AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 3 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 3 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI Shi kuwa zama ya yi fuskarsa a daure hankalinta ya tashi, ta yi tsugune a gabansa tace kayi hakuri,adnan wallahi ban taba waya da Sageer ba sai yau, kuma ka san dan’uwana ne” Cikin tsawa ya ce, “Na tsani wannan sunan, na haramta fadarsa a gidan nan matukar kina son zaman lafiya”. Wallahi ba zan Kara ba”Wai me Sageer yake da shi wanda ni bani da shi, ki fada min?”Ta sa hannu ta toshe bakinta saboda kukan da ya cika ta. “Adnan kar muyi haka da kai, ni ba ka sona kar ka cutar dani”.Fada min, me kika ajiye masa?”Na yi tsuru, na ce, “Ba komai”. Ya ce, “Karya kike, yanzu zan karbi ajiyar, in kuma yana son saurana shi kenan”. Tun tana magiya tana tuba har dai ta soma cizo, yakushi, ta hakura ta yi lakwas. A yau ta rasa abin da ta yiwa Sageer tanadi. Shin mene ne rayuwar duniya? Anya kuwa Adan yana da imani? Babu tausayi babu komai ya gurjeni yadda yake so. Bacci sama-sama ta yi sabuda yadda jikinta yake ciwo, tana bude ido suka hada ido, yana z…