MUSABBABI CHAPTER 5 BY HAJ HABIBA

shi yake bukatar nasiha tare da dora shi a hanyar

Allah.

Kuma dole na so masa abinda na ke so ma kaina, domin imanin dayanmu baya cika, har sai mun soma Dan-uwanmu abinda muke so: ma kanmu. Saboda haka ki cire damuwa a zuciyarki, zan goya miki baya dari bisa dari har sai kin cimma burinki

Murmushi ya subuce a fuskar Afrah, ta kura ma. Ya Sayyadi ido, hakika kallo daya za ka yi masa, ka san yana cikin matsananciyar damuwa, âmma baya son bayyanawa. Hakika Ya Sayyadinta ya cika gwarzon maza, ya cika jarumi.

“Hakika Ya Sayyadi ban taba ganin namiji me zuciyar imani da tausayi da kuma fahimta irinka ba, tabbas ina taya kaina jaje da bakin-cikin rashin masoyi irin ka, sai dai tarihin rayuwata na san ba zai taba kammala ba, ba tare da ka shigo ciki ba, ba zan taba mantawa da kai ba har na koma ga mahaliccina.”

Ya injina kai yana Kokarin maida hawayen da ya taru masa a ido, ya ce “Babu komai Fateema, haka Allah ya tsara mana, ba kuma za mu taba yin fushi da yinsa ba, domin ya yi mana na’ imomi da yawa, don ya hanamu abu daya bai kamata mu sa damuwa ba, bayan ya fi mu sanin dalilin da ya sa ya tsara hakan. Ita ma ta sa hannu kasan nikaf dinta ta goge hawayen da ke fito mata, sannan ta.ce “Ina neman alfarma daya daga gareka Ya Sayyadi.” Ya dago ya dubeta ya ce “Wace irin alfarma ce?

” ta ce “Ina neman alfarmar ka zama yayana, wanda zan nufo shi a duk lokacin da na ke bukatar taimako, ina son ka ci-gaba da kasancewa malamina wanda zai dinga yi min nasiha a duk lokacin da zan kauce hanya, ina son ka kasance me karfafa min guiwa mashawarcina a wannan sabuwar rayuwar da zan shiga, wacce ban san daga inda zan fara ba.”

Ya Sayyadi Habib ya goge hawayen da suka ziraro masa, ya yi saurin juya bayansa, domin ko kadan baya son ta fahimci damuwarsa ta tsananta, ya ce.

“Kada ki damu, duk a yadda ki ke son na kasance miki zan kasance, na yi alkawarin zama yayanki kuma malaminki, har karshen rayuwata, duk abinda yaya yake ma kanwarsa, na yi alkawarin zan yi miki, ke ma kuma ina rokon alkawari daya daga gareki”

Afrah ta ce “Me ka ke so Ya Sayyadi?” Ya ce ba tare da ya juyo ba “Ina son ki yi min alkawarin ba za ki daina neman ilimi ba, ba kuma za ki daina koyar da dalibanki ba, za kuma ki kasance mai hakuri da juriya a cikin wannan auran naki.”Afrah ta kara goge hawayenta tace “Na yi maka alkawari Ya Sayyadi, na yi maka.’

» Daga nan

ya juya ya dúbeta ya ce “Tashi ki tafi gida.

Ta yi masa wani irin kallo mai cike da tausayawa ta ce “Na yi zaton tare za mu tafi, kamar yadda muka saba” Ya girgiza kai ya ce “Kada ki manta a yanzu matsayin yaya na ke a gunki ba masoyi ba, saboda haka ki tafi, zan taho daga baya, don kin ji an fara kiran sallar magariba.”

Ta gyada kai ta ce “To na gode, sai gobe.” Ya ce “Allah ya kai mu.” A sanyaye ta tashi ta tafi, a yayin da ya koma kan kujerar ajin ya zauna yai tagumi hannu bibiyu, komai ya tsaya masa cak! Bai taba zaton haka lamarin zai tsaya ba.

Allah ya sani ya yi, bakin-ciki na rabuwa da Afrah, domin da ita ya yi mafarkin gina rayuwarsa, zuciyarsa ta yi Kuna, ya rasa inda zai tsoma ransa ya ji dadi, yana son Afrah matuka, amma dole ya goya mata baya, domin zama cikakken masoyinta. Bayan sallar Issha’i. Mansur da Kabir sukazo amsa kiran mahaifinsu, duk suna zaune akan tabarma a kofar dakin Malam Mahmud.

Mama Hauwa na zaune akan kujera ‘yar tsugunno tana jin maganar da Malam Mahmud yake yi. “Duk Kokarina na hada Na ima da Musaddik aure, abin ya ci tura, saboda rashin samun goyon bayan mahaifiyarku.

Karshe ma Hauwa ta dauketa ta boyeta ba tare da na san inda ta kai ta ba, don haka na kiraku, domin na gaya maku Afrah ta share min hawayena,. ta amince za ta auri Dan-uwanta, shi ya sa na kiraku domin na shaida maku, na ba Musaddik Afrah, na kuma sanya ranar bikinsu uku ga sabon wata me kamawa”

Mama Hauwe ta yi karaf! Ta amshe cike da farin-ciki

*Alhamaulillahi, hankalina har ya

kwanta. Allah ya ba su zaman lafiya, yanzu ka yi magana, dama Na ‘ina ai ba ta yi dai-dai da shi ba, ita ma Afrah ta gama kinibibinta matsalarku, ni dai tunda Allah ya kubutar da ‘yata komai yayi dai-dai.”

Mansur ya kalli Kabir sannan ya dubi Malam

Mahmud ya ce “Baba amma anya ka na ganin wannan lamarin me yiwuwa ne?” Ya gyada kai ya ce “Kwarai kuwa, Mansur me ka gani?”

Mansur ya gyara zamansa yace “Baba gani nayi kamar ba’ayi mata adalci ba na hada ta aure da mutum irin Musaddik. Baba ko yanzu da zan taho nan na hadu da shi yana rangaji alamar a buge yake, gaskiya ina ganin bai kamata a hada su aure ba, domin babu ta inda suka dace, halayen Musaddik a gaskiya sun Kazanta.”

Kabir ya ce “Kwarai kuwa Baba, idan aka aura ma Afrah. Musaddik, gaskiya ba’ayi mata adalci ba, ba za ta iya zaman rayuwa da shi ba.

Baba kai ma ka san ko waye Musaddik, gaba daya aure ma bai dace da shi ba, domin babu macen da zai iya rikewa, don Allah ka janye wannan maganar.

Malam Mahmud ya numfasa ya ce “Na ji dadin yadda ku ka damu da rayuwar kanwarku, sai dai ku sani, ina da manufar hada auran Afrah da Musaddik.

Tunda kuma ta yarda ta ba ni goyon baya, babu abinda zai canja, uku ga wata zan daura auransu, idan lallai kun damu da ita, to ku tayata addu’ar Allah ya ba ta ikon cinye jarabawar daya dorata akai”

Mansur ya ce “Amma…Bai karasa ba.

Mama Hauwa ta katse shi “Kai ya isheku, ba Yarsa bace, yana da damar da zai yi duk abinda ya ga damar yi da ita, ina ruwanku”

Malam Mahmud ya yi mata wani irin kallo me cike da tsana ya ce “Ni ban sa maganar nan da ke ba, ban gayyatoki cikinta ba, don haka zai fi sauqi idan ki ka kama harkarki, ki ka fita harkar da bata shafeki ba.

Mama Hauwa ta saki tsaki ta ce “Dama ai ban ce ya shafe ni ba, ka ga wanda ya shafenin ai na. hana, na’ kuma dauke ‘yata, goben nan kuma za ta dawo gidan ubanta. Allah ya kawo mata miji na-gari, ba tambadadde irin Musaddik ba.

Ta mike ta shige dakinta, a yayin da Malam Mahmud ya dubi su Mansur cikin 6acin ran maganganun Mama Hauwa ya ce Ita kenan

maganar, kuna iya tafiya, ku gaida mutan gidan.

Allah ya ba mu alheri.

Yana gama fadin haka ya tashi ya shige dakinsa, ya bar su nan zaune suna kallon juna, daga bisani su ma suka tashi suka shiga dakin mahaifiyarsu.

Suna shiga Mama Hauwa ta hau fada “Ina ruwanku da za ku hana shi hada auran Afrah da mahaukacin dansa, can su suka sani, meye naku?

Shi ya fi kowa sanin waye Musaddik, ai kuma ita kanta wacce ku ke kokarin kwato mata ‘yancin, na yi imanin kunya za ta ba ku, don yadda na san wannan kinibabbiyar yarinyar.

To ba za ta taba kauce ma umarnin. Mallam ba, matúkar dai ya bude baki ya nemi ta auri Musaddik, to tabbas duk duniya babu wanda zai hana hakan faruwa, sai dai Allah, don haka ban ga amfanin sanya bakinku cikin wannan maganar ba. Mansur. ya kalleta ya ce “Mama rayuwar

Musaddik kullum Kara lalacewa take yi, babu wani abu burgewa ko kadan a rayuwarsa. Ko wacce ba ni da dangantaka da ita, ba zan so ta aure shi ba, domin na san rayuwarta ta gama lalacewa.

Balle jinina kanwata Mama, amma tunda ba’ a bukatar gudunmuwar shawararmu, to Allah ya sanya alheri, fitinar da ke ciki. Allah ya kare. Afrah kuma Allah ya kawo mata mafita.”Ta yi masa wani sakaran kallo ta ce “To Shehin Malami, addu’ ar taka ta yi.

.” Kabir ya ce ” Ai duk maganganunsa gaskiya ne. Allah ya sa hakan shi ya fi zama alheri”

Gaba dayansu suka tashi ba su damu da hararar da take banka masu ba, suka yi mata sai da safe, suka kama hanyar gida.

Ita ko Mama Hauwa zuciyarta cika ta yi da tsananin farin-ciki, dama ba ta taba yi ma Afrah fatan samun miji na-gari ba, burinta ya cika Afrah za ta yi auran wahala, ta yi wani busasshen murmushi, domin dukkan mafarkinta akan Afrah ya kusa tabbata.

. Ta lalubo wayanta da ke Kasan filo, ta kira lambar Na’ima, tana dauka, bayan sun gaisa ta ce

“Na’ ima ki shirya gobe ki dawo gida.” Na’ ima ta ce

“Na dawo gida Mama?” Ta ce “Eh, ki dawo gida, saboda komai ya wuce, maganar auranki da Musaddi& an maida shi kan Afrah”

Na’ ima ta ce “Mama kan Afrah, ta kuma yarda ta amince?” Mama Hauwa ta yi dariya ta ce

“Tana da zabi ne? Ai in dai akan mhaifinta ne, ba ta da zabi, duk abinda yake so shi take so, ko da ba ta so, kinibabbiya ce mai Kokarin maida kanta mara

*yanci, saboda farin-cikin mahaifinta, don haka ta yarda, duk kuma abinda zai biyo baya, wannan ruwansu, su ta shafa”

Na’ ima ta ce “Amma lallai Afrah ta shiga tara ma ba uku ba”. Mama Hauwa ta ce “Idan ana shiga dari ma, to ta shiga, auran mashayi sakarai wanda bai san darajarsa ba balle ya san darajar wani.”

Na’ ima ta ce “Lallai kam!”

“Saboda haka ki tattaro ki dawo, dama kadaicin rashinki ya dameni”Zan dawo goben

nan, kamar yadda ki ka ce Mama. Daga nan suka

yi sallama. Gida ne Katon gaske mai kyakkyawan fasali, kallo daya za ka yi masa, ka tabbatar da cewa gida ne na masu hannu da shuni, gidan Alhaji Mansur mai fata. Hajiya Kilishi na zaune akan daya daga kujerun da suka mamaye Katon falon nata, idonta ta dore akan akwatin Talabijin. Sallamar Musaddik ta sa ta kalli kofar falon ba tare da ta amsa sallamar

ba.Shi ma bai jira ta amsa ba, ya shigo lokaci daya, ya zauna yana Kokarin gaisheta, ta amsa kamar kullum ranta a bace, fuska ba walwala,

“Daga ina ka ke yau kwana biyu kenan rabon ka da gidan nan?”

Musaddik ya sosa kansa ya ce, “Daga cikin gari na ke, don wani aiki ne ya tsareni.” Ta yi masa wani kallon banza, ta ce “Aiki, har wani aiki ka ke da shi, ka na can dai yawon gantalinka, ai ba hanaka zan yi ba. Allah ya bada sa’ a

Musaddik ya numfasa, duk da baya jin dadin yadda Hajiya Kilishi take bi da shi, to fa bai hana shi yi mata biyayya tare da tsoron bacin ranta ba, bai kuma taba kallonta a matsayin mai kinsa ba, asalima tana daya daga cikin Mutanen da yake:

tsananin ganin girmansu tare da mutuncinsu.

Ya dago yana kallonta, a yayin da ta maida kallonta kan akwatin Talabijin dinta, tana fadin «Idan yunwa ce ta kawoka, ka shiga kicin ka debi abinci, don Lami ta fita balle ta kawo maka”

Ya girgiza kai ya ce “A’a a koshe na ke, magana dai na zo ma yi da ke.” Ba tare da ta kalle shi ba ta ce “‘Wace magana ce?”

Ya dan muskuta ya gyara zamansa, sannan ya ce “Magana ce mai muhimmanci akan aurena da ya taso.

” A gaggauce Hajiya Kilishi ta juyo ta kalle shi, hankalinta a tashe, kamar wacce aka gaya ma sakon mutuwa.

«Auranka?” Ta maimaita a tambayance, ya daga kansa ya ce “Eh, Kawu Mahmud shine ya ba ni ‘Yarsa Afrah, ya kuma sanya rana auran uku ga watan da zai kama, shine ya ba ni damar na zo na sanar da ke..

Ta katse shi a matukar fusace ta ce “Ka zo ka gaya min, a matsayina na wa, me na isa, sannan meye amfanin gaya min, tunda har sai da ku ka gama Kulla komai sannan aka turoka ka gaya min.

To meye amfanin gaya min?

Musaddik ya rude, a dalilin ganin bacin ranta

ya ce Don Allah ki yi hakuri Hajiya. Kada ki sa damuwa akan wannan maganar, ni kaina a kurarran lokaci aka gaya min, sannan bai dau lokaci ba ya sanya rana”. Ta sakar masa harara ta ce “A Kurarren lokaci, komai Kurewar lokaci, don me ba za ka iya zuwa ka gaya min ba?

Hmmm