CANJIN RAYUWA CHAPTER 20 BY HALIMA A K/MASHI

CANJIN RAYUWA CHAPTER 20 BY HALIMA A K/MASHI

 

 

nemi otal, kar su kama na bakin hanya. Ta titin Kagoro suka shiga, inda suka sami wani otal suka kama. Mimi ta ce su kama mata dakinta daban khalil yace dear zaki iya kwana ke kadai? Tace eh mana karka damu yace  shikenan Daki biyu suka kama a sama. Khalil ya kalli Sadau bayan sun kwanta, “abokina ina kake ganin ya dace muje?” Sadau ya ce,

“gobe ku shiga motar Sakkwato ko

Zamfara. Ba za a yi tunanin za ku je can ba.

Khalil ya ce, “Ni da Lagos na so mu tafi, mu boye kamar na sati daya.” Sadau ya ce, “kai banza ne, wane sati daya. Ai in nine kai sai na dinke yarinyar sannan za mu fito. Yadda•dole za a aura min ita.

Khalil ya tashi zaune, “ban gane ba.”

Sadau ya ce, “ina nufin,” ya yi kwatance da hannunsa da cikinsa. Khalil ya ce Allah ya sawwake. ba ni da niyyar in cutar da Mimi.

Zan bari mu yi halastaccen aure da ita.” Sadau ya ce, “ka ji matsalarka. A shawarwarin da na ba ka, wacce ce aka Samu matsala? Na ce ka sai da gwal din Mom dinka, mun sai da. Na ce ka dauke ta ku gudu, ba ga shi ka yi nasara ba?” Khalil ya ce, “ban dauke ta da niyyar aikata wani abu ba, sai don in fid da ta daga auren wani na. Kai dai naka da safe ka kai mu garejin mota mu tafi. Kai kuma koma gidanku, mun gode.”

Mimi kuwa ta kasa barci, sai juyi take yi. Wayarta tana ‘silent’, amma tana kallon kira. Da wani ya yanke, wani zai shigo. Da farko ta ki dubawa, amma daga baya sai ta duba. Kiran Dad dinta ne da Momy Nafisa, har da su Na’ima. Kuka take ta tayi tare da tausayin mahaifinta. Ji take kamar ta daga ta ce su zo su dauke ta, kuma ta amince za ta auri wanda suke so. Amma sai shaidaniyar zuciyarta ta kangare, ta kuma hana ta aiwatar da hakan. Da zazzabi ta farka tare da ciwon kai mai tsanani, don haka sai batun tafiya ya fasu. Sun fita suka sayo mata doguwar riga da hijabi ta saka, sannan suka dauke ta zuwa asibitin Biba.

Gado likita ya ba ta, don tana cikin damuwa. Hankalin Khalil ya Kara tashi, tsoron sa kar wanda ya san shi ya gan shi. burinsa su bar Kaduna, amma da yake daki na musamman suka kama, sam ba ya fitowa ko kofar daki. Duk abin da suke so Sadau ke zuwa ya sai musu.

Su kuwa su Momy Nafisa ba su ankare ba, suna can suna ta hidimar ganin kowa ya samu abinci. A zatonsu tana can suna hotuna da kawayensu. Sai lokacin da Na’ima ta zo tana cewa “Momy ina Sis Mimi? Ga Abbas sun zo da abokansa.” Nan fa aka shiga neman Amarya, ba ta babu dalilinta. Hankula suka tashi. Nan dai biki ya kare. Momy Nafisa kuka wi-wi. Nan ta kira Alhaji Bishir tana fada masa cewa Mimi ta zo gida? Ya ce, babu wanda ya zo gidan nan. Shi ma zuwansa ke nan. Daidai lokacin da suke yin wannan wayar da a ce ya waiwayo da zai ga Mimi, tunda gilashi ne ya raba falonsu da nasa.

Ta ce masa, “to Mimi dai an neme ta an rasa ta, ko kasa ko sama. Har zuwa sha biyun dare ana ci gaba da neman ta lungu da sako, banda wayoyi da ake ta yi don ji gurin abokanen arziki. Matuka hankalin Alhaji Bishir ya tashi sosai. Alhaji Akilu ya kira shi yana jajanta masa. Ya ce, “amma Alhaji Bishir da ma yarinyar nan ba ta hakura ba?” Alhaji Bishir ya ce, “ta hakura mana. Ga shi ana ta biki. Sai yau a ce ta gudu?”Alhaji Akilu ya ce, “ba ka ganin ko yaron da suke yin soyayyar ne ya zo ya sace ta?” Alhaji Bishir ya ce, “komai zai iya faruwa, amma bari mu gani zuwa da safe.Alhaji Akilu ya ce, “in ko ya tabbata yaron nan sace ta ya yi, lallai babu abin da zai hana shi zaman gidan yari. Ka ga halin da Abbas yake ciki kuwa?” Alhaii Bishir ya ce,

“ko ni ma ba zan kyale iyayansa ba bare shi, tunda daga gani ba da yardarta ya sace ta ba, domin ba ta bar wani sako ba, sannan ba ta dauki komai na sawarta ba.’ Alhaji Akilu ya ce, “kun kira lambarta?” Yace, tana ta ringing ba ta daga ba.

Kusan Karfe dayan dare, Alhaji Bishir ya kira Hajiya Sauda. Tana barci, ta dauka, tana fadin, “Alhaji lafiya?” ya ce,ina fa lafiya, an sace Mimi.” Ta diro daga kan gado. “An sace Mimi kuma?” Ya ba ta labarin komai. Hajiya Sauda ta ce, “ko dai guduwa suka yi tare da saurayin nata?” Ya ce, “ba na tunanin haka, saboda ta nuna min ta hakura. Kuma sun shirya komai da mijinta, har kudi ta cire a account din ta don gyaran jiki. Sannan ba ta dauki komai ba.”Hajiya Sauda ta ce,

“Allah ya kyauta.Amma a zuciyarta ta fi yarda cewa Mimi kudi ta diba suka gudu. Ta ce,to yanzu

wane mataki ka dauka?” Ya ce,mun sanar

da ‘yan sanda, sannan gobe za mu je

Kaduna gidan iyayensa. Sauda tace,to ku kuma hada da addu’a.Bayan sun yi sallama da kansa ya taka gefen masu masu aiki, ya kwankwasa kofar dakin Isma’ila, sannan ya yi sallama. Isma’il ya amsa, don lokacin yana ta juyi cikin damuwar rashin masoyiyarsa Zainabu. Jin muryar Alhaji ya bude kofar cikin fargaba. Ya ce, “Alhaji lafiya?” Ya ce ba ka ji abin da yake faruwa ba ne?”Isma’il ya ce, “ban ji ba Alkaji. A zatosa ma barayi ne suka shigo gidan. Alhaji ya ce mu shiga daga ciki. A tsakiyar dakin suka yi cirko-cirko. Alhaji yace, Malam Isma’il a gurin shagalin biki aka sace Mimi. aka sace Mimi? Ismail ya maimaita. Alhaji Abbas ya ce, na zo gurin ka ne saboda ina son a taya mu da addu’a kafin gobe in samu Malamina sabodo ya duba min inda suka boye ta.Ismail ya ce,Allah ya kyauta, ya kuma bayyana ta. Sai dai Alhaji ba ka tunanin ko sun gudu ne?Alhaji ya ce, ba na

tsammani, tunda ba ta bar wata alama da za ta nuna hakan ba. Sannan ba ta dauki kayaba. Isma’il ya ce, haka ne. shi ke nan insha Allah zan taya da addu’a. ikon Allah a gabana suka hau mota Alhaji da za su tafi.

To, ni dama muna yin isha’i, na yi shafa’i nake shiga in kwanta da wuri saboda ina tashi cikin dare. Alhaji ya ce, to bari mu je mu yi sauraro. Isma’il ya ce Allah ya jishe mu alheri. Bayan fitar Alhaji, Ismail ya yi ta mamakin Mimi. Tabbas sun gudu ne, tunda ta fada masa cewa sun samu mafita.

Ya kira layinta, ya yi ta ringing har ya tsinke. Haka ya yi ta kira har ya gaji. Alhaji kam yana tafe yana tunanin maganar Isma’il, haka Sauda ta ce ko sun gudu ne.

Shi ma ga shi ya ce hakan. Momy Nafisa ya samu ta zabga tagumi bakin gadonsa. Ya dafa ta, kar ki damu Nafisa za a gan ta. Ni damuwata ma da Sauda ta ce ko dai guduwa suka yi. Haka ma Malaminta ya fada min yanzu. Sai dai ina shakku don na san Mimi ba zata guje ni ba ta bi wani sakarai.

Momy Nafisa ta ce, haba ba za ta gudu ba. Don ta tabbatar da ya zai yi in gudun ta yi, sai ta ce, ko ta gudu ma, ai dole ta dawo. Ya ce, me kika ce? Ya mike cikin tashin hankali, ya ce, kuskure mafi girma da Mimi za ta yi shi ne ta guje ni. Kin ji na rantse miki, in Mimi guduwa ta yi saboda ta kunyata ni, to ni kuma sai na yi mata abin da ba za ta manta da ni ba. Wannan alkawarina, ne.Tunda asubahi Momy Nafisa ta shiga dakin Na’ima ta ce, Na’ima tashi ki ji, ga fa dama ta samu. Na’ima ta gyagije. daga barci. Momy ta ce, wannan gudun na Mimi ya yi matukar zuwa mana a daidai.

Yanzun abu daya ya rage mana. Shine Dad dinku ya san cewa tana sane ta bar gida.

Na’ima ta ce, in ya sani mene ne? Nan Momy ta sanar da ita alwashin da ya ci.

Sannan ta ce, kuma tabbas Mimi ba sace ta aka yi ba. Ga shi na yi ta kiran ta ba ta daga ba. Amma zan ci gaba da kira. In ta daga zan sa ta fada wa Alhaji cewa ta gudu ne.

Safiyar ranar Ismail yana masallaci zaune, Alhaji ya fito zai fita. Ismail ya nufe shi ya gai da shi cikin girmamaw.annan ya dada jajanta masa. Alhaji yayi

Godiya. Isma’il ya ce, sai dai jiya na yi mantuwa.

Sai bayan ka tafi na tuna. Alhaji ya ce, ta

› me? Isma’il ya ce, Alhaji duba haramun ne a Musulunci. Akwai inda yake zama shirka ma,

wato mutum ya fita daga

Musulunci. Alhaji yace istihara ce ai za’a yi Malam Ismail. Isma’il ya ce, Alhaji ai stihara kai ne za ka yi da kanka, ba wani ne zai yi maka ba, kamar yadda wasu Malaman suke cewa don su ci kudinku.

Alhaji ya ce, shi ke nan. Ana jira na. In na ‘dawo za mu yi maganar.

Bayan ya koma daki ne ya ga kiran

Hajiya Sauda. Nan take ya kira ta. Cikin girmamawa ya gaishe ta, sannan ya jajanta mata abin da ya faru. Ta ce, Isma’il na kira ne ina son ka taya ni da addu’ar Allah ya tsare yarinyar nan, don ina zaton guduwa ta yi tare da yaro nan. Isma’il ya ce, ina yi.

Hajiya ni ma na fi zaton sun gudu ne.

Ta ce, ina amfanin gatan da ya nuna mata. Ai da ma kuskure ne mutum ya gina dansa a kan cewa duk abin da yake so sai ya samu. Gara ka nuna wa yaro cewa akwai samu, akwai rashi. Akwai tsautsayi akwai kuma kaddara. Amma sam ita ba ta san wannan ba. Duk abin da take so zai mata.

To yaya yanzu ba za ta turbure ya ba ta wanda take so ba? Isma’il yace, hakane.

A ransa ya ce da ma Hausawa sun ce, ka sa danka kuka, kafin ya sa ka.

A fili ya ce,

Allah zai saukaka mana lamarin da yardarsa. Hajiya Sauda ta ce, Allah ya sa.

Abbas kuwa shi ma cikin tashin hankali yake. A nasa zaton an sace ta ne, tunda ya ga gab da bikin ta saki jiki. Da alamu ta yarda za ta aure shi. Cikin mutunci ta amshi kudin gyaran jikin da ya kai mata.

Sannan ranar da aka yi Family night sun yi ta hotuna tare. Sannan a ce an sace ta. Ko dai masu yin garkuwa da dan Adam ne?

Alhaji Akilu ya ce, *kar ka damu. In ma sune za mu ba da ko nawa ne don su sake ta.

Alhaji Bishir ya sanar da duk masu kafofin sadarwa don neman ta, ko in ce cigiyarta. Da kamfanin layin MTN aka gane cewa tana Kaduna, don haka can suka dosa. Kwamishinan ‘yan sanda na Kaduna shine ya kira Mahaifin Khalil ya sanar da shi cewa ga iyayen yarinyar da dansa ya gudu da ita sun zo. Bai yi kasa a guiwa ba, ya iso gidan Kwamishinan. Sun tattauna da Mahaifin Khalil, ya ba su hakuri, tare da tabbatar musu cewa dansa Khalil ya gudu tare da ‘yarsu. Sannan ya fada wa Kwamishina cewa in ya zo a kama shi kamun barawo don ya dauke sarkar

Hmmmm