MUSABBABI CHAPTER 15 BY HAJ HABIBA

MUSABBABI CHAPTER 15 BY HAJ HABIBA Cikin hawaye Afrah ta ce “Allah ya saka mata da alheri.” Ta koma ta zauna, tana kallonsa, a yayin da ya maida rigarsa ya koma shi ma, ya zauna. Zuciyar Afrah ta cika da kaunarsa, domin ba ta tabbatar ma kanta ta fara son Musaddi ba, sai da baya gidan, har take kuma tunanin yana cikin wani hali, a hankali ta ce. “To yanzu meye amfanin wannan rayuwar, don Allah Yaya, don darajar Annabin rahama ka natsu, kai fa ba Karamin yaro bane, ka dubi irin shekarun da ka ke da su, ka sani da kyar ne idan za ka Kara shekarun da ka yi a baya, ka gyara rayuwarka, ka koma yadda ka ke da, irin wacce ka yi a baya. Ka gyara rayuwarka, ka koma yadda ka ke da. Ka yi yaki da shaidan. Ka rabu da abokanka na banza, ka koma ma abokanka na da, na-gari, ka yi tsaftatacciyar rayuwa. Ko ka dawo da kima da darajarka da ka rasa, wannan ba irin rayuwarka bace, ba ta kuma dace da kai ba ko kadan. Shin ya za ka yi da ‘ya’ yanka, idan ka fara haihuwa?” Musaddik ya yi kasa da kansa, zuciyarsa n…