CANJIN RAYUWA CHAPTER 17 BY HALIMA A K/MASHI

CANJIN RAYUWA CHAPTER 17 BY HALIMA A K/MASHI

 

 

ya ji alat.

Momy Nafisa an dawo daga Dubai, sannan ‘yan gidan su Abbas sun kawo kayan lefe. Ran Hajiya Sauda ya baci da yadda Alhaji ya nuna mata. Matsayinta na wadda ta haifi Mimi ya kyautu a ba ta hakkinta ko da na shawara ne, amma Alhaji ya yi mata dif, tunda ta ce ba za ta shiga lamarinsa da Mimi ba, ita ‘yar ba da shawara ce. Ba ta fadi hakan da wata manufa ba, sai dai nuna ma Alhaji kurensa, amma ya dauka da zafi, don haka ta lashi takobi ita da yaranta babu inda za su je, domin auren Abba a nan Katsina aka yi shi, na Mimin in ba za a kawo nan ba, to su je can su yi kayansu.

Biki saura kwana goma Mimi ta yi wanka, cikin sauri ta zura doguwar rigarta atamfa, sai dan bakin karamin mayafi. Takalmi mara tudu ta saka, sannan ta kwashi katinta na ATM daga jakarta da take zuwa banki, ta zuba su cikin jakarta da takan je saloon, ta rataya jakar. Sannan ta kwashi wayoyinta. Tana sauka kasa, Momy

taba wannan account din Mimi?” Ta ce,

“Dad ba ni da kudi ne, kuma zan yi gyaran jikina ne.

» Ya kalli Alhaji Akilu, sannan yace, “shi ke nan ya isa, ki bari zan ba ki kudi.

Kar ki kuma cira daga wannan account din, saboda ina son yi miki wani tsari ne da kudin. Za ki yi kasuwanci kina daga gida, kuma na manyan kudi. Kin gane?” Mimi ta ce, “eh Dad. Ba zan Kara cirewa ba.” Ya ce,

“shike nan.”

Alhaji basheer, cikin dariya ya ce, “ka ji ‘yar kwal uba? Wai tana fadin ba ta so, amma ta zo tana dibar kudi wai za ta yi gyaran jiki.” Suka sa dariya. Alhaji Àkilu yace, “me na fada maka? Kiyayyar mata ba ta zuwa ko’ina. Amma shi ma Abbas din ai shi ya dace ya ba ta kudin gyaran jikin.” Alhaji Bishir ya ce, “ai ita da shi duk daya ne. Ka rabu da shi, zan ba ta.” Alhaji Akilu ya kira layin Abbas. Bayan ya dauka, ya ce,

“Abbas ya ba ka bai wa Amaryarka kudin gyaran jiki ba?” Abbas ya ce, “Dad taqi ba ni damar in san abin da take bukata ne.

Amma zan ba ta anjima.” Ya ce, “shi ke nan ka je ka ba ta. Ka lallade ta, ka san yarinya ce.” Abbas ya ce, “insha Allah Dad.”

Mimi gida ta wuce ta adana kudinta da duk abin da ya kamata ta tafi da su, amma banda kaya.

Ismail ya dangana har zuwa ranar ashirin da tara da Alhaji Bishir ya yi musu albashi.

Duk da kin karatun da Mimi ta yi, bai sa Alhaji canzawa daga dubu darin da ya alkawarta zai ba shi ba. Ismail ya yi ta juya kudin a cikin dakinsa, yana farin ciki. Sam bai taba rika su ba a hannunsa ko na wani ma bare nasa. Lalle goben nan sai Katsina, ya je ya biya kudin gaisuwa, ya hada kayan sa rana, ya sai ma Zainabu waya, sannan ya yi alheri, ya yi sabbin dinkuna, yana ta baje burinsa. Nan ya kira Mahmud ya sanar da shicewa gobe yana tafe.

Tun dare yake ta shirin sa, washegari ya kira Hajiya Sauda ya fada mata cewa yau• yana son zuwa gida ya ga ‘yan uwa. Ta ce ba laifi, sai ka iso. In ka zo kuma don Allah ina neman ka. Ya ce babu matsala. Sai dai ina son don Allah ki sanar da Alhaji saboda ban san lokacin da zai fito ba. Ta ce, “ya ba ka albashi dai ko?” ya ce, “wallahi ya ba ni. Ki yi min godiya.

YAR TSANAR ZINARI COMPLETE HAUSA NOVEL BY JIDDARH UMAR

A BAKIN WAWA HAUSA NOVEL BY Hijjart Abdou

ADNAN~-~ADEENA


,” Ta ce, “to zan sanar da shi

yanzun nan.Ba a yi minti talatin ba, sai ga

Hamisu Direba ya ce Ismail ya je in ji Alhaji. A falo ya same shi. Ya zauna, sannan ya gai da Alhajin cikin girmamawa. Alhaji ya ce, “Sauda ta kira ni, ta sanar da nicewa za ka je gida yau. Haka ne?” ya ce, “eh Alhaji. Ina son in je in ga ‘yan uwa ne.” Alhaji ya ce, “da fatan ba mu takura maka ba ko? Ina nufin ka ji dadin zama da mu?” Isma’il ya ce, “na ji dadi sosai.” Alhaji ya ce, “to ina fatan za ka dawo.” isma’il ya ce,

“ehto, na ji ana cewa za a yi wa wadda na zo in koyar da ita aure, shine ban sani ba ko hakan yana nufin ni mana gama aikina ke nan?” Alhaji ya yi murmushi, “ai in na lura ita din ba ta yin karatun, amma kannenta suna yin karatun. Sannan kana yi mana salla. Ga yaran nan suna yin karatu sosai, suna yin salla a kan lokaci. Wannan ya fi min komai. Yanzun ma da ka ce za ka je

Hmmmm