MUSABBABI CHAPTER 19 BY HAJ HABIBA

Ita kuwa Hajiya Hudah Yunus ta kan sami dumbin natsuwa a duk lokacin da take tare da Musaddik, hankalinta kuma yana kwanciya,

zuciyarta ta yi matukar yarda da Musaddik.

Tana jinsa a jikinta da zuciyarta tamkar wani jininta, ko kadan ba ta son yin nesa da shi, wanda ba ta san dalilio hakan ba. Amma ta sami kanta da

matukar son ta kyautata masa tare da mutunta shi.

Don haka yake da matukar kima da daraja a

wajenta, kowace rana idan zai dawo gida sai ta ba

shi kudin kashewa gami da wasu alhairan. Don

haka kwarai da gaske Musaddik yana jin dadin

aiki da Hajiya Hudah, domin ta inganta rayuwarsa.

Ta tsamo shi daga cikin fitina tare da daidaita

tsakaninsa da matarsa, da yake matukar kauna.

Domin samun aikin nan ya sa Afrah ta sami

kwanciyar hankali, ya kuma fahimci farin-cikin da

yake kwadayin ya ba ta ta samu, a dalilin aikin nan

nasa, haka zalika yadda Hajiya Hudah ta maida shi

ta kuma dauke shi da daraja, yana matukar jin

kunyar aikata wani abu da za ta fahimci sakarcinsa. Ya zama dole ya rike girman da take ganinsa da shi, ita kanta Hajiya Hudah halinsa da take gani da yanayinsa ya tilasta ta karyata maganar da Alhaji Hamza ya gaya mata tun farkon da za su fara mu’ amala da shi na cewa dan iska ne, me zaman banza da shaye-shaye, ga shi duk tsawon lokacin nan da suka dauka ko karan sigari ba ta taba ganinsa a gabanta yana sha ba.

Yadda take gaminsa da daraja, haka shi ma yake. ganinta da daraja, hakan kuma ya kan cika da damuwa da mamaki, idan ya ga yadda Alhaji Yusuf Sanda ke kwashe dimbin watanni ba tare da ya zo gun matarsa ba. Ya rasa wane irin mutum ne shi, da sam baya kishin iyalinsa, bai kuma damu da su ba.

Dukiya tafi masa akan iyalinsa, shin baya tunanin hakkinta da ke kansa ne. Ita kuma ba ta damuwa ne da rashinsa? Wannan lamarin ko addini, bai yarda da shi ba, domin yadda namiji yake da juriya akan rashin mace, ita mace ba ta iyayin wannan juriyar.

Sannan a iya dan zaman da ya yi da ita, ba zai yi mata shaidar tana bin maza ba, ko wani abu makamancin haka, shin wane irin juriya gareta haka?

Irin wadannan tunani da tambayoyin suna damun zuciyarsa kwarai da gaske, amma kasancewar ba abin da ya shafe shi bane, ya sa yake boye komai’ a cikin zuciyarsa, yake kuma aje hangensa a gefa, don bai san wace irin rayuwa suka shirya ma kansu ba.

Tunda Alhaji Hamza ya gaya masa cewar dukiyar Hajiya Hudah yake sarrafawa, a in da yake zuwa, don haka me yiwuwa da amincewarta da kuma yardarta yake dadewa bai dawo gareta ba, idan kuma haka ne wannan ya rage ruwansu.

A yau Alhamis babu makarantar Islamiyya, saboda haka tun kafin Musaddik ya fita. Afrah ta nemi izininsa nason zuwa gidan Inna Halima da kuma gidansu, domin ta gaida su, kasancewar ta

• rabu da zuwa. Ya yi mata izini. Bayan haka ya kwaso duk kudin cikin al’ jihunsa.

• Wanda Hajiya Hudah ta ba shi jiya, kasancewar ba abin da ake nema a gidan, ya sa ya ba ta Naira dubu goma ne cif! Dama da dari biyar, dari biyar din kadai ya dauka ya ba ta sauran ya ce, ta kai ma Inna Halima dubu biyar. Ta kai ma mahaifinta dubu biyar.

Farin-ciki da mamakin yadda wannan kyakkyawan tunanin ya zo masa, ta karba gami da yi masa godiya me yawa, murnar kadai da ta nuna

-ya wadatar da Musaddik, domin shi kansa a yanzu ba shi da buri irin ya ga ya sanyata farin-ciki.

Bayan tafiyarsa ne, ta shirya cikin shiga ta kamala, kamar yadda a kullum ta saba idan za ta fita ta nufi gidan Inna Halima, wacce ta yi matukar farin-ciki da zuwanta, domin a yanzu Afrah ta Kara samun daukaka da kauna daga Inna Halima, tunda hakarsu ta kusa cimma ruwa.A dalilinta sun dade suna hira. Bayan Afrah ta yi mata gyare-gyare a gidan. Inna Halima ta dubeta cike da kauna da so, ta ce, “Zahiri Afrah na yi rashinki, a kullum wannan ranar ta zagayo, sai na yi tunaninki, kin sangartani, ba kya jin wahalar jikinki akan aiki na.”

Ta yi murmushi ta ce, “Inna kenan, ni fa yau ma wata magana ce ta kawoni gunki”. Ta Kara kallonta ta ce, “Wace magana ce Afrah? Ai ke

*yardardamu ce, duk abin da ki ke so, kada ki yi

Jinkirin fadi.”

Cikin jin dadin maganarta ta yi murmushi, sannan ta dauko Naira dubu biyar ta ce, “Kafin mu yi dai maganar tukuna, ga wannan Yaya Musaddik ya ce na kawo miki domin neman albarkarki.” Inna Halima ta bude baki cike da matsananciyar murna.

Ba wai kudin bane suka sa ta murnar ba, a’a kawai yadda Musaddie har ya yi tunanin aikata wannan kyakkyawan aikin, irin aikin mutanen Kirki masu cike da kvakkyawan dabi’u da halaye.Ta karba tana kallonta

“Alhamdulilfahr. Allah kai ne abin godiya.

Ubangiji ka fara cika mana burin mu. Allah ka dubemu akan kyakkyawan niyyarmu”.

Ta kara kallonta ta ce “Inji Musaddik?” Afrah cikin Afrah ta ce “Kwarai Inna, ga ma na Baba nan shi ma

Naira dubu biyar.

Inna Halima ta yi dariya sosai ta ce

“Alhamdulillahi, shi ma yaya na san zai yi farin-ciki kamar yadda na yi. Allah ya yi miki albarka.

Ta ce “Amin, ai Inna hakika wannan samun aiki na Yaya Musaddik ya janyo mana farin-ciki, ya sa kuma mun fara sa rai da cewa zai dawo Musaddik dinsa na da

Inna Halima ta ce “Kwarai da gaske Afrah, don haka babu abin da za mu ce da wannan matan, don a gaskiya ta taimake mu”. Afrah ta ce “Ni kaina Hajiya Hudah banda wata kalman da zan mata godiya, ko na saka mata, sai dai na daukar ma kaina alkawarin yi mata addu’a a duk lokacin da na yi sallah.

Domin tana daya daga cikin mutanen da ba zan taba mantawa da ita ba, domin ta kawo farin-ciki da kwanciyar hankali a rayuwata”.

Inna Halima ta ce Haka ne. Allah ya ci-gaba da

taimakonsa, ya dawo da shi hanyar da ya bari.

Allah ya yi maku albarka.”.

Daga nan ta dan gyara zamanta, ta ce “Na dawo gareki, wace magana za mu yi wacce ta kawo ki?” Afrah ta ce Inna goyon bayanki na ke nema.

” Ta ce “Goyon bayana akan mene?” Ta ce “Inna ki na daya daga cikin wadanda suka san mafarki na da abin da na ke son zama a rayuwa a game da karatu, don haka na zo gareki.” Ta gyara zama gami da hadiye yawn bakinta sannan, ta ci-gaba da magana.

“Inna maganar karatu ne, ina ta ajiye da takarda, wanda za ta yi min amfani, amma har yanzu ban yi komai da ita ba, don haka tunda na fara samun kan mijina, shine na ke son ci-gaba da karatuna, don haka na zo gareki akan ki taimaka min.

Ni zan yi magana ga Yaya Musaddik, ke kuma ina rokonki da ki je ki yi magana da Baba, ki yi masa bayanin yadda zai fahimta. Don tabbas zai iya cewa na hakura da maganar karatu, amma karatun nan zai yi mana amfani gaba daya a gaba.

Inna Halima ta numfasa gami da yin dan murmushi tace, «Tunaninki me kyau ne Afrah, don haka ba na tunanin shi kansa Yaya Mahmud zai ki yarda, amma na yi miki alkawarin zan yi. masa magana. Kada ki damu kin ji ko. Allah ya taimake ku akan komai Afrah, ya yi maku albarka. Cikin jin dadi maganarta tayi mata

godiya.Ta dan Kara daukar lokaci a gidan kafin ta yi mata sallama ta wuce gidansu, ana gab! Da kiran sallar magariba ta isa gidan, don haka tayi sa’ar samun mahaifinta a gida. Sai dai bai samu

Hmmm