CANJIN RAYUWA CHAPTER 21 BY HALIMA A K/MASHI

hankali yake. A nasa zaton an sace ta ne, tunda ya ga gab da bikin ta saki jiki. Da alamu ta yarda za ta aure shi. Cikin mutunci ta amshi kudin gyaran jikin da ya kai mata. Sannan ranar da aka yi Family night sun yi ta hotuna tare. Sannan a ce an sace ta. Ko dai masu yin garkuwa da dan Adam ne? Alhaji Akilu ya ce, kar ka damu. In ma sune za mu ba da ko nawa ne don su sake ta. Alhaji Bishir ya sanar da duk masu kaffin sadarwa don neman ta, ko, in ce cigiyarta. Da kamfanin layin MTN aka gane cewa tana Kaduna, don haka can suka dosa. Kwamishinan ‘yan sanda na Kaduna . shine ya kira Mahaifin Khalil ya sanar da shi cewa ga iyayen yarinyar da dansa ya gudu da ita sun zo. Bai yi kasa a guiwa ba, ya iso gidan Kwamishinan. Sun tattauna da Mahaifin Khalil, ya ba su hakuri, tare da tabbatar musu cewa dansa Khalil ya gudu tare da ‘yarsu. Sannan ya fada wa Kwamishina cewa in ya zo a kama shi kamun barawo don ya dauke sarkar uwarsa Gidan su Abbas din ma da suke ta zagin ki, wai kin bi namiji. Wa ya san ab…