DUKAN RUWA HAUSA NOVEL

DUKAN RUWA HAUSA NOVEL
Bismillahir Rahmaanir Raheem.          *DUKAN RUWA...* FARKO. Ta yi zugum kanta jingine jikin kujera tana kallon halittun manyan  duwatsun da suke ratsawa a wannan dajin, tafiya suke yi tamkar ba za su kai ba. Wani lokacin idan sun gifta bukkokin jama'ar wani yankin, takan yi murmushi cike da al'ajabin ta yadda mutum ƊAN ADAM ke iya rayuwa a wannan wuri. Tun tana kallon har dai ta zame ta gyara zama gami da lumshe idanu, bacci ke ƙoƙarin ɗaukarta tana yakicewa. Babu abin da ta tsana sama da bacci a hanya, hanyar ma da ko a mafarki ba ta taɓa ganin za ta bi ba,  zuwa Nijeriya daga Nijar. Ajiyar zuciya ta saki tamkar wacce ta ci gudu, lokaci guda nannauyen tunanin da take ƙoƙarin kaucewa na ƙara yi mata saukar aradu a kwakwalwa. Idanunta ta sauke akan matar dake kusa da ita, baccinta take haiƙan har carbin da ke riƙe a hannunta tana ja, ya faɗi. Sai dai duk da baccin da ta lula, hakan bai sa ta saki yaronta ba, yana rungume a kirjinta ɗam! Kai ka ce wani ne zai ƙwace mata shi. Juya …