MUSABBABI CHAPTER 19 BY HAJ HABIBA
Ita kuwa Hajiya Hudah Yunus ta kan sami dumbin natsuwa a duk lokacin da take tare da Musaddik, hankalinta kuma yana kwanciya, zuciyarta ta yi matukar yarda da Musaddik. Tana jinsa a jikinta da zuciyarta tamkar wani jininta, ko kadan ba ta son yin nesa da shi, wanda ba ta san dalilio hakan ba. Amma ta sami kanta da matukar son ta kyautata masa tare da mutunta shi. Don haka yake da matukar kima da daraja a wajenta, kowace rana idan zai dawo gida sai ta ba shi kudin kashewa gami da wasu alhairan. Don haka kwarai da gaske Musaddik yana jin dadin aiki da Hajiya Hudah, domin ta inganta rayuwarsa. Ta tsamo shi daga cikin fitina tare da daidaita tsakaninsa da matarsa, da yake matukar kauna. Domin samun aikin nan ya sa Afrah ta sami kwanciyar hankali, ya kuma fahimci farin-cikin da yake kwadayin ya ba ta ta samu, a dalilin aikin nan nasa, haka zalika yadda Hajiya Hudah ta maida shi ta kuma dauke shi da daraja, yana matukar jin kunyar aikata wani abu da za ta fahimci sakarcinsa. Ya zama dole ya rike girman da …