MUSABBABI CHAPTER 14 BY HAJ HABIBA
Ta ce “Ka gaya masa, idan babu damuwa ka wuto da shi gidana ya kwana, tunda dare ya yi, gobe ya tafi gidansa.'(Alhaji Hamza ya yi murmushi ya ce.
“Na san za ki ft bukatar hakan, don haka na yi masa maganar hakar, ya kuma amince, muna hanyar gidad-ki yanzu. Ta yi murmushi ta ce Allah ya kawoku lafiya”. Daga nan ta aje wayar.
Har suka isa katon get din gidan Hajiya Hudah. Alhaji Hamza mamakin lamarin Hajiya Hudah yake yi.
Wane irin gamon jini ne ya shiga tsakaninta da
Musaddik. Me ya sa ta damu da lamarinsa? Suna isa. Mai-gadi ya bude masu get. A zahiri gidan Hajiya Hudah ya ba Musaddik mamaki, saboda kayaturwarsa.
A gaskiya Hajiya Hudah ta aje kudi. A hankali ya dubi Alhaji Hamza,, bayan sun zauna a katon falon kasa. “Yanzu wannan ma gidan Hajiya Hudah ne?”
Ya gyada kai ya ce “Eh, wannan gidanta ne da take kwana a ciki, wancan da ka hadu da ita a ciki, ai gidan bakinta ne.•» “Ammo matar nan ta tara kudi
ba kadan ba, siyasa ta karbeta, ta shekara hudu kan kujerar ta, ga shi ta Kara komawa”.Alhaji Hamza ya yi dan murmushi ya ce.Hmmm! Ai Hajiya Hudah ba ta dogara kadai da siyasa ba, domin tun kafin ta shiga siyasa tana da matukar kudi.
Bai Karasa maganarsa ba, sallamar daya daga cikin masu hidimar gidan ta katse shi. Ta shigo falon tana kallonsa. Ta ce “Sannunku da isowa, dama ku na ke jiran isowarku, domin na nuna maku inda za ku kwanta, ita ta ce na gaya maku ta kwanta, sai gobe za ku hadu.” Musaddik ya dubi Alhaji Hamza. A yayin da lokaci daya suka mike, sannan a hankali suka bi hadimar a baya.
Har zuwa wani katon falo mai dauke da dakuna uku a ciki, kowannensu ta bude masa dakin da zai kwanta tare da ba su tabbabcin za su sami duk abinda suke bukata a cikin dakin. Sai da suka shiga dakunan, sannan ta tafi. Shigar Musaddik dakin ya dade, yana kallon kayatuwar dakin, komai na dakin na alfarma ne.
Sai daya dumama cikinsa da ruwan Tea hade da wani daddadan Cake. Sannan ya shiga bandaki, wanka ya yi sosai, saboda tsananin tsamin da jikinsa ya yi, ga wari da yake yi.
Saboda datti jikinsa, har wani danko-danko yake yi, ba karamin dadi ya ji a jikinsa ba. Yayi mamakin ganin riga da wando kananan kaya masu matukar tsada a jiye a cikin dakin, amma daya tuna abinda hadimar ta fada.
Sai ya daina mamakin, tunda ta ce duk abinda zasu bukata, yana cikin dakin. Don haka ya aje nasa kayan da suke surma uban wari, ya sanya wadanda ya gani a dakin ba tare da tunanin komai ba, Sai Karfe uku ya samu ya kwanta.
Asubar fari Musaddiq ya tashi ya yi alwala ya yi sallah, bai jira komai ba, ya fice zuwa falon kasa na farko, nan ya hadu da hadimar gidan, ta yi masa kallon mamakin irin samamakon tashin da yayi ta ce.
“Har ka fito haka da wuri?”
Ya gyada kai ya ce. “Eh, zan tafi ne, taimaka ki bude min kofa”. Ta wuce zuwa wajen kofar tana fadin “Me zance wa ranki ya dade, idan ta tashi?
Bayan ta ce za ta ganku da safe”. Ya yi mata kallon tsaf!
Ya ce “Ki gaya mata na tafi gida wajen iyali na”. Ta jinjina kanta, lokaci daya ta bude masa kofar, ya fice da gaggawa, duk da ba shi da ko kwandala ‘a aljihunsa. Haka ya yi ta tafiyarsa a kasa, tamkar wanda baya cikin hayyacinsa. Sai da gari ya gama wayewa tangaran! Sannan Musaddil: ya isa gida, a zahiri Baba Mai-gadi ya ji dadin dawowarsa. Afrah na zaune akan kujera kuka take sosai, turo kofar da aka yi, ya sa ta yi saurin kallon kofar dakin. Ganin Musaddik, ya sa ta mike zumbur!
Tana kallonsa daga sama har kasa, tana kallon kayan da ke jikinsa, a sanyaye ta kira sunansa Yaya Musaddik.” Ya amsa Na’am”
Cikin tausayinta ya nemi kujera ya zauna, a yayin da ya aje riga da wandon daya taho da su, domin bai bar su a gidan Hajiya Hudah ba, saboda warin da suke yi.
“Koma ki zauna”. A hankali ta koma ta zauna tana ci-gaba da kallon sa. “Yaya Musaddiq ina ka shiga don Allah, ina ka shiga ka bar ni cikin tashin hankali da tunanin wani abu ne ya faru da kai, wane irin daukar hakki ne wannan?
Ka san lafiyarka Kalau, don me ba za ka fahimtar da ni hakan ba, sai ka bar ni, ina wahala a kanka. Alhalin ka na cikin Koshin lafiya. Na rantse da Allah ba ka kyauta min ba, ba ka kyauta ba…
Ta barke da kuka, cikin damuwa da tashin hankali ya tashi ya dawo kusa da ita ya zauna. Ya dora hannunsa a bayanta yana bubbugawa, lalamar lallashi, sannan ya ce. “Ki yi hakuri, ki kuma natsu, ki fahimcen
Ta ce cikin kuka “Wane fahimta zan yi maka
Bayan irin fahimtar da na yi maka”
• Ya girgiza kai ya ce. “Abinda ki ke zato haka bane, na san na kan kwana ba a gida ba, amman muna magana ta waya, muna sanin halin da jun: mu ke ciki, amma wannan karon tunda ki ka ji shiru wannan shirun, ba ni ba waya, hakika kin san ba lafiya ba”
Ta dago da jajayen idanunta tana kallonsa ce. “Ba lafiya, ba amma jikin ka ai bai nuna hakaba, ga ka nan fes! Da sababbin kaya a jikinka.” A hankali ya cire hannunsa a bayanta, ya mike tsaye ya cire rigar jikinsa, ya juyo mata bayansa yace
“Ki bude idonki ki kalli bayana.”
Afrah ta dago ta dora idanunta akan bayansa duk a farfashe, wani wurin ma ya kumbura, ta mik da sauri tana fadin “Subahanallahi! Waye yayi maka wannan aikin, wane mara imanin ne?”
Ya juyo yana kallonta cikin sanyin murya ya kwashe labarin komai ya ba ta, ya Kara da cewe
“Hatta wannan kayan a gidanta na samu nasa.
Ita ce ta taimakeni ta fitar da ni daga wannar kangin, ba don haka ba, yau din nan za’a kaini Abuja. Idan ko aka kai mu wannan garin, sai yadde hali ya yi, domin miliyan daya ba za ta fitar da ni ba, don haka Allah zamu yi ma godiya, sannan Hajiya Hudah, ta cika halaccinta a gareni.”
Hmmm