BUZU BOOK 2 HAUSA NOVEL

Jamila ta fashe da wani irin kuka tana tsuma, ta ce "Na shiga uku, yanzu Aljani ne ya kwanta da ni?"
BUZU BOOK 2 HAUSA NOVEL
BK 2 52 Jamila ta fashe da wani irin kuka tana tsuma, ta ce "Na shiga uku, yanzu Aljani ne ya kwanta da ni?" "Eh amma a jikin bil'adama ya shiga, ya yi amfani da ke" ta gaya wa Jamila kai tsaye, ba tare da ta ji nauyin hakan ba. "Na shiga ku, yanzu waye zai aure ni a haka? Ya zan yi. Na lalata rayuwata" Hajiya Sa'a ta riƙo hannun Jamila ta ce "Na sha gaya miki, matsoraci ba ya zama gwani Jamila. Shi fa auren nan ba dole ba ne ba. Idan kina tare da ni duk abin da ki ke so za ki samu a tare da ni. Idan ma auren ki ke so miji sai kin zaɓa, kuma tsaf za a yi miki gyara babu wanda ya isa ya gane an taɓa amfani da ke. Kuma ƙungiya ta bayar da kuɗinki na shekara. Su na gurina zan din ga baki a hankali saboda kar a gane. Ki kwantar da hankalinki, ki ƙwarara jikinki, kar wani abu ya razana ki. Kuɗi kin same su kin gama ki saki jikinki ki mori duniya. Ke ce yarinya mafi ƙanƙanta a cikin ƙungiya. Ni dai ina matuƙar ƙaunar ki ne. 'yar uwakki na so na kaw…