ™arfafa mana gwiwa. Ku din ga haΖ™uri". Ta jinjina masa kai kawai ta ce "To"


****

Nana bayan sun idar da sallar asuba, ta Ι“ungire ta hau bacci, saboda yadda suka kwana jiya babu bacci. Ya zauna a gabanta ya zuba mata idanunsa, yana jin tamkar ya haΙ—iyeta ya din ga jinta a cikin jikinsa. Me zai yi wa wannan halitta domin nuna mata Ι—umbin godiyarsa da farincikin kasancewa da ita. Ƙarshe ya Ι“uge da sumbatarta yana shafa fuskarta, daga bisani ya tashi ya fita.

Sashen Gimbiya Bilkisu ya wuce, ya tarar ba ta fito ba, ya wuce Ι—akin da yake kyautata zaton Asal tana ciki. Aikuwa tana ciki Ι—in fuskarta ta kumbura suntum ta yi jawur, idanunta sun yi wani irin kumburi mai ban tsoro. Jikinsa a sanyaye ya Ζ™arasa gabanta ya zauna ya zuba mata ido, ta kawar da kanta gefe ta yi shiru, ji take kamar ta shaΖ™e shi ya mutu ta huta.

"Asal" Ya kira sunanta. Ta Ι—ago ta kalle shi a Ζ™ule.

"Ina roΖ™on ki da kar ki Ι—auki damuwa da tashin hankalin lamarin nan ki saka a cikin ranki. Duk abin da ya faru a cikin rayuwarmu abu ne da Allah ya riga ya Ζ™addara"


"Hammad ba na son jin komai daga gare ka, ka tashi ka tafi ka bani guri. Macuci ma ci amana, ba ka ji daΙ—in halinka ba"


Ya ce "Na ji na kuma yadda, duk abin da za ki kira ni da shi na karΙ“a, na san kina cikin fushi ne, amma ina mai roΖ™onki kar wani ya ziga ki ko ya tayar miki da hankali aurenmu ya samu matsala"


"Ka riga ka haifar da matsala a cikin aurenmu da kanka, matsalar da ba ta da magani. Har ka yi aure ka haihu ko Hammad, ba ruwanka da matsala ta kanka kawai ka sani. Ka tashi ta fita ka bani guri. Kuma wallahi ina mai yi mka rantsuwa da Allah, sai na yi mata mummunar illar da ba zata moru ba, sannan in saka a hallakata sai ta san ta jangwalo rigima mafi girman da ba zata iya tare ta ba a rayuwarta. Wallahi Hammad kai nawa ne nikaΙ—ai ni Asal ba zan yi tarayya da Ζ™asΖ™antaciyar mace a koma mene ne ba"

Ya yi murmushi ya ce "Ni dai ina roΖ™onki ki kwantar da hankalinki, kar ki biye wa zuciyarki dan kaf cika da batsewar Agadez ke Niger gaba Ι—aya babu mahalukin da zai raba ni da matata da Ι—ana. Dan gara na bar muku Agadez Ι—in da mulkinku na bi farin ciki da kwanciyar hankalina. Ba zan taΙ“a wulaΖ™antaki ko na yarda a wulaΖ™antaki ba, saboda matata ce ke kuma 'yar uwata. Amma wallahil azim duk abin da ya samu Asma'u ba zan Ι—aga wa kowane mahaluki Ζ™afa ba, a kanta komai kusancina da shi kuwa, dan Asma'u rayuwata ce, dole kuwa na bawa rayuwata dukkan wata kariya dan babu gangar jikin da take fatan rabuwa da ruhi"

Wani irin kukan kura ta yi, ta din ga kai masa duka ko ta ina, tana gaya masa maganganu masu zafi, amma ko gezau kawai ya tsaya yana kallonta. Gimbiya Bilkisu ce ta shigo da gudu tana tambayar ko lafiya saboda jin ihun Asal da ta yi.

Ta Ζ™araso ta rirriΖ™e Asal ta ce "Imam me ka yi mata?"


Ya ce "Babu abin da na yi mata"


Asal cikin gunjin kuka ta ce "Ammi ya cuce ni, ya bar gida tsawon lokaci ya je ya yi aurensa a Ι“oye ya haihu ban sani ba, sai dai na ji zance sama taka, kuma yarinyar da na kawo a matsayin kukunsa. WataΖ™ila ma shirya komai suka yi, an cuce ni am zalunce ni, wallahi Ammi ba zan zauna da wata ba. Ya aka yi na fara son shi na bari son Hammad ya yi mini illa. Ni yake gaya wa kaf Agadez babu mai raba shi da waccan Ζ™asΖ™antaciyar halittar wallahi sai na kashe ta"

Gimbiya Bilkisu ta rungume Asal ta ce "Yi shiru ki daina magana, ki daina faΙ—ar wannan maganar. Ki kwantar da hankalinki"

"Ammi zuciyata ciwo take yi mini, ko ganinsa ba na son yi, ya tashi ya tafi ya bani guri"


Gimbiya Bilkisu ta numfasa ta ce "Imam, ina ga kamar yadda ta buΖ™ata ka tashi ka tafi kawai, ka bata lokaci ta samu nutsuwa. Domin magna ta domin Allah ba ka kyautawa Asal ba, dole ta shiga damuwa da tashin hankali"


Hammad ya ce "Allah ya taimake ki, kar ki zaΙ“i Asal saboda 'ya take a gurinki, a zamana da ita har zuwa abin da ya faru ban zalunce ta ba.

Cikin Ζ™araji Asal ta ce "Ammi kin ji ko? Kina jin abin da yake faΙ—a"

"Imam ka tashi ka je kawai" Ya miΖ™e tsam ya fice daga Ι—akin, Asal kuma ta ci gaba da kuka.


Fita ya yi, ya nufi wani sashi na gidan, ya yi umarnin a je a zo masa da Sarkin baka.

Yana nan zaune hadimai biyu suka shigo, tare da Sarkin baka, ya tarar da Hammad fuskar nan a Ι—aure tamau babu annuri.

Sarki ya ce "Barka da wannan lokaci"


Hammad ya amsa da yauwwa barka.


Ya Ι—ora da cewa "Ammm duk da zan iya cewa baΖ™on Sultan ne kai, amma saboda ni aka kawo ka gurin nan, kuma ina tunanin ina da damar yin magana da yanke wa kaina hukunci"

Sarkin baka ya ce "Wannan gaskiya ne"


"Ina ganin tun da babu wani abu da ya yi saura, ka ce ba zaka iya yi mini magani ba, yakamata ka yi magana da Sultan a sallame ka ka tafi"


"Saboda ba ka son na kula matarka ko?" Hammad ya yi shiru yana kallon Sarkin baka.

Sarki ya yi murmushi ya ce "Ai duk taka tsantsan Ι—inka ina da yaΖ™inin Nana ta fika, kuma ko da take yi mini kallon ba a kan daidai nake ba, ta san ni ba mutumin banza ba ne. Wannan gidan naku ba zan taΙ“a tafiya na bar Nana a cikinsa ba saboda balahirar da na gani a gidan"


Ya kalli Sarkin baka ya ce "A matsayinka na wa?"


"A matsayina na Ι—an uwanta, ba ka san ina da alaΖ™a da ita ba? Duk da na san zaka kalli alaΖ™ar ba wata ta kusa ba, amma a yadda ba ta da kowa a cikinku daga ahalinta ina ga zan wakilci ahalinta a nan. Ina da dangantaka ta kakannin kakannin da ita. Ka kwantar da hankalinka ni ba zan cutar da kowa ba, ko na shiga tsakaninku ba amma dole zata buΖ™ace ni, idan kuma ka bari na tafi wallahi ba zan dawo ba bar abada kuma hakan ka iya zame muku matsala. Kuma ya zama dole ka bata duk wata dama ta ganawa da ni a duk lokacin da ta buΖ™aci hakan, ta nan ne za a iya samun warwarar abubuwan da suka baibaye ka. Ba na son a ji daga bakina ne, kuma ina son ta fahimci akwai abin da idan yana cikin Ζ™addararka ba ya nufin ka saΙ“a wa Allah, amma Allah na iya amfani da kai ya kawo wa wani bawan nasa mafita" Hammad ya yi shiru yana jujjuya maganganun Sarkin baka, duk da ba komai ya gane ba. Amma ya numfasa ya ce a mayar da Sarkin baka masaukinsa.


Ya tashi ya fita, ya Ι—auki mota ya bar gidan. Ya yi tafiya mai nisa aΖ™alla ta awa guda sannan ya iso wani makeken katafaren gida. Bayan ya shiga da motar ya ajiye, sai gaishe shi hadiman suke yi yana amsa musu cikin girmamawa.

Ya shiga cikin gidan ya bi wata hanya ya hau kan bene.

Ya Ζ™wanΖ™wasa wata Ζ™ofa, sannan ya saka kansa ya shiga da sallama.

Yana zaune ya harΙ—e Ζ™afa Ι—aya kan Ι—aya, yana cin inibi tare da wasu Ζ™anan yara su uku, jikin bangon Ι—akin kuma Ζ™atuwar TV ce take yi, ana shirin cartoon.

Cikin nishaΙ—i yaran ke ta cin inibin su na zubarwa, Ι—aya daga cikinsu kuma yana jikin mutumin yana tana jagwalgwala nasa inibin cikin nutsuwa.

Sallamar da ya yi ne ya sanya su waiwayawa, Muhsin ya jefar da inibin hannunsa, ya nufi Mahafinsa da gudu. Hammad ya Ι—aga shi yana murmushi ya Ζ™arasa shiga cikin falon sauran yaran maza su ma suka nufi Hammad.

Ya rungume su yana murmushi ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Kai ne ka ke wasan da su da sassafen nan?"

Zahradeen ya yi murmushi ya ce "To ya na iya, su wannan biyun sun hana mamansu sakat da rigima, shi ma Muhsin sai kuka yake yi yau, yana kiran Umma, duk sun rikitata, shiyasa na kwaso su muka dawo nan"

Hammad ya yi murmushi ya ce "Ina godiya sosai da sosai"

Zahradeen ya tsuke fuska ya ce "Da aka yi me?"

Hammad ya sake yin murmushi ya ce "Tuba nake baban Muhsin"

Imam Zahradeen ya zauna sosai ya ce "Yaya ake ciki ne? Sultan bai kuma ce maka komai ba haryanzu?"

Hammad ya girgiza kai ya ce "Ina dai jiran abin da zai ce, kawai dai yana yawan ce mini, sai abin da aka yanke na shawara"


"Ka ga Imam, ka tsaya ka nutsu da kyau ka duba makomarka da makomar wannan jaririn yaron naka. Yaron nan na buΖ™atar mahaifiyarsa, kuma ina ganin ka dawo da mahaifiyar Mahmoudu gidan nan, su zauna kafin komai ya daidaita, na ga ya saba da ita sosai. Ka san ba abu ne mai sauΖ™i su bari ka fito da ita daga gidan nan ba. Saboda ina tsoron shawarwarin da Matawalle da kum Sardauna za su yanke a kan matsalar nan. Ba dan kar na yi musu Ζ™azafi ba, da na ce sun fi mutunta Al'adar Agadez sama da addininsu."


Hammad ya ce "To ina nan dai ina sauraren su, na ji hukuncin da za su yanke Ι—in"


Imam Zahradeen ya ce "To, Allah ya sanya mu ji alkhairi"


Imam ya amsa da Amin.


****

Jikin Shukura ne yake tsuma, tana kallon Yusra a inda suke Ι“oye, ga ta rungume da jariri da yake ta Ζ™oΖ™arin farkawa ya tsala ihu.

Yusra na riΖ™e da jaririn tana yi wa Shukura alama da ta kwantar da hankalinta.

Ɗaya bayan Ι—aya mutanen suka fita daga cikin Ι—akin, Ι—ayan ya kira wayar Alhaji Zailani. Yana Ι—agawa ya ce "Yaya kun same ta?"


"Alhaji mun caje Asibitin nan kaf bamu ganta ba, ga shi sun yi mana barazanar kira mana jami'an tsaro kar su kama mu"


"An bani tabbacin ta na cikin Asibitin nan, a yadda binciken nan ya nuna, dole ku nemo ta ba sai na ganta ba ku kashe ta kawai, dan ba za ta tona mini Asiri ba"

Jaririn hannun Yusra ne ya tsala uban ihu, hankalin mutanen ya dawo kan Ι—akin, Ι—aya daga cikin su ya juya da sauri ya nufi Ι—akin.


*****


Nana tana tsaye a gaban mudubi, ta saka riga ta alfarma, gaba Ι—aya jin ta take kamar a cikin tarko, ta gaji da zaman guri Ι—ayan nan, hankalinta na kan a Ζ™arΖ™are abin da za a yi, a bata Ι—anta ta koma Nigeria.

Gefe guda kuma zuciyarta na ci gaba da wasi-wasi da son lallai sai ta ga mene ne a rufe a wannan Ι—akin na gidan tarihin Agadez.

Asal ce ta bankaΙ—o Ζ™ofar Ι—akin da Ζ™arfin gaske sai da Nana ta tsorata. Ta kalli Nana cikin doguwar riga mai maΙ—auri, ko 'yar uwatta mace zata sarawa kyawun dirin da Allah ya bata, balle Ι—a namiji. 

Wani abu Ι—acin gaske ya taso wa Asal, Gimbiya Bilkisu ce ta biyo bayan Asal. Nana dai ta tsaya Ζ™yam tana kallon su.



AREWABOOKS 


Da sauri ya dawo, ya buΙ—e Ι—akin jin kukan jariri, kawai ya tarar da Yusra a zaune a kan gado, tana jijjiga jariri.

Cikin tsawa ya ce "Ke, me ki ke yi a nan wace ce ke?"


Yusra ta ce "Kamar yaya? Nice a Ι—akin nan, lafiya suwaye ku?"


"Ya aka yi da muka shigo Ι—akin nan bamu ganki ba?"


Yusra ta ce "Ku na tsaye a bakin Ζ™ofa na zo na wuce ku, na je na karΙ“o jaririna daga Ι—akin jarirai ne, an sallamo shi daga can"


Ɗayan ya ce "Ke Ζ™arya ki ke yi, mene ne sunanki?"


Yusra ta ce "Ban gane mene ne sunana ba, suwaye ku tukuna me kuma ku ke nema a gurina ni ban sanku ba"

Ɗayan ya dubi hoton cikin wayarsa, ya kalli Yusra ya ga sam babu haΙ—i. 

Ya tunkaro Yusra ya ce "Ki gaya mana mene ne sunanki?"

"Yusra, sai kuma me?"

"Na ke ce wata mata ta tsinto, ta kawo Asibitin nan ba?"

"A ka tsinto kuma kamar wata kuΙ—i? Ni ban san zancen ba, mijina tare muka je na Ι—aukko jaririna. Yanzun nan yayata kuma za ta dawo da take zaune tare da ni. Amma mene ne dalilinku na zuwa ku ritsa ni kuna tuhuma ta." Ta yi maganar cikin dakiya tana tsare mutumin da ido. Ƙasam zuciyarta fata take yi, Ubangiji Allah ya sa kar Shukura ta ce za ta fito ta tona musu asiri.

Ɗayan ya ce "Ba fa ita ba ce ba, mu koma mu gaya masa ba ta Asibitin nan, ba a ba shi bayanin daidai ba" Suka Ζ™ara Ζ™are wa Yusra kallo sannan suka fice.

Abin da ya faru kuwa, Shukura babu yadda ba ta yi da Yusra ta tafi ba, amma ta ce babu inda za ta je Ζ™afarta Ζ™afarta, ba za ta tafi ta bar ta ba. Ga shi ta uzzura mata da tambayoyin yaya aka yi ta Ι“ata aka neme ta aka rasa. Alamu ya nuna mata haryanzu Yusra da saura kan babu daΙ—i dan haka ta ce mata sace ta aka yi, ta kuΙ“uta da Ζ™yar shi ne wata mata ta tsinto ta ta kawo ta Asibiti.

Yusra ta ce "Lallai kin auna arziki tashi mu tafi to"

Shukura ta ce "Ai ba a sallame ni ba, ba zai yiwu mu tafi ba, ba ni da cikakkiyar lafiya fa"

"To ba sai mu koma Asibiti a can cikin gari ba, kin ga yadda mamanki ma hankalinta yake a tashe, idan muka je da Baban Haidar ta yi ta kuka"


Wata Nurse ce ta yi sallama, suka gaisa da su Shukura, ta yi wa Shukura allurai. Wata ce ta sake shigowa da sauri, ta kalli Shukura ta ce "Ke ce Shukura ko?"

Ta jinjina kai.

"Wasu mutane ne suka zo, wai 'yar uwassu ce ke dubiya suka zo, amma yanayinsu kamar marasa gaskiya, mun ce babu mai wannan sunan, saboda mun san case Ι—inki, amma ga shi can ana ta faΙ—a da su sun ce sai sun caje Asibitin nan, 'yar uwassu ce ke dole su ganki"

Tsoro ne ya bayyana Ζ™arara a fuskar Shukura.

Nurse Ι—in ta ce "Ki kwantar da hankalinki, ai an kore su ma, kar ki damu" Bayan sun fita a rikice ta kalli Yusra ta ce "Ina ga wanda suka sace ni ne suka biyo ni nan, dan Allah ki tashi mu tafi "


Yusra ta ce "Ai da tuni mun tafi ki ka dage, yanzu bamu san suwaye ba, idan muka fita ai sai a samu matsala. Dole mu jira zuwa anjima sannan mu saci jiki mu gudu."

Da Ζ™yar Shukura ta amince sai dai da aka jima suna tsaka da shirin guduwa, suka ji muryar mutanen a waje, Shukura ta rikice, Yusra ta yi dabarar janta su Ι“uya.


*****


Bin su da kallo Nana take yi , Asal ta Ζ™araso gaban Nana cikin huci da zafin rai, tana kallonta kamar ta kai mata duka.

"Munafuka, muguwa, na jawo ki jikina ashe haΙ—a baki aka yi da ke a cuce ni? Kin auri mijina kin haihu da shi ban sani ba, kuma da yake ke munafuka ce, ba ki taΙ“a gaya mini saboda ba kya tsoron Allah. Wallahi idan ba ki rabu da shi ba, sai na kashe ki, na kashe Ι—an naki dole ki koma inda ki ka fito a yau ba sai gobe ba, 'yar matsaiyata Ζ™asΖ™antacciyar halitta"


Nana ta dubi Asal ta ce "Subhanallah, ai Allah kaΙ—ai ya san Ζ™asΖ™antaciyar halitta ba ke abar halitta ba. Kuma Ι—an ja da baya, numfashinki yana takura mini a fuskata, sai na baki amsar maganganun"


Asal ta rikice ta kalli Gimbiya Bilkisu ta kalli Nana, ita kanta Gimbiya ganin Nana da ta yi ta Ι—auka sokuwa ce ba ta magana. Nana ba ta jira me za su yanke ba ta matsa daga gaban Asal ta ce "Wannan abubuwan da ki ke faΙ—a, duk ba ni za ki gaya wa ba, Sayyid za ki gaya wa domin igiyar aurena a hannunsa take. Sai ki ji amsar da zai baki. Kuma ni Allah ya bani haΖ™uri da na zauna ina kallonki da mijina ban nuna miki komai ba, na biki a yadda ki ke so zuwa lokacin da ya dawo hayyacinsa ya gane ni.

Dan haka yanzu da ki ka san komai, ni ba baiwarki ba ce, kuma ba kukun mijinki ba ce, matarsa ce wato kishiyarki"


Asal cikin Ζ™araji ta hankaΙ—a Nana ta ce "Wallahi na fi Ζ™arfin na yi kishi da ke 'yar matsiyata Ζ™azama, baΖ™a mummuna. Wallahi sai na kashe ki na kashe abin da ki ka haifa." Gimbiya Bilkisu na Ζ™oΖ™arin riΖ™e ta, amma sai fizge-fizge take yi tana ihu.


"To Bismillah Asal, ki kashe ni idan har hakan zai sanya ki huce. Ba za ki taΙ“a canzawa tuwo suna ba, Hammad mijina ne, wanda na fiki Ζ™aunarsa"


"Ke ya ishe ki malama, dan kin ga na yi shiru saboda ba ki da kunya da mutunci sai ki tsaya kina gaya mata maganganun banza? To bari ki ji na gaya miki, sai kin bar gidan nan a yau ba sai gobe ba. Sai kin bar gidan nan buzayen jinin sarauta ba sa raΙ“ar talaka, balle su aure su su rayu da su. Sai kin bar gidan a wulaΖ™ance cikin Ζ™asΖ™anci kuma sai an hukunta Hammad kan laifn da ya aikata"


Nana ta Ζ™are wa Gimbiya Bilkisu kallo ta ce "Haba Mama, ke da ba da ke nake kishin ba? Nifa kamata ya yi a sara mini akan haΖ™urin da na yi. Kuma ko ba komai, dole sunan 'yar matsiyata ya shiga kundin tarihin Agadez, mace ta farko da ta karya tarihi bayan Ι—aruruwan shekaru. Ku daina zagina dan ban yi muku komai ba, abin da na sani kawai na fi Asal son Hammad har Duniya ta naΙ—e, haka zalika ba ni da tsara a zuciyarsa ki yi haΖ™uri"


"Ƙarya ki ke yi, yadda na yi amfani da kuΙ—i na mallake ki ta Ζ™arfin tsiya, haka zan yi amfani da su na yi maganinki mummunan a bar Ζ™yanΖ™yami"


Nana ta ji zafin maganganun Asal, amma ta yi murmushi ta ce "Ke kin ga alamar muni a tare da ni, kalli da kyau Gimbiya Asal. Kodayake ba wannan ba ma; kar ki manta kina magana da matar da ki kai gidan da ki ke kwana kina shaye-shaye da kaΙ—e-kaΙ—e da Ζ™awaye a lokacin da ba ta san halin da mijinta yake ciki ba, kar kuma ki manta matar da ki ke bawa magani ta zuba a shayin Imam Hammad, haka zalika matar da ta san kina ajiye masa takarda mai hoton Ζ™warangwal da yake ci da wuta, wanda shi ne yake burkita masa hankali da lafiyar jiki; wannan matar ita ce matar mijinki kuma baΖ™a mummunar da ki ke ta kushewa ki ke iΖ™irarin kashewa"


Dummm Ζ™irjin Asal ya buga da Ζ™arfi, ta Ζ™walalo ido tana kallon Nana.


Nana ta ci gaba da cewa "Ni ba karabutin mutanen da ki ka saba wulaΖ™anwatawa ba ne, kasancewar Hammad mijina ya sanya na bar idanuna a buΙ—e ta kowace kusurwa a kansa, tunda na haihu da shi, har abada ba zan bari wani abu mummuna ya same shi ba"


Asal ta tattaro jarumta ta yi murmushin Ζ™arfin hali, bayan da mararata ta cika taf da uban fitsarin tsoro.


"Ƙarya ki ke yi, ba ki da abin da za ki kawo Ζ™arshena a masarautar Agadez, saboda ba ki za hujja a kan wannan soki burutsun da ki ke yi" Ta yi maganar tana tsare Nana da ido.

Nana ta ce "Kwantar da hankalinki, ba na buΖ™atar wata hujja ko wani abu, dan har gaban Abada ba zan taΙ“a tona miki asiri ba. Ai Hammad yana sonki kuma ko ba komai 'yar uwassa ce ke, dan haka ki kwantar da hankalinki, amma daga yau da rana mai kamar irin ta yau, muddin ina tare da Hammad da ke da duk wani abu da yake kawowa rayuwarsa wani tarnaΖ™i"


Gimbiya Bilkisu ba ta bari Asal ta sake magana ba, ta kama hannunta suka yi waje.

Nana ta ja numfashi tana bin bayansu da kallo, kafin tsunduma tunani.

Gimbiya Bilkisu ta kalli Asal ta ce "Ke, kina wani wawanci har ki ka bari ta san kina wannan abubuwan? Asal kina da hankali kuwa?"


Cikin kuka ta ce "Ammi yaya zan yi, wallahi ban san da wata alaΖ™a a tsakaninsu ba, ban sani ba. Kuma ban san za ta kawo wani abu ba. Na shiga uku ba zan iya rayuwa babu Hammad ba wallahi Ammi ina son mijina, kuma ba zan iya buΙ—e ido na gan shi da wata ba ki taimake ni"

"Nutsu ki kwantar da hankalinki, bari na yi wa babanki magana a san abin yi a yau ba sai gobe ba, dole a san yadda za a yi da yarinyar nan ki daina kuka" Da kyar ta din ga rarrashin Asal.


Nana na zaune na zaman jiran dawowar Hammad,furucin Asal ya tsorata ta, ta fuskanci da gaske kowa na iya aikata duk abin da yake so, a wannan gidan domin cimma burinsa.

Ita ba ta kanta take yi ba, ta Ι—an jaririn Ι—anta da ba ta san inda yake ba ta shi take yi. Ta Ζ™udurce a ranta, idan Hammad ya dawo, bori za ta yi masa sai ya fitar da ita daga gidansa komai zai faru, amma Ζ™asan zuciyarta yana ta azalzalarta a kan son a buΙ—e wannan dakin na gidan tarihin.

Bayan azahar ya shigo, sai dai yanayinsa ya nuna mata a cikin damuwa yake.

Ya nemi guri ya kwantar da kansa a kan cinyarta. Nana ta shafa kan a hankali ta ce "Lafiya kuwa?" Ya jinjina mata kai kawai.

"Ka ci abinci ne?"

"Na ci" ya amsa a hankali.

"To meyafaru?"

Ya ce "Babu komai"


Nana ta numfasa ta ce "To dan Allah ina son ka dawo mini da Muhsin, kuma nifa na damu na koma gida, Sayyid hankalina a tashe yake wallahi, na san iyayena sun gaji da nema na"

"Asmy kar ki Ζ™ara mini damuwa dan Allah, ina sane da komai, a tsare nake yin komai in sha Allah zai wuce"

Cikin damuwa ta ce "Zai wuce yaushe? Shekera ta uku nake shirin yi a Ζ™asar nan, nima ina da ahali bai kamata na tare a nan ba" Ya tashi zaune cikin damuwa, ya kalle ta zai yi magana, amma bai yi ba ya ciro wayarsa da take vibrating"

Da to kawai ya amsa ya tashi ya fita. Nana ta koma ta nemi guri ta zauna cikin damuwa.

Da sallama ya shiga Ι—akin, ya tarar da Asal ga Sultan, ga Matawalle ga Tafawa da Sardauna sai Gimbiya Bilkisu da take ta Ζ™oΖ™arin rarrashin Asal. Gefe ga Imam Asadullahi ga kuma Imam Zahradeen rungume da Muhsin. Asal ji take kamar ta haΙ—iyi zuciya ta mutu ganin Muhsin, dan babu abin da ya banbanta shi da Hammad.

Yayi mamakin yaushe aka yi masa wannan gangamin har haka? Bayan bai jima da barin gidan Imam Zahradeen ba ya tsaya a gurin Mahmoudu.

Sardauna ya ce "Ka je ka zo da babar yaron nan" Babu kara ya karΙ“i Ι—ansa a hannun Yayansa Imam Zahradeen, ya tafi inda Nana take. Ya kai mintuna sha biyar, sannan suka dawo tare. Nana suka yi ido huΙ—u da Asal da idonta ya kumbura, Nana ta sakar mata murmushi ta kawar da kanta gefe. Guri ya tsit sai Muhsin da yake ta hawa jikin Nana yana yi mata surutunsa na yara.


Zahradeen ya ce "Imam Muhsin, ka yi shiru"


Sardauna ya yi murmushi ya ce "Har ya zama Imam shi ma?"


Zahradeen ya ce "Eh mana Allah ya taimake ka. Ɗan Imam ai Imam ne" Suka yi murmushi.


Tafawa ya ce "Yakamata mu yi abin da ya tara mu, ba tare da Ι“ata lokaci ba."


Sardauna ya ce "Haka ne kam, Imam Hammad" Hammad ya Ι—aga kai ya kalli Sardauna. "Duk da mun san aurenka da ita wannan 'yar Nigeria, Ζ™addara ne daga Allah, Amma ina fatan ka sanar da ita matar taka, sharaΙ—in Ζ™asar Agadez na rashin auren bare?".

Gaban Hammad ya faΙ—i, Nana kuma ta kalle shi suka yi ido huΙ—u.

Sardauna ya dubi Nana ya ce "Ina fatan ya yi miki bayani?"

Nana cikin girmamawa ta ce "Eh ranka ya daΙ—e. Ya yi mini na sani"

Sororo ya bi Nana da kallo.

Tafawa ya yi caraf da zancen, ganin ana neman a Ι“ata masa lokaci.

"Amm dama na nemi a yi wannan zaman ne, domin na san mene ne makomar 'yata, sannan wane hukunci za a Ι—auka a kan Hammad, bisa karya dokar Agadez"

Hammad ya numfasa ya ce "Ai ni ba ni da wata matsala da Asal, ban sake ta ban kuma yi wani abu da...


"Kai dalla rufe wa mutane baki, ai na san baka saketan ba, amma mene ne matsayinta? Zaka zauna da ita ne? Ka saki waccan yarinyar ko kuma mene ne?"

Hammad ya tsuke fuska ya yi shiru.

Matawalle ya ce "Amma mai girma Tafawa, bai kamata a je ga wannan maganar ba. Kana neman sanin matsayar Asal ne?"

Tafawa ya ce "Ka bari mu yi magana da shi ka daina saka mini baki"

Hammad ya ce "Makomar aurena da Asal, yana daga gare ta, idan tana son zama da ni, ba wani abu dama ni ban ce ba zan rayu da ita ba. Amma ina mai neman afuwarku ina shirye na Ι—auki duk wani hukunci da za ku yi mini, amma sau Ι—aya a rayuwata, nima ina neman ku yi mini alfarmar nan, ba zan iya sakin Nana ba, mussaman da rabo ya shiga tsakanina da ita. Ba zan iya sakinta ba".

Sak suka yi su na bin Hammad da kallo.

Sultan ya numfasa ya ce "Hammad, ba kai ka ke da ikon yanke wannan hukuncin ba, sai abin da muka yanke maka. Mai girma Tafawa muna mai baka haΖ™uri, Hammad ya tabattar da cewa aurensu yana nan daram, dan haka yakamata ta kwantar da hankalinta."

"Babu batun kwanciyar hankali a nan, sai zuwa yaushe zamu san matsayarta, yarinyata tana wuni ta kwana babu bacci. Kuma da haka ku ke shashantar da duk wani laifi da zai aikata ba tare da an hukunta shi ba. A wannan karon dole a bar doka ta yi aiki a kansa, kuma a zartar da duk wani hukunci da yakamata a kansa. Ya saki matar nan a yanzu ya bata Ι—anta ta tafi inda ta fito shi kuma a hukunta shi"

Hammad ya girgiza kai ya ce "Zan karΙ“i kowane irin hukunci, amma ba zan rama sharri da alkhairi ba"

Asal ta rushe da kuka tana rirriΖ™e Gimbiya Bilkisu.

95

1k ne via 0069685771

Aisha Adam stanbic 

08081012143


Tafawa a fusace ya ce "Kun gani ko? Abin har ya kai raini ya shiga tsakaninmu ya faΙ—i duk abin da ya ga dama. Kamar yaya ba za ka rama sharri da alkhairi ba, waye ya yi maka sharrin waye ya yi maka alkhairin?. Ya yi wa dokokinmu karan tsaye. Kuma dolensa ya yi murabus a gaban majalissa, a ba wa wani tun da ga taka mana doka, ga kuma rashin zobensa sannan wannan Ι—an da yake tutiya da shi, babu wanda yake da yaΖ™inin na halal ne tun da babu waliyyinsa ko Ι—aya a lokacin da aka Ι—aura auren."

"Zan jura komai amma ni ba mutumin banza ba ne ba, kuma kar ka sheganta mini Ι—a, ban san da wace kalmar za a yi mana bayanin halin da na shiga har na auri Nana ka yarda ba. Tsawon shekaru ina yi muku biyayya, ko ina so ko ba na so, dokar Agadez ba dokar Allah ba ce ku bari na samu nutsuwar zuciya mana, idan ba so ku ke ku wayi gari ku ga na bar muku duniyar ba. Ta yaya zan yi wa Allah butulci akan abin da nake nema? Yarinyar da ta rayu da ni a lokaci mafi tsananin da babu wanda zai iya zama da ni ina hauka, na haΙ—u da larurar da hatta najasata ita take gyara mini da hannunta ba tare da Ζ™yama ta ba. Babu biyayya ga abokin halitta gurin saΙ“awa mahalicci, Asal na da zaΙ“in zama da ni ko ta Ζ™i na bata wannan damar, amma ba zan saki Nana ba ko zaku rataye ni"

Sultan ya miΖ™e tsaye a fusace ya ce "Hammad!"

Imam Zahradeen ya miΖ™e tsaye shi ma, ya dubi Sultan ya ce "Ya kai Abbanmu abin alfaharinmu, a duniya ba na tunanin ka taΙ“a son wani abu kamar yadda ka ke son Imam Hammad, kuma bana tunanin akwai wani wanda yake yi maka biyayyar da yake yi maka. Tun da ta kai shi ga yin sa in sa da ku, to tabbas ya kai bango. Amma ko sau Ι—aya yakamata a ce mai girma Tafawa ya yi maka kara a kan Imam Hammad, amma duk lokacin da wani abu ya faru tsakaninsa da Asal,  Ζ™arara yake goyon bayanta a turasasawa Hammad yin abu dan faranta mata, sau Ι—aya ko dan saboda shi yakamata a yi wa dokar Agadez kwaskwarima.

Gimbiya Bilkisu ta ce "Zahradeen kana da hankali kuwa? Waye ya sanya da kai?"

"Ummi ki yi haΖ™uri, kina duba mafitar Ι—an uwanki da 'yarsa, nima ta nawa Ι—an uwan nake dubawa."


"Ni ka ke gaya wa haka Zahradeen?"


"Ina neman afuwarki, amma dan Allah kar ki yi mini mummunar fahimta Ummi."


A fusace Sardauna ya ce "Ya isa haka, ya isa, kun manta a gaban wa ku ke ne? Ya za a yi kowa ya din ga magana yadda ya ga dama, babu Ι—aa da girmamawa?" Kowa ya yi shiru.

Nana cikin ladabi ta ce "Ina mai neman afuwarku, na san wannan hatsaniyar ta faru ne duk a dalilina. Amma da na san wannan al'amari zai faru, ko haka dokar Ζ™asar nan take, ba zan yi gangancin auren Sayyid ba. 'yan uwansa ba su yi mini wannan bayanin ba. Haka zalika ban faΙ—i haka dan a ga laifinsu ba, kamar yadda suka gaya mini shi ya nemi a biya sadakina ya aure ni. Amma kamar yadda wannan shugaban ya faΙ—a" Ta yi maganar tana kallon Tafawa.

"Na amince zan Ι—auki Ι—ana na koma Nigeria, idan ma kun ce ba ku da alaΖ™a da shi, na yarda zan zame masa uwa na zame masa uba.."

"Babu inda za ki je mini da Ι—a, kuma kema babu inda za ki je" Ya katse Nana yana maganar cikin Ι—aga murya.

Cikin kuka Nana ta ce "Sayyid babu abin da ya fi ahali daΙ—i da muhimmanci, sai da na baro nawa na fito nemanka na gane hakan, ni na baro nawa ahalin kai ga ka cikin gata, sun baibaye ka da soyayya da Ζ™auna. Dama gudun rasa ahalin ga Muhsin ne ya sanya na fito nemanka da tsohon cikinsa." Ta saka hannu a hijjabinta ta ciro zoben da ya bata ta ce "Wannan zoben ina kyautata zaton shi ne zoben da ake ta magana a kansa, tun mu na Nigeria Sayyid ya bani shi kyauta, domin jaddada soyayyarsa a gare ni. Muhsin kai wa Abbanka zobensa, kuma ina fatan ba za a Ζ™wace kujerarsa ta shugabanci ba, sanyin halinsa zai zamo Ζ™warin gwiwa ga talakawan da ba su da Ζ™arfi. Na gode matuΖ™a da kulawa amma kar ku raba ni da Ι—ana dan Allah" Kuka Nana take yi sosai da sosai.

Imam Zahradeen ya dubi Nana ya ce "Ɗauki yaronki ki koma, za a neme ki" Nana ta durΖ™usa ta Ι—auki Hammad da ya riΖ™e zoben da Nana ta ba shi yana zura wa a baki. Ta karΙ“i zoben za ta ajiyewa Hammad shi, amma ya haΙ—a ya karΙ“e Muhsin.

Asal kamar ta haΙ—iyi zuciya ta mutu haka take jin yadda a gaban mutane ya nuna wa duniya ita zai iya rabuwa da ita, Nana ce ba zai rabu da ita ba.


Tafawa bai yi shiru ba ya ci gaba da zazzaga bala'i kamar zai ari baki. Har sai da ran Sultan ya Ι“aci. Ya yi wa Hammad umarnin ya tashi ya tafi kawai. Yana rumgume da Hammad ya ji muryar Asal a bayansa.

Ya tsaya ya waiwaya yana kallonta, tamkar mahaukaciya sabon kamu ta ce "Hammad yau nika tozarta a gaban jama'a ka zaΙ“i bare baΖ™uwar haure a kaina, ka Ζ™asΖ™anta ni a gaban mutane, Hammad ni?"

Ya girgiza kai ya ce "Asal ban Ζ™asΖ™anta ki ba, kuma har abada ba zan yi ba. Kamar yadda Nana ta faΙ—a daga ni har ke mu na cikin ahalinmu, muna da cikakkiyar ahali ita kuma fa? Sannan kuma harshenka alΖ™alinka Asal. Da raina da lafiyata da Ζ™uruciyata ki ka kalli tsabar idona ki ka din ga jifa na da kalaman ba kya sona ba kya Ζ™aunata. Duk da na yi miki uzurin Ζ™uruciya da yarinta a wancan lokacin, amma haryanzu ina ganin wani abu a cikin idaunki da ban tantance so ne ko Ζ™iyayya ba. Nana ta so ni a bata san waye ni ba, ta so ni a mutum mara asali da makoma auren shahada da kasada, ta rayu da ni da na Ι“acewa duniyarta ta ci gaba da bulayin nema na, ba dan tana sanya ran na saka mata ba. Ki duba ratar za ke tsakanin misalan da na baki" Ya wuce rungume da yaronsa ya tafi.

A Ζ™arshe dai Imam Zahradeen ne ya mayar da Sultan turakarsa sai jiri yake yi saboda Ι“acin rai. Ya Ι—ebo ruwa ya ba shi ya karΙ“a ya sha yana mayar da numfashi.

Sultan ya ce "Zahradeen"

Ya amsa da "Na'am Abbie".

"Na rasa ta ina zan Ι“ullowa lamarin nan gaba Ι—aya"

Zahradeen ya numfasa ya ce "Allah ya taimake ka, da Tafawa ne a matsayin da ka ke, komai za a yi ba zai taΙ“a Ζ™in goya wa Ι—ansa baya ba, dan ya faranta muku ba. Ka rintse idanunka ko toshe kunnenka. Ka kamanta yarinyar nan a matsayin 'yar cikin ka. Ana maganar shekara biyu zuwa ta uku rabonta da gidansu. Ka ga dai yadda yake zare idon nan, bai Ζ™i ya aikata duk wani abin kunya da zai zubar da mutuncin Agadez ba.

Abie shin ba ka tunanin wata aya ce Ubangiji Allah ya saukar mana, domin ya nuna mana fari da baΖ™i halittarsa ce kuma duk yana kishi da son abin sa? Ka lissafa Allah ya hana shi haihuwa duk da ya yi aure da Ζ™anan shekaru, aka hana shi Ζ™ara aure. Lokaci Ι—aya Allah ya jarabce shi da ciwon da sai da ya keta ya bar Niger ya tafi Nigeria rabon wannan Ι—an ya kai shi har can. Kuma duk da haka Allah ya jarabce shi da ciwon da sai tana kusa da shi yake samun afuwa. Yanzu idan muka rintse idanu daga hukuncin da Allah ya zartar dan mutunta al'ada muka tozarta baiwarsa kana tunanin Allah zai barmu? Ka duba Ι—an jaririn yaron nan da yake kai komo a tsakanin su cikin farin ciki idan aka raba su, duk gatan da za a nuna masa bai kai ya tashi a tsakanin iyayensa ba. Abie Mai girma Tafawa Ι—an uwanka ne, kuma Ι—an uwan mahaifiyata ne, amma ina mai tabbatar maka ba zai taΙ“a Ζ™aunarka ba, har gara ni yana yi mini kara saboda Ι—an 'yar uwassa ne, amma ba zai taΙ“a son Hammad ba. Kai kuma Hammad Ι—anka ne komai za a yi ka banΖ™ara shi ma ya samu abin da yake so"

Sultan ya yi shiru cikin nazari, ya numfasa ya kalli Imam Zahradeen ya ce "To yanzu kai me ka ke tunani, kuma meyasa ba ka yi mini duk wannan bayanin tuntuni ba?"

Zahradeen ya Ζ™ara nutsuwa ya ce "Ina tsoron shiga lamarin ne a baya, amma Hammad da kansa ya same ni da maganar, kuma ya nuna mini yarda ta hanyar ajiye Ι—ansa a gidana. Yanzu ka bar wani batun Tafawa da wata majalissa kai ne Sultan, idan ka yi doka dole a bi ta. Ka bar Imam Hammad da matarsa, kuma ka soke wannan al'adar da aka ba wa wannan Ζ™arfin, ka yi musu fatan alkhairi"

Sultan ya girgiza kai cikin jimami ya ce "Ba abu ne da zai yiwu cikin sauΖ™i ba"

"Ka duba dai Abie, ka duba makomarsu baki Ι—aya"

"Shikenan, ka je zan yi tunanin abin yi"

Imam Zahradeen ya ce "To shikenan Abie, amma dan Allah kar ka jira sai ka yi shawara da wani a cikin 'yan majalisarka"

Sultan ya ce "To shikenan"

Imam Zahradeen ya miΖ™e tsaye, ya ce "Bari na Ζ™arasa gurinsu, zan karΙ“i Muhsin na tafi da shi"

Sultan ya jinjina kai kawai.


Hammad ya shiga Ι—akin da Nana take, cike da takaicin yadda ta ce, ita ta haΖ™ura da shi, a bata Ι—anta ta koma Nigeria, sai dai ya tarar da ita tana kuka.

Ya kwantar da Muhsin da ya yi bacci, ya Ζ™arasa gabanta ya ce "Meyafaru kuma ki ke kuka?" Ta yi shiru ta ci gaba da kukan.

"Mene ne?" Ya sake tambayarta.

"Sayyid" Ta kira sunan shi a raunane. Ya zauna a kusa da ita ya ce "Mene ne?" Ya yi maganar yana Ι—ago ta cikin damuwa.

Ta Ζ™anΖ™ame shi tana kuka ta ce "Sayyid na faΙ—i haka ne dan su daina yi maka faΙ—a, amma ina sonka wallahi Sayyid, dan Allah kar su raba ni da kai" Ta yi maganar tana sheshsheΖ™ar kuka.

Shi ma rungumota ya yi sosai da sosai a jikinsa, yana wata irin ajiyar zuciya.

Da kyar ya tattara nutsuwarsa, ya ce "Ki yi haΖ™uri Ma vie, Ubangijin da ya haΙ—a mu ne kaΙ—ai zai raba mu. Ni da ke mutu ka raba in sha Allah"

Zata yi magana suka ji ana bubbuga Ζ™ofar Ι—akin, Nana ta motsa za ta tashi, amma ya riΖ™e ta kuma ya yi umarnin a shigo.

Imam Zahradeen ne ya buΙ—e Ζ™ofar Ι—akin ya shigo, kunya duk ta kama Nana.

Ya Ι—an tsaya yana kallonsu ya ce "Kuka ku ke ne?" Nana ta yi saurin tashi tana share hawayenta ta ce "A'a".


Imam Zahradeen ya ce "Ga idonki nan duk hawaye. Wai  me ki ke gaya masa ne, ya sanya duk ya rikice haka a kanki"

Nana ta sunkuyar da kai tana murmushi. 

Imam Hammad ya ce "Komai ma gaya mini take yi, shiyasa nake jin tamkar raba ni da ita, raba ni da rayuwata ne"


Zahradeen ya jinjina kai ya ce "Na ga alama ai. Amma dan Allah ku kwantar da hankalinku, ku ci gaba da addu'a, in Allah ya yarda a dalilinki za a sauya tsarin wasu dokokin na Agadez. Yanzu dai Muhsin zan Ι—auka zamu tafi"

Cikin marairaicewa Nana ta ce "Dan Allah ka bar mini shi a nan" Ta yi maganar tana kallon Imam Zahradeen.

Ya girgiza kai ya ce "A'a barinsa a nan babu tsaro, tsawon lokacin nan yana tare da ni a can gidana, gobe in Allah ya kaimu za a kawo masa maman Mahmoudu. Idan kuma ba a yarda da ni ba, na bar ku abinku"

Nana ta ce "A'a amma dan Allah ka tafi da ni, ina son na zauna tare da shi, kuma na ga Nene."

"Wani irin mugun kallo Hammad ya yi mata"

Zahradeen ya ce "Ai ko ba ki ce komai ba, dole za ki bar gidan nan, taso mu tafi"


Hammad ya ce "Ya haka? Ku tafi ku je ina? Kuma yaya zaka tafi da ita Sultan bai sani ba?"


Imam Zahradeen ya ce "Idan zaka biyo mu ne taso"

Nana kuwa ta yinΖ™ura ta tashi ta Ι—auki jakar kayanta dama da hijjabi a jikinta.


Hammad ya miΖ™e ya ce "Wai bin nasa za ki yi?"


"Ni ba na son zama a nan, na gaji" Nana ta furta tana tura baki.


Imam Zahradeen ya Ι—auki Muhsin, ya kalli Imam Hammad ya ce "Ɗaukko mata jakarta"


Zahradeen yana fita, Hammad ya riΖ™e ta ya ce "Dan me zaki ce za ki bi shi? Meye haka ki ke yi ne?"


"Amma Sayyid na ga yayanka ne fa"


"Ko ma wane ne, dan me za ki bi shi?"


Ta girgiza kai idanunta na cika da hawaye "Ni na gaji da zaman gurin nan? Ni gaba Ι—aya ma tsoro nake ji"


Sayyid ya ce "Muje kar ki yi mini kuka" Ya saka Nana a gaba, suka bi ta baya, sai ga su a harabar gidan. Zahradeen har ya kwantar da Muhsin a cikin motar.


Hammad ya buΙ—e wa Nana bayan motar, sai hararta yake yi, amma ta basar ta shige cikin motar ta kawar da kai. Haka nan take jin kamar ta fito daga kurku sai wani irin farinciki take ji da nishaΙ—i, a haka ya bar gidan da Nana a cikin motar.


Tafawa kuwa ya Ι—auki zafi, ya ci gaba da ziga 'yan majalisar Sultan a kan lallai su sanya ido a hukunta Hamma, sannan ya yi baΖ™in cikin fito da zoben nan da aka yi.


Matar Imam Zahradeen ita ma haka take kyakykyawar gaske, fara sol da ita, yaransu huΙ—u, kyawawa su ma. Sai dai Nana ta ga matar ba ta Ζ™yamace ta ba, ta rungume Nana tana faΙ—in yau ga Umman Muhsin, baΖ™ar Gimbiya ta farko a kaf faΙ—in Agadez.

Nana dai ta kasa sakin jiki da matar, dan duk mutanen Agadez Ι—in tsoro suke bata, kusan kowa ba abin yarda ba ne.

Ganin Nana ba ta sake da ita ba, ya sanya ta bar ta a Ι—akin da aka sauke ta.


Washegari da sassafe Hammad ya tafi gidan Imam Zahradeen. Zahradeen ya ce ba zai gansu ba sai bayan Azahar, tun da shi ba shi da kara.

Nana tare da Muhsin suka kwana, kasa baccin kirki ta yi ta rungume shi, cikin farin ciki tana shafa shi. Aka kawo mata lafiyayyen Abinci, matar Imam Zahradeen ta kawo mata kaya masu kyau, ta ce ta saka.

Hammad ya din ga yi wa Imam Zahradeen magiya.

Zahradeen ya ce "Ka ga ba fa magana ake ta kai shugabana ne ba, yanzu muna magana ne a matsayin ya da Ζ™ani, dan haka dole ka jira.

Sai da aka yi azahar Ι—in, suka yi salla, sai ga Mahmoudu tare da Nene.

Hammad suka gaisa da Nene cikin girmamawa.

Sai dai shigowar su Nene babu daΙ—ewa, sai ga Sule shi ma ya zo, tare da wani matashin saurayi.

Mamaki ya kama Mahmoudu, ganin Sule ya zo gidan, sai dai ya yi ta yi wa matashin kallon sani.


Imam Zahradeen ya kalli Hammad ya ce "Ka san wannan?" Ya yi maganar yana nuna masa matashin.

Ya yi shiru yana tsare shi da ido, ya ce "Na san shi, amma na manta a ina, na san dai na taΙ“a ganinsa"


Imam Zahradeen ya kira wayar matarsa, ya ce ta zo da Nana.


Wani irin kyau Nana ta yi, Ι—inki ne na buzaye a jikinta, sai Ζ™amshin turare take yi ta shigo da sallama. Kasa riΖ™e farincikinta ta yi, ta nufi Nene da sauri. Sai dai ta yi wani irin wawan burki, bayan yin ido huΙ—u da matashin saurayin, da girma da kamala suka bayyana a tattare da shi bakinta na rawa ta ce "Imrana!!!"


Wata irin sufa Nana ta yi, ta nufi Imrana a gigice, ta rirriΖ™e rigarsa tana zaro ido, tana son tabattarwa da gaske shi take gani, ko kuma gizo yake yi mata.

Cikin rikicewa ta ce "Imrana, Imrana kai ne? Imrana dan Allah mafarki nake yi ko kuma kai ne?"

Ya yi murmushi ya rungume ta idanunsa na cika da hawaye ya ce "Ni ne Nana, Imrananki ne"

"Imrana ka tafi ba ka sake nema na ba, ka tafi ka bar ni nikaΙ—ai, Imrana" Toshe mata baki ya yi, a hankali jikinta ya saki ya kuma yi sanyi Ζ™alau.

Ƙaisar ta hango a bakin teku, yana kallon ruwan, ta Ζ™arasa inda yake da sauri, ta ce "Ƙaisar kai ne? Ya jikin naka? Ka warke?" Ta yi maganar tana riΖ™o hannunsa, sai dai maimakon ta ji ta kama tsoka sai ta ji tamkar ta taΙ“a Ζ™anΖ™ara wani irin sanyi Ζ™alau.

Ya dube ta ya ce "Ina taya ki murna"

Ta ce "Murnar me?"


Ya miΖ™e tsaye ya ce "Murnar komai ma, alamu sun nuna Ubangiji yana sonki, tsananin da ki ka din ga shiga, ya zame wa wasu silar alkhairi, kuma sannu a hankali Allah yana warware miki komai"

Ta Ι—an yi shiru ta ce "Ban fahimci me ka ke nufi ba"

Ƙaisar ya ce "Ba sai kin fahimta ba. Ina taya ki murnar ganin Ι—an uwanki, sai dai haryanzu da Ι—an sauran rina a kaba. Shi wannan mijin naki, zuciyarsa da karsashinsa a kanki kawai yake. Amma bai damu da tsayuwa tsayin daka a kan abubuwa ba, ya kan karΙ“i abu duk yadda ya zo masa, ya tafi a haka komai zafi da raΙ—aΙ—in cutarwar da abin yake yi masa.

Kar ki kuskura Sarkin baka ya tafi, baku bankaΙ—o abin da yake faruwa da shi ba, sannan Giyaz haryanzu yana tare da shi, sai dai a galabaice yake yana jinya. Kin san bamu fiye saΙ“a alΖ™awari ba, dan haka abu ne mawuyaci ya rabu da mijinki ta daΙ—in rai, saboda yarjejeniyar da suka yi da bokan nan.

Kamar yadda na sanki, ki ci gaba da addu'a, zan iya cewa kusan komai ya zo Ζ™arshe, sai dai ban san abin da ka iya faruwa a gaba ba."


"Ma vie" Ya yi maganar yana shafa fuskarta, a hankali ta buΙ—e ido ta kalli Sayyid, ta sake Ι—aga kanta, ta ganta a jikin Imran. Kuka take sosai da sosai, da ita kanta ta kasa tantance ko na mene ne.

Imrana da yake share hawayen ya ce "Ki yi haΖ™uri ki daina kukan nan haka"

"Kukan ne yake zuwa" Ta yi maganar wasu hawayen na ci gaba da zubowa.

Ya kalli Muhsin da yake ta guje-guje a Ι—akin, ya kalli Imam Zahradeen ya ce "Wannan ne Ι—an nata?"

Ya yi murmushi ya jinjina masa kai.

Nana ta sake cewa "Imrana ya aka yi ka san ina nan?"

Ya yi murmushi ya ce "Bacci na kwanta, kawai na farka na ganni a nan"

Kukan da take yi bai hana ta yin murmushi ba. Ta ce "Nene kin ga yayana, duk duniya shi ne kaΙ—ai wanda muke ciki Ι—aya da shi"

Nene ta ce "Allah sarki, ga kammanni nan ku na yi da shi"

Imam Zahradeen ya ce "Yakamata a fara ba wa baΖ™i"

Nana ta ja jikinta ta zauna, ta Ζ™ure Imrana da ido, gaba Ι—aya ya nutsu, babu wannan hauma-haumar tasa.

Shi kansa Imam Hammad kallon Imam Zahradeen yake cike da mamaki yana jiran jin bayani daga bakinsa.


*****

Jamila ce a durΖ™ushe tana wani irin kakari, ji take yi tamkar barin duniyar za ta yi saboda matsananciyar azabar da take ji. Ta Ι—aga kai da kyar ta kalli Mama, a galabaice ta ce "Mama, me ki ka bani a cikin kukun nan na sha, Mama zan mutu zan rasa raina"


Mama ya ce "Ai gara ki mutun na huta Jamila, gara ki tafi asirina ya rufu da wannan masifar da ki ka Ι—aukko mini. Ba dai ke taurin kan tsiya ba, ai na san yadda zan yi da ke nima. Ƙwayar zubar da ciki na je na sayo a gurin Mariya Likita na zuba miki, dan ba za ki haife mini shege a gida ba".

Jamila ta girgiza kai cikin matsananciyar azaba ta ce "Mama ba ki kyauta mini ba, zan iya rasa rayuwata Mama, kin san azabar da nake ji kuwa?"


"Tun da ki ka iya jure miΖ™awa maza jikinki, dole ki jure azabar fitar cikin"


"Wayyo Allahna" Ta faΙ—a a marairaice tana sake durΖ™ushewa cikin azababben ciwo.


*****

Fadila ce ta fito daga banΙ—ain da ta shafe a Ζ™alla awa Ι—aya da rabi a ciki, tana tufaka da warwara, sosai an matsa musu a kan su tashi su bar gidan. Har ta gaji da zuwan da wanda ya sai gidan yake yi yana Ι—aga musu hankali kamar ba abokinsa ne ba. Ga shi haryanzu bai gama samun cikakkiyar lafiya ba, lallaΙ“awa kawai yake yi, shi kansa ya rasa inda zai sanya kansa saboda damuwa, Ζ™arfin hali kawai yake yi.

Tana fitowa ta tarar da shi a tsaye da waya a hannunsa. Cikin damuwa ta ce "Lafiya kuwa?"

A sanyaye ya ce "Coustom ne suke nema na a Lagos"

Ta Ι—an yi saroro ta ce "Suke neman ka kuma, lafiya dai?"

Alhaji Fatuhu ya ce "Wallahi ban san mene ne ba, ga shi ko kuΙ—in motar tafiya ba ni da su. Allah ya sa ba wani abin ne mara daΙ—i ya sake tasowa ba"

Fadila ta ce "Jikina ba ya bani wani mugun abin ne, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ne ya sanya suke neman ka. Bari na kira Umma idan da kuΙ—i a hannunta ta ara mini"


Ya ce "A'a, kin san ba shi ne da ita ba, ba dan halin da Alhaji Zailani yake ciki na Ι“atan 'yarsa ba, ai da shi zan cewa ya biya mana, ya raka ni muje mu ji ko mene ne"

Ta Ι—an tsuke fuska ta ce "Dan Allah Daddy ka daina gayyato mutanen nan haka, mu din ga shiru tukuna idan alkhairi ne idan Allah ya tabattar sai kowa ma ya ji. Da za a samu kuΙ—in sai Umman su Raudha ta raka ka. Amma hakan nan za ka yi haΖ™uri mu nemo kuΙ—i ko ta mota ne ku tafi tare. Ya hayyu ya Ζ™ayyum Ubangiji Allah ka sanya alkhairi ne.

Ya amsa da "Amin."

****

Gaba Ι—aya Shukura ta yi saranda da da ba zata tsira ba, daga ita har jaririnta, Yusra ta ce mata duk za ta yi ta nemi guri ta Ι“uya, ba za ta iya fitar da ita da jaririn lokaci Ι—aya ba, ta fuskanci mutanen nan, su na harabar inda Asibitin yake.

Shukura na kuka ta ce "Yanzu tafiya za ki yi ki bar ni?"

Yusra ta ce "To yaya za mu yi, idan ba haka ba daga ke har jaririn za ku iya rasa ranku, ki bari na fita da jaririn, ki san duk yadda za ki yi ki Ι“uya ko ki gudu. Amma Shukura suwaye wannan suke binki haka? Kuma me ki ka yi musu?"

Shukura na kuka ta ce "Dogon zance ne, ke dai tafi da shi, idan ban rayu ba ma dan Allah ki kula mini da shi"

Yausra ta bata mukullin motar da ta zo da ita ta ce "Idan kin samu dama, ki gudu ni zan san yadda zan yi" ta goya jaririn Shukura na kuka, Yusra ta fice daga Ι—akin.


****

Imran ya ci gaba da kallon Nana cikin zallar farin ciki da shauΖ™i, tare da kallon Muhsin dukkaninsu cikin shiga ta alfarma da kamala.

Ya ce "Nana, ashe zan gan ki cikin farin ciki da kwanciyar hankali haka a rayuwata? Allah na gode maka da ban tursasa ki na kashe miki aure ba, ashe alkhairinki yana tattare da auren.

Kasancewar daga Nana sai shi a Ι—akin, ta Ι—an jinjina kai ta ce "Amma an sha gwagwarmaya Imrana, duk da na gode wa Allah da ka bayyana yanzu, ka zo a gaΙ“ar da na fi tsananin buΖ™atar ka, amma meyasa ka yi fushi da ni baka sake dawowa ba, dama akwai abin da zan yi maka ka yi irin wannan fushin da ni?"

Ya girgiza kai ya ce "Babu shi, abin da za ki yi mini da zai sanya na guje ki. Amma ki yi haΖ™uri kaΙ—an za ki ji abin da ya faru. Na yi burin na samu wadata ki huta na gatanta ki Nana, amma Allah ya Ζ™addara ke ce zan huta a dalilinki."

"Ban gane ba, me ka ke nufi?"


Imrana ya ce "Za ki gane ne"


"Imrana ina Baba da su Jamila, na san ba zuwa gurin su Mama ka ke yi ba, da gurin su Ummi, ban san da wani idon zan tunkari gida ba, na tafka babban kuskure da bana tunanin za su iya yafe mini"


"To kar Allah ya sa su yafe Ι—in mana, ke dai ba kin riga kin yi gaba ba, su zauna da rashin yafiyar"


Nana ta buΙ—e baki ta ce "Lallai hali zanen dutse, Imrana kar Allah ya sa su yafe, su Baban?"


"Eh Ι—in, ai ke yakamata a ce ma sun nemi yafiyarki, idan sun yafe shikenan, idan ma ba su yafe ba za ki ci gaba da rayuwa wataΖ™ila ma babu wanda ya neme ki a cikin su"


Hammad ya dubi Imam Zahradeen bakinsa fal tarin tambayoyi, amma yanayin fuskar Zahradeen Ι—in babu alamar zai amsa masa tambayoyin nasa"


Imam Zahradeen ya ce "Ya na ga ka Ζ™ure ni da ido ne?"


Hammad ya ce "Abubuwan da na gani suka Ι—aure mini kai nake son ka yi mini bayani"


Ya numfasa ya ce "Bayani ya zama dole Hammad, amma ina fatan zaka yi mini afuwa da duk abin da za ka ji a bayanin nawa"

Imam Hammad ya ce "In sha Allah"

Kamar yadda suka taru a falo Ι—azu, haka suka sake taruwa bayan sallar la'asar.

Imam Zahradeen ya ce "Ina yi wa kowa barka da zuwa wannan gida nawa. Wasu sun san da zuwan wasu, wasu ba su zan da zuwan wasu ba. Cikinmu akwai yan gidanmu na sarauta, akwai wanda ba su da alaΖ™a da gidan namu, amma a yanzu tilas mun zama abu guda, kuma zan warware wani abu da na san wasu za su gan shi wani iri, amma yi haΖ™uri da yadda komai zai zo, duk wanda yake gurin nan abin ya shafe shi ne.

Imam Hammad, wannan bawan Allah da ku ke gani Sulei yarona ne, zamanku a tare da shi, da duk wani abu da ku ke ciki, wani abu ne na shiri da na yi shi" Gaba Ι—aya suka Ι—aga kai suna kallon Sule tare da Imam Zahradeen. Bai damu da kallon da suke yi masa ba, ya ci gaba da cewa; wannan matashin saurayin da yake Ι—an uwa ga matarka Hammad wato Imran, bayan da ya je ya same ku, ya yi yinΖ™urin tafiya da Ζ™anwarsa, hankalinka ya tashi sosai, ka kira Mahmoudu ka gaya masa, shi kuma sun yi maganar da Sulei, shi kuma Sulei ya gaya mini. Gudun kar ya kawo tangarΙ—a a rayuwar aurenku, ya sanya na saka aka bi diddigi aka nemo shi.

Aka kawo mini shi har Agadez, na yi masa bayanin komai, da ko kai waye, da alfarmar da nake nema ya yi mini na yin shiru da bakinsa ya yi haΖ™uri ya bari ku rayu da Ζ™anwarsa, kai mutum ne mai asali da daraja, Ζ™addara ce ta faΙ—a maka.

Sai dai ya fututtuke yana ganin kamar rainin hankali ne kawai, idan kana da asali da daraja dan me zan barka a wulaΖ™ance kana gadi. Da kyar ya fahimci abin da nake son ya fahimta, sai dai duk da haka gudun ya Ζ™ara burkicewa saboda na ga rigimamme ne, na aika shi waje karatu. Sunansa yana cikin jerin waΙ—anda ka ke bawa tallafin karatu a Agadez, a cikinsu na saka shi aka kuma fitar da kuΙ—in dan kai ka biya masa ba ni ba.

Fuskar Hammad ta yi wani irin ja, cikin kakkausar murya ya ce "Zahradeen"


"Hammad" Ya miΖ™e tsaye ya ce "Labarin nan bai cika ba me ka ke Ι“oyewa?"


Imam Zahradeen ya yi murmushi ya ce "Wannan rigimar cikin gida ce, ka bar maganar a haka"


"Ba zan bari ba, sai ka yi mini cikakken bayani"


Mahmoudu shi kansa Ι—aurewa ya yi, kenan duk wannan abin Sulei, kallon biri yake yi masa yake yi musu na ayaba, ya san komai, ya san waye Imam Hammad, amma ya zauna da su har da yi masa masifar kullum yana Ι—awainiya da mutumin da bai san asalinsa ba?"

Gaba Ι—aya jikin Hammad ya hau tsuma, yana neman ya fita hayyacinsa.

Hammad ya riΖ™e rigar Imam Zahradeen yana tsare shi da idanu cikin tuhuma.

Zahradeen ya yi murmushi ya kalli Mahmoudu ya ce "Ni ne nake tura maka saΖ™on cewar kar ka dawo da Hammad Agadez, lallai ka tafi Nigeria. Kuma ni na shirya yadda aka haΙ—a ku da Sule har ku ka yi aikin gadi tare. Sule ni yake yi wa aiki, duk wani abu da yake faruwa, da motsinku Sule yana sanar da ni. Kuma nine nake tura maka kuΙ—aΙ—e domin kula da Hammad da iyalin da ya aura, kuma aka sanar da ni kwanciyar hankalin da yake ciki.

Sai dai bayan kame ku gaba Ι—aya na kasa sanin halin da yake ciki, na tura Nigeria a bincika mini, aka tabattar mini da kama ku. Na ci gaba da bibiyar inda Nana take, amma binciken nawa bai cim mata ba, tayi Ι“atan dabo, ga kuma alΖ™awarin da na yi wa Ι—an uwanta, na zan tabattar da tana cikin Ζ™oshin lafiya. Sai dai da Allah ya dubi zuciyata sannu a hankali, komai ya din ga warwarewa, tun kafin ka gane ta, ni na gane ta saboda har hotonta ina da shi. Kuma aka yi sara a kan gaΙ“a ka zo ka same ni, da maganar cewa ka yi aure a Nigeria.

Sai na bika muka tafi a haka, ban nuna maka komai ba, zuwa lokacin da nake ganin ya dace ka san komai!.

96

1k ne via 0069685771

Aisha Adam stanbic 

08081012143



Hammad bai iya cewa uffan ba, kawai ya tashi ya nufi hanyar fita. Imam Zahradeen kuma bai motsa daga inda yake ba, ya zuba masa ido. Nana ta tashi a rikice ta ce "Sayyid ina zaka je ne? Kar ka yi fushi, ka tsaya ka saurare shi, kar ka yi wa al'amarin wata mummunar fassara.

Bai tsaya ba kawai ya yi gaba, Mahmoudu ma tashi ya yi ya bi bayansa da sauri.

Wannan shi ake kira da ga Ζ™oshi ga kuma kwanan yunwa.

Ga farincikin ganin Imrana, amma alamu sun nuna Hammad ya Ι—auki zafi da abin da Yayansa ya aikata, duk da ta wani fannin taimakonsa ya yi, amma ta wani fannin abin a saka masa ayar tambaya ne.


*****

Sagir kuwa kamar zai haukace, saboda tashin hankali bai fita daga tashin hankalin Ι“atan Shukura ba, ga Yusra ma ya neme ta ya rasa, tun safe ana maganar sha biyu saura na dare.

Ga shi layin wayarsa yana cikin wayar Yusra, haka a dole yaje police station ya kai rahoton Ι“acewar Yusra. Ya fara tunanin kar a fara zarginsa da ko shi ne yake aikata wani abu, matan nasa suke Ι“acewa.

Ƙarfe shida na safiya, suka ji ana bugun gate, bugu na tashin hankali kamar za a Ι“all gate Ι—in. Afujajan mai gadi ya buΙ—e gate Ι—in, babu tsammani yaga Yusra a tsaye kamar korarriya. Ya zaro ido yana kallon ta cikin matsanancin mamaki. Gaba Ι—aya gari ma bai gama waye ba, ya kalli hannunta ya ga jariri, bai yi magana ba ta banke shi ta wuce cikin gidan.

A falo ta tarar da Antynta tare da mai gidanta, saboda bugun Ζ™ofar da suka ji ana yi.

Cikin mamaki Antyn ta ce "Yusra lafiya ki ka zo gidan nan da sassafen nan haka? Daga Kanon ki ka taho Abuja" Yusra ta yi shiru ba ta yi magana ba, kallon falon Yusra ta hau yi, tana tunanin yaya aka yi ma ta zo nan. Ita dai ta san ta Ι—aukko jaririn ta fito titi, tama tafiya a hankali tana waige-waige, daga nan bata sake sanin abin da ya faru ba, ta ganta a Ζ™ofar gidan Antynta da ta koma hannunta a Abuja.

Mai gidan ya Ζ™arasa gaban Yusra, ya karΙ“i jaririn da ya fara kuka a hannunta. Yusra ta nemi guri ta zauna tana mayar da numfashi.

"Yusra dan waye wannan, a ina ki ka samo shi?"

Mai gidanta ya ce "Rabu da ita ta huta, wannan yaron a samo madara a bashi, sannan a kira mijinta mu ji ko da saninsa ta taho, kuma me yake faruwa"

Antyn ta jinjina kai cikin damuwa, da fargabar a ina Yusra ta samo Ι—a.


*****

Jamila kuwa ta din ga zubar da jini babu Ζ™aΖ™Ζ™autawa, ga azababben ciwon mara da ta din ga yi. Ta kwana ta wuni tana wata irin burgima da kuka mai ban tausayi.

Baba ne ya dawo ya tarar da Jamila a cikin wannan yanayin.

Baba ya ce "Rabi wai me yake damun Jamila haka ne, wannan wane irin ciwo ne tun jiya?"

Mama ta ce "Ba fa wani abin ba ne ba, al'ada ce ta zo mata take shan wahala."

"Haba, wahalar ta isa haka, wane irin ciwo ne haka, anya ba za a kaita Asibiti ba"

Mama ta ce "Ba sai an kai ta ba, na bata magani za ta warke"

Baba dai bai ji ya gamsu ba, amma ya Ζ™yale su kafin ta hayayyaΖ™o masa da masifa.


*****

Asal duk ta fita hayyacinta, kullum cikin kuka, ta yi wata irin muguwar rama.

Tana zaune a Ι—akinta, Tafawa ya shigo Ι—akin, ta Ι—aga kai ta kalle shi. Ya ce "Dalilin me ne ne ya sanya ba kya cin abinci?" Ta yi shiru ba ta ce masa komai ba.

"Kar ki saka damuwar abin da yake faruwar nan a cikin zuciyarki, duk yadda zan yi dole sai na tabattar da an hukunta Hammad, ba zai ci bulus ba abin da ya aikata."

Asal ta yi shiru, wani irin baΖ™in ciki na taso mata a zuciyarta, ta din ga tuna yadda mahaifin nata ya din ga ingizata da tursasa ta aikata Wasu abubuwan. Ya yi wa rayuwarta illa duk a Ζ™oΖ™arin sa na ganin ya cimma wani burinsa da abu ne mai wahala ya samu cikarsa.

Yana magana amma ta lula Duniyar tunani, ta tuna lokacin da aka kusa auren, ya kawo mata wani abu a Ζ™oΖ™o ya ce ta sha, sai bayan da ta sha sannan ya ce bai aura mata Hammad dan taje ta haihu da shi ba, domin har abada baya fatan ya haihu balle ya sanya ran samun magaji ya Ζ™ara dagula masa lissafi gurin cim ma burinsa.

Wasu irin zafafan hawaye suka zubo wa Asal, ta daΙ—e da gane rashin haihuwarta na da nasaba da wannan magani da mahaifinta ya bata, duk da a Ι“oye ta je ganin likita a kan matsalar rashin haihuwar, aka ce mata hakan yana da alaΖ™a da ta'amalli da chemicals masu Ζ™arfi da ta yi. Da fari ta yi tunanin shaye-shaye da take yi, sai dai ko da shaye-shaye ta fi kyautata zaton maganin da Tafawa ya bata ne sila.


Nana ta samu ta sake sosai da sosai da Imran ta din ga bashi labarin abubuwan da suka faru bayan tafiyarsa, wasu guraren sai da ya yi hawaye. Haka kuma ya din ga yi wa Nene addu'a, a kan abin da ta yi wa Nana na taimako.

Nene ta ce "Babu komai, Ι—a na kowa ne. Kuma in sha Allah Nana daram zata zauna a Ι—akin mijinta"


Nana ta kalli Imrana ta ce "Imrana tsoro nake ji, ban san yaya su Baba za su kalle ni ba, ban san me zan ce musu ba, ga shu kai ma tun da ka tafi ba ka je gidan ba?"


Imrana ya ce "Ba za ki daina wannan zancen ba, ba abin da za su yi miki. Nima ban je Ι—in ba"


Nene ta ce "Ai dole mu kafa mu tsare, daga nan Agadez a tashi tawaga, su je har gida a bawa iyayenku haΖ™uri, kaga yanzu kai ne waliyyinta, a tashi manya daga Agadez su je har Nigeria su ba wa iyayenku haΖ™uri a kan abin da ya faru, sannan kuma a yi. Sannan ya zama dole a yi wa Nana duk wani abu na dukiyar aure, a yi cikakken biki na 'yar gata duniya ta shaida auren yadda yakamata, dan gudun kar ma a zo a samu wata matsala a nan gaba."

Imarana ya ce "Wannan gaskiya ne, amma kina ganin za su amince da hakan?"

Nene ta ce "Dole za su amince, ko dan son da suke yi wa Ι—an su. Tun da Ι—ansu yana son iyalinsa."


Hammad kuwa gidansa ya koma, sai dai ya rasa abin da yake yi masa daΙ—i, ya din ga juyi yana tunani, tare da tambayar kansa, kenan duk abin da yake faruwa da sanin Zahradeen. Kasa jurewa ya yi ya tashi ya tafi gurin Sultan. Yana zaune Gimbiya Bilkisu ta sanya shi a gaba, tana ta maganganu a kan kar ya nuna son kai akan hukuncin da zai yanke, kuma ya duba Asal ita ma a yi mata adalci.

Babu tsammani sai ga Hammad ya shigo, yanayin yadda fuskarsa ta yi jawur, ya sanya Sultan miΖ™ewa yana tambayarsa ko lafiya? Amma Hammad ya yi shiru bai ce komai ba. Sultan ya kama hannunsa ya shiga da shi cikin Ι—akinsa, ya zaunar da shi ya ce "Ka gaya mini mene ne?" Sai gumi da yake ta tsatstsafo masa amma bai yi magana ba.

Mahmoudu kuwa daga fitowar Hammad ya biyo bayansa, ya neme shi ya rasa, yana son su yi magana, ya lallaΙ“a shi su bi abin a sannu su fahimci Zahradeen, dan ya ga alamar ya Ι—au zafi lamarin ya Ι—aure masa kai.

Matar Imam Zahradeen ta yi sallama, suka amsa. Ta kalli Nana cikin sakin fuska ta ce "Gimbiyar Imam Hammad, Imam Zahradeen yana kira"

Nana ta yi murmushi ta ce "Nana dai za ki ce"

"Ina, wa ya isa faΙ—ar sunan Gimbiya" Nana ta yinΖ™ura ta tashi ta bi bayanta.

Bayan sun shiga, matar Zahradeen ta koma, Nana ta zauna a Ζ™asan Carfet.


Ya ce "Kin ga mijinki ya Ι—auki zafi, yaΖ™i tsayawa ya saurare ni, balle ya fahimce ni, amma na ga ke kina cikin nutsuwarki, za ki fi fahimtata. Amma kafin nan kin ga ke ki ka zauna da shi, ko za ki iya gaya mini abin da ki ka sani, bayan haΙ—uwarku lokacin yana cikin rashin lafiya?"

Ta jinjina masa kai, sannan ta yi masa bayanin, abin da take ganin ya dace ta gaya masa.

Ya ce "Shikenan, Sultan ya kira ni a waya, ya ce yana nema na, na san wataΖ™ila ya gaya masa ne, tare da ke za mu je gobe in Allah ya kaimu da safe"

Nana ta amsa masa da "To"


*****

Hajiya Halima ta kiΙ—ime, tun bayan da Sagir ya kira wayarta yake tambayarta, ko Yusra ta je gidan.

Har ta fara shirin tafiya Kano, Yayar Baban Yusra ta kira ta a waya, ta sanar mata ga Yusra ta zo tun Ζ™arfe shida na safiya tare da wani jariri da ba su san a ina ta samo shi ba.

A kiΙ—ime Hajiya Halima suka shirya, suka tafi gidan Antyn, su na zuwa suka tarar da ita cikin yanayin Ι—imuwa, ba ta magana ga kuma wani Ζ™osashshen jariri da ba a san inda ta samo shi ba.


Hajiya Halima ta ce "Ai ni mijinta ya kira ni cikin tashin hankali, yake tambayata wai ko Yusra ta zo, ya neme ta ya rasa. Hankalina a tashe na fara shirin tafiya Kano, kin san uwargidanta fa ita ma an neme ta an rasa.


"Mami" Yausra ta faΙ—a da Ζ™arfi.

"Na'am Yusra, sannu"

"Ku gaya wa Daddyn Haidar yaje ya Ι—aukko Shukura, za su kuma sace ta"

Cikin rashin fahimta ta ce "Suwaye?"

"Nima ban san su ba, amma sace ta za su yi, na baro ta a can"

Duk yadda suka yi da Yusra ta yi musu bayanin yadda za su gane, ta kasa sai kukan aje a Ι—aukko Shukura kar a kuma sace ta.

Hajiya Halima ta kira Sagir da lambar da ya kira ta, ta sanar masa ga Yusra a Abuja tare da wani jariri da ba su san a inda a ta samo shi ba. Cikin kiΙ—ima da tashin hankali, ya Ι—auki mota ba tare da ya gaya wa kowa ba, ya kama hanyar Abuja.


*****

Bayan su Nana sun hallara a gaban Sultan, ta yi tozali da Giyaz a tsaye da sandarsa a bayan Hammad, sai da jikinsa duk rauni ya Ζ™ara tsufa ya yi wani iri. Jikinsa sai hayaΖ™i yake yi ya zubo mata ido.

Sultan ya dubi Imam Zahradeen ya ce "Zahradeen me ka yi wa Ι—an uwanka ne, ya Ζ™i magana, sunanka kawai ya furta ya yi shiru, a nan muka kwana tare da shi, ko sau Ι—aya bai yi magana ba.

Imam Zahradeen ya haΙ—iye wani abu mai Ι—aci a wuyansa, yana tunanin ta ina zai fara bayani.

Nana ta ce "A je a zo da Sarkin baka gurin nan, idan ba haka ba Giyaz zai iya haddasa matsala"

Duk suka kalli Nana Imam Zahradeen ya ce "Waye hakan?"

"Ku zo da shi dan Allah, kar a samu matsala wani abin yake son aikatawa"

Ganin Nana na neman burkicewa, ya sanya Sultan Ι—aukko wayarsa ya Ι—an daddana, Hammad dai bai ce komai ba.


Imam Zahradeen ya ce "Kafin na ce komai, ina mai neman afuwarku a kan abin da zan faΙ—a, kuma ina neman afuwa da ni da waΙ—anda zan faΙ—a a cikin maganata.

Na ji daΙ—i sosai da sosai da ka neme mu a keΙ“antaccen guri kamar haka, ina roΖ™on ku rufa mana wannan asirin dan Allah"

Sultan ya ce "Zahradeen, ka tafi kai tsaye ka yi mini bayani, kana ta zagaye-zagaye daga mu sai mu a gurin nan"

Ya Ζ™arasa maganar yana kallon wayarsa, ya danna ya ce "Ku ba shi dama, shikaΙ—ai ya shigo"

Sarkin baka ya shigo da sallama, ya risuna a gaban Sultan ya kwashi gaisuwa, ya juya ya gaida Imam Zahradeen, amma ya yi shiru yana kallon Imam Hammad da kuma Nana.

Sultan ya ce "Ga mai maganin an kira shi, ya aka yi?"

Sarkin baka ya ce "Uwar gijiyata, meyafaru da Giyaz ne?"

"Ƙaisar ya ce mini faΙ—a suka yi." Ta mayar da idonta kan Sultan ta ce "Allah ya baka nasara, ya ci gaba da maganar a gaban Sarkin baka, shi ma amintacce ne, idan ya fita Giyaz zai iya aikata masa wani abin"


Sultan ya ce "Waye Giyaz Ι—in ne?"


Sarkin baka ya ce "Aljanin da aka yi masa asiri da shi ne ranka ya daΙ—e"


Imam Zahradeen ya fara magana ya ce "Tabbas na san ni mai laifi ne, kuma duk hukuncin da za a yanke mini zan karΙ“a"


Ya Ι—an yi shiru sannan ya ce "Mahaifiyata, Gimbiya Bilkisu, sun haΙ—a baki da Ι—an uwanta, mai girma Tafawa, suka yi masa sihiri, aka haΙ—a shi da aljanin da zai bar garin da shi gaba Ι—aya.

Wallahi ban san sun yi ba, sai daga baya take gaya mini, saboda su na son ko ni ko Asadullah wani ya gaji kujerar Hammad. Na nuna mata rashin jin daΙ—ina, ta ce mini aikin gama ya riga ya gama, muddin Hammad ya dawo Agadez sai ya haukace, ko ma ya rasa rayuwarsa. Shi ne na Ι“oye lamba, na nemi Mahmoudu, a lokacin bai riga ya bar Ζ™asar ba, abin dai ya fara taΙ“a shi ne. Yanzun ma ba ni da yadda zan yi ne, amma ban so na tona wa mahaifiyata asiri ba"

Hammad ya sunkuyar da kai hawaye na zuba daga idanunsa, Sultan ya rikice cikin tashin hankali da damuwa ya ce "Yanzu Zahradeen amma ka Ι“oye mini wannan abin baka gaya mini ba? Yanzu Ζ™iyayyar da mahaifiyarka take yi wa Hammad har ya kai ga ta nemi ta zauta mini Ι—a ya bar gida?"


Zahradeen yana kuka ya ce "Dan Allah ka yi haΖ™uri Abie, ban san komai a kai ba, sai daga baya. Kuma gudun kar idan ya dawo ya samu matsala, shiyasa na ce kar ya dawo Niger"


Nana ta ce "Gidan tarihi, a gidan tarihin Agadez aka yi masa sihirin, kuma ba sihiri Ι—aya ba ne, mutane daban-daban sun yi masa. Ranar da muka je cikin gidan tarihin tare da shi, na ji Ζ™amshin turaren Gimbiya Bilkisu a gurin. Sannan bayan Ζ™amshin turaren ta, na ji Ζ™amshin turaren wani ma.

Gaba Ι—aya suka Ι—aga kai, su na kallon Nana.

"Duk wanda yake Ζ™amshin nan, da alama yana ziyartar gurin, kuma wanda yake yi musu aikin sihirin a cikin gidan tarihin yake. Idan gidan tarihin nan babu kowa a cikin sa, to wannan mai gadin ne bokan da yake aikin, ko kuma ya san bokan da yake yi.


A rikice Sultan ya ce "Wane gidan tarihin wai, waye mai gadin?" Sai kuma ya rufe bakinsa, suka dubi Hammad a rikice, yadda ya runtse idanunsa yana zubar da hawaye.

Nana ta rikice ta tashi ta nufe shi, Sarkin baka ya ce "Kar ki taΙ“a shi, Giyaz ne yake zungurarsa, zai iya yi miki wani abin ya cutar da ke"

Ya tafi gaban Hammad, ya kama goshinsa ya din ga karanta Bismillah da suratul Fatiha, yana tofa masa a tsakiyar kansa.

Daga bisani ya Ι—aga rigarsa ya ciro jakar nan da ya bawa Nana, ya ce "Idan baka tafi ka Ζ™yale shi ba, zan illataka da jakar nan kamar yadda Ƙaisar ya yi maka"

Nana rikicewa ta yi, duk da ba yau ta saba ganin abin mamaki ba, jakar da take hannunta, ta neme ta ta rasa, ta ganta a gurin Ƙaisar, yanzu kuma ta koma hannun mai ita Sarkin baka.

Ya kalli Nana ya ce "A gurin Ζ™amshin turaren wa ki ke ji?"

Nana ta yi shiru tana satar kallon Sultan, tana kuma kallon Zahradeen.

"Kar ki ji tsoron kowa, gaya mini" Ta Ζ™i magana tana jinjina yadda za su Ι—auki abin.

Ya ce "Muje ki nuna mini gurin, ai babu abin da zai gagara da Ζ™arfin ikon Allah"

Sultan ya tashi a rikice jikinsa yana tsuma, idanunsa sun yi jawur saboda ya kaΙ—u da abubuwan da suka fito daga bakin Imam Zahradeen. Wani irin mugun tausayin Hammad ya mamaye masa zuciya.

Ya kalli su Nana ya ce "Yanzu can gidan tarihin za mu je kenan?"

N

Sarkin baka ya ce "Eh Allah ya baka yawan rai"

Imam Zahradeen ya ce "Ko a yi wa su Matawalle magana, a tafi da wani daga cikin su, ko hadimai"


"Bana buΖ™ata" Sultan ya faΙ—a fuskarsa babu annuri, ba tare da ya kalli inda Imam Zahradeen yake ba.


Ya dubi Hammad da ya buΙ—e idanunsa, sai dai baya magana, dan tun da ya zo wa Sultan ya ce masa Zahradeen ne, bai sake yin magana ba.

Ya shafa kansa ya ce "Hammad, ka na ji na?" Ya jinjina kai.

"Ko zaka bi mu ne?" Ya girgiza kai.

"Ka na nan mu je mu dawo?" Ya Ι—aga masa kai alamar eh.

Ya girgiza kai ya ce "Ina Mahmoudu ne, ban ganku tare da shi ba, a nemo shi ya zo ya zauna da shi tukuna sai mu tafi"

Imam Zahradeen ya tafi ciro wayarsa, ya hau laluben lambar Mahmoudu. Sultan da ya kalli Imam Zahradeen sai ya ji ransa ya Ι“aci, ya yi mamaki ya kaΙ—u matuΖ™a da jin abin da Gimbiya Bilkisu ta yi wa Hammad. Ga abubuwan da Tafawa ya din ga yi masa, da tursasa shi a kan yi masa abubuwan da yake so, da shi da 'yarsa amma hakan bai ishe su ba, suka nemi a Ι“atar masa da Ι—ansa.

Sai da Mahmoudu ya zo, Imam Zahradeen ya ce "Imam Hammad ba ya jin daΙ—i ne, ka zauna tare da shi, zamu je mu dawo"

Tiryan-tiryan suka bi ta Ι—akin da su Nana suke zaune, suka buΙ—e wannan Ζ™ofar kamar yadda Nana ta yi musu bayanin ta nan suka bi, suka gangara har gidan tarihin.

Mai gadin na ganin Sultan, jikinsa ya hau tsuma ya zube a Ζ™asa tamkar zai yi masa sujuda yana kwasar gaisuwa. Sai dai gaba Ι—aya ya rikice da ganin Sarkin baka.

Ko da suka shiga cikin gurin, kawai Sarkin baka ya bushe da dariya, duk suka tsaya suna kallonsa. Ya tsaya yana Ζ™are wa gurin kallo, yadda aka rarake dutse aka gina wannan gurin, mutanen zamanin da suka yi wannan aikin sun cancanci yabo.

Sarkin baka ya sake bushewa da dariya ya ce "Sarki a dawa Sarki a gida, Ni mai Duna ni mai Salamatu, ni mai Mairo 'yar Fulani. Ni ake yi wa inkiya biyu, Garba ga Baka ga Aska, na yi gadon gidanmu, na Ζ™waci wanda ban gada ba, na fi 'yan na gada iyawa. Ni Abubakar Garba mai taΖ™ama da ikon Allah. Na ga mutum na ga Aljan, na ga cuta na bada maganinta, idan babu na ce ba ruwan Garba. Ya buga Ζ™afarsa Ι—aya ya ce "Uwar gijiyata, Ζ™amshin turaren wa ki ka ce kina ji?"

Nana ta sake kallon su Sultan, Sarkin Baka ya ce "FaΙ—i kanki tsaye, ba wanda zai yi miki abin da Allah bai yi miki ba"

Ta Ι—an sunkuyar da kai ta ce "Akwai wani Imam Omar, wanda ya kawo wa Imam Hammad ayaba tare da Yayan Asal"

"Ƙamshin turarensa ne?" Imam Zahradeen ya tambaye ta cikin zaΖ™uwa.

Ta ce "Ni tsoron faΙ—a nake, ba na son haΙ—a husuma ne"


Sultan ya sassauta murya ya ce "Ki na ji na? Ba haΙ—a husuma ba ne ba, mijinki za ki taimaka tun da ke Allah ya yarje miki gano wasu abubuwan da mu ba mu gano ba"


Bakinta na rawa ta ce "Wannan mai kama shi Ι—in, da ku ke yawan zama ku uku, mai saka shuΙ—in rawani, bayan Ζ™amshin turaren Gimbiya Bilkisu, ranar da muka zo nan, Ζ™amshin turarensa ne yake tashi, alamar bai daΙ—e da tafiya ba"

A rikice Imam Zahradeen ya ce "Sardaunan Agadez, Ζ™amshin turarensa ne"

BuΙ—e baki Sultan ya yi, ya fara numfarfashi yana kallon Nana, ya ce "Me hakan yake nufi? Ina fatan ba dai wani abin ya yi ba?" Nana ta girgiza kai cikin tsoro ta ce "Ba ni da tabbas, tun da kowa yana da damae zuwa gurin nan, mussaman a cikin manyan Agadez kamar yadda Imam Hammad ya gaya mini. Amma me zai kawo shi nan cikin dare wajen Ζ™arfe sha biyu na dare. Kuma a mudubin Ƙaisar na ga wani abu da ya sanya ban ji na yarda da Ι—akin can ba, amma ba ni da tabbas tun da maganar aljani ba abar yadda ba ce ba wasu lokutan"

Sarkin baka kawai ya nufi Ζ™ofar Ι—akin, da Nana ta yi ta nacin a buΙ—e ta, yana zuwa ya jijjiga Ζ™ofar, amma ya ga Ζ™aton mukulli a jiki.

A nutse ya Ζ™are wa sauran Ζ™ofofin kallo, ya saki mukullin ya nufi hanyar fita, yana zuwa ya janyo mai gadin nan har zuwa inda su Sultan suke.

Ya kalle shi ido cikin ido Sarkin baka ya ce "Waye kai?"


"Mai gadin gidan tarihin Agadez" Ya ba shi amsa.


Sarkin baka ya ce "Kai, mugu shi ya san makwantar mugu. Kai da gani idanun nan nawa ka san babu abin da ban gani ba. Waye da waye suke zuwa gurin nan?"


Mai gadin ya yi wa Sarkin baka wani irin kallo, ya ce "Kowa ma yana iya zuwa"


"Ba kowan ba, muhimman mutanen da ka ke yi wa aiki"


"Ni ba ni da wani aiki bayan buΙ—ewa da rufewa, da kula da ababen tarihi"


"Ka tabattar?"


Ya ce "Eh"


Sarkin baka ya numfasa ya fito da jakar nan tasa, ya nuna wa mai gadin nan,ya ce "Idan hatsabibancinka ya kai ya kawo, na san ka san wannan jakar, ko kuma ka ji labarinta, mussaman da Jaddul Jinn ya yi rayuwa a cikin Masarautar nan. Wannan jaka ce da uwar gijiyar Ƙaisar ta farko, Lanti ta haΙ—a, da gudunmawar uban duΖ™usa, ta hanyar yin amfani da wani sashi na gashin Jaddul Jinn. Da abubuwa daban-daban da baΖ™aΖ™en aljanu ba sa so. Ana iya yi wa aljani tarko da ita, ko ma halaka su baki Ι—aya. Yanzu za ka yi mana bayani ne, ko kuma na gwada maka aikin jakar nan, na hallaka baΖ™in aljanin kanka, na haΙ—a ka faΙ—a da Giyaz, sannan na kashe ka?"

Ya din ga kallon Sarkin baka, yaΖ™i magana. Nana ta ji sanyi ya fara ratsata.

Mai gadin ya Ι—an ja da baya yana kallonta. Ta waiwaya ta ga me yake kallo, kawai ta ga Ƙaisar a gurin.

Jikinsa na rawa ya nufi Ζ™ofar Ι—akin, ya ciro wani mukulli ya buΙ—e, yana buΙ—ewa wani irin wari ya daki hancinsu suka ja da baya.

Jikin Nana ya hau tsuma, Shi kansa Sultan ja ya yi da baya cikin tsoro, yana kallon gurin.

Sarkin baka ya tankaΙ—a Ζ™eyar mai gadin nan, suka shiga Ι—akin. Ɗakin duhu kafin daga bisani kawai su ga haske ya gauraye Ι—akin.

Sarkin baka ya waiwaya ya cewa su Imam Zahradeen su shiga.

Suka bi wata doguwar hanya, su na shiga suka wari yana Ζ™ara cika musu hanci. 

Ɗakin tsohuwar kurkuku ce, da daga baya a ka mayar da ita gurin aikin zinaren da ake haΖ™owa. Wannan kurkukun da aka din ga azabtar da mutane a zamanin sarakunan baya.

Gurin gwanin ban tsoro babu kyawun gani ko kaΙ—an.

Nana ta kurma ihu ta ja ta tsaya jikinta yana tsuma, saboda razana da kuma firgicin abin da ta gani.

Ƙwarangwal ne na cikakken mutum, an soke shi a jikin mashi, an kuma soke wani abu mai kama da takarda a jikin Ζ™warangwal Ι—in, da hotonsa a jiki yana ci da wuta, sai kuma sunan Imam Hammad Jalaludeen, a jikin abin mai kama da takarda an soke allurai a jiki. Sak abin da ta gani a cikin mudubin Ƙaisar. Jikinta ya din ga wata irin karkarwa, saboda razani da tsoro.

Shi kansa Sultan daskarewa ya yi yana rarraba ido, saboda razani da tsoro.

Sarkin baka ya Ζ™arasa gaban ramin, ramin ba mai zurfi ba ne ba, sai dai wasu irin manya-manyan itace ne a cikin ramin nan. Ya kalli jikin Ζ™warangwal Ι—in nan, ya yi baΖ™iΖ™irin saboda azabar wuta.

"Ya ka yi wannan sihirin?" Sarkin baka ya yi maganar yana tsare shi da ido.

Ya yi shiru.

"Wallahi idan baka faΙ—a ba, sai na jefa ka a ramin nan na kunna wutar"

Ya tsaya ya kalli ramin, ya rufe idanunsa ya faΙ—i wasu abubuwa, ya kalli ramin a take wata irin wuta ta tashi a cikin ramin. Wata irin Ζ™ara ta din ga tashi a cikin Ι—akin. Nana ta toshe kunnenta, ta durΖ™ushe a kan gwiwoyinta, ta toshe kunnenta, ta fashe da wani irin kuka na tashin hankali da gigicewa.

Sarkin baka ya ce "waye ya saka ka wannan aikin, kuma yaya aka yi kana mai gadi ka ke bokanci?"

Ya numfasa ya ce "Na koyi bokanci ne, domin na rama abubuwan da aka yi wa zuriyarmu. Na bautar da mu tun zamanin kakanni.

Nana ta fara neman ta burkice musu gaba Ι—aya, saboda sama-sama da numfashinta ya din ga yi.

A rikice Sultan, ya ce Zahradeen ya fitar da Nana, kar wani abin ya same ta.

Su na fita ta nemi guri ta zauna ta sauke numfashi cikin matsanancin tsoro da razani.


*****

Mama ce a gaban Likita kamar ta yi kuka, ta yi Ζ™asa da murya sai magiya take yi masa.

Ya kalle ta ya ce "Hajiya muddin ba ki gaya mini gaskiyar abin da ya faru ba, babu wani abu da zan iya yi a kan 'yarki"

Cikin damuwa ta ce "Likita ka san Ι—an yau ne, ka haife shi amma ba ka haifi halinsa ba, abin kunya ta kwaso mini, na yi na yi da ita a zubar ta Ζ™i, shi ne aka gaya mini wata Ζ™waya na je na karΙ“o aka ce na saka mata guda goma a cikin kunu zai fita."

Ya yi zuru da ido yana kallonta, ya ce "Amma baiwar Allah ba ki da imani, kin san abin da ki ka aikata kuwa?"

"Dan Allah likita ka yi haΖ™uri,  ka taimake ni kamar yadda Allah ya taimake ka" Sai da ya yi mata faΙ—a kamar zai yi mata duka, sannan ya rubuta abin da za a yi wa Jamila.

Hajiya Sa'a kuwa, ta daina magana gaba Ι—aya, komai sai an yi mata. Ƙarshe Asibiti aka sallame ta, ta koma gida, gidan kuma babu mai jinyarta, abin duk ya damu Alhaji Fatuhu amma babu yadda ya iya.


*****


Nana har wani irin jiri take yi, jikinta yana tsuma saboda tsoro da razanin da ta shiga.

Sultan ya Ζ™i kallon inda Zahradeen yake, zai Ι—auki Muhsin ya tafi da shi, amma ya yi masa tsawa ya ce kar ya taΙ“a shi.


Gimbiya Bilkisu sam ba ta san me yake faruwa ba, da daddare ta shiryo ta zo sashen Sultan. Yana zaune a gefen gado ya yi shiru, ji yake yi tamkar kansa zai tarwatse.

Muhsin yana kan makeken gadon Sultan yana bacci, gani yake yi idan ya kawar da ido daga kan yaron, shi ma cutar da shi za a yi, wani irin matsanancin tausayin Hammd ya hana shi sukuni. Da ya rufe idanunsa ya tuna abin da ya gani, sai tsigar jikinsa ta tashi.

"Ranka ya daΙ—e, ko nan zan kawo maka abincin daren naka ne, barori sun shirya maka abinci tun Ι—azu fa" Bai yi magana ba, ta mayar da idonta kan Muhsin ta ce "Wannan kuma a ina ka samo shi?" Ta yi maganar tana nufar gadon.

Cikin tsawa ya ce "Kar ki kuskura ki taΙ“a shi" Ta razana ta ce "Sultan lafiya?"


"Fita ki bani guri"


Cikin rashin fahimta ta ce "Me yake faruwa ne?"


"Na ce ki fita ki bani guri, ba na ko Ζ™aunar ganinki, ki fita kafin na Ι—auki mummunan mataki a kanki" Babu shiri ta juya ta fice, ganin yadda jikinsa har rawa yake yi, saboda tsananin Ι“acin rai. Ta din ga mamakin mene ne ya tayar masa da hankali ne har haka, yake wannan fushin?.

*****

Nana kuwa tun da suka baro gidan tarihin, Sultan ya ce ta zauna a Ι—akin nan da suke, ta samu nutsuwa.

Da kyar ta samu ta iya yin salla.

Tana zaune ta yi shiru, ta ga an buΙ—e Ζ™ofar Ι—akin, Hammad ta gani ya shigo, ba ta yi zaton ganinsa ba ko kaΙ—an. Ta miΖ™e tsaye ya Ζ™araso fuskarsa ya zauna a kusa da ita, ya jingina da jikin gado. Sai kuma ya Ι—ago ya kwantar da kansa a jikinta.

Nana ta Ζ™ara janyo shi jikinta, ta Ζ™anΖ™ame shi tana fashewa da kuka, wani irin tausayinsa ya mamaye zuciyarta.

"Ya aka yi ne rayuwata, kukan me ki ke yi" Ya furta a hankali yana Ζ™ara shigewa jikinta.

"Sonka kawai nake yi" Ta yi maganar tana kuma Ζ™anΖ™ame shi.

"Wannan kukan, ya fi kama da na wanda ake tausayawa, meyafaru ki gaya mini"

"Ba komai Sayyid"

"To idan dai kina so na sosai, Ι—an bani sanyin mana" Yayi maganar yana Ι—an shafa jikinta yana murmushi.

Jin da gaske kukan take yi, ya sanya ya Ι—ago, shi ma idanunsa jawur, jikinsa babu Ζ™wari ya ce "Ki gaya mini, ko wani abin su Sultan suka ce miki?"

"A'a"

"Mene ne?"

"Dan Allah Sayyid duk abin da za a ce maka Asal ta yi, ka yi haΖ™uri ka yafe mata"

Ya yi murmushi mai ciwo, ya ce "Me Asal Ι—in ta yi?"

"Na san sai Sultan ya gaya maka, amma dan Allah ka yafe mata"

Hammad ya ce "Ki na tunanin ban san komai ba ne? Lokaci ya yi da yakamata na huta"

Nana ta ce "WataΖ™ila akwai abin da baka sani ba, dan Allah ko ka sani ka yi haΖ™uri ka yafe mata"

Ya yi shiru ya sake kwanciya a jikin Nana, ta Ζ™ara Ζ™anΖ™ame shi, cikin matsanancin tausayawa.


*****


Sultan na kashingiΙ—e, yana sauraren Tafawa, da sauran 'yan majalissa, sun kafe kai da fata a kan lallai a san matakin da za a Ι—auka a kan Hammad, saboda yadda ya karya musu Al'adar masarauta.

Sultan ya Ι—ago ya numfasa cikin Ζ™asaita, kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "Amm kamar yadda kowa ya sani, Agadez ta gaji Al'adu da Ζ™a'idoji daban-daban, wanda wasu an samar da su ne, tun zamanin jahiliyyah kafin zuwan addinin musulunci, ina ga lokaci ya yi da yakamata mu kama addininmu, mu yi watsi da duk al'adun da muke ganin su na kawo mana koma baya.

Saboda haka a matsayina na Sultan mai ci na wannan lokaci, na soke wannan Al'ada a Ζ™asar Agadez. BaΖ™aΖ™en buzaye za su samu 'yanci, farin buzu ko buzuwa na da cikakken 'yancin auren duk wata Ζ™abila ko kalar fatar da yake son aure. Matar da Imam Hammad ya aura, bincikenmu ya tabattar da halattaccen aure suka yi, kuma mun karΙ“e ta. Hakazalika za mu bayyanawa duniya Ι—an da ya haifa tare da matarsa ta Nigeria.


97

1k ne via 0069685771

Aisha Adam stanbic 

08081012143


Gaba Ι—aya 'yan majalisar suka waiwayo suna kallon Sultan.


Tafawa ya ce "Jalaludeen wannan wace irin maganar banza ce, dan me zamu bar gadon al'adun da muka gada daga iyaye da kakanninmu saboda son zuciyarka da Ζ™oΖ™arin bawa Ι—anka kariya? Babu wanda zai lalata mana dokokinmu da al'adunmu. Dole a hukunta Hammad dai-dai da abin da ya aikata"


"Mutanen farko ma, gadon iyaye da kakanni ne ya halakar da su. Daga lokacin da muka gaji al'adun, zuwa yanzu me al'adar ta haifar mana bayan tarin Ι“arna kashi-kashi? Kuma ina bayar da wannan umarni ne a matsayina na Sultan, shugaba a Agadez ba magana nake yi ba a matsayin Ι—an uwanku ko abokinku ba, duk wanda ya Ι—aga murya ko kawo abin da ba shikenan ba, zan hukunta shi dai-dai da abin da ya aikata"


Matawalle ya ce "Amma Allah ya baka yawan rai, yanke wannan hukuncin haka kai tsaye, baka tunanin zai sanya wa talakawanka wasi-wasi da kawo tashin tashina a tsakanin masarauta da kuma jama'ar gari"


Sultan ya numfasa ya ce "Lokuta da dama, gyara baya buΖ™atar lallai sai ka yi wa wani daidai, ko kuma sai kowa ya soka, ya yarda da kai mai gaskiya ne ko me kirki ne.

Haka zalika zan sauke wasu daga cikin Imam Imam na Ζ™asar nan, zan yi wa dokokin Agadez garambawul da gudunmuwar dokokin Ζ™asar Niger, domin kowane Ι—an Agadez ya samu cikakken 'yanci kamar sauran Ι—an Ζ™asa ba tare da al'ada ta tauye wasu daga cikin 'yancin da suke da shi ba a Ζ™asar nan.

Sai dai na san da yawa ba zai yi muku daΙ—i ba, za a ga kamar na yi rashin adalci saboda Hammad Ι—ana ne, amma kafin ku ce haka, bari mu yi komai a buΙ—e tare da ku". Ya kalli wani dogarinsa, ya ce "Ina da baΖ™o a mararrabar fada da hanyar cikin gida, ka ce ya iso"

Duk suka yi tsuru-tsuru su na jira.

Ba a jima ba, dogarin ya dawo tare da Sarkin baka sai kuma wannan mai gadi a Ι—aΙ—Ι—aure da igiya tamau kamar Ι“arawo.

Wanda ba su san me ake ciki ba, suka yi Ζ™uri su na jiran jin ba'asi, wanda abin ya shafa kuma cikinsu ya Ι—uri ruwa.

Sarkin baka ya risuna ya yi gaisuwa a fada, cikin shigarsa ta hargi ya shigo hakan ya Ζ™ara sanyawa duk aka zuba masa ido.


Sultan ya kalli Sarkin baka ya ce "Yi musu bayani"


Sarkin baka ya kalle shi ya ce "Duk da na san, sun sanka amma ka yi musu bayanin waye kai"


Ya sunkuyar da kai ya ce "Mai gadin gidan tarihin Agadez"


Sarkin baka ya ce "Kuma me?"


"Boka da nake yi wa wasu daga cikin manyan Agadez aiki"


"Mene ne dalilinka na yin hakan?"


Ya numfasa ya saci kallon Sultan ya ce "Na haka ne, saboda huce takaicin yadda ake bautar da mu tun daga kan kakana, wannan dalilin ya sanya lokacin boka Riyan, na koyi harkar bokanci a gurinsa"


Sultan ya ce "Ina fatan kun ga Ι—aya daga cikin illolin wannan al'adun da muke yi, marasa tsuhe balle makama? Mu na jinka ci gaba"


Sarkin baka ya ce "Ba ka ji ka ci gaba mana"


"An bani wasu ayyuka, duk da ba kowa ya san ina bokanci ba, sai dai akwai wani babba a masarautar nan da shi ya Ζ™arfafe ni na koyi harkar bokanci.

Ni aka saka na yi wa Imam Hammad Asiri, da aljanin da ya sanya ya bar Ζ™asar nan, ya manta komai da ya shafe shi, ciki hadda tuna waye shi.

Sannan aka bani aikin yi masa asiri da wani tsohon aljani a cikin gidan tarihin, da yake sanya masa wannan zafin jikin da yake gigita shi".

Sarkin baka ya sake cewa "Yaya ka ke yi?"


"Da fari na haΖ™a rami a cikin tsohuwar kurkuku, ana kawo mini itace cikin dare, ina tona tsofaffin kabarurruka na cikin gidan, na Ι—auki Ζ™warangwal Ι—in, na saka shi a cikin wuta, da hatimai daban-daban da sunan Imam Hammad, duk lokacin da na babbaka wannan wutar yadda Ζ™warangwal Ι—in nan yake Ζ™onewa haka yake jin zafin a jikinsa. Idan Ζ™warangwal Ι—in ya murmushe saboda zafin wuta, sai na kuma tono wani. Daga baya kuma aka koma kawo mini sababbin gawarwaki na koma yin aikin da su, idan na saka musu wutar nan, haka yake jin wannan zafin a jikinsa"

Gurin ya yi tsit, aka rasa wanda zai yi magana. Jikin Matawalle yana rawa ya ce "Innalillahi wa Innalillahi raji'un, amma suwaye haka?"

Sultan ya ce "Ba sai an faΙ—e su ba, amma sun san kansu, kuma duk wanda yake da ja a kan maganar, yana iya zuwa gidan tarihin da kansa ya tabattar. Dan haka a yau na kawo Ζ™arshen zaman yau, dan haka zan zo da sauran bayani da abubuwan da zamu caccanza".

Nan aka ci gaba da salallami, aka rasa mai sake cewa komai.


Nana tana kwance tare da Hammad, kamar zai shige cikinta, sai shafa gashin sa take yi sannu a hankali.

Ta yi shiru tana tunanin abin da ya faru.

Yadda bokan nan ya din ga yi musu bayanin, Imam Omar da mahaifinsa Sardauna, suke zuwa da yadda suka yi masa asirin nan na zafin jiki. Kuma da sanin Tafawa, kowa fafutukarsa Ι—ansa ya samu mulki. Haka zalika Asal ta yi soyayya da Omar, ita take ajiye wa Hammad takardun nan. Ko da auren Hammad sun yi soyayya tare, kafin daga bisani da ta ga babu amfani soyayyar tasu, ta fara son Hammad ta daina biye masa.

Sai dai ya ci gaba da yi mata barazanar sai ya tona mata asiri, irin hirarrakin da suke yi. Sai dai babu wani abu na saΙ“on Allah da ya taΙ“a shiga tsakaninsu, sai dai duk wasu zantuttuka na banza har da wanda bai kamata ba, suna yi. Babu abin da bai sani ba a game da aurenta, da abubuwan da yake faruwa tsakaninta da Hammad ba.

Hatta sirrin shimfiΙ—ar aurensu, babu abin da Omar bai sani ba. Shi ya din ga ziga ta, tun daga lokacin da aka ce za a yi aurenta da Hammad, shi ya din ga ziga ta har bayan auren.

Ya ci gaba da zuwa gurin bokan nan, yana karΙ“ar wannan takardar, yana bawa Asal, wanda da ya yi tozali da takardar yake sake ruΙ—ewa, jikinsa ya rikice ya yi ta jin ihun da alajanin nan yake yi a jikin Ζ™warangwal Ι—in nan, duk ya fita hayyacinsa.

Babu yadda Omar bai yi da Bokan nan, ya yi masa abin da Asal za ta yarda shi, amma ya ce ba zai yi wannan cin amanar ba saboda Hammad yana yi masa alheri ta wasu Ι“angarorin. Gaba Ι—aya bokan ya gaya musu labarin, da abin da yake tsakanin Omar da Asal a baya. 

Babban abin da ya Ι—aga wa Nana hankali, bai wuce yadda bokan ya ce, ko za su kashe shi, zai iya lalata sihirin da ya yi da aljanin jikin Ζ™warangwal Ι—in da yake amfani da shi, amma ba zai iya raba Hammad da Giyaz ba, saboda Giyaz baya saΙ“a alΖ™awari, kuma ga Nana tana tare da Hammad, yana ganin Ι—ansa a jikinta, idan ba kashe Giyaz za a yi har lahira ba, ba zai rabu da shi ba.

Da ta zo nan a tunaninta, ta lumshe idanunta hawaye na zirarowa a hankali.

Hammad ya yinΖ™ura ya tashi zaune, ta maze ta goge hawayenta. Ya Ζ™are mata kallo ya yi wani irin tattausan murmushi, ya shafa gashin kansa ya ce "Ba Ζ™aramin kyau ki ka yi mini ba ma vie, ina kewa, Ι—an yi mini waΖ™ar mana abar Ζ™auna" Yayi maganar yana sumbatar hannunta, tare da matsawa kusa da ita.

Ta Ι—an matsa kaΙ—an ta ce "Ana ta kai ka na ta kaya"


"To ni kayan ne suka fi damuna, fiye da kayan ai. Ki kwantar da hankalinki babu abin da zan yi miki, kuma ina roΖ™on Allah kar ya kama ki da laifin guduna da ki ke yi, saboda kin fi ni gaskiya ta kowace fuska.

Amma har abada ni mai Ζ™aunar ki ne, kuma ba zan taΙ“a yarda a raba ni da rayuwata ba in sha Allah" Ya yi maganar yana sake rungume ta, wani abu mai sanya nutsuwa na fizagarsa game da ita.

"Ka daina yi mini wannan kallon mana" Ta yi maganar tana hararasa cikin wasa.

"Idan ban kalle ki ba wa zam kalla, kina nan a yadda ki ke ma vie, kamar baki haifi Muhsin ba"

Ta Ι—an Ι“ata fuska ta ce "Da na canza daina sona za ka yi kenan?"

Yayi murmushi ya ce "Haryanzu ba ki san waye Hammad ba, ke Ι—in nake so ne Asmy, babu abin da zai canza a tattare da ke, na ji na daina sonki ko kaΙ—an. Ina son Husna"

"Sake faΙ—a" Ta yi maganar tana tsare shi da ido.

"Sai kin yi mini waΖ™a tukuna" Ta yi dariya tana jan hancinsa ta ce "Sai ka biya ni tukuna."


Ya Ι—an yi shiru ya ce "Ina tuna mutane daban-daban da muka rayu da su a Nigeria, ko ina yayarki Ι—in nan, da ta yi ta Ι—awainiya da mu? Da 'yan gidanku, da mutumin nan da na tsana, wanda na yi wa gadi da farko. Sai kuma mutanen gidan da muka zauna, da muka yi aure"


Nana ta ce "Gidansu budurwarka ko?"


Ya ce "Eh nan"


"To tashi daga jikina"


Hammad ya ce "Ba zan tashi ba, ai ni ban ce budurwata ba, ke ki ka fara."


Ta yi murmushi ta ce "Babu abin da ba zai wuce ba sai ikon Allah, ni dai ina ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke a kanmu"

Ya ce "Alkhairi in sha Allah, ni nama manta, yana nemanmu anjima, ban san me zai ce mana ba. Amma ina tsammanin alkhairi daga bakinsa"

"Allah yasa ina fatan hakan nima, amma dan Allah ka sanya baki, na ga ya yi fushi sosai da sosai da Ι—an uwanka, ko zaka saka baki?"

"Ba ruwana" Ya bata amsa kai tsaye.

Nana ta ce "Kar ka ce haka" Ya miΖ™e tsaye gaba Ι—aya, sannan ya ce mata "Zan je na dawo, ki yi mana addu'a Allah ya sanya hukuncin da Sultan zai yanke, ya yi mana daΙ—i" 

Ya Ζ™arasa maganar yana sumbatar goshinta.


Kamar zata tashi sama, haka Gimbiya Bilkisu ta faΙ—o turakar Sultan hankalinta a tashe, ko haΙ—iyar yawu ta kasa, saboda bushewar da bakinta yayi.

A nutse ya juyo ya kalle ta, bayan ya gama warware rawanin kansa.

Sai kuma ta tsaya ta kasa magana.

Can kuma ta ce "Sultan, wai da gaske zaka sauke wasu daga cikin Imam? Meyasa? Kuma ina fatan babu Zahradeen a ciki?"


"Idan da shi me za ki yi?"


"Amma dai ka san bai kamata abin da ka yi, kuma a kan me zaka sauke Zahradeen yana Ι—an cikinka? A wancan karon ka naΙ—a Ζ™aninsa a matsayin shugabansa, sannan ka zo ka sauke shi ai muzantawar tayi yawa. Zai ma zama abin surutu a Agadez"


Cikin nutsuwarsa ya kalle ta ya ce "To shi ne me? Ai gara abin kunyar sauke shi daga Sultan, a kan tona muku asiri da ke da shi da Ι—an uwanki Tafawa" Ya Ζ™arasa maganar cikin hasala. Sak ta yi tana Ζ™walalo ido waje tana kallonsa.

"Kar ki kalle ni kamar ba ki san abin da ki ka aikata ba, Bilkisu kin cutar da ni, kuma kin cutar da kanki. Kin yi yinΖ™urin kashe mini mata sau biyu, saboda gudun tonuwar asirinku, yayanki ya yi uwa ya yi makarΙ“iya ya sanya muka rufe Mamman, waya sani ko a Ζ™arshe ma ke dai ki ka yi sanadin rayuwar tata? Sannan tilon Ι—an da ta bari a duniya ki ka sako a gaba da jaraba, ke kina yi yayanki yana yi, gaba Ι—aya Hammad bai ji daΙ—in rayuwarsa ba, saboda azaba da masifar sihiri da makircinki. Kuma idan ki ka kuskura ki ka buΙ—e baki ki ka musa mini, sai na tona miki asiri sannan ki bar mini gida. Allah ne ya tona muku asiri a silar matarsa ta Nigeria da ya aura, kuma bokan naku yana hannunmu, ya tabattar da abin da ya aikata.

Abu Ι—aya zan duba na rabu da ke, 'ya'yan da na haifa tare da ke. Amma daga yau na haramtawa kaina ke har abada a matsayin matata, za ki yi zaman 'ya'yanki ne kawai. Kuma kar Zahradeen ya Ζ™ara ayyana ni a matsayin mahaifinsa, kuma kar ya sake zuwa inda nake. Da ke da duk wanda ku ka aikata hakan, na bar ku da Allah. FaΙ—ar abin da ku ka aikata tamkar tona wa zuriyarmu asiri ne"


A rikice ta ce "Dan Allah Jalaludeen ka tsaya ka ji...


"Ba zan ji komai ba, fice ki bani guri kafin na canza shawara" Yayi maganar yana yi mata wata irin gigitacciyar tsawa, babu shiri ta fice tana haΙ—a hanya.

Tafawa ne ya shigo falon hankali a tashe, ya tarar da Asal tare da Asadullah.

A fusace ya ce "Gidan uban wa ku ka tafi tun safe?"

Da mamaki Asad ya ce "Kai ka kira ni a waya ai, ka ce na zo na kai Asal Asibiti, tun lokacin muna Asibiti, ba ta da lafiya sosai.

Ya sharce gumin goshinsa ya ce "To, dara ta ci gida yau, Asirinmu ya tonu a fada" Gaba Ι—aya suka Ι—aga kai suka kalle shi.


"Eh, yau da bokan da yake yi mana aiki, na gidan tarihi aka zo fada, ya tona komai sunayenmu ne kawai bai kama ba. Kuma na san ya gaya wa Sultan komai, kuma duk a dalilin haukanki da dabbancinki Asal, haka kurum ki ka je ki ka jajubo masifa ki ka kawo ta har cikin gidan sarauta. Binciken da na yi, wannan yarinyar da ki ka kawo a matsayin kuku, ita ce Ι—in dai ta yi sanadin tona asirinmu. Dan haka sai ku shirya baki Ι—ayanku, dan ban san wane irin hukunci za a Ι—auka a kanmu ba.


Asal ta Ι—ora hannu a ka ta ce "Wayyo Allah na shiga uku, Abbu sai da na ce muku mu daina wannan abin, amma kai ka saka ni, Imam Asad ya saka ni, Imam Omar ma ya saka ni da Sardauna, ku ka saka ni a tsakiya wallahi ina son Hammad, idan na rabu da shi ba zan taΙ“a samun miji kamarsa ba, wallahi ina sonsa"


A fusace Asadullah ya ce "Ke rufe wa mutane baki, ke ta wani shashasha ma ki ke yi?"


"Kai ne shashasha, dan duk saboda gobenka aka lalata tawa, an cuce ni, komai zan yi yanzu Hammad ba zai taΙ“a yafe mini ba, balle ya saurare ni"


Tafawa ya dubi Asal ya ce "Asal kina da hankali kuwa? Kin san abin da ki ke faΙ—a kuwa?"


"Abbu na san abin da nake faΙ—a, shikenan bani da makoma, matarsa ta shiga kundin tarihin baΖ™ar mace ta farko da ta auri Imam a Agadez, ni kuma zan shiga kundin tarihin matar da ta sanya hannun gurin tarwatsa rayuwar mijinta"  MiΖ™ewa tayi Tafawa yana kiranta, amma ko waiwayowa ba ta yi ba, ta fice daga Ι—akin.


****

Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama a falonsa, ga mamaki ya ga Fadila tare da uwargidansa Hajiya Suwaiba, suna zaune abin da bai taΙ“a gani ba.

Suna ganin shi suka zuba masa ido, Hajiya Suwaiba ta ce "Ka ce sai gobe in Allah ya kaimi zaka dawo?"


Ya ce "Eh, fasawa na yi na taho yau"


Fadila ta ce "Amma Daddy lafiya dai ko, Rauda kawo masa ruwan sanyi" 


Suwaiba ta ce "Wai dan Allah Baban Rauda Meyafaru a Lagos Ι—in ne?"


Ya ce "Sai kun gaya mini, me ku ke tattaunawa ne, ganinku tare ya sanya ni farinciki"


Hajiya Suwaiba ta ce "Abokin nan naka ne ya zo gidan nan, wanda ya sai gidan nan, shi ne muke tattaunawa mu tattara Ι—an abin da ya yi saura, a nemo gida mu tashi, tun da mun ga alamar mutumin nan zai iya ci mana mutunci daga mu har kai."


Ya yi murmushi tare da jinjina kai. Cikin damuwa Fadila ta ce "Dan Allah Daddy ka gaya mana, meyafaru muna fatan dai ba wani abin ne ya kuma kunno kai ba"


Ya saki murmushi ya ce "Da baku ganni a haka ba, Alhamdillah an canza sabon controller na hukumar Coustom na Ζ™asa. An sakar mini kwantena Arba'i  da bakwai a cikin kwantenonina, da na mutane da na haΙ—a na yo order kaya" A rikice suka buΙ—e ido, suna jin abin kamar a mafarki. Hajiya Suwaiba baki na rawa ta ce "Daddy, kenan suna sane suka kama ka kayan naka, ba wani laifin ka yi ba, yanzu kana nufin an saki kayan?"

Ya jinjina kai ya ce "An saki wasu daga cikin kayan, Allah ya karΙ“i addu'a" Gaba Ι—aya suka rungume shi tare da yaransa, yana kuka su na kuka, babu abin da bakunansu ke furtawa sai tsantsar yabo da godiya ga Ubangiji Subhanahu wata'ala mai zaΙ“ar wa kowane bawa abin da ya dace da rayuwarsa.


Baban su Nana ji yayi tamkar ya Ι—ora hannu a ka ya zunduma ihu, bayan da likita ya sanar masa abin da yake damun Jamila.

Duk da Mama ta roΖ™e si a kan su rufa musu asiri, amma ganin yadda Baban yake ta sintiri hankalinsa a tashe, an rasa takamaiman dalilin da ya sanya ake ta Ζ™ara wa Jamila jini. Ya sanya ya yi wa Baba bayanin, cikin jikinta da ya zube ne, bai fita gaba Ι—aya ba, ga jini ta zubar mai yawan gaske.

A tsorace Baba ya kalli Mama ya ce "Rabi, wane cikin? A ina Jamila ta samu ciki?" Ta tsuru-tsuru tana jin kamar ta kama Likitan ta yi ta gwara kansa a gurin.

"Rabi, dama abin da yake faruwa kenan ki ka Ι“oye mini? Jamila da ciki? Kin cuce ni ba ki yi mini adalci ba, kuma ki ka Ι“oye mini baki gaya mini ba ki ka nemi kashe ta da Ζ™wayoyi. Shikenan kanki ki ka yi wa, na fara zargin alhakin Nana ne duk yake bibiyarmu. Nana duk matsi da wahalar da ta sha a rayuwarta bata Ι—aukko mini magana ba, ki ka yi mata sharri ki ka saka na amince na aura mata mutumin da ban san waye shi ba, an wayi gari shekara uku, babu ita babu Ι—an uwanta, ke kuma naki 'ya'yan babu na mora daga mahaukaciya mai fama da aljanu sai lalattaciya. Abubuwan da ki ke yi wa Nana sharri da kuma yi mata gori a kai, duk sun kama ki a kan yarnki. Amma kanki ki ka yi wa Allah ya yi muku magani" Har ya gama maganar ya fita, ba ta sake iya cewa Uffan ba sai gursheΖ™en kuka da take yi. Jamila ma da ke kwance sai kukan da take faman yi.


*****


Kasancewar Alhaji Fatuhu yana Ι—akin Fadila ne, ta din ga gargaΙ—insa a kan ya ja bakinsa ya yi shiru, kar yayi saurin gaya wa jama'a cewar an sakar masa kayansa.

Ya ce "Haba masoyiyya, duk yawan jama'ar da suka taru suka jajanta mana, tsawon wannan lokacin, kusan shekara huΙ—u, kuma sai waraka ta zo mu yi shiru?"

Fadila ta ce "Sa gani a hankali, baki yana yi wa abu illa, ka san waΙ—anda zaka janyo jikinka tukuna, ka lallaΙ“a ka ga abin da Allah zai yi sannu a hankali ka fara settling komai, amma dan Allah kar ka yi saurin gaya wa jama'a"

Ya ce "To shikenan na ji, zan Ι—an fita yanzu amma, sannan goben in Allah ya kaimu, gaskiya ki shirya mu je, zamu duba Yaya Sa'a, zan kuma mayar da ita Asibiti in sha Allah"


Ta so musa masa zuwan, amma ta ga bai kamata ba, kawai ta haΖ™ura ta shanyeta amsa masa da to.


A gida Alhaji Fatuhu ya tarar da Alhaji Zailani, ya tarar da shi ya yi wata irin muguwar rama, bai matuΖ™ar ban tsoro.

Ya ce "Alhaji Zailani, lafiya kuwa me yake damunka haka? Ko duk tashin hankalin Ι“atan Shukura ne?"


Alhaji Zailani ya yi murmushi ya ce "Ba dole hankalina ya tashi ba, 'ya ta Ι“ace babu ita babu labarinta ba, gefe guda ga ciwon suga ya sako ni a gaba, yanzu an hana ni cin komai sai ganye, kusan ko ruwa na sha sai ya yi sama. Na rasa ma abin da yake yi mini daΙ—i"

Cikin damuwa Alhaji Fatuhu ya ce "Haba kai kuwa, duk lokacin da muka yi waya ce mini ka ke yi kana nan lafiya, ayyuka sun yi maka yawa shiyasa na ce ni bari na zo da kaina, ko zan samu kana gida. Ni nawa jikin Alhamdillah ya yi kyau kai kuma babu lafiya haka. Ka kwantar da hankalinka in sha Allah zaka samu lafiya. Kuma za a ga Shukura da yardar Allah. Amma kai ma ka jarraba na gargajiya ko za a dace, ni na ga alfanun ire-iren magungunan nan wallahi"

Alhaji Zailani ya ce "To shikenan, zan gwada da yardar Allah" A baΙ—ini kuwa, Aljanin da yake bawa jini ne, ya fara burkita shi yake shan nasa jinin, saboda rashin bashi abin da ya nema a wannan shekarar. Ga shi ya yi ta mummunan mafarki da Shukura tana caka masa wuΖ™a tana kuka.

Ga shi ya yi ta mafarkin Ζ™warangwal Ι—in jariri yana sha masa jini, ko yana fizgo kayan cikinsa yana ci. Idan ya tashi sai ya ji jikinsa kamar babu laka, ko hannunsa da kyar yake iya Ι—agawa. Da yaje Asibiti aka ce ciwon sugar ne, yanzu ya hau in anjima ya yi Ζ™asa ko a ganshi normal.

Ga shi ya fara surutai idan yana baccinn har Hajiya Amina ta fara tuhumar sa, da yi masa tambayoyi.


****


Hammad na gaba, Nana na biye da shi, suka shiga turakar Sultan, karon farko Nana ta gan shi cikin riga da wando na shadda, babu rawani babu takunkumin yana shan shayi, Muhsin na kusa da shi, ya Ι—ora Ζ™afa Ι—aya kan Ι—aya da nasa kofin shi ma yana sha. Ba zaka taΙ“a cewa Sultan ya haifi su Hammad ba, kamar yayansu ba mahaifinsu ba.

Muhsin yana kallon su Nana ya hau murmushi, amma bai tashi daga kusa da Sultan ba.

Sultan ya kalli Muhsin ya ce "Suwaye waΙ—ancan? Ka san su?" Kawai ya ci gaba da murmushi yana shan shayinsa. Ita Nana a zatonta, Imam Zahradeen ne ya kuma tafiya da shi gidansa.


Ta duΖ™a ta gaida Sultan, ya saki jiki sosai ya amsa mata, Hammad ma ya gaishe shi, shi ma ya amsa masa yana bin su da kallo, wata nustuwa da farin ciki na ratsa shi. Ya din da gode wa Allah, da bak biye wa su Sardauna ya kori Nana ba.

"Ina fatan duk kuna cikin Ζ™oshin lafiya?"


Hammad ya ce "Alhamdillah"


"Ma sha Allah, Nana Asma'u" Nana ta Ι—ago da mamaki jin ya kira sunanta cikke. Ta ce "Na'am Abie"

"Da farko ina mai baki haΖ™uri bisa ga abubuwa da suka faru, kar ki yi zaton ko dan muna sanya ran Hammd ya samu lafiya saboda ke ne, ya sanya na saukko. Ko kaΙ—an dama mun yi magana sosai da sosai da Mahmoudu ina ta tunanin yadda zan Ι“ullowa lamarin, ba tare da 'yan majalissata sun ga na nuna son kai ba, sai dai cikin ikon Allah a dalilinki, na fuskanci ingiza mai kantu ruwa suke yi mini. Kuma na koyo darussa daban-daban a dalilin faruwar wannan al'amura tabbas; idan bamu karΙ“i abin da ya faru a matsayin aya ba, to gaba Allah na iya jarabtarmu ta wani abin da ba zamu iya sa shi ba, a kan muguwar Al'adar da babu abin da ta haifar sai kawo mana koma baya.

Yanzu dai ina baki haΖ™uri da abin da ya faru, wanda aka yi miki da gayya da wanda muka yi miki cikin kuskure. A duniya ko a gurina da na haifi Hammad bai samu nutsuwa da kwanciyar hankalin da ya samu a gurinki ba. Ga mu da kuΙ—i da wadata, amma Hammad bai tashi cikin kwanciyar hankali ba. Ko dan albarkacin wannan abokin nawa, dole na tabattar da kun ci gaba da rayuwa tare" Ya yi maganar yana shafa gashin Muhsin.

Ya ce "Dan haka in sha Allah, muddin ina raye, babu wani abu da zai kawo muku cikas a rayuwar aurenku, Ubangiji Allah ya sanya muku albarka. Na ji duk tarihinki, har Nigeria na aika duk an yi mini binciken da yakamata, kuma na gamsu da abubuwan da na ji game da ke, da kuma rayuwar da ki ka yi da Hammad. Ina goyon bayan ku rayu tare, Hammad ba zai taΙ“a samun mace kamar ki ba Asma'u"

Kawai Nana ta fara zirarar da hawayan farinciki. Hammad ya rikice gaba Ι—aya ya ce "Abie, yanzu ka yarda na ci gaba da rayuwa da Nana? A matsayin matata duk da yadda al'adarmu ta hana?"


Sultan ya yi murmushi ya ce "Na ma soke wannan dokar, daga yau babu ita a Agadez"

Hammad ya tashi ya tafi gaban Sultan ya risuna, amma ya rasa abin da zai ce masa. Sultan ya rungume shi yana murmushi. Ya numfasa ya ce "Hammad, ban san iya adadin abin da ya rage maka na rayuwa ba, amma na baka damar ka yi duk abin da ka ke so wanda bai saΙ“a wa mahaliccinka ba, da zai sanya ka farinciki.

Sannan ka sakar wa Tafawa 'yarsa, dan babu amfani ci gaba da zama da mutumin da yake Ζ™oΖ™arin ganin bayanka, yake cutar da kai tsawon lokaci. Ka yi haΖ™uri kuma ka yi biyayya, Ubangiji Allah ya baka ladan haΖ™uri da kuma biyayyar da ka yi. Sannan ina roΖ™on Allah ya baka lafiya ya kuma warware miyagun abubuwan da suka aikata maka."Ɗan uwanka kuma wannan ganin damarka ce ka ci gaba da mu'amala da shi, amma ni na yafe shi a matsayin Ι—a na, na girgiza matuΖ™a da jin abin da suka aikata" Nana zata yi magana Hammad ya girgiza mata kai alamar ta yi shiru.

"Ke ma in sha Allah, zamu tura wakilai, zamu je mu ba wa iyayenki haΖ™uri, kuma kamar yadda mahaifiyar Mahmoudu ta nema, kuma mun amince za mu yi hakan. Duk wata Ι—awainiyar aure da ake yi wa mace, da za a aura a Agadez za mu yi miki ita, kuma zamu biki sosai kowa ya san da zamanki"


Nana ta risuna ta ce "Na gode sosai da sosai Abie, Ubangiji Allah ya Ζ™ara girma da sutura, ya kare ku daga dukkanin abin Ζ™i. Amma ni hukuncin da ka yanke mini bisa adalci da tausayi, da bani damar na rayu da Muhsin da mahaifinsa ya fi komai yi mini daΙ—i, ina ga ba sai an yi bikin nan ba, har dukiyar auren ma na yafe"


Sultan ya yi murmushi ya ce "Ba biyanki abin da ki ka yi mana zamu yi ba, kyautatawa ce daga gare mu, dan Ζ™ara nuna martaba da daraja da duk wani Ι—an Adam yake da shi, fari ko baΖ™i koma wani kalar launin fata ne. Ina Ζ™ara amfani da wannan damar, gurin Ζ™ara nuna Ι—imbin godiyata a gare ki. Kin sadaukar kin jajirce, mun san bamu da abin biyan ki, amma ina kyautata miki zato da yi miki fatan alkhairi"

Nana ta sunkuyar tana murmushi ta kasa magana ma.

"Na Ι—auki darussa daban-daban, a kan abubuwan da suka faru, komai sila ne, kuma wasu lokutan bawa baya samun Ι—aukaka ko cimma nasara, sai an jarraba shi, wasu lokutan mai sauΖ™i, wasu lokutan kuma mai tsanani. Allah dai ya baku zaman lafiya na har abada. Shi kuma mai magani Sarkin baka ko? Ya ce yana nan tare da shi za a je Nigeria. Ɗan uwanki ma an ce mini yana Agadez yanzu haka, da Zahradeen ya kai shi karatu, zan saka a kawo mini shi nan, shi ma na yi masa godiya na ba shi haΖ™uri shi ma"

Nana ta ce "Dan Allah Abie, ka duba girman abin da Imam Zahradeen ya yi, fiye da laifinsa ka yafe masa. "


Yayi murmushi kawai ya ce "Za a duba"


Hammad ma ya ci gaba da yi wa Sultan godiya, dan bai taΙ“a tsammanin zai yanke wannan hukuncin ba. Sultan ya ce Nana zata iya tafiya, bayan tafiyarta Hammad ya sake yi wa Sultan godiya sannan ya ce "Amma Abie hukuncin nan da ka yanke, ba zai janyo surutu da 'yan majalisar ka ba?"


Sultan ya ce "Hammad, zan yi duk abin da nake ganin shi ne dai-dai, har abada na daina jiran wani ya sarrafa ni, duk abin da nake ganin shi ne daidai zan zartar da shi."


Hammad ya jinjina kai yana sake gode wa Allah. Ya sake cewa "Amma Sultan meyasa ka ce na saki Asal?"


"Me za ka yi da ita? Ko ba ka ji abin da Ι—an uwanka ya faΙ—a sun haΙ—a kai da ubanta da Bilki suna neman ganin bayanka ba?"


Hammad ya jinjina kai ya ce "Haka ne"


"Amma idan kana son matarka, shikenan ba zan yi maka dole ba"


Hammad ya ce "Ba na son aikata abin da za kalle ni a matsayin mara adalci, amma kamar ku ne Ι“oye mini wani abu da kai da Maman Muhsin"


Sultan ya sake yin murmushi ya ce "To idan ma mun Ι“oye maka ai ba laifi muka yi ba, tashi ka yi tafiyarka"


*****


Alhaji Fatuhu yaje dubiyar Doctor Sharif tare da Fadila da Suwaiba, sai dai ya tsorata da yanayin da ya gan shi a ciki, tun da ya ga Alhaji Fatuhu yake kuka, amma ya kasa magana, sai da kyar kamar an fizgo maganar ya ce "Ka yi hankali da Alhaji Zailani, kuma ka yafe mini dan Allah" Hakan ma ba komai ake ganewa ba, sai dai maganar ma bata fita da kyau, da kyar suka gane me yake cewa.

Daga bisani suka tafi gidan Hajiya Sa'a, tana kwace a cikin najasa, Alhaji Fatuhu ya din ga yi wa masu aikinta faΙ—a, yana iΖ™irarin tun da komai ya fara daidaita, gidansa zai mayar da ita. Sai dai haka kurum Ζ™asan zuciyarsa ya din ga mamakin wani irin nau'in ciwo ne ake ta fama da shi haka.


Maganar da Muhsin ya yi, yana Ζ™oΖ™arin karΙ“ar wayar mamansa, ya sanya Hajiya Sa'a waiwayo wa da sauri ta kalli yaron.


Ayshercool 

08081012143


98

1K NE VIA 0069685771

AISHA ADAM STANBIC BANK 

08081012143



Cikin mamaki Alhaji Fatuhu yake kallon Hajiya Sa'a, saboda yadda ta Ζ™ure Muhsin da ido.


Ya ce "Yaya Sa'a, kin gane ni? Ko Muhsin ki ka gane?"


"Ba dole na gane wannan tsinannen yaron da Allah ya tsine wa albarka ba? In sha Allah sai ya mutu kuma kun rasa. Da shi ne ya mutu da Abbana bai mutu ba, Ι—an nawa guda Ι—aya na rasa shi, ku ga naku nan yana rayuwa "

Cikin rashin fahimta Alhaji Fatuhu ya ce "Yaya Sa'a kin san kuwa me ki ke cewa?"

Cikin tsawa ta ce "Na sani mana, na sani, ina sane. Yanzu ga Abba ya mutu a banza, ni kuma dodon Ζ™ungiya ya shanye mini wasu sassan jikina."

Gaba Ι—aya ya yi iya Ζ™oΖ™arinsa gurin ganin maganganun da take yi, ba su yi tasiri a zuciyarsa ba. Ya dubi Fadila da ta takure a gefe, tana zare ido ya ce "Fadila, kar fa ku damu ko ku Ι—aga hankalinku, kun san ba a hayyacinta take ba, tana fama da matsalar taΙ“in hankali."

Hajiya Suwaiba ta ce "Duk da haka amma mutum ko ba shi da hankali, yana faΙ—ar abin da yake aikatawa ne, amma babu rami mai ya kawo rami?"

"Ƙaryata ni za ki yi kenan Suwaiba? Meye haΙ—in Yaya Sa'a da wani shan jini, kawai raΙ—aΙ—in mutuwar Ι—anta ne yake damunta"

Fafur ya hana su magana, tare da kare Sa'a, duk da Ζ™asan zuciyarsa maganar Hajiya Suwaiba ta kama zuciyarsa, da ta ce babu yadda za a yi Hajiya Sa'a ta yi wannan maganganu idan bata da alaΖ™a da su.


*****


Imam Zahradeen ne zaune a gaban mahaifiyarsa Hajiya Bilkisu, cikin kuka take yi masa bala'i "Yanzu Zahradeen har zaka iya fifita bare a kaina mahaifiyarka, ka zaΙ“i ka tona mini asiri? Yanzu amfanin me hakan ya yi maka daga kai har ni. Duk fafutukar da na yi domin ka ne, amma a Ζ™arshe ka watsa mini Ζ™asa a idona. Ka lalata komai abin da nake harin ba zaka samu ba, saboda kai ne gwanin na iya da son burgewa, ka tona mana asiri ga shi kaima baka tsira ba"


"Ban yi duk abin da na yi, domin tozarta ki ba Ammi, duk abin da na yi, na aikata ne domin kaucewa faΙ—a wa fushin Ubangiji. Bawa bai taΙ“a isa ya yi wa bawa abin da Allah bai yi masa ba. Duk Ζ™oΖ™arin ku Ammi idan Allah bai Ζ™addara mu hau karagar nan ba ba zamu hau ba. A yanzu hakan ku nawa ne ku ke fafutuka, ko da an kawar da Hammad, kuma ba zaku samu zaman lafiya da fahimtar juna ba, kowa na sa yake son ya hau. Ammi Hammad fa shikaΙ—ai ne Ι—an uwana namiji...

"Tashi ka bani guri, kafin baΖ™in ciki ya sanya na tsine maka, ka fita ka bani guri" Zuciyarsa cike da Ζ™una ya tashi ya bar sashen ta.


Murmushin fuskar Nana ya kasa Ι“oyuwa, Ƙaisar shi ma murmushin ya yi, kamar koyaushe gyaran litattafansa yake yi. Ya ce "A karo na babu adadi, ina sake taya ki murna ma a wannan karon, tabbas ko a iya haka kin yi nasara. Kuma aya ce ke mai zaman kanta ga mutanen Agadez ba Agadez ba kawai ga duk wani mai hankali ma. Jaruma ce ke ta gaske uwar gijiyata"


"Ƙaisar"


"Na'am"


"Ina yi maka kyakykywan fatan alkhairi na har abada "

Ya ajiye littafin hannunsa ya ce "Har kin mantan Allah ya isan da ki ka yi mini a baya"

Ta katse shi ta hanyar cewa "Duk wanda yake rinjayar da laifukan mutane, sama da alkhairinsu, to zai zama mara adalci"


Ya ce "To ai ni ba mutum bane"


Ta yi dariya ta ce "Ni a gurina kai mutum ne. Alkhairinka ya shafe laifukan ka Ƙaisar. Gaba Ι—aya ji nake yi kamar ba ni ba, zan rayu da Hammad Ι—ina, da kuma Muhsin Allah abin godiya kamar komai ba zai wuce ba"


Ya zauna yana faΙ—in "Babu abin da ba ya wucewa sai ikon Allah"


Za ta yi magana ta farka daga baccin da ya Ι—an Ι—auke ta.

Da Sayyid ta fara tozali ya ce "Amarya"

"Ango" Ta amasa masa tana murmushi.

"Nene ta ce sai na mayar mata da ke, wai shirya ki za a yi, ba dai yadda zan yi ne, na fi son ta bar mini ke in din ga jin Ι—uminki. Ke ba kya buΖ™atar duk wani gyara, a gyarenki Allah ya yi ki"


Nana ta tashi zaune ta ce "Allah ya shirya mini kai, Nenen zaka gaya wa haka ko? Ni sonake ma na gana da Ι—an uwana na yi kewarsa"


Hammad ya numfasa ya ce "Kin san Sultan sun samu matsala da Imam Zahradeen, ina ta girgiza miki kai Ι—azu, ki bari sannu a hankali zai saukko zan san yadda zan yi na shirya su. Amma da farko ji na yi kamar ba zan yafe masa ba. Amma na duba girman abubuwan da ya yi na alkhairi a gare ni. Kuma ni duk mutumin da zai yi abin da zai kyautata miki to ni ya yi wa, dan haka na ji zan mayar da komai ba komai ba. Kin san wani abu ma vie"

Ta girgiza masa kai alamar a'a.

"Wallahi idan na kalle ki, na kalli Muhsin, sai in ji zan iya yafe wa kowa ma, Duniyar guda nawa take? Allah ya yi mini tagomashi da abin da na san ba dabara ta ba ce ba. Ba zan fasa gode wa Allah ba"

Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya Sayyid. Amma ina da wani roΖ™o a gare ka; kamar yadda ku ka soke al'adar haramta auratayya tsakaninku da baΖ™aΖ™en fata, ina roΖ™on ku haramta duk wani nau'i na ta'amalli da Aljanu da shaiΙ—anu"

Ta Ι—an yi shiru tana satar kallonsa.

Ya ce "Ina jinki"

Ta ci gaba da faΙ—in "Ta'amalli da aljanu, da hana iliminku na addini tasiri a cikin rayuwarku, haΙ—i da riΖ™o da munanan al'adu su suka Ζ™ara ta'azzara wasu abubuwan. Ga dai zobunanka masu Ι—auke da hadiman aljanu, amma hakan bai hana a cutar da kai ba, cuta mai munin gaske. Su ba su baka kariya ba, su ba su hana a cutar da kai ba. Babu wata halitta da zata baka kariya ko ta hana faruwar wasu abubuwan a rayuwarka. Sai dai duk da wannan abin, ina girmama riΖ™o da ibadarka mussaman salla. Kai ma'abocin salla ne. Dan Allah Imam ka Ζ™ara Ζ™oΖ™ari gurin ganin an kakkaΙ“e al'adar amfani da aljanu a cikin harkar mulki. Ga saΙ“on Allah, ga gadar wa zuriya masifa da tashin hankali. Ni da kai Ι—in nan mislai ne akan kanmu, ba zamu yi fatan ire-iren zuriyarmu su gaji wannan bala'in da muka shiga ba. Dan Allah Hammad ka yi Ζ™oΖ™ari a yi yaΖ™i da ta'amalli da su, da kuma duk wani abu da ya shafe su. A Ι—ayanta Allah, a dogara da shi duk ba kwa buΖ™atar wannan abubuwan muddin kun riΖ™e Allah ".

Ya numfasa ya ce "Maganganunki duk gaskiya ne Ma vie, kuma tuntuni na fara Ζ™oΖ™arin neman maraba da su, ni kaina na daΙ—e ba na son harkar da muke yi da su, amma in sha Allah zan Ζ™ara Ζ™arfafa hakan, har abada za a daina amfani da duk wani nau'i na gurΙ“atacciyar al'ada a Agadez"

Nana ta rungumo shi ta ce "Yauwwa farincikina, Ubangiji Allah ya saka maka da alkhairi, ya Ζ™ara kare mini kai daga dukkanin wani sharrin. Allah ya Ζ™ara Ι—aukaka mini darajarka zuwa inda zato bai taΙ“a zato ba. Allah ya yi maka kyakykywan tsari daga sharrin duk wani abin Ζ™i komai Ζ™anΖ™antarsa."

Ya tsurawa Nana ido, sannan ya ce "Ta yaya ake so na iya rayuwa babu wannan halittar? Halittar da harshenta kullum cikin yi mini addu'a da fatan Alkhairi take. 

Mai Ι—auke da zuciyar da kullum take Ζ™oΖ™arin kusantar da ni ga Allah, baiwar Allah da kullum burinta ta sadaukar Saboda da komai saboda ni. In sha Allah mutuwa ce zata raba ni da ke rayuwata. Allah ya yi miki tukuci da gidan aljanna. Ina Ζ™aunrki Asma'u." Ya yi maganar yana tsare ta da manyan idanunsa, da ba ta san dalilin canzawarsu zuwa ja ba.


"Nima ina Ζ™aunarka mijina, irin sosai da sosai, ban san ya zan misalta maka ba"


"Ba sai kin misalita mini ba, na gani a zahiri" Ta sunkuyar da kanta tana Ι—an murmushi.

Ya ce "Yanzu me za ki shirya mana, na shirin bikin? Sultan ya ce sai an yi biki sosai a Agadez, me za ki shirya mana? Me da me ki ke so?"

Ta girgiza kai ta ce "Kai kaΙ—ai kawai nake so, kai kaΙ—ai ka ishi Nana komai"

Ya yi dariya ya ce "Zan kawo miki Imrana da Muhsin, har ma da Nene anjima su Ι—ebe miki kewa"

Nana ta ce "Amma kuwa da ka kyauta, na gode sosai da sosai"

Ya dungure mata kai yana murmushi.


*****

Alhaji Fatuhu kuwa bacci ne ya gagare shi, kamar yadda dariya ta gagari kare, ya gagara yin bacci. 

Idan ya samu baccin ya fara Ι—aukarsa, kawai sai ya ga Hajiya Sa'a, tana kuka tana sake maimaita abin da ta faΙ—a da suka je. Duk yadda ya din ga addu'a, da Ζ™oΖ™arin kawar da tunanin daga zuciyarsa, amma abu ya faskara.

Sai dai ya danne ya ci gaba da addu'a.

Sai kuma doctor Sharif ya faΙ—o masa, da shi ma yake cewa ya yafe masa, to ya yafe masa da ya yi masa me? Gaba Ι—aya sai al'ajabi, ya hana shi yin farincikin dawowar kayansa. Ga shi ya zo gaya wa Alhaji Zailani,  tun da dama shi ne abokin kasuwancinsa, amma ya tuna yadda Fadila ta gargaΙ—e shi a kan haka.


*****


Sagir kuwa tun da yaje Abuja gidansu Yusra, hankalinsa ya Ζ™ara tashi. Jaririn da ya gani da shi yake kamanni, ya yarda jaririn nan Ι—ansa ne, amma babu yadda ba a yi da Yusra ta yi magana ba, ta faΙ—i a ina ta haΙ—u da Shukura ba. 

Sai dai ana ta ba wa jaririn madara. Sagir ya ce wa mamanta "Ina ga, zan koma Kano na samu iyayen Shukura na sanar da su cewar, an ga jaririn Shukura"

Maman ta ce "A'a kar ka faΙ—a tukuna, kar a zargi Yusra da wani abu, a ci gaba da addu'a dai da bincike, haryanzu Yusra bata cikin nutsuwarta.

Haka ya din ga sintiri tsakanin Abuja da Kano, ga shi ya kasa gaya wa kowa, saboda shi kansa ya san ayar tambaya za a saka wa Yusra. Sai dai al'amuran Yusran su na ba shi tsoro shi kansa, banda yana sonta kuma ya san halin da ta shiga, lokacin da Shukura ta Ι“ata, da babu abin da zai hana ya ce da sanya hannun Yusra a lamarin Ι“atan Shukura, idan ba haka ba a ina ta samu jaririnta?


****


Labari ya cika ciki da wajen Agadez, kan cewar Hammad yana da Ι—a, ya auri 'yar Nigeria, haka zalika an soke Al'adar hana auren baΖ™ar fata. 

Wasu daga cikin al'ummar garin hakan yayi musu daΙ—i, mussaman baΖ™aΖ™e, da suka din ga jin tamkar su zuba ruwa a Ζ™asa su sha.


Ɓangaren fararen buzayen kuwa, gani suke yi tamkar rage musu kima ne, da kuma rage karsashin Masarautar.

Cikin marasa gaskiya a fadar Sultan kuwa, cikinsu ya Ι—uri ruwa cike da tashin hankali, saboda tsoron hukuncin da ka iya biyo bayan tonuwar asirinsu. Ga shi Sultan ya Ζ™i nuna musu ya san su ne, kuma tun daga ranar da aka kawo bokan nan fadar Sultan, ba a sake zaman majalissar ba.

WaΙ—anda ba su san Nana ba, suka din ga sintirin gidan Sultan, su na son ga Nana, amma Nana na kauwwame a sashin Sultan.


Tuni labari ya ishe Asal, wanda hakan ya sake gigitata,  tamkar za ta yi hauka. Wani irin so da matsanancin kishin Hammad ya din ga taso mata, ji take yi tamkar za ta yi hauka. Gani take yi ta Ζ™asaΖ™anta ta tozarta, a ce Nana ce kishiyarta, matar da ta Ι—auka tamkar baiwar da ta saka kuΙ—i ta saya, amma yanzu ita ke da komai, ita kuma tana gefe ta zama 'yar kallo.

Wasa-wasa Asal ta daina cin abinci sai kuka, ga Tafawa ba ta ita yake yi ba, ta zaman jiran tsammanin abin da za a yanke musu kawai yake yi.


Duk matsanancin kishin Hammad, haka ya Ζ™yale Nana da Imarana, suka kasance tare suna ta hira irin ta 'yan uwantaka, tare bawa junansu labarin gwagwarmayar da suka yi ta rayuwa.


Ya ce "Bari na nuna miki wani abu" Imarana ya Ι—an tashi ya fita, sannan ya dawo, ko da ya dawo ya miΖ™a wa Nana waya.

Nana ta karΙ“i wayar tana kallonsa, ya yi mata alama da ta saka a kunnenta.


Nana ta saka wayar a kunnenta, zuciyarta na Ι—an bugawa da sauri.


"Assalamu alaikum, Nana" Muryar Ummansu ce ta doki dodon kunnuwanta, a wani irin rikice Nana ta tashi tsaye, ta rasa ina zata dosa ta ce "Um..umma, muryarki ce ke ce?"


"Nice Nana, kina nan lafiya?"


Nana ta durΖ™ushe a kan gwiwoyinta, ta ce "Umma, bani da bakin da zan yi miki magana, bani da idon da zan iya kallonki, ni mai tarin laifi ce"


"Shhh, Babu abin da ki ka yi mini na ba dai-dai ba Nana. Sai dai tashin hankali da fargaba na shige shi, na rashin sanin inda ki ke, da kuma wani hali ki ke ciki, ga tsohon ciki kin tafi kin bar gida. Amma Imrana ya zo inda nake, tare da Yayan mijinki, sun yi mini bayanin komai. Nana na yi sujuda na gode wa Allah, ba wai domin daular da ki ke ciki ba, ko kina auren wani ba, sai domin murnar kina cikin Ζ™oshin lafiya tare da ke da yaronki. Sun ce kar na gaya wa kowa, babu wanda ya sani, amma sun zo sun yi mini alkhairi Imrana ya zama babban mutum ya nutsu, kema hankalinki yana kwance. Ni dai fatana su yi su kawo mini ke, ko na wanko Ζ™afata na taho,amma sun ce na yi haΖ™uri kaΙ—an"


Cikin kuka Nana ta ce "Ni dai ki yafe mini dan Allah, tashin hankalin da na sanya ku a ciki, dan Allah ku yi haΖ™uri Umma" Imrana ya karΙ“e wayar ya ce "Umma sai anjima, da na sani ban haΙ—a ku ba, nema take ta rikice"


****

Hajiya Amina tana zaune tare da Alhaji Zailani, tana ta lallaΙ“a shi a kan ya ci abinci, amma ya Ζ™i ci, saboda shikaΙ—ai ya san bala'in da yake ciki. Tun da ya yi mafarkin an huda saitin zuciyarsa, dodon Ζ™ungiya yana sha masa jini, ya farka ya ji saitin zuciyarsa ya yi masa wani irin nauyi.

Ga jikinsa sai yi masa wani irin raΙ—aΙ—i yake yi, kamar ya yi wanka da yaji. Yana jin yadda wayarsa take ta ringing amma ya Ζ™i Ι—agawa.

Daga Ζ™arshe, Hajiya Amina ta saka hannu ta Ι—auki wayar, ta saka a kunnenta tana sallama.

Jin ta yi shiru ya sanya Alhaji Zailani Ι—agowa ya kalle ta, sai dai ta tsare shi da idanunta ba ta ce masa uffan ba.


Jiran Hajiya Amina yake yi ta yi magana, amma ta yi shiru ba ta yi magana ba. Jiki babu Ζ™wari ya ce "Ya dai? Meyafaru?"

Jiki a sanyaye ta ce "Daga makarantar su Yusuf ne, wai yana kwance a Asibiti babu lafiya, yau kwana uku kenan"

Ya waro ido ya ce "Yusuf Ι—in?" Ta jinjina masa kai.

"Ki kira su ki gaya musu, ni ba ni da lafiya, babu lallai na iya driving su dawo mini da Ι—ana gida"

Hajiya Amin ta jinjina kai tare da mayar da hankalinta  kan wayar.


*****


Gidan Baba ya zama tamkar maΖ™abarta, babu walwala ko kaΙ—an, ko Ζ™aunar tunkarar gidan baya son ya yi.

Saboda matsananciyar damuwa, da takaicin abubuwan da suke faruwa a gidan.

Jamila kuwa kullum tana Ι—aki, dan ta sha baΖ™ar azaba, sai da ta kwana tara a Asibiti, da kyar aka samo kanta kamar ba zata rayu ba.

Ya daina shiga harkar Mama da yaranta gaba Ι—aya, ko abincin gidan ya daina ci. Ga damuwa da kewar yaransa Nana da Imrana da suka addabi zuciyarsa.

Ya fito daga cikin gida da buta a hannunsa, ya yi alwalar sallar Azahar sai ga wata danΖ™areriyar mota irin ta matafiya, sabuwa gal sai Ζ™yalli take yi ta shigo layin.

Bai damu ba, ya idar da alwalarsa ya Ι—aukko wayarsa, yana son kiran can Buda, saboda yaga kiran wayarsu, bai samu ya Ι—aga ba. Sai ya ga motar nan an tsaya da ita a Ζ™ofar gidan. Sai ya yi tsuru yana kallon motar.

Sulei ne tare da Mahmoudu suka fito, suka nufo Baba. Ya tsaya saroro har suka Ζ™araso inda yake.

Suka durΖ™usa har Ζ™asa suka gaishe shi, ya amsa musu yana bin su da kallo, kasancewar sun rufe fuskokinsu da takunkumi.

Bayan sun gaisa, Mahmoudu ya ce "Baba mu na tare da baΖ™i ne daga Agadez"

Baba ya Ι—an yi shiru, shi dai ya san babu wanda ya sani a Agadez, amma ya miΖ™e ya ce "To bari na kawo muku abin zama" Ya tashi ya shiga cikin gidan, ya Ι—aukko tabarma ya shimfiΙ—a musu, ya koma ya aiki Nasiru ya sayo ruwa. Ya zata iya su Mahmoudu ne baΖ™in, kawai ya ga Sulei ya je ya buΙ—e motar, wani dogon mutum mai jiki ya fito da wani matashi, shi ma sanye da rawani suka fito, suka nufo shimfiΙ—ar. Shi dai Baba duk abin ya Ι—aure masa kai, tsoro ya shige shi.

Ya yi musu barka da zuwa, suka zazzauna, Mahmoudu ya sauke rawanin fuskarsa ya ce "Baba baka gane ni ba?" Baba ya yi shiru ya ce "Kamar dai na sanka, amma ban gane ka ba"

Imam Zahradeen ya sauke rawaninsa shi ma, shi ma dai Baban ya yi masa kallon sani.

Mahmoudu ya ce "Baba kamar baka gane mu ba ko?"

Baba ya ce "Gaskiya dai"

"BaΖ™i ka yi daga Agadez"


"To bawan Allah, ni wa nake da shi Agadez, kuma ba Ι“atan kai ku ka yi ba?"


Mahmoudu ya ce "Ba mu yi Ι“atan kai ba, na yi mamaki da ka ce ba ka gane ni ba, amma ai ka tuna buzun da ka aura wa 'yarka shekarun da suka gabata"

A razane Baba ya Ι—ago ya kalli Mahmoudu, sai kuma ya riΖ™e rigarsa, ya ce "Dama ku ne? Ba ku yi mini adalci ba, ku ka tattara ku ka gudu, ku ka bar mini 'ya da jinyar Ι—an uwanku, shi ma daga Ζ™arshe ya gudu ya bar ta, saboda wauta da rashin hankali wai ta tafi Niger neman shi, haryanzu shekara ta uku kenan, babu wanda ya san inda take, baku kyauta mini ba" Baba yayi maganar yana kuka kamar Ζ™aramin yaro.


Imam Zahradeen ya ce "Baba, ka yi haΖ™uri abubuwan da suka faru ba a kyauta maka ba. Amma mu na da kyakyawan albishir ne"


Baba ya ce "Kai ba kai ne mijin nata ba?" Yayi maganar yana nuna Imam Zahradeen.

Zahradeen ya ce "Baba ai na fi wancan tsufa, shi ya fi ni Ζ™uruciya, ya kuma fi ni kyau, ni yayansa ne. Zancen da nake yi maka, a kowane lokaci mahaifinmu zai iya aiko da mutanensa daga Agadez da kayan auren Nana za a sake gagarumin bikin aurensu"


Baba ya ce "Ashsha! Yarinyar da nake gaya muku shekara uku babu wanda ya san inda take, kuma babu wanda ya waiwaye ta tunda ku ka gudu kuka bar ta. Kuma ni mene ne haΙ—ina da Sarkin Agadez da zai kawo kayan aure? Ni dai na yi nadamar abin da na aikata na aurar da 'yata ga mutumin da ban san daga inda yake ba"

Imam Zahradeen ya lura ran Baba a Ι“ace yake.

Ya sassauta murya ya ce "Baba sunana Imam Zahradeen Jalaludeen Agadez, ni Yaya ne ga Imam Hammad Jalaludeen Agadez. Kuma 'ya'ya ga Sultan Jalaludeen Agadez, wato Sarkin Agadez na yanzu. Buzun da ka aura wa 'yarka, Ι—an uwana ne, kuma  Ι—a ne ga Sultan na Agadez."


Baba ya kalli Imam Zahradeen kamar yana raina masa hankali.

Ya ce "Ɗan sarki ne zai zo baro Ζ™asarsa ya zo Nigeria yana aikin gadi?"


Mahmoudu ya ce "Baba, idan baka manta ba, ko lokacin da aka yi aurensu, a yanayi na rashin lafiya yake,  rashin lafiya ce ta kama shi"


"To yaya za a yi a ce Ι—an sarki ya zo Nigeria gadi, ni abin ya bani mamaki ne. Kuma na kasa yarda, ni kar ku sake dugunzuma mini hankali bayan halin da nake cikix


Zahradeen ya ce "Baba ba dunguzuma maka hankali za mu yi ba. Mun zo mu sanar da kai batun zuwan baΖ™inka ne daga Agadez, kafin su zo Ι—in."


"To wai su zo, su yi mini me?"


" 'yarka Nana, tana gurinmu tare da Ι—anta Muhsin"

Baba bai san ya aka yi ya tashi tsaye ba, yana zazzaro ido ya ce "Nana Asma'u dai 'ya ta? Yaya aka yi ku ka same ta? Tana ina? Kun taho mini da ita?"


Mahmoudu ya miΖ™e tsaye ya ce "Baba shi ne bayanin da muke yi maka, Nana tana tare da mu, za a kawo dukiyar aurenta Nigeria za kuma a yi bikin aurensu sosai da sosai. Duk abin da za mu gaya maka yanzu ba za ka fahimce mu ba, saboda a cikin damuwa ka ke, kuma abubuwan da suka faru su na da tsawo da sarΖ™aΖ™iya akwai buΖ™atar a yi maka bayani daki-daki. Ba Nana ba hatta Imrana yana tare da mu a Agadez, akwai tarin bayanai da sai ka nutsu, an yi maka bayani zaka fahimce su"


"Amm bawan Allah, ni ko yanzu a shirye nake, mu tafi Agadez Ι—in na karΙ“i 'ya'yana. Bayan Nana kuma me ya haΙ—a ku da Imrana"


Imam Zahradeen ya ce "Alkhairi ne, a cikin satin nan, zuwa mai kamawa in sha Allah; za a sake turo maka baΖ™i daga can. Kuma za a yi bikin su al'ada saΙ“anin yadda ya gudana, kuma za a yi maka bayani kamar yadda nake nanata maka. Amma kafin nan mu na son za a gyara maka gidan nan, ko kuma a canza maka wani"


Baba ya girgiza kai ya ce "Ba na buΖ™atar haka, muddin Nana yake so, babu amfani a raina inda ta fito, ni dai fatana na gansu cikin Ζ™oshin lafiya"


Zahradeen ya ce "Ba raina maka aka yi ba, matsayinka da girmanka ne ya sanya za a yi maka." Fafur Baba ya Ζ™i yarda da hakan, da kyar suka rarrashe shi suka tafi, dan cewa ya yi ba za su bar Ζ™ofar gidansa ba, ba tare da ya ga yaransa ba.

Kasancewar duniya makarantar da ko babu malami, ta biya maka darasi dole ka Ι—auka ce, ta karanta wa Baba darasin da duk son abin Duniyarsa, yanzu tsoro yake ji. 

Zuwansu Imam Zahradeen babu wanda ya sanarwa, saboda gani yake yi tamkar Ζ™arya Buzayen nan suka zo suka sharara masa.

Ya kasa gaya wa kowa, sai Uwani ya kira ya sanar mata. Sai dai a Ζ™arshen maganar Baba ya ce "Amma Uwani ni ban ji na yarda ba, ji nake kamar Ζ™arya kawai suke yi ban ji na yarda ba"

Uwani ta ce "Alhamdillah, ni dai na ji na yarda har cikin zuciyata. Ko ba hakan ba ne, ina fatan Allah ya tabattar da shi ya zama gaske. Wallahi zuciyata ta daΙ—e tana bani, mijin Nana ba Ζ™aramin mutum ba ne, to ita Nanan da gaske tana gurinsu, kuma har da Imrana sun haΙ—a ku ko a waya ne?"


Ya ce "A'a, shiyasa na kasa yarda ma gaba Ι—aya"


"Isa, yarda ni dai na gama ta, zamu duΖ™ufa mu ci gaba da addu'a in sha Allah Nana suna cikin kwanciyar hankali tare da Ι—an uwanta" Kalaman Uwani suka Ι—an Ζ™warara wa Baba gwiwa.

Bayan sallar isha'i ya shiga gida, yana zaune yana jin radio, Mama tana cikin Ι—aki tare da Jamila da ta koma so silent, ko magana ba ta iya yi.

Ihun da Jamila ta yi ne, ya sany Baba jifa da radio ya tashi tsaye yana rarraba ido.

"Mama! Mama!! Dan Allah ki taimake ni, dodon Ζ™ungiya zai shanye mini jini. Hajiya Sa'a kin cuce ni, kin cuci rayuwata, na kasa samun aminci da salama. Na baku Abba me kuma ku ke nama a gurina?"

Cikin rashin fahimta duk suke kallon Jamila, Baba ya ce "Me yarinyar nan take faΙ—a ne haka?"

Mama ta ce "Nima ban sani ba wallahi, ina ga jikin ne ya motsa."

Baba ya ce "Jikinta ya motsa kuma take irin wannan maganganun?"

Ba ta ko saurare su ba, ta ci gaba da surutanta. "Ni ban so shiga kungiyar nan ba, dole ki ka yi mini, ga shi kin sanya ni a bala'i, na rasa mutuncina, kin saka nayi kisan kai, yanzu kuma na kasa samun kwanciyar hankali, sai tsorata ni ake yi, nima ana nema na a kashe ni, kin cuce ni"

Baba ya ce "Jamila, meyafaru ne? Me ki ke faΙ—a wai?"


"Baba riΖ™e hannuna, Baba ku taimake ni"


Ya Ζ™arasa ya riΖ™e hannun Jamila, cikin kuka ta ce "Baba na shiga uku, na aikata mummunar Ι“arna, Baba hakki ne zai yi ajalina"


Baba ya ce "Jamila, ki gaya mini, me ki ka aikata?"


"Ƙungiyar asiri, Baba Ζ™ungiyar asiri aka shigar da ni, saboda na kai jinin Nana"


Kamar ta watsa wa Baba wuta, haka ya fizge hannunsa ya ja da baya, yana kallon Jamila da take ta uban kuka.

Mama ta ce "A'a baban su Jamila, dan Allah kar ka yarda da abin da ta faΙ—a, ka san ba ta da cikakkiyar lafiya, wataΖ™ila zafin ciwo ne, amma wace irin magana ce wannan, a ina Jamila za ta ga wata kungiyar asiri ta shiga"


Alhaji Zailani ne a durΖ™ushe a gaban gawar Ι—ansa Yusuf, bayan an dawo da shi daga makaranta, dama babu rai aka dawo da shi. Ba shi ne abin da ya Ι—aga masa hankali ba, sama da ganin busashshen jini a baki da kuma hancin Yusuf. Ba dan ya yi iya Ζ™oΖ™arinsa ba, da tuni ya aikata abin da zai fallasa kansa. Wani irin raΙ—aΙ—i da zafi ya din ga ji a zuciyarsa ya kasa magana, ya kasa ko Ζ™waΖ™wΖ™waran motsi.

Ba a jima ba, gidansa ya cika da jama'a, Hajiya Amina sai kuka take, ga Shukura ta Ι“ata, ga kuma mutuwar Yusuf.

Ya hau neman lambobin yaransa, da ya sanya su kashe Shukura, a kan kar su kuskura su kashe ta, amma ya kasa samun su. Duk da daΙ—ewar da yayi yana aikata zalunci kala-kala, mutuwar Yusuf ta dake shi, ta tsaya masa. Ya din ga jin tamkar ya yi ta kururuwa yana burgima, ko zai ji daΙ—i.

Ko da aka yi jana'izar Yusuf, Alhaji Zailani tafiya ya yi ya kulle kansa a Ι—aki. Kaf yaransa babu kowa sai Shukura yanzu, Shukuran ma ba a san inda take ba. Kuma ita ma baya tsammanin za ga tsallake sharrin dodon Ζ™ungiya, tun da ya gaza bashi jinin shekara.


Sosai ake ta shirye-shiryen gudanar da bikin auren Imam Hammad, da matarsa 'yar Nigeria. Ita Nana abin har mamaki yake bata.

Tun da Sultan ya amince da auren Nana da Sultan, Nene take sintiri kawo wa Nana kayan gyaran jiki. Ban da matar da ake ware mussaman Nene take zuwa da ita, take yi wa Nana wani irin gyaran jiki na mussaman.

Nana ta ce "Nene duk wannan abin fa ihu ne bayan hari"

Nene ta ce "Ke, gyaran ne ba kya so?"

"To Nene ya riga ya sanni a yadda nake, me kuma zan gyara?"


Nene ta ce "To kar ki gyara, komai yana buΖ™atar gyara ai"

Aka ajiye wa Nana kayan sakawa, da na ado irin na Buzaye. Nana ta Ζ™udurce a ranta, bayan ta tare, kayanta na 'yan Nigeria za ta saka Hammad ya ajiye mata, saboda ita ma tana son tata al'adar.

Shi kansa Hammad ya so a Ζ™yale masa ita a haka, dan shi komai nata ya yi masa. Sai dai gyaran jikin da ake yi matan ba Ζ™aramin kyau take yi ba.

Ga shi tare da Muhsin suke kwana da Nene, hakan ya Ζ™ara sanya ta farin ciki.

Hammad ya ce ta fita ta Ι—an zagaya, amma ta sanya takunkumi ta rufe fuskarta.

Har mamaki Nana take yi, yadda idan Muhsin ya ga raΖ™uma ko shayi, kamar zai tashi sama saboda murna. Sarkin baka ta hango, suka nufe inda yake.

Cikin jinjina ya ce "Barka da tattaki uwar gijiyata" Nana ta yi dariya ta ce "Dan Allah ka daina kunya ka ke bani"

Shi ma yana murmushin ya Ι—ago ya kalli Nene, ya ce "Ni kuwa dama ina ta son na yi miki magana, Allah bai yi ba"


Nene ta ce "Ni Ι—in ko? Ka sanni ne?"


Ya ce "Eh, ai duk inda muka ga juna, muna gane kanmu"


Ta yi dariya ta ce "Na ji, ai ban yi zaton haryanzu akawai abin da tattare da ni ba"


Sarkin baka ya ce "Ni na ji na gane ai. Kuma ni Ι—alibin marigayi Sa'adu Aska ne"


Nene ta waro ido ta ce "Kana nufin Babana?"


Sarkin baka ya ce "Ƙwarai da gaske, ya sanar da ni magunguna, sai muka kwana casa'in tare da shi, a mabanbantan dazuzzuka, daga bisani muka rabu, ban sake ganinsa ba. Mahaifinki mutumin kirki ne, ba zan manta da shi ba har abada"


Nene ta ce "Ikon Allah"


Nana ta ce "Sarki kai komai ma ka sani ne? Kuma kowa ya sa ka"


Yayi murmushi ya ce "Na san dai abin da Allah ya sanar da ni, kowa ya sanni kuma na sha yawon duniya ne" Yayi maganar yana Ι—aukar Muhsin.


Nana ta ce "Sarki ka ga Nene ta daina harkar bayar da magani, kaima ina fatan zaka daina?"


Ya ce "Meyasa zan daina? Ba a daΙ—e ba ni ba, ke kanki ki ka bayar da magani zan ce, ko ba ke ki ka tono inda aka yi wa mijinki asiri, meyasa Allah ya zaΙ“e ki ya nuna miki, duk yawan jama'ar da ke Ζ™asar nan. Abin da ki ke ta gudun sai da ya faru"


Jiki a sanyaye Nana ta ce "Ba ina nufin ka daina bayar da magani ba, ka daina aiki da aljanu, shi ne Ι“arnar. Sannan ka yi ilimi na zamani, cikakke domin ka inganta harkar maganin naka. Ya zamana maganunnanka da awo kar ka bayar da abin da zai cutar maimakon a samu lafiya"


Yayi dariya, Nene ma ta yi, Ya ce "Yaro yaro ne. Nana a dalilinki wallahi na daina surkullen haΙ—a ayoyin Alkur'ani da wasu abubuwan na yi sihiri. Saboda uban gidana ma, Allah ya ja zamaninsa uban duΖ™usa ko in ce Ƙaisar, shi ma ya ce na daina wannan, na kuma daina. Na daina surkulle da sihiri na tuba, amma ba zan iya daina aiki da aljanu ba"


Nana ta ce "Amma saboda me?"


"Saboda Ι—ebo mini magani, wasu ayyukan kuma dole su ne nake aikawa su yi wani aikin."


"Sarki, ta'amalli da aljanu da ka ke yi ba shi da wani alkhairi shirka ne, dan Allah ka daina. Kana cikin mutanen da nake son mu tsira Duniya da lahira."


"Ni ba ni na nemi aljanu na fara aiki da su ba, aljanu su suka takura ni, kamar dai ke da kuma wannan baiwar Allah.

Bana ta'amalli da aljanu, na bayar da kuΙ—i, ko na yi wa wasu sihiri, ko wani abu makamancin haka, ai kin je gurin maganin nawa kin gani"


Nana ta ce "Sarki, kar mu shiga wani bugire da bai kamata mu shiga ba, mu kalli gaskiya kai tsaye kar mu yi mata wata kwaskwarima saboda son zuciyarmu"


"Asma'u babu kwaskwarima domin ba wa Ζ™arya kariya a maganganuna. Su turawan da ku ke taΖ™ama da su, su na amfani da ku, da daΖ™ile magungunnku ne, saboda gina nasu kasuwancin. Kuma Nana magunguna na da awo nake bahar da su. Ban Ζ™i ba akwai masu bayar da magani, saboda neman abinci. Amma wanda ya sani ya sani, wanda bai sani ba, bai sani ba kawai. Kuma banda abin ki tun a zamanin baya magungunan 8su na da awo, wani a ce ka auna da Ι“awon gyaΙ—a,ko farce, wani a ce ka sha safe da yamma, duk sharri ne wasu abubuwan da ake faΙ—a, da Ζ™oΖ™arin kashe mana magungunanmu. Sai a  ce ku daina shan magungunan gargajiya saboda Ι—aci, hanta ba ta son Ι—aci, amma Allah ya halicci maΙ—aciya a tsakiyar hanta. Idan hanta ba ta son Ι—aci, Allah ba zai sanya matsarmama a cikin hanta ba. Kuma su magungunan baturen, ba Ι—aci ne a cikin su ba. Ba zan kushe wa kowa ba, amma kar a kuskura a kushe mini nawa. Yakamata mu daina wannan musun haka,kowa ya riΖ™e abin da yake ganin shi ne dai-dai "

Nana ta Ι—an yi jimm tana tunani, daga bisani ta ce "Wasu maganganun naka na kan dai-dai, amma kowa ya riΖ™e abin da yake ganin shi ne dai-dai!"


"To ki daina takura mini a kan lallai sai na yarda da abin da ki ke kai"


99


1k ne via 0069685771

Aisha Adam stanbic 

08081012143



Har Nana za ta sake magana, Nene ta riΖ™o hannunta, ta ce "Nana mu koma ciki, ai kin Ι—an tattaka, kin san baya son a ganki, ko a gane ki a yanzu. Ɗan uwa idan muka kuma haΙ—uwa zamu tattauna sosai mu gaisa.


Sosai shirye-shirye suka yi nisa, hankalin Sultan gaba Ι—aya ya koma kan shirin zuwa Nigeria da bikin da za a gudanar. Sai dai yana ta fuskantar Ζ™alubalanta a kan hukuncin da ya zartar.

Gimbiya Bilkisu ta rasa inda zata sanya kanta, ta tuntuΙ“i Tafawa ta sanar masa da matakin da Sultan ya Ι—auka a kanta, amma ya ce mata shi ma ta kansa yake yi, hankalinsa a tashe yake.

Duk yadda ta kai ga Ζ™oΖ™arin yin dabarun da Sultan zai saurare ta, fafur ya Ζ™i ko kallo ba ta ishe shi ba.

Ranar Ζ™arshe ma da ta je Ι—akinsa kamar zai dake ta ya ce "Bilkisu bana Ζ™aunarki bana Ζ™aunar ganinki, tun da har za ki yinΖ™urin sabauta mini rayuwar Ι—a, idan ki ka sake zuwa inda nake, sai na yi miki abin da baki taΙ“a tsammani ba, fice ki bar mini Ι—aki kafin na yi miki illa" Abin ya Ι—aure mata kai, bata taΙ“a tunanin zai yi irin wannan fushin har haka ba.


Jamila ta koma gata nan gata nan, ita ba mahaukaciya ba, ita ba mai hankali ba, kuma ita ba mara lafiya ba. Shi Baba gaba Ι—aya ma yanzu tsoro suke ba shi. Ya riΖ™e istigfari ba dare babu rana, gaba Ι—aya yaransa sun watse babu wani na kamawa.

Gaddafi ya zo gida, ya tarar da gidan nasu duk wani iri. Yayi mamakin ganin yadda Jamila ta wani rakwakwkwaΙ“e, jiki babu Ζ™wari, ta yi wata irin muguwar rama ta fita daga hayyacinta kamar ba ita ba.

Sun dawo daga sallar Asuba, tare da Baba, Baba ya numfasa ya ce "Gaddafi ka ga yadda Allah ya yi da gidanmu ko? Gaba Ι—aya babu wani mai Ι—an dama-dama"

Gaddafi ya ce "Na gani Baba, ina son na yi magana dai na fasa, na ga Suwaiba ta daina magana gaba Ι—aya, har da dalalen yawu take yi. Jamila kuma na kasa gane abin da yake damunta"

Baba bai Ι“oye masa komai ba, jikin Gaddafi ya din ga tsuma, ya dubi Baba ya ce "Baba, Jamila ta yi ciki, kuma tana maganar Ζ™ungiyar asiri? Innalillahi wa Innalillahi raji'un"


Cikin matsananciyar damuwa Bab ya ce "Babarta ta ce zafin ciwo ne, amma na kasa yarda nima" Ya yi maganar yana zubar da hawaye.

Gaddafi ya ce "Shiyasa Baba na din ga maganar kuΙ—in da ta din ga ta'amalli da su, amma mahaifiyarta ta nuna ba ta so, ta nuna baΖ™in ciki nake yi, da ci gaban Jamila ka ga irin abin ko? Shikenan sun lalata mana gida"

Baba ya yi kuka ya ce "Ina kyautata zaton hakkin yaran nan ne, su Nana, dan sai daga bayan nan, nake duba wasu abubuwan da na aikata musu na ga sam babu adalci a cikinsa. Amma wasu mutane sun zo wai daga Agadez sun ce mini tana gurinsu" Nana Baba ya gaya wa Gaddafi abin da su Mahmoudu suka zo masa da shi.

Gaddafi ya rikice ya ce "Baba kuma baka karΙ“i lambar wayarsu ba ko ka bi su ba?"

Baba ya girgiza kai ya ce  "Ban karΙ“a ba, ni tsoro ma na ji, ji nake kamar Ζ™arya suke yi. Na bar wa Allah ikonsa"

"Amma Baba akwai mamaki a cikin abubuwan da suka faΙ—a, masu sarΖ™aΖ™iyar gaske"

Baba ya ce "To ai shiyasa ban ma gazgata ba, sai abin da hali yayi"

Gaddafi ya ce "Ba wani abu, in sha Allah mu tsammaci alkhairi"

Baba ya jinjina kai cike da gamsuwa.


****

Nana ce a tsaye, tana kallon Ƙaisar, yana zuba wa wata tsuntsuwa abinci a cikin keji.

Nana ta kalli tsuntuwar ta ce "Ƙaisar ita kuma wannan fa, a ina ka samo ta?"

Ba tare da ya kalli Nana ba ya ce tsinto ta na yi a daji, za ta mutu, ban zaci ma zata rayu ba, sai kuma na ga ta farfaΙ—o yanzu ta ware ma"

Nana ta Ζ™arasa gaban kejin ta zauna, sannan ta ce "To kuma tsuntsuwa ce ita, ko kuma aljana ce?"

Ya kalli Nana ya ce "Dama akwai tsuntsu mutum da aljan ne?"

Nana ta Ι—an yi shiru tana kallon tsuntsuwar.

Ya ce "Mutum jinsinsa daban, aljani daban, haka ma tsuntsu daban. Babu Aljani tsuntsu sai dai Aljani ya shiga jikin tsuntsun, ina fatan kin gane?"

Ta gyaΙ—a kai, ta ce "Haka ne, wai ni kuwa Ƙaisar ina Haulat? Ka fara son nata?"


"Ban sani ba" Ya yi maganar yana hararta.


Nana ta yi murmushi ta ce "To shikenan kai ba zaka yi aure ba kenan? To sonta ne baka yi ko kuma me ta yi maka?"

Yayi mata shiru, yana rufe kejin tsuntsuwar nan.

Nana ta numfasa ta ce "Ƙaisar ina kewar gida fiye da tunani, zuciyata kuma ta cika da fargabar rashin sanin abin da zan je na tarar. Ina jin kunyarsu ban san da wani idon zan kalle su ba. Duk da Imrana ya haΙ—a ni da Mama, ta yi mini Addu'a ta ce na kwantar da hankalina, amma kunyarsu nake ji ban kyauta ba abubuwan da na yi"

Ya ce "Za ki tarar da alkhari in sha Allah, da abun da zai yi miki daΙ—i da wanda ba zai yi miki ba. Ni na din ga shagaltar da ke daga tunaninsu, da tunaninsu ya yi tasiri a zuciyarki, da ba ki cimma wannan nasarar ba, da kin rushe komai, dan idan ki ka koma gidan babu abin da zai canza"


Cikin mamaki Nana ta kalle shi ta ce "Ban gane ba, kai ne ka sanya na daina jin damuwar da na din ga ji a baya, da son komawa gida?"


"Sosai, saboda ruhi ne mu, mu na iya shiga ko ina a jikin ku, kuma muna iya hargitsa tunani da sanya muku rashin nutsuwa"


Ta yi shiru tana nazari, ta sake cewa "Ƙaisar ka sanya ni a fargaba, abin da zan tarar a gida da gaske mara daΙ—i ne? Kodayake ko ka gaya mini ma idan na tashi na san mantawa zan yi sai abin da na je na tarar kawai"


"Kin yi zaton da mugunta kawai nake nuna miki abu na mantar da ke ko?" Nana ta jinjina kai.


"Ba haka ba ne, duk da ta wani fannin haka Ι—in ne, muguntar ce da takaicin Ζ™in yarda da abin da na zo miki da su.

Mafarki ya kasu kashi-kashi, duk da shi ma ina kan bincike a kansa. Akwai mafarkin da yake daga Allah ne, akwai mutanen da akan yi wa ishara a cikin bacci, na kusantowa ko kuma faruwar wani al'amari da bai faru ba kwata-kwata. Wasu kuma a nuna musu makamancin abin, wasu kuma su ga abu a duΖ™unΖ™une sai an fassara musu.

Galibi waΙ—anda aljanu ke nuna wa mutum a mafarki, na haΙ—in faΙ—a ne. Abu ne da aka yi shi a bayan idon mutum bai san an yi ba, sai su nuna masa. Kuma ba su fiye nuna abin alkhairi ba sai akasin haka. Wasu idan sun gani su na iya shiru da bakinsu, wasu kuma basa iyawa sai sun faΙ—a. Sai su sanya a din ga yi wa mutanen wani kallo na daban, wasu a dole dalilin hakan kan sanya su fara bayar da magani.

Ke na biyo miki ne ta hanya mai sauΖ™i, saboda bana son tilasta miki, na fi son ki amince da kanki. Sai na nuna miki abin da ya faru da baki sani ba, ko kuma wanda yake shirin faruwa, ko wanda nake hasashen abu ne mawuyaci bai faru ba. Akwai abin da idan na Ζ™yale ki, ki ka tashi da shi a Ζ™waΖ™walwarki, ba za ki iya yin shiru ba, za ki yi yinΖ™urin Ι—aukar mataki, wanda hakan ka iya haifar da fitina, saboda idan ki ka haifar da matsalar ba ki da maganinta, tun da ba ki amince da bayar da magani ba.

Ɗan Adam kuna da nau'in ciwo na gangar jiki, da kuma na ruhi, amma ba kwa damuwa da ciwon da yake damun ruhinku, kun fi damuwa da na gangar jiki. Mutum zai iya kashe maΖ™udan kuΙ—aΙ—e, a kan lafiyar gangar jikinsa, amma sam wani baya yadda ma ruhinsa yana rashin lafiya."

Nana ta ce "Nima ban gane ba"


Yayi murmushi ya gyara zamansa ya ce "Ruhi shi ne asalin rayuwa, da gangar jiki ta dogara a kai, wanda ba a iya ganinsa, ko taΙ“a shi, amma wanzuwarsa ce take sanya gangar jiki motsawa. Ruhi yana da alaΖ™a da hankali domin shi ne, ku 'yan Adam ku ke amfani da shi, gurin sarrafa duniyarku da gangar jiki. Lafiyayyen ruhi da tunani suke samar da nutsatsiyar gangar jiki mai cike da karsashi. Rashin lafiyar ruhi, ta fi ta gangar jiki hatsari. Idan ruhi yana rashin lafiya, yana kashe gangar jiki baki Ι—aya.

Sannan warkar da gangar jiki ya fi sauΖ™i a kan warkewar ruhi. Na san bayan nan nawa sun Ι—an yi miki tsauri, amma bari na Ι—an sauΖ™aΖ™a miki bayanan.

Kamar yadda na ce miki ruhinku yana rashin lafiya, tabbas yana yi ciwukan da ido baya iya gani, sai dai ciwon na sanya hankalinku ya Ζ™wace, ku aikata abin da ba shi kenan ba. Misali Alhaji Zailani ruhinsa na fama da ciwon Hassada, amma bai taΙ“a tsayawa ya fahimta ba, saboda hankalinsa ya Ζ™wace har ya din ga aikata miyagun ayyuka. Wasu lokutan ku kan ji duniya ta yi muku zafi, kun tsani komai babu laifin tsaye babu na zaune, yana daga cikin alamomi na ruhinku na buΖ™atar kulawa ba shi da lafiya. Dan wasu lokutan shi ne yake taΙ“uwa sai hankali ya taΙ“u, nan da nan sai a ce Ζ™waΖ™walwa babu lafiya, idan ciwon ba shi da alaΖ™a da irin matsalolin da muke haddasa muku a ruhi. Hassada, Ζ™yashi, yawan Ζ™arya baΖ™in ciki babu dalili, burin gushewar ni'ima ga wani, yawan raya faruwar munan abubuwa. Yanke tsammani daga samun rahama, ko wani abu na alkhairi a rayuwa. da wasu cututtukan ma da ku kan danganta su damu, alamomi ne na rashin lafiyar ruhi, duk da mafi yawa wasu lokutan mu ne muke haddasa rashin lafiya a ruhinku. 

Idan ku ka ji alamu na Ζ™yashi ko hassada, ba ku fiye sakankankancewa ku roΖ™i Allah ya yaye muku ba, ko ku miΖ™e ku nemi maraba da hakan ba, ba ku fiye Ι—aukarsa komai ba. Sai dai a hankali idan ya tsananta sai hankalinku ya gushe gangar jikinku ta aikata Ι“arna. Kamar dai abubuwan da suka faru a masarautar su mijinki. Da abubuwan da aka yi masa. Ƙyashi, baΖ™in ciki hassada, son kai, da makamantansu duk larurar ruhi ce da ke kashe gangar jiki.

Sai dai a zamana da ke na Ζ™ara fahimtar wani abu, babu abin da ya kai addu'a kusanta mutum da Ubangiji, kuma duk ruhin da yake da kusanci da Allah zaka same shi cikin nutsuwa. Babu wanda ya san inda ruhin Ι—an Adam yake sai Allah, amma galibi cututtukan da suke alaΖ™a da Ζ™waΖ™walwa da abubuwan da zuciya ka iya rayawa su na da alaΖ™a da ruhi.

Lokuta da dama sai bawa ya yi ta addu'a, ya ga kamar bata karΙ“uwa, amma tasirin Addu'a da kusanci da Allah na sanya mutum a cikin nutsuwa, ta yadda zai ga wani da irin kaddararaa koma wadda ba ta kai tasa ba, amma ba shi da nutsuwa da kwanciyar hankali.

Yanzu mu tsaya a nan, ma ci gaba wani lokacin, zan je Ι—ebo wani magani ne"

Nana ba ta yi magana ba ta ji Muhsin yana kiran sunanta, yana kiran ruwa.

Ba ta motsa ba, ta ji Nene ta tashi ta nemo ruwan ta ba shi.

Abubuwan da suka tattauna da Ƙaisar kaf suka dawo kanta. Ya gaya mata wasu abubuwa da hannalinta bai taΙ“a kai wa kai ba. Tabbas Ι—abi'ar zuciya ce jin Ζ™yashi ko hassada ko son kai wasu lokutan, hakan na nufin ruhin mutum babu lafiya kenan yana buΖ™atar attention?.


*****

Babu kowa a gidan, Mama ta ritsa Jamila, cikin matsananciyar damuwa da tashin hankali take tambayarta "Jamila ki gaya mini gaskiya, da gaske ne abubuwan da ki ke faΙ—a cewar kin shiga Ζ™ungiyar asiri, ko kema aljanun ne suka taΙ“a ki ki ke wannan soki burutsun?"

Jamila ta sunkuyar da kai. Ta taΖ™arΖ™are ta dunΖ™ule hannu ta Ι—irka wa Jamila dundu ta ce "Za ki gaya mini ko sai na danne ki da fulo na kashe ki?"


"Ki daina duka na, ba soki burutsu nake yi ba, da gaske nake Hajiya Sa'a ta saka ni a Ζ™ungiyar asiri ba tare da sanina ba. Ta Ζ™ulla alaΖ™a da ni ne, saboda na kawo mata jinin Nana ta ba wa Ζ™ungiyarsu ta yi arziki, da ban kawo jinin Nana ba ta saka ni a Ζ™ungiya. A can aka fara lalata mini rayuwa, sannan tsautsayi ya sake shiga tsakanina da Ι—anta Abba, cikin jikina da ya fita nasa ne. Shi ya sadaukar da kansa saboda kar da na bayar da kowa a Ζ™ungiya, amma haryanzu aljanun Ζ™ungiyar bibiyata suke yi, suna nema su kashe ni nima, wannan ce gaskiyar da ki ke son ji Mama, wannan ce bayan ita babu wata kuma"

Kafin Mama ta yi magana suka ji muryar Baba yana kuka ya ce "Jamila kin cuci kanki, ba ki kyautawa kanki ba, Jamila Ζ™ungiyar asiri, kuma aka nemi jinin Nana"

"Wallahi Baba ban bayar da jinin kowa ba, ba dan son raina na shiga ba, ban san ya aka yi na shiga ba."

"Rufe mini baki, ni ta wani fannin na gode Allah da na yi wa Nanan aure ma, ta bar muku gidan. Kuma ki tattara yaranki ku bar mini gida Rabi, ko Ζ™aunar ganinki bana son yi. Ku je ku da Allah" Yayi maganar yana kuka. Mama ta rasa bakin magana, tabbas ita da din ga Ζ™ara tunkuΙ—a Jamila jikin Hajiya Sa'a, ba tare da tunanin abin da ka iya faruwa ba.

Daga cikin Ι—aki Jamila na kuka take faΙ—in "Dan Allah Baba kar ka yi mini baki, ka yi haΖ™uri ka yafe mini dan Allah, ko iya haka na sha wahala, ina kan sha ma na san ba tsawon rai zan yi ba, ba za su bar ni haka ba nima kashe ni za su yi"

"Gara su kashe ki, sai ya fi mini kwanciyar hankali" Ya goge hawayensa ya fice.

Yana fita ya ci karo da Ummi, ta kalle shi ta ce "Baba fita zaka yi, ina ta sauri saboda na cim maka, ina ta kiran wayarka amma ba ta shiga"

Ya ce "Eh, fita zan yi Allah ya sa dai lafiya?"

"Lafiya Ζ™alau, mu shiga daga ciki"

Ya girgiza kai ya ce "Ba na son sake shiga cikin gidan nan"

Ummi ta ce "Amma Baba meyasa, magana ce mai muhimmanci"


Ya ce "Ki yi ta a nan kawai"


Jiki a sanyaye ta ce "Ranar da 'yan uwan mijin Nana suka zo gurinka sun je gidana" Sai Baba ya gyara tsayuwarsa, ya ce "Yaya aka yi suka san gidanki?"


Ta ce "Nima ban sani ba, amma har magana na yi da mijin Nana, ka san lokacin da suka samu matsalar nan, da ba shi da lafiya sun zauna a unguwarmu"


"Haka ne, amma nifa ban yarda da abin da suka gaya mini ba"


Baba ya nuna wa Ummi guri suka zauna, ya ce "Ummi da gaske ke kin yadda?"


Ummi ta ce "Baba ga zahiri nan kana gani, tun daga Nijar suka taho fa. Sun gaya mini ma an so gyara maka gidan nan ka ce ba ka so"


Ya ce "Bar ni Ummi, ni yanzu na shiga hankalina da al'amuran rayuwa, babu abin da ya kai kwanciyar hankali da nutsuwa daΙ—i" Nan ya bata labarin halin da suke ciki da Jamila.

Jikin Ummi ya yi sanyi sosai da sosai, ta ce "Baba idan ka kori Jamila ina za ta je yanzu? Ƙaddara ce Allah ya aiko dole a yi haΖ™uri da ita. Yanzu dai sirukanka za su ranar Lahadi idan Allah ya kaimu, sun kira ni a waya, an ce ba a samun lambarka. Mijin Nana ya sai duk wani abu da za a tarbi 'yan uwansa da za su zo. Kawowa kawai za a yi kafin su iso. Dan Allah ka kwantar da hankalinka ka bar batun Jamila mutanen nan su zo lafiya su tafi lafiya.


*****

Asal na kwance a gadon Asibiti, Hasna na gefenta ta riΖ™e hannunta, sai uban kuka take yi.


"Hasna wallahi ina son Hammad, ji nake mutuwa zan yi idan ya sake ni, ga shi haryanzu ban san a wani bugiren ya ajiye ni ba, bai sake ni ba, bai ce mini komai ba. Babanmu ne duk ya janyo mini da zigar Imam Omar."


"Asal ki yi haΖ™uri mana, kar ki illata kanki a kan sa, shi fa yanzu ya samu wata ne da yake rawar Ζ™afa a kanta, ke sai ki kashe kanki fisabilillahi"


"Hasna ba ki san me nake ji ba, wai ni ce nake da kishiya, wadda na Ι—auka Ζ™asΖ™antacciya mara galihu na shiga uku"

Hasna ta rungume ta, ta din ga rarrashinta tana yi mata nasiha.


Kwanan Yusuf huΙ—u da mutuwa, tsufan Alhaji Zailani ya sake fitowa, duk ya fita hayyacinsa ya yi wani iri. Alhaji Zailani ya zo duba shi, yana ta rarrashinsa yana ba shi haΖ™uri. Mutane jefi-jefi na shigowa su na yin gaisuwa.

Wani mutum ne ya yi sallama, suka amsa masa ya shiga, duk suka bi shi da kallo, dan babu wanda ya san shi a cikinsu.


AREWABOOKS 


Sai da suka Shukura ta biyo bayan mutumin, sannan suka rikice gaba Ι—aya suka miΖ™e, banda Alhaji Zailani. Hajiya Amina ta nufi Shukura da gudu har tana neman faΙ—uwa, ta rungume ta cikin tsananin tashin hankali da manakin ganinta ta ce "Shukura, ke ce? Ina ki ka shiga aka din ga neman ki, ina cikin jikin naki?" Wani irin tausayin Hajiya Amina ya shiga ran Shukura, ta rungume Hajiya Amina tana kuka.

Alhaji Fatuhu ma cikin matsanancin mamaki yake faΙ—in "Ikon Allah, Allah da girma da iko yake. Sannu Shukura" Alhaji Zailani dai yana zaune yana kallon su, bai ko motsa ba.

Idanun Shukura suka sauka a cikin nasa, ta ji tamkar ta yi tsalle ta shaΖ™e shi, saboda wani abu mai Ι—aci da ya tsirga mata.

Mutanen da ya sabauta rayuwarsu, duk ga su a tare da shi a zaune.

Ta ce "Mummy wai na ga rumfa a harabar gidan nan, me yake faruwa ne?"

Hajiya Amina ta ce "Ba wani abu bane ba, Shukura ina ki ka tafi?" Kan ta ba wa Hajiya Amina amsa ta durΖ™usa ta gaida Alhaji Zailani ya amsa mata cikin damuwa ya ce "Shukura kin sanya mu a tashin hankali, meyafaru wannan bawan Allah kuma waye?" 

Shukura ta numfasa ta ce "Garkuwa aka yi da ni, wannan mutumin Likita ne, shi ne wanda ya taimake ni, a gidansa na Ζ™arasa jinya"

Suka gaisa da mutumin, Alhaji Fatuhu ya din ga yi masa godiya. Hajiya Amina ta ce "Daddy, ba ka ga Shukura ba, Shukura ce fa ta dawo" Ya sauke numfashi ya ce "Na ganta"


Alhaji Fatuhu ya ce "Haba Zailani, amma atleast yakamata ka yi farincikin dawowarta ko, yarinyar da ake ta nema ba a gani ba, ta dawo kuma ka yi fuska"


Alhaji Zailani ya ce "Ni yanzu ta mutuwar Ι—ana nake yi, dan Allah ku Ζ™yale ni" A burkice Shukura ta ce "Wane Ι—an nasa?"

Tsit suka yi aka rasa mai yi mata bayani, Alhaji Zailani da kansa ya gaya mata Yusuf ne ya mutu. Shukura ta gigice cikin matsanancin tashin hankali ta hau kuka, tana faΙ—in "Shi ma ka kashe shi ko? Da ni ba a kashe ni ba sai ka kashe mini Ι—an uwa, wallahi ba zan yadda ba sai na tona maka asiri Duniya kowa ya san abin da ka ke yi" Likitan da ya rako ta, ya tashi tsam ya yi musu sallama, ya ce zai dawo.

Duk yadda suka so Shukura ta nutsu amma ta Ζ™i, ta din ga surutan da ba su gane kansu ba, kuma Alhaji Zailani ya yi mursisi ya yi shiru.


*****

Nana jikinta har wani sheΖ™i yake yi, ta yi kyau sosai da sosai, sai dai ganin Hammad ya yi mata wahala, saboda yana ta kai kawon shirin bikinsu. Yadda ta lura lamarin ba da wasa suka Ι—auke shi ba, sai gayyatar mutane suke yi. Bangaren Sultan yana ta shan suka, da Ζ™orafe-Ζ™orafe, a kan ya ci mutuncin Al'adar da aka gada daga iyaye da kakanni. Bai tsaya a iya nan ba, ya ayyana rushe majalisar Imam da ake da ita. Ya sauke Tafawa, ya sauke Sardaunanda wasu daga cikin muΖ™arrabansa, tare da cewar za a ayyana waΙ—anda za su maye guraben su, a lokacin shagalin bikin Hammad da matarsa ta Ι“oye da zai bayyana wa Duniya yanzu.

Nana a ranta take Ζ™ara jinjina ikon Allah, sai dai tana ganin lamarin bikin nasu, kamar a Ζ™asar turawa, sun yi aure sun haihu har da Ι—a, sannan za a yi shagalin bikinsu.

Gefe guda sannu a hankali take Ζ™ara yi wa kanta fashin baΖ™in, bayanan da Ƙaisar ya yi mata a game da rashin lafiya da ya ce ruhin Ι—an Adam yana yi. Kuma ga yadda ta fuskanta, babu wani magani tattare da hakan face ka yadda kana da ciwon, sannan ka tsananta addu'a Allah ya raba ka da shi. 

Tabbas ko a kankin kanta ta ga misali, ta Ζ™ara samun nutsuwa da yarda da komai lokaci ne, lokacin da take addu'a Allah ya kawo mata Ι—auki a kan matsalolinta, gani take kamar ba za su wuce ba, kamar waraka ba za ta zo ba. Ashe wannan addu'a da take yi, ke Ζ™ara samar mata da nutsuwa da kwanciyar hankali, tabbas banda haka, da irin azabar da ta ci da tuni ta amince da al'amarin bori, ko ma haukace saboda wahala da yadda ratuwarta ke tafiya kamar ba ta mutane ba.

Ta kalli yadda a yanzu ba ta aikin fari bata na baΖ™i, sai dai kawai a kawo mata ta ci, ta yi ibada ta kwanta. Sai dai ta dage da roΖ™on Allah, kar Ni'ima ta sanya ta shagala da neman kusancinta da shi.


****

Gidansu Nana, Mama ta yi mamaki, ganin Uwani ta zo ranar Asabar, wai zata kwana, da azahar ma sai ga Ummi da uban kayan cefane, har ma da Yaya Atine.

Mama ta ce "Wai lafiya duk na ganku, meke faruwa ne?"

Uwani ta ce "Kamar yaya meke faruwa? KarΙ“ar kayan auren Nana muka zo ayi da mu mana"

Ta yi saroro ta ce "Nana kuma, wace Nanan?"

"Nana wacce da wacce ku ke da ita a gidan nan? Ba dangin mijinta ne za su zo daga Agadez ba?"


Mama ta ce "Ban fa gane ba, yaushe aka ganta"


Uwani ta ce "Ke Ummi, ba ku gaya mata ba ne?"


Ummi ta ce "Ina ga Baba bai gaya mata ba, Nana tana Agadez can hannun dangin mijinta, gobe in Allah ya kaimu za su zo kawo kayan aurenta"


"Shi ne kuma dan munafunci ba a gaya mini ba? Kuma wane irin kayan aure kuma bayan wanda aka yi"

Ummi ta ce "Wallahi nima ban sani ba, sai dai sun zo za mu ji"

Mamaki ya cika Mama, domin babu wanda ya tsaya ya yi mata cikakken bayani, kamar ma ba a son ta ji abin da yake faruwa.

Washegari tun Ζ™arfe sha Ι—aya na safe, gidan abincin da aka sai Abinci a hannunsu, suka kawo abinci mai rai da lafiya cikin kuloli na alfarma. Baba ya din ga shiga yana fita, shi fatansa kawai ya ga Nana ba wai abin da za a kawo na auren ba.

Da azahar motoci biyu suka iso, Ι—aya guda Ι—aya ta alfarma Ι—aya kuma ta matafiya.

Ƙaton carfet dama aka shimfiΙ—a a tsakar gidan, aka shirya wannan uban kayan Abincin.

Manyan mutane ne, farare sol Turaki da Matawallen Agadez, sai kum Tafida, sai kuma Imam Zahradeen, Mahmoudu Sulei, sai kuma Imrana.

Kai tsaye Imarana ya nufi Baba, aikuwa Baban ya rungume shi yana fashewa da kuka. Yadda ya ga Imarana a nutse cikin kamala kawai ya sanya shi mantawa da tarin baΖ™in cikin da yake ciki, kuma sai a lokacin ya gazgata mutanen nan da gaske suke.

Imrana ya ce "Baba kar ka yi magana, ka ga mu na tare da baΖ™i" Baba dai kai kawai ya iya jinjinawa yana sake riΖ™e shi, kamar zai sake guduwa.

Ta taga Mama take Ι—an leΖ™owa, ta saki baki tana kallon ikon Allah, suturar jikin buzayen kawai ya fallasa cewar a cikin rufin asiri suke, ba Ζ™ananan mutane ba ne.

Bayan Baba ya Ι—an nutsu, duk sun nemi guri sun zauna, suka gaggaisa. Imam Zahradeen ya ce "To Baba mun sake dawowa, mun zo mu cika alΖ™awari da muka Ι—auka, waΙ—anan 'yan uwan mahaifinmu ne, ga shi muka zo tare da su"


Suka sake gaisawa Matawalle ya ce "Ɗan uwa, Sultan ne ya aiko mu wakilci mussaman, mu zo mu yi godiya, mu jinjina wa namijin Ζ™oΖ™arin da ka yi, na aura wa Ι—anmu 'yarka ba tare da sanin waye shi ba. HaΖ™iΖ™a mu yarinyarka alkhairi ga ahalinmu da Ζ™asar Agadez baki Ι—aya ma. A madadin Sultan Jalaludeen ya ce "Mu ce maka mun gode, mun sake gode wa. Mu na tafe da dukiyar aurenta, kamar yadda ake yi wa kowace 'ya da ake yi wa kabilar buzaye. Sannan ya ce ita wannan 'ya yanzu ta zama tasa, yana kuma gayyatarka da duk wani wanda yake sha'awar zuwa, gagarumin shagalin bikin yaran nasa. Hammad da kuma Gimbiya Asma'u."

Baba ya numfasa yana ganin abin kamar a mafarki, ya ce "To ai tun da dai da aure a tsakaninsu, a ganina da an haΖ™ura da bikin shagalin nan"


Turaki ya ce "To ai Ι—an gidan mulki ne, abu ne aka yi shi da babu wanda ya sani, kuma ya saΙ“a wa al'adarmu, wands a dalilinta an soke al'adar ma gaba Ι—aya, dan haka dole a yi shagalin bikin domin nuna wa Duniya ita. Saboda gudun abin da ka iya biyo baya, saboda mutum ne mai mulki mai faΙ—a a ji a garin Agadez. Dan haka nan da mako guda za a yi bikin, duk adadin waΙ—anda za su je, za a Ι—auki nauyinsu tun daga Ζ™asa Nigeria har can, domin yin wannan shagali" Daga cikin Ι—akin Uwani ta rafsa wata irin guΙ—a mai Ι—an karen sauti tana faΙ—in "Alhamdillah" har sai da hankalinsu ya koma kan inda sautin guΙ—ar ya fito. Gaddafi dai daga baya ya shigo, suka yi ido huΙ—u da Imrana. Imarana ya tashi ya nufe shi, rungume juna suka yi. Gaddafi ya ce "Imrana, wannan karon nisan kiwon naka har ya kai tsawon wannan lokacin?"

Imrana ya ce "Wani nisan kiwo, kame ni a kayi, a ka kai ni makarantar dole, abubuwa ne da yawa suka faru" Ai tuni suka manta da wani batun ba sa jituwa, saboda girman alaΖ™ar jini, suka din ga murnar ganin junansu.

Daga nan aka shiga shigo da kayan auren Nana, sai da Baba ya saki baki, a ransa ya fara tunanin anya mutanen nan su na da hankali kuwa. Saboda shi yanzu al'amuran abin duniya tsoro suke ba shi.

Domin karrama abin da su Baba suke da shi, su Turaki suka ci abincin da aka kawo musu.

Aka gabatar musu da 'yan uwan Nana, Yaya Atine sai rawar kai take, tana nanata musu ita yayar Baban Nana ce uwa Ι—aya uba Ι—aya, ita ta saki Nono ya kama.

Haushi sai da ya kama Imran, Gaddafi ma ya tsuke fuska ya ce "Matar nan duk abin da aka haΙ—a da ita sai ta yi hauka"

Imrana ya ce "Har da wani ita ta saki nono ya kama, kamar nonon akuya, ko kunya ba ta ji ba, kamar ba da ita aka dinga muzguna wa Nana ba"

Ta din ga rawar Ζ™afa tana jan su da hira, sai da ta ba wa kowa haushi.

Da suka tashi tafiya kuwa, Haka Ummi ta shiga maΖ™wabta ta karΙ“o kayan da aka shirya, na tukuci da za su tafi da shi, dan kar ma wani ya sanya zalama. Kaji, da kayan snacks masu yawan gaske, da dabino kusan kwano biyar da tasoshin turare.

Turaki ya ce karramawar da aka yi musu ta isa, ba za su karΙ“i komai ba, ai Nana 'yar Sultan ce.

Gaddafi ya ce idan ba su karΙ“a ba, ba za su ji daΙ—i ba.

Baba ya ga za su tafi ya yi musu godiya sannan ya ce "To ba za a kawo mini Nanan ba, ita yaushe zan ganta?"

Imam Zahradeen ya ce "Zaka ganta Baba, sai kun zo Agadez biki, za ku ganta in sha Allah, ga Imrana mun kawo maka har gida ai"

Jiki a sanyaye ya ce "Nanan dai nake son gani, amma shikenan mun gode sosai da sosai"

Imrana ya ce "Tun da ni baya son ganina, bari na biku mu koma"

Cikin sauri Baba ya ce "A'a Imrana, kai ma na yi murna da ganinka"

Suka yi murmushi baki Ι—aya, su Mahmoudu ya ce "Duk wanda za su je, a kira a gaya mana adadin mutane, za a Ι—auki nauyin zuwansu da dawowar su, sannan kuma idan an gama ganin kayan da su za a tafi. Daga nan suka hau mota suka tafi.

Da suka koma gida, aka fara sauke kaya ana bubbuΙ—ewa, Baba komawa ya yi gefe ya fashe da kuka, domin hatta shi akwati guda aka yi masa.

Uwani ta ce "Isa meye haka kuma, ai abin farinciki ne, ka daina kukan nan dan Allah"

MaΖ™wabta ma ba a bar su a baya ba, suka din ga shigowa, sun Ι—auka ko kayan auren Jamila aka kawo ko na Suwaiba. Mama baΖ™in ciki ya cika mata ciki, ganin yadda nata 'ya'yan duk suka zama abin da suka zama, babu wani na kirki, ta din ga cizon yatsan ina ma nata 'ya'yan ta saka aka aura wa buzun ba Nana ba.

Uwani ta ce "Allah ba azzalumin sarki ba ne, Nana ta sha wahala a rayuwa, ta yi Ι—awainiya da yaron nan, da jikinta da Ζ™arfinta. Allah ya yi tana da rabon jin daΙ—i tun a Duniya"


Ummi ta ce "Wallahi Uwani, Nana ta sha wahala, da shi sosai da sosai, Allah ya nuna ikonsa. Kuma shi ma ya yi halacci"


Uwani ta ce "Ba kaΙ—an ba, Allah dai ya ba su zaman lafiya"


Imran ya ce "Dan ma ba ku ji wahalar da ta sha a Niger Ι—in nan ba, da yawon nemansa" Nan Imrana ya gaya musu abin da ya sani. Yaya Atine ta ja baki ta yi shiru.

Uwani ta ce "To Isa, ina fatan ya zame maka izina, akan abubuwan da ka aikata wa yarinyar nan. Kuma ya zama dole a kira mahaifiyarta a sanar da ita komai, kuma a yi shirin tafiya da ita gurin bikin nan, dan ba za ka ci gaba da wannan jahilcin ba"


Imrana ya ce "To ai a Bauchi muka kwana, an je har gida an kai wa Umma lefen ta gani, an yi mata godiya sannan muka taho nan yau"


Uwani ta ce "Ikon Allah, haihuwa mai rana" Duk yadda Mama ta so Ι“oye Ι“akin cikinta abu ya ci tura.


Can gidan Umman su Nana, ta yi sujuda babu adadi na tsantsar murna da farinciki. Iliyasu kansa bakinsa ya Ζ™i rufuwa, amma ko kallo bai ishe ta ba. Dan ta wani fannin guduwar Nana, sauΖ™i ya sama mata, dan tun da ya san ya yi sanadin Ι“atan Nana, duk abin da take yi masa baya cewa uffan.


"Mai Jidda kin ga ikon Allah ko? Ashe ta wani fannin gara da Nana ta je neman mijin nata, da tana zaune a nan babu lallai su haΙ—u. Allah sarki rayuwa"


Maijidda ji ta yi kamar ta make shi, ya ga abin Duniya, jikinsa sai tsuma yake yi.


*****

Asal na zaune ta damΖ™e wayarta iya Ζ™arfinta, saboda ganin hoton katin gayyatar bikin taron bikin Hammad da matarsa, da kuma naΙ—e-naΙ—en sarauta.

Hasna ta ce "Asal, ki ajiye wayar nan ki samu ki saka wani abu a cikinki mana" Ta girgiza kai hawaye na gangarowa daga idanunta.

Ji suka yi an buΙ—e Ζ™ofar Ι—akin, suka Ι—aga baki Ι—aya. Hammad ne ya shigo, jikinsa sanye da shiga ta alfarma. Ƙamshin turarensa ya mamaye Ι—akin baki Ι—aya.

Hasna ta risuna cikin girmamawa tana gaishe shi. Asal kuwa ta sunkuyar da kanta, zuciyarta na tsananta bugawa cike da tsoro da fargaba, saboda ba ta taΙ“a tsammanin ganinsa ba. Kuma ba ta san me yake tafe da shi ba. Da yatsunsa biyu ya yi wa Hasna alamar ta fita ta ba su guri.


Ayshercool 

08081012143

100

LITTAFIN KUƊI NE, A BIYA KUƊIN KARATU KAN A KARANTA.

0069685771

AISHA ADAM STANBIC 

08081012143


Asal ta sunkuyar da kanta Ζ™asa, ji take yi tamkar Ζ™asa ta tsage ta shige, saboda matsananciyar kunyarsa da take ji.

Ya Ζ™arasa ya zauna a gefenta, ya ce "Me ya same ki haka?" Ba ta Ι—ago ba, ta girgiza masa kai.

Shiru ya wanzu tsakanin su, babu wanda ya yi magana. Ya ce "Tun da ba za ki yi magana ba shikenan" Har ya yinΖ™ura, ta riΖ™e rigarsa ta ce "Sakina ka zo ka yi ko?"


"A'a, dama ai ni ban kore ki ba, na dai ba ki zaΙ“in zama da ni ne, amma na ga kamar ke da mahaifinki, kun fi gamsuwa da na sauwwaΖ™e miki."


"Dan Allah Hammad ka yi haΖ™uri ka yafe mini, na san laifukana ba za su Ζ™irgu ba, sai a wannan karon Allah ya tona asirina"


Yayi murmushi ya ce "Ba zan yi miki dole ki zauna da ni ba, muddin kin san zuciyarki haryanzu tana son Omar" Wata irin Ι—agowa Asal ta yi a razane jin abin da ya ce.

"Hmm Asal kenan, duk tsawon zaman da na yi da ke, babu abin da ban sani ba, kar ma ki yi zaton ko wani ne ya gaya mini. Saka mini magani da duk wani nau'i na Ζ™oΖ™arin illata ni da ki ke yi, duk na sani, kuma ina kallonki. Ba domin babu yadda zan yi da ke ba, sai domin ina jin tausayinki, kuma ke Ζ™anwata ce"

Zamowa ta yi Ζ™asa cikin kuka ta riΖ™e rigarsa ta ce "Wallahi na yi nadama Hammad, na san ko ba ka ce mini komai ba, Hakkinka ba zai bar ni ba. Amma ba laifina ba ne ba, ka sani dan Allah ka yi haΖ™uri ka yafe mini, kar ka sake ni. Wallahi ina sonka"

"Dama ai ban ce zan sake ki ba, mahaifinki ne ya nemi hakan, kuma nima na so aikatawa amma na duba idan na yi haka, ba ki da wata kyakykywar makoma, bayan gama lalata rayuwarki da aka yi. Kuma ba na son asirinki ya ci gaba da tonuwa a idon Duniya. Uwa uba Nana tana ta yi mini magiyar kar na rabu da ke. Na so samarwa kaina cikakkiyar nutsuwa da rayuwa da wadda bata harin komai daga gare ni sai alkhairi, amma ban san me Allah zai yi mini a sanadin yafe miki ba. Asal zaki koma Ι—akinki bisa sharaΙ—i, dan ta ni ko yanzu ki ci gaba da duk abin da ki ke yi mini, bai dame ni ba; amma muddin ki ka yi wani na yinΖ™urin cutar mini da matata ko Ι—ana, wallahi sai na Ι—aure ki, Ι—aurin rai da rai ma kuwa. Ba zan taΙ“a yin wasa da duk wani abu da ya shafe su ba, dan haka zaki amince da babu ruwanki da duk wani abu da ya shafe su, balle a zo ga batun cutarwa"

Wani abu raΙ—aΙ—i ya tsirga wa Asal,  wai ita ake gindaya wa sharaΙ—i a kan Nana. Sai dai babu yadda ta iya ta jinjina masa kai ta ce "Na amince"


Ya ce "Ki yi tunani da kyau, kar ki saΙ“a abin da ki ka ce daga baya, na Ι—auki mataki ki ji haushina"


"Na tabattar da na amince"


Ya ce "To shikenan, tashi" Sai dai Ζ™afafuwanta suka yi mata nauyi, ta kasa tashi, saboda haryanzu tana jin nauyinsa, kenan har soyayyar da suka yi da Omar ya sani, amma ya Ζ™yale ta a gidansa.

Babu tsammani ta ji ya saka hannu ya Ι—ago ta tsaye. Ya ce "Na saka an Ι—an yi mana gyara a gida, zan canza miki komai. Har cikin zuciyata na yafe miki, na san wasu abubuwan ba laifinki ba ne, kuma ko dan kusanto da Nana gare ni da ki ke yi yakamata na yafe miki. Allah ya sanya kin yi tabbataccen tuba" A duk lokacin da ya ambaci Nana, sai ta ji baΖ™in ciki kamar ya halakka ta. Ya sumbaci goshinta, ya mayar da ita kan gadon ya zaunar da ita, ya ce "Allah ya baki lafiya" Daga haka ya juya ya fita. Wani irin kuka ta saka, gaba Ι—aya alamu sun nuna, a yanzu baya ganin mutuncin komai idan ba na matarsa da Ι—ansa ba. Ƙarara a idonsa da mu'alarsa ake iya karanto tsagwaron son da yake yi wa Nana.


Duk da yadda Sultan ya yi watsi da Imam Zahradeen, amma bai yi zuciya ba ya yi uwa ya yi makarΙ“iya a kan shirin gudanar da bikin Ι—an uwansa.

Tuni baΖ™i suka fara hallara, aka Ι—auke Nana daga cikin gidan Sultan, zuwa estate Ι—in da yake mallakin masarauta, da galibi ake saukar baΖ™i a can. Estate Ι—in da sunan Hammad aka saka masa, wanda a nan ta fara zama tare da Asal da Ζ™awayenta a Ι—aya daga cikin gidajen.

Nana ba ta yi zato ba, ba ta yi tsammani ba, kawai ta tarar da mahaifiyarta da Ζ™annenta su Walida.

Gaba Ι—aya Nana ta yi wata irin rikicewa, jikinta ya hau tsuma.

Maijidda da kanta ta tashi ta nufi Nana cikin farinciki. Nana ta faΙ—a jikinta ta rirriΖ™e ta, cikin dashewar murya ta ce "Um.umm.Umma! Umma ki yi haΖ™uri dan Allah"

Maijidda ta ce "Shhh, kar ma ki kawo wannan zancen, ni yanzu lokacin farinciki ne da murna, dan haka kuka ya Ζ™are. Abin arziki da farinciki ne ya tara mu. Ni dai na gode wa Allah da ya sanya ina da rabon sake ganinku cikin kwanciyar hankali da kuma Ζ™oshin lafiya"


"Umma idan ba ku yafe mini ba, hakkinku ba zai bar ni ba, na yi wauta na yi shirme, na bar ku da fargaba da kuma zullumi."


"Duk ya wuce, ya zama tarihi, Alhamdillah tun da Allah ya amsa addu'armu ya haΙ—a mu cikin aminci da kwanciyar hankali." Tuni idanun Nana suka rine zuwa jawur, ta Ζ™anΖ™ame Maijidda duk da babu wata shaΖ™uwar a zo a gani a tsakaninsu, amma wani irin abu ne mara misaltuwa Nana take jin sa a zuciyarta game da Umman nata.

Ta Ζ™waΖ™ume ta, ta Ζ™i sakinta ta kwanta lamo a jikinta.

Maijidda ta ce "Ai mijin naki ma ya zo mun gaisa, Ubangiji Allah ya sanya alkhairi ya baku zaman lafiya. Na ce a kawo mini jikin nawa na gan shi, aka ce mini yana Ζ™arΖ™ashin kulawa ta musamman, zan gan shi amma ba yanzu ba" Nana dai babu baki, ba ta iya cewa komai ba. Sai yanzu take Ζ™ara jinjina girman laifin da ta aikata. Ta tuna lokacin da aka raba ta da Muhsin na Ι—an kwanaki tashin hankalin da ta shiga, ita kuma ta bar gida kusan shekara uku ba ta waiwaya ba, kuma still ana rarrashinta.

Nene ce ta zo, tare da hadimai, da tarin kayan abinci, tare da su Anty Fati 'yan uwan Mai jidda da ta su motar isowarta kenan.

Babu abin da Nana take yi sai gode wa Allah, sai murna suke yi da ganinta, tare da taya ta murnar matsayin da Allah ya Ι—aukaka ta ya kai ta.

Nana ta ce "Nene ga Ummana, Umma ga Mamana ta Niger ni yanzu a iyaye bayan ke, ba ni da wata uwa da ta wuce Nene. A hannunta na haifi Muhsin, ban san ya zan misalta miki riΖ™on da Nene ta yi mana ba Umma. Ki yi mata godiya."


Nene ta ce "Dama idan uwa ta yi wa Ι—anta abu, sai an yi mata godiya ai hakkinta ne ta yi"


Ta miΖ™a wa Maijidda hannu suka gaisa, su Anty Fati suka hau yi mata godiya. Nene ta ce "Ni ina Ζ™aunar Nana saboda Allah, dan haka duk abin da na yi mata ina jin kamar na yi wa Ι—an cikina ne" 


Sam ranar Nana bata rintsa ba, ji take yi tamkar mai Jidda ta mayar da ita cikinta, gani take idan ta yi bacci zai zamana abin da yake faruwa mafarki ne.


Aka din ga Ι—awainiya da su, Maijidda da ta taho da 'yan kayanta, na Ζ™ara gyara Nana, yadda ta ga Nene na faΙ—i tashi a kan Nana, sai ta kasa komai.

Washegari su Imrana suka iso, mota uku ta 'yan Kano, hatta Suwaiba da ba ta da cikakken hankali, da Jamila da babu cikakkiyar lafiya, haka Mama ta tarkata ta taho da su. Saboda a yi komai a kan idonta.

Ana cewa ga motar su Baba can, Nana ta zabura za ta yi waje, Nene ta ce "Nana ya haka? Dole fa ki canza yadda ki ke gudanar da al'amuranki, da da kuma yanzu ba Ι—aya ba ne ba. Ki bari za su shigo ai.

Ummi ce ta fara shigowa, suka rumgume juna ita da Nana suka fashe da kuka. Su Uwani ma suka shigo gaba Ι—aya sai falon ya kaure da koke-koke.

Uwani da Ummi kamar su haΙ—iye Nana, Uwani ta ce "Ummi ke ce haka? Kin ga wani irin kyau da ki ka yi?" Nana ta yi murmushi.

Ta riΖ™o hannun Jamila cike da farinciki, duk Ζ™asan zuciyarta cike yak da mamakin, yadda ta ga Jamila ta yi wata uwar rama mai ban tsoro.

Duk da ba miji Ι—aya suke aure ba yanzu sai da Mama ta yi turus ganin Mai Jidda, ba ta taΙ“a zaton za ta ganta gurin bikin Nana ba. Ta ganta tsaf da ita cikin nutsuwa.

Uwani ta zauna kusa da Maijidda da su Anty Fati, suna hirar yaushe gamo.

Nana dai kasa hirar ma tayi da su, gaba Ι—aya kunyarsu ta hana ta cikakken sukunin haΙ—a ido da su.

Bayan sallar isha'i, barori suka nemi da a yi shiru, Imam Hammad zai shigo. Aikuwa kamar ruwa ya cinye kowa aka yi shiru.

Shi ne ya shigo tare da Mahmoudu, da hadaimai biyu, suka tsaya a bakin Ζ™ofa shi kuma ya shiga. Yana ganin Uwani ya saki murmushi, ya tafi gabanta ya durΖ™usa.

Ta ce "Ɗan nan, dama babban mutum ne kai? Ka gane ni?"

Ya ce "Ɗa ba zai manta uwa ba ai, kuma Ι—an halak baya manta alkhairi. Ba zan manta da ke ba, Allah ya saka da alkhairi"

Ta ce "A'a ai Ι—a baya yi wa uwa godiya, mun same ku lafiya?"

Ya ce "Alhamdillah" Ya kalli Ummi da take ta murmushi ita ma, ya ce "Babbar Yaya, fatan kun sauka lafiya, kuma kun ji daΙ—in Ζ™asar tamu"


Ummi ta ce "Alhamdillah, mun same ku lafiya?"


Ya ce "Lafiya Ζ™alau, ina sake amfani da wannan damar, gurin sake baku haΖ™uri, da abin da Asmy ta yi, duk laifin a kaina yake, nine mai laifin amma ina bayar da haΖ™uri dan Allah a yafe mana. Sannan ina sake yi muku godiya sosai da sosai, Sultan ma ya ce a gaishe ku"

WaΙ—anda ba su san shi ba, suka din ga yaba kyawu da kamalar Hammad.

Daga nan ya nemi zai tafi da Nana, za ta je gurin su Baba inda suka sauka su gaisa, sannan a dawo da ita.


Su na shiga mota, ya kwanta a jikin Nana yana sauke numfashi ya ce "Da na yi niyyar idan aka gama taron nan, ki yi kwana biyu ki huta, sannan ki tare amma gaskiya yanzu na fasa, ji nake kamar na gudu da ke"


Ta marairaice ta ce "Dan Allah ka bari a kwana biyun"


"Ba zan iya ba, ana tashi kawai a kai mini ke gida, gidanki ya kammala komai an saka mana, mukaΙ—ai muka rage mu shiga" Yayi maganar yana sumbatar bakinta.

"Ya naga jikinki ya yi sanyi ne, kamar wata amarya?"


"Wallahi Sayyid tsoro nake ji, ban san da wani idon zan kalli Baba ba, ban kyauta ba abin da na yi ko kaΙ—an"


"A'a ki kwantar da hankalinki, Baba fa tun kafin su zo, na tura an ba shi haΖ™uri, yau da suka zo an kai shi har gurin Sultan, ya ba shi haΖ™uri, nima na je na same shi, shi duk damuwarsa ma ya ganki ne. Babu wani abu in sha Allah"

Haka suka Ζ™arasa jikin Nana a sanyaye duk a tsorace take.

A wani sashi na gidan Sultan, aka sauki su Baba, tare da Imrana da Gaddafi.

Nana ta tsaya cak, ta sanya hannayenta, ta toshe bakinta, wani irin kuka mai Ζ™arfin gaske yana kufce mata.

Gaddafi ne ya taso ya riΖ™o hannunta, ya Ζ™arasa gaban Baba da ita. Sai da Sayyid ya ji wani iri, duk da kasancewar Gaddafin yayanta ne.

Nana tun da ta buΙ—e ido, Baba bai taΙ“a rungume ta ba sai yau, tana kuka yana kuka. Da kyar maganarta take fita ta ce "Baba ka yi haΖ™uri, ka yi haΖ™uri dan Allah ka yafe mini. Baba na yi wauta da rashin hankali Baba ka yi haΖ™uri na san na sanya ku a tashin hankali"


Sai da Baba ya yi kuka mai isar sa sannan ya iya furta "Babu komai Nana, ni dai na gode wa Allah tun da kina nan cikin Ζ™oshin lafiya, Alhamdillah, Alhamdillah na gode wa Allah".


Haka ta rungume Nasiru ma tana kukan farinciki, ta Ζ™ara tabattar da duk lalacewar naka naka ne, ta shiga farinciki mara misaltuwa da ganin ahalinta a tare da ita.


Har Alhaji Fatuhu ya tafi ranar, Shukura ba ta yi musu bayanin komai ba, sai dai ta kaΙ—u ta shiga tashin hankali da mutuwar Ι—an uwanta. Hajiya Amina ma babu rarrashin da ba ta yi mata ba, amma ba ta yi mata bayanin komai ba.

Washegari da rana, sai ga Yusra tare da Sagir da Hajiya Halima da Siyama. Hajiya Amina ta karΙ“e su hannu bibbiyu. Ta ce "Sagir na zata zan ganka tun a jiya, na kira gidanku na sanar da Shukura ta dawo. Ya ce "Mummy bana gari ne, ina can Abuja fa, Yusra babu lafiya"


"Wai Yusra haihuwa ki ka yi ne?" Mummy ta yi maganar tana kallon ta.


Shukura ce ta fito, Yusra ta ajiye wa Sagir yaron, ta nufi Shukura ta ce "'yar uwa babu abin da ya same ki ko?"


Shukura ta jinjina kai ta riΖ™e hannun Yusra ta ce "Yusra na gode sosai da sosai, na gode"

Yusra ta rungume ta tana rarrashinta.

Shukura ta ce "Mummy, ki kira Daddy a yi komai a kan idonsa, na kira Baban Rauda ma a wayarki"

Cikin rashin fahimta ta ce "To wai meyafaru?"

Shukura ta ce "Shi zan yi bayani"

Tana rufe bakinta, Alhaji Zailani ya fito, ya tsaya yana kallon Yusra da kuma Shukura.

Yayi murmushi ya ce "Har gangami ki ka yi na tona mini asiri Shukura? Shikenan, mu jira zuwan Fatuhun, ai tun da ki ka dawo na san za a yi hakan."


Gaba Ι—aya suka tsaya su na kallon Shukura.


Hajiya Amina ta ce "Shukura mene wai? Alhaji ka yi mini bayani mana"


Su na cikin maganar, Alhaji Fatuhu ya Ζ™araso gidan, ya tarar da su a tsaye a falo. Ya ce "Hajiya Amina lafiya kuwa? Shukura ta kira ni a waya ta ce lallai na zo"


Hajiya Amina ta ce "Wallahi nima ban san abin da yake faruwa ba, shi ma na ji yana zancen za a tona masa asiri na kasa ganewa"


Ya kalli Shukura ya ce "Shukura, mene ne ki yi mana bayani"


Shukura ta yi shiru tana kallon Alhaji Zailani, amma ta kasa magana, kawai ta fashe da kuka.

Yusra ta ce "Ina gida wayar Baban Haidar ta lalace, ya saka layinsa a wayata, Shukura ta kira ta ce tana wani Asibiti a can wata Ζ™aramar hukuma a Kano. Wai garkuwa aka da ita ta kuΙ“uta, wata mata ta tsince ta, ta kaita Asibiti. Na ce ba zan tafi ba sai tare da ita, da magariba wasu suka zo Asibitin su na nemanta za su kashe ta. Shi ne na tafi da jaririn, ni ban ma san yadda aka yi ba na ganni a gidanmu na Abuja daga Asibitin. Amma babanta ne ya saka a sace ta"

Gaba Ι—aya suka kalli Yusra cike da mamaki.

Alhaji Fatuhu ya ce "Kin san me ki ke faΙ—a kuwa?"

Yusra ta ce "Na sani mana, ba fa Ζ™arya nake yi ba. Ai ita da kunya ta ce ga abin da ya yi, amma ni dai ku yi haΖ™uri na faΙ—a"


Alhaji Fatuhu ya ce "Amma kamar an ce ai ba ta da cikakkiyar lafiyar Ζ™waΖ™walwa, wataΖ™ila...


Shukura cikin kuka ta ce "Yusra ba Ζ™arya take yi ba, Daddy ne ya sanya a sace ni, saboda ina bin diddigin yadda aka ce jaririna ya mutu, kuma saboda ya bayar da jaririna a matsayin sadaukarwarsa ta shekara a Ζ™ungiyar asiri. Na so rufa masa asiri na yi shiru, amma ba zan iya ba, mussaman idan ina kallon mutanen da ya zalunta, da yadda yake ganin bayan rayuwarsu. Ni Yusuf ma ina kyautata zaton shi ne ya bayar da shi a kungiyar"


Cikin tsawa Alhaji Fatuhu ya ce "Shut up Shukura, mahaifinki ne fa, ki ke yi masa wannan tonon sililin a gaban mutane. Kuma tayaya za ki haΙ—a kai da abokiyar zaman ki, ku yi masa wannan Ζ™azafin?"


Shukura ta ce "Ko zan yi wa kowa Ζ™azafi yaya za a yi na yi masa? Bana jin komai ko a gaban waye zan tona masa asiri, iyaka dai a yi mini gori wataran hakan ba zai dame ni ba. Ɗana ya Ι—auka ya bayar aka yi tsafi da shi aka yi maka asirin da ka rasa komai ka yi rashin lafiyar nan. Suka haΙ—a baki da Doctor Sharif aka yi mini tiyata aka ba su jaririna.

Tayaya zan iya rufa wa mutumin da ya yi mini wannan zaluncin asiri?. Nan Shukura ta din ga faΙ—ar miyagun ayyukan da Alhaji Zailani ya gaya mata ya yi da bakinsa.

Wani irin bugu zuciyar Hajiya Amina ta yi, take ta ji jikinta ya yi wani irin sanyi, tamkar an zare mata lakar jikinta. Wani irin gumi ya fara tsatsafo mata ko ta ina.

Alhaji Fatuhu bakinsa na rawa ya ce "Zailani, abin da yarinyar nan ta faΙ—a haka ne, ko kuma Ι—imuwa ta shiga ne?" Yayi shiru bai yi magana ba, sai tsare su da idanu da ya yi.

Sagir ya Ι—an daddana wayarsa, mutumin nan da suka zo tare da Shukura ne ya shigo, tare da wasu Ζ™arti majiya Ζ™arfi su uku.

Bayan ya yi musu sallama, ya yi musu bayanin shi jami'in tsaro ne, kuma Likita, shi ne ya haΙ—u da Shukura a lokacin da nutanen da Alhaji Zailani ya tura, suka gano ta, suka yi yinΖ™urin kashe ta, ya yi amfani da Ζ™warewar aiki, ya kama mutum biyu daga ciki. Kuma sun tabattar da Alhaji Zailani ne ya saka su wannan aiki.

Bakin Hajiya Amina na rawa, da kyar ta ce "Me na yi maka haka Zailani?" Daga nan ba ta sake cewa komai ba, ta silale ta faΙ—i Ζ™asa.


Alhaji Fatuhu shi ma kasa ko Ζ™waΖ™Ζ™waran motsi ya yi, ji yayi tamkar numfashinsa zai Ι—auke. Sai yanzu wasu abubuwan da suka faru suke dawo masa, amma bai taΙ“a zaton Alhaji Zailani zai iya aikata masa wannan mugun abun ba.

Kafin a bar gidan da shi, ya tsaya ya kalli Alhaji Fatuhu ya ce "Kar ka yi mamakin abin da ya faru, domin ban taΙ“a sonka ba, duba da yadda ka fini ta ko ina, kuma ban yi nadamar abin da na aikata maka ba. Duk abubuwan nan da na yi babu wata cikakkiyar shaida da za a iya kama ni da laifi da ita, balle a hukunta ni. Sai shaidar sace 'yata da na yi, wannan ma na san yadda zan fitar da kaina.

Sai dai dole mu yi mutuwar kasko, domin ba ni kaΙ—ai ba ne a Ζ™ungiyar asirin, har da yayarka, da ta sadaukar naka da Ι—anka da ya mutu, dan haka ko wani mataki zaka Ι—auka a kaina, sai ka haΙ—a da ni da ita, gara ni abokinka ne kawai, ita kuma 'yar uwakka ce!".


*****


Nana ta so sanya kayanta na Nigeria, a gurin bikin nan, Hammad ya ce shigar buzaye za a yi mata. Ta sha gyara ta yi kyau. Agadez ta Ι—inke da tarin jama'a.

Tun daga kan gashin kanta, lungu da saΖ™o na jikinta, babu inda bai ga gyara ba.

Sai da ta tuna da lokacin bikinsu na farko, yadda aka kawo mata shadda ta alfarma. Yanzun ma haka ne, rigar ta sha aiki ita kanta shaddar Ζ™amshi take yi na musamman.

Babu babban abin da ya razana Nana, irin sarΖ™ar da aka saka mata ta gold da ta sauka har cikinta. Ta kalli mai kwalliyar ta ce "Ni gaskiya a cire mini wannan sarΖ™ar ba zan iya saka wa ba, fariyar ta yi yawa"

Matar ta ce "Ba fariya ba ce shugabata, ado ne na mutanen Ζ™asar nan, dan Allah kar ki ji wani abu, ai ana kammalawa dole za ki cire ne" Sai da aka yi ta fama da Nana sannan ta haΖ™ura, gani take yi kamar ba ta hanyar da ya dace ta yi wa Allah godiya ba kenan, da wannan fariyar.

Ta din ga istigfari, da fatan Allah ya sanya kar hakan ya sanya ta ji wani abu na girman kai ko tinΖ™aho.


Ƙaton Ι—akin taro ne, ta kowane Ι“angare mutane ne, daban daban, 'ya'yan sarakuna da manyan mutane gurinsu daban, Ι“angaren danginta daban, abin har ya fara bata tsoro ta ji kanta yana juyawa. Ba iya wannan ba, shi kansa Muhsin da kusan kwana biyar rabon ta da shi, an yi masa ado, kayansa iri Ι—aya da na mahaifinsa.

Aka buΙ—e taro da addu'a, da karanto jadawalin abin da za a gudanar a gurin.

Aka fara da sake tabattar da rushe majalisar Imam, da zimmar duk wani Ι—an sarki Imam ne, amma babu majalisarsu, da kuma cewar lallai su za su gaji sarauta.

Aka sanar da sauke wasu daga manyan makusantan Sultan, ba tare da faΙ—ar cikakken dalili ba, sai cewa saboda za a yi gyare-gyare ne a masarautar Agadez.

Aka gabatar da roΖ™o ga gwamnatin tarayya, a kan ta bayar da tallafi su haΙ—u da masarautar Agadez, a gyara gidan tarihin nan, a faΙ—aΙ—a shi a Ζ™awata shi, ya zamana gurin buΙ—e idanu sosai ga baΖ™i. A kuma gina Hotel a ciki ko wajen gidan, saboda samar da masauki ga baΖ™in da za su din ga zuwa yawon buΙ—e ido.

Daga nan aka sake jaddada dokar, halattawa Ζ™abilar buzaye auren duk matar da suke so, daga kowace Ζ™asa.

Aka yi ta kaΙ—e-kaΙ—e ana shiga ana fita da abinci kala-kala.

Daga bisani aka yi wa Imam Hammad naΙ—i aka ba shi sarautar Sardaunan Agadez, yayin da Imam Zahradeen aka ba shi sarautar Tafawa.

Sai kuma abin da ba a taΙ“a tsammani ba, Sultan ya yi wa Mahmoudu Sarautar Tafeedan Agadez, tare da ba shi auren Ι—aya daga cikin 'ya'yansa, wanda za a gudanar a nan take. Gigicewa Mahmoudu ya yi, Nana ma ta waro idanu saboda mamaki. Hammad kuwa ya sani, tare da Sultan suka shirya komai. Kuma ya tabattar Ζ™anwar tasa ta amince da auren Mahmoudu, ita ma tata mahaifiyar rasuwa ta yi, ita ce 'yar autarsu. Dama ba shi da matsala da Mahmoudu, kuma ya fuskanci su na shiri sosai, shiyasa ya nemi alfarmar Sultan ya yi wannan haΙ—in.

Aka fito da Muhsin, aka gabatar da shi, a matsayin Ι—an Hammad, da Duniya ba ta san da shi ba, kuma a ka yi masa naΙ—in Imam kuma Yariman Agadez mafi Ζ™arancin shekaru a tarihin Agadez, haka zalika kuma Imam da mahaifiyarsa ta sauya tarihin Agadez baki Ι—aya. Nan manyan mutane suka din ga bajinta, da gwangwaje Muhsin da tsadaddun kyaututtuka na ban mamaki. Har sai da Nana ta kalli abin a matsayin Almubazzaranci.

Daga bisani aka din ga koΙ—a Nana ana yi mata kirari, ita ma aka gabatar da ita, a matsayin matar sabon Sardaunan Agadez, kuma mahaifiyar Yarima.

Nana gaba Ι—aya sai ta rikice, kawai ta fashe da kuka.

Aka bata mic a kan ta yi magana, amma ta kasa Ζ™arshe kawai ta yi sujudu shukur a gurin, jikinta na tsuma tana wani irin kuka. Hammad ne ya din ga rarrashin ta, yana ankarar da ita ranar farin ciki ce a gare su. Ba a bar uwar Yarima haka ba, sai da ta samu sarautar Garkuwar matan Ζ™asar Agadez.

Haka matan manyan mutanen nan, suka din ga guΙ—a, suna yi mata kyaututtuka.

Hammad ya yi godiya ga tarin al'ummar da suka halarci taron, tare da fatan Ι—orewar Canjin da aka samu, na halatta auratayya da kuma tabattar da 'yancin kowane kalar fata.

Ya yi godiya ga dangin Nana, tare da jinjina mata, da kamba mata a gaban tarin jama'ar nan. Duk bai fito ya bayyana wa mutanen abin da Nanan ta yi yake ta wasa ta ba, amma ya nuna wa Duniya yana Ζ™aunar Nana, kuma komai zai yi ba zai taΙ“a biyanta soyayyar da sadaukarwar da ta yi masa ba.

"HaΖ™iΖ™a yau rana ce mai girima, da Ι—umbin tarihi a gare ni, da ma al'ummar Ζ™asar nan, duk da akwai ranar da ta fi ta da ba zan manta da ita ba, ranar da na mallaki Gimbiya Asma'u a matsayin matata. Ba ni da kalaman da zan yi amfani gurin yi mata godiya, da nuna muku girma da matsayinta a rayuwata ba. Ni dai na san halitta ce mai girma, da ta cancanci na wasa ta, na yabe ta, na so ta na kambama ta ko a ina ne. Asma'u ke rayuwata ce" Ya Ζ™arasa maganar a raunane.

"Allah ya yi miki mafificin tukuici. Haka zalika ba zan manta da Ι—an uwana ba, ba sabon Tafawan Agadez ba, dama wannan yayana ne. Ina nufin Tafeedan Agadez. Ba ni da abin da zan iya faΙ—a, sai dai za ku dauwwama a cikin zuciyata da kuma addu'ata. Sai mai gayya mai aiki uba na gari mai girma Sultan uban Ζ™asa uban kowa da kowa. Mu na godiya da tarin karamci da dattakunka a gare mu.

Iyayena na Nigeria, kafataninku muna Ζ™ara sake miΖ™a godiya a gare ku"

Nana kam kasa jurewa ta yi, ta rasa ma kukan me take yi, na murna ne ko kuma na damuwa.

Ba Nana ba hatta iyayenta, sai da suka yi kukan murna, Baba bai taΙ“a tsammanin a zuriyarsa za a samu irin wannan tagomashin ba. Sai dai shi Allah, mai aikata abin da ya so ne a lokacin da ya so, ya kan Ι—aga abu a lokacin da ya ga dama, zuwa Ζ™ololuwar matsayin da zato bai taΙ“a zata ba.

Taro ya watse lafiya, aka tashi cikin farin ciki, duk da zukatan maΖ™iya ba haka suka so ba.

Ai kamar yadda Hammad ya ce, a ranar za ta tare, babu wani abu da ya yi saura da ake jira.

Batun sabbin naΙ—e-naΙ—en da aka yi, ya sake cika gari, wasu suna ganin Sultan ya nuna son kai, gurin cire manyan mutane masu muΖ™amai, ya bawa 'ya'yansa.

Nana ta so ta huta kafin ta tare, amma Maijidda ta ce a'a, tun da haka mijinta ya ce yana so.

Baba duk abin sa, sai ga shi ga babar su Nana, a gurin bikin Nana. Abin mamaki Imrana ne ya sanya su a gaba ya din ga yi musu nasiha, da nuna musu illar gabar da suka din ga ya haifar musu.

Nene ta riΖ™e hannun Nana ta ce "Gimbiyarmu, dan Allah a yi mana godiya, tabbas Hammad ya cika jagora, na ji daΙ—in abin da ya yi wa Mahmoudu, Ubangiji Allah ya saka da mafificin alkhairi"

Gaba Ι—aya Nana ta so ta sake sosai a cikin 'yan uwanta.

Hammad yana ta shiri a Ι—akinsa, Mahmoudu ya shigo, dan bai samu sukunin haΙ—uwa da Hammad ba, saboda karΙ“ar baΖ™i.

Hammad ya kalle shi ya ce "Ango ka sha Ζ™amshi"

Ya buΙ—e baki zai yi magana, Hammd ya girgiza masa kai ya ce "Ɗan uwa kai ka ke bi na bashi, dan haka babu buΖ™atar wani dogon jawabi ko godiya a tsakaninmu, mai girma Tafeeda Allah ya taya riΖ™o" Ya yi maganar yana fesa masa turaren hannunsa.

"Sardaunanmu, godiya ta zama dole a tsakaninmu ai, godiya dole na...

Hammad ya tsuke fuska ya ce "To jeka waje ka yi godiyar"

Mahmoudu ya yi murmushi ya ce "Wallahi jin abin nake kamar a mafarki, bawa ya zama saraki ikon Allah, amma kana ganin Hanin ta amince da auren nan, tsakaninmu ba soyayya raha ce dai da girmama junanmu"

Hammad ya ce "Ka na tsoro ne? Hanin na sonka, da amincewarta aka yi komai".

"To kuma tana son baΖ™ar fata"

Hammad ya yi tsaki ya ce "Ka na da abin haushi wallahi. Kaf Ζ™abilar buzaye, ban taΙ“a ganin baΖ™i mai kyanka ba, har fararen ma, idan kuma duk baΖ™ar fata gaba Ι—aya matata ta fi kowane baΖ™ar fata kyau" A tare suka yi dariya. Hammad ya ce "Kai mutumin kirki ne, mai nagarta na san na yi wa Ζ™anwata kyakykywan zaΙ“i ne, dan haka ba ni da fargaba" Suka ci gaba da tattaunawa cikin raha.

Nana tamkar wadda za ta yi sabon aure, haka aka zaunar da ita aka din ga yi mata nasiha, Mai jidda ta nanata mata batun riΖ™e addu'a a duk inda take.

Sai da aka kai ta har gurin Sultan nan ma ya yi musu nasiha sosai ita da Hammad.

Daga bisani, Hammad ya Ι—auke ta daga can gurin Sultan suka tafi, ya ce akwai walimar cin abincin dare tare da ita da danginta kaΙ—ai, washegari kafin su wuce Nigeria.

Asal kamar za ta mutu, haka take wani irin kuka tana rirriΖ™e Hasna.

Tafawa ne yake ta bala'i ya ce "Wallahi ko za ki mutu sai ya sake ki, ban ga amfanin ki ci gaba da zama da mutane marasa mutunci ba, babu kunya babu tsoron Allah Jalaludeen ya sauke ni daga kujera ta, ya bawa 'ya'yansa, zai ga matakin da zan Ι—auka a kansu."

Asal ta girgiza kai ta ce "Dan Allah ka yi haΖ™uri, amma zan koma gidan Hammad, iya rufin asirin da ya yi mini ya isa, na yi maka biyayya iya yi na, amma Ζ™arshe na faΙ—a halaka, kuma buΖ™atar taka bata biya ba"


"Wallahi Asal ki ka koma gidan Hammad babu ni babu ke, na gaya miki sai dai ki canza uba!"


101

Alhaji Sabo ya ce "Ya na ga ka tsaya cak haka?"


Da kyar ya harhaΙ—o maganganun ya ce "Sabo, ce mini kai fa Amina ta mutu?"


Ya ce "Eh mana, ranar da ta mutun mutane na ta tambayar ina ka ke, aka ce kana Asibiti, likitoci sun hana a zo gurin ka. Yanzu sai ka maze duk wanda ya yi maka gaisuwa ko ya zo dubiya kawai ka amsa. Ita kuma Shukura lallai ka san yadda za ka yi da ita, ka Ι—auki mataki a kanta, ko kuma ka gaggauta bayar da jininta ga Ζ™ungiya kawai"

Ya yi shiru bai sake cewa komai ba, har suka isa gidansa, mutane na ganinsa suka din ga zuwa yi masa sannu, suna yi masa gaisuwa.

Bai iya amsawa kowa ba, Alhaji Sabo ya ce su yi haΖ™uri ba ya iya magana, saboda yanayin jikinsa. Har sashensa Alhaji Sabo ya raka shi, suna zuwa ya tarar da hijjabin Hajiya Amina da sallayarta gurin da ta yi sallar walha, kafin ta fita ta bar Ι—akin su Sagir su zo. Ya Ι—auki hijjabin ya kalli Alhaji Sabo, ya ce "Kana nufin Amina ta mutu? Kalli hijjabinta fa inda ta yi salla"


Alhaji Sabo ya ce "To shi ne me, kowa ma na haka ne ai. Kana ganin zaka iya zama a gidan nan kai kaΙ—ai, ko a samo maka wanda zai tayaka zama?"

Ya girgiza kai jiki a sanyaye, duk da mutuwar Yusf ta dake shi, amma bai taΙ“a jin mutuwar da ta daki zuciyarsa kamar mutuwar Hajiya Amina ba. Kan Ζ™iftawa da Bismillah. Ya Ι—auka aljanin da ya bawa mahaifarta shikenan ya tseratar da ita daga Ζ™ungiyar, abin da bai sani ba shi ne, bai isa ya tseratar da ita daga ajalinta ba.

Ya nemi guri a gefen gado ya zauna, kawai ya din ga ganinta tana yi masa gizo. Duk izza da Ζ™afafa ta matan masu kuΙ—i, da ta'amalli da 'yan aiki, Hajiya Amina ba ta yadda mai aiki ta dafa masa abinci ba. Duk da son da yake yi mata, baya hana shi ya ci mata mutunci wasu lokutan. Amma ko ta yi fushi na lokacin ne ta ware.

Ya yi mata wani irin so, mai wahalar mantawa.

So yake yi ya samu damar zubar da hawaye, amma abu ya gagara. Vibrating wayarsa ta yi a kan gadon, ita ma yadda ya tafi ya bar ta, haka ya dawo ya tarar da ita. Ya Ζ™ura mata ido daga bisani ya kai hannu ya Ι—auka ya duba.

SaΖ™o aka turo masa da lambar Doctor Sharif, ana sanar da shi Allah ya yi wa mai wayar rasuwar, za a yi jana'izarsa da yammacin ranar.

Ya fito daga cikin saΖ™on, ya ga saΖ™on Yusuf na Ζ™arshe, da yake ce masa Daddy idan ka ga saΖ™ona ka kira ni dan Allah na kasa samun ka a waya.

Ya tuna yadda suka yi waya, Yusuf yana tsara masa yadda zai yi walimarsa na kammala master's da ya yi, suka da daΙ—e su na waya cikin raha da barkwanci. Ya tuna yanzu duk ba sa Duniya.

"Saura kai, nan da anjima kai ne zaka mutu" Ya ji wata zuciyar ta raya masa. A take zuciyarsa ta tsinke ya buΙ—e idonsa a razane ya miΖ™e tsaye yana waige-waige. Wata irin fargaba ta shige shi, wani abu da bai san ko mene ne ba, ya tsirga masa tun daga cikin kansa har Ζ™afafuwansa. Da sauri ya fita daga Ι—akin ya koma falonsa yana mayar da numfashi.


****

Hammad ya kalli Asal da take ta kuka ya ce "Ko ki yi mini shiru, ko ki fita ki koma tun da ba dole na yi miki ba" Ba shiri ta hau goge hawayenta ta ce "Yi haΖ™uri, na daina" Ta yi maganar muryarta Ζ™asa-Ζ™asa.

Gaba Ι—aya zuciyarta babu daΙ—i, har ga Allah ba ta son saΙ“a wa mahaifinta, amma ta san ba a kan gaskiya suke ba. Kuma idan ya kashe mata auren yaya yake son ta yi?.

Ta yi shiru ta rakuΙ“e a gefen motar, kamar mai tsoron wani abu. Ya saka hannunsa ya janyo nata ya Ι—ora a kan cinyarsa yana murzawa a hankali hannu Ι—aya kuma yana tuΖ™insa. Ta Ι—aga kanta ta kalle shi, ta ga ya mayar da hankali sosai a kan tuΖ™insa.

Ji ta yi kamar ta kwanta a jikinsa, amma ta tuna girman laifuffukan da yake kallonta da su yanzu, dan haka ta fasa.

Ko da suka je gidan, ta tarar an yi wa gidan gyara sosai, an canza furnitures. Ta kalle shi za ta yi magana, amma sai ta fasa saboda gani take kamar fuskarsa a haΙ—e take.

"Ina fatan canje-canjen da na yi ya yi miki, ban Ι“ata miki rai ba"

Da sauri ta ce "A'a sun yi na gode sosai"

"A'a faΙ—i gaskiya dai, na san ki da iyayi da Ζ™aΖ™ale, idan bai yi ba a mayar da kayan a canzo wasu, tun da kamfanin wata uku suka bayar idan bai yi ba a mayar"

Ta girgiza kai ta ce "Yayi sosai da sosai"


Duk barorin gidan ba wani sonta suke yi ba, saboda fi'ilinta da wulaΖ™anci, amma da suka ga ta dawo sun yi murna, dan duk da wulaΖ™ancinta akwai kyauta. Hannunta a buΙ—e yake sosai da sosai gurin ungo.

Shi ya zo musu da abincin da ya saka aka kawo, daga gidan Abincinsa na Agadez.

Ya ci kayansa kamar ya share ta, ganin ta Ζ™i sakin jiki ta ci, duk da ya ce ya yafe mata, amma wasu lokutan da ya kalle ta wasu abubuwan suke dawo masa. Duk da yafiya aba ce mai wahala wasu lokutan, amma mantawa da laifuka ya fi komai wahala.

"CheriΓ©, ba za ki ci abincin ba ne?"

Ta ce "Na ci"

"Ba ki ci da yawa ba ai, ke da na san ki da son abinci, matso na baki a baki" Haka ya yi ta Ζ™oΖ™arin danne komai, kamar yadda ya saba yi a baya.

Da suka zo kwanciya ma, kasa sakin jiki ta yi, sai raΙ“e-raΙ“e take yi, tana satar kallonsa. Shi kuwa hankalinsa yana kan wayarsa, yana tsokanar Nana da roΖ™onta dan Allah kar ta kasa bacci, zai zo su haΙ—e ta mafarki.

Emojin dariya ta tura masa, ta ce "Da kenan, ka ke yi mini wannan rufa idon, yanzu ina gane komai, ka yi addu'a ka kwanta sai da safe" Ya yi murmushi ya rufe data. Ya juya ya kalli Asal ya ce "Na canza kamanni ne?" Ta Ι—an sunkuyar da kai tana girgiza kai. Ya miΖ™a mata hannunsa ya ce  "Ƙaraso mana" A hankali ta Ζ™ara, ya rungumo ta jikinsa, ya kwantar da ita sosai a kan gadon. Ya tashi ya je ya kashe fitilar ya dawo ya kwanta a kusa da ita. A Ζ™asan zuciyarsa ya din ga roΖ™on Allah ya sanya yafewa Asal da ya yi da sake karΙ“ar ta a matsayin mata, kar ta sake yinΖ™urin cutar da shi.

"Ya Allah da kyakkyawar niyya na yafe wa wannan baiwa taka, saboda ina tausayinta. Ubangiji Allah ka sanya ta gyara rayuwarta mu zauna lafiya"

Sosai ya sake da ita, tamkar babu wani abu na rashin daΙ—i da ya faru.


*****

Duk yadda Alhaji Zailani ya so kawar da komai a ransa a kasawa yayi. Ya din ga zagaya gidan yana kallon hanyar Ι—akin Shukura, da har a yanzu idan ta zo gidan, a nan take kwana. Ya kalli inda Yusuf yake zama mussaman idan zai kalli ball. Suna kallon Ζ™wallo tare dukkanin su akwai team Ι—in da suke supporting. Ya tuna kai komon Hajiya Amina a tsakaninsu, da Ζ™oΖ™arinta na ganin kowa ya samu abin da yake buΖ™ata. Amma yanzu babu Yusuf babu Amina, Shukura kuma babu wani abu da ta tsana a yanzu sama da shi. Gidan ya yi masa wani irin zafi Duniya ta din ga juya masa. Dama salla ba wani damuwa ya yi da ita, domin rashin kiyaye ta na daga cikin dalilan da yake kawo musu rashin jituwa tsakaninsa da Amina.

Ya din da ga jin sa tamkar a cikin wata Duniya yake, aka bar shi shikaΙ—ai.

Bugun Ζ™ofar da ya yi yawa ne ya tashi ya je ya buΙ—e Ζ™ofar main falon, ya tarar da mai delivery ya kawo masa abinci, kamar yadda Alhaji Sabo ya yi masa order, ya yi shiru yana tunanin ina mai gadi, da har mai delivery ya shigo haka. Ga harabar gidan babu kowa yan gaisuwa ma duk sun watse ya karΙ“a ya koma ya ajiye ya nemi guri ya kwanta.

Rufe idanunsa ke da wuya, ya ga duhu ya yi, alhalin yamma ce da sauran haske. Ya buΙ—e idanunsa ya yinΖ™ura zai tashi, amma ya ji tamkar an saka igiyoyi an Ι—aΙ—Ι—aure shi, ya kasa motsa ko da yatsansa. Yana jin yadda zuciyarsa take bugawa ya sare cewa kan shi ma ya mutu ne, ya din ga rarraba idanu ya ga ta ina zai fara ganin mala'iku sun bayyana. Ya hango cewar shi ma yanzu likkafani za a saka masa a je a binne shi a rami a tafi a bar shi. Ya yi wani yinΖ™uri domin ya tashi amma abu ya gagara. Wata irin dariya ya ji ana yi mara daΙ—in ji, cikin sauti mai Ζ™arfi. 

"Abin da ka ke gudun sai ya faru, ba za ka tsere wa mutuwa ba, dole ka biya wa dodo buΖ™atar sa, ko kuma ya yi ajalinka. Ɗif ya daina jin muryar, sai kuma fuskar matarsa ta farko da Ι—anta na fari, suka fara fitowa a Ι—akin. Ya sake rikicewa sai dai bai iya kowane yinΖ™uri ba, Shukura ta bayyana jikinta duk jini, kamar ba ta daΙ—e da haihuwa ba, ta tunkaro shi gadan-gadan da wuΖ™a ta fara Ζ™oΖ™arin caka masa. Kamar wanda aka tasa daga bacci ya gan shi a tsakiyar titi, Ζ™afafuwansa ko takalmi ko babu. Ya kalli jikinsa babu suturar kirki, gari shiru ko ina duhu alamar dare ya tsala. Sai da ya yi da gaske sannna ya gano cam gaban unguarsu ya tafi. Rashin gurin zuwa ya sanya tilas ya sake koma wa gidan nasa, ya ci uwar tafiya da Ζ™afa ya koma.

Sai dai Ζ™ofar gidan a buΙ—e, babu masu gadi, abin da bai sani ba tuni zancen ya fara zagayawa, a kan abin da ake zarginsa da shi, kasancewar mai aikin gidan na laΙ“e ta ji maganganun da aka yi. Suna watsewa da aka tafi da Hajiya Amina Asibiti, aka tafi da Alhaji Zailani ta tattara kayanta ta gaya wa mai gadin abin da yake faruwa ta gudu.

Alhaji Fatuhu ya Ζ™i sanar wa Iyalinsa abin da ya faru, sai dai gaba Ι—aya ba shi da nutsuwa, ga kayansa ana ta saya babu Ζ™aΖ™Ζ™autawa amma ba ya iya taΙ“uka komai, sai dai ya Ι“uya ya yi kuka.

Babu tsammani Fadila ta ritsa shi yana kuka, ya kasa cin abinci.

Cikin damuwa ta ce "Daddy, ina gama ka da zatin Allah ka gaya mini abin da yake damunka, da ba haka ka ke yi ba fa. Gaba kamar ma a tsorace ka ke Duniyar, kuka fa ka ke yi dan Allah ka faΙ—a mini mene ne?"


"Wallahi Fadila a tsorace nake da Duniyar, komai tsoro yake bani, ni dama rashin lafiyar da na yi na mutu, ban tashi ba da ban ji wannan abubuwan da damuwa da baΖ™in cikinsu zai halakka ni ba, bayan warkewr da na yi daga jinya ba"

Ba ta san lokacin da ta fara kuka ba ta ce "Dan Allah Daddy mene ne?"


"Fadila ba zan iya gaya miki ba, ku yi haΖ™uri kawai, Allah ya sanya mu dace" Haka ta gaji da rarrashin ta Ζ™yale shi.


Shukura kuwa Sagir da Yusra ba abin da suke yi sai aikin rarrashinta, da bata haΖ™uri, Yusra ce take kula da Haidar da jaririn da ta haifa aka saka masa Ahmad Annur.

Sai dai ta kasa yin lafiya, kusan kullum tana kwance, Alhaji Fatuhu duk kwana biyu sai yaje gidan ya rarrashe ta, ya bata haΖ™uri tare da kwantar mata da hankali.


****

Da sassafe Asal ta nemi Hammad ta rasa, ta tashi ta fita falo, ta hango shi a kwnace a kan kujera yana video call da Nana.


Ta tarar da shi yana cewa "Ba fa na ganin komai ma vie, dan Allah ki cire bargon nan"


"A'a nifa bacci zan yi ka ke takura mini"


"Zan rama ne Asmy, me za ki dafa zan shigo anjima in ganki in sha Allah"


"Ba zan dafa komai ba, ai yau kana gurin matarka ta dafa ta baka"


Ya marairaice ya ce "Ni ko? Shikenan tun da kin daina so na. Ɗan yi kissing goshina" Yayi maganar yana kara screen Ι—in a fuskar sa. Da sauri Asal ta koma Ι—aki, wani irin abu yana taso mata kamar za ta fita hayyacinta. Ji ta yi tana neman yin danasanin biyo shi ta dawo gidansa, amma ta tuna damarmakin da ya bata bayan da ya aure ta. Amma ta din ga muzguna masa, saboda hure mata kunne da Imam Omar ya din ga yi. Bai san daΙ—in aure ba sai da ta fara hankali ta fuskanci ba ya tanka duk rashin mutuncin da za ta yi masa. Idan zai yi magana a dankwafe shi. Sai a gaΙ“ar da ta dawo hayyacinta ta gane shayi ruwa ne, take sonsa a lokacin ta fara karΙ“ar sakamakon abin da ta aikata. Yanzu ba ta da wani abin cewa sai abin da ta gani kawai. Ta sha kukanta ta gode wa Allah.


Nana an kai mata hadimai, duk da ba komai ta sakar musu ba. Har gida aka kawo mata dalleliyar motar da aka bata a gurin bikinsu, wanda Imam Zahradeen sabon Tafawan Agadez ne ya ba ta. Banda uban gwala-gwalai da ta samu. Ta fuskanci gold ne kyauta mafi tsada da muhimmanci da suke ba wa mutum mai muhimmanci mussaman ma mace.

Lefenta kuwa, sai da ta din ga addu'a, saboda yadda mutane suka camfa duk auren da aka yi Ι“arna a gurin yin sa ba ya Ζ™arko. Sai dai Hammad ya ce mata ai abin da aka yi mata kyautatawa ce, ba wai dukiyar aure ba. Kuma Allah ne ya tsamo ta ya bata rabonta ne. Ya kuma tuna mata a yadda aka yi auren su.

Nana abin har kunya yake bata, yadda manyan mata wasu ma sun haife ta suke zuwa gidan, wai sun zo su gaishe ta, kuma in dai za su zo sai sun riΖ™o abin bata.

Ta fara yi wa Nene Ζ™orafin ita wannan abin da ake yi mata ta gaji. Nene ta ce "Waye ya gaya miki ana shiga dawa dan Ζ™arya? Ai girma ne ya hau kanki, dan haka dole ki yi haΖ™uri. Ba kuma a yi wa masu mulki kyauta su mayar su ce a'a, dole ka karΙ“a. Kuma dole kema ki zama mai yawan kyauta. Sannan ki Ζ™irΖ™iro wani abu da zai amfani mata a Ζ™asar nan, saboda tabattar da za ki iya riΖ™e muΖ™amin da aka baki"


Nana ta ce "To Allah ya bani iko, abinka da ba a saba ba"


"Ke yi wa mutane shiru ke da ba a saba Ι—in ba, dole a saba yanzu"


Haka Nana ta din ga jin tamkar an Ι—aΙ—Ι—aure ta saboda takura.


Ranar da Hammad zai dawo, ya dawo tare da Muhsin, ta din ga murna dan har ta fara karaya Zahradeen ba zai bata Ι—anta ba, ga shi tana jin nauyinsa, amma ta fara matsuwa da son ta yi magana.


Nana ta ce "Sayyid amma ya dawo kenan ko?"


Sayyid ya ce "To gamu nan dai, babansa sai masifa yake yi, sai da Sultan ya kira shi ya ce ya bamu Ι—anmu. 'yan biyu sai kuka suke yi."


Nana ta ce "Ina ma zan iya bar masa shi, amma raba ni da Ι—ayanku kamar raba ni da rayuwata ne"

Hammad ya ce "Idan ma bayarwar ne, ba gara ki ba wa Asal ba?"


Wani mugun kallo ta yi masa, da ya sanya shi yin shiru, ta saΙ“a Ι—anta ta yi Ι—aki.


Baba gaba Ι—aya ji ya yi kewar Nana ta dawo masa sabuwa fil, kamar a lokacin ta Ι“ata, daga ita har Imran, amma mussaman ma ita Nanan. Gaba Ι—aya ganin da ya yi mata ya ji Ι—anΙ—ani haukaci ne. Kusan kullum sai sun yi waya ta what'sapp. Har yake gaya wa Nana an kai wa Gaddafi kuΙ—in aure. Ta din ga murna sosai. Ta ce "Baba Dan Allah ka yi wa Sarkin baka magana a kansu Suwaiba, dan Allah"

"Wallahi Nana a kan yi mini maganar yaran nan, zan daina kira mu yi magana"

Gaba Ι—aya Nana ba ta jin daΙ—in hakan da Baba yake yi. Haka take kiran Ummanta ma, su yi waya da su Walida. Sai ga Iliyasu da karΙ“ar waya, su gaisa da Nana yana neman yafiyarta a kan abubuwan da suka faru.

Har ga Allah Nana ta tsani mutumin nan, ba zata manta abubuwan da ya yi mata ba, amma ta duba matsayin da Allah ya kaita a yanzu, dan haka ta ga ba girmanta ba ne ma zaman jin haushin wani ba.


****

Kwanaki huΙ—u kenan, Alhaji Zailani kamar wanda aka yi wa asiri, ya kasa barin gidan, ga shi dare da rana tsorata shi kawai ake yi a gidan nan. Banda ihu marasa daΙ—in ji, a Ι—auke shi a yi ta bugawa da Ζ™asa.

Ko ya yi ta maΖ™abarta waΙ—anda ya bayar a Ζ™ungiyar asiri, suna ta kokowa da shi za su danna shi a cikin kabari su rufe, yana ihu yana Ζ™oΖ™arin fitowa, ko kuma ya ga su na Ζ™oΖ™arin kashe shi. Duk yadda ya so sarrafa tunaninsa domin ya je gurin Malam Gambo neman mafita, amma ya kasa jin sa kawai yake yi a wata Duniyar daban.

Tsawon kwanakin nan ya galabaita, ba ci ba sha, ba wanka ga kufcewar hankali. Yaje kitchen ya Ι—aukko wuΖ™a ya riΖ™e yana zazzare ido, da nufin yana ganin sun fito masa ya caka musu.

Sai dai Shukura ta bayyana, da wuΖ™ar nan a hannunta, su na ta kokowa da shi, yana Ζ™oΖ™arin kar ya caka mata, saboda zuciyarsa na raya masa, itakaΙ—ai ta rage masa yanzu. Kawai ya hango Alhaji Fatuhu na Ζ™yaΖ™ayata masa dariya yana faΙ—in "Yanzu wa ya yi nasara? Ka rasa komai Zailani. Ba ka da kowa, ka kashe kowa naka, dukiyar kuma ba zata amfane ka ba. Ni kuma da ka yi niyyar hallakawa, komai nawa ya dawo, ga shi kuma dole mutuwa zaka yi" Ya saki Shukura ya nufi Alhaji Fatuhu yana faΙ—in "Na tsane ka, ba na Ζ™aunarka. Ba zan taΙ“a sonka ba kuma sai ka mutu, sai ka riga ni barin duniyar nan, na yi yadda nake so". Ya yi maganar yana cakawa Alhaji Fatuhu da yake gani wuΖ™ar nan a cikin sa.

Jini ne ya fara fitowa ta bakin Alhaji Fatuhu,  ya ce "Zailani wannan shi ne Ζ™arshen duk wanda ya gaza sarrafa ni. Ka kasa kula da ni a lokacin da na kamu da rashin lafiya. Ciwon Ζ™yashi ya kama ni, son duniya, hassada, mugunta, Ζ™eta na bushe na yi baΖ™i, har ka gaza sarrafa ni kullum burinka biya mini buΖ™atar duk da na bijiro maka, wanda ina bijiro maka buΖ™atuna ne, saboda samun sassaucin wannan ciwukan da suka kama ni, ka Ζ™i kulawa ka bani magani. Ga shi biyan buΖ™atuna ya sanya ka aikata abu mafi muni, ga Ζ™arshe mara kyau"

Alhaji Fatuhu ya sake caka wa Alhaji Fatuhu da yake gani a gabansa. Wata irin zabura ya yi tare da kurma wani uban ihu, jin wani irin gigitacciyar azaba da raΙ—aΙ—i ya ratsa cikinsa.

Abin da bai sani ba, da ya Ι—auki wuΖ™ar nan kansa y fara cakawa, ya fita waje yana tangaΙ—i, yana faΙ—in "Na kashe ku Ι—in, na fi son duniya a kanku. A lahira rahamar Allah za ta saka na shiga aljanna a Duniya kuma Ζ™oΖ™arina ne zai tara mini abin duniya" Ya din ga surutu yana faΙ—ar miyagun ayyukan da ya din ga aikatawa. Kafin a yi Ζ™oΖ™arin Ζ™wace wuΖ™ar ya sake caka wa kansa a cikinsa, ya sulale ya faΙ—i Ζ™asa, jini yana zuba a jikinsa. Yana faΙ—uwa bakinsa a buΙ—e, Aljanin da ya mallaka ya bar gangar jikinsa.


(Ya hayyu ya Ζ™ayyum ya zuljalalu wal ikram Ubangiji Allah ka sanya mu yi kyakykywan Ζ™arshe, Allah ka raba mu da mummunan Ζ™arshe, Allah kar ka sanya mu cuci kowaπŸ™πŸ™πŸ™πŸ˜­)


Abin ka da zamani na amfani da social media, a lokacin da Alhaji Zailani yake wannan tamΙ“elen, aka samu masu ciro waya suka Ι—auki abin da ya din ga yi, suka sanya a shafukan sada zumunta, duk wasu shafukan an sauke videos Ι—in, saboda abin da yake ciki na tashin hankali.

Tuni aka nemo jami'an tsaro, suka Ι—auki gawar Alhaji Zailani. Sagir ne ya fara gani a social media ya tashi hankalinsa a dugunzume, ya tafi gidan Alhaji Fatuhu ya yi sallama da shi.

Ya kalli Sagir ya ce "Lafiya kuwa? Ko Shukuran ce babu lafiya, na ganka kamar ba a nutse ba?"

Ya ciro wayarsa ya nuna wa Alhaji Fatuhu abin da yake faruwa. Sai da ya jingina da bango sannan ya din ga maimaita Innalillahi wa Innalillahi raji'un. Ya daΙ—e cikin mawuyacin hali, kafin ya daidaita nutsuwarsa ya dubi Sagir ya ce "Shukura ta gani?"

Sagir ya ce "A'a, ai babu waya a hannunta ma"

"To ka yi duk yadda za ka yi, kar waya ta shiga hannunta. Tun da Allah ya riga ya yi masa rasuwa, komai ya Ζ™are. Yanzu muje gurin 'yansanda mu roΖ™e su a taΖ™aita lamarin binciken nan, a yi masa sutura a binne shi" Sagir ya sara wa zuciya irin ta Alhaji Fatuhu, a irin abin da Alhaji Zailani ya yi masa, yake cewa su je su karΙ“i gawarsa a binne shi.

Sun sha fama da 'yan sanda, dan hana gawarsa suka yi, sai da aka je gidansa, domin zurfafa bincike. Sai dai da bincike yayi bincike aka din ga gano, abubuwa na tsaface-tsaface da suke Ι“oye a cikin gidan. Sannan aka buΙ—e wayarsa, yanayin tattaunawar sa da wasu daga cikin abokansa, ciki har da Malam Gambo, ya sanya jami'an tsaro kama su.


*****


Sayyid a gurin Asal yake, amma yaje yana damunta. Sai da ya fara shirin tafiya, ta ce masa ya jira tana da baΖ™i su gaisa.

"Suwaye baΖ™in kai a Agadez? Umma ce? (Da yake haka yake kiran Nene, kamar yadda Mahmoudu yake kiran ta)"

"Ba ita ba ce"

"To suwaye?"


"BaΖ™i masu muhimmancin gaske ne, za ka gani"


Ya ce "To bari na je masallaci, kafin su zo" Ya yi alwala ya fita falo, ya ga Nene tare da wata mata da namiji da alamu suka nuna mata da miji ne. Su na ganinsa suka Ζ™ara nutsuwa, domin sukan ji zancensa a bakin Nene. Cikin girmamawa suka risuna su na gaishe shi. Ya amsa yana mamakin dalilin shigo masa da Ζ™ato haka har cikin falo. Ya dake ya ce "Umma dama ke ce baΖ™uwar, ta dage kar na fita sai kin zo?"


Ta yi murmushi ta ce "Ba ma nice baΖ™uwar ba, ga baΖ™in nata nan" Ta yi maganar tana nuna masa mata da mijin. Ya yi shiru yana kallonsu, ba su yi kama da 'yan Nigeria ba, sun fi kama da hausawan Niger, mussaman daga yanayin hausar su.

Nana ce ta buΙ—e Ζ™ofa ta fito, da gudu ta nufi Hajara ta rungume ta, Muhsin ya biyo bayanta ya ja ya tsaya a kusa da mahaifinsa.


"Hajara, dama zan sake ganinki?"


"Gani kuwa shugabata" Hajara ta yi maganar cikin girmamawa.


Nana har Ζ™asa ta durΖ™usa ta gaida Auwwal, takaici ya kama Hammad, haryanzu Nana ta kasa gane mene ne matsayinta. Banda haka ya za a yi ta durΖ™usa har Ζ™asa tana gaida mutumin da shi kansa ya girme shi, da ma dattijo ne da sauΖ™i.


Nene ta ce "Nana ba girmanki ba ne, ai shi yakamata ya gaishe ki"


Shi ma a tsorace ya ce "Wallahi kuwa"


"Kash, Nene ba ni da wani girma, ni na kasa jin girman nan. Meyasa ba zan girmama mutane mafiya karamci a gare ni ba?" Ta taso tana kallon Sayyid fuskarta sharkaf da hawaye ta ce "Wannan gidan su ne je, lokacin da na baro Agadez na nemi Nene na rasa, a can gidansu aka Ι—aukko ni. Sayyid lokacin da na zo Niger na sauka a MaraΙ—i, ba ni da kowa sai Allah, Allah ya dubi zuciyata ya ji Ζ™aina ya haΙ—a ni da mutane masu karamci. Wannan su ne sanadin haΙ—uwa ta da Nene." Nan ta kwashe komai ta gaya masa. Sannan ta Ι—ora da cewa "Ina tambayar Nene su, ta ce mini sun tafi ci rani can Ζ™asar Mali. Sai yau Neme ta kira ni ta ce mini sun zo Niger, su na Agadez za ta kawo su mu gaisa. Ni na so mu je har inda suke amma ta hana" Kukan da Nana take yi kawai ya tabattar masa da ba Ζ™aramin karamci suka yi mata ba.

Ya taka ya Ζ™arasa gaban Auwall da kansa yake Ζ™asa, ya miΖ™a masa hannu su yi musabaha. Da kyar ya iya miΖ™o masa hannu.

Suka gaisa Hammad ya dafa kafaΙ—arsa ya ce "Na gode sosai da sosai. Mutane a zamanin nan abin tsoro ne, amma ka zama mutum na farko gurin bawa matar da baka sani ba taimako.

Na gode sosai da sosai, dama Umma uwata ce, kai ne dai ban sani ba, tabbas tana bani labarinku. In sha Allah ba zaka sake zuwa Mali ci rani ba, da yardar Allah  na gode sosai da sosai Allah ya biya ka"

Ya kalli matarsa ita ma ya yi mata godiya sosai.


Tare suka je Salla da Auwwal, Hajara ta yi nufin Ι—aukar Muhsin, amma ya Ζ™i saboda Ζ™yuya.

Hadimai suka gabatar da Abinci, da abubuwan sha daban daban. Sayyid a dole yake Ι—aga Ζ™afa a wasu abubuwan duk da azabar kishin Nana da yake yi. Ya yi iya Ζ™oΖ™arinsa a kan kar ya yi wani abu da ran su Auwwal zai sosu ko na Nene, ko dan albarkacin Ι—awainiyar da suka yi da Nana.

Har da kyautar kayan wasan Yara, suka kawowa Yarima Muhsin. A hirar ta su suke gaya wa Nana haryanzu Allah bai ba su haihuwa ba. Ta yi ta musu nasiha da basu misalai masu kwantar da hankali.

Sai isha'i suka tashi tafiya, Hammad ya yi musu alkhairi, tare da jaddada musu godiya, ya kuma gaya wa Auwwal lokacin da zai zo MaraΙ—i, ya ba shi katinsa ya ce idan yaje ya nuna katin za a bari ya gan shi, zai ba shi abin yi.

Bangaren Nana ma, kyaututtuka ta ba wa Hajara sosai, da ta ce ba zata karΙ“a ba, abin da suka yi wa Nana, dan Allah suka yi mata, Nene ta ce mata ba a mayar wa da masu mulki kyauta.

Sai da Nana ta karΙ“i lambar wayar Hajara, ta din ga yi musu godiya kamar ta tsuguna musu. Hammad ya Ι—auki Muhsin ya ce da kansa zai mayar da su har gidan da Nene take, kasancewar a gurinta suka sauka a Agadez. Daga can ya so wucewa gurin Asal da Muhsin dan yana kyautata zaton bata taΙ“a ganinsa ba, amma Nana ba ta sani ba, tsaf za su iya yin faΙ—a a kan hakan. Kuma da gaskiyar Nana kome nene Asal ce ta janyo, kuma duk abin da Nana za ta yi domin ta ba wa Ι—anta kariya. Bugu da Ζ™ari kuma ba ya son duk wani abu da zai kawo musu matsala, saboda wata irin kwanciyar hankali ya tsinci kansa a ciki. Ga taraiya da soyayya da yake samu daga gurinta. Duk da haryanzu Giyaz yana taΙ“a shi. Amma idan yana tare da ita, da ya gaya mata alamomin da yake ji, take yi masa addu'a ko ma muraran ta ga Giyaz Ι—in tare da shi.

Ya tattara hankalinsa a kan Nana da ta nufo shi, ta sanya doguwar riga ta cika ta, rigar ta zauna a jikinta.

Ta ce "Wannan kallon sai ka saka na faΙ—i tukuna?" Yayi murmushi ya ce "Sai na riΖ™o ki kafin ki faΙ—in.

Ta yi murmushi ta zauna a kusa da shi, ta kai kofin hannunta bakinsa ya buΙ—e baki yana sha. Ta ce "Amma ka yi sauri fa"


"Eh, ina kai su na juyo ne, in sha Allah idan muka haΙ—u a MaraΙ—i, zan sama masa aikin yi"

"Gaskiya ka kyauta, Allah ya saka maka da alkhairi" Ta ci gaba da ba shi labarin irin taimakon da suka yi mata.

Ya Ζ™are mata kallo sannan ya ce "Lokacin mu na Nigeria, ba wuya kin samu rabo, Allah ya sa Niger ma haka ne, Allah ya sanya Ζ™ani ko Ζ™anwar Muhsin sun samu a cikin nan"

Nana ta tura baki ta ce "Sai Yarima ya shekara biyar"

"Wace shekara biyar kuma? Kowa so yake sai ya karΙ“e shi, Zahradeen nata masifa, ga Sultan ya ce gobe na kai masa shi, amma idan Allah ya sa ki ka haihu, ko an Ζ™wace shi mu na da wani ko?" Kawai ta yi shiru tana murmushi, dan ji take gara ta haifi wasu a Ζ™wace da a Ζ™wace mata Muhsin.

Su na hira ta Ι—auki wayarta, za ta nuna masa abu, sai dai tana buΙ—e data videon Alhaji Zailani ta fara cin karo da shi a dandalin sada zumunta.

MiΖ™ewa ta yi tsaye jikinta na wata irin tsuma, kamar za ta zare. Ya karΙ“i wayar hannunta ya kalli videon. Ya ajiye wayar ya ce "Shiyasa wasu lokutan shafukan sada zumuntar nan duk ba su da wani amfani"

"Sayyid ba ka gane waye ba?"

Ya girgiza kai ya ce "Ni ban san shi ba"


"Ba ka tuna Alhaji Zailani ba?" Ya yi shiru ya tafi tunanin, kamar ya san sunan, can kuma ya ce "Na tuna, mutumin da muka fara gadi a gidansa da su Mahmoudu. To Allah ya kyauta ke mene ne naki na shiga tashin hankali haka?"


"Dan Allah Sayyid ina son zuwa Nigeria" Ta yi maganar cikin tsoro da tashin hankali.


"Sati uku da gama hidimar nan ki ce za ki Nigeria, a Ζ™alla nan da wata biyu nake son mu je tare"

Sai ta rikice masa gaba Ι—aya a kan ita fa dole Nigeria take son zuwa. Abu kamar wasa ya Ι—auka da wasa take yi, sai da ya ga ta yanke jiki ta faΙ—i, jikinta ya yi sanyi Ζ™alau. A hankali ya Ι—aga kai ya kalli tsuntsun da yake shawagi a saman Ι—akin, da hakan ya tabattar masa da Ƙaisar ne ya zo mata.

A ransa ya Ζ™udurce lallai a shirya tafiya Egypt Ι—in nan, kafin su zo su ci gaba da samun matsala, su sake hana su zaman aure cikin kwanciyar hankali.

Sai dai idan ya ce a yi mata passport a Niger, zai Ι—an Ι—auki lokaci, dan haka ya yanke shawarar za su je Nigeria a yi mata, sai su tafi. Har wajen Ζ™arfe goma na dare yana tare da Nana, sai dai ba ta dawo hayyacinta ba. Ya kira Asal ya gaya mata Nana babu lafiya, dan haka ta yi haΖ™uri ba zai samu damar dawowa a ranar ba.

Asal kamar ta haΙ—iyi zuciya ta mutu, gani take kawai faΙ—a yayi, dan ya zauna ya kwana a gurin Nana, amma babu yadda ta iya. Shi kansa sai da ya raya za ta yi tunanin hakan, amma babu yadda za a yi ya tafi ya bar Nana a wannan yanayin.


Duk yadda su Sagir suke yi wa Shukura Ι“oye-Ι“oye, sai da ta san Allah ya yi wa mahaifinta rasuwa.


Hajiya Suwaiba ce ta fara ganin Videon nan, sai ba ta yi wa Alhaji Fatuhu magana ba, ta je gurin Fadila. Fadila ta Ι—an yi mamakin ganin Hajiya Suwaiba a falon ta.

Bayan sun gaisa ta ce "Fadila, ko Daddy ya gaya miki abin da yake damun sa?"


Fadila ta ce "Wallahi bai gaya mini ba, na yi na yi ya Ζ™i ya gaya mini"


"Kin ga wani video"


Fadila ta karΙ“i videon tana kallo, jikinta ne ya hau karkarwa ta ce "Wannan ai Alhaji Zailani ne? Wai yana nufin Alhajinmu ya yi wa abin da yake faΙ—ar nan?"


"Nima abin da ya Ι—aure mini kai kenan"


Alhaji Fatuhu ne ya yi sallama, ya ga duk sun zubo masa ido, kamar marasa gaskiya.


"Lafiya kuwa?"


Hajiya Suwaiba ce ta yi kokarin cewa "Daddy wani abu muka gani, shi ne dama abin da ka ke Ι“oye mana?"


"Me na Ι“oye mukun?"


Ta miΖ™a masa wayarta, yana kalla ya ajiya, ya zauna cikin damuwa, ya ce "Koma mene ne ya faru, ya riga ya faru, dan Allah a bar maganar nan ta wuce"


Hajiya Suwaiba ta ce "Amma ya batun maganganun da ya din ga faΙ—a, yana cewa shi ya yi maka sihiri?"


"Suwaiba a bar maganar nan dan Allah"


"Amma ya zaka ce a bar ta, mutumin da ya tsugunar da mu, ya saka mu a wahala, to wallahi ni dai ban yafe ba."


Fadila ta sha mamakin abubuwan da ta ji a videon nan, kuma ta tsorata imani ya Ζ™ara shigarta, sai dai tun da ta ji Alhaji Fatuhu bai musa ba, to tabbas an yi hakan.


*****

Nana Bakinta ya Ζ™i rufuwa, wani irin farinciki take ci, ganin sun kama hanyar Nigeria.

Ta din ga tuna lokacin da ta yi balaguro, daga Nigeria zuwa Niger tsawon shekaru, ta tafi zuciya a cunkushe cike da rashin sanin makoma, sai dai kyakykywan yaΖ™ini da dogaro ga Allah. Sai ga shi a wannan karon ta nufi zuwa gidan, cike da farinciki da kwanciyar hankali. Ta so tahowa da Muhsin, amma Hammad fafur ya hana, wai sai zo Ι—aukarta zai taho da shi.

Sai da suka samu saΙ“ani kafin ta taho, dan cewa ta yi muddin Asal zai kai wa Ι—anta gara ta haΖ™ura da tafiyar. Ƙarshe sai da suka kai shi gidan Zahradeen, sannan ta hakura ta taho.

A garin Bauchi ta fara yada zango, duk da nan ma abin da ya faru ba zai taΙ“a gogewa daga cikin Ζ™waΖ™walwarta ba. Mama tana ta kiranta a waya ta ji ko ta kusa Ζ™arasowa.

Ko da Nana suka isa, Iliyasu ta fara gani a Ζ™ofar gida, ya tsaya yana washe baki, ganin Nana ta fito daga danΖ™areriyar mota da aka kawo ta a ciki.

"Maraba, sannunku da zuwa, sannu da zuwa"

Ita Nana ma abun da yake yi matan, kunya ya din ga bata. Ta tarar da su Adda Maryam da Fati da wasu daga dangin Umman, duk sun cika gidan. Sun yi murna sosai da sosai da ganin Nana. Suka din ga yi mata barka da zuwa.

Nana ta sha karramawa, mijin umman sai nan nan yake yi da ita, yana washe mata baki har da yi mata raha.

Baba ya din ga kiran Nana yana tambayarta sai yaushe zata Ζ™araso. Ta ce masa ai ta sauka a Bauchi, sai ta kwana biyu za ta zo. Gaba Ι—aya bai ji daΙ—in hakan ba, saboda yadda yake Alla-Alla ta zo ya sake ganinta.

Sai da Nana ta kwana uku a Bauchi, Mama tana a kaita tasha a saka ta a mota, ta ce ai direbanta yana nan a Bauchin bai tafi ba.

Suka sake Ι—aukar hanyar Kano, jalla babbar Hausa yaro ko da me ka zo an fika. Nana ta yi kewar garinta na haihuwa ba kaΙ—an ba.


Da sallama Nana ta shiga gidansu, Iya suturar jikinta, da yadda ta yi kyau mai Ι—aukar ido ya sanya Mama yin saroro da kasa amsa mata sallamar. Nasiru ne ya fito da gudu yana faΙ—in Oyoyo ga masarautar Agadez da kanta. Masu arzikin zinare, masu kyauta da dama hagu ma ba ta san ana yi ba. Barka da zuwa Garkuwar matan Agadez ke ta Afrika ma gaba Ι—aya." Kawai Nana ta tsaya tana murmushi, Jamila ta fito daga Ι—akin, ta zo ta rungume Nana, sai Nana ta manta da batun wata Mama, ta hau murnar ganin 'yan uwanta. Nasiru ya je ya Ι—aukko mata Akwatinta a mota.

Nana ta dake ta ce "Mama ina wuni?"


A dole bisa yaΖ™e Maman ta ce "Lafiya Ζ™alau Nana, ai kasa gane ki na yi, irin wannan gwala-gwalai haka. Ai na zata ba zaki sake saka su ba, dan kar ki yi almubazzaranci tun da da muka je fama aka yi ta yi da ke, ki ka ce ba kya so"


Nana ta yi murmushi, tana tuna karatun da Ƙaisar ya yi mata, amma ta ce "To Mama yana iya, masu abu da abinsu, an ce mini haka suke adonsu, idan ka je gari ka ga 'yan gari da jela, aka ce kai ma ka nema ka maΖ™ala. Gaba Ι—aya Mama ba ta san baΖ™in cikinta ya fito muraran ba.

Baba ma da ya dawo ya ga Nana, bakin nan a buΙ—e ya din ga murna yana yi mata maraba. Babu laifi sun yi nata karΙ“a mai kyau. Ta yi musu tsaraba mai yawa sosai kamar yadda ta yi wa mutanen Bauchi.

Da daddare suna Ι—aki suna ta hir da Jamila, take gaya wa Jamila abun da ta gani a waya, Jamila ta Ζ™ara bata cikakken labarin abin da ya faru, da yadda Hajiya Sa'a take bayar da 'ya'yan Alhaji Fatuhu har ma da rashin lafiyar da Alhaji Fatuhun ya yi sai da ta bata labari. Jikin Nana ya din ga tsuma ta shiga tashin hankali, ta Ζ™udurce a ranta lallai a washegari za ta je gidan Alhaji Fatuhu, za ta je.

Suwaiba ma ta dage ta din ga yi wa Nana hira, duk da galibin hirar tata shirme ce, tayi baΖ™i Ζ™irin duk ta bushe kamar wadda aka tsotse wa sinadaran jikinta.

Gaddafi ma sun sha hira sosai da sosai da Nana. Da Safe da ta ce zata fita sai da Baba ya yi ta mitar daga zuwanta za ta fara yawo.

Amma Nana ta nuna masa fitar ta dole ce, gidan Ummi za ta je. Tare da Jamila suka tafi gidan Alhaji Fatuhu.

Sashen Fadila suka je, sai dai har suka gaisa ba ta gane su ba, har gara Jamila tana ta Ζ™oΖ™arin tuna ta.

Yaronta Muhsin ne ya fito ya taso daga bacci, kamarsa Ι—aya sak da wancan Muhsin Ι—in.

Nana na ganinsa ta miΖ™e tana faΙ—in "La haula wala Ζ™uwwata illa billah. Banda na zo gaisuwar Muhsin, da cewa zan yi Muhsin Ι—ina ne nan". Ta yi maganar tana Ι—aukar Muhsin tana shafa kansa.

Fadila ta ce "Ya salam, Anty ai sai yanzu na gane ki, malamar Muhsin ko? Ai kin canza kamanni ne gaba Ι—aya. Tun da ki ka yi aure bamu sake ganinki ba"


Hawaye ya cika idanun Nana, ta Ζ™anΖ™ame Muhsin, tana tuna wancan. 

Jamila ma cikin kuka ta ce "Na yi dana sanin Hajiya Sa'a, da tuni wannan ma ta bayar da shi kamar yadda ta bayar da wancan"

A razane Fadila ta kalle ta ta ce "Me ki ke nufi?"

Nana ta ce "Babu abin da take nufi"


Fadila ta ce "A'a ga abu nan tana faΙ—a, kenan da gaske Hajiya Sa'a ita ta bayar mini da Muhsin Ι—ina? Ya aka yi ki ka sani"


"Fadila na gaya miki wannan zancen ba haka yake ba, meyasa ki ke da gardama ne? Wannan Ι—in suwaye su?"


Ya kalli Jamila ya ce "Wannan ba ke ce nake gani a gidan Sa'a ba? Ya aka yi ki ka san wannan zancen?"


Nana ta katse shi, ta hanyar gaishe shi, ya amsa sai dai tana magana ya gane ta.


Ya ce "Nana ke ce?"


Nana ta jinjina masa kai tana murmushi.


"Baiwar Allah kin san tsawon lokacin da na Ι—auka ina neman ki? Na din ga mafarkai daban-daban da ke. Jinya na haΙ—u da ita bayan kin yi aure"


Fadila kasancewar ba wannan maganar take buΖ™ata ba, cikin Ι—imuwa ta ce wa Jamila ta gaya mata abin da Hajiya Sa'a ta yi wa Ι—anta.


Alhaji Fatuhu ya fara Ζ™oΖ™arin karewa ya hana, amma Jamila ta ce "Dan Allah ku yi haΖ™uri, na haddass muku fitina, amma gara na faΙ—a dan abu ne da yake ta damuna." Nan ta kwashe komai ta faΙ—a, har abin da Alhaji Fatuhu bai sani ba, da yadda ta shiga Ζ™ungiyar asiri duk sai da ta faΙ—a, da yadda Abba ya mutu maimakon Muhsin.


Cikin kiΙ—imewa Fadila ta riΖ™e Alhaji Fatuhu tana faΙ—in "Amma ka zalunce ni, saboda ka kare 'yar uwakka, ka din ga yi mini wasa da hankali ka Ζ™i yarda da abubuwan da take faΙ—a. Ɗana gudan jinina aka ba wa matsafa. Ɗana fa Ι—an da na sha wahala na haifa."


Nana ce ta sauke Muhsin, ta je ta kamo Fadila ta rungume ta cikin rarrashi ta ce "Yanzu wannan da ki ka haifa kin san Allah zai baki shi? Dan haka ko da ita ko babu ita, Allah ya Ζ™addara ba rayayye bane ba. Kuma da na san Jamila zata faΙ—a ba zan yadda mu zo tare ba. Ki yi haΖ™uri ba zan ce sai kin yafe ba, amma kar ki Ι—aga masa hankali, tashin hankalinki yake gudu ya sanya ya Ι“oye miki. Kina kallo ya rasa Ι—ansa dalilin yar uwassa, abokinsa ya cutar da shi da mugun baΖ™in sihiri, kar ki ce za ki huce a kansa dan Allah"


Ayshercool 

08081012143

Littafin kuΙ—i ne, a biya 1k via 0069685771 Aisha Adam stanbic 


103


Fadila ta saki rigar Alhaji Fatuhu, ta koma da baya tana zubar da hawaye cikin matsanancin tashin hankali da damuwa.

Nana ta din ga yi mata nasiha mai shiga jiki tare da ba ta misali da kan kanta, irin faΙ—i tashin da ta din ga yi bayan auren ta.

A hankali kuma sai Fadila ta din ga samun nutsuwa, tana jin damuwar ta ta, ta ragu ta kaΙ—u sosai da sosai da jin irin iftila'i da Nana ta din ga faΙ—awa ita ma.

Alhaji Fatuhu ya ce "Sannu Nana"

Nana ta yi murmushi ta ce "Yanzu ga shi komai ya wuce, amma soyayyar da nake yi wa marigayi Muhsin, ta sanya bayan na haihu na sanya wa yarona Muhammad Muhsin, shi ma sunan shi Muhsin, zai yi sa'an wannan Muhsin Ι—in" Ta yi maganar tana kallon Muhsin da ya kwanta a jikin Alhaji Fatuhu.

Fadila ta ce "Yanzu har sunan Muhsin ki ka saka wa yaronki?"

Nana ta ce "Ƙwarai kuwa, Allah shaida ne na so Muhsin yaron nan ya shiga raina nesa ba kusa ba. Bayan shi sai Haidar Ι—in Shukura jikan Alhaji Zailani, gaba Ι—aya zuciyata ta tsinke ina tsoron a ce shi ma wani abin ya faru da shi"


Alhaji Fatuhu ya ce "A'a yana nan cikin Ζ™oshin lafiya shi"


Nana ta sake cewa "Dan Allah Maman Muhsin ina sake baki haΖ™uri, kar ki ga laifin 'yar uwata tun da har ta nemi yafiyarki ta bayyana duk abin da ya faru ba tare da tsoron abin da zai biyo baya. Yadda aka bi aka saka ta a Ζ™ungiyar asiri ba da saninta ba, kuma a garin ta ceci wannan Muhsin Ι—in, Ι—an Hajiya Sa'a ya rasa ransa kuma ita ma haryanzu fama take yi da rashin lafiya"


Alhaji Fatuhu ya ce "Babu komai, dukkaninmu nan bamu wuce jarrabawa ba. Sai dai mun gode Allah, muna fatan ya zama kaffara a gare mu, domin ni jinya na sha, da sai da na din ga wari da raina, na yanke tsammani da rayuwa na rasa komai. Na Ζ™i yarda a yi mini maganin addini, ina tunanin ko na Asibiti ne. WataΖ™ila ma da Muhsin na amince an yi masa na addini da ko zai mutu zai samu afuwa.

Ni kaina mafarki na din ga yi da ke kina ce mini sihiri aka yi mini, na nemi magani na yi mafarkin nan ya fi a Ζ™irga sannan na yarda na fara neman maganin addini. Wallahi rasa Ι—ana Muhsin bai yi mini zafin yadda nake tausaya wa Shukura da Zailani ya salwantar da rayuwarsa domin wai ya ga bayana ba. Innalillahi wa Innalillahi raji'un" Yayi maganar yana fashewa da kuka, saboda dauriya kawai yake yi, amma abin yana mugun cin sa. Ya kasa sakin jiki ko Allah ya isa ya yi wa Zailani da 'yar uwassa gani yake iya bala'i da masifar da suka jefa kansi ma, ta ishe su a wajen Allah ba sai ya Ζ™ara musu da Allah ya isa ba.

Sai azahar su Nana suka bar gidan, sun yi hira sosai da Alhaji Fatuhu jin sa take yi kamar uba. Yake tsokanarta da zai din ga aika mata da kaya Niger tana sayarwa.

Daga gidan Alhaji Fatuhu gidan Ummi suka wuce, jikin Nana duk a matuΖ™ar sanyaye, sai abu ya faru ta yi ta tunanin a ina ta san abin, a ina ta taΙ“a gani, sai ta nutsu sai ta tuna Ƙaisar ne ya nuna mata.

Ummi ta din ga yi wa su Nana masifar dan me za su zo da rana haka, bayan tun safe take saka ran ganinsu. Cikin jimami da damuwa, Nana ta kwashe komai ta gaya wa Ummi.

Ummi ta kaΙ—u ta tsure da jin labarin da Nana ta bata, sai dai sam bata bayyana mata, wai Jamila har Ζ™ungiyar asiri ta shiga ba, ita ma Ummin bata nuna mata Baba ya gaya mata ba.

Ummi ta ce 'Ina ta saka ran ki zo mu sha hira, amma kin zo mini da abin tashin hankali.

Suka watsar da wannan hirar, suka shiga wata. Hira tayi hira har take ba wa Nana labarin Saleh yana gidan yari, saboda sayen kayan sata da suka yi na gwangwan an kulle shi a Lagos.

Ta tambaye ta su Barira, ta gaya mata auren Barira ya mutu, Sajida kuma tashi suka yi daga unguwar gaba Ι—aya.

Ta gaya wa Nana cewar sau biyu Hammad yana aiko mata da kuΙ—i masu tsoka, ya ce ta Ι—auki nata ta tura wa Uwani sauran.

Nana ta ce "Ni bai taΙ“a gaya mini ba ma, ha tsaraba kuma ya sake bani na kawo miki"

Ummi ta ce "Allah sarki, Nana kin sha wahala ashe dai Allah ya yi kina da rabon jin daΙ—i a duniya"

Nana ta ce "Ke dai bari, irin wanda ban taΙ“a tsammani ba. Amma wahalar da na sha sai da na yanke tsammani da samun afuwa. Sai kuma a hankali na lura da wani tsananin da na din ga shiga, shi ya din ga sadani da hanyoyin warwarewar matsalolin nawa. Na koma na din ga istigfari saboda na yi wa Ubangiji halin namu Ι—an Adam, raki da kuma gaggawa Allah dai ya Ζ™ara datar da mu" Jamila sai koma wa tayi gefe ta yi shiru, ba ta iya cewa komai.

Da suka koma gida bayan magariba, Baba ya yi ta faΙ—an Nana ga ga da aure, amma taje ta yi dare a waje.

Ta idar da sallar isha'i, tana Ζ™are wa Ι—akinsu kallo, Ι—akin da ta din ga shan azabar a Ƙaisar a cikin sa. Kawai ta tuna lokacin da ta ga bararoji na shan jinin Suwaiba. Ta kalli inda Suwaiban take, ta koma kamar wata mai shan inna, duk ta bushe ko abincin kirki ba ta ci, Ζ™waΖ™walwarta ta taΙ“u sosai da sosai.

Ba shiri ta tashi ta aika Nasiru, ya nemo mata tazargade.

Da kanta ta Ι—auki Alqur'ani ta din ga karantawa tana busa wa a ruwa.

Ta idar ta ba wa Suwaiba, ta shashashfa mata ruwan a jikinta, ta rungume ta tana ci gaba da yi mata karatun Alqur'ani Ζ™asan zuciyarta ta din ga yi mata addu'a da fatan Allah ya yaye mata wannan ciwon.

Kullum sai Sayyid sun yi waya da Nana, aka fara processing yi mata passport, da kuma visa a Nigeria.

Kwanan Nana uku, sai ga Suwaiba na iya cin abinci, Jamila ma tana cewa yanzu tana iya bacci sosai, ba tare da ana tsorata ta ba. Nana ta yi mata nasiha sosai da sosai a kan kula da ibada da kuma yin addu'a.

Yaya Atine da kanta ta wanko Ζ™afa ta zo gidan, tana bala'in Nana ba ta je ta gidanta ba.

Da ta ga Nana ba ta kula ta ba, sai kuma ta hau kame-kame tana faΙ—in "Haba ta gidana, a ce kin zo takanas bayan tsawon shekaru ba kya nan a ce, kuma ba ki taka kin je inda nake ba? Babu faΙ—a me ya kawo gaba Nana?"

"To Yaya Atine kwata-kwata yaushe na zo garin, sai a hankali ai nake zagayawa amma kin zo kina ta faΙ—a"

Nasiru ya ce "Ke ma dai Yaya Atine da fitina ki ke, ya za a yi ki zo ki rufe basarakiya da faΙ—a haka, kin ma ci sa'a da ta kula ki. Nanan yanzu fa ba wadda ki ka sani da ba ce"

"Aikuwa na ga alama, maganar ma da kyar take yi, aishikenan"

Nana duk gidansu ta rasa wanda ya ke da lambar Sarkin baka, kowa sai ya ce mata ba shi da ita.

Nana ta kira lambar Sagir, kamar yadda ta karΙ“a a gurin Alhaji Fatuhu.

Bayan sun gaisa ta ce masa kwatancen gidansa take nema, za ta zo gurin Shukura. Ya kwatanta mata ta yi masa godiya ta kashe wayar.

Tana katse kiran, kiran Sayyid ya shigo wayarta.

Ta yi murmushi ta Ι—aga ta ce "Masoyi"


Ya yi murmushi ya ce "Bayan kin tafi kin bar ni, kewa duk ta dame ni. Jina nake yi kamar maraya. Tabbas Nana ke rayuwata ce, ina roΖ™on Allah ya bamu jinkirin rayuwa mai amfani tare da ni da ke masoyiyya"


"Amin ya hayyu ya Ζ™ayyum. Ni kaina duk da ina farincikin ganin yan uwana, amma ina kewarka kai da Yarimana"


Hammad ya kalli gefensa da larabci ya ce wa Muhsin "Zo ga Ammi, zo ka gaishe ta"


Muhsin ya matsa kusa da Hammad ya kalli screen Ι—in wayar, ya kwaΙ“e fuska kamar zai yi kuka ya ce "Ammi ki dawo"


Jikinta ya yi sanyi ta ce "Haba yarimana, kar ka yi kuka ka ji, da wuri zan dawo ba zan iya jure ganin ka yi kuka ba" Ya jinjina mata kai.

"Wai zuwa ka yi ka Ι—aukko shi?"


"Eh mana, karΙ“o shi na yi aro, muka taho gida, tun jiya ma yana gurina"


Kamar ta yi magana sai ta fasa. Ya ce "Ki kwantar da hankalinki, ban kai mata Ι—anki ba, amma dole zan kai shi ta gan shi, ko da kuwa ba ta Ζ™aunarsa, amma zan yi hakan ne idan ki na nan. Ki zama cikin shiri daga kowane lokaci wataΖ™ila ta nan Nigeria za ki tafi Egypt mu haΙ—u a can"

"To ai saura kwana uku na taho"


"Eh, za a jinkirta tahowar ne, gara ki tafi ta Nigeria."


Nana ta Ι—an langaΙ“ar da kai ta ce "To ai ni ban san ya ake abubuwan ba, kuma idan na zo ina zan yi?"


Yayi dariya ya ce "Idan kin je ba Ι“ata za ki yi ba, ni zan je na taho da ke"


Sun daΙ—e su na waya, sannan ta ajiye ta shirya. Tun da Nana ta zo gidan nan abinci mai rai da lafiya ake ci sau ukun nan, kuma duk abin da aka girka har maΖ™wabta ake kaiwa. Mama ga shi tana cin arzikin nata amma baΖ™in ciki kamar ya yi ajalinta, da ba 'ya'yanta ne a wannan daular ba.

Gaddafi ma da yake ta shirin aure, shi ne yake kai komo gurin shirin tafiyar Nana Egypt. 


Ta gama shirinta, suka fita da Jamila, Baba har mamaki yake yi yadda Nana ta shiga cikin su take rayuwarta, domin shi Jamila tsoro ma take ba shi. Ita kuwa Nana abubuwan tashin hankalin da ta gani a rayuwarta, ba ta Ι—auki wata Ζ™ungiyar asiri da Jamila ta shiga da Muhammad ba.

Su na ta sallama a falo babu kowa, can Ζ™asa-Ζ™asa suka ji an amsa. Nana ta yi shiru tana tunanin kamar ya san muryar.

Yusra ce ta fito tana amsa sallamar. Tana ganin Nana ta ruΙ—e ta tafi ta rungume ta, "Ƙawata kece? Ina ki ka tafi ban sake ganinki ba, kowa na yi wa maganar ki, sai a ga kamar shirme nake faΙ—a".


Cikin mamaki Nana ta ce "Ƙawata me ki ke yi a gidan nan kuma?"


Cikin zaΖ™uwa ta ce "Ai Sagir ya dawo da ni tuntuni"


"Ma sha Allah, Alhamdillah ya gida ina Hajiya da Siyama?" 

"Su na Abuja"


"Ƙawata kin canza kamanni, kin yi kyau kin Ζ™ara Ζ™iba tubarkallah, ina mijinki buzun nan?"


"Yana Agadez. Ni gidan wata Shukura aka kwatanta mini kuma na zo na ganki"


"To ai ita ma gidanta ne, ba Maman Haidar ba? Mijinmu Ι—aya bari na kirawo miki ita, ba ta da lafiya ne ma"


Ta juya ta nufi wata Ζ™ofa, Nana ta din ga mamaki.


Jamila ta ce "Ita wannan Ι—in a ina ki ka santa?"


"Gidan da muka yi gadi, a gidan suke"


Mintuna kusan goma sha biyar, sannan Yusra ta fito, rungume da jariri a hannunta, ga Haidar ya zama saurayi Sagir kuma ya riΖ™o Shukura tana takowa a hankali.


Nana ta miΖ™e tsaye, ganin Shukura ta rame sosai ta yi duhu, tana ganin Nana ta fashe da kuka. Cikin sanyin jiki Nana ta nufe ta tana "FaΙ—in Subhanallah"


"Nana kin gani ko? Ki ka ce mini mafarki ba gaskiya ba ne ba, ni ga shi ya zama gaske Daddy ne ya yi amfani da Ι—ana ya yi tsafi, Mummyna ta mutu, ya kashe Yusuf ya kashe mahaifiyarmu da babban yayanmu. Nana ban yi dacen uba ba"


Sagir ya ce "Shukura meye haka wai? Wannan ba sirrinki bane da yakamata ki Ι“oye ba?"


"Babu abin da zan Ι“oye, Nana ta riga ta san komai"


Nana ta rungume Shukura tana kuka ta ce "Kina nufin Yusuf da Hajiya Amina sun mutu? Tayaya mafarki ya zama gaske? Waye ya gaya miki da gaske ya bayar da jaririnki, ba gaskiya ba ne"


Tamkar za ta shiΙ—e ta ce "Wallahi gaskiya ne, shi ya gaya mini da bakins, bayan ya saka an sace ni, da niyyar ya sake kashe mini jaririna"


Jikin Nana ya yi wani irin sanyi, ta tuna Ƙaisar ya ce mata aljanu na iya nuna wa  mutum abu a mafarki saboda su haΙ—a faΙ—a. Sai dai ga shi abin ya tabatta. Ta rasa tausayin wa za ta fi ji ne? Fadila ko Shukura?

Haka nan ma ta din ga rarrashinta tana ba ta haΖ™uri, tana tuna yadda ita ma Alhaji Zailani ya sako ta a gaba. Yanzu duk daΙ—ewarsa a duniya, duk tara kuΙ—in da burin tara arzikin ya tara ya tafi ya bar shi a banza, ga tonon asiri da mummunan Ζ™arshe, waΙ—anda ya bari da za su iya yi masa addu'a duk ya bar musu mummunan tabo a zukatansu, da babu lallai su iya yafe masa balle ya samu addu'a.


Ta kalli Haidar ta ce "Ka gane ni Haidar?"


Ya yi murmushi ya ce "Eh Anty Nana ce"


Sagir ya ce "Amma baka gaishe ta ba?"


Ajiyar zuciya da Shukura ta yi, ya sanya Nana mayar da hankalinta kanta, Nana ina ji a jikina nan kusa zan mutu nima, nauyin da Ζ™irjina yake yi mini da numfashi da nake yi da kyar, na san nima nawa ajalin ya zo. Ki zama shaida idan na mutu kar a ba wa kowa Ι—ana sai Yusra. Da fari na Ι—auki mugun kishi na saka a raina, amma daga bisani abin da Yusra ta yi mini na alkhairi na tabattar da ba kowace kishiya ce kishiya ba, Yusra tana da kyawun zuciya"



AREWABOOKS 




Cikin tashin hankali Yusra ta ce "Ka ga zata ci gaba ko?"


Sagir ya ce "Dan Allah Shukura ki daina maganar nan, kina ganin ba ta da cikakkiyar lafiya, tun da ba ta so ki daina dan Allah"


Nana ta matsa kusa da Yusra da tuni manyan idanunta suka tara hawaye, ta kalli jaririn hannunta, ta ce "Wannan naki ne?"


"Na Maman Haidar ne"


"Ma sha Allah"


Kawai Yausra ta miΖ™a wa Nana hannu tana murmushi. Nana ta kama hannun nata. A take ta ji jikinta ya yi sanyi.


"Haula" Ta furta a hankali.


"Ina yi miki barka da Gimbiyar Agadez, mai Ι—auke da abin al'ajabi"


Nana ta ce "Haryanzu ba ki rabu da ita ba dama?"


"Ke kin sanmu akwai alΖ™awari, ina yi miki fatan alkhairi" Ta zare hannunta daga na Nana.

Nana ta dubi Sagir ta ce "Kana nema mata magani kuwa? Ko kaima ka fi yarda da ciwon Asibiti ne yake damunta?"


Ya ce "Haka suka ce mini a gidansu, Asibiti muke zuwa ganin likita"


Nana ta ce "Gaskiya yakamata a yi mata na islamic ma"


Nan ma Nana ta daΙ—e tare da su, sosai Shukura ta ji daΙ—in zuwan Nana, ita kanta Yusra ta ji daΙ—in zuwan nasu.

Nana ta yi wa Shukura alkhairi, suka yi musayar lambar waya, ta tashi suka tafi.


Daga gidan su Yusra, kasuwa suka je, Nana ta yi wa su Jamila sayayya sosai da sosai. Su na tafe a hanya Nana ta ce "Jamila, to kuma da gaske kin iya kasuwancin saye da sayarwar da Hajiya Sa'a take yi, ko kuma ba kasuwancin ku ke ba gaba Ι—aya?"


Jamila ta ce "A'a tana kasuwancin, na iya"


"To jari nake son baki, ki je ki fara kema, na yi magana da Nasiru ma, da makaranta nake son ya koma, amma ya ce; shi gara na ba shi jari, zai fara sayar da omo da sabulai da ake yi a kasuwa. Dan Allah Jamila idan kin fara Allah ya sanya albarka, ki kula da iyayenmu. Kuma duk abin da ku ke buΖ™ata muddin bai fi Ζ™arfina ba, ki yi mini waya tun da Alhamdillah inda nake babu abin da zan ce wa Allah sai godiya. Kuma na san ba wayona ko dabara ta ce, ta sanya Allah ya kai ni inda nake ba. Kuma Allah bai tsame ni ya yi mini wannan ni'imar dan ya fi sona ba. Kuma ina fatan a cikinmu Allah ya Ζ™ara Ι—aukaka wani, sama da inda nake ni a yanzu" Jamila har da kuka, tare da bawa Nana haΖ™urin abubuwan da babarsu da su suka yi mata a baya.


"Jamila, idan Allah ya yi wa mutum ni'ima, idan ya yi gaba ba ya waiwayen baya, idan ba alkhairi zai kalla ba, ki manta komai ya wuce kamar ba a yi ba".


Jamila ta yi ta nuna wa Mama kayan da Nana ta saya musu, da batun jarin da za ta bata, amma ta kwaΙ“e baki. Nana ba ta damu ba, ta yi wa Baba Ι—inke-Ι—inke.


Gaddafi ya shigo, ya ce "Nana, mun yi waya da mijinki, ya ce bai same ki ba. Ki shirya jibi in Allah ya kaimu, jirgin Ζ™arfe goma za ki bi, zuwa can Egypt Ι—in"


Nana ta ce "Kai da wuri haka, na Ι—auka za a kai irin kwanakin nan"


Gaddafi ya ce "To ai abin da yake naku ne manya, kuna da alfarma a ko ina, ga shi nan har an yi an gama"


Baba ne ya kalli yadda Mama ke yamutsa fuska, a hasale ya ce "Wallahi Rabi idan ba ki yi wasa ba, baΖ™in ciki ne zai kashe ki. Duk da abubuwan da ki ka din ga yi wa yarinyar nan, ga shi kina ta cin arzikinta da ke da 'ya'yanki, ba ta yi muku baΖ™in ciki ba, amma da ta motsa, ta yi wani abin alkhairi ko wani abin alkhairi ya same ta, sai ki kwaΙ“e baki ko ki kushe"


"Ni kar ka yi mini sharri, me na yi wa Nanan, Allah na tuba me Nana take da shi, da zan yi mata baΖ™in ciki?"


Baba ya ce "Eh batabda komai, sai abin da yake tukunyarki ki ke ci kika yatsins fuska saboda baΖ™in ciki"


Takaici ya ishi Nana, ta tashi ta bar gurin.


****

Nana tamkar idanunta su faΙ—o, saboda rarraba idon neman Sayyid. Sai kalle-kalle take yi kamar ma dai a tsorace take.

Fararen fata da baΖ™aΖ™e, sai kai wa suke yi suna komowa.

"Kamo ta nan" Yayi maganar yana rungumota, ta zabura a tsorace.

Ya yi dariya ya ce "Matsaoraciya kawai, sai rarraba ido ki ke yi"


"Shi ne zaka tsorata ni, da na yi ihu fa?"


"Sai a yi miki dariya" Yayi maganar yana jan karan hancinta.


Ya miΖ™a mata hannu suka gaisa, ya ce "Ya mutanen Nigeria su na lafiya?"


Ya ce "Lafiya Ζ™alau Alhamdillah, su na gaishe ka"


Ya ce "Ma sha Allah, in sha Allah da mun dawo, zamu sake zuwa tare, na gaishe su"


Ya riΖ™e hannunta, suka shiga taxi suka tafi.


Katafaren Hotel ne, suka sauka a ciki, gaba Ι—aya Nana jin ta take yi, kamar ba ita ba, kamar mafarki take yi.

Ya yi order Abinci, aka kawo mata, ta yi wanka tayi salla.

Abinci kawai ya iya bari ta ci, ba tare da bata damar hutawa ba, ya ce sai ta biya shi kwanakin da ta yi a Nigeria ba ta nan.

Nana dai da ya ishe ta, kawai ta hau kuka, ya lumshe idanu yana Ζ™are mata kallo.

Ya yi murmushi ya ce "Ke yanzu dan Allah ba ki ji kunya ba abin da ki ke yi mini?"

"Kai dai za ka ji kunya, haba daga zuwana?" Ta yi maganar tana hawaye.


Ya tashi zaune yana leΖ™a fuskarta, fafur taΖ™i kallonsa, Ζ™oΖ™arin kare fuskarta take yi, amma yaΖ™i bata damar hakan. Ya ce "Ni fa zuwan nan namu da biyu, honeymoon muka zo"

"Wane honeymoon, wanda ka yi a Agadez bai ishe ka ba, sai ka dame ni, daga zuwana ni dama ban zo ba"


Hammad ya ce "Gaskiya na Agadez bai ishe ni ba, na fuskanci Ζ™anin Yarima da rigima ya zo, lokacin Yarima ai ni ake lallaΙ“awa ina jan aji. Idan kuma ba haka ba, mutum ya musa na tuno wa mutum abin da ya aikata" MurguΙ—a masa baki ta yi, tana goge hawayen fuskarta. Shi kuwa ya saka ta a gaba, ya din ga yi mata dariya.

Sai da suka shafe kwana uku, da zuwa, har sai da Nana ta manta da abin da ya kawo su, sai dai ta ci abinci Hammad ya yi rigimarsa.

Kwana na huΙ—u suka bar garin da suka sauka, suka tafi garin da malamin yake. Kafin su bar garin, sai da ya zagaya da ita ta ga gari sosai da sosai.

A can garin ma da suka je, a Hotel suka sauka, sai dai a wannan karon ta tarar da Sultan da Matawalle su ma duk su na Hotel Ι—in kowanne Ι—akinsa daban amma.

Sultan kamar ya ga 'yar cikinsa, ya din ga tambayarta ya ta baro 'yan uwanta da iyayenta.

Washegari da safe suka hau mota, suka tafi gidan mutumin.

Balarabe ne, sai dai yana jin turanci, tun da suka je gaban Nana ya tsananta faΙ—uwa.

Ya yi musu kyakykyawar tarba, sai dai Nana ko buΙ—e bakinta ta kasa yi, balle ta gaishe shi.

Ya kalli Nana cikin harshen turanci, ya ce "Sannu da zuwa" 

Ta sunkuyar da kai ta yi shiru, ta Ι“angaren Hammad ma, jikinsa sai tsuma yake yi.


Da larabci suka din ga tattaunawa, Sultan da mutumin, tana iya fahimtar abin da suke faΙ—a amma ba duka ba.


Ya miΖ™e tsaye ya kalli Hammad, ya ce ya biyo shi, da shi da Sultan.


Nana ta koma gefe ta rakuΙ“e, ta din ga tunane-tunanen da ita kanta ba ta san daga ina take yin su ba.

Gaba Ι—aya ba ta cikin nustuwarta, ba ta kuma iya tantance abin da take ji. Wani irin sanyi ya din ga ratsa ta, sannu a hankali ta din ga jin wani irin ihu mara daΙ—in ji.

Ta saka hannu biyu ta toshe kunnuwanta, ta din ga jin tamkar ana Ι“arar da kaya, ko ana kokowa da wani irin abu mai nauyi.

Har azahar ta yi, Nana ba ta ga fitowar Hammad ba. Aka bata ruwa ta yi alwala ta yi salla, aka kawo mata abinci, amma ta kasa ci, hankalinta a tashe ba ta ga Hammad ba, ga kuma yanayin da take ji a jikinta mara daΙ—i.

Sai wajen la'asar, sannan aka fito da Hammad, Sultan ya riΖ™o shi idanunsa a lumshe.

Hankalin Nana ya tashi, ta miΖ™e tsaye tana faΙ—in "Lafiya meya same shi?"

Sultan ya ce "Babu abin da ya faru, ki kwantar da hankalinki zai wartsake in sha Allah"

Dattijon nan shi ne mai maganin, ya fito ya jagorance su har wani Ι—aki.

A ciki aka kwantar da Hammad, sai ajiyar zuciya yake yi, jikinsa yayi jawur hatta gashin kansa a hargiste, rawaninsa ma da babbar rigarsa a hannu Matawalle ya fito da ita. Ta din ga mamakin, yaya aka yi haka? Me aka yi masa ya fita daga hayyacinsa haka. Sai warin wasu mayuka yake yi, da ta gaza gane kowane iri ne.

Su Sultan suka fita yin salla, Nana ta Ζ™arasa kusa da Hammad, ta taΙ“a shi, ta shafa gashin kansa ta ce "Sayyid, Sayyid ka na ji na kuwa?"


"Mmm" ya amsa da kyar.


"Mene ne, me ya yi maka?"


Ya girgiza kai ba tare da ya buΙ—e idanunsa ba.

Da su Sultan suka dawo, suka tarar da ita hankali a tashe.

Matawalle ya ce "Ki kwantar da hankalinki, zai wartsake a hankali in sha Allah. Ya ce sai dai mu kwana a nan, mu ga yanayin jikin nasa tukuna, sannan kema ya duba ki"

Kasancewar mutumin babban malamin ruΖ™iyya ne, da magungunan musulunci yana da gurin saukar baΖ™i, saboda yadda ake zuwa daga garuruwa gurinsa.

Sannu a hankali Hammad ya dawo hayyacinsa, har ya yi salla ya ci abinci, amma kana kallonsa zaka gane ba ya jin daΙ—i. Nana dai ba ta iya tambayarsa komai ba.

Sultan ya tambaye ta, za ta iya kwana da shi, ko a bata wani Ι—akin, ta ce zata iya zama tare da shi.

Ba da wani shiri suka taho ba, kasancewar ba su san za su kwana a gidan ba. Gidan Sarkin baka ne ya faΙ—o mata, da irin gane-ganen da ta yi a gidan.

Ta nemi guri ta kwanta a kusa da Hammad, ta ji ya matso da ita jikinsa, ya Ζ™anΖ™ame ta.

Kamar wadda ta farka daga bacci, haka ta ganta a Libraryn Ƙaisar.

Sai dai gurin ya Ι—an yi duhu, sheshsheΖ™a ta din ga jiyowa daga wani guri, ta tafi a hankali tana sanΙ—a. Tana buΙ—e Ζ™ofar da take jiyo sautin ta ga wani irin Ζ™aton guri, Ƙaisar na durΖ™ushe a kan gwiwoyinsa, ya saka wani abu dogo da ba ta san ko menene ba a gabansa, yana wani irin kuka. Da sauri ta Ζ™arasa gabansa, ta gefen mayafin take hango wani abu baΖ™i Ζ™irin kamar an Ζ™ona itace.

Sandar Giyaz ta gani kwance a gefen abin da yake gaban Ƙaisar Ι—in, a razane Nana ta ce "Giyaz ne ya mutu?"


Kawai Ƙaisar ya sake fashewa da kuka, yana yaye mayafin da ya rufe Giyaz. Ya yi wani irin baΖ™i kamar dutse yayi gobara. Ga wani irin tsawo mara misali da yayi, sai gemunsa da ya Ζ™ara wani irin tsawo. Nana ta ja da baya a razane. Ƙaisar ya kifa a kansa yana wani irin kuka.

Ji ta yi an girgiza ta, ta buΙ—e idonta, ta ga Hammad ya tsare ta da ido ya ce "Lafiya kuwa? Meyafaru?" Kasa magana ta yi, sai ajiyar zuciya da take yi kamar za ta shiΙ—e. Duk da jikinsa babu Ζ™wari haka ya din ga rarrashinta, yana tambayarta mene ne, amma taΖ™i magana. Da kyar ta tashi ta yi sallar asuba. Aka kawo musu abin karyawa, amma ta Ζ™i ko kallon abincin. Da ta tuno yadda Ƙaisar ya rungume Giyaz yana kuka, sai ta hawaye yana zubo mata.

Hammad ya fita daga Ι—akin, bayan mintuna kaΙ—an, ya dawo ya ce ta taso. Jikinta gaba Ι—aya babu Ζ™wari, ta tashi ta bi bayansa.

Ko su Sultan kasa gaisar da su ta yi, tana ganin Hammad ya nufi hanyar da aka bi da shi jiya, ta ja ta tsaya.

Ya ce "Meya faru ne? Mu Ζ™arasa mana" Ta girgiza kai ta ce "Kai dai ka je, ni ba zani ba"


"Saboda me?" Ta yi shiru ba ta ce komai ba.


"Ma viee, ki yi haΖ™uri babu abin da zai faru in sha Allah, magani za a yi mana mu rabu da wannan larurar, mu samu kwanciyar hankali mu zauna lafiya mu rayu kamar sauran mutane"


Ta ce "Ni ba na so" Ta yi maganar tana kuka.

Sultan ya Ζ™araso ya ce "Meyafaru ne?"


"Ni ba zan je ba, a Ζ™yale ni ba na so"


Da gaske Nana ta kafe, ta ce ba za ta shiga ba, Matawalle ya shiga ya yi wa mutumin magana. Mutumin na fitowa ta juya zata arta da gudu. Hammad ya riΖ™o ta, ya ce "Amsy me yake damunki ne?"


"Wallahi ba za a kashe Ƙaisar kamar yadda aka kashe Giyaz ba. Wallahi ba zan je ba. Da ya kashe shi gara ni ya kashe ni"


"Asma'u, kin zaΙ“i aljani a kaina da rayuwar aurenmu kenan? Ki nutsu mana"


Hammad ya yi mata magana cikin tsawa.


Tana kuka ta ce "Wallahi ba zan tsaya ba, shi ma mai rai ne, kuma yana son rayuwarsa, ba zan tsaya a kashe Ζ™aisar ina gani ba"


Mutumin ya tambayi Hammad, me take faΙ—a ne.


Hammad ya yi masa bayani, cikin harshen turanci, yake gaya wa Nana, ba shi ya kashe Giyaz ba, taurin kai Giyaz yayi shi ya kashe kansa da kansa, amma ba shi ya kashe shi ba"


"Ni dai ku Ζ™yale ni, zamu rabu a hankali, idan na bari aka kashe shi a dalilina ban yi masa adalci ba, ko ya cutar da ni ta wani bangaren bai cutar da ni ba. Ni dai kar a kashe shi dan Allah."


Sultan ya sassauta murya ya ce "Kina ji, ba kashe shi za a yi ba, za yi miki tsakani da shi ne ya rabu da ke, amma ba kashe shi za a yi ba. Wancan Ι—in ma ba shi ya kashe shi ba, shi ne ya kashe kansa dan kawai an nemi ya musulunta ko a Ζ™ona shi"


Nana ta girgiza kai ta ce "Ƙaisar kuka yake yi, an kashe babansa, ni ku bari zan yi magana da shi, yana cikin jimami dan Allah kar ku kashe shi" Ta Ζ™arasa maganar har da haΙ—a hannayenta biyu alamar magiya.

Hammad ya rungume ta, ganin yadda take neman ta fita daga hayyacinta, ga shi yana kyautata zaton tana Ι—auke da juna biyu. 

Nana tana da matuΖ™ar raunin zuciya, da tausayi banda haka ya za a yi abin da ya wahalar da ita, ta din ga wannan kukan ta ce ba za a raba ta da shi ba.

104



Sosai Nana ta rikice musu, take ta uban kuka, babu irin ban haΖ™uri da rarrashin da Hammad bai yi mata ba, amma ta Ζ™i saurararsa tana cewa ita ba za a kashe Ƙaisar ba.

Malamin ya ce su rabu da ita, su koma masaukinsu su kwana biyu ta samu nutsuwa, sai su dawo da ita.

Har suka koma masauki, Hammad bai kula Nana ba, gani yake yi kawai kamar ta fifita zama da Aljani a kansa, ban da haka ita da kullum cikin taka tsantsan take da imaninta da rayuwarta, me za ta yi da zama da aljani, aljanin da babu abin da ya yi face wahalarwa da muma azabtar da rayuwarta.

Ita ma ba ta kula shin ba, ba ta bi ta kansa ba, Sultan ya ja masa kunne sosai a kan kar ya yi mata faΙ—a, ko kuma ya ce zai takura ta.

Kamar wasa Nana abu har da rashin lafiya, zazzaΙ“i sosai da sosai, ta Ζ™i cin abinci. Da ta tuna yadda ta ga Ƙaisar yana kuka, sai jikinta ya yi sanyi, shi ma halittar Allah ne, cutar da shi ba zai kawo masalaha ba, wataΖ™ila sai ma ta'azzara wasu abubuwan.

Tun bayan tariyarsu, ba su taΙ“a yin faΙ—a ba sai a wannan lokacin.

Da daddare ma a Ζ™asa ya kwanta, ba ta ko saurare shi ba, ta haye gado duk da rashin cin abinci da ta yi, ya tsaye masa amma ya dake ya Ζ™i kula ta.

Gefe guda ta hango Ƙaisar, yana zaune ya saka wata hanya a gaba ya takure yana kallon hanyar.

Jiki a sanyaye Nana ta Ζ™arasa gefensa ta zauna ta ce "Ƙaisar" Ya waiwayo a hankali ya kalli Nana ya ce "Na'am"

Ta yi ajiyar zuciya ta ce "Ina matuΖ™ar jin nauyinka, da kuma kunyarka, ban ma san me zan ce ba, ina mai baka haΖ™urin rashin mahaifinka da ka yi".

Ya Ι—an jinjina kai ya ce "HaΖ™iΖ™a mahaifina ya so ni, so mai tsanani, duk mai sonsa to ya so ni. Sai dai bayan mun raba gari babu yadda ban yi ba ya gane gaskiya, amma abu ya gagara. Ban ji baΖ™in cikin mutuwar mahaifina kamar mutuwar da ya yi a matsayin kafiri babu ta inda zan yi masa addu'a na roΖ™a masa Allah gafara. Tabbas Giyaz shi ya kashe kansa bayan malamin nan ya takura masa a kan ya musulunta ko ya Ζ™ona kansa." Ya yi maganar cikin matsananciyar damuwa.

Nana ta rasa abin yi, a hankali ta ce "Ka yi haΖ™uri, babu wanda ya isa ya shirya wani, idan ba Allah ba, wannan ita ce taka Ζ™addarar"

Ya jinjina mata kai, sannan ya ce "Me yasa ba kya son a kashe ni? Ko a raba mu?"

Nana ta ja numfashi sannan ta ce "A tarayyata da kai, duk da akwai Ζ™alubale mai tarin gaske, amma na koyi darrussa daban-daban, kuma na fahimci abubuwa da dama. Tabbas yadda muke da mutanen kirki da kuma Ι“ata gari, kuma ku na da na kirki da Ι“ata gari a cikin ku. Kamar yadda nake yawan faΙ—a, idan ka na son ka zama mafi alkhairin mutane, ka rinjayar da alkhairi a kan sharri. Kuma bayin Allah ne, ku na taku da rayuwar Allah ya sanya mu rayu da mu da ku a Duniya Ι—aya, duk da mu na da banbancin halitta, bai kamata Ι—ayanmu ya zamana yana cutar da Ι—aya ba, ko amfani da Ι—aya gurin fin Ζ™arfi da mugunta ba. Ni dai a yanzu zan iya bugun Ζ™irji na ce a cikin halittar aljanu akwai bayin Allah, sai dai su ma ajizai ne su na aikata laifuka kamar yadda Ι—an Adam yake yi"


Ƙaisar ya jinjina kai kamar ba zai yi magana ba, sai kuma ya ce "HaΖ™iΖ™a nima tarayyata da ke na fuskanci abubuwa da dama game da rayuwa, kuma ina son baki wasu saΖ™onni da yakamata bil adam ku sani. Na Ζ™aru da abubuwa da dama ta Ι“angarenki. Tabbas ba na cikin baΖ™aΖ™en aljanu, kuma ni musulmi ne, sai dai ban tsaya na fahimci addini yadda yakamata ba, gaba Ι—aya na fi mayar da hankalina gurin burina, na sanin magunguna.

Na ji daΙ—in samun ahalinki, gurin amfani da su, domin baje kolin baiwar da Allah ya yi mini, sai da kash, Duniya Ι—aya muke rayuwa da ku, amma tsarin taku rayuwar ya banbanta da namu da cikin Ζ™iftawar idanu zamani yake canzawa.

A lokacin da ki ka zo, nake farincikin samun cikakkiyar damar ci gaba da ayyukana, ashe lokacin ilimin addini ya daΙ—e da yawaita, duk da wasu sun rintse idanunsu daga kallon ilimin, su na aikata Ι“arna fiye da ta sauran mutanen baya da suka rayu da jahilci.

Rayuwa tare da ke, ya Ζ™ara haska mini juriya a cikin Ζ™addara, da taka tsantsan da tsananta imani da Allah. Duk tsanani da zafin Ζ™addarar da ka ke ciki. Sannan kasancewaka mutumin kirki, ko mai tsoron Allah baya canza Ι—abi'ar duniya ta zama mai adalci a gare ka, ko hakan ya hana Allah ya jarrabe ka. Wasu lokutan jarrabawa ta fi tsananta ma a lokacin da ka fi tsananta addu'a.

Haka zalika idan Duniya za su taru domin su amfanar da kai wani abu, ba za su amfanar da kai komai ba, face abin da Allah ya rubuta maka, haka zalika idan za su taru domin su tauye ka da wani abu, ba za su tauye ka da komai ba face abin da Allah ya rubuta maka. Ban taΙ“a tsammanin tsakanin ke da mijinki wani ba zai mutu ba, saboda tasirin mugun tsafin da aka yi masa, ni kuma ga haushinki ina ji, ga burin Giyaz na Ι—aukar fansa a kan ki.

HaΖ™iΖ™a wanda ya dogara da Allah, Allah ya isar masa, ko ba a zo wannan gaΙ“ar ba, ni da kaina zan tafi na bar ki, na yi nesa da ke da zuriyar ki. Zan yi Ζ™oΖ™arin shafe duk wani tarihin abin da ya faru a tsakaninmu da zuriyarku, kar a samu wani ya fito daga tsatsona ya nemi sake Ι—aukar fansa. Ni kaina zan tafi inda ba a sanni ba, saboda kar wataran na ji na karaya na nemi sake dawowa gare ku, na kasa cika alΖ™awarin da na Ι—auka. Zan ci gaba da neman ilimin addini, zan ci gaba da rubutu, da kuma bincike mai zurfi a kan ilimin sarrafa tsirrai. Sai dai na yi miki alΖ™awarin zan rubuta labarinki da girmamawa, da alfaharin kasancewarki uwar gijiyata, na fito da kyawawan halaye da kuma Ι—abi'unki ababen koyi. Tauhidinki, juriya da kuma gudun Duniya. Zan yi iya yi na na kare wannan rubutu tsawon Ζ™arnuka, domin ya zama misali mai kyau ga duk wanda zai karanta. Domin zan yi Ζ™oΖ™arin nesanta kaina da duk wani abu da zai sanya na shiga harkar bil'adama.

A Ζ™arshe ina fatan ki sanar da mutanenku, darussan da ki ka koya, a tsawon zaman da muka yi, sannan ki fahimtar da su aikata ayyukan jahilici da duk wani abu da kauce hanya, saboda kana iya shukar da ba za ta fito ba wataΖ™ila sai shekaru masu yawa a gaba, a sanya wanda ba su ji ba, ba su gani ba girbe abin da ba su shuka ba, kamar dai yadda ya faru da ke. A Ζ™arshe ina yi miki kyakykywan fatan alkhairi, da fatan Ubangiji Allah ya sanya jarrabwoyin da ki ka shiga, su zame miki silar shiga aljanna, Allah ya raya miki yaronki da abin da za ki haifa a gaba ya shirya miki su. Ya baki zaman lafiya da kwanciyar hankali na har abada.

Ina kuma fatan halittun Allah su gane cewa, jinkirin amsa addu'arsu a gurin Allah, baya nufin Allah ba ya son su, kuma zafin Ζ™addara da jarrabawa baya nufin Ubangiji yana Ζ™in ka, sai ka yi duba ga rayuwar annabawa da salihan bayi.

A Ζ™arshe ina roΖ™on dan Allah ki yafe mini,  dan na san muddin ba ki yafe mini ba, sai Allah ya saka miki cutar da ke da na yi, ba tare da wata halattacciyar hujja a kan shari'a ba."

Nana na kuka ta ce "Ƙaisar na yafe maka duniya da lahira Allah ya yafe mana gaba Ι—aya, Ubangiji Allah ya albarkaci rayuwar ka ya sanya ka cikin salihan bayinsa. Ba zan taΙ“a mantawa da kai ba har abada"

"Nima ba zan manta da ke ba Asma'u jikar Lanti. Ina fatan za ki yi ilimi mai zurfi ki karanci fannin ilimin magungunan musulunci da na gargajiya "

Nana ta ce "Na yi maka alΖ™awarin haka. Amma daga nan ina zaka je?"


"Can nesa da Duniyarki, zan nemi ilimi sosai "


"Dan Allah ka tafi da Haula mana, tana matuΖ™ar sonka da Ζ™aunar ka"


Ya miΖ™e tsaye yana murmushi, ta ga ya zama wani irin dogo mara misali. Ta ja da baya tana kallonsa. Ta din ga jin muryarsa a sama ya ce "Yi haΖ™uri, kar na tsorata ki, duk suffar da ki ke ganinmu a cikinta da ni da Giyaz, ba suffofinmu ne na halitta ba, idan muka fito muku a siffofinmu na halitta zaku iya rasa rayukan ku, ko ku zauce. Mu kan suffantu da abubuwa ne da idanunku za su iya kalla. Na gode sosai da sosai uwar gijiyata ina yi miki fatan alkhairi."


"Wayyo Allahana, shikenan ko ziyara ba zaka sake kawo mini ba. Tabbas a kan ka na yarda a sauran halittu akwai bayin Allah na Ζ™warai, ba zan taΙ“a bari a raba ka da rayuwarka ba kai ma. Ina yi maka fatan alkhairi uban Ι—akina, kuma Ι—an uwana. Na san ba haka kurum Allah ya haΙ—a ni rayuwa da kai ba, duk da mu na da banbancin jinsi"


Kuka take yi iya Ζ™arfinta, Hammad yana riΖ™e da ita gam a jikinsa, sai mimmiΖ™ewa take yi tana ci gaba da kiran Ƙaisar.


"Asmyna, ki yi haΖ™uri ki daina kukan nan haka" Ta buΙ—e idanunta a hankali ta kalli Sayyid, ta kalli dattijon malamin nan, ga su Sultan a gefe duk a cikin wani Ι—aki. Ta fashe da kuka ta ce "Shi ma an kashe shi ko?"


Ya girgiza mata kai ya ce "A'a yarjejeniya kawai aka yi da shi, ya ce kun riga kun gama magana ma, ya yi miki alΖ™awarin ya tafi ya rabu da ke har abada"


"Shikenan ba zan sake ganin Ƙaisar ba? Ya cutar da ni, amma... Sai ta kasa magana ta ci gaba da kuka.

"Na sani, na san komai Asmy ki yi haΖ™uri, mu na da banbancin da ba zai yiwu ki ci gaba da rayuwa da shi" Haka suka din ga rarrashin Nana. Shi kansa malamin ruΖ™iyyar cewa yayi bai taΙ“a samun case mai rikitarwa kamar na Nana ba, domin shi kansa Ƙaisar sai da ya yi kuka ba kaΙ—an ba, kafin ya Ζ™ara tabattar wa malamin ruΖ™iyyar nan cewar ya bar ta har abada.


Kwana biyu suka Ζ™ara a Egypt, Nana sam ba ta walwala kamar wadda aka raba da mahaifinta, gaba Ι—aya memories Ι—in abubuwan da suka din ga faruwa a rayuwarta a tsakaninta da Ƙaisar suka din ga dawo mata. Tabbas za ta kasance cikin biladama masu ban mamaki da suka yi rayuwa mai kusancin gaske tsakaninsu da Aljanu.

Sai da suka Ζ™ara kwana biyun.

Haka Hammad ya haΖ™ura ya din ga rarrashinta, saboda yadda duk ta danu, domin yana iya tuna wasu abubuwan da suka din ga faruwa tsakaninsa da Ƙaisar saboda Nana.

Suka koma ta Nigeria, har da Sultan da Matawalle, suka gaisa da iyayen Nana, tare da sake jaddada musu godiyarsu, bisa ga abin da Nana ta yi wa yaransu na kulawa, tare da yi musu bangajiya na zuwa biki da suka yi Agadez.

Tun da suka koma Agadez, hasashen Hammad ya tabatta, domin kuwa laulayi ne sosai ya kada Nana.

Babban abin da yake damun Hammad, bai wuce duk yadda ya so, ya haΙ—a kan Nana da Asal ba, Nana ta Ζ™i yarda ta ce masa komai zai yi Asal ta riga ta furta mata ba ta Ζ™aunarta, kuma duk mutumin da zai nuna baya Ζ™aunarka ba ta ga abin mu'amala da shi ba. Sai dai ya ci gaba da matsa mata har ya yi fushi.

Ta ce "Sayyid, bari na yi maka gwari-gwari tabbas ina jin zafin Ζ™iyayyar da Asal ta nuna mini, amma muddin za mu din ga haΙ—uwa, ko ka ce sai mun haΙ—a kai, ba zata taΙ“a sakewa ba, zan zame mata takura kasancewar na san sirrinta, za ta din ga ganina da abin. Bana fatan zame wa kowa matsala a rayuwata, ba na fatan Asal ta rayu a takure saboda ni. Dan haka ka yi haΖ™uri ka Ζ™yale ni"

Ya gaji ya gaya wa Sultan halin da yake ciki da Nana, ya ce duk ya kai masa su can gida.

Tun da Asal ta ga Nana, hankalinta ya Ζ™ara tashi, ganin Nana da juna biyu a lokacin ya Ι—ago sosai, ga kuma Muhsin da tana ganinsa a wallpaper Hammad. Nana ta Ζ™ara cika ta yi kyau sosai da sosai.

Sultan ya yi musu nasiha sosai da sosai, tare da roΖ™onsu a kan komai ya wuce, idan ba haka ba muddin suka tafi a haka, to irin jahilcin da ya din ga faruwa a baya, na faΙ—an 'ya'yan sarakuna a baya, to kuma zai iya faruwa naku gidan, dan haka ku yi haΖ™uri ku tura komai baya. Nana sai da ta Ι—an sha jinin jikinta, ko a lokacin yanayin yadda ta ga Asal kamar gaba Ι—aya a tsorace take, duk ta kame jikinta babu izzar nan da jin kai da take yi a baya.

Suka yi masa godiya, Nana ta tabattar masa da in Allah ya yarda komai zai canza. Asal ta lura da yadda shi kansa Sultan ta Nana yake yi, yanzu baya nuna mata kulawar da yake ba ta a baya. Ta lura Hammad ne kawai ya yafe mata yake yin ta.

Duk yadda ta so share Muhsin, son da take yi wa Hammad, da kamanin da suke yi da Muhsin Ι—in, sai da ya sanya ta tsaya kula shi. Babu inda ya bar Hammad a kamanni.

Nana ba ta fasa jin kewar Ƙaisar ba, ita kanta har Ζ™oΖ™arin faΙ—a take yi wa kanta, amma sabo turken wawa, babu yadda ta iya, idan abin ya ishe ta har kuka take yi.

Jamila ta riΖ™e istigfari da addu'a, da magungunan da Nana ta bata, cikin ikon Allah ta din ga samun afuwa, a kan lamarin larura da take fama. Lamarin Suwaiba ne dai ba arziki. A hankali tana juya kuΙ—in da Nana ta bata, idan jarin ya karye ta kira Nana, ta Ζ™ara bata wani, gefe Nana tana lallaΙ“a Baba har ya haΖ™ura yake shiga sabgar Jamila. Gaddafi ma ya yi aure, ya sha tagomashi daga gurin Nana. Nana ba iya gidansu ba, hatta maΖ™wabtansu sai da suka shiga rigar arzikinta. Tana samun kuΙ—i sosai a Agadez, ga allowance Ι—in ta na sarautarta, ga na kasamcewarta matar Sardaunan Agadez. Ga shi Hammad yana sakar mata kuΙ—i sosai da sosai. Ban da tarin kyaututtuka da take samu.

Nana ta Ζ™yale Hammad yake zuwar wa da Asal Muhsin, sai dai ta tsananta addu'a. Su Tafawa suka zama ba su da wata power ko Ζ™arfin faΙ—a a ji, dan hatta dogarai da jami'an tsaron da suke tare da su, sai da aka janye musu, aka yanke albashin da masarauta take biyansu.

Hakazalika duk wani kasuwanci da masarauta ke gudanarwa, ake samun riba da Nana da Muhsin a ciki.

Watan Nana tara da sati biyu cif ta sake haihuwa namiji.

Hammad kamar ya zuba ruwa a Ζ™asa ya sha, kasancewar kaf Agadez Nana ba ta da uwar da ta wuce Nene, ita ce tsaye a kanta a kan komai. Nana ta yi mamakin ganin Asal ta zo yi mata barka.

Ahmad aka sanya wa jaririn, ake kiransa da Hamdan. Har da kyaututtuka Asal ta bayar a ba wa jaririn. Sosai take jin tausayin Asal, a zuwa ukun da ta yi ganin jaririn, duk lokacin da ta zo, daga gaisuwa babu abin da yake haΙ—a su da Nana, amma idan ta karΙ“i jaririn tana daΙ—ewa sosai da sosai tana kallon yaron.

Iya Ζ™oΖ™ari Hammad yayi, a kan mantawa da duk wani abu da Asal ta aikata, amma bakin alΖ™alami ya riga ya bushe, lokuta da dama abubuwan da ta aikata masa su na dawowa zuciyarsa.

Ita kanta a dole, take Ζ™oΖ™ari take rintse idanunta ta kawar da kanta daga wasu abubuwan da yake aikatawa, Nana ke da miji Nana ne da 'ya'ya, kuma take da goyon bayan uban miji, da masaurauta ma baki Ι—aya.

Gimbiya Bilkisu ta din ga ziga ta, a kan lallai ta haΖ™ura da auren nan, amma Asal ta ce ba za ta haΖ™ura ba.

Wataran Mahmoudu ya kawo musu ziyara, tare da matarsa, ana falo suna ta hira, yake bawa Mahmoudu labarin, darun da aka sha da Nana a kan raba ta da Ƙaisar.

Mahmoudu ya hau dariya ya ce "Wasa-wasa fa, Gimbiya akwai daru, banda ita wa yake fatan tarayya da Aljani?"

Hammad ya yi dariya ya ce "Mahmoudu sabo turken wawa, ita idan ka lura da ita ne, gaba Ι—aya rayuwarta ba ta da damuwa, kuma tana da matsanancin tausayi amma Aljanin nan ya azabtar da ita, ni kuma ga mahaifinsa na gana mini azaba, wallahi yarinyar nan Allah ne yake kare ta, da wata ce tsaf zata haukace.

Saboda azaba har a zahiri muke ganinsu, na zo da muka koma Buda hannuna na dama ya shanye, bakina ya koma gefe nikaΙ—ai na san azabar da nake sha. Ga laulayi tana yi ga jinyata. Idan na fita daga hankalina na yi yinΖ™urin kashe ta, sai na dawo hayyacina sai na ga abin kamar a mafarki. Duk yadda zan kwatanta maka azabar da muka sha mutum sai dai ya ji kamar labari. Saboda jarabar Ƙaisar da babansa aka tashe mu daga wani gida da muka zauna aka ce mayya ce. Amma sau Ι—aya Asmy ba ta taΙ“a nuna mini a fuskarta za ta rabu da ni ba, saboda ta yi imanin idan ta rabu da ni wa zai kula da ni. Amma yarinyar nan ina lallaΙ“ata ina tuna mata abubuwan da Ƙaisar ya yi mata na cutarwa sai cewa ta yi ina ruwana, lokacin da na gudu na bar ta na san me ya yi mata? Kuma ai ta yafe masa tun da ya yi mata abin alkhairi. An sha daru kan su rabu. Tana nan tana gaya mini sai ta rubuta littafi guda, a kan Aljanu saboda Ƙaisar. Tun ina kishi da aljanin nan na haΖ™ura da na gane dai duk abu ba jinsinmu Ι—aya ba"

Suka din ga dariya, Asal dai ta yi shiru, ita zancen ma tsoro ya hau bata.

Fadila kuwa ta din ga yi masa tambayoyi, a kan yadda aka yi ya zamana Nana Ι—auke da Ι—a a jikinta shi kuma Uba.

Babban abin da ya bata tsoro da mamaki, cewar da ya yi, har ciwon Ι“arin jiki yayi, da irin wahalar jinya da Nana ta yi. Ya din ga misalta musu irin yadda yake ji, idan ciwon nan ya tayar masa yadda yake jin kamar ya kashe kansa saboda azaba.


Asal duk sai ta tsargu, ta kalli fuskarsa ta ga hirarsa kawai yake yi, hankali kwance, ba domin da alamar wata manufa a fuskarsa ba.


10YRS LATER 

Muhsin na da shekaru goma sha huΙ—u a Duniya, Nana ta kammala karatunta, na ilimin magungunan addinin musulunci. Hammad ya taimaka mata, ta gina katafariyar cibiyar koyar da addinin musulunci, wata a Agadez wata a Nigeria.

A lokacin Nana yaranta huΙ—u duk maza, tana sanye da glass a fuskarta tana rubuce-rubuce, Hammad ya kira ta ya ce mata Asal ce ta kira shi ba ta da lafiya, ko za ta tura mata ko Yarima ne, idan da wani magani da za a bata kuma a bata.

Nana ta ce "Ahh me Yarima zai iya yi, bari na je da kaina".


Ko da ta je gidan kuwa, tuni Muhsin yana can, Nana ta ce "Amma maimakon ku kira ni ku gaya mini, me Muhsin zai iya yi miki?"


Asal dai ta yi shiru, Muhsin yana kusa da ita ya ce "Kawai zuwa na yi nima, na tarar da ita bata da lafiya"


Nana ta ce "Ina ganin kawai mu tafi Asibiti" Nana ta taimaka mata ta canza kaya, suka tafi Asibiti.


Likitoci suka ce tiyata za a yi mata a cire abin da yake cikinta. Nana ta kira Hammad ta ce masa lallai ya dawo, tiyata za a yi wa Asal ana buΖ™atar a saka hannu.

Ya ce "Ki saka, ba zan iya dawowa a yau ba, sai zuwa gobe in Allah ya kaimu"


Nana ta ce "To ai ba zai yiwu ni na saka ba, ko a kira mahaifinta a waya?"


Da sauri ya ce "A'a bari na kira Sultan, kuma ki tsaya ki bayar da order, kar wani ya zo a ba shi Ι—ana, idan ba ke ko Sultan ba, babu yadda zan yi na dawo ne"


Haka aka yi, Sultan ya je Asibiti da kansa ba wakilici ba, ya sanya hannu aka ciro wa Asal jaririyarta. Nana aka fara ba wa yarinyar, ta yi wata irin ajiyar zuciya tare da gode wa Allah, sannan ta kai wa Sultan ita.


Ya rungume yarinyar yana kallonta cike da Ζ™auna, ya ce "Kin ga ikon Allah, bayan shekaru kusan ashirin da aure, sai yanzu Allah ya yi ikonsa"


Nana ta ce "Tabbas Allah abin godiya, Abin da na yi ta gaya wa Sayyid kenan, ba a cire rai da rahamar Allah.

Asal na kwance a post up room, ta buΙ—e idanunta a hankali, ta kalli Nana da take ta shafa kan jaririyar. Tsawon wannan shekarun, babu wata jituwar arziki a tsakaninsu, sai dai tun kiran da Sultan ya yi musu, ya yi musu nasiha Nana ta daina hana yaranta zuwa inda Asal take.

Aka sanar da haihuwar Asal, amma aka hana kowa zuwa Asibitin da take.

'ya'yan Nana haka suka kewaye Asal da jaririyar nan, wannan ya Ι—auka wannan ya Ι—auka.

Da kyar suka tafi gida, saboda makaranta. Ƙarfe sha biyu da rabi Hammad ya iso Asibitin. Ya tarar da Nana tana shirya jaririyar a cikin kaya.

Bakinsa ya kasa rufuwa, ya miΖ™a mata hannu ta bashi, Nana ta ce "Ba tukuici babu komai"

"Zan baki idan muka haΙ—u" Tana murmushi ta miΖ™a masa jaririyar, ta tashi ta basu guri. Ya Ζ™arasa kusa da Asal yana murmushi ys rungumota ya sumbaci goshinta. Ya ce "Kin ga ikon Allah ko CheriΓ©?"

Ta yi murmushi ta ce "Na gani, kalli kamar ta Ι—aya da Yarima, duk kamar ka suke yi"

Ya yi dariya ya ce "Ba dole su yi kama da ni ba, ni Ι—in na wasa ne. Alhamdillah bayan samari da Allah ya bamu ga 'yar budurwa."


Asal ta ce "A saka mata Asma'u" da sauri ya waiwayo ya kalle ta, ya ce "Ba na son wasa"


"Da gaske nake, na ga kana sonta da yawa, ko ita ma za ta ci albarkacin son da ka ke yi wa rayuwarta, ka so ta sosai"


Hammad ya ce "Kin ga ni ba na son rigima daga haihuwar ki, ke cewa na yi ba na sonki ne?"


Ta girgiza kai ta ce "Ai ba Ζ™arya na yi ba, da na ce ka na sonta sosai, kuma ta cancanci ka so ta, na gane hakan bayan da na saurari yadda aka yi ka aure ta, da irin rayuwar da ku ka yi da kunnen basira. Duk a ajiye wannan a gefe, tsawon wannan lokacin na rayu da ci gaba da sanya ran samun haihuwa da kalamanta da suka bani Ζ™warin gwiwa. Lokacin da na dawo gidanka, babu daΙ—ewa, cikin dare na tashi fitsari saΖ™o ya shigo wayarka Ζ™arfe uku na dare. Na Ι—au wayar na duba sai na ga saΖ™onta ne, ta ce ; Albishirinka yanzu na tashi daga barci, na yi mafarkin Asal ta haihu, ana ta shagali har na tashi ina jin abin a jikina da zuciyata, ko a kusa ko a nesa mafarkin nan zai zama gaske in sha Allah, ka samu maΖ™ubaci ka bayar da nannauyar sadaka, Allah ya tabattar mana. Kuma idan mace ce sunana za ka saka"

Duk da a lokacin da naga saΖ™on nan, na cire rai da samun haihuwa, amma a duk lokacin da na tuna saΖ™on nan, sai na ji ina Ζ™ara sanya rai. Tsawon shekara goman nan, wannan saΖ™on nata yana cikin kaina, ina jin sa ina fatan Allah ya tabattar da shi. Babu wanda na taΙ“a gayawa sai yanzu da nake gaya maka. Bayan haka sanin sirrina, da abubuwan da na aikata bai taΙ“a sanyawa ko sau Ι—aya ta kalle ni ta yi mini gori, da abubuwan da na aikata ba, banda barazanar da ta yi mini, lokacin da na gano matarka ce ita. Kuma bata taΙ“a yi mini wani abu, na gadara ko makamancin haka ba, saboda ta haihu da kai ni ban haihu ba. Ko na yi yunkurin sanya wa zuciyata irin wannan tunanin Hasna da Fadila su na ankarar da ni, mussaman da Fadila ta gaya mini Nana tana addu'ar ka da Allah ya sanya mata jin wani abu a ranta, dan ta haihu ni ban haihu ba, balle ta yi wani abu da zai sosa mini rai.

A Ζ™arshe, na san maganin da ka kawo mini, ita ta sarrafa shi a kaina ta yi gwajin maganin haihuwa, kuma Allah ya amsa.

Babu riba yin adawa da mutane irinta, rayuwarta take yi kai tsaye, ba tare da Ζ™yashi ko baΖ™in ciki ba. Kuma kasancewata tare da su Hasna, suna Ζ™ara saita ni, saΙ“anin da da nake tare da miyagun Ζ™awaye.

Na san ba zan taΙ“a kai wa ko rabinta a zuciyarka ba, kuma ba zan yi maka dole ba, iya wannan jihadin na zama da ni ka yi, ya isa a kira ka gwarzo, kuma hakan ne hukuncin da ya dace da ni, kana iya Ζ™oΖ™arinka a kaina, amma ni dai ka saka mini sunanta, ba kuma na yi hakan dan na burge ku ba ne, ko a ce tsirfa ba ce, a'a na yi hakan ne saboda jin wani sashin na damuwata da ta yi kamar tata."

Gaba Ι—aya jikin Hammad ya yi sanyi sosai da sosai.

Ya rungumo Asal a jiknsa, yana sumbatar goshinta ya ce "Abubuwan da suka faru sun riga sun wuce, ki daina dawo da su. Kuma tun farko abubuwan ku ne na kishi da yake damunku, amma tabbas Nana tana da halaye da Ι—abi'u na kirki, ina fatan Ubangiji Allah ya haΙ—a mini kanku gaba Ι—aya ya shirya mini yarana".

Nana ta Ζ™wanΖ™wasa Ζ™ofar ta yi sallama, suka amsa, ta shigo da kwanukan Abinci.

Hammad ya ce "Wai gida ki ka je?"


"Eh na je na Ι—aukko Abinci ne, mutane na ta son su zo su ga jaririya fa."


"Ki Ζ™yale su, idan sun koma gida a ganta"


Har ranar suna Nana ba ta san sunanta za a saka wa jaririyar ba, aka shirya gagarumin suna a Agadez. Nana ta yi wa jaririyar nan kaya na alfarma. Kawai ta ji Hammad yana gaya wa Zahradeen wai sunan jaririya Asma'u. Nana ta yi turus ta ce "Sayyid, amma da wasa ka ke yi ko?"


"Kamar yaya wasa? Da gaske nake"


Cikin damuwa ta ce "Dan zatin Allah ka yi haΖ™uri, wannan ai rigima ce, kawai salon ka ja mini magana a garin nan, shekara da shekaru tana neman abu, ta sha wahala ta haihu kuma a saka sunana?"


"To ai ita ta nemi hakan ba ni ba"


Nana ta girgiza kai ta ce "A'a ka yi mata fin Ζ™arfi dai, Asal ba za ta yarda a saka wa yarinyarta sunana ba. Ni dai dan Allah ka canza"

Kawai ya hau dariya, ya ce "To ni yaya zan yi muku? Idan kin je gurin sunan, ki tambaye ta"


Nana ta ce "A'a ni dai na yafe, dan Allah ka canza mata suna, ya za a yi ka yi mata haka, salon kawai ka saka a Ζ™ara tsana ta"


"To ai ni ina sonki dan a tsane ki ba komai tun da ina sonki"


Da gaske Nana ta fututtuke ta ce bata yarda ba, sai da ya Ι—auke ta suka je gidan.


Asal ta ce "Dan na ce a saka wa jaririyar ki sunanki shi ne za ki ce ba kya so? Kina jin haushina kenan tun abubuwan da suka faru tsawon shekaru goma"


Nana ta ce "Wallahi ba haka ba ne ba, ba na son a yi miki fin Ζ™arfi ne, a takura miki abin da ba kya so"


Asal ta ce "A'a ni na ce a saka mata, babu wanda ya takura mini" Nana ta yi wa Nana bayani kamar yadda ta yi wa Hammad, sannan ta Ι—ora da cewa "Nana ni da ke mu na da tabon juna, da ba zai taΙ“a yiwuwa na ce sai mun yi nu'amala da juna ba. Amma ina son yaranmu su tashi da haΙ—in kai, kamar yadda ki ka kawar da kai ki ka nuna mini yaranki nawa ne. Ba na fatan a sake samun matsala na rabuwar kawuna saboda mulki ko abin Duniya a tsakanin yaranmu. Ina fatan za ki saka mini takwarar ki a cikin su Yarima, ta samu kyakykywar kulawa. Kuma ina godiya da dukkanin wasu abubuwa na alkhairi da ki ka yi mini, da Ι—aukar damuwa ta taki, duk da ba jituwa muke yi ba"

Wani irin farinciki ya mamaye ta, ta ce "Tabbas takwarata kin haife ta ne, amma ni ki ka haifawa. Kuma na yi wannan alΖ™awarin na sanya ta cikin jerin 'ya'yana. Ya hayyu ya Ζ™ayyum Ubangiji Allah ya kawo biyar a bayan ta"


Asal ta ce "Biyar sun yi yawa ai, yadda shekaruna su ka ja Ι—in nan? Ita Ι—in ma na gode Allah"


Nana ta ce "Taskar Allah babu abin da babu, ko ba biyar ba Allah ya Ζ™aro mana wasu, shekara iyanzu a ce an kusa haifo mana wasu. Na gode sosai da sosai da karamcin nan da ki ka yi mini"


Jin sunan da aka saka wa jaririya, ya janyo cecekuce sosai da sosai a garin. Da ganin kamar ba a yi wa Asal adalci.


Kwanan Husna arba'in, Nana ta buΙ—e cibiyar magungunan musulunci.


Manyan mutane duk sun halarta, har da 'yan uwan Nana na Nigeria. A daidai lokacin ta kammala rubutun littafinta, da ta yi bincike tsawon shekaru, a kan aljanu, da ilimin ruΖ™iyya da ladduban yin ta.

A cikin sunayen mutane masu muhimmanci da ta lissafo a cikin littafin, sai da ta sanya sunan Ƙaisar Giyaz.


Ko da aka nemi Asal ta tofa wani abu a gurin taron, Nana ba ta zaci za ta yi magana ba, amma ta karΙ“a ta taya ta murna, tare da shaidawa duniya, a kanta Nana ta fara gwajin maganin haihuwa kuma Allah ya amsa.

Nene ta taimakawa Nana sosai a Ι“angaren magungunan, haka Sarkin baka ya halarci taron, Hammad ne da kansa ya gayyace shi. Ya din ga yi wa Nana dariyar ba a guje wa Ζ™addara.

Nana ta yi murmushi ta ce "Na karΙ“e ta ta hanyar da ta dace ne" Nana ta yi shiru tana kallon gurin nata. A hankali ta furta "Na cika maka alΖ™awarinka uban Ι—akina"

"Nima na cika wanda na yi miki uwar gijiyata, na rubuta tarihinki da alΖ™alamin zinare a cikin kundi na mussaman da ba zai Ι“ace ba" Ta ji tamkar muryar Ƙaisar a gurin. Idonta ya sauka a kan award da ta yi da sunansa ta ajiye a gefe guda.


Shukura wannan rashin lafiya da ta yi ta fama, da damuwar da take ciki ne yayi ajalinta, Yusra ta shiga damuwa da tashin hankali sosai, sai dai ta rungumi yaran Shukura da waΙ—anda ta haifa.

Jamila ta samu wani jami'in Ι—an sanda mai mata biyu ta aura, Allah ya taimake ta, ya ware mata gidanta sai dai tana shan azabar kishiyoyin duk da haka. Ta rungumi sana'arta sosai da sosai. Suwaiba kam Ζ™waΖ™walwa ta riga ta taΙ“u haka Mama ta ci gaba da wahala da ita.


Allah Al-musawwiru, shekarar Husna Ι—aya a duniya, ta sake samun juna biyu, a dole Nana ta Ι—auke ta, ta yaye ta. Ta haifi yara biyu mace da namiji.

Nana kuma sai a haihuwa ta Ζ™arshe, ta haifi 'ya mace, duk da ba wani shiri suke yi ba, amma kan yaransu a haΙ—e yake sosai da sosai. Nana tsaye take a kan tarbiyya da kuma ilimin yaran mussaman na addini.


Hatta garin Buda sai da suka amfana da Nana, dan ta sai filin da kukar Lanti take, filin da kukar da aka yi wa Lanti girka, aka buΙ—e islamiyya. Sannan duk shekara suna samun abin alkhairi na kayan masarufi mussaman da azumi.


Ummanta duk ta aurar da Ζ™annenta mata, Imrana bayan ya kammala karatunsa, ya yi zamansa a faransa, sai da Nana ta matsa masa da batun aure, sannan ya ce ta samo masa duk wadda ta yi mata zai aura.


Suka rayu cikin kwanciyar hankali, da son juna. Ta samu kulawa da tsantsar soyayya daga miji, yaransu gaba Ι—aya suna matuΖ™ar sonta da Ζ™aunarta. Husna kuwa tamkar babbar 'yar Nana. Yayin da Yarima yake Ι—an gurin Asal.

Ta shiga cikin mata da aka sanya sunansu a kundin tarihin Agadez.

Ta rayu cikin aminci da nutsuwa, a rayuwar da sai ta so ta yanke tsammani saboda gwagwarmaya. Sai Ι—an sauran Ζ™alubale da faΙ—i tashin rayuwa da ba a rasa bawa da shi.



A hankali ya yi ajiyar zuciya, ya kalli matashin da yake zaune yana saurarensa, ya ce "Ka ji labarin Gimbiya Asma'u, to kai ma shigen abin da ya faru da su ne yake shirin faruwa da kai"


Ɗaya matashin ya ce "Allah ya yi mini tsari, idan kuma ni ban taki irin wannan sa'ar da Nana ta taka ba fa? LallaΙ“awa zan yi na bi dare na gudu na bar garin nan, sai ta koma bin wani. Haka kurum mahaukaciya ta liΖ™e mini ta din ga bi na"


Ɗayan ya kwashe da dariya, ya ce "Dan Allah kar ka yi haka. Yau wuni ta yi a Ζ™ofar gidan ku, an bata abinci ta Ζ™i ci, Yaya kawai take faΙ—a, dan Allah ka je ka bata Abinci kamar ma ba ta da lafiya"


"Kai wallahi ba zan koma ba hauka ake yi, idan ta gaji ta Ζ™ara gaba ta nemi wands za ta bi"


*Tofa, ko su kuma wannan matasan suwaye? Waye wannan aka ba wa labarin BUZU da Nana, shi kuma wace mahaukaciyar ce take bin sa. Sai mu tara a gaba a cikin jerin littattafan da za su zo muku daga alΖ™alamina nan kusa ko a gaba*


(WaΙ—anda suka gaza juriya, a farkon littafin da ganin na matsa rayuwar Nana a farko, ina fatan a Ζ™arshe kun fahimci abin da nake son ku fahimta. Ba kowace Addu'a Allah yake karΙ“a a take ba, ya kan jinkirtawa bawa, ya amsa masa lokacin da ya fi dacewa. Annabawan Allah misali ne a kanmu. Har kullum ina fatan zamu din ga kamanta wasu darussan da muke karantawa a littafi, da rayuwarmu ta zahiri, hakan ne zai sanya a Ι—auki gyararrakin da yakamata.)



TAMMAT BI HAMDILLAH. KOMAI NISAN DARE GARI ZAI WAYE. ALLAH YA KAWO MU ƘARSHEN WANNAN LITTAFIN LAFIYA.

DUKKAN YABO DA GODIYA DA JINJINA DA KIRARI SU TABATTA GA BUWAYIN SARKI GAGARA MISALI DA YA BANI ARON RAI DA LAFIYA, NA KAWO WANNAN LITTAFIN BAYAN SHAFE TSAWON SHEKARU BIYU INA BINCIKE A KANSA. INA ROƘON ALLAH ABIN DA NA YI NA KUSKURE YA YAFE MINI.

GODIYA TA MUSAMMAN GA TEAM ƊIN BRIGHT PENS 

Aisha Adam Ayshercool 

Zainab shehu kumurya

Na'ima Suleiman

Nazeefa sabo Nashe.


Ƙungiyar YOUNG TALENTED WRITERS ASSOCIATION YOTA. 


Godiya ta mussaman taki kekaΙ—ai

Amanar Cool


Sai kuma gaisuwa ta mussaman da godiya, bisa taimakawa bincikena da ku ka yi.

Maryam Muhammad Mum amnash

Dr. Salihu Nura Adam (Salihan nur)

Fatima A abdou Nijar

Da ma kafatanin marubuta baki Ι—aya.

Hakazalika ina godiya, ga masu gyara, sharhi da shawara Ubangiji Allah ya saka muku da alkhairi ya fi ni yabawa.


Na gode sosai da sosai, da jimirin bibiyata, ina roΖ™on Allah duk wanda ya karanta littafin nan, ko ya Ζ™aru da wani abu, ko bai Ζ™aru ba Ubangiji Allah ya tabattar da zukatanmu ni da ku a kan Imani.


Ina miΖ™a godiya sosai da sosai, ga waΙ—anda suka kasance tare da ni a tafiyar nan, tun daga telegram har AREWABOOKS.

WaΙ—anda na yi wa kuskure, ina mai baku haΖ™uri, saboda Ι—an Adam ce ni, mai ajizanci.


Wanda ku ka sarrafa mini littafi, ta wasu hanyoyi ba da izinina ba, ba a yafiya ranar lahira.


Wanda kuka karanta mini baku saya ba, ga account number na zan saka, ku bani hakkin wahalata na wata shida, akasin haka ina muku tuni da duk mai son ci gaba a nasa neman, baya yi wa wani mugunta. Kuma hakkin wani komai Ζ™anΖ™antarsa na iya kawo maka naΖ™asu a naka neman. A saka mini hakkina dan Allah, ko na bar mutum da Ubangijin Musa da Harun, ubangina ubangijinku.

0069685771

Aisha Adam stanbic bank.


Sai mun haΙ—u a littafi na gaba, idan Allah ya bamu aron rai d