MUSABBABI CHAPTER 18 BY HAJ HABIBA
Bai matsa mata ba, domin ya san tana da dalilin kin tsayawa ta ci, don haka ta yi masa sallama. Ita ko Mama Hauwa ko amsa mata ba ta yi ba, saboda bakin-ciki, ita ma ba ta saurareta ba, ta yi tafiyarta, sai gidan Inna Halima. Ita ma ta gaya mata. Inna Halima cike da farin-ciki ta sanar da ita dazun nan Musaddik yazo ya gaya mata da kansa. Ba ta dade ba daga gidan Inna Halima ta tafi gida zuciyarta cike da faria-ciki. Domin wannan samun aikin nasa, ya kawo farin-ciki rayuwarsu duka. Washegari kuwa har falo Afrah ta sami hajiya Kilishi tana zaune tana mulki tana shakar numfashi tana fesarwa, tamkar mutuwa da rayuwa a hannunta suke, ta sameta ta gaya mata abin farin-cikin daya samesu, cewar ‘Yar Majalisa Hajiya Hudah Yunus ta ba Musaddik aikin yi tare da albashi me tsoka. ‘A kishingide Hajiya Kilishi take, amma tana jin wannan maganar, ta tashi ta zauna sosai, tana kallonta. fuskarta cike da bacin rai hade da mamakin jin maganar.Ya sami Aiki?? • Ta maimaita, ta gyada kai tace, “Eh, ya sami aik…