ba, sai daya tabbatar lafiya, sannan ya sami kwanciyar hankali. Wannan zuwan ma sam Mama Hauwa ba ta bi ta kanta ba, sai da ta ga kudin da ta ba shi, da kuma bayanin Musaddik ne, ya ce a kawo masa.Sannan ta tsaya da tukin tuwon ta shiga zuba masu harara.
Yadda ko Malam Mahmud yake murna tare da sa masa albarka. Shi ya kara tunzira ta, ta saki tsaki ta ce “Ai dama kwadayin hakari ya sa ka hada auran. Allah ya kyauta mana da wannan gurbatacciyar rayuwar”
Malam Mahmud ya dubeta cike da jin haushinta ya ce, “Wannan irin tunaninki ne, don haka babu wanda zai hana ki fadan tunaninki, sa. dai shi dadin abin. Allah ya fi mu sanin kanmu da kanmu, kuma shi ne shaidar kowane bawa”
Ta Kara sakin tsaki ta ce “Ummh! Kanku dai ake ji.” Zaiyi magana kenan, Afrah ta dakatar da shi, a hankali cikin sanyin murya ta ce.
“Don Allah Baba ka daina biye mata, hankalina yana matukar tashi, raina kuma yana 6aci, yadda duk zuwan da zan yi gidan nan, sai kun sami matsala da Mama.”Kafin ya yi magana. Mama Hauwa ta daka mata tsawa, “Ke da Allah can munafukar banza, idan ba kya so mu dinga samun matsalar, ki daina zuwa gidan mana, ki je can ki zauna da min naki mashayi, mara kan gado, wa ma ya san in da ya
samo kudin. Tunda dai ban ga wata ya kare ba balle ace albashinsa ne, wa ma ya sani ko kudin, sata ne.”
Malam Mahmud ya ce,A’uzibillahi!
Hauwa ki ji tsoron Allah, ki sani fa ke ma kin haifa kuma duk takardancin Musaddik ban taba jin ya dauki ko da kwandalar wani ba, don haka ki kiyaye kanki da yi ma ‘”ya’ yan mutane mummunan zato.
” Hawaye ya cika idanun Afrah.
Shin me ta yi ma Hauwa ne, da ba ta kaunarta, ba kuma ta yi ma rayuwarta kyakkyawar fata? Ba ta saurari komai ba, ta mike ta yi ma mahaifinta sallama, ba ta bi ta kan Mama Hauwa ba, ta yi tafiyarta gidan mijinta. Ranta a bace.
• Rana zafi, inuwa Kuna. Ita gidan mahaifinta
Mama Hauwa ta zamar mata kaya, gidan mijinta Hajiya Kilishi ta zamar mata sartse. Allah dai ya kawo mata karshen wannan fitinar.
A daren ranar da Musaddik ya dawo. Afrah ta yi kokarin zaunawa da mijinta, don ta sami
tattaunawa da shi game da son ci-gaba da
karatunta.
Ta kuma yi matukar sa’a ya amince mata tare da yi mata alkawarin zai ma Murtala magana,
“Tunda kin san ya san malamai a makarantar. faranta ran Afrah Musaddik kuma ya Kara samun karin martaba a gurinta.
Haka zalika Musaddik ya cika alkawarinsa, domin tun washegari ya sami Murtala da maganar, ya gaya masa ba damuwa, an fada akan kari, domin an fara sai da form.
Don haka Murtala da kansa ya yi alkawarin zai sai mata form din, zai kuma nemi taimakon Malaman daya sani a makarantar, domin su taimaka wajen samar mata da (Admission), hakan da Murtala ya yi, ya sa Musaddik da Afrah farin-ciki, mara misaltuwa.
Ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa ta ci-gaba da asarar kudinta a wajen malaman tsubbu domin
. ganin bayan Musaddik, a yayin da gefe daya
Afrah ta Kara sadaukar da kanta wajen yi ma
Musaddik addu’a. Domin tabbas zuwa yanzu ta fara zargin abubuwa da dama a game da rayuwar Musaddik.Akwai tambayoyi da dama. da take bukatar
amsarsu.Don haka ta Kara jajircewa akan addu’a, domin koma meye, ta san bai gagari Allah ba, lokaci a kullum mikawa yake yi, da yardar Ubangiji. Cikin hukuncin Ubangiji Afrah ta sami (Admission).
•Har ma ta fara zuwa makarantar, wacce ba ta sami matsala ba, tunda ta saba mu’amala da jama’a, tana karanta (Accounting), ta, ci-gaba da kare kanta da mutunta kanta, musamman irin shigar da take yi, abin koyi ne ga kowa, dole ta’aje koyarwa a Islamiyya, saboda wani zubin lokaci yana haduwa dai-dai da zuwa makarantarta.
Aje koyarwar kuwa sam! Bai yi ma Ya Sayyadi Habib dadi ba, amma babu yadda ya iya, tunda ci-gaba Afrah ta samu, gara ta ci-gaba da karatunta, domin kuwa ya san burinta kenan, tun fil’azal!
Don haka shi kansa yana tayata mura, sai dai ya san sun yi asarar daliba kuma Malama me halin kwarai da dattako, me hangen nesa fiye da shekarunta.
Ta maida hankalinta sosai akan karatu, tare da ci-gaba da kulawa da mijinta da kuma yi masa addu’a, haka zalika ta ji dadin yadda ta sami goyon bayan mahaifinta akan ci-gaba da karatunta, ta kan kuma sami natsuwa akan irin addu’o’ in da yake yi mata, su ne kuma suke Kara mata karfin guiwa.
Amma ci-gaba da karatun Afrah ya tayar da hankalin Hajiya Kilishi, shine kuma ya sa ta Kara ba da kaimi wajen ci-gaba da asarar imaninta, amma wanda ta dogara da shi wato, Boka Mai Rakwacam har zuwa wannan dogon lokacin babu labarinsa, sai a wani zuwa da suka yi ne.
Ita da aminiyarta Hajiya Rakiya suka sami karin bayani a wajen wani bafulatani, cewar Mai Rakwacam fa. ba shi da lafiya, yana can kasar Nijar yana Jinya wajen wani Kanin tsohonsa.
Kwarai da gaske Hajiya Kilishi ta shiga damuwa da jin hakan, ta kuma sami kanta da addu’ar Allah ya tashi kafadar Mai Rakwacam, domin yadda take kashe kudi.
Ta san da shine yake yi mata aiki, da tuni ta sami biyan bukata. (Wa’iyazubillah! Hakika Hajiya Kilishi ta yi nisa, ta manta Allah shi kadai ne me biyan bukatar bayinsa, kuma duk wanda ka kama ba Allah ba, to ka shiga rububi, ka tabe.
Tabewa me muni Karshe idan ka yi wasa sai ka zama makamashin wutar jahannama, duniya da sonta da son kyale-Kyalen cikinta, su.ne suke wahalar da Dan-adam tare da mantar da shi lahira).
:A cikin irin wannan lokaci ne. Allah ya dora ma Afrah wani irin matsanancin ciwo, wanda aka rasa kansa, har sai da aka dangana da asibiti, in da aka kwantar da ita. Wanda daga bisani aka yi nasarar gano ciwon koda ke damunta. Kuma abin takaicin ma, ba a ankara ba. Bayan daya kodar ta farko, da ta samu matsala.
Sannu a hankali, cikin rashin sani. Ko ace rashin daukar matakin gaggawa. Ta biyun ma ta kamu. Tirkashi! Zahiri Musaddik ya shiga wani irin mugun hali na damuwa. Kuka riris! Yake yi da
Hmmm