hankali yake. A nasa zaton an sace ta ne, tunda ya ga gab da bikin ta saki jiki. Da alamu ta yarda za ta aure shi. Cikin mutunci ta amshi kudin gyaran jikin da ya kai mata.
Sannan ranar da aka yi Family night sun yi ta hotuna tare. Sannan a ce an sace ta. Ko dai masu yin garkuwa da dan Adam ne?
Alhaji Akilu ya ce, kar ka damu. In ma sune za mu ba da ko nawa ne don su sake ta.
Alhaji Bishir ya sanar da duk masu kaffin sadarwa don neman ta, ko, in ce cigiyarta. Da kamfanin layin MTN aka gane cewa tana Kaduna, don haka can suka dosa. Kwamishinan ‘yan sanda na Kaduna
.
shine ya kira Mahaifin Khalil ya sanar da shi cewa ga iyayen yarinyar da dansa ya gudu da ita sun zo. Bai yi kasa a guiwa ba, ya iso gidan Kwamishinan. Sun tattauna da Mahaifin Khalil, ya ba su hakuri, tare da tabbatar musu cewa dansa Khalil ya gudu tare da ‘yarsu. Sannan ya fada wa Kwamishina cewa in ya zo a kama shi kamun barawo
don ya dauke sarkar uwarsa
Gidan su Abbas din ma da suke ta zagin ki, wai kin bi namiji. Wa ya san abin da za kuje ku yi? Mimi tana kuka ta ce, shi ke nan.
Zan yi Momy. Ta ce, yanzun nan za ki yi, Mimi tana kuka ta ce, to.
Suna cikin yin musabaha don yin sallama message din Mimi ya shiga wayar
Dad dinsu. Bai yi kasa a guiwa ba, ya bude ya soma karantawa kamar haka: Ka yafe ni Dad in na bata maka. Na yi kokari in yi maka biyayya, amma na kasa. Ba na jin zan iya zama da Abbas a matsayin mijina. Zan dawo. gida, in ka amince za ka ba ni wanda nake so. Ya dago ya kalli Alhaji Isa, wanda da shi suka zo Kaduna, sannan ya ce, ka gani ko? Karbi ka karanta. Ka gani guduwa suka yi, ba sace ta ya yi ba. Ni kuma zan nuna mata cewa ta yi mummunan kuskure.
Da kyar Alhaji Bashir ya kai cikin gida saboda ciwon kai. Amma kafin ya kai tsakiyar falo, tuni ya zube kasa. Sabon al’amari ke nan wanda ya ta da hankalin mutan gidan. Nan da nan aka yi asibiti da shi. Ya farfado, inda aka tabbatar’ masa jininsa ya hau sosai. Sannan an gano yana da ciwon sugar. Cikin abin da bai fi minti talatin ba, dukkan iyalansa sun samu labari.
Kuka sosai Hajiya Sauda ta yi domin ta san
Mimi ce silar komai.
Karfe sha daya Momy Nafisa ta kira
Na’ima ta ce, ga lokacinki fa ya yi, Daga yanzun zuwa da safe. Na’ima ta ce, shi kênan Momy ya farka ne? ta ce, eh, in ya farka yana tambaya ta wai ga shi gobe daurin aure, bai san yadda zai yi ba. Na dai lallaba shi. Ki shirya zan fita in sa Hamisu Direba ya dauko ki, don shi ya kawo su Kawunku da suka zo biki.
Tana fitowa ta leka ta ce ma Hamisu ya je ya dauko Na’ima. Alhaji Isa ya ce, ta yi me da daren nan? Momy Nafisa ta ce, kuka take yi sosai. Kuma ta ce tana da magana da shi. Cikin kuka Na’ima ta shigo dakin. Momy ta rungume ta, yi shiru mana Na’ima, ai jikin da sauki. Kalle shi har ya farka. Ta isa gurin sa,
Dad, ta kama hannunsa. Dad, kar ka damu. Nina amince in har Abbas yana so na, gobe a daura auren da ni. Wallahi Dad ba na son in rasa ka. Ya yun kura. zai tashi, Momy ta rike shi. Ya jingina, sannan ya kama hannuwan Na’ima, da gaske kina son Abbas? Na’ima ta ce, ni ban san so ba Dad. Amma zan koye shi a gidan Abbas. Zan so shi in ya zama miji gare ni. Alhaji Bishir ya rungume ta.. Na gode ‘yata, Allah ya yi miki albarka. Ya kalli Momy Nafisa, kin ji abin da Na’ima ta ce? Momy ta ce, Naji. Allah ya yi miki albarka. Kar ka damu, ka kira Alhaji Akilu din. Bai san ma akwai wannan matsalar ba.
Bai san kana asibiti ba. In ya zo sai ku tattauna. Ya ce, hakane. Ke ma din Allah yai miki albarka.
Momy Nafisa ta ce, amin. Yace, lekaki kira min Alhaji Isa. Nan suka shigo, ya sanar da su abin da Na’ima ta ce. Suka yi ta sa mata albarka. Alhaji ya ce, to kowa ya koma gida, insha Allah, biki babu fashi. Momy ta ce,
alhamdulillahi ga shi da ma ‘yan biki sun cika gidan,
‘yan Masari da yan Malumfashi. Hajiya Binta da ma ba ta taho ba, tana shirin zuwa ta ji labarin atar Amaryar, don haka ta dakata. Yanzu kuma sai ga labarin ciwon Alhajin, don haka dole gobe sai Abuja.
A daren, Alhaji Bashir ya sanar da Alhaji Akilu komai. Da yake kowannensu ba damuwar ‘ya’yan ba ne, su dai hada surukuntar ne kawai don cimma burinsu.
Ba tare da neman shawarar Abbas ba, ya amince da auren Na’ima. Sai da asubahi bayan sun dawo sallah yake sanar da Abbas din canjin da aka samu. Nan take Abbas ya ce shi sam bai son Na’ima. Alhaji Akilu ya ce, ba damuwata ka so ta ba. In auren ya dauru burina ya cika. Ka aure ta in ya so daga baya ka auri wadda kake so. Abbas ya ce, Mimi nake so. In kuma ina auren kanwarta, yaya zan yi in aure ta? Alhaji Akilu ya kawo iyaka wuya, cikin fada yake cewa, kai ma za ka yi min irin abin da ‘yar Alhaji Bishir ta yi masa ne? To bari kaji. Ba zan dauki rainin wayo ba. Kawai ka yi abin da nace. Dukkan su ai mata ne. Abin da waccan ke da shi, wannan ma tana da shi.
Yanzu an daina auren soyayya, sai auren me zan samu. Ka gane? Na fada maka nasarar da zan samu ta hulda da Alhaji Bashir, so kake sai ka ja min asara ne? Abbas ya’ce, shi ke nan Dady, na yarda. Har da hawaye ya bar gurin. A dakinsa kuwa ya ci kuka. sosai, domin ya kallafa rai a kan Mimi.
Suna idar da sallar asubahi Isma’il ya ce wa Hamisu Direban yara, don Allah kai mu asibiti mu duba Alhaji. Har da Kanin Alhaji da “ya’yansa mata suka tafi tare. Sun samu Alhaji yana salla. Don haka suka zauna Momy Nafisa ce ta kwana a gurinsa.
Ita ma tana sallar ne. Bayan sun idar, ta leka ta ce, ku shigo mana. Suka shiga suka gai
da shi. Ya ce, na samu sauki. Nan da karfe bakwai zan koma gida. A ci gaba da biki.
Kun ji Na’ima ta share min hawaye ko?
Ismail da bai san kan maganar ba, sai ya kalli Alhaji, daidai lokacin da kanin Alhajin ke cewa, mun ji za ta auri shi yaron da waccan Ja’irar ta gudu domin sa. Yanzun ai sai ta dawo. Alhaji ya ce, ta dawo ina? Ai ko ta dawo, ita ma sai na yi mata abin da ta yi min. Suka ce hakuri dai za a yi. Isma’il ya yi wa Alhaji addu’a. Sannan suka ce za su koma. Alhaji ya ce, Malam Ismail na gode. Sai na zo.
Suna komawa gida, Ismail ya kira layin Hajiya Sauda. Har sau biyu ba ta daga ba. Don haka ya bari. Yana gugar kayansa, sai ga kiran ta. Ya daga suka gaisa. Ya ce, kin samu labarin ciwon Alhaji? Ta ce,
tun iiya. Yanzu ma ga mu nan ni da yara za mu biyo jirgin Karfe takwas. Yaya jikin nasa? ya ce, da sauki.
Ta ce, an ji labarin Mimi? ya ce, eh to, na ji dai an ce tunda tayi masa text ne cewa ba za ta dawo ba sai in zai yi mata abin da take so, shi ne ya fadi. Amma yanzu Na’ima ta yarda za ta auri wanda Mimin ba ta so. Hajiya Sauda tace, oh ni Saude! Allah ya shirya wannan yarinyar. Shike nan sai mun iso.
Bakwai da rabi Alhaji ya iso gidansa, jama’a sai shigowa suke. Ya yi wanka, sannan ya karya. Ya sha magani, ya dan kwanta kafin tara. Daurin auren sai karfe biyu, in an idar da salla a babban masallacin
Abuja.Tara saura Hajiya Sauda da Abba da
Abdulkarim da su Hasana da Usaina suka
shigo. Na’ima ta rungume su Hasanan, sannan ta gai da Hajiya. Ta ce, Ina Momyn taku?
Na’ima ta ce, tana dakin Dad.
Dukkan su suka shiga. Ya tashi barci suna magana da Nafisa. Momy Nafisa ta ce, oyoyo, sannun ku da zuwa. Nan yaran suka gai da ta, sannan suka nufi gurin
Dadynsu. Ita kuma ta ci gaba da yi wa
Hajiya Sauda mita.Ba ki zo ba da “yata ta
bata, amma da jin an ce mijinki babu lafiya,
kin debo yara kun taho.Sauda ta ce, shi
ne dole na, “yarki, ai ba dole na bace. Suka
gaisa. Ta ce, ina Muktar? Hajiya Sauda ta ce, mun yi ta jiran sa bai karaso ba. Na ce,mu tafi, ya zo.
Sauda ta isa gurin mijinta, ta zauna daf da shi. Ya kama hannunta, har kin zo?Ta ce, jiya ban yi barci sosai ba, amma yadda na ga jikin naka, alhamdulillah. Yace, ashe ina da ciwon sugar ne. Kwanaki kina ce min duk na rame.Sugar? Sauda
ta tambaye shi. Ya ce, tabbas. Har ya soma yi min yawa. Yanzu dai Likita ya dora ni kan magani da dokoki da kuma abincikan da zan kiyaye. Hawaye suka zubo a idon Sauda. Ya dafa ta, a’a kar ki yi kuka Sauda, insha Allah zan warware. Ta ce, Allah ya ba ka lafiya. Ya ce, amin. Ya kalli Abba, ina takwarana?
Abba ya ce, suna gida.
Za su zo da Mamansa. Alhaji ya ce,.
Madallah, Allah ya yi maku albarka. Kun ji abin da Mimi ta yi min ko? ya dinga kallon su da dai-dai, sannan ya, dan sunkuyar da kai. Na san har da hakkinku.
Ina mai ba ku hakuri. Abba ya ce, haba Dady, babu komai. Allah ya ba ka lafiya.Sauda ta ce, to yanzu ya ake ciki?Ya ce, na me fa? ta ce na bikin. Ya ce, Na’ima za a daura da ita.Ya kalli
Abdulkarim, ya nuna masa wayarsa, miko min wayar can. Ya miko masa. Ya ba ta, bude ki ga sakon da yarinyar nan ta turo min. Hajiya Sauda ta kammala karantawa cikin kuka. Sannan ta ce, Alhaji ba zan gaji
Hmmmm