CANJIN RAYUWA CHAPTER 17 BY HALIMA A K/MASHI
CANJIN RAYUWA CHAPTER 17 BY HALIMA A K/MASHI ya ji alat. Momy Nafisa an dawo daga Dubai, sannan ‘yan gidan su Abbas sun kawo kayan lefe. Ran Hajiya Sauda ya baci da yadda Alhaji ya nuna mata. Matsayinta na wadda ta haifi Mimi ya kyautu a ba ta hakkinta ko da na shawara ne, amma Alhaji ya yi mata dif, tunda ta ce ba za ta shiga lamarinsa da Mimi ba, ita ‘yar ba da shawara ce. Ba ta fadi hakan da wata manufa ba, sai dai nuna ma Alhaji kurensa, amma ya dauka da zafi, don haka ta lashi takobi ita da yaranta babu inda za su je, domin auren Abba a nan Katsina aka yi shi, na Mimin in ba za a kawo nan ba, to su je can su yi kayansu. Biki saura kwana goma Mimi ta yi wanka, cikin sauri ta zura doguwar rigarta atamfa, sai dan bakin karamin mayafi. Takalmi mara tudu ta saka, sannan ta kwashi katinta na ATM daga jakarta da take zuwa banki, ta zuba su cikin jakarta da takan je saloon, ta rataya jakar. Sannan ta kwashi wayoyinta. Tana sauka kasa, Momy taba wannan account din Mimi?” Ta ce, “Dad ba ni da k…