MUSABBABI CHAPTER 9 BY HAJ HABIBA
kyakkyawar kulawa da take samu daga gare shi, wannan lamari ya fi komai tayar ma da Hajiya Kilishi hankali.
Musammam da ta fuskanci da gaske Harira ciki, gareta don haka ta ci-gaba da asarar kudinta a wajen Malamai, domin a lalata cikin Harirah.
Amma ina. Alkawarin Allah baya tashi. Komai tayi a banza, cikin Harirah ya ci-gaba da girma da kuma samun kulawa.
Har zuwa lokacin da ya isa haihuwa. Da yake
Allah ya riga ya rubuta Harirah ba za ta rayu da danta ba, ya sa tana haihuwar dan. Allah yana daukar ranta, ga koshi, ga kwanan yunwa kenan!
Alhaji Mansur na murnar samun abinda ya dade yana addu’ar samu, ga, tashin hankalin rashin matarsa, uwar dansa daya tilo daya fara samu.
Wacce yake sa ran za ta kula masa da dansa har girmansa.
Ta bangaren Hajiya Kilishi kuwa, ba Harirah ta so ta rasu ba, dan ta so ya rasu, domin tana ganin shi ne bala’ inta, don haka don Harirah ta rasu, ai ta barta da bala’i.
Wato kashe an maciji kenan, ba a sare kan ba.
Rasuwarta ba wata fa’ida ita a gareta, gaba daya tsanar dan da Harirah ta haifa ya gama ratsa jinin jikin Hajiya Kilishi, ko kadan ba ta kaunarsa.
Hankalin *yan-uwan. Harirah da na Alhaji Mansur ya fi na kowa tashi, a dalilin rasuwar Harirah, ga sankacecen da ta bari, tunaninsu daya.
Waye zai iya daukar Musaddik ya raine shi? Inna Halima wacce ita ke bin Harirah a haihuwa, da yake kuma shekarunsu ba wani tazara bane sosai, ya sa tare aka yi masu aure.
Inna Halima kuma ta rigata haihuwa da makwanni hudu, danta ita ma namiji ne, mai suna Abdullahi, don haka ta roki Alhaji Mansur daya ba ta Musaddik ta ‘hada da Abdullabi ta shayar da su.
Alhaji Mansur ya yi farin-ciki matuka, ya kuma sami dimbim natsuwa ya kuma kalli inna Halima a matsavin maganin matsalarsa, kuma mai.
• taimaka masa akan gudan jininsa Musaddik dan da yake jin kamar ba shi da kowa duk duniya.
Sai shi. Dan da yake jinsa har cikin jinin jikinsa, wannan shi ne dalilin da ya sa Inna Halima ta dauki Musaddik ta hada shi da danta da ta haifa.
Wanda ba haka Hajiya Kilishi ta so ba, ta so Musaddik a bar shi ya tagayyara ne, ga rashin nono, ga rashin uwa, har shi ma ya bi uwar ta sa, amma sai ga shi ya sami wata uwar wacce take da tabbacin za ta kula da shi, kamar yadda mahaifiyarsa za ta kula da shi, koma fiye. Bayan ‘yan watanni, lamarin ya fara kwanta ma Hajiya Kilishi, musamman da yake ba ganin Musaddik take ba, ta kuma mallaki hankalin mijinta waje daya, domin baya sha’awar ya Kara wani auran. Amma abu daya ya ci-gaba da nukurkusar zuciyar Hajiya Kilishi tare da hanata samun sukuni, shi ne ganin irin yadda Alhaji Mansur yake matukar kulawa da Musaddik.
Domin hatta gadon da zai kwanta, sai da ya saya masa, kaya kuwa na sawa na alfarma yake saya masa, duk wani abu da ake ma da dan gata, to fa shi yake ma Musaddik, kuma kullum kwanan duniya, in dai yana kasar, to duk aikin da ke gabansa, sai ya ture ya je yaga Musaddik sau uku safe rana da daddare, hakan ya sanya shakuwa tsakaninsa da dansa.
Su kansu su Inna Halima rikon Musaddik ya amfanesu sosai, tunda mijinta ba shi da wani karfi, don haka Alhaji Mansur ya dauke shi ya ba shi aiki a daya daga cikin kamfanoninsa, wanda ake yin takalma, sannan kuma shine ya rushe gidansa, ya Kara gina masa sabo dai-dai da rayuwar dansa.
Wannan lamari ya tayar ma da Hajiya Kilishi hankali, dalilin da ya sa kuma kenan ta tsani Inna Halima, domin ta sha nikar gari ta je har gidan ta ci mata mutunci ta kuma kirata da makwadaiciya, tun tana shanyewa har ta gaji, ta gaya ma Alhaji Mansur. Wanda hakan ya yi sanadiyyar da suka sami sabani da Hajiya Kilishi. Ya yi mata kaca-kaca, ya kuma gargadeta da kada, ta Kara taka gidan Inna Halima da sunan cin mutunci, idan kuma ta kara, ta shaida a bakin auranta.
Hakan ya sa dole Hajiya Kilishi ta hakura da zuwa gidan Inna Halima, ba don ta so ba, ko don ta daina jin zafinta ba, sai don tana son igiyar auranta da take tunkaho da shi.
Shekarun Musaddik hudu, ya fara makaranta wacce ta masa sunanta, a lokacin ne kuma Hajiya Kilishi ta fara sa kahon zuka tare da tusa ma Alhaji Mansur son ya amshi Musaddik ya dawo hannunsu.
Amma Alhaji Mansur ya ki daukar hudubarta, domin ya fi kowa sanin halinta, yana da tabbacin
Musaddik ba zai taba jin dadin zama da ita ba.
A haka a daddafe har Musaddik ya kammala firamare, cikin kyakkyawan yabo da sakamako, ga kyakyawar tarbiyyar daya samu daga uwar rikonsa, halinsa na hakuri da son mutane ya Kara taimaka masa wajen cikar kammalar rayuwarsa. Musaddik tun yana yaronsa, kyakyawa ne sosai me cikar kamala, kwarjini ga farin-jini.
•Burin Hajiya Kilishi bai cika ba na raba Inna
Halima da Musaddik har sai da Musaddik ya kai aji hudu na sakandire, sannan Alhaji Mansur da kansa ya zauna da Inna Halima da mijinta Malam Saminu da kuma Malam Mahmud mahaifin Afrah, ya bukaci zai maida rikon dansa hannunsa, ya kuma yi masu godiya a bisa rikon da suka yi ma marayar dansa.
A ranar Inna Halima ta yi kuka har hawayenta suka kare, domin ta shaku da Musaddik tana kuma kaunarsa fiye da ‘ya’ yanta da ta haifa, babu wanda bai tausaya mata ba a cikin wadanda aka yi zaman
da su.
Alhaji Mansur ya ba Inna Halima da mijinta da Malam Mahmud kyautar kujerun makka, tare da kudi masu tsoka, domin ya yi ikirarin ba shi da wanda suka fi masa ‘yan-uwan Harirah.
Domin sune suka taimake shi akan dansa a lokacin da yake bukatar taimako, kuma ba zai taba mantawa da ‘Yar-uwarsu Harirah ba, wacce ta ba shi abinda zuciyarsa ke shaukin samu, ta kuma rasa ranta a dalilin hakan.
Wannan karamci da Alhaji Mansur ya yi masu, ya ba su sha’awa sun kuma yi masa godiya sosai, sai dai kamar yadda Inna Halima ta shiga damuwa akan rabuwa da Musaddik, haka shi ma Musaddik din ya shiga matsananciyar damuwar rabo da Mamansa, ya yi kewarta, ya yi kuka mai tsanani, amma ba shi da yadda zai yi, domin haka
Allah ya kaddara ma rayuwarsa. Komawa da rayuwarsa gidan mahaifinsa ya fuskanci bambanci matuka na kulawar uwa abinda ya saba Inna Halima, na yi masa, da nuna Kauna tausayi da soyayya, sam ba haka ya riska a gidan mahaifinsa ba.
Daga matar ubansa, domin babu abinda yake fuskanta sai tsana da tsangwama daga Hajiya Kilishi. Amma a bayan idon mahafinsa, domin a gaban idonsa, duk duniya babu me kima da mutunci irinsa a gun Hajiya Kilishi.
Hakan ya sa Alhaji Mansur ya sami natsuwa, domin a tunaninsa Hajiya Kilishi ta canja halinta, tana zaune da dansa domin Allah akan mutuntawa.
Shi kam Musaddik masifar tsoron hajiya. Kilishi yake yi, don haka ko a cikin tunaninsa.
Bai taba tunanin ya gaya ma mahaifinsa halin da yake ciki da Hajiya Kilishi ba, sai dai idan abin
-ya dame shi, ya kwaso jiki zuwa gidan Inna Halima da kukansa, yana gaya mata.
Amma ko ta yi kokarin ta je ta gaya ma
Alhaji Mansur, sai Musaddik ya hanata, a cewarsa baya bukatar duk wani abu da zai tayar da hankalin mahaifinsa, don haka idan tana son farin-cikinsa, to kada ta gaya masa komai, har kullum Inna Halima tana sha’ awar halin Musaddik na damuwa da farin-
“cikin wasu fiye da farin-cikinsa.
Haka lamarin ya ci-gaba har zuwa lokacin da
Musaddik ya kammala makarantar sakandire, inda Alhaji Mansur ya yanke shawarar kai Musaddik Kasar waje, domin ya samu Digree dinsa a can.
Tashin hankali!
Hajiya Kilishi ta samu matukar damuwa akan hakan, shin wace irin kulawa ce Musaddik yake samu fiye da ‘ya’yanta, wadanda tuni suna ma aure, ita shi kenan ba ta da wani abu da za’a kyautata masu, kamar yadda Alhaji Mansur yake kyautata ma Musaddik.
Me ya sa ya fi son Musaddik akan kowa? Ko don shine Magajinsa? Ita shi kenan haka za ta tashi a tutar babu? A gaskiya Musaddik ya zamar mata fitina, yanzu har kasar waje zai je ya yi karatu, domin idonsa ya Kara budewa. Ya san yancinsa, ya gagareta ya kuma buwayi rayuwarta. Duk hanyar da za ta bi, don ta kawo cikas akan kai Musaddik kasar waje, ta bi, amma ba ta sami nasara ba. Don tuni Alhaji Mansur. ya samar ma Musaddik (Admission) A jami’a, watau (Oxford University London), haka zalika ba’a dauki wani dogon lokaci ba, aka gama komai. Alhaji Mansur da kansa ya dauki Musaddik zuwa London, bai dawo ba sai da komai ya yi dai-dai. Watau ya tabbatar da Musaddik ya fara shiga aji, sannan ya dawo gida
Najeriya kan kasuwancinsa, a yanzu ji yake ya mallaki komai na duniya, tunda yana da babban da namiji kamar Musaddik, wanda zai iya daukar nauyin
kasuwancinsa, zai iya kula masa da dukiyarsa, shi ya sa yake kokarin ba shi ingantaccen ilimi da zai amfane shi.. Ya kuma amfani rayuwarsa. Baida fargabar komai a yanzu, koda mutuwa ya yi.
A yayin da Hajiya Kilishi kullum take kwana take tashi da tunanin yadda za ta yi da Musaddik, domin ta dauke shi a matsayin shi ne matsalar rayuwarta.
Musaddik ya dage wajen mutunta rayuwarsa a
London, ya rike mutuncinsa, duk wata harka, idan ba ta arziki bace, ba za ka taba ganinsa a ciki ba, ya rike addini da al’ adarsa, abinda ya kai shi, shi yake yi, ya maida hankalinsa sosai wajen karatu, domin ya fuskanci abinda mahaifinsa ya fi bukata kenan.
Don haka ba zai taba ba shi kunya ba, zai tsaya ya yi abinda ya kamata. Dalilin hakan Musaddik sai da ya zama (Best Student), cikin haka har ya kammala Digree dinsa, ya kuma dora Masters dinsa, sau uku kawai ya taba dawowa Najeriya.
Sai dai Alhaji Mansur da yake Kokarin ziyartarsa akai-akai, har ya kammala Masters dinsa ya tattaro ya dawo gida Najeriya, ya zama nagartaccen Magidanci me kwarjini da cikar kamala, me kyakkyawan hali, abin koya ga al’ umma. Dawowar Musaddik Najeriya bayan kammala karatunsa. Alhaji Mansur ya sami cikar burinsa, gaba daya ya ji ya gama mallakar duk wata Ni’ ima ta duniya, mako uku da dawowarsa.
Aka yi gagarumin bikin ba shi kamfanin yin siminti na Alhaji Mansur daya mallaka masa, ya kuma mallaka masa katafaren gida, da mota. Amma wannan karon sai da Hajiya Kilishi ta yi bore akan ba za ta taba yarda da wannan hukuncin ba.
Domin ita ma ‘ya’yanta da ta haifa ai ‘ya’ ya ne, ganin yadda ta tada hankalinta, ya sa akan dole ya sai ma ‘ya yanta motocin hawa, duk da suna gidan mazajensu, hakan ne kawai ta sassauta mata damuwar da take ciki.
Sai dai tana ganin lokaci yayi da za ta dauki kwakkwaran mataki akan Musaddik. A lokacin ne kuma Alhaji Mansur ya bukaci Musaddik ya fito da mata, ya yi masa aure.
Domin cikar kammalarsa, domin duk a rayuwarsa abinda ya rage ya yi masa kenan, ya cikasa rayuwar dansa, shi kam! Musaddik ba shi da wata mace da yake so, asalima shi bai tada tsayawa ya yi soyayya da ko wace mace ba.
Ko da ya je gidan Inna Halima ya gaya mata abinda mahaifinsa ya umarce shi da yi, shawara kawai ta ba shi akan ya tsaya ya nemo ma ‘ya yansa uwa ta-gari, don haka ya yi taka-tsantsan! Wajen samun matar aure. Domin zai iya yiwuwa macen ta so shi domin abinda ya mallaka ko don gidan daya fito ko don kyau da cikar kamalarsa. Tabbas! Maganar Inna Halima gaskiya ce. Ya zamar masa dole ya tsaya ya nemi abokiyar rayuwa ta-gari.
A yayin da gefe daya Mama Hauwa ta fara yi ma Malam Mahmud maganar mai zai hana Musaddik ya zo ya nemi ‘yarsu Sakina, ayi tuwona maina.
Malam Mahmud nan da nan ya gargadeta akan kada ta fito da maitarta a fili, idan Musaddik yana son Sakina, da kansa zai furta. Tunda ai gidan ba bakonsa bane, yana zuwa yana kuma ganinta.
Don haka idan yana sonta, ba sai an yi masa magana ba, da kansa zai furta, hakan tasa dole Mama Hauwa ta yi shiru da maganar. Sai dai ta dora Sakina a hanyar ta dinga nuna ma Musaddik so da kulawa a duk sanda ya zo gidan, har ya fahimta.
Amma abinda Mama Hauwa ba ta sani ba, shi ne tuni Hajiya Kilishi ta gama shirinta tsaf akan kokarinta na farko na wajen ganin ta tarwatsa rayuwar Musaddik.
Ta yi tunanin had auran Musaddik da ‘yar. Kanwarta Hannatu da suke zaune a birnin tarayya Abuja, ta bukaci ta dawo nan Minna gunta da zama, tunda ta gama makaranta zaman banza take yi kawai.
Hmmmm