MUSABBABI CHAPTER 17 BY HAJ HABIBA
aureka a haka. Don haka wanda ya aureka akan wannan dalilin, ne ya sa ka ke son rabuwa da shi akan irin dalilin?” Ta hadiye yawu ta ci-gaba da magana. “Dduk abinda ka ke hange akan rayuwata a dalilin auranka, ni ma na hangi irinsa kafin na aureka, amma kai ne mijin da Allah ya Kaddara min, kuma kai ne wanda na ke fatan na gama rayuwata da kai a matsayin mijina.” Haka nan wani dadi ya bakunci zuciyar Musaddik, wani irin so da Kaunar Afrah me tsanani ya Kara samun wajen zama a cikin zuciyarsa, darajarta da kimarta suka Kara fadada a ransa, ta zuba idanunta a cikin masa, sannan ta ci-gaba da magana. “Eh, na yarda a lokacin da na aureka, biyayya ce da son cika buri da umarnin mahaifina. Amma babu soyayyarka a zuciyata, amma a yanzu ina tabbatar maka da cewa zuciyata cike take da soyayyarka, ina sonka da zuciya daya, ba kuma na fatan rabuwa da kai, don halayenka munana. Yadda na sanka da a kullum, ina sa ran wata rana za ka koma haka. Na kuma amshi komai a matsayin kaddarar rayuwata, don haka ni…