UWAR RIKO CHAPTER 2 BY FIRDAUSI
UWAR RIKO CHAPTER 2 BY FIRDAUSI Bayan kwana biyu da zuwan Malam Musa nema wa dansa aure, sai ya sanar da Abubakar kudirinsa, bai dade ba ya fahimci wadda ake nufin hada su. Yasan Hajjo wadda asalin sunanta A’isha, daliba ce a makarantar da yake koyarwa, wani • lokacin ma yakan leka ajinsu, tana daya daga cikin daliban da. ake yabo a makarantar. Don haka da yamma ta yi ya kimtsa cikin shiga ta mutunci ya. isa gidan, ya kuma aiki wani yaro domin ya yi masa kiranta. Yaron ya fito ya sanar da shi tana zuwa. A can cikin gidan ta gama gyara jikinta ta fito, kasancewar mahaifinta ya sanar. da ita komai, ta hanyar mahaifiyarta, kuma ta gane waye Abubakar din ta amince. Bayan mintuna biyar Abubakar yana jira, sai ga ta ta fito. Da sallama ta rusuna ta gaida shi cikin boye füska, kasancewar malaminta. Suka samu wuri suka zauna a dakalin wani kofar gida. Bayan shiru na dan lokaci saboda rashin sabo, musamman daga Abubakar sai ya dan gyara, zama, da alamar nauyi a maganarsa. “Ina fata Malam… Baba ya y…