MUSABBABI CHAPTER 14 BY HAJ HABIBA

MUSABBABI CHAPTER 14 BY HAJ HABIBA Ta ce “Ka gaya masa, idan babu damuwa ka wuto da shi gidana ya kwana, tunda dare ya yi, gobe ya tafi gidansa.'(Alhaji Hamza ya yi murmushi ya ce. “Na san za ki ft bukatar hakan, don haka na yi masa maganar hakar, ya kuma amince, muna hanyar gidad-ki yanzu. Ta yi murmushi ta ce Allah ya kawoku lafiya”. Daga nan ta aje wayar. Har suka isa katon get din gidan Hajiya Hudah. Alhaji Hamza mamakin lamarin Hajiya Hudah yake yi. Wane irin gamon jini ne ya shiga tsakaninta da Musaddik. Me ya sa ta damu da lamarinsa? Suna isa. Mai-gadi ya bude masu get. A zahiri gidan Hajiya Hudah ya ba Musaddik mamaki, saboda kayaturwarsa. A gaskiya Hajiya Hudah ta aje kudi. A hankali ya dubi Alhaji Hamza,, bayan sun zauna a katon falon kasa. “Yanzu wannan ma gidan Hajiya Hudah ne?” Ya gyada kai ya ce “Eh, wannan gidanta ne da take kwana a ciki, wancan da ka hadu da ita a ciki, ai gidan bakinta ne.•» “Ammo matar nan ta tara kudi ba kadan ba, siyasa ta karbeta, ta shekara hudu kan …