AUREN BIYAN BASHI CHAPTER 1 BY ZAHRA’U BABA YAKASAI
Ina shiga cikin marhaba hotel sai naga an
turo mutum irin motar nan ta tura marasa lafiya, an rufe shi. Cikin baka ya sani na matsa daga
gefe don in basu wajo su shige, cikin tausayi da jimami ina fadin “Allah ya bashi lafiya”.
Ashe kallo neya koma sama, domin ba kowa bane akan motar marasa lafiyar ba face mutumin da soyayyarshi take azabtar dani. Sageer!” Na fada ina kallon Kawunmu da yake binsu. Nan da nan ‘yar tawa matsalar da nazo da ita dan ganin likita tuni na neme na na rasa. Cikin Kunan rai nace Shi kenan Sageer, yaji labarin babana ya bada ni za’a aurar dani, don nan da kwana uku ina gidan wani mijin da ban san ko waye ba.
A gaskiya ban kyauta ba, ko da yake kunya ce ta hanani in tarbi Sager in fada masa halin da nake ciki, kuma a gaskiya ni bazan iya yiwa mahaifina musu ba, domin ina tausayinsa sosai, bana son duk abin da zai tashi hankalinsa. Hakika ko waye ya ji labarin mahaifina zai tausaya masa. bare ni da nake ganin halin da ya shiga, wanda ko da Allah (S.W.T) yana tausayin mai arzikin da Ya samu kansa a halin talauci. Kai soyayya kenan”.Na bi bayan Kawu Aliyu, ina me cewa, “Kawu me Ya sami Sageer?” Cikin jin haushina da tsanata yace,
“Ban sani ba, ko mo ya same shi aike kika jawo masa” Ya ci gaba da fadar maganganu masu ciwo da zafi a gare mu Maganarsa ta Karshe ita ce tafi komai daga min hankali, inda yace Sageer yace. Ba zai yafe miki
Yaudarar da kika yi masa ba, kuma in Allah ya yarda sai Allah ya saka masa Nace, “Kawu ba laifi na bane, ba zan iya musawa mahaifina abin da yake so ba, na zabi son ran mahaifina akan soyuwar zuciyata. Ubangiji Allah ya bawa Sager lafiya, Allah ya ba shi wacce yafi sonta dani, kuma Allah ya hada fuskokinmu da alheri”. Na juyo na tali zuciyata na kuda, ko likitan ban gani ba na koma gida.
“Bahiya, abin da nake so dake yanzu shine, ki bi zabin mahaifinki kamar yadda tun farko kika nuna amincewarki, amma yanzu kin shiga damuwa wanda in mahaifinki yaji ba zai ji dadi ba, kinga sai sa miki albarka yake. Haba Bahiya, ya za ki zama uwa ta gari in kinki yin biyayya?”
“Ummana”. Bahiya ta kalli mahaifiyarta tace
“Umma ina mai farin cikin sanar dake, a shirye nake da in faranta muku matukar yin hakan bai sabawa addini ba. kuma ko yin hakan zai rabani da farin cikina”. Ta sa hannu ta share hawayenta, tace, “Umma, Bahiya tafi son ku da kanta, ina son in zama ‘ya ta gari kamar yadda
Qannena za suyi koyi dani”.
Umma ma kuka take, domin a matsayinta na uwa ta san nayi biyayya ne kawai, kuma tasan boye damuwata nake domin in faranta musu.
Ban san mijin ba, ban san ko waye ba. Shin waye mijin da babana ya zaba min a matsayina na wacce nayi ilimi da wayewa? uwa uba kyau, wadda nake ganin a duniya ma ina cikin mata masu kyau. dan irinmu ne in mun zo guri ko ‘yan’uwana mata sai na zame musu abar kallo. Kwata-kwata satina biyu da dawowala daga bautar kasa daga jihar Imo, yanzu na san na rabu da Sager ko da wa zan rayu?
Ina zaune Kawata Shukura ta shigo, na kalli
ta kalle ni, tace “Amarsu”. Na yi murmushi, dan bana son ta gane halin da nake ciki, du kuwa da cewa bani da sama da ita. Ta ce, “Ni dai Bahiya rowar angon kike min”. Nace Au har yanzu baku hadu ba?”
Ta harare ni, “Mun hadu mana tunda kin kawo shi”
“Ki yi hakuri za ki ganshi”
“Wai shirye-shiryen yaushe za mu soma, fa ko rabo ba muyi ba jibi kamu”
Na ce, “Ba wani taro za’ayi ba, saboda kin san halin rayuwa
“Allah sai munyi”. Ta fito da I.V tace, “Ni rabo zan soma, bani bukatar komai maki duk Mamyna ta dau nauyi
Na kalli Shukura na bude baki, dole na yi mata godiya. Ranar muka yi rabo, wasu kuma waya muka yi musu. Biki kam ya kankama, abubuwan da Shukura ta yi min yana da yawa, anyi biki na birgewa. Abuja aka dauki amarya dan kaita, amma har yanzu tunanin halin da Sageer yake ciki take, sai dai ta mahaifinta yafi na kowa.
Washe garin kaita kowa ya watse, aka barta ita kadai a gidan, ga girma ga gidan ya hadu. Tana zaune falo ta ga wani mutum ya fito daga wata hanya wace bata ma kula da ita ba, dan bata yawata ko ina ba a gidan ba.
irin mutanan nan ne masu fadin rai da ji da kai da isa.
Ya kalle ta ya watsar kamar ya ga kashi, ya ce, “Ke ba kiga mutum ya shigo bane?” Ta kalle shi da tsumammun idanunta masu tsuma ‘yan maza. Tace, “Ka yi sallama ne kona san waye kai?’ Yace, Kai! Ba ki sanni ba? To ba kowa bane ni sai mijinki. Ko da yake haka naji ance ke matata ce, sai dai ina takaicin sanar dake kin shigo kurkuku, kamar yadda kika sa aka rabani da farin cikina,
kema kin yi bankwana da farin ciki. Banza kawai!”
Kallon sa kawai take, dan tana mamakin shi
wannan wane irin mutum ne wanda bai san mutunci ba? Haushi ya kamata, ta mike tayi masa tsaki.
Ji ta yi an kamo jelar gashinta ya nade hannunsa,
cikin zare ido ya ce, “Ko ubanki bai isa yayi min tsaki ba bare ke, ko kin san matsayin aurenki? To in ba ki l sani ba ki sani ba, bashi mahaifina yake bin ubanki ya kasa biya shine ya nace akan ya aurar dake a bakacin kudin, tausayin ubanki ya sa mahaifina ya amince. Amma kece silar yankewar cikar burina. Bush girl!” Jan gashin yake cikin Karfinsa har sai data saki fitsari saboda zali. Ya ringa dariya yana cewa, “Banza!”
Yana sakinta tayi wajenta ta haye sama zuwa bed
room dinta tana kuka. Auren Biyan Bashi aka yi da ita.
To me ya sa babanta bai fada mata ba’? Ai da ya barta ta nemi aiki Kila ta iya fansar kanta. Kai wannan mutumin mugu ne. A nan ta yini a kwance, sai da yunwa ta ishela ta tashi ta shiga kicin ta soma girki, komai da akwai, saboda haka girdki ta shirya.
Tana falo tana ci ya shigo yana harare-harare, ta basar. Ya ce, “Ina abincina?’Ni ban girka da kai ba”
“Kai! Ba ki girka dani ba’ ubanki ya kawo mana
abincin?” “Wai kai bakinka baya hutawa da zagin babba ne? Ka daina zagar min uba, domin Karshe in soma zagin naka uban” Ya ce, “Kai!”
Ta ce, “Ya ka gani, uba ya fi uba ne?”
Ya ce, “Wallahi duk randa kika yi gigin yin haka jiki zai tsami” Ta ce, “To nima ba zan juri zagin iyaye ba, dan ni ina girmama iyayena
Sallama ta katse su, ta juyo taga wani aminin mahaifinta ne wanda ba bakon ganinta ba ne da shi da matarsa. “Lah, Mamee sannu da zuwa”. Ta ce, “Yauwa Bahiyya”. Ta mike da sauri ta cika su da kayan cima, ta durkusa har Kasa tana gaida su.
Alhaji Sa’ad ya ce, “Adan ba dai ba ka fada mata zuwanmu ba?” Cikin shagwada ya ce, “Na fada mata”
Na kalle shi, ko kunyar Karya bai ji ba.
Hira sosai suka yi da mahaifinsa, ya yi tayi mana nasiha da muyi zaman lafiya, ya yi min alheri me yawa.
Har mota na raka su.
Kwata-kwata satinta biyu ta fuskanci halayyar
Adnan, mutum ne me shegiyar mita, dan abu kadan zaka yi ya yi ta fada a gidan nan, dole da na ji ya soma zan gudu dakina. In nayi shiru ya ce ina ji yana magana dan raini, idan na tanka kuwa abin ba zai yi kyau ba.Wata ramar lahadi suka shigo da ‘abokansa falo, ni kuma ina kicin ina ‘yan hidimomina, riga da siker ne na atamfa a jikina, sun karben sosai, atamfar fara ce me blue din ganye, na yi kyau sosai. Na fito da niyyar shirya tebir na ga Karti a falo, na zagaye su na shige. Na juyo daya daga cikinsu yace Amarya ba magana” Nace Sannun ku”
Adnan ya bata fuska, na kawo ruwa da lemo na kawo musu. A kicin ya ritsani, ya sami kunnena ya ja,
“Ba ki da hankali za kije gurin Karti a haka?” Ta ce,
“Ban san dasu a lfalon ba, laifinka ne Adnan, ya za ka shigo dasu babu Sanarwa?” Kuma, sai ya sake ni, “haka ne”. Ya juya. Ina zaune a kicin na yi tsuru ina tunanin A Inan, wani irin bahagon mutum.Sai dana dena jin motsinsu na fito na gyara falona.
Adnam bai taba shiga dakina ba, nima ban taba shiga nasa ba. A kwance yake a falo nima ina zaune, waya tayi Kara ya dauka.
“Sweet heart na kira na ji layinki a kashe”. Ban san me aka ce ba,naga ya zabura “Da gaske?” Ya mike.
Nima kicin na shiga ina ta hidimata, dan ina son girki sosai, in zauna inta girkina kala-kala.
Shima Adnan saiya abincina, kuma mutum ne mai sakin hannu baya kyautar kasa da dubu dari, dan zuwa yanzu na yiwa iyayena aike kusan sau uku, duk kowa da cewar .
Adnan ya dena shigowa da abokan sa nan falon, sai dai ya kai su wani falon.•
Na kammala abinci, naje nayi wanka nasa English wears masu kyau riga da siket na tumke gashin kuma, na yi kwance a falo. Sallama na ji, su Jamila ne kannen Adan, daria na sa da zuwan su, na, tare su.
Jamila ta kalle ni tace, “An taba gaya miki ke me kyau ce Na yi murmushi nace, “Tun ina Karama na san haka”
Hmmmm