CANJIN RAYUWA CHAPTER 20 BY HALIMA A K/MASHI
CANJIN RAYUWA CHAPTER 20 BY HALIMA A K/MASHI nemi otal, kar su kama na bakin hanya. Ta titin Kagoro suka shiga, inda suka sami wani otal suka kama. Mimi ta ce su kama mata dakinta daban khalil yace dear zaki iya kwana ke kadai? Tace eh mana karka damu yace shikenan Daki biyu suka kama a sama. Khalil ya kalli Sadau bayan sun kwanta, “abokina ina kake ganin ya dace muje?” Sadau ya ce, “gobe ku shiga motar Sakkwato ko Zamfara. Ba za a yi tunanin za ku je can ba. Khalil ya ce, “Ni da Lagos na so mu tafi, mu boye kamar na sati daya.” Sadau ya ce, “kai banza ne, wane sati daya. Ai in nine kai sai na dinke yarinyar sannan za mu fito. Yadda•dole za a aura min ita. Khalil ya tashi zaune, “ban gane ba.” Sadau ya ce, “ina nufin,” ya yi kwatance da hannunsa da cikinsa. Khalil ya ce Allah ya sawwake. ba ni da niyyar in cutar da Mimi. Zan bari mu yi halastaccen aure da ita.” Sadau ya ce, “ka ji matsalarka. A shawarwarin da na ba ka, wacce ce aka Samu matsala? Na ce ka sai da gwal din Mom dinka, mun sai da.…