AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 3 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 3 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI

 

 

Shi kuwa zama ya yi fuskarsa a daure hankalinta ya tashi, ta yi tsugune a gabansa tace kayi hakuri,adnan wallahi ban taba waya da Sageer ba sai yau, kuma ka san dan’uwana ne” Cikin tsawa ya ce, “Na tsani wannan sunan, na haramta fadarsa a gidan nan matukar kina son zaman lafiya”. Wallahi ba zan Kara ba”Wai me Sageer yake da shi wanda ni bani da shi, ki fada min?”Ta sa hannu ta toshe bakinta saboda kukan da ya cika ta. “Adnan kar muyi haka da kai, ni ba ka sona kar ka cutar dani”.Fada min, me kika ajiye masa?”Na yi tsuru, na ce, “Ba komai”.

Ya ce, “Karya kike, yanzu zan karbi ajiyar, in kuma yana son saurana shi kenan”.

Tun tana magiya tana tuba har dai ta soma cizo, yakushi, ta hakura ta yi lakwas. A yau ta rasa abin da ta yiwa Sageer tanadi. Shin mene ne rayuwar duniya? Anya kuwa Adan yana da imani? Babu tausayi babu komai ya gurjeni yadda yake so.

Bacci sama-sama ta yi sabuda yadda jikinta yake ciwo, tana bude ido suka hada ido, yana zaune bakin gado ya yi zugun. Ta rufe ido, hawaye kuwa suka soma zuba. Nan ya soma shi mata albarka, dan shi a nasa tunani ma tunda tana son Sageer tuni ta ba da kanta a gunsa. Ya yi gyaran murya ya ce,

“Bahiyya, Allah ya miki albarka, Allah ya bani

‘ya’ya masu albarka ta bangaren ki. Ina yi miki addu’ar samun ci gaba a rayuwa, kin sauya min tunani Bahiyya”.Tana son yi masa tsiwa babu bakin yi. Daga shi har ita da zazzabi suka tashi, kasancewar sa dan hutu ga uban cizon da ya sha, shine ya tashi dá zazzabi.Da kansa ya yi mata wanka. Waya ya yi asibitin da yake zuwa likita ya zo ya duba shi. Ya ce, “Ita Bahiyya a turo mace ta duba ta”. Babu dadewa wacce za ta dubata ta zo, nan dai aka duba ta aka ba ta magani. Shi ya fita yayo masu take away, gaba daya rarrashinta yake, saboda taki dena kukan, tunanin rayuwarta ya dawo mata sabuwa.

ASALIN LABARIN

Bahiyya shine sunana, mahaifina shine Alhaji Labaran Maude, mahaifiyata sunanta Hassana da yake ‘yan biyu ce. Cikakken sunana Bahiyya Labaran Maude, mu ‘yan asalin garin Kano ne cikin Karamar hukumar Rogo. Garin Rogo gari ne mai dinbin tarihi, mahaifina su uku mahaifiyarsu ta haifa, da dan’uwansa Idris, sai Kanwarsu Ummu Kultum, wacce ake cewa Kattime.

Asali mahaifina yana zaune a garin Rogo da iyalansa da mahaifiyarsa, tunda kuwa tana raye. To Abba ya bani labarin Kuruciyarsa, dan kusa da gidansu a wancan lokaci yana da aboki wanda tare aka yi musu shayi, kuma sun shaku, ta inda daya in bai ga daya ba hankalinsa zai tashi, tare suka yi makarantar Primary, sai da suka je S.SI suka rabu, saboda Kanin babansa ya dauke shi zuwa Zaria.

Abba shi kadai ya ci gaba, domin rashin amini abokinsa yana matuqar damunsa, rashin Sa’ad abokinsa.

Haka dai har ya kammala Secondary ya tafi jami’ar Maiduguri, ya yi karatun sa har ya yi digiri.

Basu sake haduwa da Sa’ad ba har mahaifina ya auri Ummana, muna zaune lafiya, domin dai za’a samu biyan bukata tunda dai yana aiki.

Kwatsam rannan sai ga Sa’ad yazo murna gurin Abba babu magana, ya shigo da shi gida.

Kakarmu ta yi ta murmar ganinsa. A nan ya sami labarin ashe Sa’ad a waje ya yi karatu, yanzu ma kasuwancinsa ya fi karfi a waje. Nan dai ya nemi mahaifina da suyi joining ya amince, amma da yardar mahaifinsu. A lokacin Idris yana jami’a yana kardatu, ita kuwa Baba Kultum tuni an aurar da ita.

Abu ya yi dadi, ya ja mahaifina zuwa kasuwanci, ya shiga da kafar dama, harka ta bude, ya fi Karfi a Kano.

Nan dai ya tamfatsa masa gida a Nassarawa

G.R.A. Kafin shekara uku labarin Rogo ya yi suna, amma har lokacin Umma bata haifeni ba, ‘yan’uwa dangi suka yo ca kan Abba akan sai ya yi aure. Ya yi amma dai jiya i yau, ganin haka Abba ya tura kaninsa

Idris Maude ya taff OXFORD UNIVERSITY London, shi kuma Abba ya ci gaba da kasuwanci. Alhaji Sa’ad shi kuma ya fi zaman London. Haka dai rayuwa ta juya. Lokacin da Baba Idris ya shekara hudu ya kammala karatunsa lafiya, ya yi waya a tare shi. Business din ya karanta. Umma ta yi shiri sosai na karbar bakon

London, girki iri-iri ta yi masa. Gari na wayewa Abba ya shirya ya tari dan’uwansa, murnar da suka yi ba ta boyuwa, dan ya dawo da sakamako mai kyau.

Ganin kasuwanci Abba Idirsi ya karanta

Abbana ya dorashi ciki, dan yanza Abbana kudinsa yake juyawa. Bayan wata biyu da dawowar Abba Idris, ya yi aure da Momi Bulkisu, dama sun dade suna so juna, dan itama ta yi karatu sosai. Basu dade da aure ba ta haif Muhamad Kabir, wata shekara ta haifi Muhamad Sageer. Umma na ita ta yaye Kabir.

Wata shekarar ta haifi Rayyan, sai da ta yi hudu sannan ta huta, kuma duk Umma ke rainon su, har

lokacin Umma da amaryarta basu hailu ba. Daga karshe Abba Idris ya bawa Umma rikon Sageer.

Sageer dan lelan Umma na son sa da yawa, wanda ba ta boye son sa a ko’ina. Shima kuma baya son ta matsa. Sai da Sager ya shiga Primary 5 aka haifeni, ni Bahiyya iyayena sunyi murna sosai, na zama ‘yar lelan Sageer, baya so ko kuda ya taba ni, na taso cikin gata. Ko da na isa yaye kakarmu Inna ita ta dauke ni, nan kuwa shima Sageer kayansa muka koma bangaren Inna. Ba°a dade da yayeni ha Umma ta sake haihuwa, tun daga nan haihuwa ta bude.

Duk wata dawainiyata Sageer ke yi min, ko makaranta ya je ya dawo sai ya kawo min abin da ya ci ya rago min, ba shi da aikin da ya wuce na sister Bahiyya.

Kiwa’ ce dani babu me daukata sai Ya Sageer, gani irin manyan yaran nan ne, amma haka zai dauke ni. Inna tai ta tausayinsa wai kar ya yi ciwon kirji, amma shi ina sister Bahiyya ce burinsa.

Direban da ya dauko ni daga school ya bude min mota, na yi ciki da flas dina ina kuka. Inna ta fito da gudu saboda sautin kukana, kowa ya kwana ya tashi a gidan babu wanda be sanni akan kukan banza ba, kuma babu me kwadata. Inna na sona, haka Ya Sageer. Shi kuwa Yaya Kabir in ya zo ya ringa zare min ido kenan, wai na fiye shagwaba. Ta kamoni ta rungume, wai me ya dame ki? Na ce,

“Kawai ni bana son school din nan ta su Ya Sageer nake so”. Ta ce, “To za a kai ki yi shiru”.

Wata irin shakuwa muka yi da Yaya Sageer,

wanda ko ciwo daya ya yi tare muke jinyar, muna

son junanmu, tare muke cin abinci, duk inda za mu tare, bani da maganar da ta wuce ta Ya Sagecr.

Na rayu da shakuwar Sageer, da soyayyarsa wacce ina ga tunda nazo duniya da ita na dira.

Dakinsa na nufa, ina shiga dakin na ji sanyin A.C. ga kamshi na tashi. Ina dube-dube tare da kiran

sumansa, “Ya Sageer”. Shura. Ashe yana kwance kan bed ya rufa da bargo sai baccinsa yake, na bude shi na dora hannuna bisa kansa na ce, “Ya Sageer, Inna

ta ce kanka yana ciwo”. Ya ce, “Ya yi sauki, dama na rashinki ne a gidan nan”. Na wangale baki na ce,

“Inna tace makarantar ku zan koma”. Ya ce, “Ko, ai makarantar ma babu mata”. Na ce,Ai sai insa

kayan maza nima in zama namiji”.

Ya Sageer ya ringa dariya ya ce, “To kuma ai ba ki kaini tsaho ba, na ce sai a je a siyo min”. Ya

mike ya ce, “Zo muje wajen Inna mu tambaye ta inda ake sai da girma a siyo miki ko koma ni”.

Muka tafi yana dariya, ni kuma ina murmar za’a siyo min girma. Muna isa falo na fadawa Inna, ta yi

dariya. Ya ce, “‘Shiryata mu fita shan Ice-cream”.

Ta shirya ni, na ci abinci muka tafi wajen Umma. Ta ce,

Shureim Sageer ya ciwon kan?” Ya ce, “Ya warke”. Ta harare ni, “To sarkin shagwada ina za ku?” Na ce,

“Ya Sageer zai kaini shan Ice-cream. Kannena suka ce za su, na rada masa kar muje dasu Abba yana kaisu, kuma kai duk sanda za ka kaini sai ka je dasu.

Na fashe da kuka na ce, “Ba’a zuwa”. Ya sa hannu yana goge min hawaye, ya ce, “Umma gaskiya yau ba zamu dasu ba mun suyo musu”. Umma ta ce, “Ai kuwa ko ba za ta ba sai kakai min yarana”. Suka biyomu ina ta aikin kuka. Ya goge min ido ya ce,

“Muje kar ki damu”.

Sageer mutum ne mai natsuwa, ga ladabi da biyayya, yana da hakuri, dan tunda nake da shi bai tada dukana ba sai dai tsawa. Sageer ya haifu, yana da zumunci bai ware ‘yan gidanmu da ‘yan gidansu.

Umma ita ce uwarsa, da ita yake shawara, rayuwar Yaya Sageer simple ce, bai dauki duniya da fadi ba, yana bani sha’awa.

Sageer bafulatanin asali, iri fulanin garin Rogo.

Dogo sambalele jajer da shi, hancinsa har baka, ba shi da son magana, ga gayu ga tsafta, komai nasa tsaf, har yanzu dana ke baku labari ban dena son

Sageer ba.Na fito daga wanka, dama na yi alwalata, na ta da sallah. Bayan na idar na zauna gaban mirrow na soma shafa mai Lotion Nie, da yake duk collection dina Nive ne. Na kammala na shafa lips tie, nan da

nan labbana suka hau kyalli, na kalli kaina a mirrow na yabawa kyauna, domin a gaskiya ina da kyau sosai. Kallon Kwayar idanuna ma kawai ina ruda mutane, barin in ina tafiya duk ilahirin jikina rawa yake tun ina Karama, Umma har dukana take wai in dena, amma halittace.

Na bude woodrops dina na zabo kayan da za su dace da yanayin, lokacin na shirya tsaf dani, na feshe jikina da turaren nawa A.P rose, na yi kyau. A lokacin ina J.S.S3. Na shiga wajen Ya Sageer, ya ce,

“Sister Bahiyya, sai ina?’ Nace Nazo kiranka kazo  muyi lunch”. Ya ce, “A’a, ni ki zauna a haka inyi ta kallon ki zai fi faranta min rai”. Na zubari baki na zauna, na ce, “Gani nan ka yi ta kallona, in kaga dama

ka hadiye ni karewar kallo”

“Au kin yi fishi ne?” Na ce, “A’a, ni dai yunwa nake ji”. Ya ce, “Jeki ki ci abincin ki”. Na ce, “Na koshi in dai za ka yi fushi ban ci’. Ya ce, “Ni bana fushi da kanwata, taho muje mu ci”.Na zauna kan dinning table dan cin abinci, na soma duddubawa ina cewa,

“Bari muga me aka dafa?” Flas din farko fride rice ce, na duba dayan alkubus ne da miyar agushi, na uku kuma ferfesun yan shila. Na yi mana service, mun ci abinci cikin nutsuwa da kwanciyar hankali. Hannuna dauke da cup ina shan coconut drink, naga Ya Sageer ya Kura min ido na ce, “Wai lafiayarka Kalau kuwa?’ Yace,

Hmmmm