MUSABBABI CHAPTER 16 BY HAJ HABIBA

MUSABBABI CHAPTER 16 BY HAJ HABIBA musabbabin hada auranku, don haka zai taimakemu, kada ki yanke tsammani, ki sa a ranki shi komai lokaci ne. Don haka idan Allah ya kawo iyakar lamarin. Shi kenan, sai ki ga kamar ma ba’a taba yi ba. Shiriya da batarwa duk suna hannunsa, wanda kuma Allah ya 6atar. Idan duk duniya za ta taru ba su isa su shiryar da shi ba, wanda kuma ya shiryar, babu wanda ya isa ya batar da shi, komai yana wurin Ubangiji. Mummunar kaddara da kyakkyawar kaddara, duk daga gare shi ne. Shi ya sa ya ce mu yi imani da kaddara me kyau ko mara kyau. Saboda haka ki sa Musaddik da lamarinsa a matsayin Kaddarar rayuwarki, ki yi hakuri, ki yi komai domin Allah, sai ki ga Allah ya taimakeki. Ki ci-gaba da yi masa nasiha da addu’a tare da biyayya a matsayinsa na mijinki, wanda duk lalacewarsa. Aljarnarki tana karkashin kafarsane.” Cikin hawaye Afrah ta ce. “Na ji, na gode kuma za ka sameni me biyayya tare da tsare dokokin aurena” • A hankali ya ce “Allah ya yi miki albarka, ya ba ki abinda k…