UWAR RIKO CHAPTER 3 BY FIRDAUSI

“Saura kuma in Kara jin wata magana, tunda ita ta amince idan na ji batun zuga ta, ko muguwar huduba daga wurinki to ki kuka da kanki Ya yi waje fuu! A fusace. Ladidi tasa hannu da haba ta rafka tagumi. Ta tabbata idan Malam ya fadi magana ba ya maimaitata, sai dai kawai aiki.Malam Isah a nan garin Bauchi yake zaune, yana da mata biyu da yara kusan goma. Uwargidansa Ladidi (mahaifiyar Sahura) na da ‘ya’ya shida duka mata, Sahura ce ‘ya ta biyar a gidan. Sai amaryarsa Asabe tana da maza biyu, mace daya. -Malam Isah haifaffen garin Bauchi ne, domin kuwa nan ne asalin tushensu. Yayyen Sahura kowacco na dakin mijinta, sunada aure, sai Sahura kadai ta rage da Kanwarta. Mahaifiyar Sahura itace mafadaciya ta kin Karawa, ga ta da kishin tsiya, ba kamar Asabe (amarya) ba, mace mai sauki kai, ga ta da kawaici da gudun magana. ‘Ya’yanta ba karamar wahala suke sha a wurin Ladidi ba, da ita kanta, don ma dai Malam Isah ya fi karfin gidansa, yana tsawatar musu, duk da dai wani abun ba a kan idonsa ake yi…