CANJIN RAYUWA CHAPTER 23 BY HALIMA A K/MASHI

jikin Dadynsu da sauki a sa musu abinci su ci. Nice ma ban riga na ci ba. Saboda na fi son abu mai ruwa da’ safe, mai kuma dumi kamar shayi. Hajiya Binta ta ce, ya fi dadi ai. Hasana sa min wainar. Allah ya rufa asiri, Suka ce amin. Duk da gudun da motar da su Mimi suka shiga take yi, gani take yi kamar ba gudu ba. Sannan ba ta tada shiga motar haya ba tunda aka haife ta sai yau. Bugu da Kari ba ta ta6a shan wahala ba a rayuwarta tunda take kamar wannan lokacin da ta bar gidan iyayenta. Shirun da ta yi daga zaune. abubuwan da take lissafawa ke nan. Duk da tsananin son da take yi wa Khalil ba ta jin za ta sake barin gida, ba tare da yardar Mahaifinta ba. Abin nufi ba tare da sun yi mata aure ba. Cikin haka ne ta ji mutanen cikin motar suna salati, wadansu kuma wadanda ba musulmi ba suna ambatar abin da suka yi imani da shi. Ta zaro idanu, lokacin da ta ga motar ta su ta saki hanya. Sosai ta firgita, ta soma fadin Wayyo Allah! Daf da wani rami motar tasu ta tsaya cak. Wai ashe taya ce ta …