MUSABBABI CHAPTER 17 BY HAJ HABIBA

 

aureka a haka. Don haka wanda ya aureka akan wannan dalilin, ne ya sa ka ke son rabuwa da shi

akan irin dalilin?”

Ta hadiye yawu ta ci-gaba da magana. “Dduk abinda ka ke hange akan rayuwata a dalilin auranka, ni ma na hangi irinsa kafin na aureka, amma kai ne mijin da Allah ya Kaddara min, kuma kai ne wanda na ke fatan na gama rayuwata da kai a matsayin mijina.”

Haka nan wani dadi ya bakunci zuciyar

Musaddik, wani irin so da Kaunar Afrah me tsanani ya Kara samun wajen zama a cikin zuciyarsa, darajarta da kimarta suka Kara fadada a ransa, ta zuba idanunta a cikin masa, sannan ta ci-gaba da magana.

“Eh, na yarda a lokacin da na aureka, biyayya ce da son cika buri da umarnin mahaifina. Amma babu soyayyarka a zuciyata, amma a yanzu ina tabbatar maka da cewa zuciyata cike take da soyayyarka, ina sonka da zuciya daya, ba kuma na fatan rabuwa da kai, don halayenka munana. Yadda na sanka da a kullum, ina sa ran wata rana za ka koma haka.

Na kuma amshi komai a matsayin kaddarar rayuwata, don haka ni ba zan rabu da kai ba, zan zauna tare da kai da dadi ba dadi, zan ci-gaba da yi maka addu’ a tare da zama mata ta-gari a gareka.

“Kaji shawarar da na yanke.” Ta gyara zamanta ta ci-gaba da cewa “Ya rage naka, ka kyautata min tare da sauke hakkin da ke kanka nawa. Ko yin akasin haka.”

Tana gama fadin haka, ta yi gaggawar tashi za ta shiga uwardaka, a gaggauce Musaddi& ya sa hannu ya riko hannunta gami da janyota gaba daya ta fado jikinsa, a zafafe ya sa hannayensa biyu duka ya rungumeta tsam! A kirjinsa tamkar zai tsaga jikinsa, ya sanyata a ciki. Haka nan ya sami kansa da kuka sosai, hawayensa na sauka a gadon bayanta.


A cikin kuka yake magana. “Afrah na so na ba ki farin-cikin da ki ke bukata, na so na natsu, na koma mutum na-gari, saboda soyayyarki, ke ta daban ce Afrah, ina sonki fiye da dukkan tunaninki”. Ita ma cikin hawayen take magana. “Ni ma ina sonka Yaya Musaddik, kuma zan iya zama da kai a cikin kowane hali da yanayi.”

Musaddik ya ce, “Kaunarki ita ce ta sa na ke miki hangen kyakkyawar rayuwa a wani wajen, don na san ba za ki yi farin-ciki tare da ni ba”. Ta ce

“Kayi kuskure, domin da kai kadai zan iya zama na

 

sami farin-ciki.Musaddik ya dagota yana kallon

fuskarta gami da goge hawayen da ke zuba mata yace.Ba zan yi miki alkawarin zan daina duk abinda na ke ba, amma zan yi Kokari na dainan ba tare da na yi miki alkawari ba.” Afrah tayi ajiyar zuciya ta ce “Allah ya tabbatar da hakan”. Yace

“Amin. Allah ya Kara ba ki hakuri da juriyar Zama dani”

‘. Ta gyara zamanta a saman cinyarsa.

• Ta ce “Amma ina da shawara daya.” Ya ce

“Na mene?” Ta dan dube shi fuska sake, sannan ta ce “Me zai hana ka nemi aikin yi, ka na da takardunka, tun daga Primary har Masters.

A yanzu ne za su yi maka amfani, samun aikinka zai rage abubuwa da dama, kuma hanya ce ta samun natsuwarka, wannan zaman babu aiki, shi ne musabbabin Kara lalacewarka”.

Ya kamo hannunta ya rike yana kallonta ya ce, “Wannan yana daya daga cikin maganar da na ke son na yi da ke, saboda na nemi shawararki, don yanzu ba abinda zan yi ba tare da shawararki ba, don na fahimci ban da kowa duniya, sai ke”

Tajil dadin maganarsa, ta yi murmushi ta ce,

“To ya aka yi?” Ya gyara zamansa ya kwashe duka yadda suka yi da Hajiya Hudah ya gaya mata, “Har mijin nata na fahimci yana matukar son na karbi aikin, sai dai ina ganin kamar aikin yana da hatsari, kuma ba zan sami lokacin kaina ba”

Afrah ta runtse idanunta cike da fara’a ta ce,

“Ai rashin samun lokacin naka, shi zai sa ka nisanci abokanka na banza, ya kuma nisantaka da aikata halayen banza, tunda cikin jama’ar kirki za ka dinga shiga, dole ka dinga jin nauyin aikata abubuwan da suka saba ma nasu halayen.’

Ta dan aje numfashi ta ce, “Sai dai ban so irin wannan aikin ba, yadda ka ke da takardunka, na so ace aiki zaka samu daidai da karatunka, amma wannan din ma.Allah ya yi masa albarka da zaman banza, ai gara wannan din, , sai dai duk da haka, ka bazama. neman aiki, a duk lokacin da ka samu aikin, sai ka aje mata aikin ta, ka rungumi wanda ka samu”.

Musaddik ya gyara kai ya ce, “Na gamsu da maganarki, zan nemi abokina Murtala na ba shi, domin ya tayani neman aikin.” Ta ce “Da kyau

Yaya Musaddik, godiya na ke da karbar shawarata.

» Ya sa hannavensa ya rungumeta. A wannan daren.

Afrah da Musaddi& sun raya shi da jin dadin juna da faranta rai, domin tunda suka yi aure ba su taba jin dadin juna irin na wannan daren ba, saboda zuciyoyinsu fes! Suke.

Ba su da sauran wata damuwa ko jin zafin juna, haka zalika soyayyar junansu ta riga ta zauna a cikin zukatansu yanzu. Allah kenan, mai sauya lamura, duk sanda ya so. Washegari karfe biyu na rana Musaddik yana gaban ofishin da Murtala ya koma, tun bayan barinsa kamfanin Musaddik. Ya ji dadi ya kuma yi murna da ganin Musaddik har ya yi tunanin neman aikin yi. A zahiri sai yanzu ya fara sa ran shiryuwar Musaddik, a dalilin auransa, abinda ya dade yana addu’ ar tabbatarsa.

Ya dubi Musaddik ya ce, “Na ji dadi kwarai.

Inshaa Allahu kuma zan yi iya kokarina wajen nemar maka aiki, domin ba zan taba mantawa da irin taimakon da ka yi min ba a lokacin da na ke aiki a kamfaninka, ba ka daukeni ma’aikacinka ba, ka daukeni aboki, kuma amini, kuma kaddara da karayar arziki babu wanda ya gagara Allah ya jarabce shi.

Musaddik ya jinjina kai, karo da yawa kenan daya tuna irin daula da arziki da dimbin dukiyar daya mallaka a baya, wanda babu takamaiman abinda zan iya fadi, na dalilin faruwar hakan ba.”

Ya ce “Haka ne Murtala na gode kwarai da gaske. Allah ya taimaka.” Murtala ya ce, “Allah ya shirya mana kai ka dawo da irin rayuwarka ta asali.”

“A hankali ya ce “Amin Murtala, na gode”.

Dai-dai lokacin wayarsa ta kunnansu gami ta sallama, daga can daya bangaren Alhaji Yusuf Sanda ya yi gyaran murya ya ce,Alhaii Yusuf

Sanda ke magana” Musaddik ya gyara zamansa ya ce,

“Alhajin Allah barka da rana. Ya amsaYauwa ka na

lafiya?” Ya amsa “Lafiya Kalau.” Alhaji Yusuf

Sanda ya ce.Na sami lambarka a wayar Hudah ne, sannan na kiraka ne, domin naji shawarar da ka yanke akan aikin da Hudah ta ba ka, saboda ni gobe zan koma Paris, shi ya sa nake son na ji, inda aka kwanan a maganar.”

Musaddik cike da mamakin yadda ya ga

Alhaji Yusuf ya damu da lamarin aikin, wanda shi a ganinsa bai ga dalili ba. Musaddik ya dan muskuta ya ce “Ba damuwa, na ji, na kuma amince zan yi aikin.”

Alhaji Yusuf ya yi murmushi sosai gami da gyada kai yace, “To shi kenan, sai ka bullo zuwa yamma, domin ka ji yadda tsarin aikin yake”. Ya ce

“To na gode, sai na’ zo.” Lokacin daya suka aje wayoyin, a yayin da Murtala ya dubi Musaddik ya ce,

“Waye?”Ya ce.Alhaii Yusuf Sanda ne. Mai-gidan

Hajiya Hudah, akan aikin da na yi maka bayani, shi ne ya kirani, na gaya masa na riga na amince.”

Murtala ya numfasa ya ce.

“A gaskiya ka yi taka-tsantsan! Kuma ni na ma kasa gane wane irin miji ne Alhaji Yusuf Sanda, wanda baya kishin matarsa, har neman me kare lafiyar matarsa yake a bayan idonsa. Musaddik ya ce, “Ni kaina abin yana daure min kai, ya damu kwarai da maganar aikin”.Murtala ya ce,Koma dai menene, ka sani dole sai

ka natsu ka san abinda ka keyi.”

Ya ce, “Haka ne Murtala, na kuma gode da shawararka, zan kuma kula sosai”

Murtala ya ce “Sai dai fa babbar dama ce ta sameka ta yin aiki a Karkashin mace kamar Hajiya Hudah *Yar Majalisa, ko da ban san nawa ne albashin da za ta yanka maka ba, na san za ka sami damar wadata iyalinka, aikin kuma zai sa ma maka daraja da kima. Allah ya taimaka.”

, Ya ce, “Amin na gode.” Daga nan suka ci-gaba da tattaunawa har zuwa lokacin da Murtala ya tashi aiki, daga nan suka dunguma tare suka tafi.

Wajen karfe biyar Alhaji Hamza ya zo har kofar gidansu Musaddik ya dauke shi zuwa gidan hajia Hudah. Ta sha kwalliya sai walkiya take yi, gafenta Alhaji Yusuf Sanda ne.

Haiiya Hudah ta rasa dalilin da ya sa take rasa natsuwarta, duk lokacin da Musaddik ke gabanta.

Kuma ko mutane sun kai dubu, ta kan ga Musaddik ya bambanta da kowa, musamman wajen kwarjini.

Sun tattauna sosai akan aikin, sai dai Musaddik ya nuna mata ba zai dinga kwana a gidanta ba.

Domin shi ma yana da iyali, kuma duk wata tafiya da za ta yi, idan ta kwana ce, ba za shi ba, kuma zai dinga tashi aiki karfe shida zuwa bakwai na yamma, idan sun amince da wannan sharadin, to zai yi aikin, idan kuma ba su amince ba, to a bar shi kawai.

Zahiri Hajiya Hudah tana matukar son ganin

Musaddik kusa da ita, wannan aikin ma ta dai bukaci ya yi ne kawai, amma tana da ‘Yan Sandanta masu gadin gidanta.wadanda take tafiya tare da su, don haka wannan sharadin na Musaddik, bai dameta ba. Don haka ta yi saurin amincewa. Kafin Alhaji Yusuf ya yi magana ta ce.

“Ba damuwa Musaddik, duk sharuddanka na

Ji, na kuma amince.” Alhaji Yusuf ya ce, “Tunda ta amince, shi kenan”. Musaddik ya ce,Na gode.”

Hajiya Hudah ta ce.Dama saboda na tabbatar na yi tafiya da kai a cikin siyasata, bayan na ci zabe, ya sa na ba ka wannan aikin, saboda ka sami abinda za ka dinga ciyar da iyalinka, ba tare da ka ci-gaba da yin bangar siyasa ba”Alhaji Yusuf ya ce

“Don bangar siyasa ba ta

dace da kai ba, amma ka ga yanzu rayuwa za ta yi maka sauki, kuma kamar yadda ta fada ne, saboda ta taimaka maka ne, domin kamar yadda ka ke gani, akwai ‘Yan Sanda masu kula da ita, saboda haka babu komai, sai ki gaya masa nawa ne albashinsa”.

Hajiya Hudah ta ce, “Duk wata zan dinga ba ka’ Naira dubu hamsin, ina fatan sun yi?” Musaddik ya cika da farin-ciki, cike da fara’a ya ce, “Na gode, ya yi, na gode kwarai da gaske.” Daga nan Alhaji Yusuf ya mike yana murmushi ya shige daki, a yayin da Hajiya Hudah ta ci-gaba da tattaunawa da Musaddik. Hakika Afrah ta fi kowa jin dadin samun aikin Musaddik, domin har Ya Sayyadi Habib ta gaya ma a lokacin da ta je Islamiyya, shi ma ya ji dadi kwarai, daga Islamiyya kuwa bayan an tashi gida ta wuce.

Babu wata kyakkyawar tarba da ta samu da gun Mama Hauwa, sai ma harare-harare da kumbure-kumbure da take yi. Ita kuwa Na’ ima. dama ba ta nan, ta tafi Suleja bikin kawarta.

Haka Afrah ta ci-gaba da zama a darare, tana zaman jiran mahaifinta, yana ko dawowa, ta gaya masa maganar samun aikin Musaddik har da iya adadin albashin da zai dinga kwasa duk wata.

Mama Hauwa na gefe tana ji, bakin-ciki ya cika mata ciki taf!

Yaushe Musaddik har ya yi hankalin da zai yi tunanin neman aiki, kuma aikin ma me tsoka, ko ba komai yana tare da manya. Hajiya Hudah ‘Yar Majalisa guda, ai alheri kala-kala ya dinga samu kenan daga gareta.

Zahiri ba ta ji dadin wannan al’amari ba. A yayin da Malam Mahmud farin-ciki ya cika zuciyarsa ya ji dadi sosai, ya kuma yi masu addu’ a ta-gari, tabbas tun bayan auransu da Afrah.

•Sai yanzu ya dan fara samun natsuwa. Ya so kwarai ta tsaya ta ci abincin dare, tunda an kusa gama tuwo, amma Afrah ta ki, saboda yadda ta ga Mama Hauwa na yi.

Hmmm