MUSABBABI CHAPTER 16 BY HAJ HABIBA

MUSABBABI CHAPTER 16 BY HAJ HABIBA

 

 

musabbabin hada auranku, don haka zai

taimakemu, kada ki yanke tsammani, ki sa a ranki shi komai lokaci ne.

Don haka idan Allah ya kawo iyakar lamarin.

Shi kenan, sai ki ga kamar ma ba’a taba yi ba.

Shiriya da batarwa duk suna hannunsa, wanda kuma Allah ya 6atar.

Idan duk duniya za ta taru ba su isa su shiryar da shi ba, wanda kuma ya shiryar, babu wanda ya isa ya batar da shi, komai yana wurin Ubangiji.

Mummunar kaddara da kyakkyawar kaddara, duk daga gare shi ne. Shi ya sa ya ce mu yi imani da kaddara me kyau ko mara kyau.

Saboda haka ki sa Musaddik da lamarinsa a matsayin Kaddarar rayuwarki, ki yi hakuri, ki yi komai domin Allah, sai ki ga Allah ya taimakeki.

Ki ci-gaba da yi masa nasiha da addu’a tare da biyayya a matsayinsa na mijinki, wanda duk lalacewarsa. Aljarnarki tana karkashin kafarsane.” Cikin hawaye Afrah ta ce. “Na ji, na gode kuma za ka sameni me biyayya tare da tsare dokokin aurena”

• A hankali ya ce “Allah ya yi miki

albarka, ya ba ki abinda ki ke nema duniya da lahira”

Ta amsa da “Amin Baba.” Sannan suka aje wayar lokaci daya. Mama Hauwa da take tsaye tun bayan daya fara wayar, ta yamutsa fuska ta wuce

abin ta. Domin tun daga ranar da Malam Mahmud ya yi mata takarar kada ta Kara shiga harkar Afrah da auranta, ta daukar ma kanta alkawarin ba za ta Kara sa bakinta ba. Ko da kome zai faru. Hakan ya sa duk da ta san meke faruwa, ba ta yi magana ba, balle ta jajanta. Babu abinda ya dameta.

Afrah ta yi mamakin yadda Musaddik ya ki fita ko’ina, tun bayan dawowarsa, barci kawai yake yi, ko wayarsa bai bude ba. Hakan ya sa bai san irin neman wayarsa da Alhaji Hamza yake yi ba, har sai wajen karfe goma na dare daya bude wayarsa, yana budewa, wayar Alhaji Hamza tana shigowa.

Bayan ya dauka, tambaya Alhaji Hamza ya jefo masa, “Meye dalilin kashe wayarka? Bayan ka tafi ba tare da kayi sallama da kowa ba?” Ya dan runtse idanunsa yace.Na gaji ne, barci na yi, shi ya sa ban bude wayar ba, ya. aka yi ne Alhajin Allah?’ Daga nan Alhaji Hamza ya gaya masa bukatar Hajiya Hudah na amsa gayyatar Party din murnar cin zabenta.

Musaddik ya jinjina kai ya ce. “Karfe nawa ne goben?” Ya ce, “Karfe bakwai na yammaci, wannan gayyatar ta musamman ce, da fatan za ka amsa?” Ya gyada kai ya ce. “Babu damuwa. Allah ya kai mu.Daga nan suka yi sallama. Hakika yana son. mutum me cika alkawari, daga dukkan alamu kuma Hajya Hudah mace ce me cika alkawari, da alama.wannan gwamnatin za ta amfane shi.Washegari kuwa tun karfe bakwai da rabi.

Musaddik ya isa tankasheshen (Hall) din da ake gabatar da liyafar, haka zalika duk da dimbin jama’ar da ke wajen, sai da Musaddik ya samu tarba ta musamman daga Hajiya Hudah.

Wacce ta ci kwalliya da kaya masu matukar daukar hankali. Daga wuyanta zuwa kunnenta da yatsun hannayenta duk zinare ne, sai daukar ido suke, ta sha kyau har ta gaji.

Cike da farin-ciki da annashuwa ta dubi mutumin da ke gefenta, wanda shi ma yake cikin shiga ta alfarma, ta nuna Musaddik ta ce. “Yallabai ga mutumin da na ke ba ka labarinsa da irin taimakon da ya yi min tun a waya. Musaddik”

Mutumin ya dubi Musaddik ya yi masa kallo daga sama har kasa, sannan ya ce Sannu Musaddiq

mun gode da Kokarinka, duk da komai an yi shi ba na nan, to na sami labarin duk kokarin da ka yi da kuma hatsarin da ka tsallake, sannu da kokari”

Musaddik ya yi murmushi, domin ya ji dadin yadda a yau aka maida shi mutum mai daraja, wanda rabonsa da ganin hakan har ya manta, ya dubi mutumin ya ce “Haba ai babu komai, ni ma na gode”. Hajiya Hudah ta dubi Musaddik ta ce « Musaddik wannan shi ne mijina. Alhaji Yusuf Sanda” Musaddik ya yi gaggawar kara bude idanunsa cike da matsanancin mamaki, ya Kara duban Alhaji Yusuf Sanda ya ce “Mijinki?” Ta amsa masa da Eh, shi ne mijina.”

Ya Kara kallonsa ya ce “Sannu Mai-gida, da fatan ka na lafiya? Alhaji Yusuf Sanda ya Sara Kura masa ido tamkar yana wani tunani, sannan ya ce

“Lafiya kalau Musaddik. Daga nan ya wuce a hankali zuwa kujerar da zai zauna, a yayin da Alhaji Yusuf Sanda ya bi shi da kallo.

Har aka yi liyafar nan aka tashi Musaddiq. yana cikin matukar mamakin kasancewar Hajiya

Hudah matar aure, domin koda wasa bai taba kawowa a ransa cewa Hajiya Hudah matar aure. bace, domin babu alamar hakan. Kwarai ya so kebewa da Alhaji Hamza, don kuwa haka nan ya ji yana son sanin wasu abubuwa game da Hajiya Hudah.

Amma hakan ba ta samu ba har sai da ya yi sallama da Hajiya Hudah, ta kuma bukaci tana son ganinsa gobe karfe sha biyu na rana, kafin ta wuce Abuja.

Ya kan rasa irin kallon da Alhaji Yusuf Sanda yake tsare shi da shi. Sai da zai tafi ne, sannan Alhaji Hamza ya dauke shi, domin ya kai shi gida a bisa umarnin Hajiya Hudah. A lokacin kuwa karfe biyu saura kwata ne na dare, sun dan yi nisa da fara tafiya, sannan hakurin Musaddik ya gaza, inda ya dubi Alhaji Hamza ya ce “Alhajin Allah, dama Hajiya Hudah matar aure ce?” Alhaji Hamza ya dan saki numfashi, sannan ya ce “Matar aure ce mana, kai ba ka san hakan ba?”

Ya girgiza kai ya ce. “Ban san hakan ba, ban kuma taba tsammanin hakan ba, domin ban dade ina yin hulda da ita ba, kuma kai na sani akan harkokinta.

Tunda kai ne ka nemeni akan aikin nata.

Sannan kuma yanayinta da yadda take gawutacciyar

*yar siyasa da yadda take gogaggiyar mace, ban taba tsammanin mace irinta za ta iya zaman aure a karkashin wani ba, musamman ma yadda take da masu gidan rana a hannunta.”

Alhaji Hamza ya yi dan murmushi ya ce.

“Haka ne maganganunka, amma lalle ka na bukatar ka san wace ce Hajiya Hudah, domin ka kore ma kanka shakka akan rayuwarta, amma dare ba zai ba mu damar na tsaya na gaya maka wace ce ita ba.

Sai dai abu daya zan gaya maka, tabbas duk da dukiyar da Allah ya ba ta, to fa Allah ya jarabceta da son yin aure, domin cikar kamalarta, kuma tabbas Alhaji Yusuf Sanda a yanzu shi ne mijinta.”

Musaddik ya dube shi ya ce, “To amma a matsayinsa na mijinta, me ya sa ba’a san shi ba, musamman akan lamuranta na siyasa, me ya sa kuma har muka sami damar kwana a cikin gidansa, ba tare da mun gan shi ba, sannan duk abubuwan siyasa, me ya sa babu shi a ciki?”Alhaji Hamza ya amsa. “Mun kwana a gidan

‘sa ne a dalilin ranar baya ma kasar, yau din nan da rana ya sauka, yana Paris, duk wannan badakalar siyasar.”Me yake yi a Paris? Da ya fi masa shiga harkar matarsa, a lokacin da take da bukatarsa?”

«Saboda can din ma a aikinta yake yi, domin kusan shi yake rike mata da kasuwancinta na kasashen waje, don haka bai cika zama ba a Najeriya, kusan duk sabgoginsa ya fi a kashashen waje.

Musaddik ya jinjina kai, ya yi shiru ne kawai, ba don wai tambayoyinsa sun kare a kan Hajiya Hudah ba, a’a sai don bai ga dalilin da zai zauna yana tambaya akan matar da baida wata mu’ amula ko dangantaka da ita ba, don haka ya ja bakinsa ya tsuke har suka kai kofar gidansa. Sannan ya yi ma Alhaji Hamza godiya, ya shiga buga get din.

Baba Mai-gadi ya bude, domin ya san

Musaddik ne ya shigo. Abu daya ya yi ma Baba Mai-gadi dadi, shi kuma ya hana ya yi masa fada kamar yadda ya saba kullum, wato ganinsa cikin hayyacinsa, babu alamar ya sha wani abu balle ya bugu. hayyacinsa, babu alamar ya sha wani abu balle ya bugu.Ya shiga ya tadda Afrah tana kan sallar nafila, don haka ya wuce uwardaka ya kwanta zuciyarsa cike da tunanin Hajiya Hudah, da yadda tana matar aure, ta zabi shiga harkar siyasa gami da nadamar kwanan da ya yi a gidanta, domin tabbas daya san matar aure ce, babu yadda za’ayi ya amince ya kwana a gidanta, domin kuskure ne babba yin hakan.

Karfe goma sha biyu dai-dai na rana. Musaddif ne ke zaune a falon Haiiya Hudah, kan dayar kujerar me zaman mutum biyu. Hajiya Hudah ce zaune ita da Mai- gidanta Alhaji Yusuf Sanda. Hajiya Hudah ta dan muskuta ta gyara zamanta, sannan ta ci-gaba da magana.Irin kokarin da aka yi da kuma alkawarin da na yi maka cewa ba zan taba mantawa da kai a cikin tafiyata ba, ya sa a daren jiya na yi shawara da mijina, ya kuma amince shi da kansa ma ya kawo shawarar irin aikin da ya kamata ka yi a karkashina, domin kamar yadda. Alhaji. Hamza ya yi min bayani, ba kada wani aikin yi.”Ya gyada kai ya ce, “Haka ne.” Ta dan dubi Alhaji Yusuf a lokacin da yayi dan murmushi da kallon Musaddik, sannan ya ce, “Zuciyata ta sami natsuwa da kai, tun daga ganina da kai na farko, na kuma gamsu da lamuranka, don haka na yanke shawarar za mu daukeka a matsayin me kare lafiyar Hajiya Hudah, na musamman”.

Musaddik ya yi gaggawar kallonsa, a yayin da ya gyada kai ya ce,

“Eh, Musaddik, idan ka karbi wannan aikin, zan fi kowa farin-ciki, zan kuma fi kowa samun natsuwa, domin akalla na san matata tana tare da mutum irinka,’ wanda zai iya kare lafiyarta, koda a bayan idona ne, wannan aikin ina rokonka da karbe shi, domin kai ma ci-gabanka ne. Hajiya Hudah ta dan aje numfashi, sannan ta ce, “Kada ka damu da albashi, domin zan yaka maka albashi mai tsoka, wanda zai isheka daukar

•dawainiyar kanka da iyalinka, tunda dama Alhaji Hamza ya gaya min matarka daya ba ka da da kuma, don haka abu ne mai sauki, albashinka zai jiyar da matarka dadin da kowace mace ke mafarkin samu.”

Alhaji Yusuf Sanda ya ce, “Ka ga ka huta da zaman banza, wanna wata hanya ce ta ci-gabanka, don haka me ka gani? Ina fatan ba za ka ki karbar wannan garaba sa ba?”Musaddik, ya gyara zamansa, ransa da zuciyarsa cike da dimbin tunanin wannan aikin, sannan ya ce, “Na ji bayananku da gaske, amma ina bukatar dan lokacin da zan yi tunani.” tunanin duk kuma abinda ka : yanke, ina sauraronka.”

” Alhaji Yusuf ya ce, “Ina fatan duk

tunanin da za ka yi, Karshe ya zama eh ce amsarka, saboda aikin zai yi maka amfani.” Ya gyada kai ya ce, “Na gode, ba damuwa Mai-gida.” Daga nan ya tashi. “Ni zan tafi.”

Alhaji Yusuf ya karkace, ya dauko kudi masu yawa a aljihunsa. ya mika masa. “Ga shi ka shiga mota”. Ya karba gami da godiya, sannan ya fice. A yayin da Hajiya Hudah ta bi shi da wani irin sansanyyan kallo, shi kuma Alhaji Yusuf Sanda ita yake kallo gami da jinjina kai.

A ranar da wuri Musaddik ya koma gida, bai bari ya yi daren da ya saba ba, saboda yana so ya yi magana da Afrah, musamman akan shawarar da ya ce ta yi. Yau ita ce rana ta biyu. Afrah na zaune akan kujera, zuciyarta cike da tunane-tunane.

Musaddik ya yi sallama ya shigo, cike da mamakin dawowarsa da wuri, ta amsa sallamar, ya shigo ya zauna a kujerar da take fuskantarta.

Bayan ta yi masa sannu da zuwa ne, ta tashi domin ta dauko masa abinci, ya dubeta ya ce “Ina za ki je?” Ta dan dube shi ta ce, “Zan je na dauko maka abinci ne”

Ya girgiza kai, ya ce “Dawo ki zauna, ki yi hakuri ba na jin dadin ciki na, ba zan ci abinci ba”.

Ta dawo a hankali ta zauna tana kallonsa, zuwa dan wani lokaci Musaddik ya fara magana. “Afrah ina son na ji shawarar da kika yanke akan maganar da nayii dake shekaran jiya?” Ya fadi maganar ne cikin faduwar gaba, domin bai san dalilin da ya sa ya sami kansa da addu’ ar Allah ya sa ba ta zabi rabuwa da shi ba.

Ta dube shi sosai, sannan ta ce “Me ya sa ka ke so ka rabu da ni kai?”

Ya kalleta a hankali ya ce

“Kin fi kowa sanin dalili. Afrah kin san ni da ke ba mu dace ba, ki nada dukkan hali na-gari, miji irina bai dace da ke ba.

Ina yi miki kwadayin samun ingantacciyar rayuwa ne da ke da ‘ya yan da za ki haifa, na san kuma gareni babu wata ingantacciyar rayuwar da za ku samu. A zahiri ina da dalilai na masu matukar yawa”

Afrah ta yi dan murmushi, sannan ta ce, “Shin ka san musabbabin aurena da kai, da kuma dalilin daya sa na aureka?” Ya girgiza kai ya ce, “Ban sani ba, amma na san duk wani musabbabi, ba zai wuce bin iyaye ba.”

Ta gyada kai ta ce, “Ba zan ce babu ba, tabbas akwai biyayya a ciki, amma ina son ka sani, na aureka ne saboda rashin kamun kanka.

• Na aureka ne saboda ba ka da halin kwarai, akan kyakkyawar niyyar mu na kokarin saka ka hanya ta-gari, ba kamun kanka na aura ba, balle ka ce ba ka da kamun kanka, za ka rabu da ni, duk halinka, ba wanda ban sani ba, na kuma yarda na

Hmmmm