AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 1 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 1 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI Ina shiga cikin marhaba hotel sai naga an turo mutum irin motar nan ta tura marasa lafiya, an rufe shi. Cikin baka ya sani na matsa daga gefe don in basu wajo su shige, cikin tausayi da jimami ina fadin “Allah ya bashi lafiya”. Ashe kallo neya koma sama, domin ba kowa bane akan motar marasa lafiyar ba face mutumin da soyayyarshi take azabtar dani. Sageer!” Na fada ina kallon Kawunmu da yake binsu. Nan da nan ‘yar tawa matsalar da nazo da ita dan ganin likita tuni na neme na na rasa. Cikin Kunan rai nace Shi kenan Sageer, yaji labarin babana ya bada ni za’a aurar dani, don nan da kwana uku ina gidan wani mijin da ban san ko waye ba. A gaskiya ban kyauta ba, ko da yake kunya ce ta hanani in tarbi Sager in fada masa halin da nake ciki, kuma a gaskiya ni bazan iya yiwa mahaifina musu ba, domin ina tausayinsa sosai, bana son duk abin da zai tashi hankalinsa. Hakika ko waye ya ji labarin mahaifina zai tausaya masa. bare ni da nake ganin halin da …