MUSABBABI CHAPTER 9 BY HAJ HABIBA
MUSABBABI CHAPTER 9 BY HAJ HABIBA kyakkyawar kulawa da take samu daga gare shi, wannan lamari ya fi komai tayar ma da Hajiya Kilishi hankali. Musammam da ta fuskanci da gaske Harira ciki, gareta don haka ta ci-gaba da asarar kudinta a wajen Malamai, domin a lalata cikin Harirah. Amma ina. Alkawarin Allah baya tashi. Komai tayi a banza, cikin Harirah ya ci-gaba da girma da kuma samun kulawa. Har zuwa lokacin da ya isa haihuwa. Da yake Allah ya riga ya rubuta Harirah ba za ta rayu da danta ba, ya sa tana haihuwar dan. Allah yana daukar ranta, ga koshi, ga kwanan yunwa kenan! Alhaji Mansur na murnar samun abinda ya dade yana addu’ar samu, ga, tashin hankalin rashin matarsa, uwar dansa daya tilo daya fara samu. Wacce yake sa ran za ta kula masa da dansa har girmansa. Ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa, ba Harirah ta so ta rasu ba, dan ta so ya rasu, domin tana ganin shi ne bala’ inta, don haka don Harirah ta rasu, ai ta barta da bala’i. Wato kashe an maciji kenan, ba a sare kan ba. Rasuwarta ba wata f…