ABUNDA KE BOYE BOOK 1 CHAPTER 1 HAUSA NOVEL

wajajen yamma liss daga asibiti ayayin da na’urar E.C.G ke famar kara wata siririyar hawaye guda daya ta sulalo daga cikin idon Zainab Arifah ba tare

 







⏯️4️⃣1️⃣

wajajen yamma liss daga asibiti ayayin da na’urar E.C.G ke famar kara wata siririyar hawaye guda daya ta sulalo daga cikin idon Zainab Arifah ba tare da ta farka ba, kusan ba'a cikin hayyacinta ba tafara wani irin gane ganen mugayen halittun aljanu masu muni da matukar tsoratarwa tareda gigitarwa dakyar da wahala ta kwaco hanklinta duk dama time to time haka zakana tana yawan razana ita daya..


zazzabin ne me tsananin zafi yake yawan rufeta ta ciki haka za tay ta ɓarin sanyi, saida har tay kwana biyu akwance anan asibitin amma ba agane meke damunta cos duk dama tana jin zafin zazzabin amma duk na'uran gwaje gwaje yakan nuna musu cewa lafyarta kalau ne gabaki daya kan likitoci yabi ya kulle sosai...


babban asibitine da kwarrarun likitoci it was hard for her to believe its imcompetnce ace tanajin ciwo ajikinta snn ace wai ba aga komi ba, gashi ta hana sam a kira babanta sbda tanaso ne ita ta fara fahimtar abunda dake damunta kar ya kasance matsalarta da ibaad ne.


arana na biyun ne nala ta kirata awaya da zimman zata shimfida mata karya akan batun sihiri da sukaje yi kamar yadda ta shirya...


saidai ko samun daman furtawa batay zainab arifah ta tsareta da labarin abubuwan dake faruwa da ita da irin mafarkin datakeyi da kuma razana datakey sosai,..


bakaramin faduwa gaban nala yayi ba tace zata kira Ani qompas taji me ake ciki, after like one hour da yin wayansu nala takira zainab da rudani aranta tace mata kawai tabar asibitin taje gida ciwon bana asibiti bane Ani qompass tace zata duba musu abunda ke faruwa nan. babu shiri zainab arifah  ta tattara inata inata batama jira sallama ba ta kira drivernta aka kaita gida, she took a break from class, cut contacts, tay ma babanta karya cewa zataje boot camp a singapore har sai ta dawo zata nemesa.


tunda kuwa tay wann karyan ta dawo gida jikin ta ya zama babu kanta, dan tamkar asbitin ma yafi mata sauki dan agidan nata ne komi yafara mata afresh aljanu suna hanata baccin dare, hka kawai saitanajin motsi ko tanajin dariya, ko taji ana kiran sunanta abayan labule, koda kuma ta samu baccin daga ta kashe lamp sai taga an sake kunnawa..


she remain very scared nd traumarized lamarin daya jawo nala tazo UK tafara jawo ta cikin shaye shayen kwaya dan ya bugar da ita tana samun bacci.


rukayya kuwa tunda ta wuce dubai bata sake kiransu awaya ba, she just ghost them, gabaki daya sukuma sun bala'in tsorata sun gigice, sunkira Ani gompass yafi sau akirga amma shiruuu ba a dagawa gashi mahaifiyar nala ta dada tsoratasu, ta dinga musu masifa tace meye kaisu har wajen manyan matsafa? da ma wani local boka kawai suka nema ya musu aiki amma zuwa har can nepal dolene akwai consequences, koda kuwa aikin yayu.


sukam ma gabaki daya suka bar batun wani magani aka dawo neman wa zainab arifah mafita, dan tunda ta aje kaskon ranar shikenn ciwo ya nadeta waje guda bata kara maganansa ba, nalan ce kawai tazo suna zama tare sunajira desprately suji me Ani gompas zatakira tace musu, shiru shiru har suka ci sati guda zainab arifah gabaki daya ta dawo wata abar tausayi kullum sai tay kuka ga tsoro ya kamata sosai gashi tasha kwaya da kayan maye sosai wai danya cire mata tsoro ko yasata bacci har taji babu dadi.



karatun ta da walwalan ta gabaki daya ya tsaya cak, da tsananin damuwa tafara tunanin kawai gara ta kira gida tagaya babanta komi karta mutu ba asan asalin meya kasheta ba.


suna kan wnn rikicin da nala har tay bacci, on the 8th day sai tay mafarkin cewa drwer inta inda ta aje kaskon yana ci da wuta wutar kuma har ya kama mata jiki da wani irin balamammen tsoraccen ihu da firgici ta farka saida nala dake bacci agefenta tay wani wawan tambul ta rikoto akasa amugun tsorace tafara ihu tsakar dare.


"zainab..zainab lafya "meye haka?? jikin zainab na rawa rawa cikin tsoraccen kuka ta sauko akan gadon da sauri t tana kuka me cin rai tace nala wallah wallah i regret following ur advice wann wani irin tashin hankali ne for god sake what is happening to me... ur evil magic ppl are traumatising me..


nala zata riketa tay wani kukan kura tawanka mata mari a rikice tana kukan sosai,


da mugun fushi ta juya zata bude drawa ta dau passport dinta ta kama hanyar airpot a daren danta dawo gida tana budewa sai taga sholl babu kaskon data aje.


wani cak kukan ya tsaya mata ta daga ido a mugun tsoroce ta juyo hawauynta na zuba bakinta na rawa rawa ta kalle nala tace "na...n...n..nala The clay pot is no longer here sun dauke abunsu, .


da sauri nala ta karaso wajen tace "but dats...impossble!

arikice zainab arifah tace wallah anan na aje shi anan na aje ranar, nala tace a'a maybe ure just confused baridai mu kara dubawa..


ahujajan suka hau birkita waje tsakar dare wajajen karfe uku da rabi suka haukata dakin da dube dube saida suka leka ko ina basu gani ba..


nala tace tabbas bacewar abun nan ne ya jawo musu wann buhun bala'i atake atake sai suka laka ma masu aikin gidan laifin komi..


maids suna bacci sukaje suka daddasa musu mari suna masu tuhumarsu inda kasko yake..duk sun rikice sun ma manta da cewa rukky tazo kowa yay rantsuwa yace bai dauka ba.


Haka har safiyar ranan yay zainab da nala suna ci mata mutanen nan mutunci jira ma suke safiyar yagama washewa su mika su wa police sosai suka razana maaikatan gida har mai gadi basu kyaleshi ba


suna cikin wann rikicin ne Ani gompass ta kira, sukaje daki nala ta saka musu a handsfree tace musu basu suka dauka ba, kuma anyi musu wasa ne da aikinsu shiyasa aljanun da akayi binding sihirin dashi suke bibiyarta dan haka ta nemo wanda ta dauki abun sunan ta kawai ake bukata kuma har sai ta nemota kafin nan su samu sauki.


bakaramin rudewa zainab arifah tay ba, musmn da ta san wai zuwa gidanta akay aka dauki kaskon nan, ranar wuni sukayi suna bincike, boyayyer CCTV footage na jikin flower vase a dakin wanda ko nala bata san dashi ba shine ya nuna musu zuwan ruqayya dakin da daukarta da duk maganan da tafada.


jikinsu yana rawa rawa suka kalle juna yau bakaramin mamaki suka sha ba, dan gabaki daya a rayuwa basu taɓa kawowa cewa rukkaya zata iya aikata haka ba, cos she always appear yar baruwanta kuma yar gaskiya itace me bada shawara me kyau me gayan musu gaskiya.


kai tsaye nala ta gane cewa Rukky tana son ibaad ne shiyasa ta furta wancan maganan ita kuma zainab arifah tace sam kishi da hassada ne rukkyn ta rike ta dashi...


tunda suka gano bakin zaren suka kira Ani gompass suka gaya mata sunan rukkyn sai a sann Arifah ta dena jin wasu abubuwa ajikin ta duk dama taji zafin da tay asarar kudinta da lkcinta sosai.


Ani compass tace ma nala dama babban curse ne rukky taso tajawo ma zainab arifah data ƙona abun, sam sam bataso data kona ba, cos burning a magic is d same as destroying the spell forever dan bazata iya sake hada mata wani ba. nala bata ji dadi ba but atleast she thank God da bata gaya ma zainab arifahn Amfaninsa ba dan tasan da bakaramin bura uba zasuyi ba dan zainb arifah bazata taba yarda ace mata only chance inta na samun soyayyar ibaad kenan aka mata asararsa ba


she kept lying to her, tace mata ai yanxu maganan aiki ya dan tsaya kawai su dauki revenge akan rukky su san meyene  asalin manufarta na sace ma zainab kasko...


hassada da kishi ne ko dagske ne akan ibaad ne...dakyar suka samu nitsuwa, bayan kwana biyu suka harhada tarko sukata bincike har suka san inda taje haka suka dinga spying har saida suka san yadda zasuy ta dawo tun hutunta bai kare ba sabida zainab arifah ma tanakan shiri zata koma gida hidimar mika mata kujera da babanta yace zaiyi..


shafewar basira yasaka Rukky ta dawon kuwa after a day of convincing, taci kwlliyarta ran asabar da yamma liss tazo gidan zainab arifah, but dake zainab din bata da hakuri, tana zuwa tafara daddaure mata fuska, haka sukaje can sama  saman balcony inda babu kowa daga su saisu dama kuma sunyi niyyar daureta ne da igiyaa su mata lilis sai ta fada musu gaskiya, but zainab decided to question her akan ko dagsken ibaad take kauna. 


suna hawa sama taga sun sakota a tsakiya nan aka fara magana tun anayi cikin habaici ya dawo baqaqen maganan suke jefawa junansu sosai


rukky tanata so ta juya maganan akan nala, she was busy insinuting cewa ai nala ce take zama da ita ba tsakani da Allah ba snn nala ta tsaneta tana kishinta aboye..


koda zainab ta nuna mata videon abunda ta sace mata sai bakinta ya mutu she have no choice bakinta na rawa  tafara tono asiri ta gaya mata gaskiyar cewa karyafa nala ta mata bokan nan cewa tay bata da future da ibaad kota auresa is going to be her karma nd misery kuma nala is only after her money.


tunda rukky ta saduda tay tone tone snn tay admiting cewa she was also obssessd with ibaad kuma yafara ne tun ranar da tafara ganinsa lkcin da suke ss1 da prof ya dinga matsa masa yana zuwa schll dinsun dauko zainab a makrnta idanun zainab arifah ya balain rufewa da mahaukacin kishi da zafin betrayal


she was begin zainab cewa wallah ita iya abunda yake damunta aranta kenan amma bata tsaneta ba kawai ibaad take so kuma shiyasa ta fasa kaskon sihirin nan.

 

gabaki daya ita kuma nala ta haukace da bori tahau kara wuta ta zuzuta maganan tace wallah karya rukky takey tana shifting blames ne dan tanaso ayafe mata, they kept accusing each oda agaban zainab


itakuma zainab baqar kishi da haushi ya rufe mata ido, ynxu cewa da rukky tay tana son ibaad yafi ci mata rai fiye da komi bata batun nala take yi ba. kan kace wani abu suka kama dambe duke duke suka taru ma rukkyn akai... 


agarin zata fixgota a hannun nala tay wani irin loosing balance cikin kiftawar ido da bismillilah ta tureta tun daga saman bene rukky tasa wani irin ihu jin tafara rikitowa daga gidan sama zatay kasa caraf ta rike rigar zainab arifah  tana ihu tana cewa help me zainab pls help me..


wani irin kallo zainab ta mata azafafe tace 'help u? ai wallah  saidai ki mutu rukky, i trusted u but u stab me at my back, da abokai irinki gara in mutu ko inje mana ina kwana da macijin dana san sareni zaiyi wata rana, wawiya kawai butulu, inda asrinki be tonu ba danima kasheni zakiyi akansa kenan..ba ibaad kikeso ba? toh saikije lahira ki auresa..


idonta a rufe da fushi ta kara hankadeta tace 'he is mine..


da wani gudu nala ta miƙe daga kasa zata hana zainab karasa ture rukky kasa amma inaaaa kafin nala ta karaso harta fincike riigarta da karfin tsiya tare da kara hankadeta da hannu cikin kiftawa da bismilla sukaji saukar ta akasa gwaraf aikuwa sai gawa...


wani irin tsoraccen ihuuu nala tay tace "what did u do?..u pushed her, u killed her...wayyo Allah mun shiga uku


arikice zainab ta dago kai sai kuma jikinta ya fara tsananta rawa rawa tama rasa me zatace suka sauka kasa da gudu Allah ya so su bayan gidan ne taciki inda babu kowa.


suna zuwa kasa suka gan rukky laying on the ground cold dead dan kuwa kanta tafasa 


rungumar juna sukayi sukasa ihu zainab taje arikice zata taɓata dan ta tabbarta nala ta janyeta da sauri cikin rikicewa da ihu tace dont touch a dead body are u insane???? 


zainab arifah tana kukan firgici duk ta gama rudewa tafara tambayarta me zasuyi dakyar suka nitsu, gashi yamma ya fara rufawa sosai jinin rukky yana malala akasar wajen sosai.


bata da yadda zatay she just called her dad tanata kuka kuma a mugun tsorace ta gaya masa they got into a fight with rukky kuma ta tureta amma ta fado ta mutu mata a agida.


yanacin abincine amma da wuri ya bari ya miƙe tsaye yace 'what??  nala ta amshi wayar ta kara masa bayani atake atake yace musu kar su sake suje kusa da gawan su matsa gefe su tsaya har saii ya turo mutane...hakan kuwa sukayi, bada jimawa ba wasu gardawan maza sukazo da plastic bag suka dauke gawan rukky aka clearing duk wani tiny evidence cikin daren suka discarding bodyn rukky, aka goge traces na waya, he had alot of ppl dat are doing a clean job for him that night dan kawai ya kare rayuwarsa dana yarsa cikin gaggawa



before morning rayuwar 

ruqqy ya zama tarihi with no traces of her, nd her last knwn location was shifted to be dubai, call history, chats, komi aka cire na ranan da kisan ya faru yay kamr sunyi sati biyu basuy magana da su arifah ba



ranar ko bacci basuyi ba dan tsoro, gashi babanta ya zare mata ido yace maza maza ta dawo cikin hayyacinta ta koma yin rayuwarta normal kar tasa ayi suspecting inta snn yay assuring inta cewa inhar yana raye babu abunda zai sameta har abada


dake bata taba kisan kai ba Abun ya taɓa mata kwakwalrta sosai, nala was forced to stay with her, tun bata saba shaye shaye ba ya zamo ita dakanta yanxu take sayan kwaya su sha sosai suje clubs dan su mance da komi.


in oda to make thing less suspicious shima baizo US din ba, mamanta ma batazo ba, itama basu barta tazo nigeria ba..nan baban nata ya daga duk wata hidimar da zasuyi na bata kamfani akan har sai abun yafice mata aranta kafin su dawo da rayuwarsu normal.


shakuwa mai karfi ya shiga tsakaninta da nala within this days duk dama aranta tana tuna maganganun rukky time to time, daga suje england sai su zauna manhatan, yawan shaye shayen kwaya yasaka tuni suka fara mancewa da abubuwan da suka aikata. 


within a month suka hada babban party awajen da rukkyn ta rasu time to time haka suke zuwa gidanta suna nemanta gashi dama rukky bata da mahaifi mum dinta ne kawai me bala'in kudin, for one good month ana nemanta until rukky was declared missing in dubai with no traces of her where abouts.



daga nan nigeria kuwa ibaad yana cikin watan sa na hudu dafara bautar kasa su ayaana suka yi jamb result din ta ya fito taci sosai so he gifted a sport car key tsakaninta dashi amma basu nuna ma kowa ba kawai hoton motar ya nuna mata da zimmn tana gama schll din gabaki daya sai tay deciding intanaso akawo mata nan gida saiya kawo mata, she was soo happy da wann babn kyautar, her first car was given to her by her love..shakuwa me yawa yana dada ninkewa acikin kolulwar zukatansu


bayan nan suka fara rubuta waec dinsu, Wann lkci ne kuma uncle moh ya sako kai sosai shima, ynxu baya ma fiye boyewa har hajya mairo tay kamar zata gano meyake nufi amma dai tay shiru ta zuba masa ido batace komi ba. 


week din da zasu gama waec din ya zama wata guda da kusan sati biyu kenan da mutuwar rukky a hannun arifah. su hajiya mairo suna zaune aka aiko musu katin gayyata wajen hidimanta wanda za'ay ne agidansu ranar asabar mai kamawa.


kowa yanata mamaki dan prof bai taɓa gayyatar su gidansa ba sai gashi da zai naɗa yarsa akan kujera yau ya aiko musu gayyata har gida wann abu bakaramin dadi yay ma hajya mairo ba cos she secretly wishes yaranta su hada kansu yadena ware yan uwansa sabida abun duniya


Haka ta taro meeting tun daga kan bappa zaidu tace dole ne kowa saiyaje wann hidimar zainab da za'ayi ko dan a karfafa zumunci.



atake atake tasaka aka fara shirye shiryen abubuwan gudumawa da ire iren abincin da suma zasu kai ranar


week din ibaad yaje UK duba gidansa, ranar kuma ayaana suka gama waec tana fitowa kawai tazo taga uncle moh yazo har schll dinsu  tsabar kunya dataji duk wani abu daya kawo bata iya karba ba sabida kowa daukawa yay ko babanta ne ma


da girmansan nan duk wani shirmen red rose da bonquet da akewa yan mata haka shima yaje ya jajibo, safiya kuwa suna isowa gida tsabar kishi ko cire uniform batay ba taje ta gayama anty safeerah komi da yafaru. 


tun daga wnn ranar anty safeerah ta fara mugun daure ma ayaanah fuska har takaiga inba a cikin mutane ba bata amsa gaisuwarta bare tay mata wani magana


da ita da safiya suka sako ayaanan agaba da silent anger turned into pure hatred..hutun sati biyu ne tsakanin Waec da neco gashi ibaad bai dawo nigeria ba bare taji sanyi tasan kuma dole zaijeshi wajen jamal ko farhan, kuma bata isa taje gidan ammi babba wajen sultana ba haryau dai Ammi babba can't even stand her. saidai suyi waya, ko in zataje gidan tare da hajy mairo.


ganin kowa ya daure mata fuska agidan yasa ta maida hankli wajen zuwa shagon hajy kullum sai ta bar musu gidan taje ta wuni acan tana kan koyan abubuwa masu amfani, but still hanklin anty safeera yana kanta, she is secretly spying on her, takan sa mutane awaje suna dubawa ko in ayaana taje shago mijinta yana zuwa wajenta hira dan haryau bata gama gane meyake nufi akan ayaanan ba.


ranar da safiya ta kawo mata gulman ma bakaramin habaici ta masa ba amma sai ya nuna cewa ai ayaana is exceptional shiyasa yake mata haka...


tun kuma aranar ta nuna masa she is no longer okay with relshp dinsa da ayaana tunda ayaanan ta mallake hanklin kanta yanzu, kuma gasu bappa zaidu, su ammi karama da uwa uba ibaad suna kulawa da ita. kuma ai su basa yin abunda shi yakeyi..sosai ya lura cewa da anty safeera ta fara ganosa but he just ignored her ya maida abun wasa sai bata kara cewa komi ba ta kyalesa tacigaba da saka ido ma ayaanan kuwa sosai.



Satin ayaana daya da fara zuwa shago zainab arifah da kawarta nala suka dawo nigeria aka fara shirye shirye, yanxu tana shan hard drugs, zaka sha mamaki yadda ta dawo big girl kamar ba ita ba

but deep deep inside her brain is soo damaged da guilt na abubuwa dayawa da suka faru.


yanxu haka bata da lafyar kwalkwalwa sosai she is living with a supressed mental depression wanda yake fara kkrin dawo mata full blown schizoprenia tunda tay kisan kai innn, amma fuska da hali normal mutum zaka ganta burbbling nd alwys hot like nothing has ever happend to her. ciwo brain inne kawai yake damunta aboye amma ynxu bata iya tuna komi data aikata



kusan kullum ayaana tana tare da ruthy a restaurant in hajiya but dabiun ruthy yanzu ya sauya bakamar da can ba, dan hiran da sukeyi ma duk ta dena tafara shiru shiru saidai suy aiki a rabu,..


sosai ayaana tazo ta fara gane cewa kmr ruthy tana cikin wani matsala da damuwa kuma kamr matsalane ta samu da abokanta da suke ankon jan kaya, saidai ko ta tambayeta bata gaya mata komi saidai tace mata stress ne yanxu bata da saurayi she barely have sex shiyasa batajin dadin rayuwa. 


jin maganan ruthyn ya fara ma ayaana nauyi sai ta kama kanta tama dena tambayartan.


alhaj ameer dake kkrin kara aure dake ya saki first wive dinsa zai karo wata haka ya tsaya ma uncle moh a wuya akan lallai yay inviting ayaana suje dinner awani waje kawai yay proposing mata batun aure.


shikuma anan yagama lura da anty safeera yanxu ta hankaro gabaki daya baison ya kunna wata hayaniya yanxu duk dama niyyarsa kenan yaga ya gabatar da niyyarsa ma ayaana cikin satin nan


ana saura kwana daya hidimar zainab arifah ibaad yay dawowar cikin dare dake ranar friday ne anan agida wajen amminshi kawai ya sauƙa 8:30pm bayan ya gama gaiswa da kowa ayaana takai masa abincin data dafa masa har dakinsa suka ci tare snn suka sha soyayyarsu me sanyi da saka nitsuwa har wajajen 10;30pm snn ya sallameta taje daki ta kwanta suna chating akan hidimar gobe..


he asked her if he can take her out on gobe da yamma bayan hidimar zainab arifah sabida prince hassan zaizo da wife to be insa yasmin zasu halacci wani taron siyasa na babanta a kano nd he invited them tunda sune kawai close mutanensa daya sani a garin kano..babu tantama ayaana ta amsashi da eh at same time taga sakon uncle moh he is also requesting if they cud meet sumwher else on sunday evening sai tay ignoring bata amsa ba tay maza ta share saqon suka gama chat dinsu da ibaad tau addua tay bacci



washe gari gidan ya tashi a rububi, ahalin bappa zaidu da sassafe sukazo haka anty safeera tay ma sultana da safiya wata mayyar make up professional standard amma banda ayaana, yau bakaramin kyau su sultana sukayi ba.


hakan kuwa ko kadan bai dame ayaana ba dan tasan ibaad baiya ma son ta fiye fenta fusksrta sosai dan haka sama sama tay nata make up, dayay balain fito da glowing natural beutynta, koda ta fito kowa saida ya kalleta anfita kwalliya amma ko kadan ba fita kyaun fuska ba. dukansu tsadaddun laces suka saka su ammi ne kawai suka saka manya manyan atampopi masu bala'in tsada da kyau , ammi karama tasha mamaki yadda su anty safeera da ammi babban suketa wani nuki nukin boye kayan da suka siyo irinnata awajen mum ramlat collection dariya ma abun ya bata sosai


#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[09/12, 20:48] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️4️⃣2️⃣

9.30am prof zayyanu almansur's residence.


Cikin Wani babban decorated hall wanda daga hangen kyaun wajen kasan if you're not in the first social class bazaka zo wajen ba, kyale kyalen dresing da kamshin turare dake tashi kawai ya isa ya bayyana maka cewa ba kananun mutane ne zaune a wajen babu abinda ke mamaye da wajen yake kuma dauke ido sai Top nocht party decors musmn ma kyalkyalin golden tabards da Hefty electric flower present da kuma pure white royal seats na VIPS wanda suke baza kyalli kmn ba'a taba zama akansu ba.


The floor is lined with red carpert a tsakiya gefe da gefe kuwa angama basa hakkin sa wajen lailaiya shi da vintage rugs daga samansu eight bright chandeliers na haske da ganin wajen baka isa ka shiga ba sai kana wane ko Dan wane


hidimar nasu na few friends and family ne babu hayaniya, dan haka matasa sun kai su tara agefe sai hira suke suna dariya kowa kagani awajen is cute in his or her own way wasu farare,wasu exremely white wasu kuma chocolate wasu dark they all look cute acikin designer suite and toxidos da gowns na da half jumpas designer wears duk sunyi mugun kyau kaman su suka zabe kansu.


duk wanda zaka gani yana rike ne da wani irin customised red disposable cup irin mara nauyin nan and they're all chilling ana jiran saukan manyan iyaye time to time ana daukar hotana, manyan Mata suka saka atampopi da leshuna tsadadu wasu matan kuma da yan mata kuwa duk an bi layin turawa ne an cake da stylish designer gowns fuskan nan tasha make up an kwalkwaleta.


jin kadan babban filin gidan ya fara cikawa da varieties of xclusive Convoys of cars duk irin Manyan manyan jiga jigan yan business men of the top forbes list kowa ya sauko ne da securities dinsa da familyn sa wankan su is filled with class da hadaddun yaran su masu ilimin business dana zamani.


Tuni taro ya fara bada ma'aana inda party ogarnisers sukayi assorting kowani babban mutum awajen daya dace dashi, wajen zaman yan kasuwa maza da mata baka jin komai sai surutu is like thy r dyieng to meet each oda kowa nada abunda yake burin cimmawa na samun karin cigabansa arayuwa.


masu saida kwayayi kuma da duk wani mai illegal business sune kamammu sun zauna kim kamar qumaka sai saa saa zagaka suna magana nd u wudnt wan to hear what they are saying cos thy look so wicked nd tyrannical babu komi acikin ransu sai kudi da power da lamarin daya shafi kisan kai ko binne asiri.


Hidima ne daya amsa sunansa hidima aka hadawa zainab Arifah domin nadata wannan babban matsayi, She is going to be the youngest CEO of almansurs fin tech holdings na U.S branch

 

duk wann gayyar taron kwata kwata jama'a da aka gayyata basufi 70 ba, including his family members sauran duk shaqiqan iyayen ne da kawaye, da wanda ake so anuna so ma zainab arifah sabida suna bude mata hanyoyin cigaba tare da bata kariya acikin duniyar kasuwanci nan gaba.


kusan Last set of ppl da suka shigo babban hall na gidan Are the family of al-mansoors duk yadda hajiya mairo ta so suyi rawan jiki da sammako bappa zaidu saida ya wargaza mata komi, he deliberatly fixed his meeting dat morning haka aka gama shiri aka sha zaman jiransa agida har saida ya dawo dan kwata kwata baiga dalilin da zai saka suyi rawan jiki a inda ake bala'in raina musu wayo da hankali ba wanda ita kanta hjiya tasan prof zayyanu hve only invited them dan kar duniya tace babu familynsa awajen amma bawai har cikin ransa bane yaso yagansu acikin gidansa


in a grand way cikin salon da yaja hankalin kowa hajiya mairo tare da yaranta uncle moh da bappa zaidu, da kuma surukananta da duka jikokinta maheer ne kawai yazo amma kulthum da mujaheed duk basa nan sabida already kulthum din tana fama da laulayin cikinshi sosai.


kayan jikin su is so gorgeous bappa zaidu yasa wani irin baqin yadi yoloyolo me tsadan gaske data haske farar fatarsa ta masa kyau bana kadan ba, shikuma uncle moh ya saka designer half jumpa in oda to look more younger, ppl kept staring at his fine shoes sabida akwaishi da iya daukar wanka babu karya, maheer da ibaad suka saka tailored fitted french zegner suits maheer ya sa blue ibaad ya saka all black frm head to toe which makes him look like a very wealthy classy guy dat he is. calmy suke  tafe da hannunshi daya acikin aljihu, but still idon masu kudin nan nakan agogonsa daya saka wato Richard Mille ana rumor cewa its cots $1m dollars fa ba naira ba, you know the kind of classy watch that make even the rich ppl stare, kusan shine a tsintsiyan ahannun ibaad, dat queit wealth da bayayin hayaniya, dan Kallo ɗaya zaka ma ibaad ka gane cewa this man belongs to rooms where money can’t buy him. dan Ba wai tsadar watch din bane kawai, da bala'in wuya ake samunshi.


ganin irin wankan ajin da suka shigo dashi yasa tuni prof zayyanu ya aje girman kansa acikin zuciyarsa ya taho na musamman shida matarsa hajiya hamida datasa wani mayen tweed dress da rawan jiki suka tarbesu  aka shigo da su, tsabar ya rainasu ko wajen zama na musmmn ba a ajiye musu, shigowar sun in a grand style yasa maza maza aka creating musu special table batare da wani hayaniya ba aka gaggaisa da juna


Gabaki daya prof ya shiga shock ganin ammi karama cos he always tot of her as a naive little girl da late bro dinsa ya auro hmm ashe har ta girma tay kyau haka abun ya bashi mamaki sosai dan ranar graduation in arifah bai tsaya ma ya kallesu ba sai yau da aka gaggaisa sosai. tsakaninsa da bappa zaidu ne kawai basu wani yi gaisuwa me tsayi ba cos ppl kept asking about thier striking resemblance hajia mairo kuwa sai kan bazawa take yi cewa ai yan biyunta kenan muhammadu ne auta. 



Alaman Shigowar Mai hidimar yasa aka dan nitsu aka tattara hankli waje guda kowa yana so yaga karshen wanka..


Very dim white colour light aka kunna zallan inda zai dau attention akan zainab arifah babban kawarta nala ce ta soma bayyana ta sako green kaya mai daukar hankli zainab arifah kuma with her pure white Embroided nude gown mai highly detailed jackect tayi mugun kyau kamar wata fallen angel yanayin shigowr su is queite in an intimidating manner.


kai tsaye ta iso inda iyayenta suke, Prof. Zayyanu ya miƙe tsaye Ya ɗan rungume ta, ya sumbaci goshinta cikin nuna tsananin kauna tareda rage murya yace Welcome, Miss CEO.. yafaɗa a hankali da wani irin murmushin jin dadi ta amsashi snn hajy hamida ta karaso aka musu hoto atare



nan take idonta ya sauka a inda families ɗin Al-Mansoor suke zaune cos all her tot was on ko ibaad zaizo ko bazaizo dan itace tadada cusawa babanta ra'ayin cewa yay ma family gayyatar dakansa tasan dolene hajy zatasako kowa agaba yazo..


tunda ta wara idonta akansu ta hangosa taji komi ya tsaya mata, jikinta ya hau matukar rawa taciki cikin kasa tatattara nitsuwarta waje guda bayan tagansa kurkusa da ayaana rabi hanklinsa nakan fuskar ayaanan dake gefenshi da alama bai masan celebrant ta shigo ba.


atake tafarajin irin wann mix emotion din na tsana da kishi zcyarta atake yafara huruwa yana harbawa wajen saka idanunta da hanklinta akansu cike da yanayina baqar kishi dake cinta akasar zuciyarta duk da taga ayaana ce kawai batay wani make up bt idonta nuna mata yake kamar tafi kowa haskawa..


kusan tare da iyayentan suka xo wajen dakyar ta sako wata siririyar fuskan murmushi ta kalli Hajiya Mairo me tuwo tana murmushi ta gaishe ta

Dakyar ta iya danne wutr kishi yau ta kama kanta batama iya ma ibaad rawan kai da shishigi ba saboda zamansa dayay kurkusa da ayaanah.


kusan kowa awajen da irin gaisuwar da ta masa, wasu cikin aminci da karramawa wasu sabanin haka daganan aka bude taro inda hajiya hamida da mijin ta prof suka gabatar da manufar partyn tare da jadadda ma mutanen shi cewa a shirye suke su fadada harkokin bunkasa hnyar samun kudi da arziki da taimaka ma jama'ar su...


Sosai ake tafa musu babu kalar toast din da ba'ayi raising anan ba, the moment was so spicy musamman wajen da nala da zee arifah suka kasa dena zagin kwlliya da dressing din jama'a a zukatan su bayan jawabi da gaishe gaishe prof yace


Ladies and gentlemen wlcome to a defining moment in the history of Al-Mansur FinTech Holdings..Today is not a celebration of wealth,” yana mai riko hannun yarsa ya cigaba, “it is a celebration of vision, power, responsibility, and trust snn yay nuni da yarsa zainab arifah dake tsaye a tsakiya


"From today, the US branch of Al-Mansur FinTech Holdings recognizes my beautiful doter as its Young Chief Executive Officer.


wani irin tafi wajen ya kaure dashi ya mika mata insignia snn yace congratulations zainab Arifah al-mansur, tana murmushi tace thank you daddy ta juya takalle mum dinta tace thanks mum.


Ba ta yi dogon jawabi ba ta kalle kowa tace “Thank you, I am not here to prove myself. I am here to work cos i believe leadership is not inherited it is tested nd I am ready. thank you soo much daddy!


nan aka kara tafawa sosai kowa daga cikin baqin sunajin tana burgesu sosai.


Bayan nan kowa ya tsunduma yin abunda ke gabansa maza maza iyayenta suka janyeta tare da hanata muamala da su  hajiya mairo sai nunna ta sukeyi ga manyan kusoshin kasa ana formal introduction ana batun business da kudi


da kyar dai zainab Arifah take bada iyayenta hadin kai ta na fadada murmushin ta da saukaka yanayinta ta hanyar kara sake musu fuska dan ita kanta tana mugun son taga tasaka babanta awani matsayi na alfahari amma Duk  damuwarta ayanxu baifi tsananin kishin zaman ayaanah a table din ibaad ba, cos she desperately wanted to sit with him nd talk to him tana mutuwar so ace itace ake yawan ganinsu haka manne da juna bada ayaanah ba.


Gashi introduction na business yakici yaki karewa contact din mutane ixuwa yanxu har yakusa ya cika mata waya..


Bayan anyi nishadi anci ansha anyi rabe raben kayan duniya dana alatu kusan bappa zaidu ne yafara karawa da gaba sabida yana da abubuwan yi agabansa kuma bayason abunda za'azo a rainashi.


uncle moh was busy taking advantage yana makale da maza yana tattaro sabbin intl connection ma career sa da harkokinsa.



Ammi karama bata ko motsa ba tana zaune da hajiya mairo dake jama'a suna yawan xuwa gaisuwa tuni su ammi babba tabisu anty safeera ciki suka ja gefe cikin manyan mata aka hada tantin gulmace gulmace da hayya hayya kowa na fadin albarkacin bakin su. cikinsu kowa awajen millionaire ne ammi babban ne kawai ba a san ubanta ba amma dake ta iya cusa kai sosai ta saje dasu.


anty safeerah already tasaka safiya da sultana acikin ribibi  ayana kuma ibaad bai kyaleta ta bar wajen ba tana zaune a gefensa duk inda zaije tare suke zuwa su dawo sai can yamma bayan komi ya lafa baqin duk an ragu nan maheer yace ibaad ya rakasa waje dan shima zai wuce kasr malaysia by 4pm bazai kwana anan kasar ba yana da return ticket dinsa sbd jikin matarsa daya bari agida. 


suna ficewa ayaana ta haura sama inda su sultana suke da zimman tay fitsari snn tay alwala. ganin wucewrta saman yasa zainab arifah tay sauri ta fito waje ta tsaya tana jiran ibaad yagama sallamar maheer dan ta tsaresa da hira awaje inyaso sai sake shigowa cikin hall din atare...she really want all this hot girls nd guys to notice cewa she is with him, tana mutwr so a shaida cewa shine yake kulata dan ajinta ya kara yin sama sosai jin yadda ake gulman kyansa da ajinsan nan. 



dagata fannin ayaana kuwa tana hawa sama ta bullo cikin wani hadadden falo dake gidan kusan aljannar duniya ne yana da wani irin girma sosai ultra mega mansion ne.


tay ta neman su sultana har awaya bata samesu ba, nan ta bullo cikin wani katafaren falo zata wuce kenan taga taron su anty safeera suna zaune da su hajiya hamida da wasu yan uwansu masu kudi tare da tsirarun kawayen hajia hamida masu kudi..


da wani irin kurarrren kallon kwakwafi duka manyan matayen nan suka bita dashi wanda saida kafafunfa suka fara harhadewa tafara ji kamar ta juya ta koma inda ta fito.


kafin ta karaso ciki anty safeera tabi ta dauke wuta jin har manyan matayen sun fara ƙoda kyan ayaanah harga Allah yanzu mugun haushi ayaanah take bata musnm data lura da dabiun uncle moh akanta har yanzu.



idanuwan ammi babba kamr zai zube kasa wajen kallonta cikin dauriya ta karaso tafara gaishesu wasu suka amsa wasu suka bita da wlkntaccen kallo


kafin tay tambayar inda sultana suke a mugun walaknce hajiya hamida tace safeera wacece wannan lost creature din kuma amma dai ba yar gidan ku bane ko??? 


kafin anty safeerah ta amsa caraf ammi babba tace 

"wann ai wata Jikar hajiya mairo ne data jijibo a kauye basufa hada jini ba kinsanta dai da kwashe kwashe


cikin yatsinawa hjy hamida tace ohhh nagane kice dai irin yar ciranin nan ne aka kawo muku


wani irin dariya akayi


wata mata tace but the girl is fine o.. ammi babba tace hmm jar miya wasa ne?? ai gasu nan su safeera ne aka jajiba musu kulawa da ita nikam ai ba a isa ba wallh tuni na raba kaina


...wata matar tace ahh wallh kin burgeni haka fa uwar mijina take wann harkan debo kazaman yara a titi jahilai barayi takawo wai marayu hmm Allah saka dai bata taba muku sata ba..


da mamki hajy hamida ta kalle anty safeera cikin kyabe baki tace ke kuma saikika zauna aka baku rainon yar kauye kika karba sabida baki da hankli?


..murya ciki ciki anty safeera tace 'ahh fa anty hamida ma anty fatima dai aka bawa yarinya can su karata.. ni babu ruwana aciki.


cikin katsesu wata mata tace the girl look devilish, keeeeee karaso nan wnn yarinya daga ganinta zatay rashin kunya..


fargaba yasa ayaana taji kafafunta sun mata nauyi wani irin daka mata tsawa ammi babba tay kafin ta dawo hayyacinta ta karaso ciki..


you are very stupid wato ke harkin girma kin bude ido ko da zaki gaishe mu daga kofa snn manya suna kiranki kina tafiya kamar hawaiya waye sa'anki anan eehhh?


sunkuyar dakai ayaana tay batace komi ba kuma bata bari hawaye sun sauko mata ba..


suka cigaba da kare mata kallo kowa yana baza hassadansa akan kyanta tun bayn matar data ce she is fine har yanxu ba'a sake fadin alheri akanta ba..


daga mai cewa tana kama da aljanu sai me cewa tana warin talauci ahh hancinta yay dogo dayawa, ayy idonta kalar na karuwai, ahh hala babanta almajiri ne masu haihuwa barkate sukasa ci da yara azo ana sadaka dasu, wasu cewa suke inda sune da a yar wanke wanke zata kare badai ta zama yar gida ba dan talaka ba dan goyo da zani bane ..kusan kowa da shinanigan dinsa suka sako yarinya a tsakiya.


har saida hawaye ya ciko idanunta ayaana sosai jikinta ya fara rawa ahankli ahnkli


saida suka gama cimmata fuska snn kawar hajy hamida datake cewa wai ayaana tana mata karnin talauci tace  ke yar kauye jeki kasa ki kawo min platter na meat bag nd pls hurry up..


tun kafin ammi babba ta daka mata tsawa ta juya zata fita anty safeera ta umarce akan ta aje wayarta akan desk dan ta musu sauri haka ta aje wayar ta fita


tana ji suka cigaba da zaginta for no reason kowa yana fadin albarkcin bakinsa na yadda suka tsane jinin talaka musmn ma yan kauye. muryan ammi babba kusan yafi na kowa tashi dadi taji musmn dataga anty safeerah ma ta jonasu tana bada labarin yadda su ammi karama da hajy mairo suke kan sakalta ayaana ake fifita harma fiye da yaran gida.



ayana tana fita hawayen datake dannewa suka sauka mata ta rasa meke mata dadi, gashi bata ga alaman su sultana akusa ba. da kyr ta share hawayenta ta sauka kasa kallo daya tay ma wajen zamansu taga har yanxu ibaad bai dawo ciki ba.


kai tsaye taje ta dauko meat bag platter din jikinta a sanyaye ta haura sama dashi har tay nisa ibaad ya hangota daga kofar kasa ayayinda zainab arifah da kawarta nala suka cikashi da surutan da bama jinsu yakeyi ba.


at first yay tunanin ko ayaana tagaji da jiransa ne ta haura ta same su sultana asama


suna karasowa ciki suka zauna tare da su zainab arifah akan seat tafara rawan kai ta fadi wann ta fadi wancan gata da bala'in son dora masa hannu ajiki..


ganin yaci minti biyar ayaana bata leko ba ya ciro wayarsa yafara daddanawa he call her like 4 times ba a daga ba. ya mata sako akan ta sauko su wuce gida still baiga reply ba atake yaji abun bai masa ba kuma yasan inya aike zainab arifah sama ba zuwa zatay ba


tana tsaka da masa bayanin programs na sabon kmfaninta ya miƙe tsaye tare da gyara zaman suit dinsa dakyau yace musu "excuse me. very swifly witout any explanation ya barsu azaune awajen suna tumɓaleɓale da baki kamr wasu fans dinsa ya kara da gaba fuskar nan nashi a murtuke.


zainab Arifah ta bishi da wani irin kallo, feeling so embrassed tamiƙe ta fara binsa da sauri gashi idanun kowa yana kanta u can easily spot irin vibe dinnan na cewa she is just throwing her self for ibaad's attention wnda yasa ajinta ya dan zuba a idon gayu.


ibaad was walking fast yana jin bugun zuciyrsa na karuwa sosai saidai ya rasa menene ke faruwa da ayaanah dayake jin sudden uneasiness .


da sauri sauri yake tafiya ayayinda zainab arifah da nala suke binsa kamar jela abaya 


yana kaiwa saman he looked at few places baiganta sai can daya faro jiwo muryan ammi babba tana masifa ita da kawar hjiy hamida data dora ma ayaana sawun kafarta akan cinya wai ta danna mata ayayin da takecin meat bag din, lkcin ne ma ayaana taji hawaye masu zafi yazo mata sosai.


itadai batace musu komi ba dan dukansu awajen zasu iya haifar ukun ta ma


tana durkushe acikinsu tana matsa ma dayan hajy kafa da suka sakata na dole waidan akan hawayen datake yasa ammi babba take mata masifa inda take shiga bata nan take fita ba.


ibaad yanajin yar kauye walakntacciya yana flying a iska yay sauri ya karaso wajen baiko musu sallama ba idonsa yasauka akan ayaanah a durkushe da kafar mata data dora mata ajiki kmr ta samu baiwa...


kamar kiftawar ido fuskarsa yay wani irin jaa da bacin rai ya tsaya yana kallonsu 


anty safeera tay maza tama dayan hjyn ido akan ta dauke kafarta akan cinyar ayaana 


ganin wajen ya dauke cak da shiru kowa ya zuba ma ibaad ido yasaka matar dauke kafarta itama ta kallesa


nan..sai ga su zainab arifah sun leko,..


baice musu uffan ba ya karaso ciki fuskrsa kamr mala'ikal mutuwa daga masu hararar haduwarsa sai masu jin sha'awarsa 


tun kafin ya kamo hannun ayaanah da wani irin borin kunya ammi babba tahau cewa tohh munafuka sai ki tashi kije ai bagashi anzo a daukeki ba? dama ai hawayen makirci kike yi waiku kenan yaran zamani babba bai isa ya saku aiki ba sai ku hau kuka dan ace ana zaluntarku kedai ayaana kin shiga uku wallah. 


idanunsa kusan a rufe ya jawota daf kusa da shi ganin idonta har yanxu da hawaye ya tallabo fuskarta yace "what is wrong?? girgiza mai kai kawai tay hawayenta na kara zuba 

ji yay kamar kirjinshi zai amon wuta yaja hannunta ahnkli yace "lets go!..yana rike hannunta zai jawota su fita out of guilt anty safeera tace ibaad bafa wani abu aka mata ba kawayen anty hamida sukace taje musu aika shine take kuka


..tsaki yaja mata kuma ko kallonta baiy ba, yafara jan ayaana a jikinsa da kulawa ya ciro hankynsa ya fara share mata fuskarta, zainab arifah ta shigo ciki tana kallon mum dinta kanta adan kulle tace "mumy wai me aka mata?...


cikin yatsina tace oho

ke ni karki dameni...


da sauri zainab ta juyo ganin har sunkai kofa tace "ibaad pls wait!!


da tsawa hajy hamida tace "ya jira ya miki me? just them go yafi ruwa gudu mana..yaron nan tunda yaga yagirma yake bala'in raina mutane zai wani shigo tsakiyar mata bai gaishe mu ba ana masa magana kuma yana basar da mutane yawani ja hannun yarinya ya fita da ita and who is his mate here..


da wani irin rashin kunya arifah tadaka ma maman nata tsawa tace mum but you cant talk to him like that, i knw ure just bullying the girl...for god sake i was on a date with him muna wani magana ne dashi fa but 

you and ur friends have to ruined it for me...ina ruwan ku da yarinyar ehhh.


kusan ba acikin hanklinta take masifar ba tace u knw he will react kuma bazai sake zuwa gidan nan ba sabida abunda kukayi yanxu


nan su anty safeera da kawayen maman nata suka hayayyako zasu tsareta da surutai atake atake ta haukace musu ta kunce musu bori


har jikinta na rawa da wani irin rashin kunya...tace karda wata mata tamata magana ai hidimarta ne kawai su tashi su tafi subar musu gidansu hidima ya kare ita batason ganinsu..


cikinsu kowa na mamakin kalar rashin tarbiya da kunyarta while ita kanta batasan meye hatsala ta take masifar ba, dan harga Allah jikinta na bata cewa ibaad zai dauki tsatsauran mataki wanda dole ne itama ya shafeta..


wasu hajiyoyin da abun ya musu ciwo atake suka dau jakarsu suka fice da fushi


da hatsala hajiya hamida tace "Zainab how dare u asked my frends to leave kina hauka ne



da ihu tace "they ruined my day badan su ba ibaad wud have been talking with me by now

...nd mum zanje na kirashi wallah ure going to apologise if not zan kai kararki wajen baba ai bake kika hada min hidimar ba u cant ruined it for me



tana fadin hakan da wani irin bori ta fita nala tabita abaya banda kallon juna babu abunda ammi babba da anty safeera suke kowa na hmm hmmm..


da sauri zainab ta sauko kasa dan ta bawa ibaad hakurin abunda ya gani anama ayaana sai sholl batagansa bare ayaanah su hajiya mairo ne kawai suke kan zaune da alama basu ma san abunda yake faruwa ba


wani irin haushi ne ya kama zainab arifah taje ta samu babanta ta fara masa kuka sanadiyar haka yasa securities suka kore dukkan wasu kawayen mamanta agidan with immidiet effect duk saida tasaka aka walakantasu aka rakasu har waje sosai ta kunyatar da mamanta.



dagata bangaren su ayaanah kuwa kusan dakyar ibaad ya danne zuciyarsa ganin har yanzu tana hawaye harda shesshka dan maganganun banza da matayen suka mata sosai yake dawo mata kai yanxu yana mata zafi sosai dan tasan ita ba marainiya ba ce kuma iyayenta ba talakawa bane duk dama akauye suka taso, saidai irin zagin cin mutuncin data kwasa yau ko almajira albarka.


tafiya kadan sukayi suka tsaya awani hadadden quest house na abokinsa prince zarko suna shiga mai gadi ya bude musu gate suna masu miko masa gaisuwa tun bai sako kasa ba.


dede wajen parking ya paker black GMC yukon jeep dinsa ya sauko da wuri ya bude mata kofa ta sauko snn ya kama hannunta suka shige ciki.


the place was so quiete gashi yamma ne wajajen 5:30 basu furta ma juna komi ba har suka kai cikin wani irin hadadden falon hutawa bai kaita cikin bedroom baison yay rarrashin da zai saka ya taɓa mata jikinta sosai..



suna zama lallausar kujera ya zuba mata rikitattun idanunsa dat are sharp nd piercing kamr wanda xai hadiyeta, ahnkli take sshhka har ta share hwayenta snn ya kamo hannunta cikin nashi ahankli yace are u ready to talk to me now? 


dago kanta tay kafin ta amsashi taji ya dada saukar mata kai da muryansa kasa duka wanda kusan bai taɓa marairace mata haka ba .


da sanyin tausayinta a kwayar idanunshi yace Did you know it hurts me when u cry?sai yayi shiru na seconds kaɗan, kmar wanda yake kam neman wasu kalmomin da ba su saba fita daga bakinsa ba. 


kara matsowa kusa da ita yay sosai har ta ji dumin jikinsa cikin murya mai kashe jiki yace“I don’t like it,” not bcos i want to force u to be strong but every time you cry, I feel like I failed you somewhere.”


jin haka yasa tay sauri xuba maraitaccun idanunta acikin nashi da wani irin kasala ayanayinta batare da tace masa komi ba hawayenta masu sanyi na zuba masa hannu.


Yatsunsa taji ya ɗora akn fuskarta yana share mata hawayen ɗa suka dan ragen slowly kamar mai jin tsoron taɓa mata zuciya yana cewa "kisani, I notice everything about you. Even the tears you pretend are nothing. Hannunsa ya zamar akan nata ya kara riƙe natan sosai, ba da ƙarfi ba. yace I want to be the place you soften ba inda kike nuna taurin kai ba, i dont care how strong you try to be…all I want is to hold you till you stop hurting

okay? yana maganan a nitse 

kallon bakinsa take bata ko kiftawa dan jin kalaman nasa takeyi kamr ruwan kankara ake xuba mata cikin zuciyarta dake mata zafi tanajin koinnta na daukawa da wani irin sanyi tereda matsanancin sonsa dake kkrin taɓa mata kwakwla


with each word dayake furtawa ji take kmr zuciyarta na narkewa ahnkli ba acikin hayyacinta babu shiri yajita ta fado kan kirjinshi in a very melting way da wani irin shauqaqiyar tsumayi ta rungumesa tare da lafewa akan kirjinshi idanunta a lumshe take sauke nannuyar ajiyan xuciya...


dakyar ya iya control kansa ya dora hannunsa agadon bayanta calmy yana dan patting inta.


sunfi minti goma haka kafin taji sanyi ta dago suna kallon idanun juna da sanyin murya ahnkli tace "when you held me everything softens inside me. a maraitace tace i am sorry i cried nd u its u who get hurt! shafa kanta yay yace its okay..But i still want to knw what happen me suka miki?

jingina kanta tay ahnkli akan kafadun sa tafara magana bata boye masa komi ba har saida ta gama..


nan ya tallabo fuskrta yace next time anyone try to hurt nd disrespect u like this dont respect them back kinji ko?? 


ahnkli ta gyada masa kai yadora bakinsa akanta yay kissing goshinta lightly muryansa kasa kasa yace"i apologise on thier behalf

...murmushi me sanyi almost in a whisper tace thank you, and Don’t stop talking to me like this It will make me feel chosen...murmushin bazata ya kufce masa yana kallon kwayar idonta baice komi ba ya kara sakar mata soft kiss asaman goshi yakara jawota jikinshin sosai ..dan karamin shiru ne ya ratsa wajen tana lafe ajikinsa har saida yaga ta samu nitsuwa snn ya kalle agogonsa yace "kije can dakin kijirani i will go nd get u some cloth nan da 40 min prince hassan zai karaso sai muje wajen program din nasa tare ko? ahnkli tagyada masa kai tace okay toh saika dawo kallonta yake har ta miƙe da sanyin ladabi ta shige ciki shikuma ya mike ya fita waje...


gobe zanje na duba hakorina please use this pages as ur tmowrw page snn karku manta saura kiris ne mu rufe book 1..

#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[11/12, 14:11] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.




⏯️4️⃣3️⃣


ibaad yana ficewa cikin motarsa ya buɗe ya shiga ciki ya zauna snn yaciro hadaɗɗen wayarsa ya shiga wani site me 5str rating yay odering full set na kayan sawa da zata saka ajikinta hade da duk wani abunda suke buƙata for the night including a make up artist All his oders secured are arriving by 7pm on d dot cos they need atleast 1hr to get ready. yana gamawa ya kunna motarsa ya fice ya koma gida agaban masallacin bappa zaidu yay parking after few words dashi yajasu akayi sallahn magrib suna daf zasu shiga isha aka kawo masa duk wani kayan da yay oder in a fancy bag yasaka acikin motarsa


ana idar da ishai da minti 5 ya fice sharply yajeshi family house dan already bappa zaidu ya gaya masa cewa kowa ya dawo.



zuwa yay ya samu any cirko cirko ana ta hayya hayya a sashen hajiya mairo anty safeera ce kadai a sashenta sam taki fitowa dan tun awajen hidiman ashe sultana da safiya sukaji labarin abunda ya faru  abakin masu aiki dake can sama suke lokcin da ake korar kawayen hajiya hamida duk sunji me sukecewa gameda walakanci da cin fuska da akayiwa ayaana.


sultana kuwa tun suna sauka kasa awajen ta zo tagaya gayawa ammi karama sosai ran ammi ya baçi tafara gayawa hajiya mairo kenan su ammi babba tazo tace ma hjiya mairo sam ba haka bane yafaru ta jujjiya maganan tace kawai ibaad ya sakalta ayaana ne dayawa waidaga an kirata za'a aiketa saitafara kuka shikuma yanazuwa sai ya dauketa suka tafi..



wann maganan har suka dawo gida anayin shi, ammi karama da nata version din, hjiya kuma tace sam ai agaban raihanatu akay komi kawai karya sultana tay ba ama ayaana komi ba sakalci me data samu ana daure mata gindi tana raina kowa.


itama safiya taxo da dogon baki na buga ruwan makirci, atake tahau bin bayan duk wani maganganun da hajiya mairo take furtawa tanamai cewa ai dama can haka yaa ibaad ya sabayi, koda ayaanah tay laifi ko rashin kunya baya mata fada ko hukunci saidai ya bi bayanta kuma shiyasa take aikata duk wani abunda taga dama.


ammi karama tay musu dasu akan wnn mgnan har tagaji da magana basu fahimce ta ba, haka hajiy mairo ta hau dokin zuciya akan batun cewa wai ayaana ta riga ta lalace kuma ibaad ke daure mata gindi tana iskncinta yadda taga dama a gidan ai baza'a taru amata karya ba.


tun dayaji tashin wnn hayaniyar sai bai shiga sashen hajiya mairon ba, ya wuce falon amminsa direct yana zama akan one sitter ya dau wayarsa ya kirata yace yana jiranta a falonta amma sauri yakeyi babu yadda batay dashi akan yazo falon hajy mairo aji ta bakinsa ba yace mata baida lkci tazo kawai.


kyalesu tay ta fice hajiy sai masifah take ta inda take shiga batanan take fita ba tanamai cewa ai rayyanu yasan baida gaskiya ne shiyasa yaqi zuwa gabanta ynxu ya fada abunda ya faru kuma wallh zata dau mummunan mataki akan irin rashin kunya da sakalcin da ayaana takey agidan nan musmn wa manya.


Da bacin rai Ammi karama tabar sashen tazo ta samesa yana zauna bayabo ba fallasa suka gaisa 


zata fara kawo masa maganan yace "mata tabar hajiya kawai ta yarda da abunda take so ta yarda dama ita hajiya mairo one sided tafiye son yanke hukuncinta kuma kodama yajr ya gaya mata gaskiya yanxu inda akan batun ayaana ne bazata taɓa yarda dashi ba..


dakyar ammi karama tabar maganan dan tasan sultana bazata taɓa zuwa tana kuka kuma ta mata karya ba beside tasan ammi babba bazata taɓa fadan gaskiya akan ayaana ba.


bayan ya lallabata tabar maganan snn ya sanar mata cewa zaijeshi program tunda ayaana na tare dashi yana neman izini awajenta zasuje tare nd he wll bring her back home safe in an tashi.


few question ammi tay masa bayan ta qamsu da inda zasujen sai batay wani gardama ba ta kyaleshi, dan tasan muddin ayaanah ta shigo gidan nan yanzu haka hala hajiya mairo bazata mata adalci taji ta bakinta zatay xuciya ne ta zazzageta akan abunda bata aikata ba.


around 15min after 7 yabar gidan ya wuce quest house inda ya bar ayaana ita daya, female wokers din wajen suka bata wajen sallah tay both magrib da isha snn suka hada mata warm bath tay wanka ta shafa lotion snn suka kawo bathrobe me kaurin gaske suka bata ta saka ajikinta wanda har kusa idon sawunta ya kai, doguwar sumanta duka ta dauresa acikin towel tay zamanta abakin gadon dakin tana Allah Allah ibaad ya dawo....


after few min tana kwance da idanunta lumshe ahankli taji anbude kofar while she is still relaxing eyes closed taji qamshin turarensa ya bule wajen atake, cikin bude ido tareda miƙewa xauna tana mai dadda gyara zman bathrobe din ajiknta da sanyin sallama ya karaso ciki da ledan kaya ahannunsa tamiƙe tsaye dq amsar sallaman abakinta snn ta karbeshi da ladabi, ya hade harda hannunta ya rike yana mata wani irin kallo yace i took so long ko? cikin idonshi take kallo tace"..uhm but i am not bored! kallon bathrobe din jikintan yay yace "mmm i can see that..nan saiya sake mata hannun tare da kayan duka cikin sauke ajiyan zuciya yace "get dress dan its almost time 


kafin ta amsa yace "i wll be in d oda room zan shirya acan, snn wata mata zata shigo nan yanxu ta tayaki shiri nd w'll meet in 15min, yeah? da sanyin murya tace "yeah..daga nan ya juya tabi bayansa da kallo yana ficewa kuwa sai ga wata siriryr mata ta shigo da wani katon akwatin kwalliya


tunda daga kofa dataga kalar kyaun ayaana ta fara mata murmushi


salam alaikum gud evening maam...


ayaanah ta amsa ba yabo ba fallasa tace kece zaki tayani shirin?


matar tace yes maam both make up nd styling can we start? ayaanah tace sure...


gaban madubi suka karasa kafin kace wani abu har sun fara the lady was very cheerful professional nd fast kusn komi zatay sai ta nemi cikakken izini awajen ayana, dan hakane ma yasa ayaana bata sake an yanke mata gashin girarta ba which save them alot of time kawai shaping insa tay tay grooming dinsa dakyau snn ta zuba mata dark eye shadows, thick feline eye liner, da nude red lipstick dayaji lipgloss me kyalli, countour din ma sama sama ganin ayaana already tana da wannan natural kyanta duk dama simple hot kwalliyar bakaramin kara fitowa da ita yayi ba. idonta da sukaji thick liner suka kara manya so sexy looking dogon hancin nan an kara shapin yay zarr kmr ita ta yanka ma kanta, da dan karamin bakinta, wani irin gyara tay ma gashin ayaana, ta zuba masa original wavy gel agaba gaba, jelar wave daya me tsayi ta sauke mata shi ta side daya in a very classy way yadda kai tsaye zaka gane cewa tana da doguwar suma kuma yolo yolo, har saida sukagama da fuskarta tsaf kafin suka bubbude kayan sawan within few minutes suka ciro su, alexandre vauthier V-neck rose red designer maxi gown, with subtle shimmers, sai YVSL sandals in nude, da sleek red clutch, earing da neck piece kuma gold ne da karamin red rubie stone ajiki..tana gama saka kayan matar ta dora mata nude turban kalar shoe inta tay mata push dashi kadan, matar sai rawan jiki take tsabar yadda taga ayaananh ta kure mata kyau she kept asking ko ita asalin yar nigeria ayaana saidai tay mata murmushi....da wuri suka gama komi tabar ayaana a tsaye tana kallon yadda tay ma kanta wani  irin kyau 


nan matar tafice taje ta kwankwasa ma ibaad kofa tareda sanar dashi cewa sun gama, he paid her nd gave her extra tip saboda ta rokeshi ko zata dau hoton fuskar ayaana ta zuba a cataloge inyaso kamfanin su zatana biyan ayaanan weekly, amma yaki sam, yace mata matar aure ce kuma baison fuskar matarsa akowani irin professional catalogue so she understood him and left.


da har zai koma dakin shi yagama shiryawa yaji kai bazai iya ba, jacket din suit dinsa dasu wayarsa da wallet dinsa kawai ya dauko ya kulle dakin da key gabaki daya qamshin jikinshi ya gama karade ilahirin gidan da wani irin sanyin dadi me ratsa zuciya da kwkwalwa signature perf dinsa zhexoff naxos tareda Tom Ford Noir Extreme ya shafasu duka atare,he is wearing a crispy white shirt me open collar mahadar midnight black tailored suite dinsa from  Brioni, irin single breasted sharp shoulders din nan with no tie da black leather chelsea shoes sai hddn agogonsa na patek philippe daya fito yana kan kkrin mannata a hannunsa cikin sauri


kai tsaye dakinta ya nufa ya bude kofar ahankli daga kofa ya tsaya cakk ya zuba mata ido fuskarsa na kkrin canzawa tana juyowa for a moment ji yay kalamai sun dauke abakinsa gabaki daya...


tana murmushi tace yaa did i look okay??


karamin murmushine ta kwace masa abazata yace "ask me that question again madam..ta makale wuya a marairace tace "is it too much? sake kofar yay ahnkli snn ya karaso ciki suna kallon juna kamr zasu hadiye kansu, kallon kyakywan fuskarta dayaji kwalliya yake a shagalce kamar wanda baya duniyar ma gaba daya


ahnkli cikin kare ma ilahirin jikinta kallo yace its nice nd dangerous"...atake tay dariya mai sanyi tace ahh yaa ibaad dangerous fa


gefen fuskarta ya shafa adan kasale yace 'yes, dangerous for duk wanda ya shagala ya mance cewa ure taken mana. 


da sauri cikin jin kunyarsa ta sauke idonta kasa kasa tana murmushi har suka karasa gaban madubi atare. 


he stood behind her close enuf batare da ya mannu da ita ko ya taɓata ba he felt restless kamar kayan data sakan da irin kyan dayaga tay sai yana kkrin cusa masa baƙar kishi aransa' babban wayarta data rike agaban madubin tanata capturing dinsu ta saukar kasa kasa jin yay shiru duk sai tarasa tunanin meyake kan ayyanawa aransa.


ta cikin mirrorn ta kalle idonsa murynta kasa kasa tace" yaa bakace komi ba..what is wrong? dan aje fuskarsa yay straight up yace "i am worried"

..ta juyo suka hade ido soflty tace "of what?..da kishi aransa yay maganan, amma bazaka taba tantancewa a fuskarsa cikin sauke ajiyan zuciya yace "this dress..so, ynxu what if someone stares at you for too long.. ko zamu canja ne kisaka wancan kayan da mukazo da shi??? 


looking serious nd sounding worried take kallonsa yacigaba da mitarsa wanda yanayi ne amma kamar bai saba ba.


kinga shiyasa bana son yawan kwalliyar nan, yay yawa mana..


he looks at her again like kamr yana famar auna wani abu a fuskartata yace this is the kind of beauty any man will get worried abt it, kude mata kun shiga uku da kyale kyale ni kuma my wife will not step out with this make up thing ban isa ba yanxu sai kowa yaje yace yanaso..


fuskrsa take kallo with immense disbelieve na sanin cewa taɓajinshi ya hade rai yana zuba dogon mita har haka ba, tareda sanin cewa sosai ne zafin kishin yake kkrin balle masa beyond his control.


ahnkli ta lumshe ido tareda budewa then ta kara step daya kusa da dashi har suna shakar numfashin juna then she gently reaches up for his sleeves, cikin nitsuwa tafara karasa gyara masa zaman wuyan rigar tasa in a calming way da sanyin murya tace

"why not stay close to me tonight tunda baka yarda da kowa ba.


girarsa na sama a dage yace "dama i wasnt planning to let u out of sight madam kawai de bana son a cuceni ne cos you have no idea how selfish i can be, murmushi kadai take iyayi jin maganan nasa yana mata wani iri kmr ta masoyan da suka mugun jimawa atare, ruwan kishi dake idonsa yasata kallesa snn ahnkli ta kara matsowa ta fado jikin shi coldly cikim tsumayi mai cike da shagwaba tareda narke mishi akan kirji cikin sakar masa wata iriyar shababbiyr malalaciyarrrrr shauqaqqiyar tsumammen runguma wnda sanda duk kasusuwan jikinshi suka amsa atake turarensu ya gaurayu dana juna sending him this high voltage of chill a duka sassan gabobin jikishi


kanta ta lafar akan chest dinsa kamr yar baby tare da sakar masa irin numfashin nan me bayyana kalmar "i am all urs"

..batare da an furta shi a fili ba. yadda ta bala'in narke masan sai yaji kmr zafin kishin take raqe masa akn kirji.


wani irin lumshe ido yay bata sakeshi ba kuwa har saida taji yana sauke ajiyan zuciya ajere ajere har saida ya nitsu sosai snn ta kwace kanta ahannun sa gently ta karbi jacket dinsa ta tayashi sawa they look so soo cute together mirror selfie data musu tasaka akan screen saver inta snn suka gama suka fito tana gefensa wayarsa yafara ringing prince ne ke kirarsa ya dauka suka fara magana yace masa gasu nan suna kan hanya...


suna ficewa ya bude mata mota ta shiga ta zauna snn shima ya shiga hannunsa daya acikin nata daya yana tukawa har suka isa wajen program din da za'ay wanda already duk an hallaro..


The event hall glows with soft golden lights, music swirling lightly in the background. duk wasu manya manyan tables are elegantly set.


Ibaad’s presence is calm nd controlled amma there’s a subtle edge in his eyes irin quiet warning din nan to anyone who dares to look at his girl dake tahowa agefensa dan shikansa baisan yana da wann kishin ba sai yanxu ashe gara ma daya jima da hanata yin kwalliya da kuwa ace radin kanta tay yau da sai yasaka ta goge but unfornatly he was the one dat odered it dan kar araina masa ajin budurwa toh babu yadda zaiyi.



wani irin glowing ayanah takey  in her rose-red gown suna isa kan table dinsu Ibaad yay sliding chair wa Ayanah in a  cute gentlemanly gesture that makes even his friend raise an eyebrow


prince yace guy sai yanzu? Ibaad yay murmushi lightly yace toh shiri da mata ai sai ahankli kasan nidai bazan yi latti ba..


prince na murmushi ya kalle ayaana yace Madam wai haka ne? nifa jikina na bani kmr karya yake miki...cikin snyin murmushi tace hmm ayi mana afuwa kawai..prince yace Bakomi amarya aike baki laifi daga nan suka gaisa snn ya nuna mata yasmin yace i want u to meet my fiance..yasmin dake kallon ayaanah tuntuni ita tafara mika mata hannu tace hi, i am yasmin..ayaana ta mayar mata murmushi suka sha hannu tace "Ayaanah. yasmin tace its nice finally meeting you...da tsokana ta kalle ibaad cikin kashe masa ido dan yasan ayaanan ta mata kyau tace..hey man, u look unsually beautiful today

..hannun ayaana ya rike anashi yana dariya me sanyi yace 'thank u hajiya nida beautiful din mungode"..prince ya karkada kai kawai yanata murmushi, the table was set with drinks nd neat template da wasu busines magazines. duk dama hidimar siyasa da busines kawai sukazo time to time ana hira zakaga sun tashi sunje sunyi sealing Q4 deals quietly har sugama su dawo, acikin mgazine din akwai huge estates na wani shudadden mai kudi da bashi ya masa yawa yasaka estate din a kasuwa, they are alrdy scretly planning to buy it ryt now to shape it into gidan haya dan su bunkasa harkokin su na real estate...ayaanah da yasmin kam na basu san meke faruwa ba kawai hirarsu suke sama sama dan yasmin kusan sa'ar su sultana ne tana 200lv ne a university going to 3 next year. amma dake ayaana tana kyan jiki da tsayi bazaka wani bambamce age insu ba


time to time haka prince yake dada wayar gfs dinsu kai akan harkan kasuwanci musmn ma wanda ake tattaunawa awajen, program din was very polical nd educative sosai suka karu da ilimi, at arnd 12 ba dare aka fara kkrin rufe taro..duk wasu abubuwan da sukay securing ibaad yay analysing dinsu yay signing wasu kmr na siyan gidajen ya bawa prince


with alot of souveniers aka bisu har waje sosai yasmin kaita taji dadin zuwan guys dinta event din sosai duk dama batason sunfita moruwa ba, they are movers and takers, they dont waste oppurtunies kusan wann babban dalilin jajircewan tasu shiyasa sukay arzikin da hankli ma bazai dauka ayan shekarun 5 inn nan ba...ga hadin kai ga intense privacy yanxu ynxu har sunyi securing 2 big deals agaban yan matansu amma cikin shiru batare da sun sani ba.


sun yi sallama kenan prince yaja yasmin suka wuce ciki caraf sai ga wani alhaj da body quards dinsa sun tun karo ta wajensu ayaanah


kai tsaye alhajin yace "yan mata can i have a word with you..kmr nasanki awani waje fa, koba zalihan saudi arabia bace.. anyways take my card koba ke bace i will like u to give me a call Beauty..i dont mind bein ur second boyfriend kyakkawan yarinya kamar ki ai kalar mu ce.


tun kafin ta gama juyawa tagama wayene me wann uban audacityn


ibaad ya juya da wani mugun harara ya kalle alhajin up and down a mugun dakile yace "Baba tsoho waimagana kake? 


alhaj yace eh da wancan beautyn nake magana zaliha ko??


ibaad yace 'ba zaliha bace, nd I don’t do sharing....saidai in kaje gaba can zaka samu yan iska kalarka akan titi sun yi layi ynxu dare yay nisa sun fito suna jiranka agaba.


kafin alhajn ya budi baki ya bude mata mota fuskarsa a harde yace "get inside..tana shiga ta zauna anitse snn ya kulle motarsa.


ta windo ta kallesu kome mutumin ya tsare ibaad yake gayawa masa oho ita dai taga kmar zasuyi hayaniya sai kuma taga ya dauke kai ya sharesa ya dawo cikin motar baice mata uffan ba suka kama hanyar gida.


tun da suka kamo hanya lafewa tay a seat tanata kallon fuskrshi yadda yake tukasu a nitse tanajin matsancin sonshi yana kara yawa aranta sosai, dan ta lura koyana cikin fushi bai fiye magana ba,he is always controling his emotions saɓanin wasu maza da suke sauke fushinsu ko su haura maka da magann banza. ko kishi yakeji kamar zai kashe shi he will still remain calm a fuska. har saida kallon son datake masa ya shiga ratsa shi yana sanyaya shi kafin nan ya dan huce snn ya sake styrng din ya kamo hannunta cikin nashi while he is driving da dayan yana murzawa ahnkli, jin kasala na neman shige mata jiki yasa ta matso kusa ta dora kanta akan krjinsa tana shaqar turarensa tana lullumshe idon kafinsu isa gida wani irin bacci me nauyi yay awon gaba da ita.


har suka isa gida yay parking bata sani ba a dakinsa ya ajeta akan gadonsa ya rage mata shoes da turban da jewries dinta duka dan baisan yaya zaije ya tarar da kanwarsa safiya ba, sharply ya shiga bayi ya kimtsa kansa yasaka jallabiya snn ya dawo palon ya barta aciki yay baccin sa akan dogon kujera.


sai can da asbuh ya farka ya tashe kowa akaje sallah ya dawo ya samu harta kimtsa masa dakinsa ta wuce dakinta itama, jin kmr ya balain gajiya sai kawai ya hau gadonsa ya kwanta bashida farkawa ba sai 9.30am amminshi kawai yaje dakinta ya gaishar babu yanda batay dashi suje sashen hajy mairo ba yaki sam har saida yay breakfast dinsa me nauyi anan snn yabita sukaje, uncle moh ne kadai azaune a falon da alama yazo ne ya fara cusa mata magann batun zai kara aure da niyyar yau da yamma idan sun fita da ayaana ya furta mata duk abunda suke ciki zaizo ya gaya ma hajiy sai afara shirin auren na da watanni uku masu kamawa.



zuwan ibaad da amminshi yasaka maganan bai iya fita a bakinsa ba, dan baison kowa yaji yafiso sai ya gama da hajy mairo yasata a team dinsa kai da fata snn ya gayawa kowa qudirinsa na auren ayaana, ibaad ya gaishesa ya amsa masa a dakile shima sai ya sharesa, tunda iya gaishe da hajiya mairo tafara masa mitar akan halayya ayaana ...cewa take ita gaskiya yau yau zata aika can jigawa ayi magana da kawun nan taawure, a isar mata da sakon cewa bazata iya cigaba da amincewa ayaanah tay wani dogon karatu ba kawai gara ta fito da miji tana gama neco amata aure tunda rashin kunya da fallin balaga tasaka agaba ta raina uban kowa. mitar duniyan nan tay ma ibaad baice mata komi ba, tagama tay shiru saiya kama hanyarsa ya fita ya barsu anan ya koma gida...ammi karama ta zauna tana dada fhimtr da hajiya ba haka halin ayaanah yake ba da kyar da wahala saida uncle moh yasa baki snn hajiya ta sauko da maganan auren nan.



toh wallh fatima gara kice mata ta nitsu tunda bakwason a mata auren dole ni da tuni inada wanda zan hadata dashi...yarinya sai gantali ta nanike da jin hudubar rayyanu da yake da wacce takeson shi..idan yay aure ya kyaleta da baqin halinta zanga uban waye zaizo yace zai aureta yara sam babu lissafi waye azamanin yanxu zai dauki wann shegen shagwaba da sakarci toh wallah ahir kuja mata kunne...kai muhammadu aikune mata iyaye toh gaskiya ku hada hannu tun kafin nay sadakarta..



he look worried nd pitiful akan maganan hanata karatun amma har aransa wani mugun dadi yaji da hajy mairo tafara maganan aure kawai zata mana ayaanah ba karatu ba


Da wannn farin cikin aransa yabarsu falon yaje sashensa yay wanka ya shirya tunda ya fice agidan ba'a kara ganinsa ba..



the same sunday morning wajajen 9 zainab arifah tafara shiri da zimman zataxo family house danta bawa ibaad hakuri ta lallabashi masu aiki kamar bayi suke kewaye da ita amata wann amata wancan


suna cikin wannan rububin kwasam sai ga iyayenta duka biyu sunxo dubata they look okay kmr ba jiya aka gama tamfatsa tashin hankli atsakaninsu ba


da murna ta taso tazo ta rungume dadynta sosai tanakan gode masa da irin hidimar da jiyan ya mata


he keep looking at her da wani irin ido, har masu aiki suka basu waje, suka zauna suka sakota a tsakiya, snn ya fito da wani shiryayye file dan tun jiya da dare suka shirya magana shida matarsa kominsu a makirce  cewa yxn ne daidai lkcin da zasu raba  alaqar zainab da ibaad sabida, ya mata abubuwan da yasan bazata taɓa iya tsallakr umarninsa ba yanxu, tunda har ta girma tay hankli kuma tasan he cover her ass up akan batun kisa ga kuma ya dauki dukiya da matsayi babba ya dorata akai..


suna zama suka fara kalallameta da kalamai hajy hamida harda bata hakuri akan abunfa ya faru jiya, suka hada baki suka nuna mata duk duniya babu abunda bazasu iyayi akanta ba, cike da hikima suke karanto mata irin dumbin gata da alfarman da suka dora rayuwarta aciki


wasu abun da baban ta ya mata rayuwa ana tuna mata ma kuka tafarayi ta kara rungumarsa...


they use manipulation nd diplomacy to make her very soft and vulnerable kafin nan prof ya fito kai tsaye yace mata its hight time ta rabu da ibaad tay focusing akan careerta da rayuwarta sabida ibaad bai dace da ita ba.


acewarsa ibaad maraya ne, koda yana da kudinma ai na gado ne, snn karamar yarinya ce ta rainesa shiyasa baida tarbiya, haka kuma zaidu ya lalatasu sun taso ne a lalace basu tashi sun nemi arxiki ba sai wankan karya da saka abubuwn da yafi karfinsu. snn dayan dalilinsa shine ibaad is just a medical doctor, and doctors are mostly paid poorly basuda time nakansu nd they cant even pull up a business dan haka tarayya da ibaad zai jawo ya zama shine matar itace mijin babu amfanin auren mijin datafishi matsayi da arziki cutarta kawai zaiyi


hajy hamida tace malaminsu mai duba ya gaya musu cewa familyn babanta ne suka mata asiri take son ibaad dan susa ya aureta, ta haihu dashi, sai su kasheta,fuk wani dukiyarta ya dawo na dansu shikenan arxikin ubanta ya koma na ibaad da dansa kenan har abada.


kai babu wani believable dalili a duniyan nan da basu fayyace ma zainab arifah ba..tun abun bai fara bata tsoro ba har saida taji kanta na juyawa sosai...


watching her mum sheding tears wai bata son ta rasata and her  father begging her with all sincirety in his eyes akan ta rabu da ibaad sai taji ta rikice ta rude gabaki daya...


they poisoned her mind so much ta inda bata da wani kalman da zata kushe dalilansu dashi


karshe kawai tace musu taji amma xatay tunani duk abunda ta yanke kuma tay alkwari zata sanar dasu, sosai suka sha mamakinta duk dama a aranar wuni sukayi suna saka masu aiko suna dubata dan kar tay wani abu drastic sai kuma sukaga shiru batay wani reaction din ba kawai tunani ta wuni yi a daki akan dukkan maganganunsu



ta fannin ayaana kuwa bakaramin drama ta kwasha da hajiy mairo ba, dan kusan irin kukan data sakata ranar shi tasake sata tace mata bata isa tazo musu da raini gidansu ba dan kaf jikokinta babu mai raina babba sai uban gidanta rayyanu...


haushi yasaka ayaanah tay zuciya ta bar gidan tun safe taje wajen ruthy da niyyar wuni awajenta sai kuma taje ta samu ruthyn babu lafiya, ita ta zauna ta mata aiki shara wanke wanke abinci ta sa mata ruwan wanka ta rakata har asibiti ashe ruthy kan ciki ta zubar na wani dan tsohon fan cult dinsu 4yrs kenan take masa kamr matarsa na aure which he can have sex with her anyday anytime haka suke gudanar da rayuwars dan shine ma yasata a cult dinsu gashi tana balain sonshi kmr ranta


kwasam rana dayace mata lallai lallai sai tahadashi da jikin ayaanah sabida bai taba muamala da virgin ba kuma a cult dinsu ance in yay zaiy arxiki itakuma sanin hakan bazai taba yuwa ba yasa ta bijire masa wanda tun daga nan kuma matsala kala kala suke bibiyar raywrta har tafarajin kishin cewa duk tarayyarta da ayaanah ne ya kawo rugujewar rlshp dinta da kuma jin dadin rayuwarta, she alwys try her best to keep it hiding sabida harga Allah tana daraja ayaana tana kuma ganin girman hajy mairo but loosing her pregnancy nd her BF jiya kuma ya saka komi ya dawo mata afreshhh


ayaana bata fahimce komi ba tsakani da Allah ta zauna da ita har yamma yay uncle moh ya dinga kirarta akai akai ita kuma ta kashe wayarta, gashi ba asan inda taje ba ranar shima bakaramin baci ransa yay ba dan sosai ya kashe kudi wajen booking musu table da romantic proposal decoration har yamma yana zaune awajen yana rubuta mata zafafan text na bacin rai wnda duk basuje ba sabida kashe wayarta datay .


dagata bangaren ibaad kuwa baccinsa ya sha agida, kafin yaje ball, yay few leisure activities dake sunday ne da yamma can ya dawo yay wanka ya saka kanann kaya saiga sultana ta shigo suna hade ido tace "yaa ibaad anty zainab arifah ce tazo tana can waje tace ince maka sauri take zata wuce if u cud spare her a minute..cikin kyabe baki yace "okay" ficewr sultana bada jimawa  ibaad ya sauko ya fito ya same zainab arifah acan kofar kusa da gate da wani katon jeep tana tsaye...tun daga nesa daya mata kallo daya yaga kamr ba acikin hayyacinta take ba. she is on high drugs sama sama takejin kanta but kwakwalrsa bai kawo masa harta fara irin wann rayuwar ba yadauka wata sabuwar iskancin kawai taxo masa dashi



idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[11/12, 19:14] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️4️⃣4️⃣

ibaad yana karasowa ta wajen motar zainab Arifah tay sauri ta sauka ta fito waje dan karma yagane a buge da kwaya take sosai..


tana sauƙa daga jeep din tay leaning back dinta to stand firmly wasu irin mayun idanu ta zuba masa ayayinda yake tahowa lokacin kwakwalwrta yakasa auna mata yadda zatay tafara ma rabuwa da wannn hadadden gayen wanda duk duniya ta zaga haryau bataga namijin da ya balain dacewa da ajinta kamarshi ba.


idanunta taji ya ciko da ruwan hawaye zazzafa, tuna nasihan iyayenta da kuma dalilinsu da suka bata kai koma ba dan haka ba, kwana nan fa tay kisan kai snn babanta ya rufa mata asiri kai tsaye, bayan nan kuma yadau arzikinsa me bala'in daraja ya dorata akai babu shakka kodan hakan ya canci ace ta iya sadaukar masa da komi na rayuwarta saidai kuma batajin soyayyar ibaad abune wanda da zata iya binnesa cikin saurki, dan duk jimawan datay acikin tunani kwakwarlwrta ya kasa bata wata mafita, abu daya kawai tasan she is very sure of inhar ta rabu da ibaad to karshen rayuwarta ne yazo dan akan abun duniya kam sam sam bazata taɓa iya tsallakeshi ta auri wani namijin ba...


sosai ta shirya daukar mataki but she has to ask him few questions kafin tasan me zatayi nan gaba.


muddiin ibaad zai aureta ta amince zata aje musu komi nasu da suka bata ta rabu dasu tabi ibaad a musu aure, idan kuma bai amince ba...she has a good  secret plan for all this eida ways tasan dai rasa ibaad a rayuwarta baya cikin options dinta gabaki daya.


idanunta nakansa bata ko kiftawa har ya iso gabanta yay mata sallama bataji ba cos she was soo lost in her tots har saida ya kira sunanta snn tadawo cikin hayyacinta suka gaisa...kai tsaye yace "u wanted to see me...wani irin gyara tsyuwarta tay tareda sauke ajiyan zuciya tace "yes..


cikin gyada kai yace okay go on kinga ankusa a kira sallah..


cikin lumshe ido da budewa tace.. a farko dai i wll like to apologise gameda abunda mummy sukayi ma sisternka ayaanah kusan a nitse yace its unfortunatez But thanks..dan shiru tay can kuma muryanta na yar rawa ahnkli tace ibaad? yadago ya kalleta da kyau baice komi ba, da wani irin yanayi akwayar idonta tace" dama akwai wasu yan tambayoyine da nake so na maka but pls answer me sincerely its very important to me..girarsa na sama a dage yace "i am all ears..go on..


cikin sace ajiyan zuciya tace and pls keep ur answers short..


yace" Enuf of this rules na gayamaki zan wuce masallaci soon ko


tace ok..uhm...dama inaso nasani ne what is actually going on betwn us kagane like inason nasani are we in a real rlshp?


kai tsaye yace "No..next question pls..


cikin hadiye bakin cikinta tace "okay, have u ever felt sumting for me? like in ur hrt baka taɓa jin kana kaunar ace nazamo matarka ba?


..yace "Bantaba ji ba. 


cikin lshe ido da budewa tace "but u're aware that i cant even breath witout u ryt? nd kana nufin dagaske ne you cant marry me saboda kana da wata macen daban?? 


yace "hold on. where are we getting at with this boring cnversation


da karsashin bruise ego a muryanta mekama dana izza da fushi cikin tsimewa tace i just want to knw.. bcos i want us to get married next week kaga ynxu i am settled kaima ure almost free. you dont have to love me now, ni inasonka. kuma bazan iya rayuwa batare da kai ba ai anayin aure ahaka.. magana tay masa kamar na asalin yar kwaya


shiru yay harta gama magananta ya kalleta yace" zainab uve got to leave cos seriously banda wann lkcin..


da taurin kai a idonta tace but i am not leaving here untill u come to ur sense nd agree with me. nide aure kawai nake so muyi, bazan iya auren kowa ba saikai, tana gama furta hakan ta bude motarta ta jawo jakarta ta ciro cheque book na apex bank of america ta yaga leaf daya aciki ta miƙa masa lkcin hannunshi na cikin aljihu sai bai karba..


desprately tace pls take this,write any amount of money nay alkwari i will compensate the girl ure obsessed with kuma i will sponsor our weding inma shiri ne bakayi ba, ive got a house nd everything..U have nothing to think abt


kwayar na wainata ba acikin hayyacinta ba tafara kkrin cusa masa cheque din a aljihunsa da wani irin sauri, 


shikuwa yana zare hannunsa daga aljihun ya wanka mata wani irin gigitaccen marin da dawuri tafasa ihu tabi ta dauke hannunta ajikinshi ta ja baya tana maidafe wajen kusan a rude .


da muryan kuka ta dago zatay magana ya hade ransa ya nunata da yatsarsa yace ive heard enuf of ur insults keee ya isheki haka.. nd for ur information daga ke har ubanki bakuyi kudin da zaku saye soyayyata ko na macen da zan aura kwanan nan ba..ke a tunaninki har wani rufin asiri kike dashi da zaki zo nan ki kirani kina gayamin wannan kalar maganan banzan?who did u think u're zainab cos to me u're nothing jst a regulat spoil brat with no self worth.. wato dan jiya andoraki akan arzikin da bakisan zafinsa ba, wanda tun kafin kizo duniya aka gama ginasa shine har kin samu audacity da zakizo kimin burga dashi ko?toh ai ke karamar yarinyace wallah infact ure classless nd very stupid..i ques dis shud be ur last time talking to me naga raini tsakanina dake yafara yawa. ya girgiza kai "...youre just lucky ure my cousin sister today da wallh sainaci ubanki anan wajen naga waye gatanki, bana son raini nd if ur empty skull have failed to comprhend that then dats ur misery, my life is already moving on without you inkinga dama karki nemi mijin auren dazaki siyeshi da kudi ki aura ki tsaya kina hauka wata rana kuwa zan miki abunda baki tsammani inkika sake kulani...

 

hannunta dafe da kuncinta hawayenta ya fara zuba tace son da nake maka ne hauka??

then u have no idea what love is..u have no idea what i did bcos of ur love da har kake cewa hauka, wallah karya kake bakasa isa ka rabu dani ba...


yace thank goodness i dint ask you to do all those things... ur life ur choices ryt?? ke da Allah kiwuce..uve got to go.. nace bazan aureki ba kije kinemi wani ki bashi kudin.


dacan hawayene ke sauka akan fuskarta kamar ruwa tanata kallon bakin ibaaad din amma dataji dirin shigowar jeep din bappa zaidu cikin compound in da wani irin karfi ta fashe masa da kuka kamar dukanta akayi....


baice mata komi ba ya kama hanyarsa yay cikin gidan yabarta atsaye, da karfi take kukan har bappa zaidu yaa karaso yay parking car insa ya taho wajen da mamakin irin kukan fitar rai datakeyi.. yace zainab meyafaru ne what is happening? da wani irin gunjin kukan makirci tazo jikinshi tace uncle zaid bansan meye nay ma ibaad ya tsaneni ba, if he cant like me atleast i am a human being he shudnt be hurting me with his words.."


dan jawota bappa zaidu yay dan yadda take kukan sosai tabashi tausayi da muryan lallashi yace "kiyi hakuri doter its okay..kidena kuka...duk lallashin nan sai batace masa komi ba ta rungumesa saida har tay kukan makiricinta na kusan minti biyar ta kara daga mai hankli sosai snn ahnkli ta kwace kanta sounding depressed tana hawaye gwanin tausayi tace "shikenan uncle zanyi hakurin tunda abunda yake so kenan, amma uncle kace masa shima yana hakuri nimafa ba yin kaina bane nake sonshi dayawa haka...dede nan ta kara fashewa da kuka wani irin tausayi tabashi sosai tace' i will like to go home now kaina namin ciwo kaima inna taba maka wani abu kayafe min dan Allah.


tana fadin hakan ta juya cikin sauri ta bude motar ta shiga within few minutes ta waina shi ta fice a compund din da sauri..


hanklin bappa zaidu a tashe ya shigo cikin gidan yanamai kwalawa ibaad kira daga kasa wanda tun be sauko ba ammi babba tay maza ta fito dan tasan bai taɓa kwalawa ibaad kira ahaka da tsawa ba


'yaa zaidu lafya kuwa naga ranka a bace


bai amsa ba saiga ibaad din ya sauko kasa cikin ladabi yace 

sannu da dawowa bappa naji kamr kana kirana..


bappa zaidu yace "yes..inaso ne insan meyafaru yanxun nan awaje tsakaninka fa zainab Arifah? and why are you treating her like this ynxu idan wani ne yay haka ma kannenka zakaji dadi?u dont like her nd so what..dat doenst mean u shud keep hurting her with ur words gaskiya ban ji dadi ba..


kan ibaad na kallonsa kasa yace "Kay hakuri bappa..nayi kuskure. saidai bansan me tace maka ba nidai zuwa tay tacemin wai tanaso muyi aure next week snn ta ciro cheque na dollars ta bani wai she wll sponsor the weding shine nace mata karta sake min haka. nd beside bappa...nifa bance zan aureta ba


jin hakan yasa bappa zaidu yadan sauko da tempernsa da mamaki yace zainab dinne ta gaya maka haka nd she gave u a dollar cheque???


ahnkli ibaad yace eh kuma hakane kawai ya faru tsakanina da ita...


da mamaki bappa zaidu yace "toh?? ikon Allah indai hakane kam toh ai bata kyauta ba dan ba a siyan aure da soyayya da kudi. but kaima ai da kayi amfani da hanklinka awajen tunda kaga ka girmeta kuma ita mace ce u shud have mind ur words amma bakomi kaje kawai zan nemeka anjima


..cike da girmamawa ibaad ya amsashi snn ya haura sama


yana wucewa Ammi babba ta kalle bappa zaidu da tsananin haushi a muryanta tace amma wallah kabani kunya yaa zaidu

...toh wann wani irin danyen hukunci ne me kake nufi da bin bayansa dakayi dan kawai yarinya ta kawo masa kudi dan tsabar tsiya na bibiyarsa shine zai ki karba?? kudin gadon dayake juyawar yake burga dashi wallah ya kusa karewa cutar kansa ma zaiyi inbe aure zainab arifah ba dan wallah rufa masa asiri zatayi.



karkada kansa yay kawai bai amsa mata ba ya kama hanya zai haura sama tabi bayansa tana masifa "aikin banza aikim wofi yaro bakomin komi ba amma ana gani yana cutar da yarinya ana zuba masa ido, waikomi ya furta sai ahau kai a zauna ahau bashi gaskiya kuma fa munsani fa dan dan ba'aso ran uwarsa ya baci ne ake nonnokewa ba ason masa fada waishi dan gwall

..mmtswwwww


wani uban tsaki taja suna dede gabar sashensa tay kwana ta wuce dakinta da sauri ta dau wayarta tafara kirar anty safeera dan ta shafa mata gulma.



dagata bangaren zainab arifah kuwa tana ficewa agidan ta share makirtaccen hawayen datay ma bappa zaidu dan dama bana gaske bane so take kawai ta hada wani zazzafan plan wanda shine take gani amatsayin mata chance dinta na karshe na samun cikar burinta akan ibaad..


tana kuma sane da maganan ruqqy ranar da zata mutu na cewa aure tsakaninta da ibaad wundt be posbble, even if it will be, then its going to be her bgst karma..but damn all this magic nd astrologies...damn her parents..duk tay banza da su. 


yanzu lokaci ne da zata cire batun iyaye da kawaye ta dauki kwakkwrar mataki a hannunta koda mutuwa kuwa zatay in ankaita gidan ibaad wallah saita aureshi....


da wann maganganun aranta

ta isa gidansu, tana gama parking ta sauka ta samu hjy hamida a falo suka gaisa kamr ba abunda ke damunta


hajya hamida tace ur dad will soon be home for dinner we wll be expecting you at the table by 8pm


babu yabo babu fallasa tace okay mummy, daga haka ta haura sama tana shiga room dinta ta kore dukkan maids dinta tace suje can can waje sai ta kirasu..suna ficewa ta kulle kofar da key ta ciki


snn ta wuce gaban drwarta dake cikin mega walk in closet dinta tajawo wata jaka ta ciro piles of cocaine ta fasa ledan kadan da zuka zukan farshem kantinta takamfato a paper tazo dakin tazauna tasha sosai yahaura mata kai taji ta fice ahayyacinta dan abunda take shirin yi ba abu bane da hankali zai dauka ita kanta tsoron karta mutu ahaka takeji but is her one nd only last chance batada wani mafita kusan dole ne ta aikata.



kayan jikinta ta cire ta saka wani mekyau,snn ta zauna akan chair ta dau scissors me kaifin gaske ta rage tsayin gashinta dakenan dede kafadarta sama sama bata yankeshi duka ba, just enuf to prove that she is mentally tortured nd unstable, nan ta zubar da gashin kasa snn ta

jawo paper da biro ta fara rubutu kamr haka.


Daddy, mummy...Ban san ko me zaku ce ba, amma ina fatan a karo na farko zaku saurare ni da kunnen basira ba tare da kun kalle ni kamar wata yarinya marar hankali ba. najima ina kokarin yin murmushi saboda ku amma wallahi na gaji... Na gaji..da jin kamar babu wanda yake ganin zafin da nake boyewa kullum game da rayuwr soyayyata.


tana gama rubuta wann ta aje papern akasa snn ta sake dauko wani fresh ta rubuta


Dearest Ibaad, masoyi na..Kai ka fi kowa sanin cewa ban taɓa roƙonka komai na duniya ba abu ɗaya kawai nakeso kabani wato zuciyrka da kulawarka da lokcinka amma Sai ka guje ni kamar ni wata mummn abace, Na san baka sona, na sani tun tuni. Amma da zafi sosai dayau ka fito ka nuna min kamar ban cancanci komai daga gareka ba.


tana kaiwa nan ta sake yagewa pagin ta jefar akasa

..ta dauko final paper ta rubuta..


the three of you shud knw dat i respected ur decisions, kuma shiyasa zan yanke ma kaina wann hukuncin bawai dan na saɓa muku ba sai dan bazan iya saba maka ba daddyna.ina rokonka kayafemin amma bazan iya rayuwa babu ibaad ba, na yi iya ƙoƙarina, na yi kuka, na yi haƙuri amma babu wanda ya kula da damuwa ta. Idan wannan rubutun nawa ya dameku ko ya taɓa ku, to hakan kaɗai ya nuna cewa akwai ɗan ƙaramin wuri na fahimta a zuciyarku da ya rage min. kada ku damu dani. inna mutu komi zai wuce mana, kowa zaiyi rayuwarsa cikin sauki..ni kuma kabari na zai zamo wuri ne da babu wanda zai iya tambayana me nake ji aciki, nide dan Allah ku yafemin! 


yours zainab arifah..


tana gama rubuta last part din tay wani irin darriyar mugunta sann shima ta yarda dashi kasa ta dauki wayarta taduba internat tay dan browsing sai tay maza ta maida hoton ibaad a screen inta tay setting maid alarm 10min sai dau scizzors ta yanka wani karamin jijiya a hannunta atake jininta ya fara zuba along with the effect of drug alarm dinta na bugawa ta wuce uncounsious.


dede nan private maid inta elizabeth ta karaso jin alarm din tay tsammanin hala wanka zaynab arifah take son tay dan baifi minti 30 ya rage babanta ya dawo ba tana isowa tay knocking sai shiru, tun abu na wasa wasa har ta sauka taje ta karbo spare key tazo tabude kofar tana ganin zainab arifah da scizzor a hannu akwance ga jini ga yankakken gashi ga 

takardu akasa a mugun razane ta fasa ihu tayo waje


hajya hamida duk ta dauka shirmensu da zainab din ne jim kadan kawai taga elizbeth ta shigo a ruguje tana ihun sunan zainab Arifah kusan arikice hajy hamida ta miƙe ta bita taje ta tarar da halin da ake ciki


da sauri suka applyng pressure a inda jinin yake zuba sosai


kafin kace wani abu gidan ya balain rikicewa marmaza hajy hamida ta kira mijinta kafin ya iso harta riga ta isa emergency da zainab wanda atake aka shige da ita cikin Resuscitation Room batare da tunanin ko zatay rai ko ma ta mutu ba..



acikin tsananin kaduwa da tashin hankli hajiya hamida take jeka ka dawo a ward din sai nanata ta shiga uku takeyi cikin kuka da dukan wasiqun a hannunta tana karantawa tanajin wani irin tsoro da fargaban rasa yarta mai tsanani yana lullumeta


jim kadan ƙofar wajen ta buɗe da wani irin karfin tashin hankali prof ne ya shigo ciki da sauri tareda gaggawa da wani irin yanayi da ko shi baisan wani hali yake ciki ba, yana tahowa kamar iska da sauri sauri gudu gudu jikinsa yana rawa rawa  kamr an zuba masa ruwan kankara kusan a rufe ya damke hajy hamida yana cewa “Ina take? Ina Zainab Arifa? Ina Arifah? kusan a muryar da ba tasaba jinsa ba yake maganan  duk hnklinsa yakai kolowar wajen tashuwa, wani irin kuka hajy hamida ta miƙe tsaye dashi babu hankali ajikinta ta bashi wasiqun jikinta na kyarma tace alhaj yanxu nan suka shige da ita ciki ta zubar da jini yayi yawa na shiga uku alhaji yata kenan kwalli daya na shiga uku


tana maganan idonsa nakan rubutun hannunsa na rawa rawa, har saida ya gama karantawa snn ya ja numfashi, tsayuwar cak yay jin Kalmomin nata namai sare masa zuciya kakkarfan jiri ne yaso ya kwashesa yay saurin  mannuwa da bango ya dafe kansa sosai, snn ya rufe idonsa da ƙarfi kamar yana ƙoƙarin hana kansa amincewa da abubuwan da ya karanta yanxu



kusan a rikice yace “hamiida Me muka yi wa yarinyar nan? Me ta rasa a duniya?”yanxu akan wann tsinannen yaron har zainab zata kashe kanta??ya furta muryarsa ta karye da karfi.


hawayen hajiya hamida na gangarowa tace alhaj ni damuwata da zainab arifah bata nuna min komi ba, bata yi magana ba, she even told me yanxu zata sauko a ci abinci only for her lock her self up and try to take her own life wallah wallah idan yata ta mutu sai dai ayi biyu babu yaron nam bai isa ya shaki numfashi a duniya ba dan da hannuna zan kasheshi



prof ya yi wani dogon jan numfashi ya share fuska da tafin hannunsa ya kara kallon letters din suicide note ɗin nata ya kara memeta karanta kalmomin dake cikinsu cikin natsuwa duk dama zuciyarsa tana farfashewa.



zuciyarsa sai tambayrsa yake wai shin yarsa zainab ce ga rubuta hak  ta rubuta haka kuma a gidansa kuma wai ba lura ba.” ji yay atake hannunsa ta yi sanyi ya kasa numfashi na dan lokaci.


yace lahawla wala kuwwa sam ni na kasa gane kan yarinyan nan i tot zainab is way more evolved than this, batay tunanin halin da  zan shiga ciki ba?? lallai yaron nan ya cuceni



cikin jin zafi hajiya ta ce tana kuka alhaj ai duk shawararka ce, saida nace maka tun tana karama a rabata da wann gurbataccn soyayya ta yaron nan dan Bana son a ce ita ce da matsala kace min sam sai tagirma toh gashnan ta girman babu abunda ya canza saima wanda yay qaru .



baice mata komi ba ya jingina da bango idonsa arufe numfashinsa ya yi nauyi inda dede lokcin ne wata Nurse ta fito dukansu suka miƙe da sauri sukayo kanta



tace sirr maaam kuy hakuri the  Doctor is stabilizing her…amma kusata a addua


atake hajiya hamida ta narke da wani irin kuka prof ya rike kujera saboda tsananin raunin zuciya.


“Zan iya ganinta?” ya tambaye nurse din cikin murya mai taushin da ba a saba ji daga gare shi ba.


Nurse ta girgiza kai tace

“Ba yanzu ba sir… but she’s 

fighting…


cikin rutse idonsa ya dafe kirjinsa for hours suna zaune cikin jimami daga su sai masu gadinsu.



daga can gidan kuma babu wanda yasan meke faruwa,

dan tunda uncle moh yay asarar kudadensa da time dinsa ya gama jiran ayaana ransa ya turmusa yay baqi ya dawo gidan yazo zai sauke haushinsa da masifarsa a gida hajiya mairo har tace masa ai ayaanah tun safe ta fice bata dawo gidan ba taje wajen ruthy sai sann yaji dama dama saidai bakaramin disspointed ya zama ba....


dake sosai anty safeera tana lura dashi ynxu sai jikinta tuni ya fara bata, haka tay ta tambayarsa meyasa mood dinsa ya canza, yace mata ai matsalar business ne kawai sai tay shiru ta kyalesa batace mai komi ba.


har saida ayaana ta dawo gidan kafi talura taga duk ya kasa zama yana ta neman hanyar da zai saka akira masa ita amma dake idon da anty safeera tazuba masa yau yawa yasa bai samu wann daman ba



washe gari kuwa da sassafen Allah labarin abunda ya faru da zainab arifah yazo kunnen hajya mairo anty safeera ce tazo tasanar dasu dan itama a bakin wata kawar hajy hamidan taji da safe cewa zainab has tried to commit suicide last night...


wann labari yasaka kaf gidan aka rude hajiya mairo ta fara ihu tana koke koke gida ya zamo kamar na mutuwa.


tun safen ta dinga kirar bappa zaidu dake monday ne wyarsa na falo shikuma yana daki bai gani da wuri ba, ammi babba ne tazo da gurmi ta hau gaya masa..


wayar dan uwansa uncle moh ya kira yaji yana busy yay sauri ya kira hajiyan kawai cewa take masa yazo ataro duka suje asibitin tare yar zayyanu kenan kwalli daya a duniya da kyar Allah ya bashi maza maza aje masa dan batasan wani hali zayyanu zai shiga ciki ba.


the story came as a shock to ibaad ya sha mamaki amma bai nuna a fuskarsa sosai ba kowa ya fara shiri zasuzo family house asan me za'ayi


within 20 min bappa zaidu da ammi babba da ibaad da sultana duka suka sauko kasa jin wani sabuwar tashin hayaniya awaje na tashi tundaga gate kakejin karar shgwan motocin polisawa


mota guda aka turosu maza sunkai sha biyar suka tunkare su bappa zaidu


"bappa zaidu yace officers lafya naganku haka dayawa a gidana?


cike da girmamwa babbansu yace "lafiya kalau sir. nan ya ciro papern arrest warant ya mika ma bappa, yana maicewa sirr we are directed frm above to come nd arrest ur son person of Dr ibaad almansur with immidiete effect...


cikin katsesu da tashin hakali bappa zaidu yace and on what charges...arrest kuma? dis is abslutely ridicoulos!! me yayi?


nan babban cikinsu yahau ma bappa zaidu bayanin wai charges ne akan Intentional Infliction of Emotional Distress (IIED), he is also going to be held in detention for infliction of emotional trauma to zainab arifah leading to self harm..


its just a protective custody detention, some interrogations nd detntion for some hours.


wani officer yana kkrin sakama ibaad handcuf bappa zaidu ya daka mai tsawa yace heys dont u dare... barawo ne, ko kuma kisan kai yay da zaku taru masa 



ibaad ya kalle bappa zaidu yace bappa karka damu i will go with them ku kuje gidan  


bappa zaidu yace Dats not ur decision to make young man...


driver ya kira aka saka su ammi babba da sultana zuwa family house hanklin sultana yay bala'in tashi tun a mota take kuka ammi babba kuwa Allah Allah take su isa ta bada kanun labarai



daga nan kuma bappa zaidu bai sake an saka ibaad a motar polisawa ya daukesa dakansa suka bisu police station din, ya zauna a waje suka shiga da ibaad ciki



fadin irin tashin hanklin da family house ya shiga da ammi babba taxo ta gaya musu antafi da ibaad an kulleshi tareda bappa xaidu bazai kiyastu ba hankalin kowa saida  yay mummunan tashi


abubuwan suka taru suka ma ayaana nauyi a kirji musmn ma tunda ammi babba tafara zuba wani irin karya da makirci agaban hajiya mairo..


nan ta kwashe labari a juye ta gaggaya musu cewa ai fada sukayi da zainab din jiya da yamma,kuma zainab din ta bar gidansu tanata kuka basu san me ibaad ya gaya mata dahar taje tay tunanin kashe kanta  tace musu kuma bappa xaidu yaxo yagani yana daure masa gindi duk da ma sunga halin da xainab din ta shiga ciki


labarin take bayarwa tana kuka agaban hajya xaka rantse da Allah agabanta akayi komi dan babu irin karyan da batay akan ibaad ba, kuma ta kwashe komi tace lefin bappa zaidu ne dama tajima tana gaya masa ya sakalta ibaad, baya ganin leifinsa ko yay laifi baya masa fada snn yana nuna fifiko da bambamci, cikin habaici tarinka cewa ai yanayi ne dan ya burge ammi karama bata dai fito fili ta kama suna ba amma babu kalar gori da habaicin da batay ma ammi karama  ba.


tun jin wann batu hajy mairo ta birkice ta fara tsine tsine tana zagin ibaad, ayaana tabar wajen ta koma daki tanata kuka dan tasan bazai taba yuwa yama xainab wani abu me muni da zaikai har haka ba, sultana ne take rarrashinta sai safiya data fice wajen jin gulma..


ammi karama batace komi ba tay shiru musm dataga kowa ne yahaura sama, uncle moh, ammi babba da su anty safeera duk magana daya suka taru suna gayawa hajiya mairo cewa laifin duka na ibaad ne kuma ya samu daurin gindi ne daga bappa zaidu .


cikinsu babu wanda yaso yay bincike ko yasan asalin meke faruwa kusan kowa ya hau dokin xuciya sai tay shiru abunta batace komi ba.


uncle moh ya kira prof yafi sau talatin amma bai daga ba maza maza yace ayi shiri kawai aje asibitin tunda bappa zaidu yana tare da ibaad a police station...



daga asibiti kuwa kusan sabida content na hard drugs ajinin zainab arifah yasaka bata farka akan lokaci ba it took her 6 good hours snn aka samu ta dawo hayyacinta she wake up very weak duk an lakaba mata IV fluids da pressure dressing a hannu


tunda asubah data farkan iyayenta kowa yaxo jikinta kowa da salonsa na nuna mata soyayya amma kuma hawaye take sam sam taki tace musu komi tun suna mata lallashi har suka aje so agefe suka fara mata fada kowa ya harzuƙa yana fadin mata asalin manufarsa akan tarayyarta da ibaad tuntunin nan saiyau suka iya cire so da gata sukahau bayyana mata asalin yadda basu kaunar ibaaad kuma suka tsane tarayyarta dashi kwata kwata..

saidai basu sanar da ita cewa har sunsan an kama ibaad din ba


their words of hatred akan tarayyarta da ibaad din'nt hurt her much sabida ta riga ta jima da lura da hakan musmn ma awajen mummynta hajiya hamida da tasan ko kadan bata kaunar dangin ubanta bare kuma ta haɗa jini da wanda take ganin kamar bai kaisu arziki ba. 


duk hargaginsu da lallashinsu shiru kawai tay tana hawaye batace musu uffan ba wanda hakan ya kara daga musu hanklinsu sosai.


strickt security akasa a inda suke, wajajen 10am manyan gidan gabaki daya suka taho asibitin a motocinsu amma haka kememe aka hanasu shiga ciki..


hajiy hamida sosai ta haukace ta haura can sama da fushi da tsana tace Burin yan uwansa kenan dama su kashe masa yarsa kwalli daya, dan shima a cusa masa baqin cikin da zai kashe shi, snn idan ya mutu a dauki dukiyarsa abasu 


tana masa kuka ta maimata masa wann maganan cikin bori da fushi yafi sau hamsin..


daga wajen kuwa bakaramin rikici akayi da hajiya mairo ba in kaganta ma daukawa xakay an mata mutuwa, can daga baya saida akazo aka mata wayo akace ai zainab din tana cikin wani hali ne ana kkrin dagata ba asok hayaniya kuma hukuma na ciki ana bincike shiyasa ba ason kowa ya shiga kawai suje gida.


bada son ransu ba ammi babba ta dawo da hajiya mairo uncle moh ne da anty safeera kawai suka tsaya a reception na asibitin.


ammi karama kuma daga wajen ta wuce police station duba halin da su ibaad suke ciki...


tana zuwa station dake ana matukar daraja familynsu sharply aka kaita wani waiting room ta samu bappa zaidu a zaune yana kan waya suka hade ido dan hawayen datake dannewa atake suka fara sauka katse wayar yayi har tagama karasowa gareshi tun basu gaisa ba yace haba Fatima meyasa kema kika zo nan kuma baga ni nan anan ba?


da matsanacin damuwa a kwayar idonta tace "yaa zaid Kay hakuri kawai so nake naga halin da rayyan yake ciki


bappa zaidu yace 'interrogations ne kawai babu komi ba tunda bawani laifi ya aikata musu ba neman fitina ne kawai. the highest they can do is to detain him here kuma insha Allah i wont let that happen.


cikin lumshe ido da budewa da karyayyen zuciya tace Amma meyasa rayyan zai saka kansa acikin wnn matsalar..cikin fashewa da kukan da yazo mata bazata tace kaikuma kamar baka ganin lefinsa. yanxu duk cikin gidan kowa yana fushi dashi, hajiya ta dau abun da zafi dan Allah inde rayyan ya aikata wani abu na cutarwa akan zainab kawai ana gaya masa gaskiya ni wallah banason hakan yaje ya jawo masa karin baqin jini acikin gidan nan dan baida kowa a duniya inbasu ba.


cikin sassauto da muryansa kasa yace haba fatima yau kece da kanki kike furta min wann maganan? i tot kinfi kowa sanin cewa ibaad kamar dan cikina na daukesa meyasa kike tunanin inhar yay wani abi ba daidai ba zan zuba masa ido in kyaleshi...in dis case he is just a victim of circumstances tsaya masa yakamata muyi bamu hau dora masa laifi ba...ita hajiyar tasan asalin meyafaru ne??


ammi tana share hawayenta tace ni bansani ba amma ai maman sultana ce tazo ta gaya mana wai fada sukayi da zainab din jiya shine ya mata wani abu hartaje tay tunanin kashe kanta..kuma tace tun jiya kay shiru baka masa fada ba duk dama agabanka akayi komi


ahnkli yace fatima

ive personally talked with zainab jiya, nazo kam na sameta tana kuka nd she told me they had a fight..da naje na tambaye ibaad kuma yace min tazo tace masa ne akan suyi aure next week, snn ta dau dollar cheque ta bashi claiming wai zatay sponsoring auren...


i scolded him sabida tace min yagaya mata magana dabai mata dadi ba, but dan yaqi karban wnn qudurintan kuma sai nahau masa fada akan me?an taba siyan soyayya da kudi ne ko ana dole ne?..kuma kekanki kinsan da wuyane in iyayentan ma suna sane da wann abun, wallah inda ya biye mata wani matsala na daban zata jefashi aciki...karshe suce yay manipulating yarsu ya sace musu kudi, ko su masa sharri cewa shi yy influencing maganan aure akan yarsu..na lura kamar kaf kuna yin abune kamar bakusan waye ubanta ba. he will protct his child bazai taba karban laifin yarsa, so why i cant protect mine, badan ganin darajar su hajiya ba da nima fa ina da dama in shigar dakara akansu ai ba a relshp na dole, sun takura ma yaron nan tunda jimawa ohh wato mune bamu iya kaiwa kara ba ko? is not fair mana haba fatima...nayi ma yara na alkawari bazan musu auren dole ba saidai a bisa qaddara kuma kema kinsani, i cant force ibaad ya aure wacce bayaso gaskiya...so wnn kananan maganan raihanatu da hajia kawai kibarsa dukn su basu san asalin meke faruwa ba...kema kiy hkuri ki kwantar da hanklinki babu abinda zai same ibaad in sha Allah..


shiru tay kanta na kallon kasa har ya gama maganan kafin can ta share hawayenta ta dago kai cikin sauke ajiyan zuciya tace "toh shikenan..inde abunda ya faru kenan da sauki 

dan wallah hanklina ya bala'in tashi da irin magngnu da ake kanyi akansa acikin gida.


yace "karki damu in few hours zamuje gidan in sha Allah babu komi sai khairan..



daga haka suka zauna awajen har sai kusan 12:30am to 1pm ma rana kafin suka sake ibaad daga interogation room ya fito ya samesu


bappa zaidu da ammi karama suka hau tambayarsa me akace masa bai boye musu komi ba ya gaya musu


after a while bayan sunyi maganan sai hukuma sukazo sukace zasu rikeshi detention sai jikin zainab yay improving out of danger zuwa yamma azo a daukesa


...bappa zaidu ya karkada kai dan tuni ya gane cewa prof ne kawai yake bada oder a case din nan bawai zunzurutun aikin gaskiya akeso ayi ba


dake shima ya kira mutanensa hakanan yasaka adinga saka masa ido, wanda yasa baiwani damu ba yasako ammi karama agaba suka dawo gida


sun iso gidan arnd 3 na yamma tun a mota yake bawa fatima hakuri saidai tunda hajiya ta gansu bataga ibaad ba tafara sabon hauka tana tuhumar bappa zaidu me ake ciki ita kuma ammi karama batace komi ta wuce dakin ta tanata hawaye sosai.


tun a wann lokcin bappa zaidu yafara ma hajiya bayanin abunda ya faru jiyan amma ta nuna masa kamr bata ma gane meyake fada ba, kowani furuci dake fita a bakinsa abaibai take jinshi, gani take bin nayan rayyanu kawai yakey ,zaa kashe mata jikarta zainab arifah, za'a kuma saka danta zayyanu acikin baqin ciki da kunci...


abu kadan saita cemai aibkao zaidu dake kai kana da zuka zukan yaranka ai dolene abun bazai maka zafi ba, mutuwa fa ba wasa ba..inda kai adali ne da kamata yay ma kace ma hukuma akai rayyanu prisona

inyaso yaje can yay muguntr sa, acan yaro shaidani, wallah wallah ubansa baida wann baqin zuciya, mustapa ba haka yake ba dan yafi kankara ma sanyi gashi da hakuri amma kuma yaje yahaihu mugun yaro

aikodan tausayin rai ya kamata rayyanu ya amshe yarinyar nan amma dake kuna goya masa baya toh gashi nan abunda ya jawo..


bappa zaidu dayaga ba fahimtarsa zatay ba hudu na yi ya mike ya wuce masallaci daga nan ya fita ya koma station din dan yajira time na releasing ibaad yay ya dawo dashi gida.



iyaka su maheer ne kawai suke kiransa uncle moh ko sau daya bai kira ba duk dama yaga miss calls din bappa zaidun na tun safe.


shida da anty safeera dakyar aka barsu suka shiga wajen zainab arifah suka duba ta saidai haryanxu taki magana da kowa sai kuka da yamma liss iyayen suka matsa akan zasu wuce da yarsu gida dan abata cikakken kulawa acan


baisani ba already zainab ta riga ta hada plan dinta da nala kafin tay aika aika ta tura ma nala text cewa tazo duk asbitin daka kwantar da ita ta aiwatar mata wani plan....


a fuska zakaga kamr she is too traumarized to even speak, amma tuni nala tazo ta zaga tabiya likita makudan kudi akay abunda zaayi aka faking result dan ta saka iyayenta su rasa duk wani makama.


ana gama processing sallamarsu doctor ya kawo ma iyayen tarin bayani game da Somatic Complaints kamr body weakness + headaches + fainting yace musu yanxu fa inhar zainab bata samu cikar burinta nan kusa ba she wil be attacked by frequent body weakness, headaches har da kuma sumewa on a regular basis.. snn zai iya haduwa mata da Adjustment Disorder me tattare da intensed Emotional Collapse where she will become too sad too withdrawn, too fragile.


in aka kira sunan ibaad zatana firgita, zataki cin abinci, zatana yawan kuka zatana tsaya cak tana kallon bango. nd with time zata samu full emotional damage wanda inbasu wasa ba sai ankaita therapy na watanni shida awani waje.


bakaramin tashi hanklin iyayen zainab arofah yay ba, dan karfin gwiwarsu na batun tsayawa kyam akan batun su na hana auren tun anan ya fara gushewa musmn ma hajiya hamida datake ganin rayuwar yarta ya kare kenan inhar suka kyaleta ta samu cikakken tabu hankli


zainab arifah is busy pretending nd watching them danma ta dada tsoratasu suna kaita gida ta dinga kuka tana kwalla kiran sunan ibaad tana jan zuciya tana suma kamr ba acikin hayyacinta sai can kuma kaga ta farfado gabaki daya sai taki musu magana taki kuma taci abinci..



komi a idonsa anty safeera akayi ga ammi babba na kiransu akai akai ana bata labari haka zata kara maggi da gishiri taje gaban hajiya mairo tazauna ta zazzageshi duk saida ta tayar ma tsohowa da ciwon hawan jininta, ranar karshenta itama ruwan drip aka saka mata sai Allah ya isa take jama rayyanu duk dama tasan abunda take furtawa yana ma ammi karama zafi sosai amma ji take kamar ai ɗa baifi ɗa ba


babban damuwarta shine rayyanu zai mata asarar jikarta snn zai jawo gaba ya tsananta atsakaninsu da danta zayyanu dan tasan bazai taba yafewa ba



wajajen 5:30 bappa zaidu ya gama processing release na ibaad, mutanen prof din har wani cewa suke in wani abu ya sake tashi zasu kara nemansa


bappa zaidu yaja tsaki ya sako ibaad agaba bai sake sunje family house tunda ya gama lura da take taken hajiya mairo ba gaskiya take da niyyar bi damuwarta na kasa ya dauki laifi dan kar na sama yay fushi


suna isa gida ibaad yay wankansa yazo masjid yajasu sallah banda da maheer daya kirasa bai sake wani magana da kowa ba after ishai bayan sunci abnci bappa zaidu baice masa komi ba yace masa kawai yaje yay bacci gobe da safen duk zasuje family house a zauna ayi magana


cikin wann daren fake draman da zainab arifah tama iyayenta bana kadan ba, suna bada baya zata sha drugs tay ta wasu abubuwa sukuma hanklinsu duk sai ya hargitsa ya tashi...


ranar haka aka zauna cirko cirko basuyi bacci ba washe gari sassafe prof yagama tunaninsa ya zaunar da matarsa yace mata bazai iya rasa rayuwar yarsa kwalli daya akan wann case din ba tunda haka arifah din ta zaba so be it...amma kuma saiyaje shi can wajen mahaifiyarsa sun tattaunawa ya dawo snn zaizo ya saka ma yuwar auren nasu tsauraran dokoki wanda dolene abi, itama zainab arifah din dole tabi. kusan babu yadda hajiya hamida ta iya itama haka ta goya masa baya dan kawai su ceto rayuwr yarsu....


da sassafen ya shirya cikin manyan kaya ya fito banda tea dayasa acikinsa baisha komi ba shidakansa yadauki babban motarsa as early as 7am da sassafen sai gashi nan a family house fuskarnn tashi a matukar daure kamar wani mala'ikal daukar rai.


 yana kammala parking tun awaje yay gamo da uncle moh da jallabiya ajikinsa kowani gaisawar arziki basuyi ba suka karasa ciki, cikin sashen hajiya mairo direct yay dashi wanda tunda tagansa tafara koke koke tana maganganu akan abunda ya faru, mrzamaza tasaka a kira mata zaidu da ahalinsa duka suzo gida ayi magana anan atare...


maheer is already on his way dan da sassafen yabi jirgi zai taho, mujaheed ma tun jiyan yafara neman exit dan abarsa yaxo amma abun baiyu ba


mujaheed ya gama waya da bappa zaidun kenan an taru a dinning za'a breakfast saiga kirar ammi karama wanda da gangan hjya mairo tace lallai ita zata kira musu zaidu ai inyaga kirarta ne zai dauka da wuri kuma yazo akan lkci....


tana kuwa kira dake wayarna hannunsa ya dauka cikin nitsuwa da sanyin murya yace "fatima antashi lafia? da wani irin sauri ammi babba ta aje cupin shayi ta zuba masa wani dan uban ido mai tafe da mugun harara


after uttering few words yace toh bakomi muna zuwa snn ya katse wayarsa ya aje akan table yay banza da batun ya cigaba da breakfast dinsa hankli kwance dan baiga abunda zai sakashi yaqi cin abincinsa akan zuwan prof na


tajira tajira taji ya musu bayani sai shiru kai can dataji abun ya cicciyota sai tace 'yaa zaidu gidan lafya daiko ina dai ba jikin hajya bane ya kara tashi?? a dan dakile yace "a'a kudai kammala breakfast dinku ahankli sai muje muji..


suna gamawa kuwa kowa ya tashi sai ya kalle ibaad yace 'ibaad kai kazo kasameni a dakina yanxu zai aikeka office dina inyaso inka dawo saika wuce can ka samemu


cikin girmamawa ibaad ya amsashi, suna shiga dakin ya bashi aiki da akalla yasan zai dauke sa 2-3 hrs kafin yagama dan kwata kwata baijin yau zai iya zuba ido aje can gidan asako ibaad agaba a dora masa laifin komi snn agaya masa bakaken magana dan yana tabbacin cewa hajy mairo intana gaban danta zayyanu ba lallaine tabi bayan gaskiya ba....


he prefer to face them alone than ya barsu su taru suci ma ibaad mutunci da sassafen nan.



ibaad ne ya fara ficewa da aikan kafin nan suma suka shirya suka fito shida matarsa da yarsu sultana suka wuce family house....


coment nd share ur tots


#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[13/12, 09:54] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️4️⃣5️⃣


Sai Wajajen karfe 8am saura kafin nan ahalin bappa zaidu suka samo isowa, wani irin shiru gidan ya dauka kamar babu mutane aciki in banda safiya da ayaanah da sultana banga wani mahalukin da baya falon hajiya mairo yau ba,

sanadiyar rashin isowar Bappa zaidu agaggauce, yasaka hjya ta umarce ammi karama akan tay musu breakfast while they wait, within few mins ammi karama ta gama aka kawo  dadin qamshin wainar kwai, da su pancakes, kunun madara, da irish pritatas duk yabi yacika hancin prof yanata basarwa da kyar hajiya mairo talallabe sa yadauki abincin ya taɓa kadan dan da wani irin gingimammen rashin mutunci da girman kai tareda mnyance ya taho yana kallon kowa dan iska awajen.


banda ma Hajiya data masa tarban nuna masa tausayi da baiyi tsammani ba da hala ko xaman jiran zaidu bazai iyayi ba.


sun fara ci kenan bada jimawa ba saiganan sallamarsu bappa zaidu idon kowa na bakin kofa ana tsammanin ganin ibaad atare da su sai shiru har suka karasa shigowa aka fara gaishe gaishe nan tay general nasiha game da abunda ya faru da furuci masu cike da nuna son kai da kuma bangaranci tanakan bayyana musu prof a matsayin wanda aka zalunta aka tashi kashe masa yarsa kwalli daya


babu wanda ya tanka har tagama nasiharta snn takore duka matayen gidan aka barta daga ita sai yaranta su ukun a kewaye da ita


wajen atake ya dauka da shiru bada jimawa hajiya mairo tafara magana cikin mita


"kai kuma zaidu ya naga bakazo da uban gayyan rayyanu ba kodan tsabar raini yasa yaga bazai iya zuwa amsa kirana ba?


ba yabo ba fallasa bappa zaidu yace ibaad ai baida raini hajya, zaizo..nine na aikesa!


cikin karkada kai tace kullum acikin shan bakin sa kake toh wallah yau kwata kwata bana son raina ya baci da ku dan wann abu daya faru da yar jikata zainabu sam baiyi min dadin ji ba ace kuna yan uwan jini aima bai kamata azo ana samun hali irinna mugaye marasa tausayi acikinku ba.


kai kuma zayyanu nasan an riga an cuceka amma hakuri zakayi kasan ance zaka haifi da ne baka haifi halinsa ba, aikai kasan waye babban yayan naku marigayi mustapa, mutunin kirki ne sam baida hayaniya, yo aiko uwar rayyanun ma ba haka take ba ni sam bansan a ina yaje ya samu nashi halin ba.


Da wani irin izza prof yace "A ina kuwa zai samu bayan irin tarbiyan da ya taso dashi ajikinsa kenan mama, ni ba nazo nan bane dan in tsaya jin wani hakuri. ke kanki kinsan anjima anaso aga bayana da ba'a gani ba shine aka turo min wani shaidanin yaro yake son ya ruguza rayuwar yata toh wallah bazaiyu ba.


cikin katsesu bappa zaidu yace hajiya ban fahimceku ba wai maganan waye akeyi ne haka? 


baki bude ta kallesa tace waye kuma inba rayyanu ba, yanxu kai zaidu abunda yayi jiya da rayuwar yarinyar nan yay mata adalci kenan? aikamata yay ace ka tasosa agaba yaxo ya tsuguna anan agabanmu ya bawa zayyanu hakuri akan tashi kashesa masa yarsa kwalli daya daya tashi yi, dan tsabar daurin gindi ai aikansa kayi kenan shi bazai nemi afuwar kawunsa ba ko??


bappa zaidu yace "aa hajya, yarsa ce dai ta tashi kashe kanta dakanta, ina kuma ruwan ibaad aciki?..snn Abunda ya faru jiya fa ya shafe kowa, bangane kina neman ki dora laifin a bangare daya ba in har abunda kika tara mu akai kenan banga amfanin zuwa na nan ba, dan inhar baza'a yi magana cikin gaskiya ba babu amfanin taro mu anan


da wani irin izza prof yace "wani gaskiya?? yanxu kai zaidu har zaka iya budan baki kay wani magana after all everything dat happened was ur fault, yes ..yaron nan a hannunka ya taso a lalace he is a liar and a manipulator bai ayyana komi ma rayuwarsa ba, kuma na jima da gane take takenka, kaine kake zugashi yana aikata min duk wani abunda yaga dama agidana toh wallah mama kigaya masa zan dauki mummunan mataki akansu dukansu.


kafin ya karasa rufe baki bappa zaidu yace ahhh ahh ahh mataki kam ai akan yarka zaka fara daukawa kafin kayi zciyat juyowa kan ɗan wani, kana magana ne kamar kai kaɗai abun ya shafa, snn Ka manta cewa muma muna da mutunci da xuciyar da kuma son yayan. Ba zaka zo ka yiwa kowa kallon me laifi ba saboda matsalarka da yarka daka kasa magance shi.



da bacin rai hajiya tace kaiii zaidu wallah banason shashanci wai meye haka kuke fada wa junanku kai da zayyanu???ashe bazaku tsaya ku fahimce junan a sulhunta maganan nan kamr na masu hankli ba



bappa yace In dai za a raba tsakanin tarbiya na gaskiya, to mu a nan muna da hujja, snn Kada kowa ya zo ya juyar da laifi ya ɗora shi kan bangare daya..


Da bacin rai prof yace mama ban yarda a yanke wa Zainab Arifah wani hukunci saboda kuskuren wani ba sabida ita akekan cutarwa, dagangan akayi ma yata haka dan anriga an tsaneni, kuma inda jiya ta mutu da kowa sai ya dandana kuɗansa agidan nan dan wallah bazan yafe muku ba


cikin jan tsaki bappa zaidu yace "inda ta mutu da babu abunda ka isa kayi saidai ace yarka ta kashe kanta abanza kuma kasan wuta zataje aiko..


da wani irin hargagi prof ya juyo zai amsa maganan


cikin katsesu uncle moh yace yaa zaidu, dan Allah kuyi hakuri wannan maganan fa mai sauki ce, wanda yay kuskurei a fito fili kawai abashi duka rashin gaskiyarsa, ita zainab macece mai rauni koda dan halacci ba ai akwai yan uwanta ka. we all know yaa zayyan dakyar ya samu haihuwar nan kuma yarsa kenan kwalli daya bazafa mu cigaba da rufa rufa muna kallo ana wasa da rayuwarta haba yaa zaidu ayi magana cikin adalci mana.


da zafin nama hajiya tace yawwa muhammadu gaya masa gaskiya dai yaji dan naga alama babu Allah acikin zuciyar zaidu, inba haka ba kiri kiri kana kallo zaa cuce rayuwar dan uwanka zayyanu wanda kuka zauna acikin tare amma ka rufe idonka kace sam ba haka ba


bappa zaidu yace hajiya inada tambaya, shin yaron nan menene yayi muku guda daya? inhar zaku iya gayamin laifinsa da kuskurensa direct wallh zan amsa 


kuka hajiya ta fashe dashi tace aww ynxu kai zaidu duk anan bakaga ga laifin rayyanun ba shifa ya jawo zainab ta tashi zata kashe kanta haba zaidu.


bappa zaidu ya kara hade rai yace "okay shi kenan yaje har gidansun yace mata ta kashe kanta ko?toh inba haka ba ya zaku taru kuna blaming dinsa shikadai akan abinda yarinya taga damar aikatawa kanta ai ita tafimu sanin ita daya ubanta ya haifa da batay la'akari da hakan ba duk bai muku ciwo ba???saishi ne da baida gata agidan nan ake so ace komi lefinsa ne bayan yariga ya gaya mata alaqa bazai yi tsakaninsu ba, mama shine me duka laifin da har za'a turo hukuma su kamashi a kulleshi??? nifa bawai inace miki ibaad baiya kuskure ba, ko ranar da abun ya faru ainay masa fada sosai sabida zainab ai ya mace ce tana da rauni, damuwata yadda kuke kkrin kuce lallai shine yasakata ta aikata wann abun wakanta gaskiya babu gaskiya ko adalci aciki, he is also a victim too, ai ɗa baifi ɗa ba..inkina jin zafi akan rayuwar zainab arifah shima ibaad din ai jikanki ne meyasa bazakiy la'akari da halin da hakan zai jefashi aciki ba wai shin ana soyayya dole ne..ynxu saiki gaya min menene wanda ya kamata yay mata tun dacan wanda baiyi b..soyayya ne yace bayayi

..kuma ya gaya mata toh menene..


da wani irin bacin rai prof ya miƙe har jikinsa na bari zai magana hajiya mairo ta daga musu hannu da muryan kuka da fushi tace "kai Ya isheku haka duk ku nitsu kafin naci muku mutunci karnasake jin bakin kowa anan dan naga alama maganan bazai kare ba, yanxu menene mafita guda daya? zayyanu kaji abunda xaidu ya fada kai meye ba'asinka...


komawa yay wajen zamansa ya zauna yana wani irin hura hanci da wani irin girman kai yafara gaya mata abunda likitansu ya fada akan lafyar kwalwlawar zainab wanda tun yana tsaka da bayanin hajiya ta rafka salati ta fashe da wani irin sabon kuka.


wayyoo Allah ni mairo, zainab yanxu haka rayuwarki ya dawo sai kace me taɓon hankli? innalillh wa inna ilaihi rajiun au dama abun har yakai haka ne zayyanu, Allah ya isa miki zainabu! toh wallah ko anaso ko ba aso dole ne mu dauki mataki, muhammadu kaine shaidata anan kace ma yayunka maza su sasanta kansu a tsaya a kan magana daya rayyanu ya sauke girman kai ayi auren nan kodan yarinyr nan ta samu lafiya bayan haka banason na karajin wani hayaniya..


bappa zaidu yay shiru ya zuba musu ido yana dai jiransu sugama


rimi rimi prof ya dinga kawo kananan magana yana hura hanci da izza yana cewa shima sharawar daya yanke da matarsa kenan duk dama yasan yafi karfin ya bada yarsa ahaka saidan samun lafyarta sabida yariga yasan cutarsa kawai xa'a yi, ana baqin ciki da daukakar da Allah ya masa anyi asiri an juya ma yarsa kwakwala da ciwon so dan kawai aga bayansa, kuma shi dukiyarsa ba'a isa aci abanza ba, inma ana tunanin anyi kulle kulle ne akan yarsa dan aga karshensa toh shiyasan yadda zaiy da mutum


yafi minti ashirin yana ma hajiya mairo magana da izza da zafin rai, yanamai dada gaya mata cewa akan dukiyar sa aka kulla komi, they cant stand the fact that shima Allah ya bashi yarinya me ilimi da tarbiya, hassada da kiyayyar da ake masa agidan ne yasaka ba acigaba, kuma wallah akan maganan zai saka ido, koda kuwa ya bada yarsa aure su sani ba a son ransa bane dan shi yasan cutarsa kawai za'ayi


maganganu dayawa dayake fadan sosai yah ma bappa zaidu zafi dan yaga alamar borin hauka kawai yakey, technically, shine yazo musu yana neman alfarman a aure yarsa amma sai yazo yana wani burga yana zage zage yana habaice habaice yana zargin kowa akan dukiya yana nuna musu kamar shine kawai zai rufa musu asiri yay musu alfarma...


hajiya mairo sai kuka take tana karkada kai batace komi ba gani take kamar eh dagaske ne anaso acuce zayyanu ne kawai akan yarsa zainab


ransa a bace ya cigaba da cewa "Dole ne asan yadda za'ayi hajiya, inaso yata ta dawo hayyacinta, snn duk wani maison ganin bayana shi zai fara faduwa ni xanyi ma yata duk wani gata har karshen rayuwarta dan haka aja kunnen yaro dan wallah next time wani abu makamancin haka ya sake faruwa hajiya kece kika haifi ni amma koke wallah baki isa ki hanani daukar tsatsaurar mataki akan yaron nan ba dan bazai kashe min yata a banza ba haukar banza haukar wofi.


cikin kukan tace kai zayyanu ya isheka haka, maganan nan ya kare, ni wallah ma tausayin yarinyar nakeji yanxu duk wata masifa da kukeji dashi ku aje kuhada kai kawai ayi auren nan, zaidu kaine uban yaro a hannunka yataso kuma yanxu kaine me wuƙa da nama ga zayyanu ya kawo batun yuyuwar auren zainab da rayyanu banji kace komi ba...dan Allah ayi ayi asaka musu rana dan yarinyar nan karta zauce ta haukace tafara shiga bololi tana tsince tsince


dago kai bappa zaidu yay cikin haɗiye bacin ran dake cinsa aransa yace "hajiya na gode da kika tabbatar ma kowa da hakan, haihuwar ibaad ne kawai banyi ba amma nina raineshi tun bai mallake hankalin kansa ba, tnk god da bakinki kince nine me wuƙa da nama..hajiya kiyi hakuri magana ta nasan bazai miki dadi ba amma hukuncin dana yanke shine ibaad bazai aure zainab arifah ba. tunda ubanta yace ita mai ilimi da tarbiyace suje ta sako ilimi da tarbiyan acikin rayuwata i assure u with time xata samu sauki, snn kuma shi uban nata dayake cewa shime dukiya ne kenan yana da halin da zai kai yarsa har bangon duniya dan ta samu lafiya kenan suna da wata hanyar mafita ba lallai sai an kulla aure ba..ni bana son auren da za'a dora ma yaro na dole akansa, snn azo ana zarginsa da kwadayin dukiyan wani ko azo ace hassada ne yasa muka badashi..to avoid all this gara ma kar afara..dama ynxu yagama cemiki baida niyyar hada jininsa damu toh banga amfanin basu auren ibaad ba tunda awajensa ibaad baida amfani, baida daraja, toh meye kuma na neman taimakon aure awajensa... ai a kyalesa kawai ya zauna da halinsa ita kuma zainab Allah ya bata lafiya tareda mijin aure nagari.


miƙewa tsaye hajiya tay in shock tace kan uban can zaidu wai abuge kake ne? waime kake cewa ne ana neman sulhu mai dorewa kai kana warwarewa ba duka rifin asirin mu bane in ayi auren nasu?


yana daga zaune yace aa hajy, wallah auren nan ba rufin asirin ibaad ne dan yafi karfin wani dan adam ya rufa masa asiri..danki ne dai yake ganin kamar zai rufa mana asiri zai mana alfarma hamshakiyar yarsa zata aure ibaad ta rufa masa asiri to wallah bazaiyu ba bama bukatar rufin asirinsu sukai kasuwa.


idonta arufe ta hargitso kansa zata shalla masa mari, uncle moh yau sauri ya riketa hajiya tafara ihu zaidu zaidu ka janye wannan maganan nan bana wasa dakai zaidu kay gaggawar janye maganan nan kafin inci maka mutunci


miƙewa tsaye bappa zaidu yay yana kallonta da taurin kai yace "Babu wanda ya isa yasaka ayi auren nan, inde wai zayyanu shine zai rufa ma ibaad asiri toh abari ibaad har ya mutu asirinsa bai rufu a duniya ba..what nonsense!!

yana gama fadin hakan yawuce ransa a bace yafita daga gidan.


gabaki daya gidan ya karade da ihunta "zaidu,..zaidu mani kake gaya ma wann magana kai zaidu ka dawo nan nace maka zaiduuuuu...


uncle moh na riirrike ta fashe da kukan mai tafe da bori prof daya sha mamakin maganan bappa zaidu ya mike da fushi muryansa harna rawa yace "hajiya ba kinga irin abunda nake gaya mikin ba..babban burin zaidu shine yaga na rasa ƴata, hassada da baqin ciki da kyashinsa yasa har ya mutu baxai taɓa zamowa kamr ni ba. kinga irin rainon da kika masa ko? dama baba saida ya fada baki iya raino ba, aida baba yana raye da ba'a isa amin wann abun ba dama kuma kece kike daure ma kowa gindi ni kin wareni sabida dama can kin tsaneni dan kawai na zabi in kare dukiyata daga wanda basa kaunata


tana kukan tace kar ka sake kagayamin bakar magana xayyanu, ubankan bashi ya lalata ka ba? kaima da kashi a tsuliyarka.. aure kuma dukanku baku isa ku hana yuwarsa ba innhar nace za'ayi ni na haifeku ba ku kuka haifeni ba.


zai magana da tsawa ta daka masa tace maza kasamu guri ka zauna ka gayamin me kake ciki shikuma zaidu zan gamu dashi bai isa ya raina ni haka ba wallah kryansa.


dakyar kura ya lafa ya zauna yana ciccin magani yafara gaya mata dokokinsa da zai shimfida, na farko ya jadadda mata cewa auren nan bada son ransa bane alfarma zaiyi, snn babu wani hidimar family da za'ayi, taron daurin aure kawai za'ayi snn zai gayyato manyan mutanen sa a bainar jama'a a masallaci, snn shi xai dauki nauyin komi har gidan da zasu zauna aciki sabida yarsa ta zama comfortable, zatayi aiki, xatay karatu snn zai hada su da likita da zain yawan zuwa duba lfyarta kwakwalta akai akai. snn duk wani kudin kashewa da sutura da komi shi zai nayi wa yarsa baya son komi awajensu face a tabbata yarsa ta kasance cikin koshin lafya kuma tana raye,..yace ma hajiya mairo ta dauke wann maganan a matsayin kwaji, inshi danta ne dagske zai gani dan ta hanyar wann auren ne kawai zai tabbatar da cewa ba son kashe masa yarsa sukeso suyi ba, snn hassada da tsana da bambamci ake nuna masa ba gaskiya bane.


duk taji abunda ya fadan amma bata yanke wani hukuci ba tace masa yaje zatay tunani daga ta gama kawai saka rana za'ayi ya gayyato mutanensa ranar daurin aure a daura.


su ukunsu suka dinƙe maganar kafin nan prof  ya fita ya dawo gida..


yanayin tashin hankali da rudanin ganin kalar zafin kai da zaidu ya nuna mata datake ciki yasaka uncle moh bai bijiro da nashi batun auren ba


can after like 2hrs bayan komi ya lafa ta kira ammi karama ta sakota agaba tace lallai lallai ta kira mata zaidu awaya yazo tana son magana dashi, tunda ita inta kirashi baya daukawa. duk sanda ammi ta kirashi zai dauka sai tagaya mai sakon yace toh zaixo amma haka suka sha jiransa baizo ba kuma still ya hana ibaad karasowa.


har saida akaci kusan kwana uku bappa zaidu yaki amsa wayar hjiya kuma yaqi yazo gidan gashi ya hana ibaad motsawa, ko maheer da yaxo shima bai barsa yaxo ba kwana biyu shikam ma yay ya koma. akwana na ukun ne abun ya isheta, tana tashuwa daga shago ta naɗe garinta da yamma taxo gidansa ko amsa gaisuwar ammi babba batay ba ta inada take shiga bata nan take fita ba harsaida bappa zaidu ya dawo daga aiki yazo ya sameta a falo


Duk masifar duniya ta masa baice mata uffan ba, dan koda yay kkrin nuna mata rainin wayon dayake cikin proposal din prof kai tsaye cemasa tay yanawa dan uwansa zayyanu mugunta da hassada. yana so ya jawo lamarin da zai saka zayyanu ya rasa haihuwa a duniya, she called him selfish nd heartless. ko ajikinsa bayan ishai ya saka aka kira masa ibaad ya shigo falon yaxo ya samesu suna xaune


fushi takey ko amsa gaisuwar ibaad din batayi ba shikuma dayafita danyen kai sai ya shareta bai kara ce mata uffan a falon ba


agabanta bappa zaidu ya maimaita duka ababen da prof yagaya nabatun cewa bada son ransa ma zai hada jini dasu ba, saidan sabida zargin zasu kashe masa yarsa ne akan dukiya, snn auren nan ma fa alfarma zai bayar dan yarsa ta samu lafiya amma badan yaso ba.


witout any bias ya tambaye ibaad ko ya amince da wannan batun aure snn yasani inhar ya amince shi bazai hanasa ba, dama shi auren dolene baya son yay masa.


tun kafin ibaad ya amsa tafara tsigeshi tana cewa bai isa yaki auren zainab ba tunda shi ya lalata mata rayuwa ya jawo mata ciwon hauka dolene ya aureta su rufawa juna asiri.


ibaad baiko kalleta ba yace ma bappa zaidu shi bai amince ba kawai Abata hakuri Allah ya bata miji nagari


bappa zaidu yace" hjy toh kinji da bakinki yace bazai aureta ba saiki isar musu ds sako.


hajya tay wani irin kukan kura zata cakumo ibaad din yay saurin miƙewa tsaye yanamai kare mata wani irin dakakken kallo wanda batasan sanda ta rusa ihu ba...ni kake min irin wann tsinannren kallon? au dukana zakayi?dukana zakayi rayyanu..tafara tutture shi, toh dakeni. nace ka dakeni..


..darajar bappa zaidu yasa ibaad yay shiru baice mata uffan ba ya tsaya yana kallonta tana hargagi.


she is doing all this to make them know she is very serious and hurt, musmm ma shi rayyanun dataga kmr bai dauki abun da muhimnci bama .


tashuwa bappa zaidun yay ya rikota tana masifa tana ihu tana cewa rayyanu wallah yadda ka lalata ma yarinyar nan rayuwarta ta haukace dolenka ne sai ka aureta

...inkun ga dama kaida zaidu kuyitayi amma maganan aure kam yana nan daram..


tanakaiwa nan ta bankade bappa zaidun ta fita agidan  tana matse ido da bakin hijabinta tana zage zage..


haka lamarin ya kasance kullum cikin tashin hankali, hajiya tana gida kullum tana bori tana rantsuwar sai anyi auren nan, amma bappa zaidu yayi burus yace ai tunda ibaad yace baiyaso baiga uban daya isa yasa a daura masa aure da zainab ba. 


week din su ayaana suka gama practicals na neco zasu fara wrting amma gaba daya hanklinta baya jikinta sabida inba a awaya ba bata samun jin muryan ibaad shima kuma ba kullum sabida bappa zaidu har wkend in ma ya datse yahana ibaad lekowa family house sabida baison suyi wani hayaniyar da zata yi amfani da ammi karama ta tursashi


duk wani hanyar wayon hajiya mairo akan auren bappa zaidu ya toshe wanda yasaka duk su uncle moh suka farajin mugun haushinsa, gashi anty safeera tana yawan fita kusan koyaushe taje gidan prof zata dawo musu da labari marar dadi game da jikin zainab arifah.


satin gabaki daya zainab ta lalace dake pretending take she had takes more hard drugs dan tay acting din da kyau wanda kwayar ya fara ramar da ita, sai taki cin abinci tayi ta amai tana birgima da fake ciwon kai da suman karya.


prof zayyanu yajira yaga kiran hajiya batun saka ranar aure amma sai shiru, gashi bai gaya ma zainab din yaje har yay maganan aurenta ba, so yake har sai abun ya kankama snn ya gaya mata dan itama yana da tsauraran dokokin dayake so yasaka mata wanda dolene ta bishi inhar auren ta zaba.


kwana sha biyu da faruwar komi lkcin su ayaana sunfara writing exams dinsu anata shirye shiryen final graduation duk hanklinta bai jikinta sosai ibaad kuma yana can yayi nisa a rubibin kammala nysc tareda tests da su exams dat will get him qualified for his intnl admission da zai yi major course dinsa a kasar waje.



kamar da wasa Hajiya mairo tay ta jiran tsammanin ko zaidu zai shiga hanklinsa ya sauko ya kyale ayi maganan auren nan amma sai shiru..


bata taɓa sanin cewa zaidu yana da wann kalar taurin kan ba ko kadan.


cikin kwanakin nan gabaki daya yabi ya sauya mata, ya canza daga mutum mai kawaici da tsananin biyayya agareta data san dashi ya dawo me taurin kai da kafiya, dan haryau tunda yay magana daya tak bai sauya ba, duk fitina duk bala'i duk tashin hankli datake tayarwa agidan kullum abanza yake karewa.. 


nd worst part ma da ibaad yay banza da abun dan ko lkcin amsa baqar magnrta bai fiye samu ba bare ma yazo har gidan.


kusan satikai biyu ana wann case din, wanda ya bala'in jawo jiji da kai da ikon da prof yake ji dashi yay sanyi, atunaninsa yana da wani izza da ikon da zai saka hajiya mairo kai tsaye ta amshi batunsa ya zama maganansa kawai akaji, ya dauka dayaje gidan aka zauna akayi magana duk zasu rusuna ne abishi asaka rana.


yana tsammanin cewa kowane acikinsu yakejin matsanncin shakkarsa, he expect them to be worshiping his words as per thr richest son of the entire family, tunda yasan iyayensa sai yasan iya abunda yaga dama yake zanta musu, a tunaninsa aiyafi sauran yan uwansa daraja ne kuma ya isa ne shiyasa tun dacan iyayensu suke yawan bin bayansa akowani case inya taso.


saidai ayan kwanakin nan sosai dan uwansa zaidu ya bashi mamaki, despite all the threats, nd tantrums na hajiya amma wai zaidu bai rusuna ya musu biyayya akan maganan ba..


hankalin prof ya tashi matuka, musmn daya ga kamar he wont be able to have full control of the marriage ayi komi cikin tafin hannunsa kmr yadda yay tsammani, dan yanaso ne ace kowa na karkashin ikonsa ne sai abunda ya gindiya musu gameda yarsa kawai zasuyi.



arana na sha hudu da faruwar Abun tunda anty safeera tazo gidan zainab arifah tay lumi tafara musu eaves droping har saida taji kishin kishin lkcin anty safeeran take kan gaya ma hajiya hamida cewa ga abubuwan dake faruwa acan agida bappa zaidu yace kaza kaza ibaad ma yace bazai aure zainab din ba haryau kuma babu wata cigaban magana akan haka. tunda zainab taji haka tsoron yuwar rugujewar shirin ta sai ya bala'in rufeta

tarasa meyake mata dadi, tay kukan, ta shiga tsananin mamakin jin wai harma kenan tay yunkurin kashe kanta amma ibaad baisauko ya rusuna ba, to kenan batasan kuma me zatay yanxu ba.


her eyes were shut nd soaked in tears cikin rasa nayi tafara jin gara kawai tabar duniyan indai zata rayuwa taga ibaad da wata macen da ba ita ba, gara ta bar duniyan kawai. it was very hard for her to decide to end her life for real tunani tay wanda yakaita har safiya, as early as 5 am ta jawo wani allura da drugs da ake ma sport horses, lkcin tasan an kusa zuwa a dubata dan 6am ake zuwa duba jikinta tana miƙewa zaune kuwa ta danna ruwan alluran a hannunta witout regret for 5 min tana zaune can kafin yafara reacting tafara birgima kasa kafin kace wani abu ta dauke gabaki daya jikinta ya dawo kamar kankara da alama her body is shutting down dakansa dan wann karon dagske takey ba wasa ba.


haka aka sake farkawa da wata sabuwar tashin hankali agidan da sassafen aka rushing inta I.C.U under strick medical attention aka fara kkrin dawowa da circulation inta da oxygen da allurai likito ci sunkai shida akanta


untill it begin to feel like she is really dying hajya hamida tana kuka daga kofa tana faduwa akasa ana riketa, ana fara saka ma zainab shock...jiri ya debi prof ya fito waje jikinsa na rawa idonsa cike da hawaye da kuma fushi


ya dauko wayarsa dacan bappa zaidu ya fara kira da niyyar zaici masa mutunci snn ya jadadda masa cewa inhar zainab ta mutu toh wallah sai ibaad ya mutu..


yakira kira for some reasons bappa zaidu yana ganin kiran amma ya share sai bai daga ba har ya gaji ya dena.


gashi dama baida layin hajiya mairo ma saida ya kira uncle moh kai tsaye, yace ya kawo mata wayar, a hujajn sassafe lokacin ta idar da sallah lenan sai gashi ya shigo..yace hajiya yaa zayyanu ne ke son yin magana dake.


tunda taji ance shi ne gabanta ya fadi da sauri kuma acikin fargaba ta amshi wayar tace zayyanu lafiya kuwa kira da sassafen nan?


tunda taji muryansa ya fashe ya zama abun tsoro yana rawa rawa tamike tsaye tana cewa meye haka zayyanu meye kar kace min zainab ta mutu? 


fadin hakan datay yasaka ya fara mata ihu yana gaya mata wasu irin tsauraran kalamai dat contains alot of threath na kisan kai kamar ba acikin hayyacinsa yake surutun ba.


suna gama wayar hajiya mairo ta yanke jiki ta fadi a sume jikinta na convulsing dakansa uncle moh yay maza maza ya daukota a hannu ahannu ya fito da ita awaje gidan ya kara rikicewa da hayya hayya ammi karama ta bishi ruwa ruwa aka kaita asibiti aka samu jinin ta ne yay mummunan hawa atake ashiga ciki da ita ana bata taimakon gaggawa


rudani yasaka kowa yay tsammanin ko mutuwa zainab din tayi, uncle moh yakira bappa zaidu da guntun rashin kunyarsa zai fara masa maganar banza kenan yaja tsaki baima tsaya jinsa ba ya katse wayar ya kira ammi karama 


lkcin tuni anty safeera ta wuce asibitin da zainab din take wanda da kyar da wahala da tashin hankli kafin ECG na zainab ya dawo 30% kuma har yanxu bata farfado ba. sai a sann su prof suka dawo cikin hanklinsu saidai sosai suka dau zafi yanxu...



kafin isowar su bappa zaidu asibitin da hajiy mairo take already anty safeera ta kirasu uncle moh da ammi karama ta sanar dasu cewa zainab tana raye but she is not out of danger yet, anadai kan monitoring dinta...


hanklinsu ya dan kwanta amma kowa cikinsu na mata addua isowar su bappa zaidu ke dawuya Ammi babba ta tada sabon gulma tanata tambyr uncle moh abubuwa wanda ko gaisawa da yayan nasa baiyi ba ya hau dokin xuciya wai shi a dole xaa kashe musu uwa


wasu maganan ma da gatse yake gaya ma ammi babba game da halinda zainab din take ciki.. bappa xaidu ko ajikinsa baice musu uhum ba, ko Allah ya sawwaka baice ba, iyaka fatima yay wa few questions game da jikin hajiya tace masa likita yace hawan jini ne.


sun zauna a waiting room for a while kafin nan akaxo akace musu hajya mairo ta farfado ta xama stable, kusan atare suka shiga suka sameta ta kifa kanta tana hawaye kowa ya mata sannu ta amsa bata amsa bappa zaidu ba. sai can da likitta yazo yay musu bayani yace kar asake barin jininta ya hau haka of not zata iya samun temporary paralysis ga jikin tsufa, ana gama bayani ta kalle bappa xaidu tareda nunasa da yatsa cikin tsananin fushi tana cewa zaidu sai ka zuba ruwa akasa ka sha tunda kay amanna saika hada kai da rayyanu kun kashe yar dan uwanka har lahira,..tace itama kawai ya kasheta yaga bayan ranta ta amince zata mutu ta bar masa duniyan ya jika ya sha shida rayyanu. 


shide baice komi ba tafara kuka duk su ammi karama suka  taru akanta suna bata hakuri kawai tafara bori tana cewa "zaidu inhar nina haifeka toh ka bari ayi auren nan kodan yarinyar nan ta samu lafya idan kuma kakiji wallah baxaka ki gani ba, kafin ka kasheni saina tsine maka albarka inde nono na kasha ka girma ba tsintar ka nay a bola ba tsinuwata wallahi saiya bika marar hankali kawai taɓabbe.


tana gama koke kokenta ya bata hakuri, shide baice eh ko aa ba. ya kama hanyarsa ya fita kowa nashan mamakin irin taurin kai da kafiyarsa. 


wajen aikinsa ya wuce direct ya shanshantr da maganan duk dama kalaman hajya ya balain sosa masa ransa sosai, sosai jikinsa yake bashi wann auren da sukeso su kullan kawai lalata rayuwar ibaad zasuyi dashi. he wil not have  freedom, or will in it, infact he wont have a say in it so suke su maidashi bawa ga rayuwar xainab arifah da mahaifinta sai abunda sukaga dama zasuyi da rayuwarsa ta nan gaba. he knws what he is doing sosai shiyasa yaki sam ya sauko dan inyayi sake tamkar yaci amanan maraicin ibaad ne dan yasan kasancewa surki awajen prof yana tafe ne da kalubale babba.


tunda yaxo office bai kara kula wani kira daga gida ba, har aka sallame hajiya mairo ammi karama ce take wahala da ita kusan komi ita take mata  asashenta. banda raki da baqaqen maganganu babu abunda hajy take xubawa daga ta kwanta sai tafara kuka tana cewa wallah wallah akan wann magana dai ta tsine ma zaidu albarka zata daga masa nono wann furucin nata sosai ya dinga daga ma ammi karama hankli.


da yamma bayan komi ya lafa prof dagacan yayi xuciya already ya fara hada case zazzafa yana neman yay sueing din ibaad a kotu da case me karfi wanda xai gigita musu hankali, kmar kuwa ammi karama tay nazarin hakan babban kawar hajy mairo tana zuwa ammi ta samu sarari ta musu sallama ta koma sashenta ta shirya sharply ta saka doguwar jilbab dinta dark green colour dayay mata kyau sosai, babu dandanin kwalliya a fuskarta ta shafa turare ta sabi jakarta ta dau motarta cikim gaggawa ta nufi ofishin bappa zaidu da yamma


ana daf da zai tashi ta iso wanda tun a mota ta riga tay duk wani nazarin da zatay akan maganan nan ba, tasan in akaci gaba haka za'ay asarar xumunci da zaman lafya atsakanin su dayawa. aganinta tunda dokokin prof bai shafe kar ibaad ya kara aure anan gaba ba, ai zai iya auren xainab din kodan darajar kwacinyr hanklinsu duka inyaso daga baya ya auro duk wacce yakeso ya aura.


da wann tunanin aranta ta shigo ta samu bappa zaidu duk dama baisha mamakin ganinta ba amma dakyar ya nitsu ya kulata, dan kwata kwata baison ta saka baki acikin case din nan, yasha mamaki ma da hajiya bata umarce ta akan ta tursasashi ko ibaad su karbi auren nan ba. duk dama yana mutuwar sonta amma it was hard for her to convince him cewa a radin kanta tazo ba hajiya bane ta aikota ta lallabeshi..she try to convinced him to her best of ability amma inaa, bai sauko ba saida yaga ta xuba masa gwiwa akasa tana hawaye tana kuma jaddada masa cewa ita kadai baxata iya langwasa ibaad ba shine kawai zai iya gayama ibaad abu snn ya amince masa kai tsaye, idan shi bai sauko sun gyara abun acikin nitsuwa da hankali ba mutunci zai zuba, kima da darajar gidansu kwanan nan zai xube a gaban kotu, snn shikansa bazaiso yay rayuwa da tsinuwa da bacin ran mahaifyarsa akansa ba


da kyar da lallami da karya masa murya ta rarrashe shi, tace zata rakasa yanxu suje gida kawai ya bawa hajiya hakuri inyaso ayi magana ta kare daga yau...


har cikin ransa baiso haka ba, amma duba da manya manyan hikima dake cikkn zantukan fatima da inda ta durkusa agabansa tana masa kuka yasa kawai ya hakura yabita sukaxo gidan atare.


wanda tun a mota yake ta fayyace mata illar da wannan auren zaiyi arayuwar ibaad, da yadda baiya kaunar ace shida hannunsa ya jefa ibaad acikin wani yanayn rayuwa dazai cutar dashi...


yana maganan muryansa harna rawa cos at some point zaka rantse shiya haife ibaad 

bcos the way he loved him nd cared for him ko mahaifinsa na asali baimasa son dayake nuna masa ba, inda kuwa an barsa da bazai taɓa saukowa ba saidai ayi duk abunda za'ayi bai damu ba dan inda gidansu ne ansha nuna irin wann son zuciyar bayau aka fara ba...


ubansu al-mansur ma halinsa kenan yafi hajya mairo son kai da nuna bangarenci da nuna bambamci, saidai baiyo tsammanin hajiy mairo son ƴayanta zai rufe mata ido harda zata zaɓi ta cutar da maraya kamr ibaad ba. wani bin sai yaga kmr ana wasu abubuwan ne dan anga asalin uban ibaad din baya raye, ammi karama kuma karamar mace ce har yanxu duk sun girmeta nesa ba kusa kai ko muhammadu ya girmeta ko tacema zata karba ma danta yanci bazasu taɓa saurararta ba dukan kawunanta na can maiduguri duk suna bin bayan hajiya ne, saidai ma agaya mata maganan da xaizo ya dameta a zuciyarta.


dada fahimtar irin son dayake ma ibaad din yasa ammi taji sanyi aranta hawayenta na sauka tanajin tausayin shi tare da kaunarsa aranta har suka iso cikin gida


idanunta sosai yay jaa, kafin su sauko sai ta dau lokaci acikin mota tana bashi hakuri da tattausar lafazi ta dinga lallabashi har suka karaso cikin gida...


yamma ne lisss ammi babba tana sama sashen anty safeerah taje jin gulma game da jikin zainab,wani dan uban dadi taji dataji cewa prof ya harxuka ya fara kiran lawyers zasu kafa babban case akan ibaad dan axo a kulleshi a walakanta sa.


lkcin gidan yay shiru ammi karama suka karaso inda tun akofar ashen hajia sukejiyo muryanta tana kan koke koke ma kawarta hajya hajara akan abunda ke faruwa da ita duk ta rasa yadda zatayi da ranta dan bata taɓa sanin zaidu yana da wann taurin kai da kafiyar kafurcin ba


ita babban damuwarta shine kawai a amshi auren kodan kar araba danta xayyanu da yarsa a duniyan nan, cewarta mutuwar matashi ya fi girgiza iyaye gashi itace musu kwalli daya inta mutu bazasu sake samun haihuwa ba har abada.


ammi karama tana gaba bappa zaidu yana biye da ita abaya anitse sunayin sallama a falon hajiya mairo ta kara hade rai tana kan jan majina jin muryan xaidu yasa bata amsa ba ta kauda kanta gefe cikin tsananin fushi..


da sanyin jiki ammi karama ta masa jagora bata barsa ya zauna akan kujera ba suka zauna akasa atare...


tun basu furta komi ba hajy hajara ta kallesa da muryan kuka itama tafara cewa zaidu wallh kabani kunya ko kadan banyi tsammanin zaka mana haka ba. kai da nace kaine zakka shine zaka watsa min kasa a ido, ace kaine dakanka ka rufe idonka akan maganar da bai taka kara ya karya ba?? kana cutar da rayuwar dan uwanka da kuka zauna aciki daya kuka fito atare, haba zaidu haba zaidu habaaa

...yanxu kaji dadi kenan da kasa hawan jinin mahaifiyarka ya tashi?? gaskiya bansan ka da wann mugun halin ba..


cikin katseta da sasanyar muryarsa me cike da dattako yace Hajiya mama hajara ayi min afuwa. daga sai bai kara cewa komi ba, har saida ammi karama ta kalleshi da fuskar magiya snn ya mike ya karaso kusa da hajiya mairon yace "Hajiya kiyi hakuri da dukkan abubuwan dake faruwa, ina sane da cewa ke mahaifyata ce wanda darajarki bai taba gushewa araina ba duk wani hukuncin da kikaga na yanke akan ibaad bawai nayi bane dan na kuntata muku saidan na kare amana da martaban maraya da yaa mustafa ya tafi ya barmana, gadai fatima tana kallo kuma tana zaune akusa dake kusan kowani lokaci tana kulawa dake but at same time kina zagin dan cikinta, kina ambatarsa da mugayen halaya duk da kinsan ba gaskiya bane, kin bijiro masa da auren dole me cike da tsauraran dokoki bakiyi la'akari da yadda abun zai gurbata rayuwarsa ba, shin kin nuna masa kenan farincikin wasu acikin yayanki yafi na wasu?inda yaa mustafa yana raye shima xaiso ne ayi ma dan cikinsa irin wannan kaskantcen auren? agabanki zayyanu yace bayason ya hada jini da mu..kuma alfarma xai ma yaron nan, snn ga zargi, ibaad fa jikanki ne hajiya, kenan farin ciki da rayuwar jikokin ki masu abun duniya da dukiya sunfi miki na shi dayake maraya ko? ke baki tunanin duk wnn abun da kikeyin zai dame zucyar ibaad? kuma zai ce inama da ubana yana raye ya karba min yanci?...shin idan muka taru muka nuna masa shi marayane baida daraja a gidan nan waye ya kamata ya tsaya masa a duniya? ina zaije yaji sanyi, bayan ga fatima anan tare dake bata taɓa saba miki ba...duk da zagin dakike ma danta koyaushe, shin hakan yana mata dadi ne? ke uwace fa hajya bazaiyu kice komi laifi bane, musmn inde har bai sauka an favorites dinki ba.


yana maganan wani irin shiru falon ya dauka cikin sauke ajiyan zuciya hajy hajara tace

hakane zaidu kay magana ta hankali amma kuduba Allah aceto rayuwar yarinyr nan, duk wani uzuri da zaka bayar baikai nauyin rai ba, duk wani qaddarar da ibaad zai dauka bazai kai wanda zayyanu zai ji aransa indan ya rasa yarsa kwalli daya daya haifa a duniya ba..memakon kuyita hayaniya maslaha zaku samo acikin wann matsalar dolene fa sai wani ya dauki mummunn qaddara acikinsu tunda shi soyayya Allah ne ya dora mata bayin kanta bane...yarinya kyakwya haka data taso acikin dukiya da gata wallah bazata so ta kashe kanta ba inba akan abunda yafi karfin tunaninta ba, zaidu ka duba Allah arufe maganar nan


yace "bakomi hajiya ni dama fatima ce ta dauko ni akan inzo abama hajy hakuri kuma in sha Allah zan tuntube shi ibaad din da maganan..saidai muy addua Allah ya bashi ikon cin wann jarabawar..


yana rufe bakinsa hajiya mairo ta fashe da kuka harda shsheka taki tace komi dan bakaramin taɓa mata zuciya kalamansa yay ba, musmn na maraici da kuma yanda yajawo hanklinta akan abunda take yawan furtawa agaban fatima.


tashi yay ya koma wajen da ammi karamar take zauna sukay magana kasa kasa 


hajy hajara kuma tana famar lallashin hajy mairo tana bata baki kasa kasa cikin kuka take cewa 'hajara kicewa fatima ta yafeni, wallah na rude ne

haka kawai bazan kuntata mata ba..sosai hjy hajaran ta tausaya mata


sai can ta dago ta kallesu tace toh zaidu yanxu sai munji kenan daga gareka...


a nitse yace in sha Allah..zuwa gobe!..yana gama furta hakan ya miƙe batare da ya kalle hjiya mairon ba da sanyin murya yace fatima muje ko?


mikewa tay da sanyin jiki tay gaba yana biyi da ita abaya har suka fice a asashen gabaki daya tarakasa har jikin motarsa suka cigaba da maganan awajen har ixuwa sallan magrib snn suka rabu ta dawo cikin gida.


kitchen ta shiga dan ta dora masu hajiya wani snacks da shayin da zasu kwana dashi ita da hajya hajara.


dagata bangaren su kuwa ficewarsu bada wuya ba kunya yabi ya lullube hajya mairo tana kuka tana fadin halacci, kawaici da alherin da fatima take mata..


hajiya hajya kuwa batay kasa agiwa ba,sosai ta cire son zuciya tay mata nasiha akan abubuwan datakeyi ta bala'in nutsar da ita musmn akan batun bambamce bambmce datake nunawa.


sunjima suna magana kafin nan ta shigo mata da maganan zaidu da fatima

..tace bata gane me ake jira dasu har yanxu ba?  da sanyin murya hajiya mairo tace "toh Allah ne dai baiyi lokci ba naje wajen malamai sunfi dubu a tudu amma duk ana cewa sihiri akay aka hanasu aure

..kullum sai ace muje mu cigaba da addua gashi lokci yana ta ja sunata tsufa...ai da tuni yanzu ta haifa masa yaya sunkai hudu ko biyar.


hajya hajara ta saki baki tace wann ma maganan banza ce, ke kuwa mai tuwo yarinyar nan fatima har nawa take? inbanda ma karya da kika dinga shera ma mutane fatima fa a yar shekara 16 tazo cikin gidan nan ko kin manta ne? har yanzu fa yarinya ce atata ace anbata shekaru arbain da hudu zuwa da biyar ba toh wallah in zaki mike tsaye ki mike bawai kawai anzauna ana ta cutar yarinya ba duk anbarta da juyi a gado me sanyi kullum ruwan  sha'awa na taruwa mata amara, tunda dai addua bai yi ba ai munjira, ynxu kawai mu hada kai munemar masu mafita.. yau kiga dai inda taje ta lallabo miki shi yaxo har gabanki ya durkusa ya baki hakuri, shin ita wancan balamar matar tasa tay miki hakan ne?shegiya mummuna banda gulma bata iya komi ba tunda nazo gidan nan ko ruwa banga tazo ta aje agabanki ba taje can tana yawo da sakakken duwaiwaka tana jin gulma awajen safeera toh wallah baxaiyu ba, inke yar kungiyar izala ce ni nariga na wuce nan sabida haka xanje 

duk inda xanje wallah sai an cire yarinyar nan a azaba an aura mata mijinta ke kuwa maituwo wann uban mugunta har inaaaa kema fa da lefinki akanbyaran nan dan fatima ba yar cikinki bace shiyasa baki damu da halin da zatana shiga ciki ba shekararta nawa babu namiji aikekuwa kya tausayawa rayuwarta


jan ajiyan zuciya mai nauyi hajiya mairo tay tace "kune fa kawai kuke ganin kamar bana tausayawa fatima amma har raina bana tsammanin inada wata a duniyar nan danake jinta kamar yar cikina kamar ita, fatima fa tasha wahala dani. kedai tunda kince zakiyi wani abu akai toh ki gwada mugani nide inhar sihirin nan ya kunce ko yau yaune zan iya sawa a daura musu aure kowa ma ya huta..malamin nan cewa yay fatima zata mutu in akay auren ba a karya asirin nan ba, yanxu so kuke na mata auren da zai kasheta inta mutu ai ni aka cuta


hajy hajara tace yanxu naji magana toh yanxu dai kibani nan da wani lokaci in sha Allah wann aure sai anyishi nan bada jimawa ba, koma waye tay asirin zanje can kauyen mijina na, kinsansu ai kabilar jukunawa ne, dole ne muma mu tashi tsaye mu gwada musu muna da yadda zamuyi haba cutarwan yayi yawa....



#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[13/12, 19:36] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️4️⃣6️⃣

tunda hajiya hajara ta gama tsige aminiyarta hajiya mairo akan batun maganan auren zaidu da fatima sai bata sake cewa komi ba, suna zaune anan suna yan hira har ammi karama ta kawo musu abin taɓawa albarka suka saka mata da har zata wuce dakinta taje tay wanka hajya hajara ta zaunar da ita ta dinga mata nasihohi masu ratsa zuciya da shiga jiki, nauyi da kunya duk yabi ya hana hajy mairo cewa kowa ba har hajiya hajara ta sallameta ta fita.


ata fannin bappa zaidu kuwa gabaki daya daren ranar juyi yakeyi akan fankacecen gadonsa da tunanin yadda zai iya bullowa al'amarin aransa saida yasamu cikakken nitsuwa yay tunani me zurfi snn ya iya sake ransa yayi hakuri.



washe gari da safe as usual suka fita sallahn fajr ibaad ya jasu bayan an idar suna shigowa cikin gidan ya kirawo shi sukaje private palonsa acikin sashen sa. ibaad yana daga kasa shi yana sama.


kai tsaye yafara sanar dashi abubuwan da ya farun jiya, dan yasan da wuya ne inyana da masaniya dake tun asubah jiyan ya fita kuma bai dawo ba saida yamma lisss.


har saida ya gama fayyace masa halin da ake ciki snn yay masa nasiha, ya kuma sanar dashi bada son ransa bane daya zo yana dawo masa da wnn maganan. su dauka kawai duk wannn abun qaddara ce dan haka umarni yake bashi da yay hakuri ya amince ayi auren, inyaso daga baya in komi ya lafa sai ya aure duk wacce yakeso ya hadasu su biyu.


tunda bappa zaidu ya furta masa wnn maganan saiyaji kamar iska ya dauke masa baya shaqar numfashi ganin yakasa amsawa yasa bappa zaidun yace masa yaje yay tunani zuwa yamma ya bashi amsa yay masa nasiha ya kuma bashi hakuri sosai..


jikin ibaad a sanyaye ya tashi ya bar wajen bai masan sanda yakai kansa dakinsa ba he laid on his bed for a while yanajin kamar baya duniyar ne gabaki daya, sai can ya jawo wayarsa yafara kkrin danna lambar mum dinsa ganin bata dauka ba kawai ya miƙe ya shirya kansa duk sonsa da tsafta yau ko kula wanka baiyi ba, karfe 7 dede saigashi ya shigo cikin gidan idonsa a rufe kai tsaye dakin amminshi ya nufa hanklinsa a tashe sosai...


tana gama gyara koina kenan zata fito ta shiga kitchen yay sallama ta amsa masa yashigo gani tay kawai ya zauna kasa jikinshi a mugun sanyaye yayi shiru baice komi


throw pillown dake hannunta ta aje ta karaso wajensa tace "rayyan ya naganka da sassafe haka lafiya kuwa? ko bakajin dadin jikinka ne...


jin kamar idan ya budi bakinsa zaiy kuka yasa ya sunkuyar dakansa can kasa gwanin ban tausayi baice komi ba saida yadan samu nitsuwa taciki.  shirun dayay yasa atake jikinta ya bata, waje ta nema ta zauna kusa dashi akasan da sanyin murya tace rayyan pls talk to mummy, kunyi magana da bappanka ne ko?


yana dago kansa taga idanunsa yay jaaa zai magana cikin katsesa tace "honey, Its for the best" Dan Allah kayi haquri none of us wanted this for u. musmn ma kawunka wallh jiya ya bani tausayi dan inda anbita nashi da ya gwammaci hajiya mairo ta tsine masa akan daya maka wann auren..pls look at it as ur destiny...kay hakuri...


cikin girgixa kai hawayensa tsilli daya ya sauko murynsa na rawa yace "Ammi wallah bana kaunarta, kuma bappa bai taɓa bani umarni akan wani abunda banaso ba sai wann karon, iyakan zamana da shi a gidansa he always defended me har sama da farin cikin matarsa, ni ynxu bansan me zance masa dan banason saɓawa umarninsa kuma harga Allah banason na aure zainab sabida bana kaunarta kwata kwata banajin zan iya kallonta a amatsyin matata..


da tausayinsa a idonta tace "nasani..dama kuma ba auren soyayya muke nema agareka ba rayyan...inada yaqinin cewa zainab wata bangare na jarabawa da kuma qaddarar kace, hala wani gwaji ne da Allah ya aiko maka dan ya jarabce rayuwarka snn karkamanta tun tana karama sosai ta fara wann abun. gashi har  yanxu ta girma dashi yaxo yanaso yay sanadiyar rayuwarta, toh da ace ka bijire ka wargaza zumunci akan rashin haquri kuma zaonab tazo ta rasa ranta sanadiyarka gara ace kay musu biyayya kay hakuri ya zamo kaine aka zalunta bakaine ka zalunce kowa ba..if ure patient Nothing evil will ever happen to u addua ta kullum yana tare da kai, nide hakuri nake dada baka dan Allah ka rufa mana asiri yazamo nan gaba baza'a a kalleka ace kaine kayi sanadiyar tarwatswer zumunci da kimar gidan al-mansur gabaki daya ba. pls dont think as her a matsayin zainab da baka kauna, just look at her as a fragile life dat needs ur company to be able to dream nd breath again, nd i know my son wudnt be the reason for sumones grieve, or life lost..u wont be the reason to tear this family apart, kaduba girman abunda zakayi a idon Allah, this is a huge secrifice for the entire family nasan mahaifinka zai yi alfahari dakai..pls keep ur desires aside rayyan, nd do this for sake of Allah... besides babu wanda zai hanaka auren wacce kakeso anan gaba

...kawai kay hkuri ka ansa wa kawunka, shima ya samu nitsuwa kaima ka samu nitsuwa gidan nan duka a samu kwanciyar hankali...inda mahaifinka na raye you know he will prefer to keep the peace too, kuma shima da abun da zai roka awajenka kenan.. duk wani walwala da farinciki da zumuncin gidan nan yanxu haka yana wuyanka ne, be the bigger person pls nd think abt it..amma koma miyene nidai dan Allah karkace ma kawunka a'a zaka kunyatar dashi, just let it go..nd let god see u throu. inma taruwa akayi agidan nan duka aka cutar da kai kabari kawai Allah zai saka maka. kuma in sha Allah zaka cinye wann jarabawar 


hawayen dayake zuba a idonsa yasaka hannunsa yashare ahnkli muryansa a sanyaye yace toh shikenan ammi tunda kema hakan kike gani bakomi zanje na sameshi in sanar dashi na amince zan aure zainab din..


kusan dede nan kalmomin nasa suka dira acikin kunnen ayaanah datazo kofar dakin da sauri da niyyar zata gaisher da ammi dan yau exams na IRS zasuyi karfe 9am dai dai tanaso ne taje tafara shiri dan tuni tagama duk wani bitan karatu da zatayi.


tana dada jin muryansa aciki ta tsaya cakkkk dan har wani yaam yaam taji kunnuwanta na neman toshewa tafara jin jiri jiri ne ko faduwar gaba ne duk ta rasa me takeji, she instantly frozed har ta gama jin conversation dinsun na karshen yadda yake tabbatar ma mum dinsa zai hakura kawai ayi aure. ita iyaka nan kawai taji..yau yaa ibaad din nata ne dakansa yake cewa zai aure anty zainab arifah??


batasan how many minutes tay a daskare ba ita bata bude kofar ta shigo ba ita bata iya jan jikinta daga shock in datake ciki ta koma room inta ba, jim kadan sai taji inuwar mutum agabanta, 


kirjinta na bugawa da balain karfi ta daga idanunta sama taga shine har ya fito, suna hade ido dashi hawayen da batasan daga ina suka taho ba suka fara sauka a idon ta jikin ta na rawa rawa ta juya da uban gudu zata koma daki yay saurin biyota yana furta "ayaanah, ayaanah..

...amma inaa bata tsaya ba tana shigewa dakin idonta a rufe kamar mai aljanu tanufi bayan gidan tay sauri ta kulle kanta aciki tareda rusunawa akasa da wani irin mtsanancin kuka me daga hankali sosai, hanklinsa a mugun tashe ya shigo dakin yana kirar sunanta safiya tay marmaza ta sauka akan gado ta fice basu waje.


kirjinsa kamar zai amon wuta ya tarwatse ya tsaya daga bakin bayin yana jin sautin kukanta yana cewa "ayanaah pls come out..is not what u think..dan Allah ki fito..kinji?? kukan kawai takeyi jikinta na rawa rawa dan ita kanta bata sanma me takeji a dukkan ilahirin jikinta ba, ji take kamar she just cant take it..gashi Allah yadora mata wani irin matsanancin kishinsa musmn ma akan zainab arifahn...


rokon duniyan nan yay mata ta fito amma taki fitowa har kukan ya lafa, muryanta na fita ahankli cikin sheshhka tace masa kawai ya tafi ita bata so tay magana dashi ne yanxu sabida batajin dadi. tun 7.30am yana tsaye har saida 8am ya wuce ayaana bata fito ba, dakyar ya hakura ya fita agidan dan kawai ta samu ta fito ta shirya taje exams dinta.



fadin tashin hanklin daya shiga wann rana bazai kiyastu ba musm da yasan ayaanah taji komi daga bakinsa nd he knows bazai taba samun nitsuwa aransa ba kuma yanxu..


tsabar kansa ya dau zafi yana komawa gida saida ya fada wanka da ruwan sanyi mai sanyi sosai, haka ya bar ruwan showern ya zuba akansa sosai, so that his muscles will calm down and relax, wnn ne karo na farko da yarasa yadda zaiyi da rayuwarsa everthing bcome so intense musmn da yaga reaction din ayaanah dan yasan yarinya kuma zaisha wahala kafin ta fahimce shi.


cikin danne abun aransa ya shirya ya wuce harkokin gabansa he tot abt it all day, yana yi yana gwada lambar ayanah amma har yanxu ji yake akashe, da yamma liss daya dawo bayan sallahn isha'i nan ya gaya ma bappa zaidu cewa "ya amince zai masa biyayya kawai dan haka yabar masa komi ahannunsa...bappa zaidu was very proud of him daya cika dan halak ya masa wann halaccin, nd for the immense secrifice nd respect for the family, duk dama baiji wani dadi ba dan haka nasiha yakara masa, yace masa wann abun jarabawar rayuwarsa ce, Hala haka Allah ya qaddara zai hadashi da wani abunda baya kauna dan yaga iya level din imaninsa da hakurinsa da juriyarsa da kuma biyayynsa ga dokokin Allah,...yace masa bama su kawai yay biyayya ba ya dinga tuna Allahn daya jarabce shi shima zaiy alfahari dashi in yay hakuri, snn zai samu ladan hada kan ahalin sa, da ladan yin hakuri da wnn mummunan qaddara, snn kar dan baya son zainab aransa yay amfani da wnn daman ko ikonsa na mijinta ya cutar da ita, dan a sanadiyar haka sai Allah ya shigar da ita aljanna shikuma rashin hakuri da rashin sauke haqqin aure akanta sai ya kaisa wuta. haquri ya bashi sosai yace masa duk yadda ake ciki shizai kasance tare dashi bazai taɓa kyalewa a cutar dashi ba, snn kowa cece yazo yace yanaso nan gaba zasuy kkri su aura masa, dan haka yay hakuri karyace komi ynxu har sai anyi aurensan zainab ta samu lafiya zasu san yadda zasuyi.


godiya ibaad yay masa suka bar maganan anan, sai ya shiga motarsa adaren yazo gida..kai tsaye ya wuce sashen amminsa zuwa yay yasamu wai ayaana tana bacci, ammi tace masa ai yau batay ma exams dintan ba a hall din taje ta fadi ta suma aka dawo da ita da zazzafan zazzabi tasha maganin kenan tay bacci..


lahawla wala kuwwata ya rika nanatawa acikin zuciyarsa hanklinsa gabaki daya baya jikinsa he stayed beside her for a while ko zata farka suyi magana ya lallabeta amma bata tashi ba, har sai wajajen 11.30 na dare kafin nan ya hakura ya koma gida.


washe gari ma sassafe haka ya dawo gidan, still ayaanah ta kulle kanta a daki taki sam ta kulashi, she missed 2 of her exams ma wann kwanakin, both IRS nd geogrphy dan wani irin kishi mai balain rufe ido yahanata numfashi ta kasa jin sauki aranta kona minti daya, duk sukabi suka dagula ma ammi karama tunani har tasoma gane cewa dole ne kawai da akwai wani abu special atsakaninsu...


ita bata san cewa ayaana taji cewa zai aure zainab arifah ba, so she cant really conclude cewa rikicin kishi da soyayya ne, shikadai yasan da hakan, arana sai yazo gidan sau hudu sau biyar duba jikin ayaana saitaga ita kuma ayaanan batason tana kulashi, sam taki su kebe suyi magana, taki sam yazo kusa da ita.



wann yanayin suke ciki har na tsawon kwana biyu lamarin auren bai hanashi bacci kamar tsnanin fushin da ayaanah takeyi dashi ba.



daga dayan bangaren kuwa aranar da aka kan shirin sallame zainab arifah da safe around 8:30am bappa zaidu yasha manyan kaya yay kyau ya shigo asibitin kai tsaye dan dama shi bai taɓa zuwa ba. koda security suka ga spitting kamannin da sukey da prof da kuma irin kwarjininsa na babban mutum mai ji da naira wata mayyar sky blue shadda ya saka garensan nan taji aiki me aji, sai maza maza suka bashi hanya, infact har ciki securiry suka rakosa ana masa fadanci har private room din da ake monitoring zainab din aciki...


her life line has increase with 50% chance of recovery saidai haryau bata magana kullum idonta a lumshe da hawaye aciki, prof yadan fita yana waya da lawyer dinsa kenan hajy hamida taji sallama a kofa...


dake ma har muryansu yana dibi sai tay zaton mijinta ne da mamaki ta amsa dan tasan mijinta baya yin sallama in zai shigo waje...


wani irin sanyin qamshin

turare taji me tsada da kuma dadi dayasa ta juyo da sauri suna hade ido da bappa zaidun atake fuskarta ya wani sauya tamiƙe tsaye da raini tana yatsinawa...


muryanta kasa kasa tace 'ohh ashe kai ne..


sama da kasa ya kalleta a dakile bai tsaya sun gaisa ba yace hamida ya mai jiki??


kafin ta amsa taga ya dauke kai ya wuceta wani irin zafi taji akan kirjinta dan tarasa wani irin jiji dakai wann mutumin yake ji dashi mutum ne da bata isa ta zageshi ko ta rainashi ba sbd kwarjininsa kuma da alama taga kamar rashin mutuncinsa da walakncinsa yafi wanda ka kanta yawa.


kai tsaye ya karasa gadon da zainab take ya zuba mata idanunshi for a while kafin yace.."Doter Zainab arifah are u awake? ya jikin naki.


..jin ance doter zainab yasa tay firgit tabude ido da sauri hawayenta na zuba ahnkli tana ganinsa tace"uncle zaid?? 


dan karamin murmushi yay yace "how are u feeling? ya jikin naki..bata amsa shi ba ta langwane tareda fashe masa da kuka sosai ta motsa kadan ta matso jikinsa tarike masa hannu ta dora kanta akan hannun nasa tana kuka a agajiye...


da muryan kukan tace 'uncle zaid i am sorry dan Allah kar kace banyi hakuri ba...i jst cant take it anymore,.pls help me. amugun makirce take furta hakan da zimman takara cusa masa tausayi dan tasan shine bbn mtsalar yanxu dan taji sarai lkcin da akace shine yahana auren..


she was just crying nd begin him yayi shiru da tausayinta a idanunsa yana shafa mata kai yana sassaita ta


..aka bar hajy hamida tana kumbura fuska kamar zata tashi sama wato ma zainab tana da muryan yin magana shine su bata musu ba take ma wann mutumin


da tsananin bacin rai ta sabule ta fita a dakin ta samu prof a gefe yana waya tana isowa tana huci muryanta kamar zatayi kuka tace alhaj alhaji alhaji.. da sauri ya katse wayar yace "meyene? da bacin rai tace "wancan mugun dan uwankan ne yazo nd u cant believe it zainab is now talking to him...tsabar ta kufula hawayenta na zuba tace "for good 3 days muna nan muna wahala zainab bata mana magana ba sai shi? nikam wallah kazo karya kara juya ma yarinya kanta i am sure he is using magic nd charms on her..


tanakan maganan yaja tsaki da mamaki yace kina nufin zaidun ne yazo nan duba jikin zainab?? kafin ta amsa azafafe yafara kiran security babbansu na zuwa kawak ya daukes da mari yace how dare u let anyone come in here witou my permission? security ya fara bashi hakuri masifa ya ke ta inda yake shiga bata nan yake fita ba, dakyar hajiya hamida ta janye shi suka koma daki suka samu bappa zaidu har yadaga zainab daga kwance ta zauna ya saka mata pillow ta jingina bayanta dashi


bai mata wani dogon nasiha ba,sama sama kawai ya gaggaya mata makomarta inta koma wajen Allah a matsayin wacce ta kashe kanta snn ya bata hakuri yace mata sunyi magana da ibaad karta damu. intay masa alkwarin zata cire komi aranta ta warke toh shida kansa zai tabbata anyi auren su da ibaad batare da anja lokaci ba, amma sai ta masa alkawari bazata sake yunkurin kashe kanta ba no matter what. .


tunda aka fara case dinnan zainab arifah bataji wani sanyi aranta ba face yau. da sauri ta amince masa, tare da masa alkwari cewa bazata sake yin haka ba. 


yace mata shikenan shima zai cika mata alkwarinta zai ma babanta magana azo ayi maganan aure kawai


babu shiri yaji ta fado jikinsa ta rungumesa da karfi tana hawayen murna tace thank you sir thank u uncle zaid ure the best uncle in this world...


cikin haka sai ga su prof din sun bankado kofa sun shigo kamar wasu mayaka, he was dumpfounded dayazo yaga zainab ta rungume bappa zaidu tana kuka tana murna tana masa godiya


hajy hamida taji kamr zata fashe, fushi ya debe prof ya karaso tare da fincike yarsa 

ajikin bappa zaidun yana cewa "how dare u show ur face here zaidu?uhhh kazo harnan zaka karasa min ita ko?to wallh ka fita kafin na maka abunda har ka mutu bazaka manta dani ba


wani irin kallo bappa zaidu yamasa yace" kai wai yaushe zaka girma ne kabar wann shirmen...as u can see ur doter is fine nd happy only bcos i came. i am not the monster u think i am zayyanu, kaine dai da kajima kana kokrin raba kanka damu kaine kake da matsala da kowa, zainab is like my doter too, i care abt her happiness.. anyways na gama duba jikintan ni zan wuce sauran bayani zakaji a bakinta


ya kalle zainab yace" doter Allah ya baki lafiya..


da wani irin murmushin jim dadi tace "thank you so much uncle zaid i love u soo much uncle..


bappa zaidu yana fita bakinsu a sake suka juyo kanta ganin tsananin farin ciki dake shimfide akan fusrkta kafin ya budi baki tace"Daddy, he said yes"


in unison suna kallonta kusan adaskare sukace "whaaaaaat?


share hawayenta tay da sauri ta sauko kamr ba itace tay kwana uku bata ko motsi ba.


tana kallonsu duka tace 'uncle zaid yace inhar na masa alkwari bazan kara memeta haka ba zai min auren,..nd i told him i promised..nd he said he will get us married..yace min he has told ibaad alredy nd kaima zakuyi magana kuje ayi maganan ranar auren.


wani irin tsaki hajiya hamida tay a mugun kufule tace nd "is that why ure fucking happy u bloody ingrate???


a daskare prof yake kallon zainab da mamaki yadda yaga tamike zaune garau 


yace hamida is enuf karki sake mata tsawa, cant u see how this news has make her happy??yaushe rabonki da kikaga princess dina haka

...ohh my baby come here

..tana karasowa ya rungumeta yace i am so happy ure back okay? zo ko zauna ki gaya min duk abinda yace miki


tana murna tace thanks daddy..i know u love me nd i love u too...but, wil u go and meet him?


yay dariya yace 'sure princess, zanje mana. amma ai sai kin cika masa alkwarinsa

...since we have two more days in this hospital. prove it to me dat u want to get better. take all ur medications, deep sleep, don't cry..alwys talk to u daddy.


murmushi tay yana karasowa jikinta ta kara rungumesa tace 'i will do just that for u daddy.. da tsananin kaunarta aransa yay kissing inta slihgtly akan forehead inta yace dats my girl. snn ya jawota sula zauna tare akan gadon.


wani irin tsaki hajy hamida tajaaa tana masa kallon mahaukaci da sauri ta fita waje tana huci me zafi..


sam sam ranta baiyi dadi da aka gama case din nan da wuri har haka ba, dan koba komi taso ace an hada case dinnan yay zafi, dan prof yayi amfani da powernsa yaci mutuncin familynsa ya tagayyara zaidu da hajiya mairo ita babban burinta kenan taga yaci mutuncin ahalinsa musmn ma uwarsa snn yahada harda tsinannen yaron nan ibaad ya karar masa da rayuwarsa a lkci guda.


she stayed outside for a while, har saida abun ya wuce mata kafin tazo ta samu zainab arifah da babanta, this rush of emotions yasaka har line inta yatashi daga 50- yakai 68% kamar ba ita take kan langwabewa ba, tana ta hira da babanta, ya aji komi aransa yanakan lallabarta dan ta warke sosai..



fannin ayaana kuwa kwana biyun nan gabaki daya takita kula ibaad dan koyazo gidan bata sakewa ta fito inya kira kuma wayarta yawanci zaiji a kashe text message dinsa gabaki daya bata amsa ko guda daya ba. he explained most of the situation to her tru text amma haryau baiga ta sauko ta amsa shi ba, sai dai ta karanta tay ta kuka danji take kamar itama mutuwan kawai zatay in ya aure zainab arifah ba ita ba. 


haka rayuwa ya kasance, 4 days later zainab arifah ta dawo cikin hayyacinta prof yana tsare da ita kome tace masa tanaso sai kaga ya mata, baiyi fushi ko ya mata fada ko sau daya ba, instead wani irin sakalta ya cigaba dayayi har likitotin abun yana damunsu aransu


everything she says shi ake ji, and everything she want komeyene shi kawai yake mata. akwana na hudun dayaga tana bada hadin kai sosai anaata jinya her ECG has reached 98% yanxu kuma tana cin abinci sai kawai aka sallamesu da dare suka dawo gida


ranar gabaki daya he was with her a room inta yana gaya mata kalamai masu tsananin dadi har tay bacci tana murmushi tareda jin matsanancin son babanta aranta sosai


the moment ya koma room dinsa kuma ya sauya fuska suka zauna sukayi magana da matarsa hajya hamida dan yasan yanxu babu yadda ya iya dolene kawai yaje family house again ayi magana asaka ranar daurin auren nan, all this while bai taba fitowa fili yagaya ma matarsa hajiya hamida boyayyen qudurinsa akan zainab ba sai yanxu.


wanda tunda ya fara fayyace mata yadda ya tsara rayuwar zainab din itama saida taji tsoro ta hau sara mashi.


cikin dare ya gaya mata dokokin da zai saka ma zainab, na farko kuma mafi muhimmanci shine babu wani hidimar biki na yar gata da zasuyi dan ko sisin su bazasu sake su kashe a auren nan ba, everything will be within the family, shine kawai zai gayyato manyan bakinsa maza aje daurin aure dan a shaida ya aurar da yarsa shikenan.


na biu kuma ya riga yagama shirinsa da likita, yace mata daga gobe, zai bata wani magani da zata rika zuwa ita dakanta tana bawa zainab arifah tana sha agabnta dan maganin hana haihuwa ne, snn zaa mata small surgery a mahaifa zaa toshe hanyar da sperm zaibi yana shiga, wata nurse zataso har na tsawom wata guda tana kulawa da ita in ayi surgeryn dan baiyasone  kwata kwata zainab ta haihu a gidan ibaad, cos he still suspect that in ya hada jini da su zasu kashe masa yarsa snn suyi amfani da abunda zata haifa a kwashe mata dukiya...


doka na uku shine zasu cigaba da yin duk yadda zasuyi suga auren zainab din baiyi lasting har abada ba ta hanyar sponsoring da providing rayuwar ibaad da komi daya shafi financial freedom, yace mata zai bawa ibaad kujeran MD a kamfanin da zainab din take jagoranta, sabida su san samunshi da rashinsa, da komi dayake ciki finances dinsa ya zama a tafin hannunsu yake.


nd he believe zainab will come back to her sense one day, cos no woman want a weak man, intaga ibaad yana karkashinta ne baida arxikin kansa sai nata zata rainashi, on the long run zasu cusa mata ra'ayin da zata ji bai dace da ita ba idan kuma aka kai matsayin da auren zai tarwatse then they will snatched their wealth frm him, disgrace him, locked him up and make him miserable nd poor forever. yarsu kuma sai ta aure wanda ya dace da ita ta haifa masa jikoki da miji within her class cikin salon alon, wai ahakan kuma gani suke sunyi maganin yan hassada da yan son amfani dayarsu dan su gaje arzikin yarsu anan gaba



hajiya hamida kamar zata zuba ruwa akasa tasha tsabar farincikin dirar plans din nan, 100% ta goya ma mijinta baya. tace masa yabar mata part din cusa ma zainab ra'ayin tsana da raina miji..cos she knw extly when to begin tace masa lokcin obsessive soyayyar ya fara gushewa dats when she will start her own.


perfectly suka hada plan dinsu, washe gari akwana na biyar they behave normal agaban zainab basu ce mata komi ba. har saida akaci one full week snn sukazo room dinta da dare zasu mata goodnite.


anan ne prof ya sanar da ita cewa gobe ne zaije suyi magana a saka ranar auren nata, but...he has his writen rules on paper like a contrct, inhar ta amince ta tasaka hannu akai toh maganan aure angama dashi.


tsabar zumudi tace masa ai koma miye dokar zata bi inde she wll get to answer mrs ibaad a rayuwarta,duk dama arazane take da reaction din nala, ta lura kamar nala is scared da maganan matarcan boka datace aurensu bazaiyi ba,but she is still counting on the fact that rukky tace mata "ko da yayu it will be her karma" meaning zai iyu faruwar kenan,. oh well then, fuck the karma, ta riga ta sa aranta tunda har akwai tiny chance na yuwar auren duk wani mummnan qaddara da zai biyo baya zata iya dashi

infact she will create her own destiny ai anty saferea ta taba cemata bokayen nan mugayen makaryata ne


tay tunanin duk dokokin babanta bazai wuce akan kudi ba, well, daya bata papern taga abubuwan daya shafi kudin, da yadda zai dauki nauyin rayuwrta dana mijinta an all that, batun rashin haihuwar ne ya mata bambarakwai kuma ya mugun daga mata hanklinta sosai..but she quickly discard it, cos is better to lose a child than the father.


ranta baiso har can can ba tay ma babanta biyayya tayi signing komi snn tace masa bazata taɓa karya dokokin sa tamasa alkwari.


tunda suka gama da wann fannin shi ya fita yaje family house, hajy hamida kuma daga safiyar ranan ta fara dura ma zainab arifah kwayoyin hana haihuwa



dagata dayan bangaren kuwa tunda aka fara maganan Auren ibaad komi ya lafa gidan sai kananan gulma dake tashi here and der msammn daga wajensu ammi babba da su anty safeera, ga hjy mairo ma inzaty magana babu sirrii sam sai kowa yaji, wanda duk dama ayaanah tana fushi da komi acikin satin nan gabaki daya saida behaviours din mutanen gidan yasaka ta gane cewa komi na dole akayi ma ibaad snn yana cikin wani hali gashi wainashi data dingay yasa yadan kyaleta dan shima yaji dakansa cos he is hurting soo much msmn dayaga ayaanah taki ta fahimceshi.


zaizo gidan baifi sau biyu ba, dayaga har yau batako lekowa bata amsa sakonsa bare kira ranar kawai sai yahakura ya dauke kafarsa yau kusan kwana biyu kenan baizo dubata ba, kuma bai kira ko ya tura mata text din lallashi daya saba kowani rana ba..


duk sai taji kuma ta damu, barinma ranar da sukayi waya da sultana sukayi dogon hira duk ta kwashe labarin wasu abubuwan da ake ma ibaad din,da wanda yake ciki duk ta fayyace mata tace mata auren nan fa bappa zaidu ne suka bashi umarni kuma dama kowa yasan hjy tace zata tsine masa, tace ai yanxu ma bata fiye ganinsa yana cin abinci agidan ba nd he look pale nd sick yanata shiri ma zaiyi tafiya kasar waje next week.


duk sai kuma ta rasa meke mata dadi, yau da safe tay tunanin duniya na yadda zata kirashi ta bashi hakuri amma takasa tabuka komi musn inta tuna irin wahala da wainashi datay akwana biyun nan. dake weknd ne ranar ma basuda exams, takira ruthy ta tambayeta me zatasha jikinta yay zafi ruth tace mata ta gwada shan yellow flagyl wasu yana sa jikin su yay dumi.


bayan sunyi breakfast ta sace key tafita da motar ammi karama tajeta chemist nemo yellow flagyl. fitarta bada jimawa ba prof yazo aka kira bappa zaidu aka taru a falo


bai rusuna ba ya gama nanata dokokinsa haka ya kawo batun cewa ai tunda zaidu yaje asibiti ya lallaba zainab a tsayin kawunta shima kenan dan ya bawa ibaad matsayi da gidan zama yakuma dauke masa nauyin ciyar da mata balaifi bane tunda shima ai kawunsa ne so yana da cikakken dama yamasa wann gatar.


haka uncle moh ya goyi bayan prof 100% yadinga maganganu yana yabonsa snn suka saka hajya mairo dole dole ta amince da komi dayazo dede da ra'ayinsu, da sunan wai ana neman sulhu da hadin kan family snn kuma adalci ne akayiwa ibaad shima kar ace ba'a masa gata ba dan ubansa baya raye.


they manipulated his intention behind doing everything suka nuna ma hajiya cewa wai gata prof yake so yay ma ibaad amatsayin shi na maraya kuma kawunshi shiyasa zai dauko nauyin komi kuma zai bashi MD na kamfani.


bappa zaidu yanata kallonsu da mamakin munafurcinsu aransa tunda yaga hajiya ta hau kai hartana wani kuka tana ma zayyanu godiya akan hallaci da gata dayama ibaad


bappa zaidu baice komi  akan batun saka ranar  ba, dan nan ma prof ne yay babakere akai yace ma hajiya sai nan da wata daya yakeso ayi auren sabida yana so a zainab arifah ta samu kwarin jiki kar akaita gidan miji da rauni bata gama warwarewa ba.


saida suka gama tass snn ta tambaye bappa zaidu ko duk hakan ya masa, ya kyabe baki yace ai dama sune da biki shidai rule dinsa dayane muddin wann ya aure bazai hana ibaad kara aure agaba ba shikenan, tunda wann na dole ne, toh ya zama dole kuwa abashi dama nan gaba yakara aure da wacce yake so. da mamakinsu prof yace shi wann bai damesa ba shidai kawai kar ynxun ayi abunda zai tabbatar masa da cewa ran yarsa ake nema ba auren kare rayuwarta kona zumuncinsu ba.


sosai ya rika jadadda musu muddin ibaad yay wani abunda zainab ta dau ranta wallah za'a fuskance walaknci da tozarci daga wajensa dan bazai taba yafewa ba kai daga ranar ma kawai gara uwarsan ta tsine masa kawai dan zai musu hukunci ne kamar bai sansu ba.


duk yabi ya cusa zcyar ma hjy mairo tsoro, nan akagama magana aka bar auren in four weeks time wanda dede lkcin da zainab arifah zata gama jinya kenan.



suna ficewa bappa zaidu ya kira ibaad awaya office dinsa yace maza maza yana son ganinsa..


lokcin ibaad yana wani important meeting ne shida jamal da farhan da prince hassan a gidan mahaifyar jamal din wata lady diana kirar yazo masa saiya roki bappa alfarma akan yabashi awa guda yanxu zaizo...


Dama kuma auditioning suka hadu sunayi, suna warware cigaban da suke samu, da inda zasu kara pushing dan lady diana ta kawo musu sabbin crude oil patners tanaso each of them ya saya 10% share a wani saudi arabian oil makert da zai na kawo musu return na billion 2 ko wani wata. haka suka tattara files suka har hada suka cire kudi, kowa ya bada nashi, but they need one more person kuma sun rasa wazasu saka, ibaad was thinking abt maheer amma daya kirasa sai maheer din yace masa bai shirya ba dan acikin yan uwansa karankaf maheer ne kawai yasan ibaad yana da wani abu waishi kudi amma haka yay shiru shima bai gaya ma kowa ba ya rike sirrin dan uwansa kmr yadda shima ya taba rike masa, ganin bai samu kan maheer ba kawai saiya siya share din ma bappa zaidu ragowar dayan slot dinsa yacike masa awajensa.


lady diana itace zata processing musu komi next week duk zasu kasance a kasar waje ayi signing duka legal documents acan dama kuma ibaad yana so yaje ya karasa gama furnishing din makaken gidansa da already last week aka gama shi tsafff...


sum shirya in sun gama meeting din kawai lunch zasuyi atare anan gidan su jamal din but due to kiran da bappa zaidun ya masa sai shi kadaine bazauna ba ya wuce office dan ya samesa acan


bayan tafiyarsa ne wajen cin abinci sama sama jamal ya gaya musu halin da ibaad yake ciki na yadda zainab arifah take kkrin manipulating din family dan a aura matashi


prince hassan saida ya fi kowa jin baqin cikin labarin nan dan sosaine ya tsane zainab arifah like everything abt her is just gross to him, farhan yace dama shi ya dan fahimce komi sabida ibaad was not himself musmn a satin nan kuma yasha jin labarin yarinyar she is complete spoilt brat kuma tana da wata kawa tantiriyar yar kwaya.


dukansu sunji tausayin ibaad bana kadan ba gabaki daya mood din prince hassan saiya lalace gabaki daya harma baici abinci ba, suka yanke hukunci kawai cewa zasu jira ibaad din yadawo dan susan wani irin support ya kamata su masa a wann lokacin dan su saukaka masa radadi.



ibaad yana isa offishin bappa zaidu ya samesa yanakan meeting ,gashi yazo da crude oil file din daya saya masa share dan yasashi signing amma baisan ya zai yafara tunkarsa da mgnn ba. wancan karon ma amminsa ya saya share a dubai na clothing line but it wasnt hard for him ya mata wala wala to get her signature and thumprint cikin sauki yasan bappnsa kam bazai signing haka kawai ba


he had been building a quiet business for his mum a kasar waje amma bata sani ba cos he want to really surprise her with it one day.

 

duk dama wekdn ne still saida ya jira for 10 min kafin suka fito shi ya shiga..


bayan sun gaisa bappa zaidu yahau gaya masa cewa nan da wata daya ne daurin aurensa da zainab arifah snn ya fayyace masa batun gida, lafiya, ciyarwa, kudin sutura da kudin kashewa da kuma MD position da prof yace zaibasa kuma ga yadda suka saka maganan agaban hajya yanxu basu isa suce basaso ba dan haka kar yace komi kawai ya karba. 


sann shi asali ba akan wnn maganan yakirashi ba, cos he just want to know, yace he had been wanting to ask him shin wani busines ne yakey, dan ya jima dayace masa yana business kuma yana ganinsa da cars da ababen duniya amma bai taba fayyace masa menene ba, he want to know now sabida kar aje a dorasa akan matsayin MD a kamfanin prof ya zamana iyakan madogaransa kenan na rayuwa, yace masa a matsayinsa na uba bazaifa yarda hakan ya faru ba, inde busines din dayakeyin bai tsaya ba yagaya masa kawai shizai iya sauka a wann kujerar tasa ya dora sa akai shi saiyay retire koma yaya ne dan kar azo ace prof ne ya dora sa akan arziki akarshe yazamo masa kayan gori snn yana da business partners in yanaso zaiyi amfani da sauran kudin gadonsa tunda yana da yawa sai yay investing kawai de shi bayaso ne ace ya zauna shiru prof yana masa komi.


ibaad yay shiru for a while, dan harga Allah yanaso ne dukiyarsa ya cigaba da zamowa anynomous kodan ya gama ganin kalar kowa, baisan ya nuna kansa a fili bare shima ya zama amfara worshiping dinsa a family kamar yadda ake ma prof dan sosai yaga illar hakan a ahalinsu, kusan wanda yake da abun duniya  ne kawai irimsu ammi babba, anty safeera,hajiya mairo da irinsu uncle moh suka fi darajawa

..saidai tunda akayi case dinnan ya lura da asalin masu kaunarsa, bappa zaidu, da mahaifyarsa sai brothers dinsa MJ da maheer wanda tunda aka fara case dinnan basu taba juya masa baya ba ko sun nuna masa baida gata ba 


sai yaga ma babu amfanin boye ma bappa zaidu komi nasa yanxu tunda har ya tambya, dan yasan mutumin nan yana sonsa tsakani da Allah snn yay masa yaqin da ko mahaifinsa ne ba lallaine ya masa irinsa ba. he tot abt it for a while kafin ya fara da neman alfarman cewa duk maganan da zai gaya ma bappa zaidun yanxu yana so ne su bari atsakaninsu ko mamansa baiyaso agaya mata, he will tell her how wealthy he is when he feel is ryt..


Da mamaki bappa zaidu yace masa toh zai masa alkwarin ne inde har abun bana cutarwa ko haramun bane.


ibaad ya ciro hadadden samsung dinsa da ga aljihunsa, yajona da printer na office din ya ciro 6 business front document ya tattara duka ya aje agaban bappa zaidu sann ya zauna yafara masa bayanin abubuwn dayake ciki, tundaga kan kamfanin Q4 sovereing grp, da su logistic, ga estates, da multinational investm firm dinsu, da private income streams insa na pharmaceuticals da wasu yan kananan tarkacen side busines


sai ya masa bayanin harda wann sabon dayau suka tattauna, snn yahau bawa bappa hakuri sosai nakin gaya makowa sirrinsa dayayi tsawon lkci, yace he just want to do sumting for himself by himself batare daya takura masa koya daura masa nauyin shige masa gaba ba....


tsabar kaduwa da mamaki da bappa zaidu yasha harsaida idonsa ya tara ruwan hawaye 


he was soo amazed abun yafara masa kamar a mafarki dan baiyi tsammanin yawan shige da fice da tafiye tafiye da tarayyarsa dasu jamal wani abu babba haka suke ginawa ma kansu ba, he salut the pure power of strong connection da networking, dan kusan shine 70% magic power da yay boosting succes dinsu daya hadu da sudin mutane me masu bala'in jajircewa da saka kai they take any favourable oppurtunity that comes deir way babu bata lokaci nd they trust each other sosai.


bappa zaidu yana hawayen murna still yana masa fada yana cemasa i am proud of u at same time still yana cewa baka kyauta min ba..har ya kusa yasa ibaad din dariya


yace "yanzu dama kana da rufin asirin ka zauna anata maka wannan wakalancin ai danasan hakane da wallah gori ma kadai sai ya ishesu kuma bazaka karbi komi nasa ba....


ibaad yana murmushi yace masa kar ya damu shi hakan ma yake so abar prof din yayi tunanin baida shi, sabida ya lura inhar kowa yasani labari zai iya canzawa, is eida shima afara bashi superior treatment sama da yan uwansa su MJ da maheer, ko kuma kawunsa prof din yay amfani da wani dama yafara jawosa kasa kmr yadda yake ma bappa zaidun makirci inyaga zai samu wani abu babba na cigaba sai yay maza yayi shige da fice yasa ayi cancel wasu contract dinsa aboye. 


shikansa ibaad saida ya fara shiga duniyan business kafin jamal ya nuna masa wasu sirrikan prof da kuma irin makircin dayake ma bappa zaidu wata rana ma su suke  budewa bappa zaidun hanya a sama batare da yasan waya taimake sa ba.


sosai bappa zaidu ya sha baqar mamaki akan haka snn ya gamsu da wannann bayanin nasa har ma yaji kamar cewa ibaad din ma yafisu wayo da dogon tunani, dan ya tabbata inhar akasan yana da wann daukakar babu shakka irinsu hajy mairo zasu nemi su lalata alaqarsa da su maheer da su mujaheed tahanyar shigo musu da bangarenci da fifiko da nuna bambamci..


is true they have to cut the generational curse kar suma wann dabi'an bambamci da fifikon ya bi generarion dinsu nd he is very proud cewa ibaad ya riga ya dau hanyar katse wann mummunan dabiar akansa da yan uwansa.



ranar murnan da bappa zaidu yay ya jima baiyi irinsa ba yasaka ma ibaad albarka yafi sau saba'in musmn daya ga share daya siya masa harda na amminsa duk ya gaya masa, bappa ya masa nasiha ya masa wa'azi,ya masa jan kunne, ya masa godiyaz kai babu abunda bai gaya masa akan ya cigaba da rike sirrin kansa ba. dan ma kar ya aje ppers din wani ya gani by mistake atake ya konasu a incinerator snn yasa masa albarka akan wanda zai fara ynxu.


yasha matukar mamaki dayaji cewa maheer ma yasan komi amma bai gaya masa ba, but he is atill proud of them, ya lura cewa kamar da alama generation dinsu sunfi hadin kai ko sune ma hala zasu kawo sauyi maikyau ma zuriarsu oho.


hirar abubuwa sukayi for like two hours suna magana akan prof, bappa zaidu ya gaya masa salo salo na yadda zai yi wasu abubuwan, da inda zai saka kafarsa da inda bazai saka ba, da irin risk din daya kamata ya guje duk ya kara masa ilimi...


yadda bappa zaidu ya kara masa kwarin giwa koshi aransa he wasnt expecting to get soo motivated nd happy da irin alfahari da kuma yabonsa da bappa zaidu yayi yanxu.


they agree to keep it secret nd just go with the flow, bappa zaidu yace ma ibaad yanxu kam hanklinsa shima ya kwanta tunda yasan goben ibaad din mai kyauce kuma yana da rufin asiri, koda kuwa ya auri zainab yanzu kambaida wani fargaba akan duk wani tsiya da shashancin mhaifinta saboda yasan yafi karfinsu.



ibaad bai bar offishin ba saida suka gama duk wata magana da zasuyi suka fahimce juna sosai ya karbi share yay signing dinsa a takardan,snn ya ma bappan nasa sallama yaje gida yay wanka da azhar ya dawo gidan lady diana ya same abokansa sukaci abinci atare aka tattauna, duk suka bashi hakuri akan abunda ke faruwa dashi, snn suka ce masa komi zaizo ya wuce tunda dai iyayen nasa basuce masa bazai aure wacce yakeso anan gaba ba. they are just hoping it will be soon, sabida duk sunce bazasu zo daurin aurensa da zainab ba amma idan akazo nashi da ayaanah they will personally sponsor the weding on deir own koda anyi kuwa saisun kara yin nasu hidiman special.


kamar da wasa suka yi hirar akayi dariya bai daukesu serious ba baisan kuwa har sun tattauna da lady diana akan hakan ba shide yasan prince ya dau abun har ransa yace ma ibaad sam sama kar ya sake zainab tau wata biyu a gidansa bai mata kishiya ba dan shi ko gidansa bazaije ba inbabu ayaanah aciki.


they spend quality time da abokansa agidan su jamal har yamma suka raka farhan airpot ya wuce gida dan ba'a nigeria yake zama ba shi. su ukun sunje buga snooker kenan a wani joint wayarsa ya fara kara yaga amminshi ne


gabansa sosai ya fadi duk ya dauka bappa zaidu got so excited ya gaya mata wani abu, yana daukawa kuwa yaji muryanta wani iri yace mata mata meya faru? nan tace masa ai ayaana ce babu lafiya jikinta yay dumi kuma safiya tace wai tay amai, tace suje asbiti kuma tace a'a wai saishone takeso yazo ya dubata agida.


yanajin hakan yau murmushi dan yasan mutumiyar tasa tay missing dinsa ne ta sauko takeson ganinsa.....


#idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[14/12, 19:44] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️4️⃣7️⃣

yana kammala wayar excusing abokansa yay yace musu zaije gida ayaanah tana zazzabi kuma wai shi takeso tagani, jamal ya fara dariya yace toh ka shirya zamowa love doctor kawai abun ya tashi, prince kuma dama takaicin zainab arifah duk yabi ya isheshi dakyar ma yake magana dangani yake kmr yarinyar is a witch for trying to ruin this beautiful love story.


sallama ibaad yay musu ya nufi gaban Lexus LS dinsa yabude ya shiga yafara tuki hankli ya nufi hanyar family house yana murza stiring at same time yana tunanin kalmomin da zai tunkare ayaanahn dashi dan bai taɓa jin faduwar gaba dan zaije wajenta ba sai wann karon dayasan ya saka ta awani hali.


wajajen 5;30pm na yamma ya tsaya a gaban wani babban pharmeceutical store ya siya wasu abubuwa snn ya karaso yay horn a bakin makaken gate dinsu mai gadinsu yaxo yabuɗe masa yashigo yayi parking car dinsa acan gefe inda kai tsaye bazaka dan yana gidan ba snn ya sauko kasa kai tsaye yawuce sashen amminsa da wata kalar sanyin sallama abakinsa.


shiru sashen ya dauka yakalle sashen sun amma sai bai nufi dakin ayaanahn kai tsaye ba cikin sauke ajiyan zuciya yawuce bed room din amminshi yay sallama tabashi izini ya shigo ciki, riga da zani ne ajikinta brown clur dayay mata mugun kyau da wani katoton  kaskon turaren wuta na zamani agabanta tadan warware dogon bakin

gashinta tana turareshi

dadin qamshin turaren ya gama bule dakin dan kadan ibaad ya lumshe ido dan shikansa kalar tsaftar amminshi na bala'in burgesa har acikin zuciya.


da sanyin murmushi ta tarbeshi yy tsugune suka gaisa ba yabo ba fallasa yace "ammi ya jikin nata?tace da sauki nadai bata magani taki sha tana kwance nima ynxun nan na bar dakin amma tunda kazo ai saikaje ka dubata, yace toh amma wani irin magani kika bata, tace dama na zazzabi ne  cos her body was quiet warm sai dan aman datayi, mikewa tsaye yay yace "its okay bari naje na dubata, cikin gyada masa kai tace inka fito dai ina sashen hajiya,ahnkli ya amsata snn ya fice ya karasa can bakin kofar dakin,


sau daya yay knocking kanwarsa safiya tazo ta bude masa kofa, suna hade ido dashi tay saurin sauke kai kasa cike da ladabi tace" Sannu da zuwa yaa. 


ayaanah najin sautin muryansa tay sauri takara narkewa aciki bargon tareda lumshe idanunta ahnkli


fuskar sa ba asake ba yace ma safiya "kema sannu" ina ayanahn take?


da hannu ta nuna masa kan gadon..tace"gatan can, yana shigowa tafara binsa zata tsaya jin gulma wani dan uban harara ya juyo ya watsa ba yace ke kuma sai ance miki ki fita kibada mutane waje kafin kiyi tunani saboda brain inki atoshe yake baya aiki ko?...


da wurwuri ta girgiza masa kai snn tajawo wayarta akan table ta fice da sauri.,.yace leave this site kwata kwata banason ganinki anan sashen get the fuck out magulmaciya kawai..


tana fita ya tura kofar yasaka key tana kukkuni ta wuce sashen anty safeerah da sauri


...cikin sauke ajiyan zuciya mai sanyi ya karaso wanda tunkan ya iso taji kirjinta ya kara sautin bugunshi da sauri sauri....


For one irrational second, fear punches him in the chest. ya xuba mata raunattun idonsa yadda yaga ta dukunkune kanta acikin lallausar bargon dayafi karfinta ta makale a edge din gadon zaka rantse bata iya ko motsi..a calm, distant gaze yake binta dashi har yazoshi ya zauna da tausayinta acikin kwayar idanunsa ita kuwa lkcin ji take kamr kirjinta zaifaso waje tsabar yadda yake bugawa da karfi..


aje ledar chemist dayaxo dashi yay akan gadon. daga nan batamasan sanda ya zauna agefentan ba duhun inuwarsa kawai taji da nitsattsen murya yakira sunanta ahnkli zai janye bargon yaga tay juyi cikin sanyin bori tajuya masa baya, kara biyota yay muryansa harna cracking yace "Ayaanah..takara tantame bargonta a shagwabe zata kara matsawa nesa dashi yasaka hannu ya fincike

bargon adan dolenta ta juya dan wani matstsen wandon jean ne ajikin ta da wani pink crop top da ko bra bata saka masa ba..


suna hade ido ahaka yaga hawayenta na zuba ahankli suman kanta data barshi in a messy bun ya barbazu suka yololo gasu so soft and wavyy

ganinta ahaka yasa koinansa mutuwa yana jin wani irin kasalallen ziriya nayawo jikin shi har ilahirin tafin kafrsa


ganin batace masa komi ba adan sucuce ya biyota kan gadon tare da fixgota jikinsa yana sauke wani irin ajiyan zuciya jin yadda dumin tsayayyun nono warta suka kwanta masa akan kirji..


lamo tay da fuska tana hawaye muryansa kusan ararrabe yace shush, nasan baki son ganina yanxu but can we talk abt what is wrong with ur health now? shiru tay jin kirjinshi na wani irin bugawa yana maganan ji yay ta malale masa akan kirji while he shyly expected her to pull away from his chest din duba da dukiyar fulanin nata a sake suke suna taboshi suna masu dagwala mai lissafi sai yaga takara narkewa can cikin muryan kuka dayazo mata bazata tace nifa bance bana son ganinka ba aikaine kaki xuwa...ka shareni..jin ta fara kukan dagske ahankli yace toh ya kike so nayi??i just thought if I gave you space xakiji sanyi aranki.. lumshe ido tay hawayenta masu xafi suna zuba masa a jiki da sanyin murya tace 'sanyi kuma? how on earth zanji sanyi..kace ma ammi zakay aure nd u left me to be hearing it sumwher else, ai in kasan zakay aurenka sai ka gaya min... da wani irin gajiya da kamewa tafadi hakan, yayi shiru yana kallon idanun nata data lumshesu gam gam da alaman bata so ma su hade ido bare ta kasa furta masa abnda yake mata ciwo a zuciya...dan kyabe baki yay muryansa a sanyaye yace ayaana amma kinsani i dint choose it..so, pls..look at me muyi magana.

...dede nan ta bude idon nata ta kalleshi a marairace yace "i dint choose to be married." sai da tay minti biyu tana kallon cikin idonsa kafin tace "i know,. yace to meyasa kike fushi kike ciwo? cikin katsesa tace kada kadauki fushi da rashin lafiyata a matsayin hukunci dana mka, Ka dauketa a matsayin zafin danakeji a raina cos its feels like i am feeling my pain, nd ur pain at the same time , ka dauka ciwona shaida ce akan yadda naji zafi. kara jawota jikinshi yay da sigar lallashi yace “hey, Idan yanayin fahimtarkice ke sa ki yin rashin lafiya tohni me ya kamata na yi da kaina knn?ayaana, akwai alaqar dake neman rabo,snn akwai wacce yake neman fahimta..shin ina da ikon karban dukkan wann matsayin a wajenki??


share hawayenta tay ahankli ta dada aje kanta akan kirjinshi araunace tace "nide  bansani ba, all i knw is nafijin tausayinka fiye da yadda nakejin fushin komi araina,

tayaya zan rayu da sanin cewa kaine zaka aureta shine kawai bansani ba...


muryansa kamr xai mata kuka yace nd what make u think dat i wanted this for us, uve missed ur final exams, u ignored my calls my texs duk kuma baki son gani na,..u tortured me when i needed u the most.. 


ashagwabe sosai tace but i read all ur texes kuma ai na fahimce su, nifa i am not angry with u....


yay kwafa yace ohhh so you just want to torture me kenan ko?


tace "noo"i just want to understand what i feel


yace "did u?kuma kin fahimce ni nima yanxu?


dan shiru tay snn tace a lil bit.. 


dagata cak yay ya dorata kan cinyarsa tabi ta sunkuyar dakai kasa dogon yololon sumanta har na kusan rufe mai idanun shi ya rike kadan, da muryan lallashi mai sanyi yana gyara mata suman baya yace "haba madam dina..pls take it easy on me mana,..I believe some connections aren’t built by choice alone.They’re assigned. Tested. Pressured. But can never erased. kidauka wann jarabawar muce.. ko yanxu zaki rabu dani ne sabida ance haka?


sunkuyar dakanta tay kasa bata amsashi ya tallabo fuskrta da tafin hannunshi suka hade ido suna masu kallon junansu da tsumayi 


ahnkli yace please tell me that we cannot be undone by this??


sabbin hawayene suka fara sauka mata tace "i know we can't. i can't even breath witout you. i was hurt.. nima aiji nayi kamr zan mutu ranar but what  am i even suppose to do.


idonsa luhu luhu akanta yace basai kinyi komi ba "just trust me kinji?nay miki alkawari i wll fix this...dan kwace fuskarta tay a hannun sa aragwabe ta jawo kansa tadora akan kirjinta kusan atare suka lumshe ido da muryan mai sanyi tace "then pls fix it fast bcos its really hurting me..


cikin kara lumshe ido da budewa yadora hannunsa akan suman kanta yana shafawa ta baya ahankli ahankli jin kansa awani duniya na daban, da karyayyen murya yace "i am really sorry, inaso kisan cewa babu wani ko wata wanda zai iya canza matsayinki acikim zuciyata nd i wont stop trying untill all our dreams come true bt If your sickness is the price of understanding me then I’m not sure I deserve to be understood at all.


lallausar hannunta tay wrapping akansa ahnkli tafara shafa masa can cikin tsakiyar kansa abazata ya saki nishi yanajin kmr xai sakin mata fitssri ajiki da sanyin murya tace " i am sorry too, ai kasan nothing will ever make me leave you.. kansa ya dada gyarawa akan lallausar chest dintan yanajin wani iri irin mahaukacin sacewr jiki idonsa a lumshe yace "hajiya Ur body is still very warm ya kamata muyi wani abu akai..yana fadin hakan ta dena shafa masa kan ta kalleshi shima ya dago taga idonsa har ya sauya kala sosai sai ta sunkuyar dakai ahnkli 


murmushi yay baice komi ba ya jawo ledan chemist in tana kallon sa ya harhada ruwan Allura within scnds suna hade ido tay firgita ta sauka akan cinyarsa ta ja baya yace meye kuma? tace nifa lafyata kalau..yace"ehm hve u studied medicine? kafin ta amsa taji har ya jawo hannunta ya kawo ta har gabansa ya dora ta kan gadon da kuka da wulla kafa da komi har ya juyata ya mata alluran zazzabi.


jikin ta amuce tay kwanciyarta flat akan gadon tana hawaye yana gama discarding syringe in ya karaso yana shafe mata wajen ahnkli yana murmushi yace you better get use to it cos i am the only doctor in my house..i wll deliver our babies. nd give u soo many injections inkika cigaba da kukan allura har yaranki suka girma haka zansa su miki dariya. tana share hawaynta cikin turo baki tace "nd how many kids are they?yay murmushi yace hmm kamar 6 boys 4 girls, baki bude tace 10?yaa yar ni innan sai na haifa maka yara goma?


..karamin dariya yay yace hm yarinya kenan wato zancen kike so ko?maybe we have 15 ma inkika iya kulawa da ni sosai..rufe idonta tay kafin ta amsa yace..cmn get up nd get dressed ki sameni a motana ynxu dan Allah, dan banaso mu jima awaje nd i want us to spend sumtime alone after seeing my friends they are bit worried abt u dan muna tare dasu akace min baki lafya.


..a mugun kasale tace "okay" kissing din forehead dinta yay calmly snn ya fice tay lumuii ajikin pillow tana mai bin bayansa da kallo, it took her a while kafin nan ta mike tsaye ta gyara zaman top inta yadda ya cukuikiya matashi dan gabaki daya qamshin jikinsa takeyi sosai...its almost 6 tay saurin fadawa wanka within 5 mins ta fito ta tsantsane jikinta tashafa body lotion sama sama ta bibbi koinnta da humra da oil perf snn ta kara da turarenta na black opium, bata tsaya kwalliya ba sama sama ta shafa powder tasaka kwalli sai dan man baki data shafa ta jawo nude abaya me bala'in kyau da tsada ta kwama ajikinta ta kara bin jikinta da turare masu dadin qamshi ta tufke sumanta duka baya ta yafa veil dinta ta hada da wayarta da side bag da shoes duk tasaka su a lokci guda snn ta fito. the house was once again quiete dan babban gidan ne bana easa ba,ammi tana sashen hajiya harta safiya kuma tana gefen anty safeera har ayaana tafice taje ta samesa acikin motarsa babu wanda ya lura..


she looked fresh nd original dake shi kullum tay simple kwalliya yafi burgeshi yana murmushi ya kunna motar  hannunshi daya nakan stiring daya na hanunta ahnkli ya doshi kofar gidan ana bude musu gate suna ficewa saiga motar uncle moh ya karyo tsaya yay bai shiga gidan ba dan duk sanda yaga ibaad da wani sabon motar zamani kuma me makahon tsada sai yaji kishin hakan ya bala'in kamasa, sabida duk gidan uncle moh shine yafi sayen abubuwan masu tsada masu daukar ido shi bappa zaidu bai fiye damuwa da nuna arziki a fili ba he is just a quiet prestige rich man that doesnt need to show off anan ne kuma sukay hannun riga da uncle moh 


tunda yaga farar lexus Ls na ibaad ta wulga yay sauri ya mika wuya a dan fixge ya kallo fuskar ayaanah sai yaji kmr bai yadda ba, gashi yaje ya gama shirinsa yau zai fadi maganan aure, but curiosity got the best of him kasa hakura yay saida yajira suka dan bashi rata snn yafara bibiyarsu a sannu ahnkli


Soyayyarsu me sanyi sukesha acikin motar suna sako hirar tsarin rayuwarsa na gaba sama sama aciki..


He already told her koma yayane zai tafi da ita kasar waje duk inda zaije anan itama zata zauna ta cigaba da karatu tsabar hirar soyayya yay dadi ko kadan basu lura da uncle moh abayansu ba ba wanda bai tashi tabbatar da cewa ayaanah bane a motar saida yaga sun sauka agaban wani eatry tare suna shiga basu jima yaga sun dawo ibaad ya rike hannunta kuma stll ya rike ledan tarkacen da suka siya


saida ya bude mata ta shiga ta xauna kafin nan ya aje ledan abayan seat ya dawo sika bar wajen, still ya dauka gida zasuje saiyaga sunyi wani hanya daban irin sabuwar estate ne na zallan masu kudi da mulki yaga anbude musu wani quest house sun shiga, tun daga irin gaisawar da mai gadin ya musu jikinsa ya bashi bayau ne farkon zuwan su nan wajen ba.


agefe yay parking jikinshi har na rawa rawa tsabar kishi da mamakin ayaanah dayakeji acikin ransa he was like dama ashe haka yarinyar nan take marar kamun kai wato bada mujaheed kadai ma ta saba fitar dare ba kenan? hmmmm kirjinsa naci da wuta ya kasa fita a motarsa har saida suka lume ciki. suna shiga ibaad yajawota sukaje palon suka same abokansa aciki


ayaanah ta gaisa da su sunata tsokananta tana murmushi dake zasuje sallah ne yanxu sai ya barbaza mata abincin da suka kawo yace taci tay sallah anan dan yana dawowa zasu fita...


lkcin already uncle moh ya sauko kasan yaxo ya same maigadi yafara tmbayarsa ko nan in hotel ne, yana so yaji dan shima ya shiga ciki, yace ma gate man wai yanxu yaga wani dan saurayi yanxun nan ya shiga ciki da wata karamar yarinya yar budurwa..


maigadi felt offended da irin tambayar amma sai bai dau abunda zafi ba yace masa nan quest ne na wani dan cikin sarkin zazzau snn is a private property ba'a barin kowa ya shiga ciki.


cikin kyabe baki uncle moh yace hmm guest house!! kasa kasa yace makansa hmm iskancin ma wato da manyan gayu ynx akeyi kenan

ya kalle mai gadi da bakar kishi a idonsa yace malam nikam koh biki akeyi aciki ne da zaku bari balaggen namiji ya shige ciki da yarinyar da bai aureta? 


mai gadin yace kaga mallam ni bansani ba, nan kuma ba gidan yan iska bane, u got to leave kona kira ma security...


jin gate man yace secuirty maza uncle moh ya kama girmansa baice komi ba ya koma cikin motarsa da wani irin matsanancin kishi me hade da fushi ya kama hanyar gida agaggauce


yana barin wajen bada jimawa ba su ibaad da jamal da prince suka fito a motocinsu kusan ajere ajere suka wuce gidan bapla zaidu dake hanya daban sukabi sai basuga uncle moh ko da a ahnya ba. a anan ibaad ya jasu sukayi mgrib da isha yakaisu ciki suka gaida bappa zaidu yasaka musu albarka snn suka dawo quest house yasamu iyaka sallalolinta kawai tay bata wani ci abinci ba haka yazauna ya bata dakansa saida taci sosai ta koshi kafin sukay sallama da aboknsa ya dauketa suka fita wani wajen very private nd quiet suka zauna sukayi hira

for quiet sometime sai can wajajen 9pm suka tafi wani designer store atare.


suka samu ankawo all this exclusive weding dresses na yaran masu kudin nan ranging from millions uptil a billion irin designer wanda ake saka kanana diamonds stone ajiki innan anakan sorting wasu za'a akai babban store na can lagos wasu abuja, sosai store in ya cika da kaya iyakan ganin idonka saidai me karamin canji bazai iya daukar ko abu daya anan ba. yana biye da ita suka je wajen shoe nd bags ta dauki few colours dataga sun mata kyau da irin rare sleek clutches innan Rose red da wani silver,  ibaad yatayata xaben designer shirts da jean da fallazos da flair skirts that are hand stitched daga india wasu multi colours wasu plain da few jeweries nd make up, tana tsaye taga ya saya mata one very fine pure red weding dress fitted riga da bajajjen skirt da yaji kwalliya da sharasharan veil dinsa dogo har kasa da jewris dinsa duk ya hada mata acikin tarkacen kayan shoping dintan, shi baidau komi makansa ba banda wasu turare da zai bawa kanwarsa safiya dan bai fiye son siyan kayan sawarsa anan nigeria ba kuma now dat he is officially a doctor he mustly will wear suits nd casuals to work kuma baison ready made suites yafison asalin tailored designer da suka saba sakawa.


they came out with almost 3 big big shoping bags ahnya ya siya mata tarkacen kayan ice creams da chokolate wanda zata sha gobe, almost to 11pm ya dawo da ita gida, ya bude mata kofar motar ta fito duk tagaji sabida uban shoping dn da sukayi


hannunshi cikin nata ya ya karbi bag dinta then he took her inside uncle moh yana can sama yanata kallonsu kamar kansa zai yi tsawa d wutan kishi dana fushi


gashi tun dazu daya dawo gidan yaxo zai gaya ma hajya mairo labarin abunda yagani sai kuma yaxo ya samu sunata magana da ammi karama hjy takira kawunan ammin na can garin maidugurin awaya anata gaggaisawa..ga hjy da shegen son hira, yay musu xiriya a falon har ya gaji ya hakura ya bari saida safe kawai zaizo ya sameta dan ransa a mugun dagule ya dawo jin cewa ya kori dansa har china akan ayaana amma wai duk bai haifar masa ɗa mai ido ba gashi ta ɓalle ta dake cigaba da badalarta da ibaad.


yau babu kalar mugayen zaton da bai kawo akan ayaanah ba, at some point yay tunani aransa cewa kawai ayaanah ce bata da kamun kai cos he tot it will be just mujaheed ga kuma ibaad kuma duk tahadasu tana fitan dare dasu..yanxu sanin how many times ibaad ya kaita quest house din nan ma bai isa ya kiyasace a ransa ba. amma yana da yaqinin koma meye yake kaita yana mata awajen da sannunta kuma bazai wuce suna morar juna ba.


gashi dama abokinsa daxu ya gaya masa ai dama yarinya karama mai kayan marmari irinta dole ne jikinta yana mata kaikayi shiyasa hala take bibiyar yara wanda zasuna latsata


abokinsa yay objectifyn inta matsiyan yar iska


shikuma he directy sexualize her in his mind yafara raya cewa dama wann saurin girma da cikowar nono da kuma faffadan kugu da ayaana tay must have to do with wani namiji daya ke latsata awani waje shiyasa tay bul bul komi ya fito ya tsaya kyamm.


kalar fatarta da dirin jikinta is very atrctive babu karya nonon ta ko tasaka riga zaka iya ganin shatin tsayuwarsu kyam  suna da shape ne kamr an hula balloon kawai gani yake dolene zataso a latsa mata sexy jikin nan nata no matter what kai dolene ma ta zama fasika.


his suspision only bcom more intense dayaga ta fito a motar ibaad dis late nd looking very tired kuma ya riko hannunta da jakarta ya kaita ciki


he instantly believe he must have fucked her,maybe ya rage zafi da ita ya gama gajiyar da ita ne ya dawo musu da ita 


tsabar zuciyarsa na tafasa ji yay kamr zai sauko kasa ya kama ibaad din da dambe


ganin ibaad ya dawo yazo ya fito da shpping bags zai kai mata ciki kawai ya wani buga hannunsa akan bango yace inaa baxai iya rainon yarinya wani kato yaxo ya more jikinta abnza agaban idonsa haka batare da aure ba..


kamar iska ya fito fuuu zaizo fada da ibaad yana sauka da stairs ma sashensu caraf sika hade ido da anty safeera ko lura da mood dinsa batay ba

ta jawosa tace "ya zaka barni akan gado inata jiranka kazo waje ka tsaya? ni wallah bacci nakeji u gat to make me sleep

...fuskarsa a takune yahau cewa safeera agajiye nake kawai kije kiy baccinki mana, ko kulasa batay ba tajawosa suka wuce dakin ayanaso bayason haka saida ya mata yadda takeso acikin daren nan


after the sex with his wife bacci ne ya dauke sa bai kara sanin meya faru a fanninsu ibaad ba. daga ta fannin ayaanah kuwa ibaad yana kawo mata bags din bayan sunyi bye da juna tamasa godiya sukay bye ya wuce gida shima aggauce akam zasuyi waya gobe da safe..


their were both happy nd relieve ya jima baiyi bacci me nisa ba kamr nayau ba, haka itama kishi ya ragu mata sosai dan tana da yqinin cewa itace kawai sarauniyr zuciyr yayanta ynxu bata damu ba tasan he can still marry her as his scnd wife duk dama sam sam bataso ace zata zauna agidansa da wata kishiya ba..


bacci mai dadi tay da tunanin kalamansa aranta washe gari  bayan sun farka tana idar da sallah ita tafara kiranshi suka gaisa snn tay bitar qur'ani tay wanka taxo tafara ciccire kayan bags din, kirjin safiya yabi ya cika da ruwan kishi kmar zata fashe tarinka kallon ayaana a matsayin gold digger tazo musu gida taxo tana cin kudin yayanta abanza..


tsabar kishi bata jira tagama kallon kayayyikin ayaanah datake jerewa a wardrp inta ba ficewa tay taje gaishe da ammi tanata kumbura fuska tana cewa ammin saidai tasaka yayanta itama yakaita shoping


har saida ammi ta dauko bag din daya aje jiya akan table dinsu da sunan ta ajiki ta bata taga ya sissiya mata perfumes masu tsada aciki itama kafin hanklinta ya kwanta tafara washe baki...


ammi tace hmm kedai safiya baqin hali da kishinki yayi yawa wallah, shikenan yayan ki bazai siya abu ma wata ba saike ko???


tana turo baki tace Haba ammi amma ai abin yay yawane inbanda traditional wears da turaren gargajiya dakike saya mana all her abayas and english wears da komi da komi fa shiyake saya mata kuma masu shegen tsada aiko ni bana morarsa kamr ita kuma fa yana tura mata kudi yana siya mata duk abunda tace zataci


cikin katseta ammi tace "ke kuma akace miki da kudina ake siya miki naki kayan ko? toh wallah safiya ki kama kanki karma ki sake wata rana yaji kina irin wann maganan. kafin ayaana tazo gidan nan hatta dan kunne inkin gani a kunnenki yayan ki ne kebani kudi asaya miki. bappanku kuma yake biya muku school fees da sauran tarkacen,duk wani abunda kikagani yake ma ayaana kema fa kisani daga aljihunsa kike ci, innaga dama in saya muku wanda naga zan iya amma karki sake wann ignorance din ya jawo miki dan bura uban duka ahannunsa karkiga wai kin girma, ni bana son wann kananan magana, ki dauke idonki akan abun hannun ayaana ke kinada kowa naki, ita waye take dashi anan garin inbashi ba?ko bakisan cewa amanarta mhaifyrta ta bashi bane nd whats is wrong with u..


cikin sanyin jiki safiya tace kai ammi aida saiki gayamin kudin sa ne ake siyamin kaya ni wallah bansani ba..kawai na dauka yadda ta sace zuciyrki kike saya mata laces da su atmfar dayafi nawa kyau haka shima ta dawo dashi.


baki bude ammi tace"lallai safiya baki da godiyan Allah, duk aka kawo kayan ma ai ke kike fara zaba,  toh ko zaki hadamu ki cinyemu duka ne? safiya i dont like dis ur self centered nd selfish habit kawai tashi kije kitchen tinda yau sunday ne saiki fara min wanke wanke ina zuwa


da kukkuni safiyan ta miƙe tareda rungumo shoping bag din tafita tana cewa kai ammi kwana nawa kenan ayaana bata miki aiki ba kullum saikice ni ni kamar nidin na mutum bace


ammi tace zan ci ubanki safiya ina data fara ciwon nan kawai kika soma shiga kitchen din karki sake kibata min rai toh


batace komi ta fita tana tura baki...ficewarta bada jimawa ayaanah ta shigo tay kyau sosai sanye da highwaist skirt da white tucked in short ta daura vintage scarf kalar skirt din jikinta ma wani irin sanyi mai dadi.


tunda ta karaso ta rusuna agaban ammi take kallonta da mamaki tace ohh oh su ayaana wato har rayyan yaxo kin samu sauki ko? adan kunyace tace ammi allura fa yamin kuma har yanxu wajen yana min ciwo bai warke ba

..ammi karama tay murmushi tace ai naji dadi sa allura ne tunda dai ke baki kaunar shan magani toh bagashi nan kin warke ba to muje kitchen yau akwai abubuwan da zan koya muku..snn zamuje GRA nasarawa can after munyi breakfs ayi spa, pedicure nd manicure,gashin kanki ma duk ya sake ya fara bushewa, ku shirya yau awajen zamu wuni.


murna ayaanah tafara cos this ryt here is her favourite part of the fun dan tana mutuwar son xuwa gyaran jiki musn tare da ammi karama sabida bakaramin gyaran take sawa a musi ba har siracin turare dana gashi ga vaginal steam da sauransu yaranta are alwys clean nd healthy bazakaga wani kalar dischge ko bashi bashi na tashi ajikn su ba tunda suka kawo girma.


Da murna tabi ammi kitchen suka samu safiya anan tana kan wanke wanke karshe ma ayaanah ta krba ta karasa kuma tay shara da mopping kafin suka gewaye ammi tafara koya musu wasu kalar breakfast na yan gayu


safiya haryau bata iya yin tuwo ko miya ba saboda bata ci tafison ire iren wnn english food in itakam shiyasa take mutuwar muradin bappa zaidu yakaita kasar waje karatu tunda tasan yayanta acan zai zauna in yayi aure tattaunwrta akan haka da bappa zaidu yay nisa shiyasa bata damu ba, and she think inde anty zainab ce matar yayanta ai kakanta ta yanke saka anty zaina nada son kyauta bata da takuri duk da rainin wayon ta amma tasan inta zauna agabanta zataji dadi




dagata dayan bangaren

kuwa uncle moh yana fitowa sallan fajr baiy kasa a gwiwa ba ya taho sashen hajiya mairo, yau kwata kwata fuskarsa ba asake ba suka gaisa har ta dauka ma rikici suka kwana yi da safeera, tun bata tuhumesa ya tuma yafara bambami sosai ta inda yake shiga bata nan yake fita ba akan tarbiyan yaran gidan


yace ma hajiya wallah sudai a zuriarsu babu mazinata sai in acikin matayen yayunsu maybe watta acikinsu akwai mazinata a zuriarsu, dan ya lura da take taken wasu agidan nan gabaki daya basa kama kansu, suna yawo da kananan yara suna kaisu hotel da dakin abokaina suna jimawa tare da su aciki snn sai su rudesu da abun duniya...


maganan sai yay ma hajiya mairo wani bambarakwai har ihu ta kusa masa akan ya fito filo ya ambce sunan wanda ya kama suna xina...yace mata shi bayason tada fitina yaushe aka gama case na zainab arifa azo ace shima ya dauko wani gulma kawai yana gaya mata ne tasan cewa shaidan zai iya shiga gidan nan..kuma zaa iya lalata yarinyar data kawo gidan nan amana ta damka musu

..sai kuma yace "inma basu suka haife ayaanah ba barasu iya bada shaidar halinta duka ba, shi gaskiy ynxu dabiun ta ne yafara bashi tsoro


hajya tanajin hakan sai kuma taji hanklnta ya tashi tace kai muhammdu dan Allah ka gaya minene ayaanahn take yawo tana aikatawa dan ynxu haka nima a kwai case inta ahannu na dan a shagon abincina naji ana gulmam cewa ta hade kai da ruthy gashi ance wai ruthy ta xubda cikin shege kuma tana kungiyar madiqo ni wallah maganan nan ya dameni amma nasan ayaana bazatay hakan ba aiba haka suka taso agabanmu uwarsu ba


ransa yaji ya kara hargitsa cikin karkada kai yace hmm hjy kidai kara bincike dan yaran nan fa ba ashan bakin su wallah. to bari ma gaya miki nasha kama ayaana tana fitar dare ma agidan nan


tun be dire ba hajy ta dora hannu aka tace laaa ha ila ha illahi, muhammadu??? a'ina ka kamata haka??? yaushe? kuma dan bura ubanka shine baka gaya min naci ubanta ba


saukar da muryansa yay kasa kasa yace aah hajiya bafa irin wnn dakike zato bane, farko dai da mujaheed na taba ganinsu sunfita da dare batare da sanin kowa ba, ko ina ya kaita oho sainaga kuma sun dawo gidan har ya sissiya mata abubuwa...hajy dan Allah karki gayama safeera wann magana amma tsakani da Allah dabiun da suke ayyanawa da mujaheed ne yasaka ma na dagasa akassr nan nakaishi karatu can china karyazo suna fitan dare yaje ya danne yarinya bamu sani ba ya mata cikin shege kinga kuwa mutuncinmu gabaki daya ne agidan nan zai zuba


hajiy ta dafe kirji tace ma shigesu, mujaheed din danake kallonsa salla salla ashe ko alwala bai iya ba dan ubansa shine zaina yawon dare a idonmu da yarinya balagagga? toh ai kay dede da kamasa haka Allah ya isa kukan danayi da zai tafi chana, duk na dauka anzalunci an turasa waje me nisa nayita tausayi ashe abun kunyar da yay niyyar jawo min kenan?


uncle moh yace toh ai bashi kadai bane mama...yo ba gara shi ba..jiya ai da kinji ina dukan ibaad agidan nan..


tace tooh?? me shikuma yay maka nide harga Allah batun dambenka da rayyanu ya fita abakinka wallah bana son nayi asarar haihuwa


yace hajiya kenan bakiga abunda yayi da yarrinyar nan bane jiya da ko bacci bazaki iyayi ba


tace meye ne dan Allah kadena samin fargaba kawai ka fito fili ka gayamin shidinma danneta ya tashi yi?



uncle moh yace "toh ni ina zan iya bada shaidar zina bayan a idona yakaita wani quest house suka shige ciki tare me gadin kuma yamin rashin mutunci yahanani shiga bare ma naje na musu fatata na dawo dasu gida


tace innnalillah wa inna ilaih rajiun kace kagansu ido ido


yace tabbas nifa har wajen nabibiyesu jiya nazo zan gayamiki ai nasamu kina tare da fatima karnafadi hsky agabanta kice na ci mata fuska na kira danta mazinaci amma tsakani da Allah hajya kiga ibaad yadda yay kato ya girma ya mallake hanklin kansa harshine zai dauko baligar yarinya yaje wani quest house sukebe acan kuma da dare shin menene zai gaya mata acan wanda bazai iya gaya mata anan gidan ba inbanda son ya lalata ta quest house ai baida maraba da hotel hajya..


kuka ta fashe dashi tace yanxu ina ayaanan take? amma wann yarinya ta cuceni daga wann sai wann ita ashe bazata aje gindinta awaje guda ba saota siyar, yarinyar nan bata da mutunci bazata kama kanta kamr na kulthum ba kaga dao

yarinyar nan har akayi aurenta da mahir bata san ya ake rike hannun namiji ba wayyo Allah na shiga uku..


ganin zata birkice masa marmaza ya katse sauran maganan dake ransa ya fara cewa  a'a hajiya ni fa bangaya miki wann maganan danki tada wani rikici ba..inda rikcin nake so da agaban kowa zan hukunta mujaheed kafin na turasa china amma tunda banmasa haka ba kema babu ruwanki dan bada shaida akan zina fa babban abu ne tunda bankamasu ido da ido ba, kema sai kiyi musu kyaakkwan zato amma kan gaskiya abun babu kyan gani dan sai tsakar dare ma ya dawo da ita.


sake kwaroro salati tay tace kai muhammadu shine bansan haka na faruwa ba.


da muryan yaudare yace yanxu daiki kwantar da hanklinki ni na riga na yanke mana hukunci na kawo mana mafita wanda zamuyi shi acikin rufin asiri da kare martaban gidan mu dana yaran mun duka, dan yanxu in aka fito da maganan nan kinga kowa mutuncinsa zai zuba toh kenan babu amfani ba kar azo mutanen waje amiki gori ace akwai mazinata acikin gidan ki kinga an anzubda ma gidan nan mutunci


tana share hawayenta da bakin hijabi tace wallah kuwa hakane muhammadu yanzu kai meye ne shawarararka


tana fadin haka ya gyara zama wani nannauyar ajiyan zuciya ya kufce masa abazata....yace toh nide nay nazari da tunani me zurfi, naga iya abunda ya dace muyi nidake dan mu ceto mutuncin yarinyr nan da kuma gidan nan baki daya shine, tunda ibaad aure zaiyi, mujhed kuma kinga karatun bai shiga jikinsa bama tukuna bare ya samu aikin yi gashi yay nisa da ace dukkansu basa nan gidan ayaanah tafara fita da maza awaje nace mai zai hana saini in rufa mana asiri duka in aureta kawai, kinga zanma fi kulawa da tarbiyanta tunda yanxu duk watsewa zasuyi bayan auren nan, ayaana tana gabana tana gaban ku koba ba nanan agidan nan nasan dai zaku samin ido akanta kuma ke shaidace zan iya kulawa da ita sosai..amma bansani ba ke yakikaga?


dan jimmmm tay jin maganan yay mata nauyi ganin age dinsa da kuma cakwaiyr da hakan zai iya haifarwa da har zatace mishi aa sai kuma ta fara tuno maganganunsa witou thinking it tru tace "ai shikenan ma wannan shawara naka muhammadu yayi sosai

dan wallah bazan iya da abun kunya ba kaga ranar auren rayyanun d sai ahada da naku ayi duka awuce wajen, kai amma nagode nagode muhammadu Allah ya maka albarka yanxu inba kai kacika dattijo na gari ba uban waye zaiji wann magann akan ya mace snn yace zai kwasheta...

toh aure kam kmar anyi an gama 


wani dan uban dadi yaji aransa yace nagode hajiya ai dama nasan ke zaki fahimceni, abu da zubda mutunci da lalacewa ai gara a katseshi da wuri sedei wani hanzari ba gudu ba hajiya wallah bansan ya zamuyi a sanar da safeera ba 


cikin kyabe baki taceb"haka dai zaka daure ai hakuri zatay ataru a rufa ma juna asiri yo ayaanan ce bata san halinta ba? yarinya data taso agabn idonta ai banajin ma yakamata tay kishi da ita wnn ai kamr yarta aka kawo mata hakuri zasuyi su zauna da juna


yace toh ita ayaana? fa, 

kode kar agaya mata yanxu sai in auren yazo kurkussa sabida...


cikin katsesa tace kai dai muhammadu kabar min komi ahannuna zan kira kawunnan ta ai akwai wani dan uwan ubanta da suka raba uwa, shi ya mutu, amma yana da manyan yara sunema suka daura ma ubantan aure da ƴata taawure, zan kira yan uwansu na jigawa abani lambarsu muyi magana, ita taawure kam ai ko bannemeta ba nay ma ayaana aure tasan dai bazan cutar da yarta ba tunda jikana ce. batun magana abari sai aure yazo dafff dani dakai zamu gaya ma kowa yaji

..kaje kayi shirinka ahankli, snn ka tabbata ka y ma safeera kayan fadan kishiya dan kar haukar su na mata ya tashi.


da matsanacin farin ciki aransa yace nagode hajiya Allah yay miki dubun abunda kika min, Allah ya bar mana ke kincika uwa hajiya godia nake.


tace uhumm babu komi muhammadu duk dai abunda kake ciki ka sanar mini karkuma ka gaya ma kowa zancen nan sainagama shirya komi nima


da murna yace tohh sukayi hira kadan snn ya fita, bada jimawa ba ya mata trasfer din almost 60million kyauta ranar wuni yay yana washe baki dan hatta anty safeera kasa gane silar farincikinsa tay 


gashi kuma taga su ayaana da ammi gabaki daya basu gidan bare tay tunanin ko ya gamu da ayaanahnce.


idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[14/12, 20:47] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️4️⃣8️⃣


haka rayuwa ya cigaba har na tsawon sati guda kowanne bangare da kalar _Abunda ke ɓoye_ acikinta, uncle moh da abokansa tuni suka hau shirin bikinsa a ɓoye kusan komin sa agidan alhaj ameer suke shiryawa na biki akwatuna da komi na amarya da uwargida ya rarumo anata cikawa da kayan gani na fada baiko damu da saka ido akan ayaana ba sabida yasan burinsa yanxu ya riga ya cikka bamai iya hana yuwar auren nan tunda hajiya mairo ta amince. babu wanda ya gane shirinsu,anty safeera ce kawai was left confuse at the middle of the chaos, dan babu wani alaman daya nuna mata cewa ayaanah is sumhw responsible da zumudin da uncle moh yake tafkawa agidan nasu kwana biyu, ayaanah is more inclined to ibaad company abokansa biyu suna gari suna yawan fita tare, daga nan kuma sai sauran exams inta dan baifi saura paper biyu ne ya rage mata sutarkata su gama makantar gaba daya ba. 


soyayyarsu suke kurba da ayaanah kamar ba auren zee arifah ke jiransa anan da sati uku ba. saidai the more hjy mairo tana ganin shakuwar ibaad da ayaana kwana biyu the more ranta na dada baci, 


tanata mamaki wai har rayyanu ne zai cuceta ya kuma cuce taawure data damka masa amanar yarinya yazo kuma yana kaita otel otel suna yawon dare. sosai ta riƙe abun nan aranta bana kadan ba, ta dawo tana ma ayaanah kallon lalatacciya badama ammi karama ta zauna sai ta fara kawo mata magangunan gyara tanacewa lallai lallai kawai aje afara gyara mata ayaanah duk a tunanin ta ai angama lalata.


ammi karama sam bata gane abun ba dake kusan dukansu take matsa masu akan batun gyaran wata rana sassafe ma zata harhada abubuwanta na hadi dakanta ta kawo musu dukansu harda safiya sai tace susha saidai na ammin da na ayanah sai kaga yafi yawa


abun har yazo ya fara damun ammi ranar data kawo kazar matsi ammi ta mayar mata tace wann abun yay ma ayana tsauri ajiki kar tay aure ya zamo sai anje asibiti daren farko,..hajya tace sam tasan metakeyi haka ta saka ayaana agaba da zagi da masifa saida tasata ta cinye duk dama dataje daki saida ta amayo da rabi waje


fannin zainab arifah kuwa duniya sosai tay mata dadi, kafin kace wani abu anyi sabbin zubin masu kulawa da ita kusan kullum ana mata gyaran jiki, abinci da sauransu, gashi ta sake ranta tana shan maganin sosai duk abunda iyayen suka sakata kuma tanayi batare da gardama ba


wann satin za'a mata small corectional surgery, the oda week kuma idan akaga she is fine zataje bridal fittings a paris babanta ya bata kudaden da zata sauya wardrobe dinta gabaki daya, in short kawai kayan da zata dawo sakawa intay aure. the house the everything da sai shafi gidan ana ta famar re arrnging they are going to live in the U.K tunda anan babu nisa da schl, work da kuma inda ibaad shima zaiyi karatu they are all within the states of United kingdom.



ana shiga sati na biyu  ibaad yafara shirin yin tafiya harkokin dake gabansu ranar da zai tafi ayaanah ce ta rakashi har aiport yariga yagaya mata in ya tafi zaiy abubuwa da yawa ba lallaine tana samun kiransa ko wayarsa ba har sai ya dawo nan da sati biyu nd dats just one week to his weding. tunda ya gama lallabata da kalamai masu sanyaya zuciya sai bata wani damu ba,bayan sun rabu ita ta tuko motarsan ta dawo masa da shi gidan bappa zaidu 


samun cewa ammi babba bata nan sai tabararraje a dakin sultana sukasha zaman hirarsu tare ranar daga suci abinci suyi kallo sai su kira kulthum suyita tsokanan tumbinta that is almost 3 months old ynxu



sai can yamma snn bappa zaidu yasaka aka kawo ayaanah gida hajy mairo batama tsaya tantance waya kawo ayaanahn ba ta kirata ta saka mata tsauraran dokoki akan yawan fita, rantsuwar duniya ayaanah tamata akan cewa agidan ammi babba ta wuni amma matar nan tay burus tace mata kartadai sake ficewa agidan inba da kwakkwaran dalili da aka sanar da manya ba.


itade batasan meye matsalar hajy mairo da ita ba,she just tot is old ppls mentality sumtimes in agaka yarinya ta zare kominta ya fito da wuri sai afara matsa mata da tsaro, ko ajikinta dan sama ibaad ne dai in yazo dole take fita toh gashinan ma baya gari kuma bazai dawo nan  kusa ba saiyaci sati biyu.


ana tsaka da satin bayan anyi wa zainab surgery ta samu dama dama itada babanta suka tafi kasar waje, mamanta ne kawai agidan yanxu.



ranan da su ayana suka je scnd to the last exams dinsu kwasam hajiya mairo ta kira ammi karama ta bata waya wai su gaisa da kawunnan ayaanah 


da murna ammi karama ta karbi waya aka gaggaisa taji mutane sunata mata godiya duk tadauka kodan rike ayaana da sukayi ne tsawon shakarun nan ashe su godiyan bada aure suke yi wai. bayan sun gama wayar ne hajiya mairo ta hau fayyace mata batare da ta fito fili tagaya mata dalili ba sabida bataso wann karon ma ta zage tarbiyan rayyanu a idon fatima ace taci mata fuska.


saka maganan tay a tsatstsaye cikin bada doka baneman shawara ba, tace ita tariga ta yanke hukunci zata aurar da ayaanah kawai wa danta muhammadu sabida ya cigaba da kulawa da ita suma ta taso agaban idonsu tunda ibaad aurensa zaiyi bataga amfanin aje ayaana tana galantoyi a titi da mutanen banza ba.


ammi tay tsammanin akn ruth ake magana dan maganan ruth ya fara zagawa gari ba zallan akan lesbianism ba har da wann sex addiction da gang din cult datake rolling dasu


ammi ko kadan bataso wann maganan auren ba dan ta san bazai taɓa zamowa adalci ace ayaana ta taso agabansu snn azo a hadata zaman kishi da safeera ba musmn ma a age inta


yau kusan cire kunya ammi karama tay ta rinka gaya ma hjiya gaskiya dakuma fayyace mata irin fitintinun da hakan zai jawo...amma hajya tace sam ai ba wann ne kadai dalilinta baz kuma bataso ta furta ne ace tay musu cin fuska dan haka kawai kowa yay hakuri ai muhmmdu baima safeera alkwarin cewa bazai kara aure ba barema wann auren na rufin asirinsu ne duka baki daya kowa yayi hakuri


tace ma ammi karda ta sake ta gaya ma ayaana komi sabida bata bukatar permision inta tunda ma ta gama magana da wakilan uwarta da ubanta kuma sunce zasu sanar da taawure zasu ma yarta aure. tace already sun wakilta wani dattojo dan uwan su juma dagata fannin kishiyar uwarsa 

sunansa Alhaji hanza ranar auren zaizo da sauran kannensa su zasu bada auren ayaana a masallaci duka duka ayi komi danasu zainab arana daya.



ko na minti daya abun baima ammi karama dadi ba, auren dole ne ma ayaana, kuma da mijin anty safeerah sosai taga rashin mutunci da rashin adalci da tsokano fitina aciki, she wanted to tell bappa zaidu hajiya tace wallah wallah inta fada ma zaidu zasuyo kaca kaca sabida babu ruwansa acikin wann maganan aikinsa kawai miƙa auren ibaad ne dana muhammadu ita bata son munafurci


tun ranar ammi karama tabi ta sauya ma hajiya mairo tazamo babu wani walawala a fuskarta kwata kwata, dan sai yanxu ta gane cewa ashe duk gyaran nan da ake ma ayaana na auren dole ne, duk sanda tay yunkuron gaya ma bappa zaidu sai kuma ta tuna irin masifar da hakan zai iya jawowa sai taja bakinta tay shiru dan karshe ciwon ayaana ne zai tashi, shikuma tace zata tsine masa in yace aa, ga safira itama ba shiru zatay ba. 


duk tausayin ayaanah takeji sosai har bata iya nitsiwa taci abinci


hardai ammin tay fushi taja baya da zuwan shashen hajy mairo kwata kwata  tacire hannunta tadena ma basu maganin mata, but still hajiya mairo haka zato biyosu har sashen har da itama tasakasu agaban tace sai sunsha.


ana cikin wannan yanayi hajy hajara ta dawo daga kauyensu na jukunawa ranar ma wuni sukayi a daki suba kuskus da hajiya mairo har tagama ta fita


washe gari sassafe tun asubah bai gama yi ba ammi karama tana bacci taji hayaki ya cika mata daki, tana bude ido taga hajy mairo ta hade rai tace maza maza ta sauko kasa tay hayakin nan..


ammi duk ta rude ta rasa meye wannan, hajiya tay burus ta rufeta da zani ta mata hayakin nan tasss for the first time da aka ma ammi karama wann hayaki wuni tay tana ciwon kai


hajiya bata daddara ana daf za'a kira magrib ta sake dawowa ta mata. harsaida sukayi haka na tsawon kwana uku snn ta kyale ammi karama, ta dawo kuma yamma zata dama mata nonon rakumi da wani gari aciki ammi ta tsane abun nan ammi haka zata tsaya aknta tace mata wallah sai tasha. bata wasa da ita.


wani bin har taji kmr zatay amai amma haka zata sha tun tuna guje ma abun harta hakura ta sake ranta hajy mairo tace mata daga tay aman jini maza maza tazo ta gaya mata tace toh amma haryau dai batay aman ba tukuna



ana kkrin shiga sati na kusa da karshe kafin aure ayaana suka gama exams aka musu mini walima agidan as usual sai yau uncle moh ya shagala ya fara nuna zumudinsa a fili 

irin reaction din kallon tsana da haushi da anty safeerah tay ma ayaana yasa ana gama hidimar da yamma suna zaune da anty safeeran a falo ta shigo da duk wani kyautarsa daya bata yau din ta dauko ta dawo masa dashi agaban matarsa tace masa ta gode amma bazata iya karba ba


tambayar duniyan nan yay mata agaban matarsa ammi taki ta amsashi firrr haka ta kama hanyarta ta fita


anty safeera tana jinshi ya dinga bambami yana daurawa ibaad laifi kan kace wani abu suka fara musu da matarsa 


tace masa karya wani lakama ibaad, kowa yasan ibaad has travel ba a ma samunshi awaya kawai de yarinya ta gajine da haukar da yakeyi kawai inzai bari ya bari, tace masa ga dansa mujaheed yana son ayaana kuma next week zai dawo auren zainab gida what if mujaheed yazo yace yana son aurenta haka kenan zai cigaba da wann creepy bvhrs din bayan yarinyan ma bataso amma sai yana cusa mata kai yake?


yadda tay maganan da zafi da kuma gatse yasa ransa ya balain baci sai baice mata komi ba kuma yana gani ta kwashe gift din su abun wuyane da atampopi da su takalma kaiwa dakinta tay tay kasonsu da sunan yan uwanta,yay zuciya bai kwana a dakinta ba ita kiwa sasafe ta kyauyar ma yan uwanta komi dake ciki.


akan wann abun saida yay kwana biyu baya mata magana abun sosai yay mata zafi...


bayan komi ya lafa su ayaanna angama secondry tunda ibaad ya tafi saudaya ta samesa awaya sukayi hira me tsawo har yau bata sake jinshi, bappa zaidu ma sao yazo yay tafiyan shima haryau dai basu dawo ba gashi anata shirin bikim nan saura kwana goma sha biyu ya rage musu kacal


bayan komi ya lafa ranar wednesday tsakiyar sati amarya zainab arifah ta dawo gida ita da babanta da babban aminiyarta nala sabida su shirya ma biki atare., her weding dress wanda zata saka shi a ranar daurin aure nd everything komi is on the processs week din auren zaa kawo mata komi.


already kayan da suka siya kuma acan kasar wajen suka bari masu aiki zasu jera mata su a new closet na agidan mijinta a UK


nan shirin aure kawai sukeyi, she still on her drugs amma tuni ta katse shan kwaya mai bugarwa dan iyayenta su tabbata lafyarta kalau, kowani dabian banza duk ta rage, dan kar ace bata hankli har yanzu wani abu ya kawo cikas ma aurenta she is still deeply scared maganam rukky

tana Allah Allah ayi auren ya wuce kar maganan rukky na cewa bazata aure ibaad ba ya zamo gaskiya..



bayan dawowartan ne garin kuskus hajiya hamida tajiyo wayar da prof yakeyi a falo da mamansa, yasata a handfree yanamai jadadda mata cewa ya gayyaci manyan mutane dan Allah kar azo a kunyatashi kuma wallh inhar ibaad ya saɓa dokokinsa ya kara cutar masa yarsa zai musu haukan da basu taba gani ba, mita ya dinga mata yana gaya mata uban kudin daya kashe wajen jinyar zainab yace ai likita yace yanxu abu kadan ne zao iya dawowa mata sa ciwo dan haka dole ne ibaad din yay hakuro su zauna har sai hanklinta ya dawo jikinta kafin duk wani abunda zai biyo baya yabiyo baya...


she have no choice face ta gaya masa toh de auren nan bana yarsa shikadai bane kaninsa karamin ma zai kara mata duk kuma a llco daya zaayi auren gabaki daya. yace shi bai damu ba kawai de lafyar yarsace damuwrta kar sake ayi wani drama da zai maida jinyar zainab baya musmn ma da likitoci suka yi gargadin bata gama warwarwa ba. shikansa baisan zainab din bane ta biya aka harhada masa wnn report din dan ya matsa ayi komi cikin sauki..



hajiya hamida najin hirar tazo ta samesa sukay maganganun banzansu akan auren uncle mohd dinsuka gama,


 prof yace ai duk zuciyar kuruciya yan uwan nasa suke dashi hakama babban yayun su marigayi mustapa yaje ya auro yar kwaila, shide haryau wnn maganan auren ammi karaman da baban ibaad din yatsaya masa a wuyarsa sosai



bayan kwana daya da wann maganan ranar friday ana gab za'a shiga week na hidiman aure anty safeera ta kira hajiya hamida akan batun waliman gida da za'ayi na kawayen hajiya hamidan a mansion din su zainab bayan daurin aure


tana yatsina tace ita 

wallah bazata iya gayyatar matan gidan su waliman zainab agidanta ba ita din kawai tazo ya isa.


anty safeera  tafara rokonta tace gaskiya bazai kyautu ace ita daya kawai zatazo waliman auren zainab ba....


hajiya hamida tace ke safeerah bari kawai na fito na gaya miki akwai wata tsinanniyar bazaura agidan nan naku mijina babu sanda za'ayi maganan gidanku bai ambace sunan ta ba kinga kuwa maganin bari karma afara



wani irin tuntsirewa da dariya anty safeera tay tace haba  haba anty hamida meyayi zafii? to wallh ki ma kwantar da hanklinki bappa zaidu yariga yay marking territorynsa kuma ma soyayya sukey auren ne kawai baiyu ba da anjima da yi bakiga shiyasa basa jituwa da ammi babba ba


hajya hamida tace what ever..kawai dai bazata kara zuwa min gida na bane..kinsan ai dama zayyan da zaid yan biyune mai yuwa suna da abun maitarsu na son abu daya, gara na datse tun yanxu shi mijina yana gane cewa yana son abu toh wallah sai ya samu koda kuwa kashe dan uwansa zaiyin


anty safeera ta kyabe baki tace toh ba damuwa anty hamida i understand nima ai bazanso amiki kishiya ba


hajyy hamida tace hmm shine ke kika bari za'a miki kwanan nan? wallh safeera kin ban mamaki da kyanki da iliminki zaki zauna namiji  har ya miki kishiya kuma it seems like ure even happy abt it..ni banga alaman kinma damu ba ,ke ko irin kishin matan nan baki dashi


kirjin anty safeera ma bugawa  tara tara tace tsaya anty hamida bangane za'a min kishiya ba..ni din?? anya kinji da kyau kuwa..ni wallh mijina bai taba mafarkin zaimin kishiya ba i use to go tru his phone sumtimes baida wata budurwa ma


hajy hamida tace hmm safeera kenan, it seem like ure abt to be shocked!! nide ba abaki na zakiji gulma ba amma wallh uwar mijinki ne jiya ta gaya ma alhaj cewa aure biyu  za'a daura dana zainab dana kaninsa muhammadu


wani kalar dariyar mahaukata mai karfi anty safeera tay kafin nan ta fashe da kuka abazata batace komi ba ta katse wayar cikin sauri


hajiya hamida tay kwafa tace hmm yanxu sai ace na hada waje kenan ko???hehehe toh Allah ya raba lafiya



****

wani irin haukataccen kuka anty safeera tay for a moment in shock, dan tasan dai hajya hamida bazata taɓa mata wasa ko karya ba...saida tay kukan sosai dan shock din ya fice ajikinta snn ta share hawayenta ta fita tana jan zuciya luckly enuf tana sharoro kwana kuwa taji muryansa a daki yana kan maganan auren da wani abokinsa ta labe a bakin kofa taji yana kyakyatwa da dariya harma maganan ma anko sukeyi na abokai..


lokcin wani hajijiya ne ya fara juyi da ita dan batamasan awani duniya take yawo ba dan tay kamar bata sama bata kasa bata tsakiyar kamr a iska kawai take yawo kirjinta yay nauyi kamar an daure dutsi a haukace ta shigo dakin tana huci suna hade ido yay maza ya katse wayar ya mike tsaye yace "lafya kuwa Safeera what is dis zaki shigomin babu sallama u cud run into my private conversations


ɓari gabaki daya jikinta ya farayi maqudaan hawayen datake kkrin dannewa suka watso mata a lokaci daya akan fuskarta suka sauko baja baja tana kallonsa kamar zata kasheshi the call has already confirmed everything to her


muryanta har yana amo tace "i cud run into ur private stupid cnvrsation ko kuma wani munafurcin kake kullawa abayan ido na bansani ba


adan rude yace meye hakane kam safeerah pls what is wrong with you ne


wani dan uban mari ta daka tsalle ta watsa masa da ihuu tace "you are what is wrong with me muhammad...how dare u..how dare u ...how dare u plan ur weding behind my back, dama sau yaushe ne zaka gaya min? bai gama farfadowa daga marin ba tay wuff ta cakumo wuyarsa a borance tace sai ranar auren ne zaka tozarni a bainar jama'a sann ka gayamim cewa zaka min kishiyya. what wrong ive i ever done to you da zaka saka min da irin wann walakancin


dakyar ya fincike hannunta da karfi ya riketa muryansa na rawa rawa guilt ya gama rufeshi dan yama rasa me zaice yafara bare bare yana cewa "safeera is not what u think...i was going to tell u bansan ya zan gaya miki bane

..you knw i love u..i care about how you will feel shiyasa ban gayamiki


kara fashewa da kula tay a mugun haukace tafara cewa "so, now you care abt how i will feel..amma da banji awani waje ba wallah da bazaki gaya min ba...kai durun uwarka, inka sake cewa you care about wallah saina kasheka, banza

..munafiki kawai,, wallh i dont deseve this frm you.., ranta a mugun bace ta fara kai masa duka tana cewa wallah baka isa kayi auren nan tunda ata hanyar munafrci zaka yi..u want to embrass me...inkaga kayi auren nan it will only mean i am dead. wallah wallh ka gwada kagani..


tana gama furta haka a zuciye ta juya zata fita wanda yasan bazai wuce gidansu zata tafi yay sauri ya biyota yaga ta kama hanyar waje kusan a guje yana kkrin  jawota kukan ta saida ya ratse koina kowa ya fito a rikice ana lafya lafya...


atake jikin ammi karama yabata abunda yake faruwa tay sauri ta rikotata snn a sann ta zube ajikin ammin kusanma ba acikin hayyacinta ba sai kuka kawai take kamr zata cire ranta.


duk su ayaana suka fito saboda kuka ne me kara anty safeera takey bana kadan ba


hajy mairo tace ke kuma safeera meye haka mutuwa akayi miki ne, muhammdu waye ya mutu..badai jikana mujaheed bako? dan jiya munyi waya dashi yace zaixo bikin nan sati na gaba


da sauri kuma a rude uncle moh yace yawwa hajiya dama akan batun aurena ne taji shine take fushi batama tsaya munyi magana ba


da muryan tausayi tace ayyoh Allah sarki yo ke safira kiyi hakuri mana karki cutar da kanki da irin wann kukan

 ...karka kanki yazo yana miki ciwo auren nan ai na rufin asirin mu ne baki daya nida nace ma bazaki ce komi ba saidai kisaka albarka...yarinya ne kin riga kinsanta tun tana karama kusan ma agabanki ta girmaa yanzu fisabillah da aka kawo miki wata shegiya awaje ba gara da za'a hadaki da ayanahn ba kinga saiki riketa kmr yar cikinki...


wani irin kukan kura anty safeera tay tace ""waaaa?? ayaanahhh fa kikace hajiya..


in shock ta kalle unlce moh jikinta na kar kar tana vibrting da tsawa da ihu tace 'dama ayaanah zaka aura??...


yace safira calm down i was abt to...wani irin mari ta kai masa saida ya kusa kifewa, 


kafin ammi karama ta rikota tay kan hajiya mairo da naushi tana ihu tana cewa" munafukar tsohuwa, azzaluma wallah sai namiki dan bura uban duka dan ni ba kalar wacce zaku walaknta bane...


adaskare ayaanah ta tsaya cak tana kallonsu ana tirka tirka sd anty safeera ta riga ta kai mata naushi tsohuwa saida ta fado akasa tana ihu uncle moh yaje da gudu yana kkrin dagata


jikin ayaana yafara rawa rawa ita da safiya suka kalle juna in shock


anty safeera tana ihu tana zage zage  tana kawo naushi dakyar ammi karama ka janta sai cewa take wallah wallah inhar ayaana zaka aura saina kashe ka..baka isaka ka dawo dakin nan ba har lahira zan kai ka yau, dacan gidan ubana zanje amma tunda abun naku walakanci ne da cin fuska wallah ina nan daram sai na kashe ka, mugu kawai, munafuki daga kai har tsohuwar taka saina numa muku cewa haukata yafi taku.


ana tsaka da wannn rikicin bazata sukaji ayaanah tafadi kasa sumammiya..


da sauri ammi ta sake anty safeera tazo kan ayaanah tana girgizata ayaana ayaanah sai shiru aka fara salati


anty safeera taja wata arniyar tsaki ta haura sama ammi ta dauki ayanaa ahannu tace safiya yi sauri ko kawomin key muje asibiti .


uncle moh yay sauri yakai hajya dakin tana ta rabza kuka kmr dukantan akayi


yana fitowa yazo ya samu dede safiya ta kawo key kenan yafara kkrin kwacewa yana cewa bani keys din ni zan kaisu...


ammi karama batasan sanda ta mike jikinta na rawa ta daka masa wani irin hatsalallen tsawa ba...


ranta a mugun bace tace muhammad are u out of ur mind? wai baka ganin abunda ka jawo ne..kaje ka kashe wutar dake gabanka mana and for ur informatiom dont u ever come near this girl ya isheka haka.


hawayenta ya fara zuba tace "Dama ai abunda kuke so kenan, inbanda son zuciya ina ayanaa da zamowa matarka kaje kawai ka juya ma hajiya tunani..wallah Allah ya isa ma yarinyar nan, inba dai so kake ka cusa ma rayuwarta baqin ciki ba meye naka da auren yar cikinka kuma wanda ta taso agaban matarka wann ai baqin jini da tsana ka siya mata nide wallh karka sake kace zakazo kusa da ayaanah enuf is enuf


...tana ga firta mai hakan ta dauki ayaanah cak ta fice da ita tana kuka ta sata mota bata kira kowa ba saida ta isa asibiti


ayaanah went into nervous breakdown aka lankaya mata engine taya numfashi bata ko motsi..


ta kira layin ibaad baya shiga, ta kira bappa zaidu duk shiru har saida ta kira maheer ya dauka sann taji sanyi ahaka ma tanakan gaya masa tana kuka, hanklin sa sosai ya tashi dajin wann maganan, ya rasa yadda zaiyi yay, haka yaki gaya ma kulthum yay shiru atake atake yace mata zaizo gida akwai wani abu urgent da zaiyi.


he left malaysia by 10am bai iso kano na sai tara na dare, yazo ya samu ammi karama ce kawai anan asibiti sai safiya har ayaanahn tafarfado ta sake komawa she is still on sedatives nd oxygen


babu alamar shigar numbar bappa zaidu bare na ibaad  kuma sam sam taki ta gaya ma hajiya asibitin datake bare suzo, anan tawuni batasan me ya gudana agidan ba.


saida maheer yazo kafin taji safiya tana bada labari cewa data koma yi musu abinci taga anty safeera ta dauko wuka tabiyo uncle moh har waje kan titi tatara masa makwabata, waihar ma yace zai saketa hajia ne tace masa a'a zafin kishi ne zata sauko.


case a gidan bai kare bahar washe gari ayaanah tana farfadowa in btwn amma daga zarar taga ba mafarki takeyi ba she will faint back...


gurmi yasaka ammi babba ta dawo gidan wai tazo danna kirji ma anty safeera amma inbanda kata hura mata wutan abun babu abunda takeyi dan agidan ma takwana komi anayi a idonta


a idon hajy mairo saita nuna hakuri kawai take bayarwa amma tana komawa sashen anty safeera sai ta cigaba da xugata sosai..ranar da abun ya faru uncle moh bai iya kwana a gidansa ba sabida tsoron ransa, kusan a hotel ya kwana shima acan alhaj ameer yazo ya karasa cire masa sauran tausayi da kunya yace masa ya share safeerah borin hauka kawai takeyi zatama yi ta gaji ta bari karda ya sake ya fasa auren nan sabida haukar kishi da matarsa safeera takeyi


BOOK 1 ZAI KARE NE A PAGE 50. PLS WANDA BASA IYA KARANTA BOOK DAGA FARKO KU daure  KUNEMI PAGE ONE KU AJESHI KURKUSA DAN IN AZO CIGABAN LAST PAGE KUGANE INDA ZAMU DOSA COS I WILL HATE TO BE ANSWERING SILLY SILLY QUESTIONS IN THE FUTURE..💋❤️❤️👍 MORE LOVE!!

[16/12, 00:53] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.



⏯️4️⃣9️⃣

Tunda Alhaj Ameer ya gama zugashi ya dada cusa masa ra'ayin cewa kar yasake borin kishin da haukar da safeera take ya hanashi auren ayaanah sai kuma ya dawo gidan da sassafe da wani gigin rashin kawaici da kunya na daban, babu tausayi ko fargaban kashesa datace zatayin kuma a idonsa cos he want to stamped his leg as a man tunda yay shige da fice  ya samu hajiya mairo suka kara tattaunawa shikn kuma gidan ba a gane komi ba. 


duk wani haukar da anty safeeran zatay basa amsawa ma bare su kulata saidai su hadu suyita nuna mata cewa itace taɓabbiya bata da hankali ne shiyasa bata fahimce cewa auren da zaiyi da ayaanan na rufin asirinsu duka bane, abu tun yana kamar wasa saida sukakusa saka anty safeera xarewa, gashi tay borin har dana fitan hankali duk saida makwabta sukaji ya xamo duk sanda hajiy mairo ta fito waje sai ka samu masu gulmanta kowa yana cewa basu kyautawa safeerah ba


kusan kwana biyu ayaana tay akwance agadon asibiti both friday nd sartuday anata jinyarta wanda tunda ta farka matsanancin kuka kawai takey tana cewa ita kawai zata tafi wajen ummanta bazata iya cigaba da zama ann dasu ba, dakyar Ammi karama da su maheer suka taru mata aka rarrasheta har tazo tasamu sauki da dare ranar asabar haka aka sallamosu suka dawo gida wanda suna dawowa hajiy mairo tabar sashenta tazo wai zata duba jikinta


suna hade ido ayaanah duk tabi ta birkice ma hjyan da ihu da kuka, tun tana gaya mata magana me zafi zafi tana cewa hjya damafa baki kaunata kin tsane ni, kin tsane farin cikina inbakiso na kawai ki maidani wajen ummana na mana ai ba'ace miki dole sai kin rikeni ba.


tay borin har ta gaji ta tsuguna da gwiwarta akasa jikinta na rawa rawa tana kuka tanata rokonta, har abun tausayi tana mata magiya akan karta mata auren dole batasonshi bazata iya aurensa ba


hajiy sai bata dau abun da wani zafi ba, ai dama tasan ayaana bazata so auren dole ba iskanci da kwadayin banza ta saka aranta she expected this xct reaction shiyasa ko ajikinta kukan ayaana da maganganunta bai dameta ba.. tace ai dama ba auren so zata mata ba, auren rufin asiri ne, inma karatun ne ai zata karasa agidan mijinta barema idan badan shi muhammadun ba waye ne zai aureta ya kula da ita sosai, ayaanah tana gabar hajiya mairo zatyi kudu


..kmr da wasa it becomes da begining of misery for them agidan, dan kuwa washe garin sunday ammi babba ta zuga anty safeera tammm tace mata ayaanan ma babban munafuka ce aisun dade suna soyyaya ne a boye shiyasa ya samu bakin cewa zai kara aure da ita, snn dan rainin wayo ma anayine agabanta all this gestures nd gift,sosai kuma anty safeera ta zugu data auna duk wasu prior bhvrs dinsa akan lamrin ayaanah, da safe anty safeera taxo sashen ammi karama tawuce dakinsu direct kawai akaga ta kama kkrin yin dambe da ayaanah zata bugeta, ihun da safiya tay ne yasa ammi taxo da gudu ta kwace ayaanan a hannun ta, anty safeera ta rufe ido ta borance ta zazzagesu tasss tace musu mugye makirai harsaida ammi kraman tamata karamar hauka tace mata karta sake zuwan sashen taje taji da wawan mijinta sann ta kyalesu.


tundaga ranar ciwon ayaana yake tashi akai akai is worst enuf da bata da number ko daya acikin abokan ibaad bare ta nemeshi anan, she called yasmin da sukay exchnging lay

tace mata ai dukansu me ma ba asamunsu a waya yanxu amma in no time zasu dawo hakan yasa ayaana ta cire kullum sai tay kuka.


yau kusan kwana uku babu kwanciyar hankli agidan gashi haryau babu duriyar ibaad din bare bappa zaidu gashi yazo maheer yay iya bakin kkrin sa amma inaa everyone is just selfish musmn hjy mairo farin cikin danta da kalamn rufin asirin kawai ta sako agaba


gani take wai gata take ma ayaanah daga baya kuma duk zasu gane


maheer yazo ma baya magana da hajiya mairon, duk shirinsa da uncle moh haka wann karon ko gaisuwa yazo baya hadasu, sumtims maheer din ne ma yake zama ya katse wasu makircin ammi babba 


kansa sosai yay zafi yanata kkrin yaga ya dawo da anty safeeran cikin hayyacinta amma inaaa kusan zaman rikici da dar dar kawai akey agidan, uncle moh ya dena zuwa sashen ma kwata kwata saidai yaxo gidan da safe ya gaida uwarsa yasake fita kwata kwata yafara dauke kai memakon kaji yana fadin kalami masu dadi saidai ya fetsa maganan banza kuma sai cancikin dare yake dawowa yaxo yay bacci yama dena kula haukar safeera, ana shiga satin bikin on monday da safe maheer ya wuce malaysia....


da yamma ammi babba ta raka anty safeera sun dawo daga asibiti suka zo suka samu an jere mata akwatuna a dakin sunkai seti total of twelve boxes masu shegen tsada wai ankawo mata na fadan kishiya, haka tasaka aka kwaso kayan har waje tsakar gida ta debo kanazir ta cinna musu wuta gidan ya kara birkicewa koina ya cika da hayaki


dakyar aka kashe wutar duk anguwan saida hankli ya fara tashi, kafin ace uncle moh ya zo gidan anty safeera tama hajy mairo zagin tasss taci mata mutunci kmr bata santa ba har saida tasa hawan jininta ya kara tashi ruwa ruwa aka kaita dakinta can kafin aka samu sa'ida aka kashe wutar, da dare haka yazo yaga abunda safeera tay yayta bori har da rubuta mata saki su ammi babba da hajy mairon suka taro suka hanashi furta sakin da kyar mgnn nan yazo ya kare gida yay shiru..


cikin wnn daren ammi babba tazaunar da ita tafara analysing mata cewa mutanen nan bazasu rusuna ba snn kamar babu fa wani abunda zata musu su rusuna da batun auren nan saidai ma nata auren ya mutu a karshe


tunda ammi babba ta gaya mata wann mgn tay kukanta cikin dare taji sauki washe gari da safe tay wanka tabar gidan, har yamma bata dawo ba har sai can cikin dare, ta dawo kuma sai sukaga tay sanyi bata hauka bata bori she was soo sullen nd unpredictable snn koyaushe fuskarta a daure yakedan ko ammi babban ma bata gaya mata inda taje ba in zatay waya kumq bata sakewa wani yaji me take cewa..


a washe garin ranan tunda aka ga ta dawo daga inda taje ta dawo shiru shiru harma aka dauka tafara gajiya ne da haukar tafara rusuna zatay hakuri


tunda aka fara case din nan ranar friday ammi karama bata sake bari ayaanah ta fito koda kofar sashensu ba dan da kyar ta lallameta ta dawo hayyacinta suna zaunensu suna ibaada sallan dare da rokon Allah ya tarwatsa auren babu wanda yake sanin ya suke ciki dan ko wjen hajiya mairo bata zuwa ynx


maheer baida yadda ya iya tun kafin su fara shirin zuwa ya zaunar da kulthum ya gaya mata gaskiy cewa babanta fa yace zai aure ayaanah sai tay kmr ta fahimce auren dole ne, saidai daga baya tana kiran anty safeera sai kuma komi ya lalace, anty safiran tashiga gaya mata karya da gaskiya tace bawani auren dole  makirci ne kawai kuma da sannin ayaana za'ayi auren nan. dat night kulthum send ayaanah a very very insultive text message har ta zagi iyayenta aciki


ayaana tay kuka bana kadan ba gashi sultana taje schll field trip kaduna batama san meke faruwa ba, duk sai ta kasa kirarta awayan itama danji take kmr zasu hade mata kai su tsaneta yanxu.


daga dakinsu sai dakin ammi bata iya zuwa koina kuma haryau bata sake ganin idon uncle moh daya riga ya lalata mata rayuwarta ba, safiya ne dai take fita taje jin gulma, ita kuwa ammi babba tunda taga anty safeera tafara dauke kai babu halin kara zugata tay hauka sai tafara bin makwabta tana barbaza maganan dan akwai taga ana zagin hajy mairo da ammi karama taji dadi, dan babu kalar sharrin da batayi musu a gari dan kawai ta bata musu suna..


daga ta gaya ma wnn sai ta gaya ma wancan,haka wasu dattijan mata kuwa har shago suke zuwa sugaya ma hajy mairo baqar magana akan auren. wasu kuma su tsare anty safeera da tausayi, wasu suce mata ai ammi babba tace itace bata iya rike miji ba bata da wayo shiyasa hakan ya faru da ita. alot of gulma was circulating. anty safeera dai ta danne zucyrta na kwana biyu batace komi ba.


shirin aure yay zafi ammi karama ta makurar matsuwa taga bappa zaidu yabude wayarsa atleast koma ya dawo gida sutaimaki ayaana amma inaa gashi ran wednesday da zazzabi sosai itama ta farka tay aman jinin da hajya mairo take jira amma tsabar ta dena  kulasu agidan sai bata sanar da ita ba, safiya ce da dogon baki taje take bawa hajya duk wani update akan yadda suke ciki harma tasani, tanajin wann batun kuwa maza ta kira hajya hajara ta sanar da ita aka sake shirin komawa wajen malami kmr yadda ya fada.


wednesday yazo ya wuce ibaad da bappa zaidu duk shiru, daga can kuma kulthum ta hau fushi da cusa ma ranta tsana haka tahana maheer firrrr sake dawowa nijeriya wai lallai sai ana daf da ranar daurin aure zasu taho tazo tay supporting mamanta shide bai ce mata komi ba dan yasan ba abu bane ma sauki dolene suji zafi


dake ammi karama bataji dadi ba Ayaanah ta farka tun asuba tanajin dama dama nan ta fara aikin kitchen tay su shara, mopping, da wanke wanke tay musu breakfast ta kawo ma ammi karaman har daki ta sameta suka gaisa kafin suka karya atare kullum ammin ke yawan tursasa tanacin abinci


around 10am ammi ta shiga wanka kafin ta fito ta samu ayaanah ta gyara mata room dinta hartasaka su turare ganin jikin ayaanahn da kyau sai ammi tace toh ita zataje asbiti a duba zazzabin nan dake damunta tun jiya tace ma ayaanah karta fita taje koina suzauna kawai anan kuma in taji su anty safeera ne karta bude musu kofa bare suce zasu daketa



after like few hours wayar ayaanah yafara ringing da sauri idonta yakai kai kirjinta na bugawa da karfi da tunanin ko ibaad ne yakira dan ta tura masa sakonni sosai saidai duk basu nuna sunje ba


hannunta harna rawa rawa ta dauki wayar tana dagawa kuwa sai taga new number tay shiru tana kallon lambr kamar bazata dauka ba sai kuma ta sauke ajiyan zuciya ta dauka muryanta kasa kasa tace salam alaikum raunataccen muryan ruthy taji ya dirar mata a kunne tace hey sis na kirane inji ya jikinki ahankli ayaanah tace "jikina da sauki..kmr bazata tay mgnn ba tace "the lord is with you..ayaanah tace thanks what happen to ur real your line?? tace "actually is one of the reasons da yasa na kiraki, ta dada sauke murya kasa kasa tace hajiy tacemin amminku bata nan so i tot kafin ta dawo pls can u help me out with sumting? ayana tace mene kenan? kinsan dai an hanani fita koina ko?..cikin muryan magiya ruth tace i know aima nafiki sanin halin dakike ciki is all over the place  dan har shago ake zuwa ayi maganan aurenki ma hjya


cikin katse maganar ayaana tace okay then what do u want to ask?


dan shiru tay snn tace Ammin wankin cikine dazu wai ashe yan biyu ne acikina dayan bai fita ba so while i was working a restaurant saikuma nafara bleeding shine doc yace inje gida i need a complete bedrest to stop the bleeding ayaana wallh bana iya tsayawa ko zama sai kwanciya ji nake kmar zan mutu, kuma bani da wanda zai kai min  deliveryna nd it remain only one person pls dont say no kitaimaka min kawai kije, basu aikan zakiyi ki dawo ynxun nan it wont pass 15mint napep zai kaiki shi zai dawo dake..i will give him d location nd the package.


ayaana bata wani so ba amma dai ta basar tace amma waye ne client din? kuma a ina ne?


ruth tana wani irin murde murde cikin ciwo tace "wasu hajiyoyi su uku da sukazo biki..

kuma tun jiyan ni aka zaba na ding serving dinsu da abincin restauran din hajiya


ayaana tace okay toh shikenan saiki bar wann layin a bude karnaje suce basu sanni ba. ruth tace yeah abude yake zanma gaya musu yanxun na zakizo sai a tsaya a kofar gidan...


ayanaah batace komi ba har suka katse wayar ta shiga daki taje tadauko golden kimono ta dora akan atampar dake jikinta snn ta rufe kanta da veil din, zama tay a falon tanata kiran layin ammi karama bt netwk unreachble, ta tura mata text bata ma lura yay failing ba withn few minutes sai ga kirar ruthy tace sis kiyi sauri ki fito mai napep ya iso aikan na wajensa he knws the place sai kuje thnk u soo much kinji my lovely sis...ayaanah tace its okay, daganan ta fito gidan ya wani irin daukawa da shiru dan almost bayan azhr ne


tana isa bakin gate dinsu ta same mai keke yana jira shidayane aciki sai delivery package me kyau na abincin shagon hajiya mairo...

...sama sama suka gaisa ta shiga ta zauna batare da bata lokci ba suka kama hanya


kusan tafiyar kurmaye sukayi tay shiru tanakan trying in layin ammi karama amma sai shiru jim kadan taga tafiya ya fara nisa tarasa wani anguwa zai kaita harta baya bayan gari sai tay shiru ta zuba masa ido 

sunayin nisa can taga ya tsaya agaban wani walakantaccen motel


idonta ya fito waje tace "malam har yanxu bamu iso gidan bane ya naga ka tsaya anan wajen.


atake atake kawai taga  mai napep ya sauya mata fuska yafara mata magana ihu ihu kamr dan daba yafara kkrin cire wuka yace kawai ta sauka masa akeke shi inda yaga daman tsayawa kenan.


abu kamar wasa har ya sauko ya fincikota waje ya hada harda package din ya dangwala mata agabanta tunma kafin ta rokesa ya maidata gida taga yaja keken sa a fusace ya kara da gaba


ta kalle gudu da yamma taga babu alaman mota bare machine bare kuma wani abun hawa dan sunyi nisa da gari sosai, gashi irin sabbin  anguwan nan ne da basu gama develop ba kusan motel din ne kawai yay kamar ya jima fentinsa green ya kokke.


ranta sosai ya dagule ya baci gashi babu wulgawar dabba bare mutum koina yay shiru ga zafin rana, tana tsaye acikin tsakar ranan gabanta yanata faduwa sosai bata motsi daga titin ba tadinga danna kira ma layin ruth farko taji shiru ta dauka netwk ne sai tayta gwadawa dakyar ya shiga sau biyu ba a dauka ba ta tura mata text taga shima yay failing, ta bar text din tacigaba da kira tafara jin user busy atakaice ta kira ruthy yakai sau talatin amma abu daya ake cewa. 


tun ranta na bace harta fara jin fargaba sosai, jim kadan tafara tunanin daukar abincin ta kara da gaba koda zata samu abun hawa ya maidata gda, ta dauka package din kenan taji muryan security man na motel din 

yace hajiya kece zaki kawo sakon abinci ko?? tace excuse me?? sai taji kuma ya kira sunan shagon hajy mairo tace ohh yess nice...quiet jovial ya karaso kusa da ita yace ayyaa sorry fa anbarki arana, let me take it frm here. batace komi ba ta daga package din zata bashi aikuwa tana mika masa memakon taga ya rike aikan sai taga ya fixgota within scnds ya danna mata wani farin hanky a baki ta suma...


daga nan bata sake gane inda take ba sai after 2 hrs data farka taganta awani daki mai bala'in duhu babu komi data rasa ajikinta face dankwalinta da gyalen kimononta, wani irin tsoraccen kuka ta fashe dashi ahnkli tana lalume har ta taba jakarta da wayarta ta jawosu da sauri sauri kuma a mugun tsorace ta kunna torch sosai ta sauke wata balaman ajiyam zuciya dataga ita daya ne sai kuma ta mike ta nemi switch ta kunna wuta


wajen is soo fucking dirty nd littered ga kwalaben giya, taba, condoms, all over ji tay kanta na juyawa a mugun  rikice ta fara kuka tana dudduba jikinta da tunanin ko raping inta akayi sai kuma taga ba'a mata komi ba..Banda wann dankwalin da aka cire mata her body was intact ga kuma kwanukan abincin data kawo ancicci an yi baja baja dashi awajen like kmr mutane dayawa ne anan and the bed was messed up ga empty bottles nd cans na kayan maye kowani irin an shassha an zubar


tanata kuka a rikice ta tattara jakarta da wayarta ta rungumosu a kirji tay bakin kofa kafafunta har na hardewa tanajin jiri jiri tsabar tsoro 


karkarwa takeyi harta iso wani empty corridor wanda har zata saka kai taji muryoyin maza suna dariya da sauri ta koma dakin tqshiga bayin gidan ta daga kai ta kalle windonsu taga irin windon da innan ne dan fadi, jakarta da su shoes dinta ta fara sakewa waje snn ta haura tadiro kasa ahankli 


tunda ta doshi hanya bata ma san ina zaikaita ba tafiya kawai take tana yin nesa da muryan mazan cikin cin sa'a sai gata ta bullo ta bakin gate batama tsaya duba waye agate din ba ta falfala da mugun gudu tafita waje....


gudu take har saida taganta akan hanya tarwal kafin ta dena gudun kirjinta na bugawa da matsancin karfi tana kuka tafara tafiya gaba gaba sauri sauri gashi har yanxu babu wulgawr wani mutum ko abun hawa, tsabar tsoro ko sau daya bata juya baya ba, sai datay nisa sosai snn ta tsaya ajikin wani bishiya ta ciro wayrta hannun ta na rawa tafara dialng number ammi kenan taji an dafata kafada batasan sanda ta daka tsallle ta tsala ihu a tsorace taja numfashi sama kamar zata suma ba..


ba acikin hayyacinta ba kawai ji tay anriketa ana kiran sunanta da karfi ana girgizata ayaanahhhh ayaanah ayaanah its me,..dakyar ayaana ta dena salati cikin tsala ihun ta dawo cikin hayyacinta taga ma ashe ruthy ne da sauri ruthy ta rungumeta ta tana hawaye tana cewa"ohh thank LORd jesus christ we found you..i am soo sorry are u okay?


ayaanah ta tsaya cak kanta na juyawa tanata kallon ruthyn datace mata bata ko iya tsayawa a tsaye, hawaye na zuba cikin idonta ta fara matsawa baya baya da ruthyn muryanta na rawa rawa tace and How did u find me?kuka ruthyn takeyi tace naita kirar layinki bayashiga kuma naga kin jima baki kirani ba naje gidanku safiya tace min baki nan so i tracked u nd follw


tanagama rufe baki ayaaanah ta sauke mata mari mai kara

a fuska tace "Karya kikey ure lieying to me ryt no..


 daga haka suka fara heated argument me zafi zafi ruthy ta tsuguna har kasa tana kuka tace ma ayaana wallah wallh banan wajen ta aiko su ba hala dai mai keken ne yaso yai scamming inta dan yaganta kyayywa shine ya hada baki da guys dinsa...


duk wann bayanin ayaana taki ji sam ta rufe ido tace zata fada agida cewa she set her up, har ta fara tafiya a zuciye ruth tafara binta abaya tana kuka tana bata hakuri

...dakyar da wahala ayaanah ta sauko dataga concerete evidences awayar ruth na cewa eh lallai banan ta aiko su ba, ta nuna mata text na hoton adress data bawa mai keken, da voice note na hajiyon yadda suka dinga complain mai kawo musu aika batazo ba.


duk da haka dakyar da wahala ta iya shawo kan ayaanah, she came with another keke suka shiga ciki akan zasu bar wajen rashin mafita ne kawai yasaka ayaana ta shiga badon son ranta ba, har kuma suka zauna ayaana tanata baya baya da ruth, ita kuma sai hakuri take kan bata gwanin ban tausayi akan ta rufa mata asiri tunda ba'a mata komi ba dan Allah kar aji wannan maganan, ayaanah taki tace mata komi ta juya kai tana hawaye... agabanta ruth din tay ta kiraye kirayen Polisawa awaya tanata musu description na waje againts all odd saida ta nuna ma ayaana hanklinta yafi nata tashi akan abunnan daya faru , she keep begging her not say anything to anyone agidansu har sai polisawa sunje sun kama mutanen motel din tundama tasan fuskan securityn din dayay mobbing inta da hankychief


banza da ita ayaana tay duk wann bare bare da bayani da kuma kkrin neman masu mafita datakeyi awajen samarukanta polisawa ayaana bata tanka mata ba.


suna sharoro kwanan shiga cikin gari lokacin 5.30 dede wayar ayaanah yafara ringin gabanta na faduwa sosai ta dauka ammi karama ne tana dagawa kuwa sai taga ibaad.


hawaye me zafi ne ya sauka a idonta abazata, da sauri ta dauka tana tare hawayen jin sanyin sallamar daya mata yasa ta lunshe ido kowani gaisawa basuyi ba yace mata yanxu ya sauka ajirgi ya kunna wayarsa kenan yaga text inta tana ina ne ynxu?? da wata sassanyar muryan kukan tace masa tanakan hanya ne zataje gida yace toh ta sauka a round about kawai ta jirashi awajen zaizo ya dauketa ynxun nan.


..tana gama wayar tun basu karasa round abt din ba tacewa mai keken ya sauketa anan itakam.


ahnkli tashe ruthy tace "meyasa? batace mata komi ba tasauka itama ruth in tana shirin saukowa da masifa ayana tace "why dont u just leave me alone kije inda zakije kawai and pls dont call my phone everr again!!


tana fadin hakan ta kara da gaba a zuciye akabar ruthy da sakakken baki tanata bin bayanta da kallo.



cikin kyabe baki ta koma keken  tazauna aranta tace"..lallai yarinyar nan da tasan irin taimakon dana mata da bazata namin wnn attitude ba...inbadan ma naji tausayinta dan tanamin mutunci ba wallh dasaina bari su smoker suyi abunda suka daman yi da ita sai kuma inga ya zatayi da rayuwarta

..mtssss.


tana gama raya hakan aranta asalin wayarta ya fara kara ta dauka da ladabi tace "Aiki ya gamu fa alhaji the package is with us..kawai wire us the half payment aikanka kuma zai iso hannunka aranar da mukayi dakai 


dan shiru tay snn tace okay sir sai najika.., tana katse wayar kuwa alert na 2 million naira cash ya sauka a acct inta wani irin murmushi tay dan wann gabaki daya ribarta ne sauran gayun basu san dashi ba, cos she will use it to pay all her debt sa saurayinta yake binta

..in aka biyasu balance kuma sai su raba da gayu.the plan was actually rape or any sort of sexual asault amma dake she still like ayaanah sai bata bari anyi haka ba they just got some content out of her nd she made it look like a non- deliberate mob by street rascals...


Da kafa ayaana ta karasa round abt dake babu wani nisa tafiyar extra 10min ne,kuma bawai batada kudin abun hawa bane she just want to walk slowly dan ta dawo cikin hayyacinta, nutsuwarta ma ya dawo. tana tafiya ahnklo tanata tunanin duk abunda ya faru, sumtimes sai yana mata kamar brain inta yana hallucinating wani abu like she was awake nd in d middle of those guys dan hanyrnxu tana jin amon dariyarsu da muryoyunsu duka acikin kwakwalar duk tarasa meke faruwa da ita kodai tsabar tsoro ne yasata brain inta yake creating fake delusions, kafin ta isa round about dai tay kkri ta kaucar da tunanin cos tunda Allah ya sa gayun nan dai basu mata komi ba she will focus on her bigger problem at hand wato na auren uncle mohd in just 2 days time


tsayuwar minti 7 masu kyau tay awajen jim kadan saigashi nan ya karaso kan titin kusan agaban ta yay parking wata dunkulallayr bakar Audi S8 tasha bakin tinted yana rage class din suka hade ido cikin sauke ajiyan zuciya me nauyi ta bude gidan gaba wanda tun bata gama rufe kofar ba mixed emotions,intense fear da anxiety yasaka tay saurin fadowa jikin shi ta rungumesa sosai tana sauke ajiyan zuciya tana dada narke mishi ashgwabe kmr yar baby musmn dataji yay wrapping inta da strong arms dinsa ahnkli ya dora kansa akanta idonsa alumshe sosai ahnkli yace "madam yadai sai kace wanda nayi shekara biyu ban dawo ba??? kincewa komi tay tana hawaye ajikinshin ta girgiza kai ya kyabe baki da karamin murmushi me sanyi yay leaning ajikinta kadan ya jawo mata kofar ya rufesu kirif suna kallon juna yace ahh toh lets go home mana saiki gaya min what does all those texts means...adan shagwabe ta share hawayenta da sanyin murya tace mishi toh, da ita ajikinsa ya kunna motar suka fara tafiya ahankli zucyarta yay nauyi sosai tanata so ta gaya masa abunda ya sameta yanxu sai kuma taji ta kasa iyawa, cos she knew they dont have that time anymore, gara shi inya aure zainab arifah zai iya juyowa ya aureta as scnd wife ita kuma daga zarar ta aure uncle moh tasan duk wani dream dinta na zama matarsa ya wargaje kenan har abada..


yana tukasu ahankli takara sakalce mishi ajiki tana dan sauke hawaye mai sanyi duk hanklinsa nakanta yana tukin yana dan leka fuskarta yanata murmushin shagwabr duk yadauka ko rikicin rashin samunsa awayan takeso tamasa ynxu..


cikin jan aji yafara janta cikin hira specifically dan ya wanke kansa yafara mata labarin abunda yafaru acan dayasa bai kara kiranta ba, yace bayan sungama business meeting ne ciwon zucyr mahaifiyar jamal ya tashi they have to rush her into Coronary artery bypass surgery a John hopkins and fortunatly he was permited by the expert cardiologist to join the surgical procedure.. shi yana cikin wajen operation sauran abokansa kuma suna kofa suna kara ma jamal karfin giwa nd they promise each oda no distractions har sai mum din jamal ta farfado shiyasa dukan su ba'a samesu ko da awaya ba. sosai hirar yadan bata tausayi tace mishi if possble zata so tay musu gaisuwa yace mata toh amma sai ya huta sai ya hadasu. hirar da sukayi kenan har suka iso gidan bappa zaidu.


almost six suka shigo suna sauka yace mata ta shiga ciki ta samu sultana tay sallah yanzu zaizo..bata musa masa ba ta sauka dan dama Allah Allah take tay wanka ta dada duba jikinta sosai dan gabaki daya a tsorace harynxu take ranta bai gama sakewa sosai ba...


har ta haura sama zatay dakin sultana da wani irin fargaba aranta dantun bayan maganan aurenta basuyi waya ba kuma itama sultanan jiya da dare akace sun dawo daga field trip sai taga bata nemeta ba..


har takai bakin kofar sai kuma tsoron kalar fassarar da sultanan zata mata yasa tay reverse tay sauri tabar sashen ta nufi dakinsa datasan baya kullewa ta bude ahankli tashiga ciki


kimonon tafara cirewa ta aje akan gyararren gadonsa tashiga bayi da sauri ta kara kunna haske ta dudduba jikinta sosai taga ashe she is absolutely fine din snn ta kara sauke ajiyan zuciya...


ruwa ta watsa a kanta da fuskarta sosai har saida taji sanyi kafin tay tsarki ta doro alwala tazo tafara sallahn magrib tana idarwa ta dau wayarta ta kara gwada lambar ammi karama a ringing na biyu ammi ta dauka ta rasa me zata fara gaya ma ammi at first, anan ne ammin take gaya mata ai ibaad ma ya riga ya kirata tun yana hanyar shigowa gari kuma yace mata suna tare shi zai kawota gida anjima itama wani kauye suka shiga dazu da kawar hajya mairo shiyasa bata dawo gida da wuri ba., ayaanah was abit relieve tunda taji cewa ammi tasan inda take ynxu..hanklinta a dan kwance tay su ishai wanda batajima da idarwa ba saiganan ibaad din ya shigo suna hade ido da mmki yace mata meyasa bataje wajen sultanan ba...


tasowa tay daga kan sallahyan tazo inda yake jikinta a sanyaye


yanayinta yagani yace "what is wrong? bata amsa ba yace "zauna to mana muyi magana

meyasa zaki rubuta min texts cewa inbandawo ba zaki koma wajen ummanki what is wrong with you???da dan wasa a muryansa yace anmiki wani abu a gidan da bana nan?


yana gama furta hakan 

taji zafin abun na dawo mata kai ita kanta bata san sanda ta fashe masa da kuka ba...


atake ya hade ransa tare da jawota suka zauna abakim gado sai yaga jikinta na rawa rawa ta sunkuyar dakanta can can kasa sosai ta lumshe ido  tana kukan sosai.


hanklinsa atake ya fara tashi yace "kee wai meye hakane zaki sani agaba kinamin kuka did anyone hurt you..da sauri ta gyada masa kai yace and who is that? dede nan ta bude idonta ta kallesa muryanta na rawa tace "yaa, kana tafiya ranar haka kawai hajiya tazo tace wai aure zatamin kuma

..kuma..dede nan ta kara fashewa da matsanancin kuka saida ya riketa, da tsananin  rudano d fushi a muryanta tace "waifa aure zatamin da uncle muhammad.. bai jira next word inta ba yace "whaaaaat?...ke karkiy wasa dani kinaji ko..kara sautin kukan tay tace "wallah bawasa nake maka ba yaa. nan ta fara bashi labarin duk abunda ya faru bata rage masa komi ba tun yana zaune har ya miƙe tsaye atake take taga idanunsa sunyi jaaa sosai....gashi kuka take masa sosai tana cewa yaa Wallah bazan iya aurensa ba,dan Allah karki bari hakan ya faru inkuma bari zakayi ni gara na tafi wajen ummana nasan bazata tabamin auren dole ba, kuma na gaya ma hajiya banaso banasonshi but she refuse to listen to me..if not becos banason kaji haushina da na gudu tuntuni nide wallah bazan aureshi ba..


jin yadda take maganan da tashin hankli da kuka mai zafi yasa yay sauri ya dawo gefenta ya jawota jikinsa da sigar lallashi, idonsa ya mugun tara ruwa ahnkli yana shafa bayanta muryansa harna cracking like he is utterly disgusted nd angry cikin dauriya yake cewa its okay babyna ya isa haka kidena kuka 'i won't let that happen okay? kanta kamar zai fashe ta shige jikinsa tareda lara kankamesa kamr wacce zaa kwace matashi, kusan ba acikin hayyacinta ba take cewa" i can't take it. ni bazan dauki wnn qaddarar ba..i dont want to...baisan sanda zzfr hawayensa ya gangaro kasa yana sauka a fuskarsa ba maganganun ta gabaki daya suke dawo masa kai yanajin wani irin zafi kamr ana tafasa masa tsokar zuciyarsa da ruwan dalma, dakyar yay contolling angernsa can har saida ya shanye hawayen ya share snn ya tallabo fuskarta suna kallon juna ahankli yace "hey..trust me no one will take you away frm me, i promise i wll fight, if not for myself but for you kinji???

gyada masa kai tay ya jawota jikinsa ya rungumeta kadan har saida ta nitsu snn yace "can u give me a minute?? ganin yayanayin da jikinsa yake rawa rawa ahnkli yasa tace okay snn ta mike tsaye ta dauki veil din kimononta ta wuce dakin sultanan dataki 

zuwan dazu.


tsabar kukan datay gabaki daya idanunta ya kumbura tay kncking ahankli after like 3 min 

sultana ta bude suna hade ido ta sauke waya a kunnenta da mamaki tace "ayaanah? da sanyin murya da fargaba ayaana tace can i come in?? tace sure sure nan ta jawota ciki tana dada kare mata kallo hankli tashe tace what is wrong with u ya naga idonki yay jaa haka are u okay sis?? 


hawaye masu sanyi suka fara sauka a idon ayaanah suna zama abakin gadon tace how can i ever be okay sultana

...havent u heard..cikin katseta sultana tace "i did...and i wont judge you ayaanah, sabida iyakan zamana dake i know u cant do this..da muryan kuka tace"thank you sultana..wallah ina cikin tashin hanklin da ku kanku bakusan yawanshi ba..i feel like everyone hates me


ta dauki wayar tace"kiga text din da kulthum ta tura min fa..bamtaba tsammanin zatay tunanin wai inaso na aure babanta ba..kuma har tana zagin tarbiyan da iyayena sukamin?


hawaye ya ciko idon sultana tace 'kinga ayaanah tun ina camp muke magana da ita nina katse maganan nace saina dawo yanxu haka ma da ita muke waya kuma niyyata muna gamawa zan kiraki kema. u guys shud schill, we are sisterrs fa. we shudnt betray or mistrust each oda haka...ayaanah tace amma fa na dole aka lakamin maganan nan sultana, so how is this even a betrayal? i am feeling like i cant breath anymore i am all tied up...da tausayi sultana ta rike mata hannu tace ayana kulthum ko anty safera duk bazasu fahimceki yanxu ba, akwai zafi akwai kishi akwai zargi but despite all this akwai qaddara..in Allah yace uncle moh shine mijinki duk ya zamuyi


ayaana tana kuka ta kwace hannunta ta miƙe tsaye tace sultana this has nothing to do with qaddara..ba a forcing in qaddare akan mutum, wllh dashi da hajiya dukansu they are forcing this marriage on me bawani qaddara..kuma ina da wanda nakeso sultana, is bad enuf that i cant have him now, amma harga Allah bazan iya auren uncle moh ba, dan dana auresa gara kawai na mutu ko wani abu ya sameni

...jikin sultana a sanyaye ta biyo ta tsaye itama tana hawaye tace"haba ayaanah haba ayaanah pls stop saying things kamr bakida ilimin addini pls dont even think of doing to urself what anty zainab did akan yaa ibaad to trap him into marriage dan kece zakiy asarar rayuwarki duniya da lahira so pls stop it


tace sultana is not abt what choose is abt how i feel i am truly nd deeply in love with sumone else kuma narasa yadda zanyi..sultana tace nd did he know zakiy auren? a sanyaye ayaana ta gyada mata kai, suna tsaka da hakan ibaad yabude kofar yanayin yadda ya kalle ayaanah yasaka sultana tuni tagane inda ayanah ta dosa..


sounding confuse tace yaa.. ibaad..good evening ya ibaad

...adan tsime yace 'how are u doing? ahnkli tace fine yaa. ya kalle ayaanah yace "are u done?


tana share hawaye tace uhmm i will be with u in a minute

..yana sake kofar yace be fast..


...da sauri tashiga bayi ta wanke fuskarta tafito sultana ta rakota bakin kofa tariko hannunta tace ayanaa i think i might knw who ure in love with

..ayana tace ohh pls forget it kawai innaje gida zamuyi video call...


daga haka suka rabu ta tabishi a mota dats filled with hrt breaking  silent..time to time yana murza hannumta cikin nashi in a comforting way ita kuma ta sunkuyar dakanta kasa sosai tama hawaye mai sanyi tana imagining ya rayuwarta zai kasance idan babushi aciki


suna kaiwa gidan saikuwa ga uncle moh a kofa shima ya zo da babban abokinsa alhaj ameer sun gama gaida hajiya mairo kenan zai rakasa, tana ganin su harzata ki sauka a motar ibaad ya hade ransa yafito ya bude mata kofa yana kallonta yace baby muje ciki

..jikinta a sanyaye ta sauke kafarta kasa tana daga ido taga ya miƙa mata hannunsa ahnkli ta kama hannunsan har tafito ta tsaya agefensa snn ya kulle motar,hannunsu sarkafe da juna suka fara tahowa gata da bala'in iya shige masa wani irin daf daf dashi take kmr zata koma cikinsa.


suna tahowa tundaga kofa Su uncle moh din suka zuba musu ido kamar wanda zasu hadiyesu da kallo, ayaanah ta kasa daga idonta, gashi fuskar ibaad babu sauki he is wearing one all black hoodie na puma yadaura hular hoodien akan bakin facecap da white medicated glass a idonsa daya toshe dashi daga ganinsa kao kasan ba weathern mutunci yazo gidan dashi ba..


shida abokinsa suka kalle juna alhaj ameer din ya masa wani irin kallo da yay sake...


wani irin shiru harabar gidan yay su ibaad suna daf zasu kai kofa uncle moh ya kasa hakuri da karfi da kuma izza da iko a muryansa yace' "ke ayaanah kizo nan...


maimakon yaga ta juyo saiyaga ta kara tantame hannun ibaad din sosai tay kamar batajishi suka cigaba da tafiyarsu ahankli har suka shiga ciki.



da wani irin huci ya taso zai biyosu ciki alhaj ameer yace kai da Allah kyaleta, inka bisu yanxu sai ya gasa maka baqar magana. yaran ne akwaisu da rashin kunya amma kwana nawa nema ya rage ta dawo naka..u will have all the time in the world to deal with her dan ya kamata ka gyara mata zama ta dena bibiyar maza


rai abace uncle moh yace ai ba ita kadai bama harda wancan marar kunyar yaron kaga yadda ya wuce kamar ba mutane yagani ba


alhaj ameer yace jst let it go muje kawai kai meye naka na fushi ma in 2 days time fa zaka more wahalarka ajikintq   saura kuma ka karka bita ahnkli dan naga yarinya ce danya shataf ...


dariya sukay uncle moh yace ai banaji ranar akwai bacci kaima check out mana how did u see her..najima ban taba fresh nonon budurwa ba


suka kara fashewa da dariya alhaj ameer yace ai sabuwar mota ce zaka jima kana morarta kuwa ..


yace hmm toh i hope so..dan naga kanta na rawa sosai

Allah yasa in sameta a mace dan wallh inbansameta a mace ba washe gari zan saketa dan ban isa inci raguwar wani kato ba..


daga haka suka shiga mota suka fita joint insu banda hirar batsa da first nite babu abinda sukeyi...



fannin su ibaad kuwa suna shiga cikin gidan ya tura ayaanah tawuce sashen ammi karama after giving her a wa comforting hug to calm her down


yana kallo saida har ta shiga snn ya juyo kai tsaye ya wuce sashen hajiya mairo kasar wuyarsa yay mata sallama ya sameta tabaza tsokokin gasashen kaji da alhaj ameer ya kawo mata a plate ita daya tana kan ci tana jan santi


...yanayin yadda taga ya karaso ciki fuskrsa a mugun daure saida yasa taji gabanta ya mugun faduwa yana kawowa gabanta daga tsaye yasaka booth dinsa ya wani irin ture plate din gabantan gefe da wani nauin rashin mutunci akwayar idonsa saida duka abunda ke ciki ya zube 


ransa mugun harde yace "hajy wai me nakeji batun wai zaki ma ayanah auren dole agidan nan?who ask u to make dat decision..


a take idonta ya ciko da ruwa daga zaunen ta kallesa tace shine zaka wani shigo min kamar..


cikin runtse idonsa da budewa yace "Don't joke with me ni bazuwa nayi muyi musanyr yawu ba...yadda kika kulla wann shashancin haka zaki warware kona miki abunda zai dameki agidan nan...


jikinta har na rawa ta mike tsaye da masifa tana cewa aa kai fa ba ubana bane rayyanu akan me bazan ma yarinya aure ba tadau hanyar lalacewa kuma ai akwai hannunka aciki


"..cikin daka mata tsawar dayasa ta razana yace sai akace kimata auren dole? ke kika haifeta ne da zaki yanke mata wann hukuncin wazatay rayuwa dashi ke waya miki haka ko tsabar zalunci da son zuciya kike son kara nunawa duniya wanda kowa yasan kin jima kina da shi..i am sure he just selfishly asked and obliged...sabida gaki katuwar pushover ko?bakisan abunda ya dace wanda bai dace ba komi da zaibi ta kan favourn yaranki shine kawai zakiyi toh wallah wallah wann karon kam baki isa ba. i am  warning you for the last time to call this weding off this night.. 


a mugun rude ta saka masa ihu wayyo Allah na rayyanu zai min duka  muhammad muhammadu wayoo Allah kuzo ku ceceni


tana kan ihu ya jawo hannunta da karfin bacin ran dake ci a idonsa yace ki kira kowaye yazo nan ina daidai daku, kuma wallah daureki zanyi saikije can prison kigaya musu uban waye ya baki ryt kima yarinyan nan auren dole da sokon danki wanda baisan ya girma ma kuma tunda kince ke zalunci zakiyi daga ke har shidin saina daureku wallh



yana sake mata hannun ya saka kai ya fita baiko je sashen mamansa ba saboda ransa sosai yake bace, cos bayan ayaana ta fita a dakinsa dazu he called maheer on phone babu wani abunda maheer bai sanar dashi ba.


har yakai motarsa yana jin ihun hajiya mairo bai sake sanin meya faru ba ya ja motarsa ya wuce gida.


ko 2 min da fita baiy ba ihunta yasa aka cika  akanta hawaye sharbe sharbe na zuba a idonta tana ihun radadi tana cewa wayyo hannu na wayyo hannu na fatima danki yace zai kasheni,zaikaini prusona wayyo hannuna wayyooo

....kusan ba acikin hayyacinta take ihun ba duk ta razana ta gigice


ammi karama tana duba hannun kuwa taga har ya langwashe da sauri sauri ta dagata suka dunguma har dasu ayaanah aka kaita asbiti acikin daren..


ihun azaba kawai hajy take tana raki ana dubawa aka samu karyewa ashe wajen daya riken yayi.


gabaki daya hajy mairo ta dawo abar tausayi radadi yabi ya sa tafice a hayyacinta


aka kira likitan kashi

maza maza akay ciki da ita, sauran kaza da akay fero dashi safiya ta makalo suna zaune tanaci suna jiyo ihun hajy mairo aciki bataji sauki ba kuwa har saida aka mata alluran bacci bayan angama daure mata hannu


uncle moh bai dawo gidan ba ammi karama kuma bata masa magana bare ta kirasa suka dai suka kwana a asibitin duk basu samu daman magana da ibaad ba dan yana isa gida ya kashe wayarsa



washe gari friday da sassafe aka tashi da hargitsatsen case uncle moh yana jin labarin an karya masa hanuun uwarsa yazo har yana wani fuffuka wai zai je ya dake ibaad babu wanda ya kulashi


still hajy mairon ne ta hanashi dan tunda ta farfado take kuka tace masa wallh shegen karfi rayyanu yake dashi daya rike mata hannu ma ji tay kamar hannun baya jikinta karyaje aje a kashe shi ana gobe daurin aurensa kawai ya bari ai zaidu zai dawo bayan auren zasu taru suci uban rayyanu..


wuni yay yana kumburi ammi karama data fishi tsiya ko abinci bata saka safiya ta kawo a asabitin ba, goma nayi na safiya haka ta tattara yaranta suka barsa da uwarsa anan.


gobe auren anata shiri kasa kasa, wasu suna ta mamakin yadda anty safeera tay burus tay sanyi kamar ma bata gidan, da yamma liss tay girki takai ma hajy mairo ta samesu su biyu a asbitin kamr mayu

...duk sun sha mamaki da suka ganta tace  oo oo ita abinci ta kawo musu..cikin gasa musu baqar magana ta dinga cewa duk dama an tozartata bashi zai hana ta manta dutynta na matar gida ba. dacan suna dar dar kamr bazasu ci abincin ba har saida sukaga dagske ta deba a plate taci snn suma sukaci borin kunya yasaka bai iya zama ba da yamma lis ya bar anty safeera da hajy asibiti snn shi ya wuce wajen aboknsa sabida babban hotel suka kama anan zasu kwana su shiryawa gobe daurin aure gashi as early as 11:am aka saka time...



daga fannin ayaana kuwa tunda suka dawo gidan bata samu ibaad a waya ba, later later sai sukyi waya sultana

wanda sai yaune sukayi hira me tsayin da har tagaya mata cewa tanason ibaad sosai kuma tana ganin kmr shima yanasonta nd they have planed thier future life together.


bakaramin tausayinta sultana taji ba, ace wanda kakeso zai aure wata kai kuma zaa bada ka ma wani..


sanyaya mata zuciya sultana ta dingay da kalamai na ban hakuri har ta gaggaya ma ayaanam rules nd regulations din da akasa masa akan batun aurensa da zainab arifa da irin severity na ciwon brain datake dashi akansa, tana cewa ai shima bada son ransa zai aure zainab din ba dan haka kawai suyi hakuri da qaddarar da Allah ya zabar musu...


shiru ayaana tay har ta gama jinta tana share hawayenta acikin ranta tace muddin kuwa auren nan zaiyu gobe toh babu abunda zai hanata guduwa kuma bazata dawo ba har sai an warwareshi....


idan kinason cigaba da samun posting kibi shafukata 


*AREWABOOKS*

*@SURAYYAHMS*


*WATTAPAD @SURAYYAHMS*



*WASAP CHANNEL ND GROP: SAVE MY NUMBER 08060712446 TO BE ADDED*



#SURAYYAHMS

#COMEBACK SERIES

2024/2025

[16/12, 23:01] Ányà Bá’kó̄̄̄ M.: ABUNDA KE ƁOYE💫

arewabooks@surayyahm.


Book1

⏯️5️⃣0️⃣FINAL PAGE 

tunda suka gama waya da sultana ayaana ta koma bakin gado ta rafka wani uban tagumi dan kwata kwata kalman qaddara ko hakuri akan lamarin rabuwarta da ibaad baya sanyaya mata zuciyarta ko kadan


ana gobe da safe daurin aurenta for the first time ranar daya kamata ace tafi kowa zumudin gani saidai tamkar mutuwar ta haka takejin fargaban tunkararsa, she stayed up very late har wajajen 2pm nadare tana xaune tana tunani, saican data juya taga safiya har tay wani lalle dasu kitso na shagalin bikin yayanta kyabe baki tay sai taji kishi gabaki daya ya dawo mata sabuwa..


mikewa tay da sanyin jiki ta fara tattara iya kayan da zata gudun dashi adan karamin jaka within few min ta gama, da tunanin gobe zata gaya ma ibaad inda zataje inyaso inyay auren nasa saiyana zuwa inda take dan suna haduwa, harsai sun samu mafita dan tasan inhar yana sonta sosai bazai hanata kubutar da kanta gobe daga wann mummunan qaddarar ba.


har saida ta gama haɗe kayanta tass snn ta bi lafiyar gado ta kwanta bada jimawa ba bacci me nauyi ya kwasheta..


ata fannin zainab arifah kuwa gabaki daya ranar juma'an shagali guda aka mata agidansu da sunan sakun lalle da wankan amarya, hajiya hamida ta gayyato kawayenta masu kudi  its was so fun aka mata komi agidansu kamar bridal shower aka mata hoto hardasu cake cake kala kala kai komi saida akayishi na nuna kai da almubazaranci.


bakaramin dadi taji da mummynta ta dinga basu labarin matsalar gidan anty safeera ba, nothing makes zainab extremely happy kamar ji datay cewa ayaanah zatay aure, auren ma ba da saurayi ba da babba wanda yasha ruwa yake da manyan yara kuma fa wai uncle moh. kai rabonta datay dariyar mugunta har cikinta yana kulewa harma ta mance.


shagali sukayi da tushe akasaka kiɗa aka cashe hanklinta gabaki daya a kwance yake sanin cewa zata zama matar ibaad daga gobe, nd then ayaana will be out of the picture bata da sauran fargaba.


har dare suna dantse rawa ita da nala duk sai taji duniyar yamata mugun dadi suna wani irin murna tsabar farin ciki dakyar tay bacci tana jin kamar safiya bazaiy ba.


daga fannin su ammi karama kuwa tunda suka dawo gida ta shiga damuwa sosai musmn da ta kira ibaad a land line na gidan bappa zaidu ta masa fada akan abun yayi ma hajiya mairo taga yana amsa mata wani iri iri da taurin kai sai taji ranta bai mata dadi ba har takai kararsa wajen aminiyarta nurse dan tasan suna shiri da ibaad din sosai ko zata iyaji musu menene asalin matsalarsa da auren ayaanah dayake cewa bazai taba bari a daura ba sai in baya raye.



duk dama tajima da sanin relshp dinsu is special amma bata kawo soyayya bane mai zafi, har gidan anty nurse din ta turashi da yamma , bayan yaje wajentan sun jima suna magana akan auren, shikansa ya sha mamakin kansa daya iya fayyace mata irin son dayake ma ayaanahn har idonsa na tara ruwa...


memakon ya zama itace ta langwasashi sai kuma tafarajin tausayinsa sosai hakuri kawai ta bashi tace yaje sai goben da ssafe zata kira mamansa suyi maganan haka ammi karama tasha jiran jin feedback ko ganin ibaad yazo bada hjy mairo hakuri amma sai shiru..


yau ranar daurin aure jirgin asubah ya dawo da bappa zaidu daga inda yaje, dan hutun daya samu kwana biyun away d stressed he looked very healthy fresh nd handsome hasken fatarsa ya dada yauqi kamar an gogeshi da ruwan madara..


6am ya masa acikin gidansa inda da ibaad din kawai suka gaisa ibaad ya masa bayani cewa by 9am jirginsu maheer zai iso, mujaheed kuma a abuja zai sauka kafin nan ya sake daukar jirgi yazo kano dan haka su maheer zasu iya rigashi isowa..


bappa zaidu yace babu komi Allah ya kawo su lafya shima yanxu haka bacci zaiyi zuwa 9am din saboda haka kar adamesa har sai ya farka. tunda ibaad baiji bappa ya masa magn auren uncle moh ba yagane cewa baisan komi akai ba all this things were planned witout his knowlegde hmm, ahnkli yakarkada kansa shima baice komi ba dan gara yay shiru hala in bappa zaidun yaje yaji yace bazai daura auren ba maybe zasu  shiga hayyacinsu dan yasan bappa bazai taɓa bari ama kowa auren dole agidan ba.


yana daga tsaye bappa zaidun yadauki sabbin fararen manyan kaya designers masu kyau ya bawa ibaad din kamar yadda yay wa maheer a aranar aurensa, yace masa yaje dashi su zaisaka yau na daurin aurensa, ibaad ya masa godiya ya karba yaje room dinsa dan dama shi baiyi wani shirin aure ba kuma basu gayyaci kowa ba,yana kunna wayarsa yaga 

text din ayaana yana ganin cewa tana son ganinsa yaji gabansa na faduwa, rigar sanyi kawai ya dora akan doguwar wandon dake jikinsa ya dau car key ya fito a gaggauce ya nufi gida..


da sanyin safiya ya iso iska me sanyi yana kan kadawa, ana bude mashi gate banda securities da suke tsaye baici karo da kowa ba ahnkli ya kyabe baki wai duk dama yau auren mutane biyu agidan kenan amma gida yay dry tamkar kabari, sosai waje ya dauka da shiru dan ko irin hayaniyar yan uwa da masu girke girken abinci ba a gayyato ba kuma dama ammi karama ta riga ta cire hannunta akan hidima ,anty safeera kuma bata saukowa yanxu sai in xata fita. 


kusan komi da za'aci odersa kawai hajiya mairo ta saka akayi snn daga can kitchen din shagonta ake duk wani girke girke da shirye shirye agidan kam kowa baccinsa yake sha ana jiran daurij aure kafin ayi karamar home walima da budar kai tareda makwabta, the house was soo unsually quite, babu motsi babu surutu hajiya mairo sosai taji tsoron abunda ibaad zaizo ya mata shiyasa tun da tabar asibitin jiya da yamma tasa aka kaita gidan hajiya hajara takwana acan shiyasa ma familyn house babu wani uban daya tashi sassafe da sunan shirin aure.


kai tsaye ibaad ya wuce ya shiga sashen amminsa ya nabude kofar dakinsa ya tura ma ayaana text akan taxo, daga nan jefar da wayar yay akan gado, jin dakin yay dumi yasa yacire rigar sanyin jikinshi ya shiga bathrum ya wanke fuskarsa da niyyar yana fitowa zai saka plain shirt yana bude kofar kuwa saiga ayaanah itama ta shigo da sauri pjamas ne marar nauyi pink colour ajikinta riga da wando mai laushi quiet revealing amma ba sosai ba, dogon yololon sumanta mai sulbi ta sakeshi har gadon bayanta, fuskarta yay extra fresh yana wani irin glowing, tsayuwar cak yay jin tsikar jikinshi ya bala'in tashi dayaga yana iya hango dangling breast dinta tacikin rigar a saukake.


Da dan sauri ta karaso gabansa suna kallon juna idanunsa na sauyawa with speed,diso dison ruwan dake sauka akan faffadan kirjinshi takalla abazata ta hadiya yawu ahankli tace Yaa Gud morning

...yace.."morning bby u wntd to see me? ta dan makale wuya da sakaltaccen murya tace yes sai ta matso daf dashi atake yaji gabansa na bugawa hos throat went dry as she stood that close irin too close in nan,


iskan dakin gabaki daya yaji ta fara masa nauyi gabaki daya, gani yay ta shagala ta kafe faffadan fresh kirjinsa da ido tanakuma clutching pjyamas din ta da hannu kamr wacce take jin tsoron girmansan


She took a step closer so close enough da dumin numfashinta yake sauka akan bare chest dinsa yanajin dirqr dumin nimfashintan har cikin ilahirin jikinsa untill His own breath staterd to hitched involuntarily.


tace “yaa bazan iya jira bane nd If I waited any longer I would lose the courage to save myself. batare da ya taɓata ya saka idonsa acikin nata yace ayaanah, this isn’t easy for me either ..amma dan Allah dont do anything stupid kinji? take idonta yacika da ruwa a dan marairace tace "kawai so nake kasan zan tafi dan karkayi fushi in baka ganni ba...yadda tay maganan da muryan kuka yasa ya juya mata baya ahnkli cikin lumshe ido kafin ya kaiga budewa yaji dirar soft hands dinta akan bare backs dinsa ta tabasa very soflty saida sigar 

jikinsa ya kara tashi


kasa motsi yay cos The touch sent a sharp shiver through him,  tace yaa dan Allah ka juyo ka kalleni mana,..jikinshi a matukar muce ya juyo And it almost broke him to see the fear of loosing him in hr teary eyes. cikin sakin sakin snnyar hawaye tace“yaa I’m scared nide kawai kagayamin inna tafi zakazo kaneme ni??


tallabo fuskarta yay da hannunsa idonsa da wani irin rauni, dumin numfashinsu na gogan na juna muryansa a raunace sosai yace ayanaah i cant give u permision to run away...in wani abu yaje ya sameki fa...kinsan kuwa sai nafi kowa shiga cikin tashin hankali ko??.


hawayenta nakan zuba masa hannu ahnkli tace' i will be careful i promis..kamr zai mata kuka yace “Ayaana, cikin katsesa da sauri tace “yaa Please, tana kallon idonshi ta dada narkewa gripping his shirtless chest ta kama fatarsa da tsumayi tace I just need to know if wont be alone...


muryansa na rawa rawa ahnkli yace “kema kinsan If you leave I will follow you anywhere.” tace nd You won’t let them stop you? dada jawota kan kirjinsan yay yana sauke ajiyan zuciya cikin lumshe ido yace “I’ve already lost you once in my mind, i won’t survive losing you in this reality. cikin kukan tafara murmushi dats soft, broken, hopeful ta kara kankamesa. tareda dada resting kanta against his chest tana sauraron yadda cikin zuciyrsa take bugawa da karfin tsiya, his hrt It’s beating so fast dat is almost melting her nd turning her on at the same time..


dada susuce mishi tay akirji ta lumshe ido duminsa ya dada gaurayata, his arms finally wrapping around her waist holding her like something fragile, dukansu suka lunshe ido suna sauke ajiyan zuciya mai sanyi kuma ahnkl ahankli, gabaki daya ne ta dagula masa lissafi, but he had to control himself dan baisan inta tafi yazai kasance yau ba ji yake kamr baison hakam amma at same time yanajin what ever it takes inda zai hana auren nan to yanaso, kawai dai bazai iya gaya mata kai tsaye yabtafi ba  saboda in ita yarinya ne shi ba yaro bane some things dont need emotions they just need simple logic..


Dumi da laushin jikinta ya shagalar dashi bai san sanda yafara shafa mata ilahirin jikinta ahnkli ba, banda saukqr numfashinta baka jin komi and There was only them, holding onto love in the quiet before d storm bt somewhere beyond those walls, destiny was already shifting for them amma basu sani ba.



bude lumsashun idonsa da suka sauya kala yay yana kkrin zai dagata daga kirjinshi taki sam ta sakeshi duk tay juyi sai yaji hard nd pointy nipple dinta sun cakkeshi a kirji...muryansa a raunace kuma ahankli yace "ayaanah kinfa san abunda kikemin..


ganin bata dagashi ba hannunsa yasa ya tattaro sumanta yana shafawa har yabi ta fatar wuyanta ahankli har cikin ramin kunnenta snn yace""i dont want us to do anything stupid ryt now if not i wud have kissed u so hard.. kkrin dagowa takeyi kawai sukaji an bude kofar,..babu knocking aka shigo jin qamshin turaren wuta yasa ayaanah tay saurin komawa bayansa ta boye fuskarta akan gadon bayansa a mugun tsorace...


he stand face to face da amminshi babu riga a jikin shi tsikar jikinshi duk atashe, gashi tun dazu ta fito neman ayaana zata mata lalle dan afara shiryata da wuri bata ganta ba sai safiya ce tace mata ai tun asuba tafitta taje dakin yaya ibaad dama kuma kullum inyazo tana zuwa wajensa itama batasan me sukeyi yawan yi adakinba.


...ganin fuskar ammi adan daure yasa ya sauke idonsa kasa dan yasan masifa kawai zata masa.. very shyly yace good morning ammi, ta hararashi cikin sharesa tace 'ayaanah...i knw u're hiding back der toh kizo maza kiwuce kije dakina kijira ni awajen yanxun nan..


cikin lumshe ido da budewa ayaanah tay simi simi tabi jikinshin ta fito sarari kanta na kallon kasa tana jajjann dogon sumanta gaba danta rufe ta gaban rigar sai kuma ta kasa motsi..


baki bude ammi ta gama kare ma jikintan kallo ganin daga ita sai pjyamas dats a bit revealing tace"fantastic' dama ahaka kikafito kikazo har nan bakiji kunya ba??? kafin ayanah ta bude baki da masifa tace "zoki fita" go to my room immidietly nd wait for me der. da bala'in sauri tace yes ammi snn tay sauri sauri ta fita ammi tabita da kallo tana girgiza kai kafin ta juyo kansa tace "kai kuma na dawo kanka care to explain what is going on here..yana kkrin jawo rigar sanyinsan yace ammi is not what u think"..a dan masife tace "aranar auren naku

..waimesa kake neman jawomin abun magana ne rayyan wato kai baka gudun shaidan ko zargi just look at urselves half naked kai da zaka mata fada kaine kake nuna mata hanyar da ba daidai ba...i honestly dont like this ur relshp..


da sauri kuma amarairace yace ammi dan Allah karkice haka..ni ban mata wani abu ba..nd u knw i won't cross any limits with her


cikin katsesa da daure fuska tace 'toh nide banaso..how did u think i wll feel in wani na samesa ahaka da safiyaz rayyan ka kama kanka ka fita harkan yarinyan nan..let her focus on her weding preparation and what ever is going on btewn u two just cut it off ryt now ni banason fitina, jiya kaduba abunda kaje kay ma hjiya jiya she is ur grand mother nd u broked her hand over an argument haba rayyan wai kasheni zakayi me agidan nan??


dan shiru yayi cikin sanyin murya yace kiyi hakuri ammi

a masife tace bazan yi ba "just leave..go nd get ready for ur own wedding bana son nasake jin wani abu daga gareka. a ladabce sosai yace yess ma. snn ya dauki wayarsa zai fita tabi shi da kallo har yakai kofa tace.."wai jiya kunyi magana da antynka kuwa naga har yanxu bata kirani ba..kansa a kasa yace"zata kiraki inbata kira ba kuma zatazo da yamma ..daga nan sai ya fita.


cikin sauke ajiyan zuciya itama ta doso dakin ta samu ayaana har ta sauya kaya,tana zama tafara mata fada ta akan kartasake fita gaban namji haka kan ayaana akasa ta bata hakuri, tea kawai suka sha at 

around 8am ta kama hannunta ta zana mata jan lalle mai kyau bana gargajiya ba all this marron indian dyes sabida basu da time she need it to dry in an hour.. arund 8:30 ta gama bata both hannu da kafa snn ta gyara mata gashi ta mata turare komi da komi suna dakin har karfe 9.30 yay....


daidai ana gama mata gyaran kenan su ammi babba sultana da su kulthum sukazo gidan haka ta gaisa da kowa amma bata ko kula ayaana ba tana gama gaishar da ammi tajanye sultana suka wuce sashen anty safeerah.


ran kulthum duk a dagule da kishin sanin ayaanah zata zamo kishiyar uwarta tashiga saidai da mamaki taje room din anty safeera, tasameta taci wani irin kwalliya ta saka kankararen leshi sosai kan kulthum ya daure musmn da bata ga anty safeera ta bata wani fuska sunyi mgn ayaanah sosaii ba she jst told her she is fine, dan za'a mata kishiya bashine zaisaka ta kasa daukar wanka ba, basuyi wani dogon zama bama ta korata dakinta tare da sultana tace musu zatay waya da yan uwanta suje daki ta huta tunda karamin ciki take turawa, tunda sukaje dakin kulthum hayaniya kawai sukeyi da sultana akan ayaanah, dakyar har saida ta fayyace mata cewa ai ayana fa yaa ibaad dinsu take so kafin nan kulthum ta dan dawo hayyacnta tafara tunani..sun jima anan suna magana amma basuje wajen ayaanan ba tukunna.


Ammi babba kuma ta fita da driver a mota akan zasu dauko hajya mairo adawo da ita da agida tunda anfara taruwa


within this hours waya kawai anty safeera takeyi a daki ita kadanta tana kyakyatawa da dariya wani abun ma inta tuna saikaga tana girgiza kai dan sosai ta shirya cin uban mijinta bayan bikin nan bana kadan ba.


fannin bappa zaidu tun ana daf da zuwan su maheer din ya farka bayan angaisa da ya sallamesu shima ya fara shirinsa ahankli, shima white shadda mai kyau ya dauko zaisaka wata buggagiya mai kyalli 


10am cikawa ya zauna abkin gadonsa yana kkrin yasaka takalma akafarsa wayarrsa ya fara ringing, ganin uncle moh ne yasa ya dauka yay sallama sai yaji wani murya ne daban

 wajen yacike da hayaniya, shiru yay har suka gama snn yay gyaran murya alhaj ameer ya dawo da nitsuwarsa kan wayar suka gaisa, bappa zaidu yace ina fatan dai lafya naga ka kirani da numbersa? alhj ameer yace ahh lafya kalau dama wata yar magana ce ta taso..


 bappa zaidu ya kwantar da hanklinsa yace toh yanajinsa,..


cikin kankanin lkci alhaj ameer ya fara fayyace masa halin da ake ciki, bappa zaidu yay shiruuu da tsananin mamaki a idonsa jin wai ashe ma dan uwansa zaiyi aure yau shine shi ba'agaya masa sai da matsalar fasa daurin auren ta taso...


sai bayani alhaj ameer yake masa cikin bayanin yana dada lalata sunan ayaanah yace masa yau da safe wajajen tara aka aiko musu package na sirrikanta snn akabi aka kira uncle moh din awaya akay threathning dinsa akan kar ya sake ya aureta, tunda lkkcin kuma suka kasa dannesa sai bori yakeyi yana musu hauka shine yace akira ace yafasa auren, zasu kuma tura shaidu..


bappa zaidu yay kamar zai katse wayar kawai yace musu babu ruwansa aciki tunda badashi aka fara ba amma kuma tunda yaga anyi nisa har haka yasan dolene hajy mairo is soley behind this.. dalili daya kawai yasaka ya amsa masa ,

dayaji batun batanci da samun wasu shaidu game da mutuncin ayanah, baiy kasa a gwiwa ba yace su aiko masa komi da komi zai jirasu gida...


suna katse wayar ransa a matukar bace  ya kira hajy mairo, saidai tunda ta dauka suka fara magana fada fada basu gama ba saida sukaci kusan rabin awa, dan gabaki daya taki ta amshi laifin komi 

tace ma itace tama muhammadu tallar ayaana ya aura sabida so take ta rufa ma yarinyar asiri snn tunda jikarta ne bai isa yahanata yanke hukucinta akanta ba


har suka gama magn bata gaya masa wani kwakkwaran magana me dadi ko mei kama hankali ba saima cewa take babu ruwansa aciki ita tay ma muhmmadu abunda ya dace ne, ransa yay matukr baci yace mata toh yanxun nan zaizo gidan su hadu awajen kawai dan kuwa akwai babban matsala.


yana katse wayar aka kawo sakon tun awaje ya bude zallan picture din yagani video din kuma a wayarsa tunda yaga kalar hotonan sai baidamu ya bude vido ba kawai yay salati ya shiga cikin gida..


shirya kansa yay tsaf cikin gaggawa yataho gidan, bayan ficewr sa ne maheer da ibaad suka dawo dan su shirya anan suma.


bappa zaidu yana isa yasa aka kira masa ammi karama, kyale ayaana tay a dakin dan ta gama shiryawan dakanta, dan already dinkinta na amarya da komi da ammi ta bayar saida safen nan kawai sukejin labarin wai anje an sace kayan gabaki daya awajen tailor


to dake garin tattara wasu kayan Ayaanan jiya ammi taga red weding dress din da ibaad ya bata kawai sai ta umarceta aka tasaka shi da bori da kuka ayaana ta karba har ammi ta fita a dakin bata dena kuka ba gashi cikin su sultana babu wanda ya leko ita dayane, safiya kuma tsabar zumudin bikin yayanta already taje beauty shop agari za'a cancada mata kwalliya



gidan yay shiru koda ammi tazo falon hajiya sosai tasha mmkin ganin bappa suna gaisawa har dacan zai fara tuhumarta da fushi sai tay saurin nuna masa wayarta da yadda ta dinga nemansa sosai tun ranar da abun ya fara faruwa..


batai kasa agwiwa itama tahau gaggaya masa ababen da ya faru baya rage masa komi ba ranta a dagule hartana hawaye, wanda hakan ya bala'in shan bambam da karyan da hajya mairo ta gaya masa in favour of her son muhammad,sosai ran bappa zaidu ya hargitsa ya baci har jikinsa yana ɓari ɓari yanajin wani irin balain mamakin son zuciya da rashin hankali irinna dan uwansa muhmmad da kuma rashin girma da hajya ta nuna acan case din gabaki daya


ammi karama tagama share hawayenta kenan saiga su hajyan sun dawo, ammi babba ne agaba da katon hijabi dan kwata kwata 20 min past 10 ne kuma 11:30am sharp zaa je masallaci a dora aure wanda anriga ance tun sassafe ma manyan bakin prof suka fara hallara anata shirin daurin aure.



ganinsu datay cirko cirko ganan fatima na goge hawaye yasa taja tsaki ahnkli tabar musu falon tawuce sama domin duba uwargida safeera


tun data barsu a falon case kawai akeyi tsakanin bappa zaidu da hajya akan batun auren ayaana, wanda sai yau ammi karama ta fitar da abunda yake ranta ta gaya ma hajiya cewa tana nuna ma ayaana warayya da rashin yarda da kuma zargi snn bata tantance magana inda akan ayaanah ne kawai daukawa takeyi.. suka fara jayayya kowa na hawaye bappa zaidu har yagaji da tsoma musu baki ya zuba musu ido kawai yay shiru ya kyalesu dan sugama fitar da abunda ke ransu kafin ya fadi abunda ke tafe dashi




fannin ammi babba kuwa tunda ta shiga ta samu anty safeera babu abinda take sai cika baki da jiji da kai da gatse take cewa anty safeeran da ta nemi taimakonta da wallah yanzu takai ta wajen malami an tarwatsa auren nan,tayita cika baki tana buga kirji ma anty safeera akan cewa tsabr wayonta da kkarinta ne yasaka duk da hjya mairo tana raye haryau fatima bata isa ta shigo gidanta ba...tsabar kuri har tay sabutan baki tahau gaya ma anty safeera duk wani sirrikanta na cewa boka da ya mata aiki akansu tace har ta mutu agidan bappa zaidu baza a mata kishiya ba....


wani baqar maganan yakan cima anty safeera rai, musmn yadda ammi babba take mata kallon yar yarinya da bata san me takeyi ba tukuna, tana mata magana kmr ta maidata abun tausayi har wani shawara take bata akan taje tay gyaran Hq sabida yanxu ne uncle moh zai fara nuna mata asalin halinsa musmn idan ya latsa na budurwa..ta dinga kushe lamarin anty safeera acikin habaici tana gaggaya mata magana kamr irin ita tagama rufe kofa tafi karfin mijinta shiyas aka kasa mata kishiya


anty safeera ta share fake hawayenta daya zuba ita dai batace komi ba tay shru tanajin ammi babba wai hartana mata tallan maganin mata na wajen zinariya




daga can kuma anata hayya hayya a falon hajiya can dataga fatima tafita gaskiya sai tafara musu rantsuwar cewa babu wanda ya isa ya hana yuwar auren nan. ita final decison dinta kenan. tafara ihu tana cewa wai duk an rainata inba haka ba ai rayyanu da safeera bazasu samu livern daga hannu su mata wani abu agidan nan ba.


ganin lokaci na tafy bappa zaisu yay gyaran murya

yace musu su nitsu su saurareshi shi ba wanm maganan bane ma ya kawosa.


bayan sun nitsun ne ya fito da hotonan ya rike a hannunsa, ya kalle hajiya anitse ya fara mata bayanin abunda uncle moh yace na cewa ya fasa auren


wanda tun bappa zaidu bai gama ba ta katsesa da ihu da bori tace sam sam laifin rayyanu ko kuma shine zaidun yaje yace ma muhmdu ya fasa shiru tay har saida tagama borinta  snn ya dauki hoton yakai har gabanta yanuna musu da  shi bai kalle video din ba ya bawa hajya suka kalla tare da ammi karama,duk jikinsu yahau rawa suka fara salati hajy ta rikito kasa ta kurma ihu tafara cewa ayaana ta tozarta....kusan wann ihun shi ya jawo hanklin ammi babba dan kuwa a falon anty safeera suka zauna suna kuma iyajin ihu akasa musmmn in yayi yawa.


a firgit ta mike da gurmi tace ke safeera bakiji hajya na ihu ba ne...cikin kyabe baki anty safeera tace "ihu kam ai dama ta saba sabida kuncacciya ce mahaukaciya in zakije kije nifa babu inda zanje ina nan, dama mujaheed kawai nake jira yazo in gansa tunda ban gayyace uban kowa awann taqadararen auren nasu ba


ammi babba tace hmm nikam dole najje toh sai na dawo...da sauri wauri ta fita ta nufi sashen hajy mairo har tana tuntuben dan kar ayi gurmi babu ita


tana fita anty safeera ta goge fake tears inta ta kwashe da dariya tace mahaukata...kadan kukaga gani..duk wanda yaci tuwo dani miya yasha..


tana daga zaune awajen jira take taji ance am fasa daurin auren kafin ta tura ma alhaji sauran balance her secret alhaj ba wani babba bane yaro ne dake mata aikin spy tun lkcin datake zargin mijinta ma shi take aikawa shago yana leka mata ayaanah yana kawo mata information...they change his name to alhaj sabida deals inta, bata so konan gaba asiri ya tonu kwata kwata a gane cewa itace ta siya deal da ruthy, tafiso a maida tunanin ga cewa wani namiji ne daban yake kkrin tona ma ayaana asiri dan ya tarwasa auren ta, alhajin ne ya kawo mata duk wani labarin rayuwar ruthy da case inta ma jim haushin ayaana da ruthyn takey abboye da tarihin gang dinsu har da bashin da ruthy take fama dasu, so she made him to do the deal on her behalf, yanxu haka ita kanta ruthy batasan cewa anty safeerah bane behind eveything duk ta dauka wani alhaj ne mai kudi.



daga falon hajya kuwa dakyar aka daga hajiy mairo akasa tana birgima tana ihu tana zagin ayaana, kowa jikinsa sai yay sanyi musn ma ammi karama da abun ya mugun daure mata kai cos ranar ayaana ai da ibaad ta dawo gida yaushe kenan har taje ta hadu da yan iskan gangs haka har tay a rayuwarta irin wnn illar?jin kamr bazata iya gane komi yasa tay shiru taja gefe tana tare hawaye...dakyar hajy mairo ta zauna akan kujera bappa zaidu ya kwace shaidun duka hannun ammi babba  

snn aka zazzauna ana zama ya hade rai ya ja musu kunne baison yaji maganan awaje, 


snn yace dole ne aji ta bakin ayaana dan haka ammi karama taje ta kirata amma kar wani acikinsu yace zai mata wani abu anan har sai angama mata tambayoyi.


hakan kuwa ya faru ammi karama taje dede ayaana ta gama bude windon ta jefar da kullin kayanta waje tana Allah Allah tajawo kujeran gaban mirror ta haura sama ta dira tafita ta backyard ta zille har ta fara jan kujerar taji ana mata kncking a mugun tsorace ta sake kujera sai taji muryan ammi karama daga kofa a raunace tace "ayaana kizo bappanku yana son ganinki nd pls be fast"..da fargaba ta amsa sabida jin kuka kuka muryan ammi datay she stood still for while, dan tasan is eida a mata adalci ko akara dulmuya ba but anyway ko an daura auren nan tariga ta gudura aranta cewa guduwa kawai zatay tunda yaa ibaad yace zaizo yanemota daga baya bata damu ba.


daukar red bridal veil din tay ta lulluba akanta tay wani irin kyau duk dama ba kwalliyar arziki ammi n ta mata ba but will the jan lalle da gyara da qamshin dake tashi ajikinta bakaramin haskawa tay acikin jan kayan ba.


cikin sanyin sallama ta shigo falon taga daga ammi babba sai ammi karama sai hajy mairo kusan bappa zaidun ne kawai ya amsa mata 


mummunan fadi gabanta yay dataga irin walaknattcen kallon da ammi babba ta mata  hajy mairo kuma ta wani dauke kai ta watsa gefe tana hawaye tana karkada kafa da tsananin fushi ayanayin jikinta


cikinsu ammi karama ne kawai bata dago kai ba amma hawayene ke zuba a idonta sosai na tausayin ayaana


kirjin ayaana na dukan tara tara ta tsuguna da ladabi ta gaishar da bappa zaidu ya amsa bayabo ba fallasa..


ganin basu da time ya fara mata bayani da tambayoyi tanajin shi tana amsawa ahnkli

she truly cant rembr anything  bayan ganin ta datay ta farka a kasa ranar, tana maganan  sai yay kamr raina musu hankli kawai takeyi hajya duk ta kara kufuluwa dataga ayaana bata amsa laifin ta ko daya ba.


kai tsaye bappa zaidu ya nuna mata shaidun jikinta da hannunta duka na rawa ta karba ta kalla tun alkcin taji kanta na juyawa bata dawo cikin hayyacinta ba har saida taji dirar kalaman bappansu na karshe...


(Recap page 1, wanda suka karanta page one basai kum nanata nan ba except akwai few abubuwan da zaku oya tsinta aciki wanda bansa acan ba) cigaban labarin nabayansa keep reading💋



Tun da ta ji kalaman Bappansu na karshe cikin lumshe ido da qarfi tasakar musu wani irin tsumammen kuka me daga hankali tareda kara cukuikuyo shararar doguwar red colour bridal veil dinta daya rufeta rass har izuwa kasa ,A hankli jikinta yake rawa rawa koinanta yadau kyarma tsaban takaici da wata iriyar matsanancin ruɗani dake famar cinta acikin ranta wanda bazata iya fasalta yawarsa ba, wasu maqudan hawaye ne kawai suka shiga gangaro mata akan fuskarta yuuu wanda daga ganinsu kasan bata shirya musu ba.


yanayinta mai cike da jin tsoro da kuma tsananin tashin hankali tadada sunkuyar dakai ayayinda take agurfane a tsakiyar babban falon 


kuka kawai take rabzawa ahankali wanda zafinsa saida yy kama da kamarna wanda zata cire ranta ta fetar wajje, cike da dauriya tadago kai jin tsananin zafin maganganun bappan nasu nadawo mata kai, babu shiri kuma dakyar tadago kai takalli ammi karama dake kusa da ita tana goge hawayen dake sauka acikin kwayar idonta tadan sunkuyar dakai da wani irin sanyin jiki babu wata alamar dai yau zata budi baki ta kareta, zuciyarta a raunace ta kalli bappan nasu da yay maganan shima fuskarsa still na hade ne tamau tamkar bakin hadari jitay bata samu kwarin gwiwar cemasa komai ba shima dan gabaki daya batasan ya zata fara fidda kanta acikin wann cakwakiyar ba, Ammi babba dake falon itama duk tabi ta tsime sai tsaki take sakewa jifa jifa dan dama ta tsani auren, babu dai wanda yace uffan acikinsu, kara runtse ido ayaanah tay sosai tadinga rabza kuka me sanyi me kuma hade da zazzafar shesheka duk ta rasa ya zatayi, can dai hannunta dake rawa rawa ya fara motsi ba acikin hayyacinta ba ta capke bakin zanin hajya data rabza uban tagumi agefen bappan nasu ta mugun tsimewa da tsananin fushi ha  idanunta sunyi jaaa zirr tanakan girgiza kafafunta a masife 


cikin rawan murya da gunjin kuka takamo hannun hajy mairo ahnkli cikin  raunateccen magiya muryanta bai fita sosai tace "Don girman Allah hajiya kicewa su bappa suy yi hakuri wallh wallah bansan komi ba banyi komi ba don Allah kice su dan saurareni ni ban san wanda yayi min haka ba..."


amugun fusace hajya mairo ta warce hannunta da wani irin fushi me tattare da buhun barkwanon masifa caraf ta mike tsaye tana cewa "Ni da Allah sakeni ki wallh haushi kike bani, wato ke har kinsan ki aje mu anan kiyita rabza mana uban rantsuwa akan karya alhalin ke din ashe babban munafukace ko Ayaanah?toh tirrr da halinki. makanki kikayi bawa mu ba dan ganan abu mun gani ido da ido me kq zakice mana kin cuce kanki, kin tozarni.. kin kuma kashe aurenki tun ba adaura shi ba. Allah ya isanmu ma irin tarbiyan da muka taru duka muka baki agidan nan nide Allah ya isa tsakanina dake muguwa kawai!wallah ko su zaidu zasu yafe miki nikam bazan taba yafe miki ba, baqar almuramura anjima ana kawomin kararki, Allah sai ya mana sharia, dan koda aka kawoki daga kauye ubanki saidai yaje har dakina yayimin zagin kaca kaca ya hadamin da mugun baki cewa zakizo gabana ki lalace a binni, wato shine kikeso ki dada tabbar masa ke asalin watsaiyace, kin zo gaban ƴayana kin zamo cikkyar marar mutunci marar kamun kai kika maida kanki yar kwaltaa abayan idanunmu yo shikenan ranar aurenki ne kika zabi ki toxartani kiji dadi ko? meye burge ki da wann rayuwan ynx uban wayema xai amince yakara aurenki a fadin duniyan nan  wayyo na shiga uku ni me tuwo Wallah baki isa ki kasheni ba wani dan uban Dukan bazata takai mata ajiki abazata tana kuka cikin raki tana cewa...


..toh wallh ki sani uwata Azumi bata tsinemin ba, kafin ki dauko mana abun kunya gwara tun wuri mu mu kunyata ki yo meya burgeki da irin wannan rayuwar ta yan iska inba samun waje ba? 


daga ita har ayanahn kuka sukeyii ganin ta kara tantameta duk dama dukanta take kanyi tanata kukan sosai kuma acikin ruɗani, bakinta har na rawa cikin kukq da magiya takecewa "Hajiya dan Allah ki saurare ni, nasan kinsan ban aikata komi ba, wallh zaki iya dubani kigani, wallah wallh wallh ban aikata abunda kuke tunanin na aikata ba.. sharri.. aka...bansan yaushe...bata karasa me zatace ba taji saukar wani dan uban saukar ginannen mari da hajya ta kai mata me mugun zafi a bqki sanda ta saketa tariqe bakin ma batasani ba.


"banace miki kiyi min shiru ba, makira kawai annamimiya duk za'a taru amiki karya ne bayan ga shaidu nan zaidu ya kawomin su kaca kaca?kece acikin bidion nan fa ayaana bayan kinsaka natara dangina da mutanen anguwa kafff, nayi shelar aurenki kina gani hakanan akayita zagina akanki, akace min naci amana, nayi son kai, har mayya sai da aka kira ni, kai meye ma ba acemin a anguwan nan ba? haka naruntse idona kyam sabida aurenki da yaron nan rufin asirine agaremu baki daya amma dan tsabr rashin sanin darajar kai saida kika kekeshe idonki kika tozarmu "Ayaanah.. ni menayi miki?...toh wallah wallah baki isa ki dora min hawan jini ba, muna da yadda zamuy dake inke ban isa dake ba ai akwai wanda na isa dasu agidan nan, ki tashi ki bace min ana kar na tattaki nakaiki har lahira.


Ayaanah ta mike jiki babu kwari duhu duhu take gani agabanta har ta fita a falon tana kuka sosai kamar ranta zai fita..


direct dakinta ta nufa don tasan komei xata ce anan babu wanda zai saurareta ders too much evidence dat are pointing againts her which she knew nothing about, bayan tashiga daki kan gadonta tanufa tana rabza kuka sosai ayayinda kanta da kirjinta ke bugawa dan harga Allah batasan wani irin hukunci kuma za'a yanke mata ba.


bayan wucewar ayaanah daki hajya mairo tana kan kuka ta kalle bappan zaidu tace "yau naga ikon Allah Zaidu. dan Allah ayaga hotonan nan bideon ma duk agoge kaji? sann ayi maza arabata da wayann mutanen banzan datake bibiya, banason wani a dangi ma yasake jin labari bare ganin shaidun nan.  


tun be amsa ba ta dada rushewa da wani kukan kmr an bugeta, "Allah mun gode maka, wai sai ka haifi ɗa amma baka haifi halinsa ba wallah mahaifyar ayaanah mutuniyar kirki ce yanxu meye wannan take so maqiya na suce akaina kenan..


cikin sauke ajiyan zuciya bappan nasu yace Ahtoh nide nagaya muku hajiya  Auren ayaanah dai ya fasu, sun kirani yace ya fasa bazai aureta ba, snn shine ma ya tura min wann shaidojin ga kuma jama'a sun taro dama sai an daura auren ayaanahn ne kafin agabatar da na su zainab Arifah, ni duk rasa mafita yanxu kam ai jin kunyan mutane ne kawai ya rage mana saidai in....


wani caraf Ammi babba ta capke maganan abakinsa tanamai cewa 'a'a, yaa Zaidu tsaya, ai magana kam ya riga ya kare tunda auren ayanah ya fasu me kuma zamuyi ai kawai afito fili kawai aje a bayyana masu kawu babba komi kar abata musu lokaci kasan yadda yaci buri akan auren yarsa zainab Arifah yatara manyn mutane kar abata musu lokci akan aikin banza. hhmm ayyuriri dama anbar yarinya tana abunda tagama dama kam ai babu wani abun da za'a samu a karshen rayuwrta face jin kunya, kuma ai wanda suka taru sua bude mata hanya ta lalata kantan sunsan kansu..


da gefen ido ta jefa baqar maganan ganin ammi karama bata ko dago kai ba taji wani irin dadi aranta dan dama wnn irin ranar kawai take jira na jin kunya danta gumsa musu bakin ciki. 


fade fade take inda take shiga bata nan take fita ba, ganin dai babu wanda yace mata uffan haryanxu yasa tafara daga musu hankli burinta kawai aje filin taro a fallasa komi..


hidima biyu ne ga lokaci nata tafiya inma tsoron zubda ma kawu babba kimansa akeyi, toh mezai hana kawai a tura ayanahn takoma inda tafito ace kawai guduwa tayi takoma kauyensu if not wallah kaf zuria sai munji kunya bana kadan ba dan abundai akwai zubar da kima da mutuncin manya aciki.


tunda ta fara maganar kauda kai kawai bappa zaidu yay kamar wanda baijin surutan nata ahnkli yanamai lallatsa wayarsa da alama yana rubuta wani sakone, yana gama rubuta sakon ya tura ya tabbata ya isa snn yakashe wayarsan, sai a sann ya juyo ya kalleta adan taikace amma baice mata uffan ba kawai ya girgiza kansa..nan take falon ya kuma dauka da wani irin shiru bakaramin hade rai ammi babban tay ba sabida ta tsani tay magana duk taga an shareta..


within 5 scnds karar waya yakatse shirun nasu ammi karama dake zaune shiru tana hawaye ita ta dauki wayar after uttering few words ta katse wayr snn ta kalli bappa zaidu da sanyin jiki ayayinda muryanta ke fita a cikin nitsuwa kuma ahnkli tace "yaa zaidu, Mujaheed ne yakira yace in sanar dakai cewa yaga sakonka kuma yana daf da isowa gidan nan shima yanzu". 


babu yabo babu fallasa cikin sassauto da bacin ran dake fuskansa ya kalleta cikin sauke karamin ajiyan zuciya snn ya amsata da "toh fatima Allah ya kawoshi lafiya, komi yar hakuri ce dan haka ki kwantar da hankalinki evrything will be fine. 


kanta akasa tana share kwallanta Tace mishi toh Ameen. dan kadan ya mayar mata da sanyin murmushi ita kuma tay maza ta sauke kanta kasa adan kunyace.


kallonsu ammi babban takeyi kamar zata tashi tsaye ta haɗiyesu su da mugun bugu, dan ɗan wnn calm gestures da yake yawan wakana tsakaninsu bakaramin kona mata rai yakey ba, wato itace datake matarsa na sunna ma bazai amsata ya bata hakuri ba caraf yahau amsa wannan makirar matan. satar kallonsu kawai take tana raya abubuwa masu tsauri aranta ayayinda babu abunda idonta yakey face hararar fatimar tareda jan musu kananan tsaki


share hawaye hajiya tay adede lokacin da wani gulluton baqin ciki ya kara rufe mata kirji inta tuna hotonan nan


ganin datayi kmar Ammi babba zata kara yin wani magana, nan tay marmaza cikin katseta a masife tace "haba, haba..ya isa haka mana ke kuwa Raihanatu, kinyi ta maganan nan duk anji ra'ayinki akan ayanah amma kisani nide ban aminta da gurguwar shawarar kin nan ba, yoo sai kuma aje har babban masallacin jumua ayi shela ace ma jama'ar Annabi S.A.W. cewa yarinyar nan tagudu ranar daurin aurenta sai kace muna kwapcen wasan kwaikwayo?,.. 


adan masifa ammi babban tace amma hajya kema kinsan halin kawu babba wallh bazai lamunci azo da batu daga gidanan a tozarta shi a bainar muhimman mutane ba aranar daurin aurensa yarsa zainab arifah ba.


fuskar tsohuwar ba asake ba takalle bappa tace "zaidu maganan nan fa ya kare bama sai anje ga tozarta zayyanu agaban mutanensa ba tunda abunda kuke gudu kenan, dolene kawai ayi auren Ayanaah ayau din nan, babu wata zancen guduwa ko fasa shi, tunda shi wanda ya sakar mata fuska ya mata alherin shi ta cutar ta tozarta, yau koma uban waye mukaga dama dashi za'a a daureta yau, inyaso taje can can gidansa ta karashe rayuwarta dashi inma kashe kanta zatayi a dakin miji gara tay da akanda tazauna min agabana ta cigaba da tonamin asiri tay karuwanci a birni ubanta juma nacan kauye yayimin dariya, aure kam kamar an daurashi ayau ko tanaso ko bataso


wani irin shiru wajen yakara daukawa a falon ayayinda fuskar sauran matayen looks soo soo confuse da furucin tsohuwar duk da alama basu wani gama fahimtar inda maganan tsohuwar ya dosa ba, to da waye kenan za'ayi ma ayana auren dolen? da mujaheed ne ko wani ne nadaban daga waje? saidai tun kafin dayansu ta budi baki tay tambaya bappa zaidu yakalle su duka biyun fuskarsa ba a sake ba still cikin gyaran murya yace ya kamata kubami wuri zanyi wata magana da hajiya"..



babu tantama kowaccensu suka mike tsaye cikin hadiye tambayar dake ransu snn suka fice waje.


Ammi babba nan tay sashen abty safeera  da uban sauri dan taje ta yafa mata gurmi


ammi karama nan tanufi dakin Ayaanah kai tsaye jikinta duk a sanyaye, ta iso kofar dakin Ayaanah bata sani ba, kife kai tay akan gadonta tana ta kuka me karsashi gashi ita kanta tarasa amsar da zata bawa kanta,  kanta duk ya kulle, she was like is this actually happening to her abu ne da batay tsammani ba sai gaba daya sai taji ta fice hayyacinta, she wish zata bude idonta taga mmmunan  mafarki kawai take, 


kwankwasa kofar dakin da akay da dan karfi yasa tadaga idonta da sukayi jaaa suka kumbura tana kallon kofar amma bata da niyyar tashi tabude har akagaji da Knocking aka bar wajen. 


Sai can wajen after good 40 mins data dan dawo hayyacinta tana xaune saman gadon kafin ta jawo wayarta da kyar da kamar zata bude sai taji xuciyarta ya kara rauni, MTN sim card dinta take son cirewa ta karyashi sai taga tarin missed calls din  kawar aikinta Ruthy yafi guda talatin da wasu irin zafafan text messages da ya ninka calls din daga wajen ango to be din nata, ko wani message data bude zance daya yake yi, " i once trusted you, nina miki kaza nina miki kaza lokcin baki da kaza..kinci amanata ayanah, bazan yafe miki ba.." kowani kalma da ya rubuto mata suna daukene rashin mutunci da gori, tsana da zafin cin amana da butulci dayake famr tunanin tay masa.


wasu irin raunattun hawaye suka shiga bin kuncinta bawai dan zafin words dinsa ba sai gani datay wai har ya aminta da komi dayagani akanta kai tsaye, dan tay tunani in akwai wani wanda zai iya bada kwararren shaida mai kyau akan iliminta da tarbiyanta da shine mutum na farko da zai bayar, ita ko kadan batay tsmmanin cewa ya jima yana zargi da kallon ta a matsayin wance tasan maza ba ashe shaida kawai yake jira dama


 fita tayi daga Inbox din hawaye me zafi na sauka a idonta, ta bude WhatsApp shi ma dai duk messages din ne har da gori masu zafi aciki, gashi shidin ba yaro bane bare tace ko yana furta kalaman nan ne da gigin yaranta wai yau namijin da ake ikirarin zai aureta ya rufa mata asirin kenan yake kirarta watsatsiya karuwa hmmm.


kirijnta taji kamar sai fashe badon fasawar auren na sao dan zafin kazafi da bata suna, Kashe wayar kawai tayi ta ciro sim card din ta karyashi into 2 pieces kamar yanda tayi niyya snn tajefar da wayar can can saman gado tana goge hawayen da ya ki tsaya mata, sam batay tsammanin haka kwakwalar maza ke aiki akan zargi ba dan wasu tsauraran maganganun nasa ya mugun tsaya mata a zuciya.


Knocking din kofa aka sake yi, ta kalli kofar sai kuma tamike a hankali ta nufi kofar ta budeshi ahankli, ammi karama ta gani tsaye suna hade ido nan da nan wasu sabbin hawayen suka ciko idonta tabi ta sunkuyar dakanta kasa cikin sanyin jiki


ammi ta shigo dakin ta kulle kofar ayaanah ta bi ta da kallo harta nemi waje ta xauna agefen gado snn ta karasa inda take ta durkusa kasa cikin sanyin murya me tafe da hawaye tace "Ammi don girman Allah kiyi hakuri, nasan kema zakice na tozarki wallah bansan komi akan wann abun ba.


ammi ta sauke wani ajiyar xuciya ahnkli cikin nitsuwa tace "Ayaanah i am not  here to judge you, bare ma ai an riga anyanke miki hukunci auren nan naki bazai fasu ba, su hjiya sunce za'a daurasa a yau, kuma tun da har bappanku ya amince da wann hukuncin da hajiya ta yanke miki kema kinsan babu me ja da wannan hukunci nasu ke dai naki addu'a, nima ina nan ina taya ki da shi.. 


wani irin numfashi me karfi ayaanah taja abazata wasu sabbin hawayen da bata san dasu ba suka cigaba da sauka mata yuuu amma batace komi ba


cikin lallami ammi karama tace is okay kiy hakuri ayaanah snn kisani nobody is perfect but as long as we learn from our mistake ai shikenen, dan Allah ki kwantar da hankalinki kinji everything will be alright kuma koma waye ya aikata maki haka sai dai mu ce Allah ya isa miki da ya janyo miki wnn masifar harda kuma auren dole da wanda ba musani bama tukuna.


a mugun mugun rikice Ayaanah tadan mike tsaye is like sai yanxu kunnenta ya farajin batun wani auren dolen da ammi ta ambata..


atake jikinta sai ya fara rawa cikin dafe kirji tare da sakin birkitacen kuka me tafe da rudewa tace "ammi Auren dole da wani wanda baku sani ba kuma? auren dole fa kikace again Ammi? dama badashi za'a daura auren ba kuma.? 


jiki a sanyaye ammi ta dan gyada mata kai tace shikam ai yace ya fasa saidai wani to wanin ne bansan ko waye ba.


a mugun ragwabe ayaanah ta fado kasa tare da durkusowa kasa cikin kuka mai kara, tarike hannun matar tana cewa dan Allah kar ayi min haka Ammi wllh xan iya mutuwa, ammi talk to him plss ai bappa yana jin maganarki sosai, dan Allah kiyi ma hajiya magana i can explain myself wallah wallah bansan komi ba, basai sun min auren dole ba nasan zata saurareki kodan karamin lokaci su karamin i will find a way out of this.


cikin runtse ido tare da jin tsananin tausayinta matar tace nima basu gaya min komi akai ba, amma dai mujaheed is on his way. kinga tunda angon shi yace ya fasa i have no idea what they are planning to do now, ga dai su can a falo inaga by now kuma inaji kmr ma har ma an daura.  i am very sorry dear, kisani cewa I trust you. but i think wann ne kawai mafita agaremu duka gwara amiki auren kawai. snn koma waye suka miki auren dashi nasan dai bazai cutar dake ba Allah yasa shine miki mafi alheri.



Ayaanah ta dada rushewa da wani tsumammen kuka cikin mugun tashin hankali take cewa "Na shiga uku Ammi, yanxu baxa ki iyayin komai akai ba?auren dole fa zasu min da wanda kemafa kince baki san shi ba, ya xan yi da raina idan hakan yafaru, wallh ko ya mujaheed din ne bazan iya aurensa baa innalillahi wa inna ilaihi rajiun..."


Mikewa ammi tayi da hawaye taff idanunta da mugun tausayinta aranta tanufi kofa da sanyin jiki ta bude tana fita takulleta da keys ta waje........



*CIGABAN LABARI...*


fannin ammi babba kuwa tunda ta shiga ta samu anty safeera babu abinda take sai cika baki da jiji da kai da gatse take cewa anty safeeran da ta nemi taimakonta da wallah yanzu takai ta wajen malami an tarwatsa auren nan, tayita cika baki tana buga kirji ma anty safeera akan cewa wayonta da kkrinta ne yasaka duk da hjya mairo tana raye haryau fatima bata isa ta shigo gidanta ba...tsabar kuri har tay sabutan baki tahau gaya ma antu safeera sirrikanta na cewa bokab da ya mata aiki akansu yace har ta mutu agidan bappa zaidu baza mata kishiya ba....


wani baqar maganan yakan cima anty safeera rai, musmn yadda ammi babba take mata kallon yar yarinya da bata san me takeyi ba tukuna, tana mata magana kmr ta maidata abun tausayi har wani shawara take bata akan taje tay gyaran Hq sabida yanxu ne uncle moh zai fara nuna mata asalin halinsa musmn idan ya latsa na budurwa..ta dinga kushe lamarin anty safeera acikin habaici tana gaggaya mata magana kamr irin ita tagama rufe kofa tafi karfin mijinta shiyas aka kasa mata kishiya


anty safeera ta share hawayenta daya zuba ita dai batace komi ba tay shru tanajin ammi babba wai hartana mata tallan maganin mata na wajen zinariya



**********

kafin nan daga falon ba ajima da korar su ammi ba hajy mairo ta sako maganan wanda ya dace 'a maida auren ayaana akansa dan su ceto kansu daga tozarta 


kai tsaye tace ai anjima dace mata ibaad yasan komi game da irin abunda ayanaa take aikatawa da rayuwrta dan haka shine ya dace ya riketa inba haka ba babu wani wanda zai aureta agidan nan asamu kwanciyar hankli da rufin asiri dalilai goma da ashirin duka ta jero masa, zaka sha baqar mamakin jin cewa ashe tuntuni taawure ta gaya ma hajy mairo cewa in ayaana ta girma ta hadasu aure da ibaad


tuntuni bata tashi tuna maganan nan ba saiyau datakeso tafito kiri kiri tay weaponising dan kawai asiri ya rufu kar yaranta su tozarta.


bappa zaidu yace shifa bazai tursasa ibaad auren kowa ba har sai inshi yace yana so suna cikin maganan kuwa sai ga su maheer da ibaad sun karaso


hajya bata bari sun zauna ba ta dau waya tace driver yaje maza maza ya karasa dauko mata alhaj hamza ace masa its very urgent.


driver na tafiya magana ta dawo sabuwa, haka hajy mairo taki firrrrr bappa zaidu ya fayyace ma su ibaad dalilin fasa auren ayanaa da uncle moh sai tay sauri sauri takwace maganan gabaki daya  abakinsa tafara tuna ma ibaad alkwarinsu da taawuure

wasu maganganun da ta boye masan ba sai yau yakeji, ashe asali wa ibaad taawure ta roki alfarman hajiya cewa abashi ita ya aura inta girma


kuma hajya tana tune da wann maganan kawai dai ta kulle zuciyarta ne tay burus, dan taso ne tahanashi ayaanan kwata kwata saita aura ma wani ko muhammadu just so that she will impressed her son zayyanu akan batun zainab arifah dan su karfafa alaka dashi ,anata tunanin ai auren ibaad da arifah shime kadai zai hada kan yaranta..


she try to hide this informations in  her words amma tuni maheer da ibaad din suka gane inda ta dosa


duk sungane cewa asali ta hanashi ayaana ne dan kawai ta turasa ya aure zainab ita kuma ayaanah tunda batada amfani a famlynsu sosai saita bada ita ma wani namijin ya aura koba dan gidan su ba,toh da muhammadu ma yazo yace yanaso ma sai ta haukai ta zauna kawai.


haka ta dinga rika rikita rikitan bayani,  tace kawai rayyanu yayi musu biyayya ynxu ya aure ayaana a rufa asirin maganan nan tunda ma muhammdu ya fasa auren ayaanah ai dama tun dacan ma shi yarta taawure tay sha'awan auren ba muhammadu ba



first time da ibaad  ya zama soo speechless kenan akabarta da maheer yana dada kwaco sauran bayanai abkinta data jima tana boyewa


jim kadan saiganan magabanta ayaanan suka iso da alhaj hanza da wasu dattijai su biyu su ukunsu suka shigo palon da tarkadan test na ayaana da hajyan ta aika masu jiya.


ana zama nan ma magana ya dada  kwabewa musmm da alhaj hamza yace ai sun kira taawure tun ranar kuma tace musu ma wani mai suna ibaad hajiya tace zata aurawa ayaanah


ashe gabaki daya bata gaya musu gaskiya ba, tsoronta kar taawure taji gaskiya ta tabi bayan ibaad ahana muhamadu mata snn asa jikarta zainab a hanun rai ko mutuwa


she was just giving them countless reason na dalilin dayasa tay hakan.


don akashe maganar bappa zaidu ya girgiza kai da takaici kawai ya tambaye ibaad, snn yace masa yayi hakuri da yanayin hajiya mairo karkuma yace mata komi yanxu, nd  if he can do this kawai ayi anan agama lokaci na tafiya 11am yawuce zasu wuce daurin aurensa sa zainab...


duk da cewa ibaad ya kara shan mamakin halim hajy mairo amma bai wani ɓata lokaci ba hade da ganin darajan dattijan nan da sukazo da tunanin cewa shine mijin yarsu, sai kawai amince atake bappa zaidu ya kara sadaki akan wanda za'a bayar na zainab 5million da suka riko, aka biya na ayaana double of it das 10 million naira snn aka yi all the nesscry ladabun aure aka daura musu auren awajen sharply 


maheer da sauran dattijan suka zamo cikakun shaidu bayan an daura auren Dr Ibaad al-mansur  da ayaana jumah, maheer kuma ya dauki su alhaj hanza ya wuce dasu can masauki


bappa zaidu ya kalli ibaad dayayi shiruuu cikin rasa abunda zai yi tunani aransa, cikin jin tausayinsa yace ya tashi su tafi wajen daurin aure inyaso su mujaheed su samesu awajen tunda har yanzu bai iso ba.


sun tashi zasu wuce kenan hajiya ta wani hade rai tace zaidu ina son nayi magana dakai, kai kuma rayyanu kabamu waje.


ibaad baiko kalleta ba ya fita baisan kuma me suka tattauna aciki da bappa zaidu, kawai yana fitowa suka shiga mota basu biya masallacin kai tsaye ba saida sukaje suka dauko wasu yan uwan babansu  snn suka wuce wajen daurin auren..


waje ya cika makilll da manyan motoci da manyan masu gida yan siyasa da daidaikun sarakuna kowa ya dau wankan kece raini babu kuma kalar mota me tsada da bazaka gani awajen



kafin su shiga msallaci wajen daurin auren ne mujaheed ya iso, bappa zaidu ya tarasu agefe dukan su ukun ya gaya musu cewa hajiya ta riga ta umarceshi da ya cike wajen muhammadu shi a daura aurensa da ammi karama...


he was straight foward to them bawai neman shawara ko yarda ba he just dont want them to freak out..maheer me ya fara supporting dinsa kafn mujaheed nd ibaad was just neutral sabida kansa gabaki daya a lulle yake, he need alot of answers to the main reason da uncle moh ya fasa auren ayaana a dying minute.


bayan they are all cool with the information ma auren bappa zaidu aka shiga masallaci aka fara dana su ibaada da zainab arifah with alot of formalities na rainin hankali da kaskamci 


tunda da suka kufular da ibaad sosai dacan da 5million dim sukazo dashi zasu bayar ibaad dayaga yadda prof yake kkrin  tozarta bappa zaodu akan kudi sai ransa ya baci, danma yadada nuna masa yarsan ba komi bane sai yace shi 500k kawai zai iya bayarwa yanxu..


bakaramin rikici akay da prof akan haka ba, ibaad yaki jin maganan kowa yace wallah shi abunda zai bayar kenan, at end prof ended up paying his doter'sa dowry in dollars just to show off da sunan cewa ai shima kawun ibaad ne da rashin mutunci ibaad kuwa ya soke kudinsa a aljihu waje ya dauka da tsegumi 


prof na zaune dake yan uwan nasa ba damuwarsa bane he dint even care to notice cewa muhammadu baya nan, next akazo daura auren bappa zaidu da fatima, maheer yace sam sam zai biya hka ya biya babansa yasha mamakinsa sosai. bayan angama aure it took them along time kafin aka gama gaishe gaishe, ibaad ne kawai hanklinsa baya jikinsa

gashi prof ya takura masa yanata nunasa ma abokansa...



Daga fannin ammi karama kuwa saida tay jimm ajikin kofar tana jin kukan ayanah snn itama tashare kwallarta daya zubo mata juyawarta keda wuya suka hade ido da hajiya mairo da alama ta fito daga falon kenan ta tsaya cak tana dan share sauran kwallanta da bakin mayafi itama 


muryan ammin a sanyaye tace ahmm hajiya kardai har an daura?..


hjy me tuwo batace komi ba tagyada mata kai cike da had'iyar wani gulluton baqin ciki aranta tace eh an daura. "Fatima, dama ke nake nema, amma kafin muje can sama dakina inaso kiyi min alkwari tun anan, kar da mubi hanyar sashe na ynx wata zindikiyar magulmaciya annamimiyar mata taje ta tareki da tambaya akan auren ayanah tunda kowa leifinmu yake gani agidan nan, nide kimin alkwari ko yankaki za'ayi agidan nan bazaki taba yin kuskuren gayawa kowa cewa an daura ma ayaanah aure yanxu afalo na ba, dan wann aure na rufin asiri da sirri ne, bana bukatar uban kowa ya san dashi, kekam dai nasan bani da wata matsala dake ynxu muje saman kawai zan miki shauran bayani



kallonta ammi karama ta dingayi baki bude cikin rasa nacewa kawai tagyada mata kai snn tabita sama domin taji dalilin wnn Ɗanyen hukunci da suka yankewa Ayaanah wanda ita kanta zuciyarta acike yake da fargaban irin mijin da zasu zabar mata a wann kuraren lokaci kuma acikin fusata da fushi...



ata dayan fannin shagalin gulma babba ammi babba ta bude awajen anty safeera tana mai fayyace mata cewa anfasa auren ayaana da uncle moh asirin ayaanah na karuwanci ya bayyana


anty safeera saita ta bar ammi babba ta gama zuba snn ta fayyace mata cewa itace man tasa aka aika hoton ta raba auren...


sosai ammi babba ta shiga shock gashi babu halin tay barazanar  tona asirin anty safera itama ta riga ta tona asirinta na cewa ita tay ma ammi karama da bappa zaidu asiri...



tunda tagane cewa anty safeera is behind all this evil sai taji ta raina kanta, tsuliya a zage tabar sashen ta wuce gidanta da borin kunya

da niyyr da yamma in lkcon walima da budar kai yay zata dawo


sosai anty safeera ta kure mata tunani haka ta dinga danasanin maganganun data yi agaban safeeran dazu


 daga wajen daurin aure da kyar ibaad ya owace kansa ya dawo gida cos he is feeling restles ,abubuwa da yawa na yawo aransa, sun bar maheer  yana tare bappa zaidu suna gaisawa suna sallaman baki wasu kuma zaayi walima dasu shida mujaheed suka dawo gidan agaggauce


direct mujaheed  ya wuce sashen mamansa saboda bakaramin kewarta yay ba dan inyaje china baiya dawowa da wuri



acikin wani irin farinciki ya samesu ita da kulthum da sultana tana cikinsu sunata mamaki yadda akay aka fasa auren da ayaanah nan shima kawai sai ya jona su and the shocking news he gave them was an daura auren bappa zaidu da ammi karama, anty safeera bata san sanda ta zube kasa tana kyakyata dariya kamar zata zare ba dariya take har tana hawaye tana tuno da ammi babba da tagama cika mata baki


. .today is literally the best day of her life dariyar data dingayi yasa yaran suka tsaya da mamaki sunata kallontaa.


tsakanin hajiya mairo da ammi karama kuma maganace ta gaskiya da gaskiya ta dinke duk ta fito fili tahau gaya mata asalin dalilin dayasa taso ta bawa muhammadu ayaanah wai tay hakane dan kawai a ibaad ya nitsu ya kula da zainab arifah dan hanklin zayyanu yadawo cikin yan uwansa da danginsa ...


snn ai muhammdu zai fi kulawa da ayaanah duk ta gama bayananta ammi karama batace uffan ba, sai can tagaya ma ammi cewa amma fa yanxu zancen ya sauya haqqin tawuree ne ya kamata, tafara kuka ta dinga maganganu can dai ta fito fili tace ma ammi wai itafa ta aura ma ibaad ayaanah amma auren sirri ne sai ta nitsu zuwa anjima zata mata bayani..


itadai ammi ta saki baki tanata kallon hajiya bayan sun gama a wannan saikuma ta mairaice ma ammi ta tafara kawo mata zancen hakuri da amana dake tsakaninsu, tanata wasu abubuwan tausayi tace inhar fatima tana mata kallon uwa toh tay hakuri da hukuncin data yanke akanta ayau dan itafa tun asatin nan ta kira kawunnanta ta musu bayanin cewa ta karya sihiiri kuma ma har anturo wakili an daura aura mata aure da zaidu a masallaci...


ammi tana zaune saida ta miƙe tsaye im shock tace "aure??hajy mairo ta cigaba da ababen tausayi tace fatima kizauna kiyi tunani inka ban isa dake ba saiki gayamin in kirasu a warware auren dama zaku zauna min ne shekara da shekaru ina kallonku inde ban isa dake ba saiki gaya min


tana fadin haka tay waje tabar ammi karama acikin dakin acikin rudan...



daga bangaren ibaad kuwa yana dosowa cikin gidan baima karasa isa shashen ammi ba yaci karo da ayaana tafito da hawaye a idonta da zimman zata zille ta gudu kawai dan tay kukan tay kukan tay tunanin tarasa menene guda daya zatai..



suna hade ido da shi taji kirjinta na bugawa da karfiz tay tunanin ko har angaya masa anfasa auren, ko an nunamasa hotonan...


atake jikinta yafara rawa rawa ganin ya tsaya yana kallonta cikin bridal dress in a daskare yasa tafara ja da baya baya dan bata san meye zai yi tunani aransa game da ita ba ynxu,...


shikuma kallon ta yake da feeling na tunanin she is his wife ryt now, his first wife for that matter and she is wearing the sexy red weding dress he bought for her, for a moment ji yay kamar mafarki yake 


shagalallun idonunnsa da sukayi nisa cikin tunanin nakanta yanajin kamar yay tsalle dan farinciki matsowa yake ita kuma tana matsawa baya baya har saida ta jingina da bango snn suka tsaya suna kallon juna...hawaye masu yawa na sauka a idonta tanajin matsanancin bugun zuciya


her heart was beating soo fast tana jiran taji next word da zai fito  abakinsa, can kuma sai taga ya wani irin lumshe idonsa cikin tsumayi ya furta "alhamdullah, kafin ta dawo hayyancinta taji ya jawota jikinsa ahnkli ya daga habarta suna kallon juna baidamu da fear da confusion dake cikin kwayar idonta ba ya dago cute lips dinta ya jona danashi ahankli 


jin dumin bakinshi mai masifar dadi yasaka ta sake mishi labbanta batare da ta shirya ba



wani irin tsotse bakin yay da shauki kamr wanda zai zuko hanjin cikinta soo deep da saida taji kamr bata duniyar nan,...


sunfi minti biyar suna tsotsar bakin juna kafin nan ahnkli ya cirota ya kalleta taga yana murmushi ya share mata hawayenta yace der is no need to run away baby..ure my wife now..


wani cak ta tsaya tana kallonsa kamr an dasata saidai bataga alamam wasa a idonsa ba, kafinma tabude baki tay wani magana sai caraf sukaji muryan hajiya mairo ata bayansu..


ibaad ya kalle ayana gently yace wifyy go inside zanyi magana da hajiya kije zanzo na sameki...


kafafun ayaanah har na hardewa tsabar ta zama soo confused har ta bar wajen bata gane komi ba....


wucewarta cikin ke da wuya atake fuskar ibaad ya zanca kala gabaki daya ya zuba ma hajiya wani irin dakakken kallo snn ya wuce sashenta da sauri tabi bayansa da fargaban mezaice mata..


ALHAMDULLAHI....


WANN NE KARSHEN BOOK 1 abunda muka fada ba daidai ba Allah ya yafe mana


*...GAME BUKATAR  CIGABA DA KARANTA BOOK DIN NAN ZAI IYA SUBCRIBE BOOK 2 DINSA KUDIN KARATU IS JUST... 700Naira*  


*WE HAVE VIP TELEGRAM 2K*


*AND VIP AREWABOOK*

*@SURAYYAHMS*


*WANDA BASA DA TELEGRAM SUMIN MAGANA ZAN BUDE WATSAP GROUP*


*ALL READING FEE SHUD BE DIRECTED TO* 

👇🏻

*9132352275*

*MOHD SURAYYA SULE*

*OPAY*


*SEND UR EVIDENCE TO*. 

*08060712446 OR 09132352275*


BOOK 2 STARTS ON 22ND DECEMBER  SHARP..


DO NOT MISS THIS LOVE STORY🔥




SURAYYAHMS




Post a Comment