Musaddik a matsayin mijin aurenta ba, shin me kaddara ta tanadar mata? Zama da mutum irin Musaddik wanda bai ma san inda rayuwarsa tasa gaba ba.
Wanda bai san yadda zai tarbiyantar da ita, ko kadan ba irin Musaddik bane mijin da take kwadayin zama a Karkashinsa. Ya Sayyadi Habib shi ne wanda ta horar ma da zuciyarta kaunarsa, ta kuma kwadaita ma kanta auransa.
Domin tana da tabbacin shine wanda zai yi mata jagora har gidan aljanna, sai dai kash! Ba ta so yadda labarin ya tsaya ba, ba ta so karshen labarin ya zama haka ba.
Domin kuwa ko ta ki ko ta so soyayyarta da
Ya Sayyadi ta zama tarihi daga lokacin da mahaifinta ya umarceta da auran Musaddik, tabbas!
Za ta yi ma mahaifinta biyayya, koda hakan. zai zama sanadiyyar fadawarta mummunar rayuwa, domin duk duniya ba ta da kamar mahaifinta.
Ba ta tunanin akwai abinda zai bukata ta yi masa, matukar tana da halin yi masa ta kasa yi, don haka za ta iya sadaukar da komai nata, domin samun farin-cikin mahaifinta, tunda Allah ya taimaketa ta samu ta yi rayuwa da shi, dole ta lallaba ta samu albarkansa, tunda Allah bai kaddari za ta yi rayuwa da mahaifiyarta ba.
Ta sa hannu ta goge hawayen da ke malala a saman kumatunta, ko kadan babu soyayyar Yaya Musaddik a tare da ita, sai dai a can karkashin zuciyarta akwai tsantsar tausayinsa, gefe daya kuma tana tausayin kanta da Ya Sayyadinta na yadda za su rabu da junansu, domin Allah bai nufa shi ne milinta ba a allon kaddararsu, ta Kara goge hawayenta.
Sannan ta yunkura ta tashi ta tura kofar dakinta, domin ta ji dadin yin kukanta, sannan ta dawo ta Kure karshen katifa ta ci-gaba da rasgar kuka, domin tana ganin hakan ne kawai zai sassauta mata radadin da take ji a cikin zuciyarta.
Haka Afrah ta kasance cikin rashin sukuni a wannan ranar, har zuwa idar da sallar, Issha’i, tun bayan idar da sallar, tana zaune akan sallaya da casbaha a hannu tana lazimi, lokaci daya ta kan yi kokarin goge hawayen da ke fita mata da daya hannun.
Tana jin dawowar mahaifinta daga masallaci, bai dade da shigowa ba, kuma ta ji sallamar Inna Halima, haka nan Afrah ta tsinci kanta cikin matsananciyar faduwar gaba.
An dau tsawon lokaci kafin ta ji muryar
Malam Mahmud, ya kwala mata kira. A daburce ta amsa da sauri, ta tashi ta aje carbin, sannan ta fice kai tsaye dakin mahaifinta ta nufa.
Mama Hauwa da ke zaune a kofar dakinta ta rakata da kallo har ta shige dakin, sannan ta saki tsaki ta tashi ta dauki kujerarta ‘yar tsugunne ta shige daki tana fadin “Halima uwar kinibibi, sai dai ya Kare kanku ba dai ‘yata ba”.
Cikin sallama Afrah ta shiga dakin, ta yi Kokarin boye dukkan damuwarta, ta nufi innda Inna Halima ke zaune, ta zauna kusa da ita. “Inna sannu da zuwa.
Ta amsa tana yi mata wani kallo me cike da kauna da tausayi, ta fara magana “Afrah ban yarda da hukuncin da mahaifinki ya yanke ba na aurar da ke ga Musaddik. Afrah ke marainiya ce, ina matukar tausayin rayuwarki, miji irin Musaddik bai kamace ki ba, gara kawai a hakura mu ci-gaba da yi masa addu’a.
Afrah ta yi dan murmushi gami da kallon Malam Mahmud, wanda ya yi tagumi hannu biyu, sannan ta dawo da kallonta ga Inna Halima ta ce
“Me ya sa za ki fadi haka Inna? Ya za ki ce miji irin Musaddik bai dace da ni ba, bayan jininmu daya.
Dan-uwana ne, kada fa ki manta a da, ba haka rayuwarsa take ba, ina ganin kuma ku na son ya yi aure ne, saboda ya samu natsuwa.
To ai ina ganin wannan jahadi ne gaba dayan mu lada za mu samu, kuma akan maganar yi ma mahaifina biyayya, ina miki rantsuwa ko wuta ya hura ya ce na fada, zan fada, domin da ‘shi kadai na samu nasara yin rayuwa, bayan Allah ya amshi ran mahaifiyata, don haka ina so ki sa a ranki, auran Yaya Musaddik shine biyayya mafi kankanta da na ke ganin zan iya yima mahaifina.
Hawaye ya digo a idanun Inna Halima, so da kaunar, Afrah ya Kara kamata, ta dubi Malam Mahmud wanda shi ma maganganun Afrah sun taba masa zuciya, ido kawai ya dora mata, yana yi ma Allah godiya a zuciyarsa daya ba shi ‘ya irin Afrah.
Inna Halima ta ce “Gaskiya ne yaya. Allah ya ba ka ‘ya daya tamkar da dubu, yau Afrah ta sa ni alfahari da ita, ta Kara dasa min soyayyarta, zahiri mun yi dace da samun ya irin Afrah.
• Me cike da tausayi, jinkai da uwa uba ilimin addini daya gama ratsa zuciya da jikinta, hakika Musaddik mun yi masa dukkan gata, na ba shi mata irin Afrah, ina kuma da tabbacin Afrah ita ce sanadiyyar maido da shi irin hanyar da yake akai a da.
Ta sa hannu ta kara jawota jikinta ta rungumeta tana fadin “Allah ya yi miki alabarka, Allah ya hadaki da dukkan farin-ciki a gidan Musaddik da rayuwarki duka, ke ma Allah ya ba ki ya’ ya masu biyayya”.
Malam Mahmud ya amsa da “Amin Halima, ai Afrah ta zama sanyin idaniyata, ta zama farin-ciki na, darajarta da kima sun Kara fadada a zuciyata, ba mi da kamarta a duk “ya’yan da na haifa. Matsayinta daban yake” Inna Halima ta ce “Tabbas haka ne yaya.”.
Kalaman Malam Mahmud sun sanyaya zuciyar
Afrah daga kunci, natsuwa ta fara zuwa mata, ta. kuma Kara dammarar amincewa tare da yarda da zabin mahaifinta. Malam Mahmud ya ce.
“Halima ki nemi Musaddik gobe ki yi masa bayanin canjin alherin da aka samu, ya zo su yi magana da Afrah, domin auransu ba na so ya wuce nan da wata daya.” Gaban Afrah ya fadi, ta runtse idanunta ta bude. Wata daya!
Da sauri ta tashi daga jikin Inna Halima ta fice. Inna Halima ta bi ta da kallo tana murmushi ta ce “Kunya ko Afrah?” Ta dawo da kallonta ga yayanta Ta ce.
“Eh, to ai daukar lokaci baida wani amfani, tunda dama Islamiyya ce kawai take zuwa, aure kuma ba zai hanata zuwa da kuma koyar da dalibanta ba, saboda hakan goben nan zan kira shi, na san kuma duk inda yake zai amsa kirana da gaggawa”
Ya ce “To shi kenan. Allah ya kai mu. Ita. kuma Hauwa sai ta jika Na’imarta ta sha”. Inna Halima ta ce “Lallai kam! Shi ya sa ai aka ce gida biyu, maganin gobara, yau da Na’ima ce kadai
‘yarka da bakin-ciki ya kashemu.”
Ya kalli agogo ya ce “Aje batunsu a gefe, tashi ki tafi gida kada Mai-gidan ya ga dadewarki”.
“To Allah ya tabbatar mana da alheri”. Ta tashi ta gyara zaman hijabinta, sannan ta yi masa sallama ta fice zuwa dakin Afrah, amma sai ta ta tadda ta tana shafa’i da wutri, don haka ta wuce zuwa gida zuciyarta fes! Da farin-ciki Afrah ta share masu hawaye.
Washegari tun safe Inna Halima ta kira Musaddik a waya, don haka gab! Da azahar ya shigo gidan, idanunsa jajir! Kayan jikinsa kuwa kaca-kaca duk sun dafe da datti, kai da gani ka san sun dade a jikinsa, sai da Inna Halima ta samu natsuwarsa, sannan ta gaya masa duk halin da ake ciki a yanzu.
Musaddik ya yi shiru, jikinsa ya yi matukar sanyi a hankali ya ce “Afrah Inna?” Ta jinjina kai ta ce “Ita fa”. Ya girgiza kansa ya ce “A gaskiya Inna ba’a yi ma Afrah adalci ba.
Matukar aka aura mata ni, domin ta kowace fuska bamu dace ba, tana da hankali, tana da natsuwa tana da kunya, uwa uba tana da matukar riko da addini, ya ki ke ganin mai irin wannan halin ta dace da ni?”
Inna Halima ta ce “Kada ka damu ko kadan, za mu hada ka aure da ita ne domin wadannan halaye nata da ka lissafa, domin kuma muna da tabbacin da su za ta yi amfani ta janyo hankalinka, ka natsu ka zama mutumin kirki kamar da, don haka wannan babbar dama ce a gareka. Musaddik ya dago ya dubeta ya ce “Amma Inna, Afrah ba ta so-na, tursasata kawai ku ka yi ta aure ni”. Inna Halima ta girgiza kai ta ce.
“Kada ka sa ma kanka dole sai ka gano tana sonka ko ba ta sonka, abu dai mafi dadi, shine da kanta ta amince za ta aureka, don haka duk ka aje wanna Kwakule-kwakulen ka yi ma Allah godiya daya ni’imtaka da samun Afrah. Kawunka kuma ya umarce ka da ka je ku tattauna da ita”
Ya Kara kallonta ba tare da ya yi magana ba, ta ci-gaba da cewa “Eh, saboda auran ba zai wuce nan da wata daya ba”. “Wata daya?” Ya tambaya a gaggauce, ta ce.
“Eh, wata daya. Ko akwai wani abin ne?” Ya girgiza kansa ya ce
“Babu komai Inna, zan yi
kokari na je, na gode. Allah ya saka maku da alheri, ya kuma ba ku ladan zumunci”
Ta ce “Amin, sai dai kada ka je mata a haka, ko yaya ne ka samu kaya masu tsafta kasa idan za ka je.
” Ya dubi kayan jikinsa, shi kansa ya san ya yi datti, yayi dan murmushi sannan ya ce “To Inna na gode.
Daga nan ya tashi ya tafi, haka nan ya ji ya
•sami kansa da jin wani farin-ciki, hakika samun Afrah a gare shi ba karamin al’ amari bane, duk da babu son aure a zuciyarsa.
To fa, sai ya ji ya samu kansa da jin dokin son auran Afrah wacce ko a mafarki bai tada lissafota a cikin matan da zai aura ba, duk da rayuwarta ta dade tana burge shi, tana daya daga cikin mutanen da yake jin nauyin aikata mummunan abu a gabansu, shi kansa bai san dalili ba. Amma ya san dai yana matukar jin nauyinta duk da kananan shekarunta.
Yau kwata-kwata a makaranta Afrah ta kasa samun natsuwar da za ta koyar da dalibanta, tana cikin matukar damuwa wacce iya yadda ta so ta boye, sai da Sayyadi Habib ya fahimci tana cikin damuwa, saboda haka bayan an tashi, suna kan hanyarsu ta zuwa gida.
Ya dan dubeta ya ce “Afrah meke faruwa ne?” Ta dan dube shi ta ce “Me-ka gani?” Ya yi murmushi ya ce “Kin tabbata ‘yar Na jeriya me bada amsar tambaya da tambaya”
Ita ma ta yi dariya ta ce “To ai ban fahimceka bane, shi ya sa na tambaya.”
» Ya ce “Ni kuma na
fahimci damuwar da ke tattare da ke ne, shi ya sa na tambayeki.” Ta girgiza kai ta ce “Ba ni da wata damuwa.
Ya ce “Ki na da ita, sai dai idan ki na Kokarin boye min, wanda ina ganin bai kamata ba, duk da ban san damuwar ba, na san idan ki ka gaya min, zan amfaneki koda da shawara ne ko nasiha, amma idan ki na ganin sanina bai zama dole ba, to ki bar shi ba sai kin gaya min ba, na dinga taya ki da addu’ar Allah ya kawo miki mafita. Nan da nan idanunta suka cika da kwalla, ta yi
Kokarin maidawa sannan ta ce “Hakika idan akwai wanda ya cancanci ya san damuwata a yanzu, to kai ne, domin damuwar ba tawa bace ni kadai, ta mu ce mu biyu”
Ya kalleta, nan da man ya ji damuwa ta cika ransa yace “To idan har haka ne, me ya sa ba za ki gaya min ba, ko don mu hadu mu shawo kan matsalar gaba daya”Ta ce “Hanyar da zan bi na gaya maka ita ce na rasa, domin ban san yadda za ka dauki lamarin ba”. Ya girgiza kai ya ce “Zan dauke shi a duk yadda ya zo min, domin Allah ya fi ni sanin dalilin yin komai”
Ta numfasa dai-dai lokacin da suka iso kofar gidansu, suka tsaya sannan ta ce “to shi kenan ka yi hakuri zuwa gobe, za mu yi magana, zan sanar da kai komai, sai dai, ina addu’a tare da fatan Allah ya sa ka fahimceni”Ya yi dan murmushi ya ce “Ba zan tursasa miki ki gaya min yanzu ba, zan jira har zuwa goben, sannan ina tabbatar miki da cewa zan fahimceki, domin na san halinki gaba da baya”.
Ta gyada kai ta ce “To na gode: Ya Sayyadi, sai goben.
Ya ce “Allah ya kai mu, ki gaida mutan
gidan.” «Za su ji.”
. Daga nan ya tafi, zuciyarsa cike
da sake-sake akan damuwar Afrah, wacce ya ji tun. kafin ya san damuwarta ta shi ma damuwar ta kama shi.Afrah na shiga gidan, ta yi turus! sakamakon ganin Yaya Musaddif tare da mahaifinta a zaune akan tabarma, ta yi saurin kallon kofar dakin Mama Hauwa, ta ganta a kulle, alamar ba ta nan, don haka ta karasa shiga. “Afrah an dawo?”
Cewar mahaifinta, ta gyada kai fuska sake tamkar ba ta cikin damuwa ta ce “Na dawo Baba, sannu”. Ya dubeta zai yi magana kenan, ta riga shi
“Sannu da zuwa yaya” Ya dago ya kalleta sosai,
Idanunsa dauke da sha awar ta ya ce “Yauwa, sannu yan makarantar?”
Ta kara yin murmushi ta ce “Lafiya kalau”
Cike da farin-ciki Malam Mahmud ya ce “Tun dazu ya zo gunki, bai san ki na koyar da dalibai ba, a irin wadannan ranakun, ganin kin kusa dawowa, ya sa na (sayar da shi akan ya jiraki”. Ta ceTo Baba,
‘bari na shiga daki.” Ya ce “Ba damuwa zai sameki a dakin Ta wuce da sauri zuwa daki, ta kintsa kayanta da ta hari kam katifa, ba ta cire hijabin ba, nikaf kawai ta cire ta nemi bakin katifar ta zauna ta takure gu daya, lokacin daya kuma tana karanta
“Tana-Lillahi’wa-Inna Ilaihir-Raji’un! Domin ta samu matsuwar zuciyarta, domin ko kadan ba ta son Musaddik, ta fahimci tana cikin damuwa akan
auransa Cikin sallama Musaddik ya shigo dakin, ta amsa masa lokaci daya ya sami kan tabarmar da ke shimfide a tsakar dakin ya zauna yana kallonta, a hankali ta gaishe shi, ya amsa, sun dau tsawon lokaci ba tare da ya iya yin magana da juna ba, daga bisani ya numfasa ya ce.
“Afrah kina ganin maganar auran mu babu cutarwa a bangaren ki?” Ta daidaita muryarta ta ce
“Cutarwa? Wane irin cutarwa?” Ya muskuta ya ce
“Ni ina ganin kamar babu dacewa a tsakanin mu Afrah, halina ba boyayye bane, rana tsaka na sami canjin rayuwa. Irin rayuwar da na ke yi a yanzu na fi kowa tsanar irinta a da, amma ban san kaddarar da Allah ya kaddara min ba, na sami kaina a rayuwar da na tsana, ki na ganin za ki iya zaman aure da mutum irina me shaye-shaye da gurbatacciyar rayuwa?”
Afrah ta runtse idonta ta bude, zuciyarta ta
Kara cika da tashin hankali ta ce “Zan iya auranka mana, zan iya zama da kai koda halin da ka ke ciki ya fi haka munana, domin ina da tabbacin wata rana za ka daina, za ka shiryu don na san wannan. ba rayuwarka bace a da.
Sha’awar halayenta da natsuwarta suka Kara kama shi ya ce “Kin yi tunani akan sadaukar da känki da kike son yi Afrah?” “Na yi tunani kuma zan aureka.”
Wannan kalamai sun fi komai dadi a zuciyar
Musaddik, ya aje numfashi gami da kallonta ya ce,
“Wanda na ganku tare ranar da na zo gun Na’ ima, meye matsayinsa a gunki?”
Tsigar jikinta ta tashi, damuwa ta Kara cika zuciyarta, kallon da ya tsareta da shi ne, ya sa jikinta ya yi matukar sanyi, ta ji kuma ba za ta iya gaya masa gaskiya akan Ya Sayyadinta ba, domin ba ta ga amfanin hakan ba, tunda ta riga ta zabe shi a matsayin mijinta.
Ta kakalo murmushi gami da gyara zamanta sannan ta ce “Matsayi kuma? Ba komai tsakanina da shi daya wuce Malami na, ni dalibarsa ce”. Ya lumshe idanunsa ya ji matukar dadi da jin amsarta ya ce. “Ki na nufin ba ki da wani da ki ke soyayya da shi, kada na zama sanadin datse soyayyar?”
Ta girgiza kai ta ce “Ba ni da kowa, ina son kuma mu bar maganar nan”. Ya jiniina kai ya ce
“An gama.”» Ta dan yi murmushi ta ce “Na ji Baba
na maganar ba za’ afi wata daya ba bikin.
Ya ce
“Eh, haka ya yi min bayani dazu,
domin har ya ba ni damar ma na je na gaya ma Hajiya cewar ya ba ni ke, ya sa kuma ranar biki wata daya me zuwa, wato uku ga watan da zai kama. Nan da nan Afrah ta ji ta Kara gigicewa, bakinta ya shiga karanta “Allahumma ajiri fi musifati wa akalifni khairan minha”.
Amma a zuciyarta, ta saki ajiyar zuciya ta ce “To Allah ya nuna mana.Ya dubeta ya ce “Akwai wani abu ne?” Ta gyara zamanta ta ce “Dama ina son na rokeka ne, akan ko bayan auran zan ci-gaba da zuwa
Islamiyya, kuma zan ci-gaba da koyar da
dalibama
Ya yi murmushi ya ce “Kada ki damu, meye ribata don na hanaki zuwa makaranta, ba wani abu, kuma babu damuwa, ki yi yadda ki ke so”. Ta yi murmushi ta ce “Na gode.” Daga nan suka ci-gaba da tattaunawa, kai ka rantse da Allah Afrah tana son Musaddik, kuma tana son auran.
Shi kuwa haka nan ya ji matukar natsuwa a dalilin hira da ya yi da ita, har zuwa lokacin da aka kira sallar magariba, sannan ya yi sallama da ita, ya fita tare suka yi alwala da Malam Mahmud.
Suka tafi masallaci, duk da ko azahar bai yi ba balle la’asar, amma ya zai yi, tunda Malam Mahmud ya sa shi a gaba zuwa masallacin. Washegari kuwa cike da fargaba Afrah ta je makaranta, haka zalika har aka tashi makarantar
Islamiyyar Afrah ta kasa had ido da Ya Sayyadi Habib, haka zalika damuwarta ta fi ta ko yaushe fitowa. A cikin ajin makarantar suka kasance, bayan an tashi kowa kuma ya watse, a natse Ya Sayyadi ya dubi Afrah ya ce. Fateema, damuwa ba’ ta maganin damuwa, haka zalika duk abinda ya shigo rayuwar bawa, to hakuri ya kamata ya runguma gami da addu’a,
* saboda haka ina son ki natsu ki yi min bayanin abinda ke faruwa, ko akwai ta inda zan iya taimakawa”
Afrah ta numfasa gami da gyara zaman nikaf dinta a fuska, sannan ta fara magana a hankali “Ya Sayyadi, da farko dai ina son ka sani, ka kuma sa a ranka kai ne da namiji na farko da zucivata ta fara SO.
Ta kuma yarda da ta zama abokiyar rayuwarka, domin ina da tabbacin kai ne wanda za « ka yi min jagora zuwa gidan aljanna da kyawawan halayenka da kuma iliminka me guda na.
Ba na hangen komai ko kwadayin komai, daya wuce na san za ka sanyani a hanyar bin dokokin Ubangiji.” Ta dan numfasa tana kallonsa, ganin bai da alamar yin magana ya sa ta ci-gaba da
cewa. “Sai dai kash! Komai Allah ya riga ya gama tsarawa, ba mu da yadda za mu yi, sai yadda ya yi da mu, qaddara ba ta rubutaka ka a matsayi mijin
aurena…. A gaggauce ya dago ya dora mata
Idanunsa da suka rikide, nan da nan suka yi jajir!
“Kamar yaya?” Ya Sayyadi ya yi gaggawar tambaya, ta jinjina kai sannu a hankali ta kwashe labarin komai ta sanar da shi.
Ta Kara da cewa “Allah shi ne shaida, ko kadan ba na son Yaya Musaddik, ban taba sonsa ba, bai tada burgeni ba, haka zalika ban taba yi ma. kaina sha’awar auransa ba, don na san babu wani alheri da zan samu a cikin auransa.
Amma abu daya na daukar ma kaina, shine yi ma mahaifina biyayya a cikin duk wani abu da bai saba ma umarnin Ubangiji ba, zan yi ma mahaifina biyayya koda yin hakan zai Kuntata ma rayuwata, zai kuma kori farin-ciki na matukar mahaifina zai yi farin-ciki.
To na ke da na yi komai, saboda haka ina mai ba ka hakuri, kai na ke so, amma Musaddik zan aura, domin cika umamin mahaifina, ka yi hakuri Ya Sayyadi, ka yi min afuwa.”
Ga tsananin mamakin. Afrah, sai, ta ga Ya Sayyadi ya yi wani bushashshen murmushi, sannan ya numfasa ya dauki wani dogon lokaci yana kallonta ba tare da ya yi magana ba, har ta gaji ta kuma kosa ya ce wani abu, sannan daga bisani ya fara magana cikin sanyin jiki da sanyin murya.
“A yau na Kara yin alfahari da ke, hakika ke yarinya ce me tsananin hangen nesa, tunaninki ya yi nisa da shekarunki, komai na rayuwarki abin burgewa ne, ki na daya daga cikin ‘ya’ yan da iyaye suke alfahari da su.”
Kalamansa sun sa Afrah ta fara samun
natsuwar zuciyarta, ya ci-gaba da magana, “Ban ji haushin biyayyar da za ki ma mahaifinki ba, hakan ma ya Kara sa min sonki da sha’ awar halayenki ne, ya kuma Kara miki wani matsayi na musamman a zuciyata, kin kuma zama abar kwatanta halayenta a wajen duk wani mai hankali.
Sai dai ina taya kaina jimami da alhinin rabuwa da mace irinki, domin ke ce irin uwar da Manzon rahama ya umarcemu da mu zaba ma
‘ya yanmu, na yi mafarkin kasancewa da ke a matsayin matata war ‘ya’yana, wacce za ta yi ma
‘ya’ yana tarbiyya, amma Allah bai nufa ba, ba zan ji haushi akan kaddararsa ba.
Domin yarda da kaddara mummuna da kyakyawa, cikar imani ne, na kuma yarda da kaddara a matsayina na masulmi.”
Ya nisa ya ci-gaba da cewa “Ba zan so kaina na ce kada ki yi ma mahaifinki biyayya ba, haka zalika Musaddik ya fi bukatar ki fiye da ni, domin
Hmmmm