MUSABBABI CHAPTER 20 BY HAJ HABIBA
ba, sai daya tabbatar lafiya, sannan ya sami kwanciyar hankali. Wannan zuwan ma sam Mama Hauwa ba ta bi ta kanta ba, sai da ta ga kudin da ta ba shi, da kuma bayanin Musaddik ne, ya ce a kawo masa.Sannan ta tsaya da tukin tuwon ta shiga zuba masu harara. Yadda ko Malam Mahmud yake murna tare da sa masa albarka. Shi ya kara tunzira ta, ta saki tsaki ta ce “Ai dama kwadayin hakari ya sa ka hada auran. Allah ya kyauta mana da wannan gurbatacciyar rayuwar” Malam Mahmud ya dubeta cike da jin haushinta ya ce, “Wannan irin tunaninki ne, don haka babu wanda zai hana ki fadan tunaninki, sa. dai shi dadin abin. Allah ya fi mu sanin kanmu da kanmu, kuma shi ne shaidar kowane bawa” Ta Kara sakin tsaki ta ce “Ummh! Kanku dai ake ji.” Zaiyi magana kenan, Afrah ta dakatar da shi, a hankali cikin sanyin murya ta ce. “Don Allah Baba ka daina biye mata, hankalina yana matukar tashi, raina kuma yana 6aci, yadda duk zuwan da zan yi gidan nan, sai kun sami matsala da Mama.”Kafin ya yi magana. Mama Hauwa ta da…