UWAR RIKO CHAPTER 1 BY FIRDAUSI
GARIN BAUCHI Malam Musa tare da matarsa Lubabatu, wadda aka fi kira da Luba, sun kasance haifaffun garin Bauchi, tun asalin iyaye da kakanni. ‘Allah ya yi wa Malam Musa da Luba haihuwar yara uku; maza biyu, mace daya; Abubakar, Yahaya sai kuma Mairo. Allah ya yi musu rufin asiri daidai gwargwado. Malam Musa sanannanen manomi ne, ba shi da wata sana’a wadda ta wuce noma, yakan nome hatsi da sauran nau’in abinci a fitar da su wasu garuruwa domin a siyar. Wannan ‘ya mayar da Malam Musa shahararren manomi a fadin garin Bauchi. Yaransa sun taso da tarbiyya da kwazo, saboda. Kokarin da iyayensu keyi don ganin sun zamo magari, suna zuwa makarantar arabiyya safe da yamma, kasancear a garin a daidai wannan lokaci an fi maida hankali akan ilimin Muhammadiyya. Abubakar yaro dan shekaru sha biyar ya sauke alkur’ani mai girma, daga nan ya maida hankalinsa kan harkar noma kamar mahaifinsa. Sauran Kannensa sun ci gaba da zuwa makaranta, Abubakar ya hada da koyarwa a wata makaranta ta addini. Shekarun Abu…