KUDIRAR ALLAH COMPLETE HAUSA NOVEL
D’AND’ANO DAGA KUDIRAR ALLAH. LITTAFIN NAZEEFAH SABO NASHE. PAID BOOK IDAN KIN SHIRYA SIYA TURA KUDIN KAI TSAYE A ACCOUNT NUMBERR NAN. 2118666253 UBA KI TURA SHAIDAR BIYA TA 08033748387. Ta Yaya zai zama jinina alhali ni na san bayan matana ban
tab’a kusantar wata mace ba?” Ya furta kai tsaye yana kallon likitan da
sakamakon gwajin yake hannunsa. Likitan yana jinjina kai ya sake furta “Tabbas
Jaheed jininka don gwajin k’wayar halittarku da komai ya tabbatar kai ne
mahaifinsa kafin a kai ga haka ma ko Kamanninku da suka zamo kwabo da kwabo sun
tabbatar da Hakan koda Ba’a yi gwajin ba.” Shiru na tsawon lokaci d’akin ya d’auka kowa da irin tunanin
da yake a ransa ya kasa yarjewa zuciyarsa shine Mahaifin Jaheed duk da
k’wararan shaidu. Abinda ya sani ko da wasa bayan matansa na aure na Sunna bai
tab’a rik’ewa wata mace hannu ba, idan kuwa ya tabbata Jaheed d’ansa ne ta yaya
ya samar da cikin nasa a jikin wacce aka kira mahaifiyarsa da ko a mafarki bai
tab’a ganin mai kama da ita ba TABBAS AKWAI LA…