yaron nan, domin mahaifiyarki ma ta zo min da zancen. Sannan ta bukaci in barki a nan ki kare hutun ki, domin ta lura ba ki cika son ibada ba, kuma ni ma tunda ba ki son yin sallah ba zan amince ba, domin abin ya yi yawa kenan Mimi. Don gaskiya mahaifiyarki tana da hujiar cewa in bar ki, Mimi ta rude, Dad don Allah kar ka bar ni, ka san fa ba sa so na.
Ya ce, suna sonki na sani Mimi, in kin dan zauna za ku shaku ni ma ba a son raina zan bar ki ba. Ta soma kuka wiwi tana fadin Dady kawai ka ce ka daina so na, Please Dady kar ka barni ba zan zauna ba.
Ya dafa ta, shikenan na ji ki yi shiru zan tafi da ke, amma kin san dole sai ta bata rai ko?
Ta ce, Dad in mun tafi za ta huce, ya ce, a’a dole mu sunkuyar da kai mu tafi da yardar ta. Ta yi shiru tana tunani, ya katse ta da cewa, dole mu samu wani malami wanda zai dinga koya miki karatu, don ni ma ba zan so a ce ‘ya ta mai kyau kamarki, amma ba ta san komai a cikin addininta ba.
Take wata dabara ta fado wa Mimi ta ce, Dady me zai sa ba za ka daukar min wannan malamin ba? Ya kalle ta, ke ki ka ce kin tsane shi sannan za ki ce a daukar miki shi? Ta kirkiro murmushi, Dady na ga yanda Hajiya ke son karatun shine. Sai na ga in shine za ta fi saurin yarda in tafi. Ya yi
‘yar dariya me wayo kawai, to zan shawarce ta, amma za ki yi karatun ko? Don na sanki duk abinda ki ka ce kin tsana, tabbas kina nufin abinda ki ka fada, ta ce, zan yi Dady.
Ya girgiza kafadarta cikin jinjinawa ‘ya ta.
Kira min mahaifiyarkin in lallaba ta ta amince sannan ina son ki ba ta hakuri a bisa laifukan da take tumarki, ta ce, to Dady zan ba ta, sannan. ta fita.
Ta sami Hajiya tana jera kayanta na sawa a cikin wadirof. Bayan sallamar da ta yi Hajiya ta amsa ta kasa cewa komai, ita kuwa Hajiya dama ba ta waiwayoba kuma ba ta fasa abinda ta ke yi ba. Ta dai san Mimi ce, Bayan shudewar mintunan da basu kai uku ba, sai Mimi ta soma magana cikin in’ina ta ce, emm, da ma zan ce ne Hajiya don Allah ki yi hakuri in sha Allahu ba zan sake ba. Kuma zan rika yin sallah ta akan lokaci. Hajiya ta ajiye kayan da ke hannunta ta dauko za ta saka a cikin durowar sannan ta zauna a bakin gado. Da hannu ta kira Mimi alamun ta zo, ta ce, zauna kusa da ni, Mimi ta zauna.
Hajiya ta tausasa murya ta kalli
Mimi ta ce, ina son ki sani ba ina nuna miki kuskuren ki don wani abu ba ne, face don rayuwarki ta yi kyau, sannan ba ina cewa ki yi sallah don ni ba ne, a’a don kanki ne ki yi don Allah. Malamai suna fada mana cewa
Sallah ita ce abu ta farko da za a fara binciken aikin bawa in ya mutu. In tayi kyau ana sa ran sauran ayyukan sa za su yi kyau. Sallah ita ce abinda ta raba tsakanin Musulmi da Kafiri.
Ita ce ta raba Mutum da Dabba, Sallah ba abin wasa ba ce, ki kiyaye. Ki zubar da duk dabi’un banzan nan da kikeyi na Yahudawa da Nasara, wanda ki ke zaton na wayewa ne, to ina son ki sani ba wayewa ba ce, duk wata wayewa ta duniya da lahira Addininmu na Musulunci ya zo da shi. Wancan kuwa da ki ka dauka bata ne, mu Hausawa da mu, ke da al’ada mai kyau wadda ba ta ci karo da Addini ba. Ina me yi miki nasiha da ki daina irin wannan shigar ta kafirai, ki kama suturar ki ta al’adarki da addininki, sannan ki dauka ke da kowa duk daya ne, ba don Allah ya fi sonki ba ne ya sa ki ka fito a gurin mahaifinki mai tarin arziki, ki mu’amalanci kowa kamar yadda Addininki ya zana.
Kan Mimi kasa, kwarai ta kosa
Hajiya ta gama wadannan zantukan da ita sam ba ta ma fahimtar Hajiyar. Ya ya ma Allah ya ba ta Ubanta, kuma Hajiya ta ce, karta yi Gadara? Ta yi dai murmushi a ranta ta ce, tab wannan ma kuskure ne, ta daga ta kalli Hajiyar, Dad ya ce, ki je. Hajiya ta mike tsaye tare da dafa kafadar Mimi na ji dadi da ki ka gane kuskurenki. Kuma in kin canza zan nuna miki kauna irin ta ‘ya da mahaifiya, murmushi Mimi ta yi, wanda ita kadai ta san ma’anar shi, Hajiyar ta fita tare da cewa Karasa jera min kayan nan cikin word durop. Tana fita Mimi tayi dariya irin wadda ta fi yi idan ta ga mugunta, a fili ta ce, ka ji Hajiya wai da talaka da mai kudi wai duk daya ne, ta ina suka hadu? Ai bambamcin ma a bayyane ya ke. Ai Talaka wahalalle ne bayin mu ne, ita Hajiya dai kawai ba ta waye ba ne, take irin wannan maganar.Shi kuma wawa sakaran malamin
Allah ya sa ya yarda ya bi ni zuwa Abuja, sai na taka shi, na ja shi, na tozarta shi, sai ya gane ya taba Mimi. Ita kuwa Hajiya da dadin rai ta fita dakin, na ta a zaton ta ‘yarta ta soma hawa hanya, tunda har ta soma bada hakuri, abinda ba ta taba yi ba a tsawon
rayuwarta. Watau ta yi laifi ta bayar da hakuri, gani take yi ta kaskanta. Da sallama Hajiya ta shiga dakin
yana zaune kan kujera, yana duba jaridar
Leadership. Ta zauna a hannun kujerar ga
ni Alhaji. Ya kalle ta, kin san dai tafiya zan yi ki ka koma dakin ki ki ka share ni ko? Yaci gaba, ni gaskiya wannan zuwan ban samu wata maraba sosai ba kamar baya. Ta yi ‘yar dariya, sai da na ce, kar ka zo da Mimi, ai amma ka ki, duk ita ce ta yi ta dama min lissafi. Yace, to na ji shikenan, ai tunda ni ma na yi mata fadan wasa da Sallah, ta daina in sha Allahu, don haka ma nike so ki taimaka ki ba mu aron malamin nan na yaranki tunda na ji kina yabon shi gurin kwazo da jaruntar koyar da yara, in ya so sai ki samo masu wani.
Hajiya ta ce, tabdi, ai ba zai yiwu ba, sai dai in a samo maku wani, ya ce, saboda me? Ba fa da koyarwan gidan nan kadai ya dogara ba. Malami ne a makarantarsu, sannan ina zaton akwai gidajen da yake koyarwa. Ka bar ta kawai ta Karasa hutu a nan, na san kafin ta koma nan da wata biyu ta samu abinda ta samu. Ya kama hannunta ina son ki kira shi, in gana da shi. In zai amince zan biya shi fiye da abinda ya ke samu. Ta ce, in har ya amince din kana ganin za ta yi karatun a can? Ya dan matse hannunta, kar ki damu
Sauda za ta yi, ta ce, shikenan zan kira shi, sai dai ban so ba zai bar yara na, ni dai suna karatu sosai a gurin shi.Hajiya Sauda ta kira Malam Ismail ta ce masa don Allah in yana da lokaci ya zo maigida yana son ganin shi. Ko yarinyar nan ce ta kai karar shi, kuma ya san halin masu kudin nan da jarabar son yaran tsiya.
Ta katse mishi tunani da cewa, kar ka damu alheri ne, bari ma dai in fada maka, a takaice so yake ya dauke ka zuwa Abuja saboda yarinyar nan, ka dinga koya mata karatu da kannen ta na can. Don Allah zan roke ka kar ka ce a’a, saboda na san zai biya ka da kyau. Kuma ni ma za ka taimake ni.
Ya ce, Hajiya gaskiya yarinyar nan da kyar in za ta bayar da hadin kai a kan karatu, sannan ga ayyuka na a nan. Ta ce, ka dai zo din a yi magana a zaune ko? Ya ce, to shikenan in na yi wanka yanzu zan taho.
Sai da ya bi ta gidan su Mahamud abokin shi, ya isa yayi sallama Mahamud ya amsa tare da cewa, dan halak! sauri na ke in zo gidanku yanzu, ashe kana tafe, ya ce, lafiya dai za ka zo? Mahamud ya ce, lafiya lau, takardun nan ne na manta, wanda Headmaster ya baka ka yi makin na dalibai.
Ya ce, shaf! na manta, ko da na zo gida fa ban tuna ba. Suka fito tare ya ce, in ba za ka fita ba Mahamud mashin din ka zan ara, zan je gidan Bashir Masari.
Mahamud ya ce, to ka sauke ni bakin kasuwa? Ya ce, to ka san me zai kaini?
Mahamud ya ce, a’a, Isma’il ya ce, Hajiya ce ta kira ni, wai tana son in koma Abuja in koyar da wannan mara kunyar da nake baka labari jiya. Wai ta san zan sami kudi. Mahamud ya ce, kawai ka je, kar ka manta da tarin bukatun ka wadanda kudi kawai suke so. Isma’il ya ce, ina sane, matsalar kawai ba na jin zan dauki rainin yarinyar ko da suna taka kudi. Mahamud ya ce, ka dai je ka ji in abin zai yiwu, amma dari bisa dari na ba ka goyon baya.
A falon baki Abdulkarim ya yi wa Isma’il jagora, sannan ya shiga ya sanar da
‘Hajiya cewa ga Malamin yaran nan tare da
‘Alhaji. Suka jera zuwa falon bakin ya gaida su cikin mutumci da sanin ya kamata, Hajiya ce ta gabatar ma Malam Ismail bukatar, ya yi shiru. Alhaji ya ce, kar ka damu na san kana koyarwa a gurare dabam-dabam ba da gidan nan kadai ka dogara ba.
Ina son ka had abinda ka ke samu a kowane wata ka fada min, in har za ka amince ni kuma zan ninka maka kudin. Abu daya dai da zan roke ka shine, ka tabbatar yarinyar nan ta iya karatu.
Hajiya ta ce, ka dinga yi mata nasiha ka tsoratar da ita. Alhaji ya daga mata hannu, wani irin tsoratarwa kuma? Karatu dai ta ce, shikenan karatu ai ya hada komai.
Isma’il dai yana jinsu kanshi a sunkuye lissafi yake tsakanin amincewa ko akasinta, can Alhaji ya katse mishi tunani da cewa, me ka ce? Ya dago ya dube shi da nufin cewa a’a, sai mutuncin Hajiya da kwarji ninsu ya hana shi fadin haka, sai ya bige da cewa, a bani lokaci domin saina sanar da gidajen da ni ke koyar da ‘ya’yan su.
. Sannan na rubuta takardan barin aiki a Islamiyyar da ni ke koyarwa. Alhaji ya ce, yanzu dai a takaice ka yarda kenan? Isma’il ya ce, na yarda, sai dai in fara watan gobe. Alhaji ya ce, shikenan, nawa ka ke samu
•duk wata? Hajiya ta ce, ai sai ya je ya yi lissafi ko Malam Isma’il? Ya ce, eh! Haka ne. Alhaji ya ce, kana da mata ne? ya girgiza kai tare da cewa a’a, ina dai nema. Alhaji yace, to shikenan, Hajiya ga ki nan, zanji komai gare ki. Amma kafin haka zan so in
san wanene Isma’il? Isma’il ya dago ya kalli.
Alhaji, Hajiya ta ce, wannan ka’idar shi ce,
in dai zai dauki mutum aiki a karkashin sa, sai ya san wani abu daga tarihinsa, ko da kadan ne.Isma’il ya ce, haka ne. Isma’il bin Abdulrahaman shine sunan da aka fi kira na. Mahaifina Malam Abdulrahaman ya
rasu tun ina JSS2, haifaffen nan Katsina
ne, dan kauyen ‘Yargoje. Amma shi ya yi
gidansa a nan kofar Soro. Hakanan
Mahaifiyata ta rasu wata shida bayan
rasuwar mahaifina, mu biyu ne ‘ya’yanta.
Kasancewar tana da ciwon sikila tana shan
wahala a gurin haihuwa ta hakura tun daga kaina, sai aka tsaida mata, kuma wannan
ciwon shine ya yi sanadiyyar mutuwarta. Kafin haka dama ba ta jin dadin, zama da abokiyar zamanta Inna, wacce ita ce uwargida. Irin matan nan ne masu kishin tsiya, yaranta goma sha daya, kuma duk su ne manya da mu, bakwai duk maza ne, sai mata hudu, kuma duk suna raye. Daga cikin yaran na ta, manya guda uku suna zaune a gidan yanzun haka da matansu da
‘ya’yansu. Daman an raba mana gado, ni na samu daki a Soro, ita kuma Ya ta da ke aure a kofar Soro sai aka ba ta wani dan fili Karami da ke jikin dakina dake a kofar gida.
Isma’il ya dago ya kalli su Hajiya, ku yi hakuri ina fada maku har da abinda bai kamata in fada maku ba. Ni ma ban san dalilin da zuciyata ta amince in sanar da ku abinda ba na son ina tunawa ba ma. Hajiya ta ce, kar ka damu ci gaba. Tunda na rasa iyayena haka na taso ba na jin dadin kowa a gidanmu, tun daga yayyina har ya zuwa mahaifiyarsu, babu mai biya min kudin makaranta. Yaya Amina kuwa, ita ma ba mai karfi take aure ba, ga yara tana da su har biyar. Don tsakani na da ita akwai tazara ta gurin haihuwa, mijinta ne ya kai ni wajen koyon gyaran TV, da yake ina son karatu
sosai, sai na mayar da hankali har na iya, da
dan abin da nake samu na biya kudin makaranta.
Islamiyya kuwa akwai mahaifin
abokina Malam Aminu shine malaminmu
na Islamiyya, shi ya dauki nauyin karatu na na Islamiyyata. Da ya lura ina son karatu
•lokacin da na kammala Sakandire di na da
saukar Alkur’ani. Haka kuma mahaifin
Mahamud shi ya tsaya min na samu shiga
Mutawassid wato JS1 na Islamiyya tare da
dansa Mahamud. Kodayake ya ce min
makarantar tana da tsada, ta yaran masu
hali ce, ya roki mai makarantar ya rage
masa biyu bisa biyar na kudin.
Amma fa akwai karatu, saboda
Malaman kwararu ne, makarantar reshen ta
yana Madina. Sukan bayar da tallafi ga
dalibai guda uku da suka zama zakaru a
matakin Difloma, don yin karatun Digiri a
Jami’ar Madina. Wannan ya sa na zage
dantsen karatu ba na wasa ba, sannan duk da Karancin shekaru na Malam Aminu
shine ya sake yi min hanyar koyarwa a wani gida, saboda in dinga samun na siyan
littatafai. Hakanan ina koyarwa a
Islamiyyar shi wanda muka yi sauka.
Da wannan ne na ke tallafe da
rayuwata. Har na kammala shekaru shida
na Sanawiyya, lokacin ne na samu koyarwa a nan gidan, wanda Malam Isa mai
makarantarmu ya yi min tayi, ya ce min
yaran a makarantarsa suke karatu, ‘ya’yan
Bashir Masari ne, in zan koyar da su. Ban yi gardama ba, don ina son ci gaba da
‘Difilomata a nan makarantarmu El-Mukhtar, yau wata, biyu da kammala
Difiloma ta, kuma na yi nasarar zuwa na
uku a ajinmu, sai dai kash makarantar da zamu je a Madina mutum biyu ta bukata, don haka ba na ciki. Sai dai ko wani lokaci za su iya neman na uku, ina burin in karanta larabci ko kuma Tafsir.
Amma a yanzu ina da haddar sittin, ina da haddar hadisai da dama. Na san
tauhidi da fikihu daidai gwargwado. Malamai da dama suna jinjina ma kwakwalwata. Malam Aminu mahaifin Mahamud yana yin tafsiri da Azumi a babban masallacin unguwarmu, sau da yawa ni ne na ke ja masa baki. Sannan kuma zuwa yanzu shekara ta ashirin da bakwai.
Ya kalli su Hajiya wadanda suka yi shiru su na saurare. Ya ce, wannan shine tarihin Isma’il bin Abdulrahaman. Alhaji ya ce, shikenan za ka iya tafiya duk yadda ku kayi zanji gurin Hajiya. Hajiya kuwa tausayin Isma’il ya cika ta, ta ce, zan iya tambayarka? Ya ce, eh za ki iya. Hajiya ta ce, a fannin boko fa, daga Sakandire ka tsaya? Ya ce, eh, amma yanzu na zana Jamb domin kar ta zama ban samu wancan damar ba. Hajiya ta ce, Allah ya taimaka ya bayar da sa’a, sannan zan ba ka ‘yar shawara ka dinga ziyartan Malamai don neman Karin ilimi, ya ce, ina zuwa Hajiya, duk asubahi ina daukar karatu. Ta ce, Allah ya taimaka.
Alhaji ya ciro kudi daga aljuhunsa ya mika masa, ga shi ka hau mota. Ya ce, ba komai Alhaji da mashin na zo ka barshi, Hajiya ta ce, ka amsa sai ka sha mai, sai na ganka, ka sanar da su. Ya amsa tare da yin godiya sannan suka yi sallama. Ismail ya buga mashin kai tsaye gidan su Mahamud ya nufa don ya kai masa mashin dinsa.
Kuma sannan ya gana da mahaifin mahamud, su kuma sake tataunawa a kan batun tafiyarsa Abuja. Cikin sa’a yana tsayawa Mahamud yana fitowa cikin fara’a, suka nufi juna Isma’il ya ce, sai ka ce dama kana jiran isowa ta?. Mahamud ya ce, wai Inna ke son alayyahu, duk ga yaran sun tafi islamiyya, suka yi musabaha tare da gaisawa, Ismail ya ce, to hau mu je a mashin mana mu je mu amso mata. Sai da suka je suka dawo sannan suka zauna a dakalin kofar gidan.
Isma’il ya kalli Mahamud, ka san cewa na kasa samun natsuwa da batun zuwa Abujan nan? Ga shi na je da nufin ince a’a ba zanje ba, amma ban san kadarar da ta sa na amsa ba. Duk sai suka yi min kwarjini na kasa kin amincewa. Mahamud ya ce, in
Hmmm