Hakane Safna, amma kilura da wani Abu had'asu akayi kowa bayaso, kinga kuwa bazaije mata gaba gad'iba kasancewarsa mutum mai d'aukar kan tsiya, towa
ABDUL-MALEEK BOOK1 CHAPTER 4
Hakane Safna, amma kilura da wani Abu had'asu akayi kowa bayaso, kinga kuwa bazaije mata gaba gad'iba kasancewarsa mutum mai d'aukar kan tsiya, towaima na tambayeki?, kin aiwatar da aikin malam kuwa?. Na aiwatar jiya, amma d'an zafinkan baiciba, canta had'osu shida ita yafito d'aki rai a 6ace daga nan yafice, Dan jiya abincin safe kawai yaci agidan, inda ALLAH yasoni baduka nazuba bama. To aii da sauk'i, yanzun ga shawara d'aya dazata kawo miki nutsuwa harki samu barci, kisamu kota window ne kilek'a su, kiga halin dasuke ciki. Kai baseera wannan ba shawara baceba, idan naje Nagano abinda zaisaka zuciyata bugawafa?. Karki damu, insha ALLAHU bazaki ganoba. Bayan sunyi sallama safna tayi tamaula tanufi bayan d'akunan, cikin ikon ALLAH window d'akinsa abud'e take, da sand'a taje wajen, bobo tahango abakin gadon zaune yana danna laptop, Rahma na kwance nesa dashi tarufa da bargo tana barci. Wata sassanyar ajiy…