MUSABBABI CHAPTER 15 BY HAJ HABIBA

MUSABBABI CHAPTER 15 BY HAJ HABIBA

 

 

Cikin hawaye Afrah ta ce “Allah ya saka mata da alheri.” Ta koma ta zauna, tana kallonsa, a yayin da ya maida rigarsa ya koma shi ma, ya zauna.
Zuciyar Afrah ta cika da kaunarsa, domin ba ta tabbatar ma kanta ta fara son Musaddi ba, sai da baya gidan, har take kuma tunanin yana cikin wani hali, a hankali ta ce.
“To yanzu meye amfanin wannan rayuwar, don Allah Yaya, don darajar Annabin rahama ka natsu, kai fa ba Karamin yaro bane, ka dubi irin shekarun da ka ke da su, ka sani da kyar ne idan za ka Kara shekarun da ka yi a baya, ka gyara rayuwarka, ka koma yadda ka ke da, irin wacce ka yi a baya.
Ka gyara rayuwarka, ka koma yadda ka ke da.
Ka yi yaki da shaidan. Ka rabu da abokanka na banza, ka koma ma abokanka na da, na-gari, ka yi tsaftatacciyar rayuwa.
Ko ka dawo da kima da darajarka da ka rasa, wannan ba irin rayuwarka bace, ba ta kuma dace da kai ba ko kadan. Shin ya za ka yi da ‘ya’ yanka, idan ka fara haihuwa?”
Musaddik ya yi kasa da kansa, zuciyarsa na tafasa tana kuna, yana matukar jin nauyinta yana jin kunyarta, haka zalika yana matukar son ya yi mata abinda take so, amma ya kasa, hakan shi ke jefa shi cikin fushi da tafasar zuciya, idanunsa sun yi jajir!
Ya dago ya dubeta ya ce. “Afrah, ki na tunanin wannan abin baya damuna ne? To duk duniya ba wanda yake damu kamar wannan, ina cikin matsananciyar damuwa, tun bayan aurena da ke.
Burina bai wuce na kintsu ba, saboda na san abinda ki ka yi min na aurena a lokacin da babu wata mace me hankali irinki da za ta iya aurena.
Amma na kasa barin koda abu daya, wannan lamarin yana damuna”
Ta gyada kai ta ce “Tunda har ka na so ka daina, to ka sa ma zuciyarka za ka iya dainawa, ka yi yaki da shaidan, ka jajirce. Duk abinda ka ga bawa bai iya ba, to bai sa kansa bane, don haka idan kasa kanka. Tabbas! Allah zai taimakeka, ka tuna fa kai maraya ne, sanda ya kamata ka taimaki kanka da iyayenka, ka kasa, na yi imani ko addu’arka ba sa samu.
Dukiyar da suka bar maka, ba ka kirkinta ba, rashin natsuwarka ya sa an rabaka da komai, saboda an san babu abinda za ka iya yi, don ba ka amfani kanka ba ma, balle ka amfani dukiyarka. Wannan babu inda zai kai ka. Shekara da shekaru ka na cikin wannan mugun hali, ba ka ko tunanin gaba.’ Maganganunta sun yi tasiri a zuciyarsa, sai dai babu amfanin da za su yi masa.Maganganunki
gaba daya haka ne, amma ni na san ba zan taba iya dainawa ba, ki yi hakuri.
.” Afrah ta goge hawayenta,
a yayin da ya ci-gaba da magana. “Shi ya sa ban so a kashe rayuwarki ta hanyar aurena ba, na san ba ki dace da ni ba, ba ni ya kamata ki zauna ki yima biyayya gami da bauta ba a matsayin mijinki, ban so ace nine me cutar da ke ba.
Domin na san a iya tsawon watannin da ki ka dauka tare da ni. Ba ki taba samun wani farin-ciki daga gareni ba, ban taba faranta miki ba, don haka bai kamata na ci-gaba da tauye rayuwarki ba.
Hakan ya sa zan kawo wata shawara tsakanin mu.”
Afrah ta Kara goge hawayenta ta ce “Wace shawara ce?” Ya dan gyara zamamsa gami da hadiye wani zazzafan yawu, alamar shi kansa abinda yake son ya furtan, ba me dadi bane a gare shi, ya dade yana Kure mata da ido sannan ya. ce,
“Shawarar rabuwa.”
Ta yi gaggawar kallonsa gami da bude baki, ta maimaita Rabuwa?” Ya gyada kai ya ce “Eh, saboda bai kamata ki lalata rayuwar ki akan rayuwata ba, amma zan ba ki kwana biyu, ki yi tunani
Domin sai da amincewarki, komai zai yiwu, amma ina son idan za ki yi tunanin, ki cire tausayina ki aje shi a gefe, domin na san shi kadai ne a ranki, babu so-na.
Ki sa a ranki hukuncin da za ki yanke me kyau, shi ne zai ba ki damar auran wanda ki ke so, kuma ya dace da rayuwarki, ki haifi ‘ya’ya daga tsatson uba na-gari. Don Allah kada ki yi tunanin tausayina da taimako na a cikin tunanninki, ni kuma duk abinda ki ka yanke, da shi zan yi amfani.”
Ya Kara kallonta, ya ci-gaba da cewa “Haka zalika kada ki damu da maganar Kawu, ni zan fahimtar da shi komai, ba kuma zai taba ganin laifinki ba, a wannan tunanin. Tunanin makomar rayuwarki kawai za ki yi.”
Bai damu da kallon kaduwa da mamakin da take yi masa ba, ya aje wayarsa. “Ki sa min caji,
barci ya cika idona, zan kwanta na runtsa.” Ba ta amsa ba, har ya wuce cikin uwardaka, ya yi kwanciyarsa ya bar Afrah da kakabin
maganganunsa. Idanunta suka Kara cika da hawaye.
Ta yaya za’ayi Musaddik ya fara tunanin rabuwa da ita, har wane tunanin za ta yi wanda ba ta yi shi ba kafin auransu?
Tabbas a da tausayinsa ne kawai a cikin zuciyarta, amma yanzu sonsa ya fara neman matsuguni a cikin zuciyarta. Ta goge hawayenta gami da addua’ Allah ya kawo iyakar wannan abin.
—————
Ita ko Hajiya Hudah bayan tashinta, babu wanda ta gani, daga Musaddik din har Alhaii Hamza din, domin shi ma bayan tashinsa daya ga Musaddik ya tafi, shi ma sai ya tattara ya nufi gidansa. Ran Hajiya Hudah ya baci, domin ita kanta bata san dalilin daya sa take kwadayin Kara son ganin Musaddik ba.
Ta kira wayarsa, ya fi a kirga, amma wayar tana kashe. Daga bisani Alhaji Hamza ta kira, ta nuna masa bacin ranta na rashin jiranta, sannan ta umarce shi daya gayyato Musaddik Party din da za su gudanar a gobe.
Domin murnar cinye zabe. Alhaji Hamza ya ba ta hakuri tare da yi mata alkawarin gayyato
Musaddik kamar yadda ta bukata.
Malam Mahmud kuwa tun da sassafe ya fita ya je (Police Station) da yawa, sai azahar ya yanke shawarar dawowa gida, domin ya ci abinci ya kuma
huta.
Zuwa lokacin kuwa Inna Halima ta kira shi a waya ya fi sau shida, domin ta ji halin da ake ciki.
Kasancewar tunda ya gaya mata, ta rasa sukuni da kwanciyar hankali. Bayan komawarsa gida. Yana idar da sallar azahar.
Kiran Afrah ya shigo cikin wayarsa, da sauri ya dauka, bayan sun gaisa ne, cikin natsuwa ta gaya masa dawowar Musaddik da kuma abinda ya faru.
Malam Mahmud ya numfasa cike da damuwa yace

 

 

Hmmm