RIKITACCIYAR ALAKA HAUSA NOVEL
\ BABI NA 1 Not just the
beginning Rayuwa cike take da tarin ƙalu-bale, takan zo wa kowanne ɗan'adam
ta mabanbantan fuskoki. Bawa ya karɓi yadda rayuwar ta zo masa ya kuma yi
ƙoƙarin kiyaye dokokin ubangiji shine zai mori rayuwar, akasin haka kuma zai iya
faɗawa ga halaka yayi biyu babu, shi ba da jin daɗin duniyar ba haka kuma
lahirar ma bai same ta ba. A cikin duhun alaƙa mai cike da ruɗani, soyayya ta fara ne
da kalma ɗaya tak, amma ta ɓarke da tambayoyi dubu. Shin soyayyar za ta iya
tsira cikin sirrin da ke ɓoye tsakanin zukata biyu? Ko kuwa RIKITACCIYAR ALAƘA
zata rusa komai kafin gaskiya ta bayyana? Pepperdine University Rick J. Caruso School of Law,
Pacific Coast Highway, Malibu, California. Babu kowa a makeken hall ɗin nasu na ɗaukar karatu sai ita ɗaya
da ke zaune a seat ɗinta, gabanta kuma wani makeken textbook ne sai kuma jotter
da take rubutu a ciki, laptop ɗin da ke gabanta ta ɗaga kai ta kalla sannan
tayi jotting wani part na abun da ta karanto daga laptop ɗin. Gaba ɗaya …