AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 4 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

“Me kika gani?” Na ce, “Yau ka sake”. “Kamar ya ya?” Ya tambaye ni.Na ce, “Naga sai wani aikin kashe min ido kake”Kefa ba ki da kunya”. Na yi saurin mikewa na yi dakin Inna, na same ta kan sallaya tana lazimi, na zauna sai da ta kammala. Tace, “Ya dai?” Nace, “Za mu fita shan Ice-cream da Ya Sagees”. Inna ta dan tsuke fuska, “Wai ke Bahiyya yaushe za ki girma ne, kullum kina yawo da Sageer”. Na bata rai, “To dan nayi yawo da dan’uwana sai me?” Ta ce, “Yanzu fa ba da bane kun girma, gara a ringa sara ana duban bakin gatari”. Nace, “Sai ki sa Abba ya bani mota, kuma • hard wani girma na yi da za’a ringa shiga tsakanina da Ya Sageer” “To ai ke din ce Bahiyya, komai kanki gadi kike, ya kamata ki ringa janye jili, dan kin dan girma’. Na tsuke fuska.Dai-dai lokacin naji Ya Sageer yana Kwalla min kira, na juya cikin iya taku na nufe shi, yana bakin mota yana jira, motarsa wacce Abbana ya sai masa End of discation dark blue, sai shaning take. Na Karaso, ya yi kyau mutuka, Kananan kaya ya sa, ya yi …