Bai matsa mata ba, domin ya san tana da dalilin kin tsayawa ta ci, don haka ta yi masa sallama. Ita ko Mama Hauwa ko amsa mata ba ta yi ba, saboda bakin-ciki, ita ma ba ta saurareta ba, ta yi tafiyarta, sai gidan Inna Halima.
Ita ma ta gaya mata. Inna Halima cike da farin-ciki ta sanar da ita dazun nan Musaddik yazo ya gaya mata da kansa. Ba ta dade ba daga gidan Inna Halima ta tafi gida zuciyarta cike da faria-ciki.
Domin wannan samun aikin nasa, ya kawo farin-ciki rayuwarsu duka.
Washegari kuwa har falo Afrah ta sami hajiya
Kilishi tana zaune tana mulki tana shakar numfashi tana fesarwa, tamkar mutuwa da rayuwa a hannunta suke, ta sameta ta gaya mata abin farin-cikin daya samesu, cewar ‘Yar Majalisa Hajiya Hudah Yunus ta ba Musaddik aikin yi tare da albashi me tsoka.
‘A kishingide Hajiya Kilishi take, amma tana jin wannan maganar, ta tashi ta zauna sosai, tana kallonta. fuskarta cike da bacin rai hade da mamakin jin maganar.Ya sami Aiki??
• Ta maimaita, ta gyada kai tace, “Eh, ya sami aiki, shine na ga ya kamata nazo na gaya miki, kafin shi ma ya zo ya gaya miki, don na san zai zo.
Hajiya Kilishi ta jinjina kai gami da kokarin boye damuwarta, sannan ta ce, “To na ji. Allah ya sanya alheri.” Ta amsa da “Amin.” Lokaci daya ta tashi ta tafi abin ta.A gaggauce Hajiya Kilishi ta janyo waya, ta danna lambar Hajiya Rakiya ta kira, bugu biyu Hajiya Rakiya ta dauka. Hajiya Kilishi ba ta damu da amsa gaisuwar Hajiya Rakiya ba, ta fara magana cikin damuwa da bacin rai, “Hajiya, kin ji wani bakin labari, wai ‘Yar Majalisa Hajiya Hudah Yunus ta ba Musaddik aikin yi?”Hajiya Rakiya ta ce Aikin yi? Yaushe
Musaddik har ya sami natsuwar da zai amshi aikin yi, kuma à ina ma ya san hajia Hudah har da za ta
‘ba shi aikin yi?” Hajiya Kilishi ta ce.
“Ina na san inda ya santa, amma na san ba zai wuce kila a wajen bangar siyasa bane ya hadu da ita, amma koma dai menene, wannan samun aikin nasa hanya ce ta lalacewar aikin da muka yi, domin ko kadan ba na so na ga ‘yar wata alama ta shiryuwar Musaddik. Na fi so rayuwarsa ta ci-gaba da tafiya a lalace”
Hajiya Rakiya ta ce, “Amma ke ki na ganin wannan tunaninsa ne?” Hajiya Kilishi ta ce, “Ni kaina ban yarda wanna ba tunaninsa bane, don ina wani tunani game da shaye-shaye, na fi yarda da cewan wannan tunanin makirar matarsa ne Afrah ce da wannan tunanin.
Shi ya. sa tun farko ban so auran ba, na so hana faruwarsa, don shi kansa auran hanyar shiryuwa ce a gare shi, ammaya nuna min auran nasa ba zai canja shi da komai ba, to ga kuma maganar samun aikinsa”
Ta nisa ta ci-gaba da cewa, “Idan ya fara zuwa aiki, yaushe zai sami damar ci-gaba da yawo da aboka nan banza, yaushe zai sami damar ci-gaba da shaye-shayensa?
Haka zalika fara aikinsa, zai dawo masa da darajar daya rasa, zai fara kuma mu’amala da mutanen kirki, maimakon mutanan banza, tunda ga shi da mata ga aikin yi, kuma Hajiya me ya rage a natsuwarsa?”
Hajiya Rakiya ta ce, “Babu, gaskiya wannan abu bai yi dadi. ba, dole kuma a dauki mataki.”
• Hajiya Kilishi ta ce, “Mataki ya wuce na raba shi da wannan matar ta sa, domin duk ita ce silar komai.
Don haka dole mu je wajen boka Mai Rakwacam”.
Hajiya Rakiya ta ce, “Abin yi kenan, gaskiya kada ki yi sanya, don dawowar Musaddik hayyacinsa matsala ce gagaruma, don zai iya waiwayar dukiyarsa, duk da ya riga ya bayar. Amma tabbas yana iya yin tasau.
Shi ne damuwata ai, bari zan gyara masu zama, daga shi har matar ta sa”. Daga nan su ka yi sallama suka aje wayoyin, duk cikin damuwa.
Washegari kuwa tun safe Hajiya Kilishi da
Hajiya Rakiya suka nufi rugar Mai Rakwacam. (Kai wanda Allah dai ya batar ya batar, domin dai. duk wanda ya rike wanin Allah.
Tabbas! Ya tabe. Hajiya Kilishi kam tana cikin hallaka, tunda ta maida boka Mai Rakwacam me biyan bukatunta, ta manta duk wanda ya je gidan boka.
Ya gaya masa bai yarda ba, bai kuma yi amfani da abinda ya fadan ba, to Allah ba zai karbi sallarsa ba ta tsawon kwanaki arba’in, kuma yana fushi da mutum. Idan kuma bokan ya gaya maka, ka amince.
Ma’ana ka yarda ka kuma yi amfani da abinda ya fadan, to ka yi shirka, ka fita musulunci, duk wani aikin Kwarai data taba yi, ya goge. Amma duk zunubanka suna nan, ka kuma fita musulunci.
Hmm! Jama’a wannan wace irin masifa ce? Saboda son duniya ka rabu da Allah da Manzonsa ka yi asarar imaninka.
Bayan ka san cewa Allah me tsananin kishi ne, yana yafe kowane irin laifi, amma banda shirka, matuKar mutum ya mutu yana shirka. Babu inda zai je, sai wuta, da shiga azaba dauwamammiya, me zai sa ka zabi abinda ba dauwamamme ba, akan wanda yake dauwamamme?
Me ya sa ba za mu hanu da abinda Allah ya hanemu ba? Meye duniyar balle abinda ke cikinta?
Mu da mutuwa take gabanmu, meye hadamar wani abu a rayuwa, har ya ja mu kauce ma hanyar Allah.
Bayan duk abinda ka ke bukata Allah (S. W.A) ya yi alkawarin amsa maka, matukar ka roke shi, shine fa wanda yake fushi da wanda baya rokonsa.
Duk abinda ka ga ba ka samu ba.
Dama can rubutacce ne a allon Kaddaararka, kuma duk abinda Allah ya Kaddara. Babu wanda ya isa ya canja shi, don haka lokaci ya yi da za’aji tsoron Allah. Mu kuma koma gare shi, mu tsarkake zukatanmu.
Amma kam! Irinsu Hajiya Kilishi sun riga sun yi nisa, domin duniyar kawai suka sa’ a gaba, sun manta mutuwa da tashin kiyama. Ranar Yauma Tublar Sara ‘ir
Wato ranar tona dukkan sirrika, bukatunta na duniya kawai ta sa ma gaba, ta manta lahira.
Kiyayya da tsana gami da son kashe rayuwar dan mijinta kawai su ne a zuciyarta).
har sukawkai, sugar boka. Mai Rakwacam, la’antar Musaddik take tare da la’antar rayuwarsa, amma cikin rashin sa°a, suka tadda boka Mai Rakwadam baya nan, don haka cikin rashin jin dadi suka dawo gida.: Haka zalika a daren ranar Musaddik ya sami Hajiya: Kilishi har falonta, ya samar da ita magahar samun aikinsa.
Amma shima bata nuna masa wani, jin dadinta ba, maimakon haka ma sai ta gyara zamanta ta kalle ‘shi tace Yanzu kai don lalacewa mace za ka zauna ka na yima bautar kare lafiyarta, kwata-kwata: wannan aikin bai dace da kai. ba, wannan ai wulakanta kai ne Ka tuna fa kayi karatu har Masters gareka,samma zaka kare da yin aikin wanda bai yi karatun komai ba.”
Musaddik ya nisa sannan ya ce, “Maganarki gaskiya ne Hajiya. Amma kada ki damu wannan aikin nadan wani lokaci ne, zan sami aiki, don a yanzu haka ma na riga na mika takarduna wajen neman aikin daya dace da karatuna”Gaban Hajiya Kilishi ya yi mummunan
faduwa, lalle ta yi sakaci Musaddik yana neman ya. dawo Musaddik dinsa na da, lalle auran Afrah da Musaddik babban kalubale ne a gareta. Yanzu Musaddik har yana da kyakyawan tunani da zai tsara ma kansa rayuwa ta-gari? Hajiya Kilishi ta yi kokarin boye damuwarta da bakin-cikinta ta ce, “Yauwa yanzu ka yi magana me kyau, hakan ya dace.” Ta dan gyara zamanta sannan ta ce, “Amma dai wannan tunanin matarka ne ko?”Ya yi murmushi gami da gyada kai yace,Eh, tunaninta ne, ai a gaskiya Hajiya na yi sa’ar mata, a kullum burinta ta maida ni hanya ta-gari, ina matukar jin dadin zama da ita, mace ce ta-gari”.
Hajiya Kilishi ta yi murmushin karfin hali ta ce, “Ai na san haka, a gaskiya Afrah mace ta kwarai, don haka ka yi kokari ku zauna lafiya.” Ya ce “Inshaa Allahu Hajiya.'” Daga nan ya tashi ya yi mata sai da safe ya fice.Lokaci daya Hajiya Kilishi ta mike ta shiga kai gwauro da mari. a tsakiyar falo, zuciyarta a zafafe, tunaninta ya zama gaskiya. Wannan duk shirin Afrah ne, lalle ya zama dole ta dauki kwakkwaran mataki a kansu, tun kafin wankin hula ya kai ta dare.
Zahiri ta shiga damuwa akan wannan lamarin, domin ko runtsawa ba ta yi ba har gari ya waye.
Addu’arta daya, shine Allah ya sa boka Mai Rakwacam ya dawo akan lokaci, domin ya warware mata matsalarta. (Allah ya kyauta). Ta bangaren Musaddik kuwa cikin kankanin lokaci ya fara aikinsa, bayan an rantsar da su Hajiya Hudah, sun kuma fara aikinsu gadan-gadan! Sai dai Hajiya Hudah ba ta koma Abuja duka da zama ba, duk da ga gidan da aka ba ta nan, amma ba ta koma ba
Hakan kuwa yana cikin tsarinta, domin ko hawanta na farko ba ta koma Abuja ba, sai dai ta kan shiga kullum. ta kuma dawo Minna. Shi kansa Musaddik wannan tsarin nata ya yi masa, domin ba zai iya barin matarsa ya bi Hajiya Hudah ya tare a Abuja ba.
Duk inda Hajiya Hudah za ta je. Musaddik yana gaban mota, duk da lamarin yana matukar tagayyara shi, kasancewar rashin samun lokacin da zai yi shaye-shayensa. Amma ya kan takura kansa, saboda alwashin daya daukar ma Afra na daina duk wani aikin assha, amma shi kadai ya san azabar da ruhinsa yake dandana a sakamakon rashin yin shaye-shaye, kamar yadda ya saba, sai dai idan ya sami dan lokaci.
Idan ya ji ba zai iya jurewa ba, ya kan zagaya wani wajen ya dan yi shaye-shayensa, shi kansa a yanzu ya fara tunanin anya lamarin nan nasa na lafiya ne kuwa?
Me ya sa ko ya yi yunkurin dainawa, baya iyawa, bayan ba abinda yake so a duniya irin ya ga ya natsu, amma ko ya yi yunkurin hakan baya tabbata, ga shi dai yana kyamatar abin. Amma kuma baya iya dainawa. Anya kuwa wannan lamatin babu wata a Kasa? Tunanin da Musaddik yake yi kenan..
A yanzu kam! Afrah ta fara samun natsuwa, hankalinta ya fara kwanciya kwarai da gaske, duk da tun bayan fara aikin mijinta, wulakanci da cin mutunci da Hajiya Kilishi take mata ya Kara daduwa.
Domin a yanzu ko gaisheta ta yi, ba ta amsawa. Wanda hakan bai dameta ba, tunda tana zaman lafiya da mijinta, yana kuma kyautata mata.
Tunda yanzu Musaddik har ya san idan zai dawo, ya tsaya ya yi mata tsaraba, a lokacin kuwa daya kwashi albashinsa na farko, kusan gaba daya akan Afrah ya kare, tun daga kan kayan abinci har sutura, sai da suka kare, duk wanda ya san Musaddik a cikin yan kwanakin nan, ya san ya canja.
Hakan kuwa shi ne yake Kara tayar ma da
Hajiya Kilishi hankali kwarai da gaske, duk wani kwanciyar hankalinta ya kau sam! Ba ta cikin natsuwarta, ta rinka komawa rugar Mai Rakwacam har ta gaji. Amma bai dawo ba.
Mutuwa ya yi, Aljanun nasa ne suka dauke shi, ko ina ya shiga, sanin gaibu sai Allah. Dama baida kowa bai kuma aje kowa ba. Ta dai yi iya bincikenta, amma ta rasa inda ya je.
Haka ma wayarsa sam! Ba ta aiki. Dole ta bi shawarar Hajiya Rakiya na canja waje zuwa wajen wani Malamin tsubbun, don haka a yanzu shi take ta lafta ma kudi.
Amma har yanzu babu biyan bukata kuma kullum yana gaya mata bukata za ta biya, kada ta sami damuwar komai, amma tabbas hankalinta ba’a kwance yake ba.
Masu Karatu, kun dai ji, ko in ce ku na kan jin irin
wannan Kalubale na rayuwa da badakala. Shin ya za ta kaya ne? Me zai faru nan gaba?
Mun san dai rigimar duniya da mai rai ake yi, wannan labari kuma yanzu aka faro shi. ,
mu je zuwa!